Reading KARFE A WUTA Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tabbas da ita wata ce, sai ta taimakawa rayuwar su, ko a mutum goma, idan biyu suka shiryu ai an rage.

Kamar wadda ta sha kayan maye, haka yau tayi bacci da wuri, gudun da tayi jikinta duk ciwo yake yi mata, ga numfashi sai wahala yake ba ta.

A wani ?aki ta ganta, mai duhu sai haske ka?an a ciki, ga karnuka duk a cikin ?akin, sai haushi suke yi mata, an ?aure su da sar?a.
Ihu take yi tana neman agaji, amma babu wanda ya san tana yi.

Can sai ga wani mutum ya shigo, dogo sosai, mai cikar halitta, ba ta ganin fuskarsa saboda duhu, ya shigo ?akin bai ce mata uffan ba, ya dan?o hannunta ya biyo tsakanin karnukan ya fito da ita daga ?akin, ya ciro wu?a zai caka mata a ciki.

Wani uban ihu ta saki, tana kiran sunan Allah, da na Abba da Nasir.

Tana bu?e ido, ta ga Abba a kanta, da Nasir, da su walida har da Anty da baba magajiya, ana ta tofa mata addu'a.

Kallonsu take yi ?aya bayan ?aya, ta ce "Abba ya na ganku a nan? Meyafaru?"

Nasir ya ce "Sannu"

Abba ya ce "Arfa ba kya addu'a ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Ina yi Abba"

"A'a ba kya yi, da kina addu'a babu yadda za ayi, ki kwanta kina yi mana ihu da safiyar nan, shiyasa nake hanaki wannan shegen fentin da bulbula turare a jikinki, dole she?anu su yi ayari, su yi ta binki"

Nasir ya ce "Dan Abba ka yi ha?uri, haryanzu a tsorace take ma, a bari ta dawo hayyacinta gaba ?aya, sannu Arfat, ki ?auro alwala ki zo ki ?auki Alqur'ani ki karanta".

Abba ya mi?e ya ce "Aishikenan, zan yi waya da Barrister, su baki day off, ki samu ki huta"

Nabila ta yi shiru tana rarraba ido, ta san lafiyarta ?alau, tsabar tsorata ne da tayi.
Tayi shiru ba ta fa?i abun da ya faru ba, suka din ga yi mata sannu.

***
YALOKO ?ARAMAR HUKUMAR UNGOGGO

Matashiyar yarinya ce, wadda dudu shekarunta ba su fi goma sha hu?u ba, take ta iza wuta a cikin murhu, gefe ga garin tuwo a cikin ?warya.

Yaro ne ya yi sallama, ta ?aga kai ta amsa masa.

Ya kalleta ya ce "Ramma ki zo ana sallama"

Ta ?an waro manyan idanunta ta ce "In ji wa? Ko Habu ne?"

"A'a, wani ne da mota"

Ta mi?e tsaye ta ce "To mota kuma, ina zuwa?"

Daga tsakar gidan ta ?an ?aga murya ta ce "Mama, wai ana nemana a waje, bari na duba waye, ruwan ya kusa tafasa"

Daga cikin ?aki matar ta amsa mata da "To ramma, hanzarta ki dawo, ina son zan fita ne"

Ramma ta amsa da "to" ta ?auki hijjabinta ta saka ta fice waje.

Mintuna goma sha biyu ta dawo, jiki a sanyaye.

Mamanta ta kalleta ta ce "Menene?"

"Mama daga Kano ne, wai Anty mai jidda ce gidan da nake aiki, ta yi waya wai azo a ?auke ni a mayar da ni, a satin nan za su dawo"

Matar tayi sak ta ce "Da wuri haka, ba cewa aka yi sai bayan wata guda zaki koma ba?"

