Reading KARFE A WUTA Chapter 46 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita daga kaina, na je na gaya wa anty, wai wallahi na ?aga maganar nan, sai ta yi mini Allah ya isa, wai zan saka ayi mata dariya, na zama kamar hoto a wurinsa, ko ?an abun ?okin nan na amarci, duk fa ban san su ba. Ke da ki ka auri wanda ake yi wa kallon sai a hankali, babu imani da tausyai a zuciyarsa kalli abun da yake yi miki fa. Ni dai dan Allah idna wani malamin ne da ke, ki ha?a ni da shi"

Cikin damuwa jauhar ta ce "Yaya hafsa ni wallahi ban san in da ake ganinsu ba ma, canza mutum daga wani abu da baka so zuwa wani, ba abu ne mai sau?i ba. Kin san ni irin wahala da gwagwarmayar da na sha kafin mu zo wannan matakin kuwa?
Da fari nima damun kaina na din ga yi, daga baya na kama addu'a babu dare babu rana, na ha?a da biyyaya da kuma ha?uri.
Master mutum ne, kallon da mutane suke yi masa daban, wanda nake yi masa daban, biyayya da addu'a ne suka canza mini shi. Alkhairin da yake yi mini nake kalla kullum, nake yi wa laifukansa uzuri, har gara ke kina da uwa a raye, ni daga ni sai Allah, da na san bani da wata mafita, na bi abun da ?addara ta za?a mini, na rungumi abuna hannu bibbiyu. Kuma Allah ya shiga lamarina Alhamdilillah, mijina talaka ne, amma ba kowace mace take da ikon da nake da shi a gidan aurena ba. A zahiri shi nake bawa girman, shi ne jagoran amma a ba?ini ni ce sitiyarin rayuwarsa, ina fatan kasancewa da shi har aljanna. Ke ma ki nutsu ki gano menene kurakuranki, sai ki gyara".

"Ba wani kuskure, ina kyautata zaton asri aka yi mini wallahi "

"A'a yaya hafsa, ki daina fa?ar haka, ki mi?a wa Allah lamuranki, wallahi zaki ga canji "

Duk yadda jauhar ta so nusar da Hafsa muhimmancin ha?uri da juriya, da dagewa a kan addu'a amma ta?i ganewa kuma ta?i yadda.

Zuwa azahar ta tafi, ta yi wa jauhar uban farfesun kaji, da abinci, ta kuma ajiye mata ku?i ta tafi.

Har a lokacin ba ta yadda har da hakkin jauhar a abun da yake faruwa da ita ba.

Al'amin ne zaune a gaban Abbu, tun da ya gaishe shi, yayi shiru.

Abbu ya ce "Ya jikin 'ya ta?"

"Da sau?i"

Abbu ya ce "To Alhamdilillah yarinyar kirki, 'yar aljanna Allah ya ?ara mata lafiya, matso ka ha?a shayi ga kayan breakfast nan"

Sai da Al'amin ya kalli Abbu, ya girgiza kai ya ce "Na ?oshi"

"Too, yau kai ne ka ?oshi da abinci kuma?"

Ya bashi amsa da "Eh na ci a gida"

Abbu ya yi murmushi ya ce "Na manta ne, ashe fa magidanci ne, ya aka yi?".

"Sonake a sayar da gadona, zan ja jari, sana'oin da nake yi, ba sa iya ri?e mu sosai, gashi ina so ta koma makaranta, babu isasshen ku?i a hannuna.
Sai kuma ina son ka bani full adress ?in hajiya, zan kaita ta gaisheta ta matsa a kan haka"

Abbu yayi shiru yana ?arewa Al'amin kallo, duk ya ?an yi sanyi daga wani rashin mutuncin, babu uwar sumar da yake tarawa da faratan da yake bari za?o-za?o, gashi yadi ne a jikin sa sa?anin da, da idan bai ga dama ba da 3quater yake yawo da shirt damatsansa a waje, ya wani nutsu sosai.
Abunka da uba da ?a, wani irin shau?i ya ji yana kama shi, a yadda ya ga tarin sauye-sauye a tattare da Al'amin.

