Reading KARFE A WUTA Chapter 45 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinin?" Yayi maganar yana kallon Al'amin.

Yayi masa banza ya?i magana.

"Wallahi sai dai ka fashe, gaskiya ce sai na gaya maka" ya ce "Liti zo mu duba ina ne za a ?auki jinin".

Mijin wasila da suka koma gefe suna kallon sarautar Allah, suka gaya musu in da lab yake.

Ba a samu irin jinin Jauhar ba, sai dai sun bayar da jinin su leda biyu, aka tafi da shi babban asibiti, za a canzo da kalar nata jinin.

Suka shiga dudduba in da Al'amin ya shiga, aka nuna musu ?akin da jauhar take.

Suka yi sallama suka shiga, an lullu?e ta da green ?in bedsheet, idonta a rufe hannunta biyu duka an saka mata ruwa.

Al'amin na dur?ushe a gaban gadon, ya ri?e hannunta idonsa yayi ja, fuskar jauhar ta yi yellow sosai alamar ?arancin jini.

Walid ya ?arasa ya dafa kafa?ar Al'amin ya ce "Mai zamani, ka yi sakaci da wauta, amma ka kwantar da hankalinka in sha Allah za ta tashi, ka yi mata addu'a. Ba a samu irin jininta ba, amma mun bayar da jinin za a canzo, likita ya ce a kira ka"

Ya mi?e a hankali, suka fito, Walid yana ta cigaba da rarrashin sa, ya ciro ku?i a aljihunsa ya ce "Wallahi ka ga dubu ?ari da hamsin aka samu, shi ma jarin kaya ne, na ?ebo su kawai, ku?a?enmu na hannun mutane, kana ganin za su isa kuwa?"

Al'amin ya ha?iye yawu ya ce "Ban sani ba, ma?wabcinmu ya bayar da dubu ?ari, sai a cire a bashi, in gani idan sauran za su isa".

Walid ya dafa kafa?arsa ya ce "Ka yi ha?uri za su isa in sha Allah, yanzu me ake bu?ata kuma?"

Ya ce "Jinin dai muke jira a saka mata"

"To shikenan, zan je na sake lalubawa ko za a samu ku?i, ka yi ha?uri ka nutsu. Amma dole a sanar da iyayenta"

Al'amin ya ce "Wallahi babu wanda ya isa ya rabani da matata, ka ma daina wannan tunanin"

"Nima ban ce a rabaku ba, haushi ka bani ne, Allah ya taimake ka, na kiyayi mai zamani" yayi maganar cikin sigar girmamawa ga Al'amin.

Al'amin ya daki kafa?arsa ya ce "Get out"

Yayi murmushi suka fita da liti.

Mamaki sai da ya kama mutanen da suka gansu suna fa?a ?azu.

Al'amin ya bawa mijin wasila ku?insa, amma ya ce kyauta ya biya ba sai an biya shi ba.

Babban burin Al'amin bai wuce ya ga ta farka ba, da ya tuna abun da aka ce na game da mahaifarta sai ya ji ya tsani kansa, sai kokowa yake da zuciyarsa ya?i bari haushin Nura guduma yayi tasiri a zuciyarsa.

Wasila ta koma gida, ta dafo musu abinci ta dawo asibitin.

Har la'asar Al'amin ya rasa nutsuwa, aka kawo jini aka saka mata.

A gigice Nura ya zo asibitin jin abun da ya faru, sai dai ko kallonsa Al'amin ya ?i yi.

Ya rasa in da zai saka kansa, mussaman da ya ga juahar a kwance ana saka mata jini, duk da tsananin kishi irin na Al'amin, Nura yana good time da jauhar, mussaman yake zuwa idan tana da aike, ya kar?a yayi mata, har kasuwa yake zuwar mata, sayen kayan beads da stone work.

Ta dafa abinci ta bashi, duk da yaron mijinta ne, kuma tana aikensa, hakan bai hanata girmama shi ba, da yi masa nasiha wasu lokutan.

Ganin shi ne sila, a ?o?arin hana shi illata lafiyar sa da Al'amin yayi tsautsayi ya fa?a kanta, ya sanya ya koma gefe yana kuka, saboda ya firgita da yanayin da ya ganta kamar gawa.

