Reading KARFE A WUTA Chapter 33 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da?i?iya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini.
Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ?azafin nan da suka yi mini, na fan?arewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba.
Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ?a da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da da?i master, wata?ila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sau?i". Tana gaya masa ra?a?in abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi.

Ya ce "You are missing her?" Yayi maganar yana kallonta.

Ta jinjina masa kai ta ce "So badly"

"Ki yi mata addu'a" ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka ha?u da wanda ku ke da irin matsala ?aya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ?yaleta.

Duk da kuka take yi, ta fara ?aukarsa a hoto tana murmushi ta ce "Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya ji?an mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu'ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma"

Har cikin ransa ya ji da?in Addu'ar da take yi masa.

Ya kuma amsa da Amin.

"To mun gama ki tafi"

"To me na yi maka ka ke korata?"

Ya ce "Sigari zan sha"

Ta ?ata fuska ta ce "Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da haya?i, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye 'yar madara, yau dai ?aya ayi ha?uri dan Allah a ?aga ?afa kar a sha da sassafen nan" kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta kar?e lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu.

"Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga le?owa saura na ga mutum ya sha wani abu"

Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa.

Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana ?agawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce "Baba na yi waya"

Baba ya ce "Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya"

"Ka hau what's app mu yi video call"

Baba ya ce "To shikenan waliyya" Al'amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi.

"Master, nan ne wurin video call ?in ko?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

Tana kira baba ya ?aga fuskarsa ta Bayyana a screen ?in wayar.

"Baba wayata touch screen ce mai kyau".

Baba yayi dariya ya ce "Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?"

"Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what's app, zan din ga kiran su kuma a waya"

"To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?"

"Master ne ya saya mini" sai kuma ta ce "Au amm maigidan ne ya sai mini"

Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce "Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki ?aya"

"Amin baba" ta kaste wayar.

"Master " ya ?ago ya kalleta.

"Na gode sosai" ya ?an tsuke fuska ya ce "Kin fa?a kin sake, ya isa haka"

"Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole".

Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take ro?on gwamna, sarki da kuma jami'an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ?a da yayi, ya soke shi da wu?a, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ?arfi, tana neman a bi wa ?anta hakkinsa.

Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al'amin, tamkar bai ji me aka fa?a a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ?ururus ?urus ko a jikinsa an mari dutse.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA


Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa????????
Ko kimin mgn ta????????
08093932955




Tunani ya fara yi, ko tana da aljanu ne.

Ganin idan ya ?yaleta, fashe-fashe za ta yi, ya sanya shi takawa ya ri?o hannunta, amma sai ?o?arin fizgewa take yi.

Kasancewar ba ta yi masa wahalar ?auka, ya sanya ya dan?ota kamar kazar cikin akurki, aikuwa ta cigaba da fizge-fizge da ?o?arin ?wacewa, falo ya shiga da ita, ya tattara hannayenta ya ri?e, hakan ya sanya ta kasa cigaba da ?o?arin ?wacewar.

"Meye haka ki ke yi? Kanki ?aya kuwa?"

Kallonta yake yi, har ta fara kuka, shi bai ma san me yayi mata ta aikata hakan ba.

"Me nayi miki ki ke jifana?"

Cikin takaici ta kalleshi ta ce "Meye ma baka yi mini ba, ni bani da wani amfani a wurinka, bani da ikon ro?on alfarmarka, komai ma yi mini ka ke yi, ko yayi mini da?i ko akasin haka, ba ka tausaya mini dama ka tsane ni, so kake yi na mutu ka huta".

"To yanzu kuma me nayi miki?"