"Kai amma 'yar nan tawa ta kyauta, amma wace sana'ar zaka yi?"

Al'amin ya ce "Da wurin buga bulo nake so, ko wurin yin buredi, amma ban gaya mata ba tukuna, ban sani ba ko tana da wata shawarar"

Abbu ya numfasa ya ce "Kana ji na Al'amin, tsawon shekarun nan, filayenka sun yi daraja sosai da sosai, idan ka bari suka ?ara kwana biyu sai sun fi haka sosai. Ka je ka rubuto business plan ?in ka kawo mini, tare da list ?in abun da za ayi mata na makarantar, sai na baka ku?in, idan Allah ya dafa maka, aka samu cigaba, sai a sayar da ko gona ce a garinsu a ?ara, ka san kana da wasu kadarorin a tofa"

Al'amin ya ce "A'a ni ba na son ka yi mini abu, daga baya azo a saka ka din ga yi mini gori, kawai dai a bani wanda na san nawa ne, kuma ma ni na fi son registration nayi mata da ku?ina da kaina, sai na fi alfahari da haka"

Abbu ya ce "Gaskiya ne, kamar ba a nan ka zauna kana ce mini, ba ka son auren ba"

Al'amin yayi shiru yana basarwa.

"Ka rubuto business plan ka kawo mini, zan san abun yi, ka je ku yi shawarar ina jiranka.

Gaba ?aya haushi ya cika Al'amin, kawai ya ji ba shi ne ba zai yi ba, ya ce "Ina ne gidan hajiya a tofa"

Abbu ya kwatanta masa, ya tashi ya fita.

A waje suka yi karo da Rahila, bai ko kalli in da take ba ya fice.

Ta shiga gidan da sauri, ta samu Abbu "Yanzu na ga Aminu ya fita, Allah ya sa ba wani abun ya aikata ba?"

Abbu yayi murmushi ya ce "Al'amin ai rigima ta ragu yanzu, duk da wata rigimar ya zo yayi mini ya tafi. Wai gadonsa yake son a bashi, saboda yayi sana'a ya kula da matarsa" gabanta ya fa?i, ?an kuwa ba ?aramin harin filayen nan take yi ba, manyan filaye ne awon gwamanti ga gidaje guda uku. Ko da Abbu ya samu karayar arziki bai ta?awa Al'amin su ba.

"Wace irin sana'a kuma, wallahi kar a sayar, ba shi da shi a ina ya samu ku?in sayen leshin dubu tamanin ya bata ta saka, kalli a asibitin da ta kwanta fa na ku?i, kalli uban kaji da naman da aka kawo gidan nan da salla, duk ba shi da ku?in yayi haka? Ni ban ta?a zaton zai iya zama soko har haka ba a kan mace wallahi, yanzu saboda kula da itan ne za a sayar da wannan wuraren?"

Abbu ya ce "Ba dai nasa bane ba, shi ya ga zai iya ai"

Jauhar ta lalla?a ta cigaba da sana'oin ta, yanzu tana iya aikace-aikacen ta, ta gama aikin, ta idar da sallar magariba, ta ji bugunsa.

Ta bu?e ta kalle shi, ta ce "Malam lafiya ka ke yi wa mutane wannan bugun haka?"

"Zance na zo"

"A me ka zo"

Ya ce "?afata"

Ta ce "Ko keke ba ka da shi ma?" Ta fito ta zauna a kusa da shi, a kan barandar gidan malam lawan ta ce "To me ka kawo mini "

Ya ajiye ba?ar leda ya ce "Gata nan gya?a ce marau, suyar yau mai zafi"

"Ka rasa me zaka kawo mini sai gya?a, anya ka na so na din ga fitowa zancen nan" ya saka hannu zai ?auke ledar, ta riga shi ?aukewa ta ce "Allah ya shiryeka, Allah master da da kanka a ka bari ka samo matar aure, za a sha wahala kan ka samu"

"In ji wa? Farinjini fa zan yi "

"A hakan kana muzurai da zare idon? Kan na saba da kai fa na da?e, tsoro ka ke bani da sosai "

Ya ce "To yanzu fa?"