Al'amin cikin tsawa ya ce masa ya fita ya bashi wuri.

Nura ya fita wajen ?akin ya tsaya cikin damuwa.

Al'amin ya je gida, ya bar jauhar da wasila, ya je ya yi wanka, ya ?aukko mata kayan da za a canza mata.

Sai bayan sallar magariba ya dawo, ya tarar da Baba tare da mama Anty zakiyya da kuma saifu a ?akin, wasi ta goge mata jikinta, da taimakon Nurses ta saka mata kaya.

Tsayawa yayi yana kallonsu, yana tunanin ma a ina ya san su.

Sai daga baya, ya tuna Baba, ya dur?usa ya gaishe shi, ya amsa masa tare da fa?in ya mai jiki.

Ya amsa da "Da sau?i" yana tunanin me Walid ya je ya gaya musu.

Baba ya ce "Meyafaru ne? Wani ya je ya ce mana abokinka ne shi, wai ka turo shi an kwantar da jauhar a asibiti, hankalinmu duk ya tashi"

Al'amin ya ce "?ari ta yi"

Anty ta ce "Amma shi ne aka je aka ?aga mana hankali, ni wallahi na zata wani abun ne ya same ta ma".

Mama ta ce "Duk da haka, tun da aka kai ga ?arin jini tana jin jiki, Allah ya sa ba wani abun ne ya faru ba tayi ?arin"

Al'amin bai ce komai ba, ya ajiye kayan hannun sa, dai-dai lokacin Jauhar tayi wani yin?uri zata fa?o daga kan gadon tana kiran "Master kana ina?"

Cikin hanzari ya ?arasa gaban gadon, suna rige-rige da shi da Saifu.

Yayi hanzarin ri?e ta ya ce "Zahra"

"Master"

"Na'am sannu"

"Meyasame ni ne? Kaina fa zai tarwatse ciwo master"

Babu kunya ya rungumeta ya ce "Zai daina, ki daina ?aga muryarki"

Cikin kuka ta ce "Master bana gani, duhu nake gani bana ganinka" tayi maganar tana tittirza ?afarta a kan gadon.

Ya ce "Zaki ganni in sha Allah, ki daina magana"

Al'amin ko a jikinsa, ya ttatara hankalinsa a kanta, Baba ya ce "Waliyiyya, sannu kin ji"

Ta ce "Baba"

"Na'am jauhar"

"Baba kai ne ka zo bana ganinku, duhu nake gani, makancewa na yi?"

Saifu ya ce "Baki makance ba, bacci ki ke ji, ki yi shiru"

"Yaya saifu, bana gani fa"

Saifu ya ce "Bacci ki ke ji ne"

Cikin fita hayyaci ta ?an?ame Al'amin ta sake cewa "Master"

"Na'am madarata"

"Kaina zai fashe, ka ri?e mini shi da ?arfi, marata ma ciwo take yi mini sosai" tayi maganar numfashinta yana fita sama-sama.

Yayi ?asa da muryarsa yana yi mata ra?a ya ce "Kina jina" ta ?aga masa kai.

"Ki daina magana, ki yi shiru baki da lafiya"

"To meyasame ni?"

"Zazza?i ki ke yi"

Ta ce "To, ka je sallar asubar ne?"

"Na je mana, har na yi mana addu'a"

"To ka ri?e kaina da ?arfi ka yi mini addu'a, jikina ma kamar an jona mini shocking nake ji"

Nurse ?in da ta shigo ta ce "Malam ya ka ?agata ana ?ara mata jini, so ake ta kwanta"

Mama ta ce "Fa?owa zata yi daga kan gadon, fizge-fizge take yi"

Nurse ?in ta ce "Kwantar da ita, sai ayi mata allurar bacci"

Ta rirri?e Al'amin ta ce "Kar ka ajiyeni, idan na kwanta bana iya numfashi".

Al'amin ya ce "To shikenan, ba zan kwantar da ke ba"

Anty Zakiyya ta ce "Wannan wane irin ?ari ne, zai saka mutum yayi ta surutai kamar mahaukaci?".