"Wu?a fa ka ?auka zaka fita, idan aka yi maka wani abun ko ka yi wani laifin nika?ai nake fama, sai su yaya walid da suke taimaka mini, amma kai gaba ?aya baka tausayina, ba ka tausayin maraicina saboda da ma ba so na ka ke yi ba. Kodayeke ba laifinka bane, tun da sama ta ka aka aura maka ni, bayan an gama ?ata ni a wurinka. Ko hira ba ka yi da ni, in tayi maka magana kayi mini shiru, idan aka ga na mutu kai ne, sai ma na rubuta na bar wasiyya, idan na mutu kai ka ?arasa ni da takaici"

Yayi shiru ta din ga yi, tana fa?a tana kuka, sai da ta gama tsaf, sannan ya mi?e ya ce "Ki kula da abun da na gaya miki, kar ki fita kar ki bar gida a bu?e, idan na yi dare ki kwanta zan hauro".

Ta ?aga idanunta da suka yi ja ta ce "Sai ka fita ko?"

"Ai na ce idan ba zaki iya ba, ki koma gidanku ko ban gaya miki ba?" Tayi shiru ranta na yi mata wani irin zafi, ya fita ya kwashe kwanukan da ta watso waje ya fice.

Unguwar su ya nufa, fa?a ya ha?a ?an unguwarsu, da ?an unguwar su madaki, yaron ya kwaso 'yan daba yaran madaki, sun shiga unguwar su Al'amin su na ta fa?ace-fa?ace.

Yana zuwa chamber su, ya ?aukko wu?a?ensa, ya fita, sai dai da ya je, yaran suka din ga darewa, saboda wanda suka ta?a karo da shi, sun san irin ?arfin da Allah ya yi masa.

Wani yaron madaki ne, da yake ji da tashen balaga da rashin mutunci, ya sha gaban Al'amin yayi yana zage-zage yana ?o?arin saran Al'amin.

Ya jefar da wu?arsa, ya nufi yaron, wanda suka san Al'amin suka din ga ce masa ya gudu, kar ya bari ya kama shi, amma kasancewar ya yi wa wiwinsa ha?in kauri da wata ?waya da suke yi wa la?abi da 'yar fara, ya sanya yake jin kansa a sama, ko barikin sojoji zai iya shiga yayi rashin mutunci.

Duk iya ?o?arin sa ya kasa saran Al'amin, saboda yadda yake da zafin nama, wurin kare saran, wanda idan ba professional athlete ne ba, babu lallai ya iya.

Ya shammaci yaron, ya soka masa ira?i a cinyarsa, a take ya kurma wani uban ihu, liti ne ya karyo kwanar, ri?e da nasa makamin yana ?igar da jini, "Mai zamani yi ha?uri, kar ka karya yaron nan" sai dai bai rufe bakinsa ba, ya ga Al'amin ya fito da dogon harshensa, ya lashi la??ansa na ?asa da su, idan har yayi haka sai aiwatar da muguntar da yayi niyya, kan liti yayi wani yin?uri ya karya ?afar yaron ya watsar da shi yana kururuwa.

"Mai zamani, yanzu zaka sake janyo mana fa?a, madaki zai ce sai ya ?auki fansa, da baka karya shi ba"

Ya ?ago jajayen idanunsa a slow, yayi wa liti wani irin kallo ya ce "Ya zo ya ?auki fansar a kaina, idan ya isa" ya wulwula ira?insa, ya cafe ya yi gaba.

Kai tsaye gidan su ya tafi, da wannan wu?ar tana ?igar da jinin da ya soki yaron nan.

Yana shiga ya wuce falo, sai ganinsa suka yi a tsaye a kansu da makami tsirarsa.

Salati suka fara yi da kururuwa, ya kalle su ?aya bayan ?aya, "Me ya kai ku gidana?" Yayi maganar yana kallon shahida.

Cikin tashin hankali ta ce "Abbu ne ya ce Mu je mu duba matarka".

"Shi ya ce ku je ku gaya mata cewar kangarewa ce ta sanya aka yi aurena da ita? Ku je ku ci zarafinta?"
Cikin tashin hankali shahida ta ce "Ba ni na fa?a ba Amira ce wallahi".