"You are my best friend ever, sau?in kai ne da kai fiye da yadda ka ke tunani, miskilanci ne kawai matsalarka wuyatta na dafa abinci mai da?i shikenan an wuce wurin "

Suka kwashe da dariya tare, a kan barandar gidan, suka cigaba da hira, suna cin gya?a, kasancewar a cikin duhu ne, babu wuta, yake ba gaya mata yadda suka yi da Abbu.

"To yanzu wanne zaka yi a ciki, wace sana'ar zaka yi?"

Ya ce "Rabu da shi, idan muka je ?auye zan saka a nuna mini gonakin, a sayar da wata na kar?o ku?ina"

"A'a kar ka yi haka master "

"Haka fa za a yi, wallahi ba zai taimaka mini ba muddin shegiyar matar nan ta sani, ban da ina duba darajar amintar da suka yi da marigayiyya, wallahi da sai na tsinke mata laka"

"A'uzibillah, wannan wace irin magana ce?"

"Mu bar wannan maganar, ?aukko key ki rufo gidan mu fita yawo " ta ce to.

Ta rufe gida, ya goya ta a babur, suka tafi ya din ga zaga gari da ita, ya kaita gidan su, ya ce ta shiga ta gaisa da baba mintuna goma ta fito, saboda ya lura shi ne kullum yake kiranta a waya, yana tambayarta ya jiki.

Baba ya din ga murna, ganin ta warware, baba da kansa ya rakota, suka gaisa da Al'amin, ya yi ta yi musu fatan alkhairi, da fatan samun wani rabon mai amfani jauhar ta yi shiru, shi kuwa ya amsa da Amin.

Ba su da wurin zuwa, ya cigaba da zagaye da ita, suna tafe suna shan iska, ya saya mata kayan ciye-ciye, su rake, awara, dafaffen ?wai kasancewar dama ba iya cin abinci take yi ba.

Har wurin sha daya sannan suka koma gida, ya ci abinci.

Ganin yana ta kaiwa da komowa tsakanin falo da tsakar gida, bayan sun yi shirin kwanciya, ya sanya ta gane shaye-shaye yake son yi.

Ta kalleshi ta ce "Master ka je ka sha, amma ka?an dan Allah, ba da yawa ba, kar ka bugu" ya ce "To"

Ya fita tsakar gida yayi abun sa ya gama, tana jin sa ya shiga ?akinsa yana wanka, ya fito ya saka turare ya nufo ?akinta, duk da yana ?an warin sama-sama amma ?amshin turaren ya hana warin yin tasiri.

"Ba ki yi bacci ba?"

Ta ce "Ban yi ba jiranka nake, na san ko na yi sai ka tashe ni"

"Allah sarki madarata" yayi maganar yana rungumeta, ya kwanta da ita a jikinsa.

"Wace sana'ar ki ke ganin zan fara?"

"Ka yi tunanin ko kala uku ce, sai mu yi addu'a Allah ya za?a mana mafi alkhairi "

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Babu laifi"

"Masterna, kai za?in Allah ne a gare ni, na gode Allah da bai sanya ni cikin masu yi masa butulci ba".

Ya ce "Ni ?in?"

Ta jinjina masa kai. Nan ta bashi labarin hafsa, ya ce "Allah ya ?ara, alhakinki ne ai, daga har ke turin jeka ka mutu suka yi mana mussaman ke, Allah ya ?ara"

"Master yayata ce fa"

"Koma wacece, ai Allah ba ya barin zalunci".

"Duk da haka master"

"Ni yanzu dan Allah da gaske kina jin da?i rayuwar da muke yi a haka?"

Ta ce "Gaya mini matar da aka ta?a goyawa a tarihi, aka yi tafiyar da aka yi da ita a baya, saboda ba ta da lafiya? Gaya mini matar talakan da ake ajiyewa masu kula da ita? abubuwa da dama da mata suka rasa a gidan aure ni na samu".