Nurse ?in ta kalleta ta ce "Jini ta zubar sosai da sosai, dan haka jikinta yayi weak, alluran da muke yi mata kuma, sune suke burkita ta, dan haka ba abun mamaki bane ba".

Al'amin yayi ajiyar zuciya, jin yadda Nurse ?in ta rufe musu ainihin abun da ya faru.

Ita kuwa tayi hakan ne, dan tausayin yadda tun da ya kawo jauhar yake ?awainiya, ko da ganganci a lamarin yayi nadama.

Sai wurin sha daya suka tashi za su tafi, dan bayan allaurai ?arancin jini ya saka ta fara haki, athma kuma ta tashi, sai da aka sakata a kan oxygen.

Sai dai daga baya ta zama stable, baba ya din ga yi mata addu'a kan su tafi ya ce tsakanin mama ko Anty Zakiyya wani ya kwana da ita Al'amin ya je gida.

Al'amin ya ce "A'a baba, zan kwana da ita ba wani abu" dama yanayin fuskarsu ya nuna ba su yi niyya ba.

Baba ya din ga yi masa addu'a, sannan suka tafi.

Har suka je gida, suna mamakin kulawa da tashin hankalin da suka gani a tatatare da Al'amin.

Su Walid ma a reception suka kwana, da an ce a nemo abu, za su fita su sayo, shi kuma yana tare da ita yadda ya ga rana haka ya ga dare.

Lokaci -lokaci tayi ta surutu, duk a dalilin mugun ?arfin da ?wayoyin suka yi mata.

Daf da asuba ta sake farkawa, sai dai ba ta zaburar, wannan karon tana gani, sai dai daga kwance ma jiri take yi.

"Master" ya ?ago daga kifa kan da yayi, ya ce "Sannu zahra ya jikin?"

"Alhamdilillah, jiri nake ji".

"Ki yi ha?uri, kin ga jini ake ?ara miki. Zaki daina ji in sha Allah, sannu" yayi maganar yana shafa kanta, yana yi wa Allah godiya da ta farfa?o.

Da sassafe Nura ya sake dawowa, har da guzirin bredi da madara da suga, ya dawo sake duba Jauhar, amma al'amin ya kore shi.

Liti ne ya dawo da shi ya ce "Haba maza, Nuranka ne fa, waye ba ya kuskure? Kar ka yi masa haka dan Allah, kuma sakacin naka ne ba na sa ba, daka kar?a kamata yayi ka zubar ai, dan Allah ka yi ha?uri"

Nura har da kuka ya ce "Dan Allah yaya Aminu ka yi ha?uri, dan Allah wallahi ban ji dadin abun da ya faru ba"

Daga kwance ta ce "Master, laifin me ya yi ka ke korar ?aninka, ayi ha?uri dan Allah, kalli ka saka yana kuka"

Al'amin ya ce "Ki daina magana kar hakin ya dawo"

"To ka ce masa ka ha?ura, ka ga kuka yake yi"

A hankali ya furta"Ya wuce"

"Yauwwa mai zamani, Allah ya ja zamanin maza" tayi maganar tana ?aga hannunta da ?yar ta ta?a fuskarsa.

Cikin jin da?i yadda take ?arfin hali, yayi murmushi ya ce "Ban hana ba?"

Murmushi ta yi masa ba ta ce komai ba.

Da nurse ta shigo ta tarar da ita, tana magana, ga su liti a gefe ta ce "Zahra gawa ta?i rami, sannu kin ji"

"Yauwwa Anty na gode "

Ta kalli Al'amin ta ce "Congratulations, na tayaka muranr farfa?owarta, dan wallahi mun sare bamu zaci zaki tashi ba"

Walid ya ce "Sannunku da ?o?ari, Allah ya biya ku"

"Amin, bari mu gyara mata jikinta, a bata abinci " su liti suka fita, ya taimakawa nurse ?in, ta gyara jauhar, ta zaunar da ita, duk da tana ta kuka da jiri da ciwon kai da na mara.

Ya ha?a mata shayi, da buredi, sai dai ta kasa ci, sai lalla?ata yake yi.

Wasila tayi sallama, suka amsa.

Ta ce "Alhamdilillah anty jauhar jiki yayi kyau, ikon Allah"

Nan suka ?ara gaisawa, ta ajiye abincin da ta zo da shi, jauhar ta ce za ta sha kunun gya?ar da ta kawo.