Ramma ta ja ta tsaya ta ce "Jikina duk yayi sanyi, wai yanzu-yanzu zamu tafi"

"To shikenan ai babu wani abu, ki yi ha?uri kin ji ramma, ni kaina ba a son raina ki ke barin gabana ba, da Allah ya sa mun tara ku?in kayan gado, shikenan sai ki dawo ki yi auren ki. Maza mu je na tayaki ha?a kayan"

Cikin abun da bai fi mintuna arba'in ba, suka ha?a kayan, suka yi sallama ramma ta bi direba zuwa gidan aikinta da yake Kano.

Yana zaune ya zuba musu ido, suna ha?a masa tea, Walid ya zuba ?wayoyi a cikin kofin, sannan ya zuba shayin.

"?ara wannan ba zasu ?auke ni ba"

Walid ya ce "Amma boss, kai fa ka ke hanamu sha a baya, tayi yawa wallahi".

"Ka ?ara mini na ce" yayi maganar a hasale.

Ya ?ara masa ?wayoyin yana kallonsa, saboda ?wayar da suke yi wa la?abi da raina kama, a baya sam baya shan irinta, saboda yadda take bugarwa, wasu lokutan rabi suke ?allawa su sha, amma ya ce a saka masa kusan biyar yanzu.

Ya ?auki kofin ya kai bakinsa zai fara sha, Walid ya ce "Yau fa madaki za su je ?aukar fansa cikin unguwa, daga majiya mai ?arfi na ji zancen, daga jiya zuwa yau ya ce idan ?an arearmu ya shiga ta su, a aika shi kawai"

Ya cigaba da girgiza kofin ba tare da ya yi magana ba, ya sake yin?unrin kai kofin bakinsa, walid ya sake cewa "Wata ta je nemanka a arear, aka kaita dabar madaki, Allah ne ya yi da kwananta a gaba, da kasheta za su yi"

Duk da cikinsa yayi wata ?ara, jin an ce mace ta na nemansa. Wace mai tsautsayin ce wannan? Me take nema a wurina?, amma ya maze ya ?ago jajayen idanunsa ya kalli walid ya ce "Ni kuma?"

Walid ya ce "Ba zan yi maka ?arya ba, da gaske nake"

Wani dogon tsaki ya ja, ya dungurar da kofin shayin, ya tashi ya ce "Ku ?ebo yaran nan na cikin unguwa, da na can wajen gari, ku sake dira a dabar madaki, ina son ?arnar da za ku yi ta fi waccan, kar ku basu damar cutar da kowa. Ko kun gaya wa jami'an tsaro ?udurinsu, babu abun da za su yi musu, ku far musu kawai, ka shirya komai, a bawa yaran na shan sigari" bai jira amsar walid ba ya fice.

Walid ya yi ajiyar zuciya, ?an mama ya kalle shi ya ce "Da gaske ka ke wata ta je nemansa, ko kuma ka fa?a ne, dan ka hana shi shan ?wayar nan?"

Walid ya ce "Duka, kai da ya sha abun nan, zai iya mutuwa fa"

?an mama ya ce "Ai rigimar da yake yi kwanan nan, ta ?ara yawa, sai an ?ara saka masa ido sosai, kashe kansa yake son yi wallahi, wasu lokutan bana son muke watsewa mu bar shi shika?ai a gidan nan".

Walid ya girgiza kai ya ce "Ba zai kashe kansa ba".

"Ya aka yi ka san hakan?"

"Yana da abun da yake son cimma, kawai kayan ne gaba ?aya ba sa ?aukarsa gaba ?aya yanzu, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, duk kayan cajin nan kansa ba ya ?auka kamar aljani, amma ina bincikawa, an yi mini al?awarin wata zazzafar ?waya, daga kudu suke kawota.
Yanzu dai wannan aikin da ya ce , maza-maza ka kira kwangila a waya, ya ha?a mana yara, a basu kayan caji, zamu fasa ?ofa, ai Madaki shi da ?aukar wata fansa a kanmu, sai dai a lahira idan ana yi. Sai mun ga abun da ya turewa buzu na?i.
?an mama ya mi?e ya ce "Ok, bari na hanzarta na fara ha?o su ta arear wajen garin nan".