"To ai wannan duk ba wani abu bane ba a kan wanda ki ka din ga yi mini, dan Allah kina jin da?in zamanmu a haka? Just recently kin kusa rasa ranki saboda ni?"

Ta ce "Ba laifinka bane ba ai" ya yi murmushi cikin jin nisha?i, yake ?o?arin canza hirar zuwa wani abu daban".

"Master"

"Mmm"

"Ban ta?a jin ka ce kana so na ba, ko dai kara kawai ka ke yi mini, saboda halaccin da kake i?irarin na yi maka?"

"Nima baki ta?a gaya mini ba, kuma ina yi a aikace ai, ba dan haka ba, babu wanda ya isa ya saka na zauna da ke ai".

Tana dariya ta ce "Sai abinci"

"Ki kiyayeni da abincin nan, kina takura mini fa"

Ta shafa bayansa cikin shagwa?a ta ce "Ba ka ce ba"

"Me?"

"Ka na so na"

"Yanzu dai jirani tukuna, na gama caji, koma menene ya biyo baya".

"Ba zaka yi cajin ba, sai ka gaya mini"

"Yanzu na tashi na yi waje, zan je na yi wanda na saba, na manta komai, yanzu za?i ?aya"

"Ni zaka yi wa wayo ko?"

"A'a ba wayo zan yi miki ba, za?i na baki".

Da safe jauhar ta fito falo, ta tarar da Al'amin a kan kujera, ta ce "Master da me ka yi wanka ne a ban?akina?"

"Sabulu"

"Wanne?"

"To ai abubuwan naki ne da yawa, kuma kina bacci kawai na ?auki na wata roba, na zuba a soso"

"Master feminine wash ne fa"

Ya kalleta ya ce "Me ke nan?"

"Abun kama ruwa ne, dan Allah yayi kama da abun wanka?"

Al'amin ya ce "Kai, wallahi tsirfarki tayi yawa, kama ruwan ma, sai an yi masa wani abu, to sai ki din ga rubutawa a jikin robar"

Cikin shagwa?a ta ce "Gaskiya sai ka saya mini wani, dubu uku fa na saya".

"Iyee dubu uku, ke fa wasu lokutan kin iya damfara, dubu uku, wannan abun ne dubu uku, car wash ne fa"

"Morning fresh ne, wai car wash kuma yasin sai ka biya ni, ina jin da?in amfani da abuna fa, kai da ba a gyarawa ka din ga lalla?owa"

"A daina gyarawar, a bar mini abuna a haka, ko kuma ki kar?i car wash"

"Sai fa ka biyani, wuyatta na soya maka wainar fulawa da zo?o mai sanyi, sai ka zazzage mini komai na aljihunka"

"Ai dama kin saba cin zalina, ki kwashe mini ku?i"
***
Tun sassafe jauhar ta shirya, kasancewar yau za su tafi tofa, gidan Hajiya, duk da ya ce wuni kawai za su yi da yamma su dawo gida, ba ta damu da hakan ba, tun da dai ya amince za su je ?in.

Ta zata tafiyar mai nisa ce sosai ma, sai dai ba su da?e ba suka isa garin, kwatancen babu wahala, suka isa har gidan Hajiya.

Da ta amsa sallamar su ba ta gane su ba, sai daga baya ta gane Al'amin.

Cikin hanzari ta tashi tana yi musu sannu da zuwa.

"Al'amin, dama zaka tako ka zo in da nake?"

"Tun da ke kin watsar da ni ko?"

Ta ce "Ba haka bane, ku shigo"

"Amarya, ki yi ha?uri ban sake zuwa ba, ina ta fama da ciwon ?afa, kuma ina tsoron wula?ancin matar mahaifinka, ko lokacin bikinka, ba ka ga abun da ta din ga yi mana ba, mahaifinka ma haushina yake ji, shiyasa na janye jikina daga gare ku"

Jauhar ta ce "A'a hajiya ki yi ha?uri, ai laifin wani ba ya shafar wani, mu dai zamu din ga zuwa muna neman albarka"

"Allah sarki, aure mai gyara mutum, yanzu a dalilin auren ya sanya ka zo in da nake"

Al'amin ya ce "Eh, ba dan ta matsa ba ba zan zo ba gaskiya, tun da kema ba ?aunata ki ke yi ba".