Ana haka su Baba suka zo, suka tarar da Al'amin yana ba ta abinci an zaunar da ita.

Gab ?aya zamansu a wurin, bai hana shi tattalin matarsa ba, dan gani yake yafi kowa sa'a farfa?owar da ta yi.

Babban abun da ya yi wa jauhar da?i, bai wuce ganin 'yan gidan su, sun zo dubata ba, ko ba komai sun nuna damuwar su da ita.

Duk saifu na ta zuga Baba ya bi diddigin yadda aka yi tayi ?arin, ko dukanta Al'amin yake yi, amma yanayin yadda suke mu'amala ita da Al'amin ya sanya kowa yin wani tunanin daban, dan sa?anin abun da ake tunani ake gani.

Har Abbu sai da ya zo duba jauhar, su shahida ma duk sun zo, Baba sai da ya yi ta yi wa wasila godiya da Addu'a, tana ta ?o?ari da jauhar, ma?wabtan su ma na ta zuwa dubata.

A kwana na uku, da daddare take tambayar Al'amin "Master wai dan Allah meya same ni ne? Na san kawai na ga lemo a ?akinka na sha, daga nan ban san meyafaru ba, kuma na ji ana cewa nayi ?ari, ya aka yi na yi ?ari ai bani da ciki, ko kuma ina da shi ban sani bane? To yaya aka yi ya zube?"

"Ki yi ha?uri, likita zai yi miki bayani in sha Allah"

"To kai ka yi mini mana, wai shikenan babyn yanzu babu a cikina" tayi maganar tana shafa cikin ?auke da damuwa.

"Ni likita ne?"

"A'a amma ka gaya mini, haryanzu ina da cikin?"

Al'amin ya ce "Wai abun da baki san da shi ba ma, zaki bi ki damu, ki yi ha?uri za su yi miki bayani"

Ta ce "To shikenan, yi mini addu'a na yi baccin".

Ya ce "To"

Gari ya waye, su surayya ma suka zo dubata, saifu ya kawo su, take tambayar ina yaya hafsa, aka ce mata ta tafi umara.

Jauhar ta ce "Dan Allah ku ce ta yi mini addu'a sosai da ni da master"

Suryaya ta ce "Wai ke kowa na gaya wa miji sunan 'yan gayu ke kina master"

Tayi murmushi ta ce "Baki ga mastern ne ba? Kuma ai mu ba 'yan gayu bane"

Kasancewar Al'amin ba ya ?akin ya sanya saifu cewa "Ke, ki fa?a mini gaskiya, wani abun yayi miki ko?"

Ta ce "A'a me ka gani?"

"Wallahi ki ka rufa masa asiri sai kin daku, har likita na saka baba ya tambaya, ko dukanki yayi ya ce babu alamar duka a jikinki da aka kawo ki"

Jauhar ta ce "Master ba ya duka, bai ta?a dukana ba".

"Na san halinki da shegiyar gwaninta ne, da kare mai laifi ki gaya mini gaskiya"

"Wallahi babu abun da ya yi mini"

Dawowar Al'amin ya sanya su yin shiru, ya ?arasa gaban gadonta ya ce "Me zaki ci?"

"Bakomai, kawai a sallame ni"

Ya zauna a gefen gadon ya ce "Ba na son rigima, wace irin sallama kuma?"

"Kai ka koya mini ai, kai fa har guduwa ka ke daga asibiti"

Yayi murmushi ya ce "Zaki gudun kenan?"

Ita ma murmushin ta yi ta ce "Kashe ku?in yayi yawa, ina iya tashi ai"

Rarrashin ta ya din ga yi, dan shi kansa ya san zaman asibiti da gundura.

Sai da ta kwana shida, an saka mata jini ya kai leda biyar, sannn aka fara zancen sallamar ta ranar.

Daga likitan sai ita da Al'amin a ?akin, yayi mata bayanin abun da ya faru, tare da gaya mata akwai bu?atar ta huta kan ta sake ?aukar ciki.

Ya yi wa Al'amin fa?a a kan ya kiyaye sosai da sosai, wannan karon sun rufa masa asiri idan ya ?ara faruwa.