Rahila kuwa hankalinta ya dugunzuma, ta ce "Ka yi wa Allah da ma'aikinsa ka yi ha?uri, dan Allah kar ka yi musu wani abu"

Ai kamar ta tunzura shi, ya saka wu?a a wuyan Amira, "Ya zama na farko ya zama na ?arshe, ayi duk cin kashin da za ayi a kaina, ban da 'yar mutane da ki ka ha?a kai ku ka cutar, idan aka kuma zan yi ?arna, wallahi sai na saka wa mutum ?arfe"

Shahida ce ta iya cewa "In sha Allah ba za a sake ba" yayi ?wafa ya fita.

"Amira kin ga abun da ki ka ja mana ko? Da ya illatamu, da kin cuce mu"

Amira kam kasa magana tayi, sai dafe ?irji tana hakin tsoro.

Al'amin wuni yayi ranar, yana partrol da yaransa a unguwar, saboda kar yaran madaki su zo su afkawa wanda bai ji ba bai gani ba.

Cikin ikon Allah, har dare yaran madakin ba su sake shiga unguwar su Al'amin ba, duk da sun yi artabu sosai da wasu, dan sai da aka yi masa rauni a cikinsa, ya kama hanyar tafiya gida.

Jauhar na falo tana karatun exam, duk da sun kusa kammala jarrabawa.

Ta katangar ya diro kamar ?arawo,s an samu cigaba, yanzu idan ya ga dama ya kan yi salama.
Sallamarsa kawai ta amsa, ba ta sake kula shi ba, ya wuce ?akinsa, mintuna goma amma ba ta biyo shi ba, ya fito ya ce "A kawo mini ruwan zafi zan yi wanka"

Ta tashi ba ta ce komai ba, ta ?aukki flask, aurensa da ita ta saba masa da wanka da ruwan ?umi, sa?anin da da har a kuddudufi wankansa yake yi ya ?ara gaba.
Yanzu kuwa kusan kullum, da an kawo wuta, take dafa ruwan a heater, ta saka a flask.

Ta zo ta ha?a masa ruwan, sai dai ta ga kamar yana ?oye wani abu.

Kawai ta le?a ta ga me yake ?oyewa, yanka ne a gefen cikinsa, ya saka rigarsa yana ?ara goge jinin kasancewar ba mai zurfi bane ba.

"Ka gani ko? Sai da ka je aka yanko ka ko? Abun da nake ta gudu, sai da ka zubar da jini ko, ba za kai daina zuwa wurin da za a cutar da kai ba ko master? Kodayake ma ni abun yake damu, kai ko a jikinka".

"Na ce ya dame ki ne? Ba jikina bane?" Idan ba gizo idonsa yayi masa ba, hararsa ta yi ta fice.

Shi mamaki ma take bashi, tun da ta yi rashin lafiyar nan, take rigima kuma kamar ta rage tsoron sa.

Ya shiga ya yi wanka, ya fito ya tarar da ita da ?an ?aramin kwanon abinci, sai kuma kayan dressing, tun na lokacin da aka yi masa wancan raunin.

Bai kulata ba, ya ja kwanon abincinsa ya cinye, awara ce da miya, ya sha ruwa.

Ita ma ba ta kula shin ba, ta saka auduga da spirit tana goge, kan ciwon, tana gogewa tsigar jikinta na tashi, kamar jikinta take gogewa, shi kuwa kamar dutse latsa wayarsa ma yake yi.

Haushi ya isheta, ta kalleshi ta ce "Wai ba zafi ne?"

"Eh babu, idan ma dirzawa ki ke da ?arfi, dan na ji zafi, ba na ji" ta tashi ta fice fuuu, tana yi masa fatan shiriya a ranta.
Kusan awa ?aya da rabi, ya shigo mata ?aki, ta yi sauri ta tashi zaune, saboda ta san tsiyar da ta aikata masa.