Jauhar ta ce "Master ya haka kuma?"

"Ba ?arya nayi ba, ki ke zare mini ido"

Sai hajiya ta kama kuka, ta ce "Wallahi da gayya ba zan yi haka ba, ina son 'ya ta ina son ku, amma an yi mini iyaka da ku, kusan kullum sai na yi kukan abun da mahaifinku yayi mini a kanku".

Jauhar ta ce "Dan Allah hajiya ki yi ha?uri, ki yafe musu, ke ce makwafin uwa a wurinsa dan Allah ki daina kallon abun da suka yi miki".

Al'amin ko a jikinsa, dan ita kanta tsohuwar haushinta yake ji, yadda laifin abbu ya shafe su a wurinta.

Daga baya kuma cikin hikima, jauhar ta din ga jan su da hira, kasancewar ranar kasuwar garin take ci, har kasuwa suka je sayen ?wan zabi, Hajiya ta ha?a wa jauhar sha tara ta arziki ta ce ita da jauhar take jikar, shi kuma ya je ya ?arata.

Yayi mata zancen gonakin mahafiyarsa, ta ce masa "Hayarsu ake bayarwa ana noma, duk shekara ana kar?ar ku?in, mahaifinka bai bani damar zama da shi mu yi magana a kan hakkinka ba, amma ku?inka suna nan ana tara su, ?anina ne yake ajiyewa, sai dai ya je Lagos yanzu"

"Idan ya dawo zan dawo nima"

"Allah ya kawo ka lafiya, ku?i ne masu kauri sosai kam".

Sai yamma sosai, sannan suka koma gida.

Ana ta kiran sallar magariba sannan suka shiga gida.

Da daddare har sun yi shirin kwanciya, Anty zakiyya ta kira jauhar a waya, jauhar ta ?aga ta ce "Anty lafiya kuwa?"

"Ban sani ba, wallahi jauhar ba kya tsoron Allah, kina so ki gama da duniya lafiya kuwa?"

Cikin tashin hankali ta ce "Anty me na yi, lafiya?"

"Ban sani ba, yadda mugun abun uwarki ya koma kanta, kema da yardar Allah sai naki ya koma kanki".

"Anty haryanzu baki gaya mini me nayi ba?"

"Asirin da ki ka yi wa hafsa, gashi an dawo da ita gida, tana ta fizge-fizge tana kiran sunanki, wallahi ki gaggauta karya abun da ki ka yi mata, kafin mu gauraya da ni da ke, ba?ar annoba kawai" ta kashe wayar.

Cikin tashin hankali ta fita falo tana kuka, ta ce "Master"

"Yes yaya"

Cikin kuka ta ce "Ka tashi ka kaini gida".

"Meyafaru a gidan?"

"Ka kaini gida kawai, ba zan iya bacci ba, wai an ce ni na yi wa yaya hafsa asiri, wai sai ihu take yi, tana kiran sunana, wallahi ni ban yi mata asiri ba".

Tashi yayi zaune ya ce "In ji uban wa?"

"Anty ce ta kira ni, dan Allah tashi mu je, wallahi ban yi mata komai ba" tayi maganar tana wani irin kuka.

"Na ga alamar sai na taka wa 'yan gidan nan naku burki a kan za?ewar da suke yi, ba Zamu je yanzu ba, sai da safe, zan je ni su yi mini bayani"



Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Cikin kuka ta ce "Ni dai dan Allah ka tashi mu je, kar ayi mini wani sharrin ina zaune ban sani ba, dan Allah ka tashi mu je"

"No ba in da zamu je, sai da safe idan Allah ya kaimu"

Kuka ta din ga yi masa, har sai da ta ?ular da shi, ya daka mata tsawa, ya korata ?aki, daga kuka kuma numfashi ya nemi ya tafi gaba ?aya, sai da ya ?aukkota ya fito da ita tsakar gida, ta kwanta ya din ga yi mata fifita.