Jauhar ta sunkuyar da kai, sai kuka.

Likitan ya ce "Menene? Meyafaru? Kuma?"

Al'amin ya ce "Bakomai, zamu yi magana da ita"

Likitan ya rubuta musu sallama ya fita.

Yana fita ya ce " 'yar madara menene kuma?" Shiru ta yi masa ta cigaba da kuka.

Duk yadda ya rarrasheta, tayi ha?uri ta ?i yin magana.

Baba ya zo da mota, ya ?auke su ya kai su gida, ya yi ta yi wa Al'amin godiyar ?awainiyar da ya yi ta yi da jauhar a asibiti, yayi musu sallama ya tafi.

Al'amin ya zauna kusa da jauhar ya ce "Dan Allah ki gaya mini menene?"

"Komai ma, kawai ka janyo na rasa babyna, kuma wai ba zan haihu yanzu ba, wata?ila ma ba zan sake haihuwa ba".

"Subhanallah kar ki yi mana wannan fatan, zaki kuma haihuwa cewa suka yi kawai ki bayar da tazara saboda yanayin jikinki".

Cikin kuka ta ce "Ai da ka daina shan Wannan abubuwan, duk da ba haka ba. Kawai ka ja na yi asara ga jinina ya ?are, kuma wai ba zan haihu yanzu ba"

Cikin tsananin nadama yake rarrashinta, sallamar mutane ya sanya ya tashi, 'yan dubiya suka din ga zuwa duba jauhar.

Al'amin na ta hidima da ita, da sassafe yake tashi ya yi aikace-aikace, girki ne kawai sai ma?wabta sun shigo suke yi mata.

Shahida ma ta yi ?o?ari sosai, dan tana zuwa ta taya jauhar aiki, a haka suka saba.

Guduma ya sake zuwa har gida ya duba jauhar, tare da gaya mata abun da ya faru.

Jauhar tayi masa nasiha sosai a kan shaye-shaye.

Al'amin ya fara bata tausayi, har rama yayi sosai, mussaman daina kula shi da tayi, sai yayi ta kame-kame.

Yau da ya dawo, normal ta kar?i abun ta.

Har ya tafi ya kwanta, ta bishi ?akinsa.

Ta hau gadon ta kwanta ta ce "Master"

"Mmm"

"Ka yi ha?uri dan Allah, komai ya wuce na ji babu da?i ne kawai shiyasa kawai"

Ya ce "To"

"Kayi magana mana, ba to ba"

"Ina jin babu da?i, missing babynki da ki ka yi, ki yi ha?uri laifina ne"

"Ba fushi na yi dan cikina ya zube ba, fushi na yi saboda bani ba har kai kana yi mini ganganci da rayuwarka, ka daina dan Allah for our own good and safety"

Ya ce "To in sha Allah"

"Yaya za a sha fankar ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Likita ya ce ki huta tukuna kar ki sake ?aukar ciki".

"Sun yi mini allura ai, ko haryanzu ba ka jin komai"

Ya ce "Da ?in ma ina ji, mazewa nake yi, a madadin hakan sai in sha in bugu in manta da ke"

"Master nawa nika?ai, daga ni ba ?ari"

"A'a saura uku"

Ta ce "To ga fili ga mai doki nan ai"

Ya ce "Filin da dokin naki ne ai, ki yi yadda ki ke so madarata"

***

Jauhar ba ta samu damar yin jamb ba, saboda rashin lafiya, dan haka Al'amin ya samu indabo ya ce A al?awarurrukan da ya yi masa, yana son ya samawa jauhar admission, tare da samawa Nura guduma aiki ko na direba ne, a manyan ma'aikatu.

Al'amin ya daina shigo da duk wani abu na shaye-shaye gidan, ko zai yi a iya waje yake tsayawa yayi abun sa.

Jarin su duk ya ?are a asibiti, dan haka ya yanke wata shawara a ransa.


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Jauhar ya fara samu da maganar, da daddare suna tare ya ce "Na ce ba"

"Ka ce me ranka ya da?e?"