Ya kunna fitila ya hau yi mata bincike a ?aki.

"Me ka ke nema?"

Ya tashi ya nufo ta, ya mi?a mata hannu ya ce "Bani kayana da ki ka sace mini yanzu"

"Ni ba na sata"

Ya ce "To baki nayi ki ka ?auka? Ko kema kin fara sha ne ban sani ba? Kodayeke biri yayi kama da mutum, da ki ka iya kallona ki ka din ga jifana nan gaba ina ga swizaland zaki saka mini ina ga"

"Ni ba na shan komai, kuma ban ?au komai ba".

"Ba ki ?auka ba ya aka yi ki ka san a kan me nake magana?" Tayi shiru ba ta ce komai ba.

Hanka?ata yayi, ya janyo ledar kayan shaye-shayen sa a cikin bargonta.

"Na gaya miki idan kin gaji ba zaki iya zama ba, ban ?aure ki ba, ki ?ara gaba"

A ?ule ta ce "Ka ?aure ni mana, zan tafi ba ka sallame ni bane, ka rubuta ka gani idan ban tafi ba. Tun da baka da tausayi idan ba mutuwa na yi ba hankalinka ba zai kwanta ba" tayi maganar tana sheshshe?ar kuka.

Ya kalleta, gaba ?aya ko fa?an ba ta iya ba, voice ?in ta sam ba na masu fa?a bane, shagwa?a kawai take yi.

Ya ce "Kin yanke hukunci kenan? Ai da kin gaya mini da duk ba a zo nan ba, zan rubuta na baki, dama na gaji".

"Kuma wallahi idan ka yi shaye-shaye kai da Allah"

Bai kulata ba, ya jefo mata kwalin sabuwar waya gal, ya ce "Gashi nan, akwai layi a ciki na yi rijista, idan kuma na yi wani laifin na gudu ke za a kama".

"Bana so" ta fa?a tana kwanciya, duk da ?asan zuciyarta tayi mamakin wayar.

Ya saka hannu ya ?auka ya ce "To kin huta" ya fice ya bar ?akin.

Ta kwanta ta yi shiru, sai ta fara tunanin ya aka yi ya ?aga mata ?afa ya ?yaleta, sai kuma ta ga rashin kyautuwar abubuwan da ta yi masa.

Bayan sallar asuba bacci ta koma, ?arfe takwas da rabi ta farka, tana ?o?arin saukkowa daga kan gadon, tayi tozali da farar takarda da biro. Gabanta ya fa?i ta ce "Na shiga uku sakin nawa ya yi?" Ba ta ta?a takardar ba, ta saukko a sukwane ta tafi ?akinsa sai dai baya nan ya fice.

Gaba daya jikinta yayi sanyi, sai yanzu ta ?ara jinjina girman wauta da aikata.

Yau rahila har gidan su jauhar ta je, suka ?ule a ?aka ita da Anty Zakiyya suna ta surutu da shewa.

"Zakiyya ina ga 'yar ku fa an gamu laulayi take yi"

"Kai haba dan Allah"

"Wallahi da gaske, ke 'ya mace shu'uma komai ?an?antarta, kin san yaron nan har gida ya zo da wu?a ya gama ta'addancin sa tana zubar da jini, zai yi mini hauka a gida wai su Amira sun je masa gida sun yi matarsa ko me oho musu, na ga tashin hankali na ce iyee yanzu har ta samu wannan matsayin. Wallahi mamaki nake yadda ta iya zama da yaron nan"

Zakiyya ta ce "Ba ki ganta ba kamar sokuwa, kafin ki ga ta yi fushi, ko tayi zuciya da abu za a jima, ko kuma kawai tsabar ?arfin hali ne da ?i fa?i ba"

Rahila ta ce "Sai ta yiwu, ya ake ciki da maganar hafsa?"