Kusan dai ba su yi baccin kirki ba.

Washegari da safe shika?ai ya karya, hankalinta gaba ?aya a tashe yake, ta kasa cin abinci, sai wajen goma sannan ya ?auketa suka tafi gidan.

Ita ta fara shiga gidan da sallama, ba kowa a tsakar gidan, duk sun tafi makaranta yaran gidan.

A ?ofar falon baba tayi sallama, ya amsa mata ta shiga ta tarar da shi a zaune yana dudduba wasu takardu.

"Waliyiyya, lafiya na ganki a yanzu menene?"

Kawai ta je gabansa ta zauna tana kuka, hankali a tashe ya dafa kanta ya ce "Menene? Wani abun ne ya ha?a ki da mijin naki? Wani abun yayi miki?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

Mama ta shigo falon, tayi turus, ganin jauhar a gaban baba tana kuka.

"Ikon Allah, sakinki yayi ne ko wani abun ne ya faru, ki ke wannan uban kukan haka?"

"Yana waje ma"

"Yana waje meyafaru?" Gaba ?aya ta kasa magana.

Ya kalli mama ya ce "Tashi tijjani ko saifu, su je su ce masa ya shigo" mama na fita, ya kalleta ya ce "Gaya mini kafin ta dawo"

Kasa magana ta yi, da ta bu?e baki za ta yi, sai haki.

Mama ta dawo ta zauna, mintuna ka?an Al'amin ya shigo da sallama, sanye da ba?ar jallabiya.

Cikin girmamawa ya gaida baba, amma mama ko kallo ba ta ishe shi ba.

"Malam Al'amin, meyafaru da iyalin naka ne? Ko wani abun ne ya ha?a ku?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, lafiya ?alau nake zaune da ita, dama na rakota mu zo mu ji ba'asin kiran wayar da aka yi mata ne jiya da daddare, da har ya hanata bacci. Bana son ace na yi wani abu na rashin kyautawa, amma zan iya cewa wannan zai iya zama zuwanta gidan nan na ?arshe kuma bana bu?atar kowa ya je in da take, in dai har za a cigaba da tafiya a haka".

Baba ya ce "Duk me ya yi zafi haka? Baka fa?i meyafaru ba"

"Baba kwanaki yayarta ta zo ta dubata, a gidan na fita na bar su ma tare, na manta sunanta, amma wadda ta auri wanda za ta aura da, kwatsam jiya da daddare an kirata a waya, wai waccan ?in an dawo da ita gida babu lafiya, tana ihu tana kiran sunanta wai ta yi mata asiri, kwana tayi tana wannan koke-koken ba ta bari mun yi baccin kirki ba, wane irin asiri ana zaune ?alau?"

Cikin tsananin ?acin rai ya ce "Zakiyyan ce ta kira ki, ta ce kin yi wa hafsan asiri?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya tashi ya fita tsakar gida, yana ?walawa zakiyya kira.

Mama tayi wani irin mugun murmushi, sannan ta maze ta cigaba da sallalami.

Tana mutsutsuka ido ta fito ta ce "Lafiya ka ke yi mini wanan kiran, ka san jiya ba mu yi baccin kirki ba, saboda jikin hafsa".

"Yanzu kin kyauta, abun da ki ka yi?"

"Na me fa?"

"?aukar waya ki kira jauhar, wai ta yi wa hafsa asiri, wannan wace irin magana ce?"

"Amma ai ba ?arya nayi ba, tun da aka kawo ta sunanta kawai take kira ai"

Ihun da hafsa take yi ne ya sanya, suka nufi ?akin gaba ?aya, ciki har da jauhar.

Sai fizge-fizge take yi, tana kiran sunan jauhar.

Jauhar ta ce "Yaya gani nan, kin ganni menene" tana jin muryar jauhar ta hau mi?a mata hannu.