"Wani abu na yanke ne, ina son na samu Abbu, ya bani gadona na wurin ummi, in sayar da abun da zan sayar na kar?i ku?i a wurin indabo na ha?a na fara wata sana'ar ina son barin sayar da wiwi gaba ?aya".

Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, tunani mai kyau, amma ba a yadda ka gaya mini haka zaka je ka gaya wa Abbun ba ko?"

"A yaya zan gaya masa?"

"Cikin kwantar da murya, zaka yi masa bayani, ka san iyaye sai ana lalla?a su, ka sani ma ko ya kai ka kasuwa?"

Ya ce "Ko ya kai ni ba na so, ya je ya cigaba da ri?e 'ya'yan matar can. Dama alhkina ne ya sa yanzu ba shi da ku?i kamar da"

Jauhar ta ce "Haba master, Abbun ka ke gaya wa haka, kai zaka ji da?i ka haifi ?a yayi maka haka?".

Cikin ko in kula Al'amin ya ce "Duk tsanani, ba zan yi wa ?a na abun da yayi mini ba"

"Master ka san shiga tsakaninka aka yi da Abbu, dan Allah ka daina irin wannan maganar".

Yayi mata shiru, ta sake cewa "Master yaushe zaka kai ni mu gaida su Hajiya?"

"Ba rana? Tun bayan kawo ki sun kuma zuwa?"

"Hmm master, Allah ya baka damarmaki, duk da ka rasa ummi da yaya sadik, da kuma uban gidanka. Ko yaya dole nan gaba yaranka su so ganin 'yan uwanka, dan da dangin uba ake ado. Ni fa duk wannan abun da ake yi, bani da wayo sanin mahaifiyata ta rasu, ba 'yar gari bace, yar jalingo ce, ba a ta?a kai ni garinsu ba, ba a ta?a nuna mini ko mutum ?aya a danginta ba, kuma ban ta?a ganin kowa ya zo daga garinsu ba. Da na fuskanci babu uwata a gidan, na nemi ba'asin in da take, baka ga dukan da mama tayi mini ba, ban ha?ura ba na tambayi baba, amma ya ce idan na kuma yi masa zancen dangin mamana, sai ya zane ni. Yadda yake nunawa da yadda su mama ke fa?a yana son mamana, amma nayi mamakin yadda ya?i yadda a kai ni garin su na ga ko 'yan uwanta, da naga ba ya so kawai na daina maganar. Kai kuwa da ka rasa uwa akwai makwafinta, yakamata mu je mu ga hajiya mu gaisheta, ni ba wanda zan kalla na ce daga wurin dangin mahaifiyata yake".

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Kuma ba ki san a ina take a jalingon ba?"

Ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, kawai iya abun da na sani kenan"

"Shikenan, zamu je mu gaida hajiya, amma sai na tambayi Abbu in da take a tofan ba zan iya tunawa ba"

"Yauwwa maigidan Allah dai ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora "

Ya shafa fuskarta ya ce "Amin madarata"

"Yauwwa milona"

Ya ce "Ga madara ga milo, sai Shan shayi" suka yi dariya tare.

Washegari da safe bayan sun karya, ya bata magunguna ta sha, tana ta lalla?a jikinta, za ta yi aikace-aikacenta, ya hanata ya fito ya yi mata share-share, har tsakar gida ya wanke mata.

Kayan da ta cire yake wankewa, aka buga ?ofa, ya je ya bu?e hafsa ya gani a tsaye, hannunta ri?e da leda.

Ya bata hanya ta shigo, a tsorace ta kalli Al'amin fuskarsa a ha?e ta ce "Ina kwana"

"Lafiya ?alau".

"Dan Allah wurin jauhar na zo" da hannu ya nuna mata falo.

Daga falon ta ce "Muryar wa nake ji kamar Yaya hafsa"

Ta ce "Nice"

Ta tashi ta taro hafsa ta ce "Sannu da zuwa".

Hafsa ta ce "Yauwwa sannu ya jiki?"

"Jiki Alhamdilillah, ya aka yi ki ka gane gidan?"

"Yaya saifu ne ya gaya mini hanya, kuma direbana da yayi tambaya aka nuna masa gidan ba wuyar ganewa".