Walid ya ce "Nima fitar zan yi, wurin liti zani, zan shiga kar?ar balance". Suka fice gaba ?aya.

Bayan tafiyar su Aminu ya koma cikin ?akin, ya fara duba in da walid yake ajiye ?wayoyi, amma ya dudduba bai gansu ba, ya zazzage ko ina, amma babu.

Wani irin takaici ya tokare masa ?irji, ya ja dogon tsaki, ya ?aga gefen katifarsa, allurar sa saura kwalba biyu kawai, kuma ya san ba ?aukarsa za ta yi ba.

Haka ya zu?e ta ya yi wa kansa, sai dai kamar kullum, yau ma ?irjinsa ne ya fara da zafi, kansa yana juya masa.

Wu?ar da take gefensa yake ta kallo, zuciyarsa na raya masa abubuwa daban-daban.

Tun da Ramma ta suka isa cikin kano, gidan da take aikatau, kayanta kawai ta sauke a ?akinta, ta hau aikace-aikace.

Duk da akwai wata mai aikin, wadda ta girmewa ramma, sosai da sosai, amma matar gidan ita ta yarjewa ta shiga sashenta, har uwar ?aka da na maigidan ta gyara mata, a cewarta ramma ta fi nutsuwa, kuma ba ta ta?a ?ar aikin da ba ta yi mata sata ba, sai ita.

Matar gidan da ?a?anta gaba ?aya sun tafi dubai hutu, shiyasa ta sallame ta, ta ce ta je gida ta huta, za su yi wata biyu kafin su dawo, kuma kwatsam yanzu sati biyu wai dawowa za su yi.

Tana falon matar gidan, tana ta uban aiki, ?an kwanakin da aka yi ba a ta?a wurin ba, duk ya yi ?ura.

?ofar falon aka shigo, ta tashi da sauri, tana kallon mai shigowar, dan ba ta yi tsammanin ganin kowa a sashen ba, dai-dai wannan lokacin.

***

Nabila kuwa kusan kwanaki uku curr, ta kasa nutsuwa da kwanciyar hankali, da ta kwanta bacci, sai mafarkin karnuka, tayi ta ihu.
Haka Anty da baba magajiya za su danneta, su yi ta shafa mata man gelo da miski, ta ja bakinta, ta yi shiru, ba ta gaya musu abun da ta aikata ba.

Yau kuwa gajiya ta yi da zaman gidan, dan baka cikin hijjabi ta shirya, ta ?auki ?ar ?aramar wayarta, ta fito falo.

Umma ta kalleta ta ce "Ke da baki da lafiya, ina zaki je kuma?"

Nabila ta ce "Wurin aiki, akwai bu?atar in je zan kai wani bayani ne mai muhimmanci"

"Amma kin gaya masa, kar ya dawo ya tarar kin fita, ya yi ta fa?a"

"Umma ba da?ewa zan yi ba"

Saudat ta ce "Mhmm, a ma fa?i gaskiya, ko yawon banza za aje".

Nabila har za ta yi shiru, ta ga idan tayi shiru, za ta cutu, dan haka ta ce "Idan fitsari banza ne, kaza ma tayi, idan yawon ma zan tafi, mai lasisi ne akwai riba, ke ki yi mana"

Umma ta kalli Sauda ta ce "Sauda dan Allah ki din ga jan girmanki, Nabila fa ba sa'arki ba ce ba".

"Na saka da ke ne?"

Umma ta girgiza kai ta ce "A'a baki saka da ni ba, Allah ya taimaka".

Sumayya tana ta aiki a news room, Nabila ta yi sallama ta shiga.

Sumayya ta kalleta ta ce "Ina aikin?"

"Ban je ba, ya aikin?"