Ta ?arasa ta ce "Gani menene, me ya same ki?"

"Jauhar, ji nake kamar na fita da gudu, ai ke na gaya miki abun da yake damuna, dan Allah ki gaya musu ko zasu yadda, Anty ta?i fahimta ta, ni a kashe auren nan na huta, bana son ku?in, bana son auren. Wallahi jauhar an kai wata guda bana iya bacci saboda ?acin rai kullum sai na sha maganin tari rabin kwalba, nake iya bacci.
Bani da nustuwa, babu walwala da kwanciyar hankali yaya zan yi ne? Ta mallake komai, ban ishe shi kallo ba, yanzu kuma ji nake kamar in fita da gudu, kamar ana yagar naman jikina" tayi maganar tana wani irin kuka mai tare da gunji.

"Yaya hafsa magnin tari ki ke sha dan ki yi bacci, ai ni ba ki gaya mini ba, shaye-shaye fa ki ka fara kenan"

"Ni ki gaya musu a kashe auren nan, ba zan koma ba na gaji" tayi maganar tana buge-buge. Babu kunya Al'amin ya tsallako, ya janye jauhar gefe, saboda kar tayi mata illa.

Asirin da zakiyya take gudun tonuwarsa, ya tonu kowa ya gani.

Baba ya girgiza kai ya ce "Kowa ya sai rariya, ya san za ta zubar da ruwa, ki tsaya a nema mata magani, wannan abun da take yi babu lalallai wani asiri ne, wata?ila shaye-shayen da take yi ne".

"Haba ya zaka ce haka? Wannan surutan da take yi ba fa a hayyacinta take ba, balle a tabattar da abun da ta fa?a gaskiya ne"

Al'amin ya ce "Amma ki ka yadda ita take yi mata asiri, count her of this please, kar a ?ar sakata a wannan maganar"

Baba ya ce "Al'amin kama hannun matarka ku tafi, in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba"

Jauhar kuwa kuka ta din ga yi wiwi, har da ro?on Al'amin ya bari ta zauna, amma ya ?i ya ce sai dai su tafi gida.

Saifu kuwa ya ce "ba dai kuna murna kun cuci marainiya kun aura mata ?an wiwi ba, kun aurawa taku mai ku?i, ai ga reshe nan ya juye da mujiya".

Jauhar har sai da ta ji haushin Al'amin, na hanata zama a wurin 'yar uwatta.

Aka rasa ainihin abun da yake damun hafsa, shaye-shaye ne? Sihirin ne ko aljanu aka kasa gane kanta, wasu lokutan babu magana abinci ma ta?i ci sai kuka, da daddare ta kasa bacci tayi ta koke-koke tana ihu kamar mahaukaciya.

Iyaka Alhaji mu'azzam ya zo dubata, ya zube musu uban ku?i ya tafi.

Jauhar ta samu admission a legal, ta fara karanta shari'a law, indabo ne ya bata scholarship, sauran hidimar makaranta kuwa shi yake yi mata.

Har keken ?inki, ya samo mata a irin wanda Indabo yake cewa zai rabawa mata goma, amma ace an bawa mata ?ari, ya ce ba zai bashi ba, sai idan ya yadda za a ?auki hoton jauhar da keken a saka a social media.

Ya ce babu wanda ya isa ya ?auki hoton matar sa, ya saka a social media, a kan wani keken ?inki kuma sai an bata.

Indabo ya ce wa Al'amin, ya saka yaron da ya ce a samowa aiki a abuja, an samu gurbin direba a wata babbar ma'aikata top 10 na Nigeria, tare da albashi mai tsoka ya ce ya kai takardunsa na sakandare da aka ce yayi.

Guduma bakinsa ya ?i rufuwa, saboda tsantsar farinciki da murna ta gaske, jin zai tafi Abuja aiki, alhalin idan da wanda ya kamata ya tafi, shi oga kwata-kwatan ne.

Mahaifiyar Nura, sai da ta zo tun daga garin da take aure, ta zo ta yi wa Al'amin godiya,

Please Login or Register in order to submit comment