Ta ce "Allah sarki yaya hafsa tun ina Asibiti nake tambayar kina ina, aka ce mini kina umara, na ce baki gaya mini ba muna chat, ai da na jero addu'a ayi mana ni da mai gida"

Tayi murmushi ta ce "yanzun ma an yi miki, wai jauhar ?arin da wahala ne, na ga kin rame haka kin yi fari?"

"Kai da wahala mana, jini na zubar sosai shiyasa na yi haka, amma kwanaki ai ?iba na yi sosai, ashe ciki ne ban sani ba"

"Allah sarki, Allah ya kawo mai amfani, sannu"

"Yauwwa ai na warware "

Al'amin ya shigo falon, jauhar ta ce "Master ba ka ganeta ba ne? Yayata ce da muka je gidanta fa, ba ka ga muna kama ba?"

Kai tsaye ya ce "Na gani, kin fita kyau"

Jauhar ta ce "Kai fa ka fiye son kai ta ina?"

"Ta ko ina" yayi maganar yana shigewa ?akinsa.

Hafsa tayi murmushi ta ce "Aikam kin fi mu kyau ai duk gidan nan"

Jauhar ta ce "Rabu da shi, shi ma fa?a kawai yayi" suka cigaba da hira, ya sake fitowa ya shirya tsaf zai fita.

"To yau me ki ke so? Kayan cikin ko ganyen wanne ki ke so?"

Ta shagwa?e fuska ta ce "Kai"

"Ni ki ke so?" Ta ?aga masa gira tana murmushi.

"Aikuwa zaki kwana da yunwa, me ki ke so?"

"Komai ka samu na gode"

Ya ce "Abun da zai ?ara miki jini aka ce ai"

"Jininka zan sha" ta yi maganar tana dariya.

Yayi murmushi ya ce "You are not serious, ki yi addu'a Allah ya sa na samu ku?i, na sayo miki kaza".

Hafsa ta ce "Ai ga miya ma na yi miki, da kazar a ciki"

Jauhar ta ce "Ashe zaku yi fa?a da master, tun da ki ka riga shi kawo mini kaza"

Murmushi ya sake yi, wanda ya bawa hafsa mamaki, take bin su da kallo, gwanin burgewa.

Har zai fita ta ce "Master"

Ba tare da ya juyo ba ya ce "Kar na yi shaye-shaye da yawa, kar na yi fa?a da kowa, banda rigima da mutane" ta kwashe da dariya ta ce "Au ka haddace ma kenan, addu'a zan yi maka ai, Allah ya iya maka, ya goyi bayanka yayi maka jagora ya wadatamu da halal ya nesanta mu da haram"

Ya waiwayo ya ce "Amin ya haiyyu ya ?aiyyum, 'yar aljannata" ya juya ya tafi.

Yana fita Hafsa ta ce "Innalillahi, jauhar dan Allah ya aka yi ki ka canza mutumin nan, dariya fa yake yi miki, kalli yadda yake yi miki, dan Allah jauhara ya ki ka yi ki taimake ni" tayi maganar cikin tsananin damuwa.

Jauhar ta ce "Ban fahimci in taimake ki ba yaya hafsa, meyafaru? Wannan ai normal ne tsakanin ma'aurata, kodayeke shi ya koya mini rashin kunya, da ko kallonsa bana iya yi a gaban mutane"

Idon hafsa ya cika da hawaye ta ce "Jauhar, wallahi tun da na auri Alhaji mu'azzam hankalina bai kwanta ba, bai ta?a bani awa biyar cikakkiya ba. Sai abun da matarsa take so yake yi, bai tare a ?akina ba sai da matarsa ta amince. Ga ku?in yana da su, yana kashe mini ya sakar mini amm ba su nake so ba, kulawarsa nake so da lokacin sa".

Juahar ta ce "Yaya hafsa ba fa abun da ki ke kalla a film ne soyyaya ba a ?asar hausa da wurin mijin bahaushiya, dole ki fara kallon wane irin mutum ne shi, kin ga mijinki mutum ne mai hidindimu da yawa, ba zai yiwu ace kullum yana da lokacinki ba yakamata ki din ga yi masa uzuri"

"Uzuri jauhar, yana da lokacin matarsa da yaransa, gaba ?aya auren ya

Please Login or Register in order to submit comment