"Mu na nan ana ta murginawa, ana shirin kawo ku?in aure, na ce lallai ta ce masa a ha?o da kayan lefe, ana sallacewa ayi auren, duk da wannan matar ta nuna bakomai na san tsohuwar muguwa ce, wata?ila wani abun zata kitsa, dan haka kan tayi wani yin?uri ayi a wuce wurin".

"Yauwwa kar ki kuskura ki sakankance ko ki yadda da ita, ni ban zaci lamarin ma zai zo da sau?i haka ba, ku cigaba da tatsarsa kuna tarin kayan aure"

Zakiyya ta ce "Ke kin ga hidima, ai ni dai Allah ya kashe ya bani, da yanzu sai dai mu ga ana yi wa waccan yarinyar jauhar"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ga mijinta can suna fama, amma wallahi ya fara son yarinyar nan, kai amma ba ?aramin ha?uri take yi ba bala'i Allah ya kyauta" suka cigaba da hirarrakinsu, da shirin biki.

Misalin ?arfe ?aya da rabi na dare, suka fito daga taron meeting, daga ofishin jam'iyya, sakamakon gabatowar manyan za?uka da za a gudanar a cikin Nigeria.

Yau bai san iya adadin meetings ?in da ya yi attending ba, suka jero da shi da mataimakin firaministan jam'iyya na jiha, ya ?an yi mi?a ya ce "Kai, yau na gaji over"

"Kai honorable, da an yi babban za?e an wuce wurin, haka ne, ka san ban yi sati da shigowa daga Abuja ba, can ma wasu tarurrukan ne, abun duk babu sau?i, ina ta ?o?ari in sha Allah sai na kawowa excellency yankina, ina nan a satin nan zan yi empowerment na matasa, ku?ina duk sun tafi a campaign ?in nan"

"Kar ka damu honorable, hannun jari ka saya, da an wuce wurin sama zaka din ga kwashe ribarka, ka mayar da uwar da ribar ka ?ace ba zasu sake ganinka ba, sai bayan shekara hu?u" suka kwashe da dariya.

Suka yi sallama, kowa ya nufi motarsa, ko da ya je gida, matarsa tuni tayi bacci, yayi wanka ya nemi wuri ya kwanta, dama ba yunwa yake ji ba, sai dai bacci ya gagare shi, ya din ga juyi a kan gadon, ga gajiya ga baccin yana ji, amma ya kasa ya ?uge da lissafe-lissafe abubuwan da yake son yi idan ya dace ya samu ya ci za?en nan.
Ji yayi kamar kansa zai fashe, saboda stress kawai ya tashi ya ?auki mukulli, ko direba bai nema ba ya hau motarsa ya fice.

Yamma da gari yayi, ya hau kan titin gwarzo road kasancewar dare ne, titin babu ababen hawa, ya sauke glas ?in motar ka?an, yana tafe a hankali yana sha?a wani abu a hancinsa. Sai d yayi nesa da cikin gari sosai, sannan ya yi parking a gefen hanya, ya rufe glasan motar, ya cigaba da sha?a abun nan, kusan mintuna talatin, sannan ya juyo kan motar ya nufi dawowa yana tafe iskar kan titin nan na ratsowa cikin motar, sannu a hankali har ya koma gida.

Jauhar kuwa tun da tayi tozali da takardar nan ta kasa nutsuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuma ta?i bu?e takardar, da ta le?a ta hangota ma, sai ta yi sauri ta fito daga ?akin, ta din ga lissafa irin halin da za ta shiga idan ta koma gida, da irin dariyar da za su yi mata.

Kuma ya?i dawowa, har dare ba ta ganshi ba, hakan ya ?ara sanyata cikin tashin hankali, ba irin tunanin da ba ta yi ba, har ta fara tunanin ko da ya saketa, barin gidan yayi gaba ?aya, sai dai kayansa suna nan, dan ita ta gyara ?akin ya watso da komai ya bar mata a wurin.

Sai sha biyu saura ya dawo, idonta biyu ya dawo ba ta yi bacci ba, sai da ta tabattar ya shiga ?akinsa, sannan ta ?auki takardar ta bishi ?akinsa.

Yana kwance a kan katifarsa, ya cika ?akin da warin taba.

Yanayinsa ya nuna a buge yake, saboda fitilar ?akinsa a kunne take, ya haye katifa ya mimmi?e idanunsa sun yi ?anana da ?yar yake ?aga su, kallo ?aya ya yi mata ya mayar da idonsa ya lumshe.

"Master sai da ka rubuta takardar nan hankalinka ya kwanta ko?"

Bai bu?e idonsa ba ya ce "Ke ki ka ce na rubuta"

"Kuma sai ka rubuta ?in ko? Saboda ina fargabar kar ka sake ni, bakomai maraici ne ya janyo mini, Allah ya gani na yi iya yi na, na yi biyayyar aure, amma kullum kallona ka ke yi wadda ta takura rayuwarka, ga takardarka nan, ban ma bu?e ba balle na san meye a ciki, kuma wallahi ban saku ba" ta dire masa takardar a jikinsa, ya ziro harshensa tare da na?e shi ya mayar, ya gyara kwanciyar sa, har ta gama surutanta, bai kuma motsawa ba.

Kasa bacci tayi, ta ?aura alwala ta tayar da salla, ta din ga addu'a Allah ya sa ya fasa sakinta, saboda ita a ganinta gara ?alubalen gidan Al'amin a kan na gidansu.

Duk rintsi ba zai daketa ko ya ci mutuncin ta ba, ko yi mata sharri ba, sai dai miskilancinsa da gaya mata ba?ar magana wasu lokutan da har da?i take ji ya kulata, ciyar da su kuma da take yi mafi yawan lokuta baya damunta, sai ma yi wa Allah godiya da take yi da ko yaya ba ya hanata abun da zata sarrafa su ci, ko yaya ta kasa abun sayarwa za a saya dan ma ana yi mata mugunta.

Bayan sallar asuba tayi shiru tana tunani, ta ga sam ba ta kyauta ba, wasu abubuwan da ta yi masa, tun daga jifansa da kwanuka, har zuwa tsiwar da ta yi masa, ita tayi mamaki ma da ya ?yaleta.

Yau ba ta iya komawa bacci ba, ta fito aikace-aikacen ta, tana yi tana le?awa ko ta gani ko ya tashi.

Tana falo ta jiyo motsinsa, ta tashi ta shiga ?akin da sallama.

Ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba.

Jiki a sanyaye ta dur?usa ta ce "Master ina kwana?"

"Lafiya ?alau"

"Ka tashi lafiya, ya ciwonka?" Sai a wannan karon ya kalleta sai dai bai ce komai ba.

"Master dan Allah dan Annabi ka yi ha?uri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi ha?uri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi ha?uri idan ka sakenin ma, ka yi ha?uri ka mayar da ni" tayi maganar cikin rauni.

Ya lumshe idanunsa ya ce "Bani wuri zan kunna haya?i"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka yi ha?uri master, ka yafe wa 'yar madara ?acin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi ha?uri"

"Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi"

"Dan Allah ka yi ha?uri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?"

"Eh ki kawo mini, sai fa kintafi"

"Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta ro?onka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da ku?i ba zaka ganni ba".

"Eh na ji, kafin ki fara ?aukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita" yayi maganar yana dan?a mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta bu?e idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata.

*Ba zan dawo da wuri ba, na bar ku?i a kan katifata ki sai wani abun ki ci*

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce "Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?"

Hamma yayi, yayi shiru ta ce "A'uzibillah" duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu'a bai yi ba, sai tayi masa.

Ta ce "Aishikenan amma dan Allah ka yi

Please Login or Register in order to submit comment