"Lafiya ?alau, meyasa ba ki je ba?"

Nabila ta ce "Ke ba wannan ba, yanzu na ga managern ku a waje muka gaisa"

Sumayya ta ce "Good, ya aka yi?"

"Rahotonki na last week, a kan case ?in yarinyar nan da aka yi wa fya?e, na ji shiru baku sake cewa komai ba"

Sumayya ta ce "Eh ya aka yi?"

Nabila ta ce "ina da intrest a kai ne, ina son shiga lamarin, na ji shiru haryanzu babu wani update, na an ?auki mataki"

Sumayya ta ce "Dalla ware, kamar wata lawyer kirki, you are not even serious about the job"

Nabila ta ce "Ke ban son wula?anci fa, am serious, na ji an ce wanda yayi laifin mai lasisi ne a garin nan, ina son sanin waye shi?"

Sumayya ta ce "Nima ban sani ba"

"Kamar yaya ba ki sani ba, am serious fa, da gaske nake sumayya ina son shiga case ?in, free of charge na taimaka wa yarinyar, na ji tausayin su sosai da sosai, yadda uwar take kuka. Kuma daga ji ?an karkara ne, masu ?aramin ?arfi".

Sumayya ta galla mata harara ta ce "Sannu ambulance uwar taimako, manyan lawyoyi sun riga sun shiga case ?in tuni, sai ki ja gefe"

"Suwaye manyan lawyoyin? Kuma wai waye dan Allah, waye yayi fya?en?"

"Ke! Nifa a rubuce aka bani, karantawa kawai na yi, hatta recording ?in da aka saka, na muryar uwar da ?ar, tararwa na yi an yi, ban ma gansu ba, ban ga suwaye ba, balle na samu wani bayani. Case ma fa lamarin ya kusa zama a gidan nan, saboda saka muryar matar da aka yi, murtala ne dama ya yi recording ?in ya saka, sai da aka kusa korarsu"

Nabila ta ce "To fa, ina murtalan yake?"

Sumayya ta ce "Ba zan nuna ba, kin ganki Nabila"

"Ba wani abu zan yi ba, sonake kawai ya ha?ani da matar da yarinyar".

"Babu fa abun da zaki iya yi a kai, shi ma bai san waye wanda yayi fya?en ba, yarinyar aiki take a gidan, ba?o ne daga zuwa yayi mata. Dan Allah ki ha?ura da case ?in nan"

A ?an fusace ta ce "Saboda me?"

Sumayya ta yi murmushi ta ce "Na ji an ce mutuniyar ki da jama'arta sun shiga cikin case ?in, shiyasa na ce ki ha?ura"

Nabila ta ce "Wa kenan?"

"Naja bunkure mana, antynki mudubinki, a bar ?aunarki" Sumayya ta yi maganar tana dariya.

A take annurin fuskar Nabila ya ?auke, haka kurum jikinta ya bata babu gaskiya a lamarin nan.

"Uban mudubin nawa, in dai wannan mudubin ne, Allah ya fasa shi na huta, wallahi sumayya tun daga abun da matar nan ta yi mini, kawai nake ji a jikina fuska biyu ce da ita, wadda take kallon jama'a da ita, da kuma wadda take ?oyewa"

"To ko ma dai yaya ne, sun shiga case ?in, kin san kuma ba zasu tsaya su saurareki ba, mussaman da ta iya yi miki kallon ke ba komai ba ce ba"

Nabila ta ce "Haka ne, amma rai dai an cire wa fara kai, lokaci ne, yana nan zuwa da zan bawa duniya mamaki, sai na saka ?afa na bi ta kanta ko da halin ?a?a"

"To ki bi a hankali, kar ke duniyar ta baki mamaki"

Nabila ta yi shiru tana tunani.

Sumayya ta ce "Ya dai?"

Tayi guntun tsaki ta ce "Sumy zaman gidanmu babu da?i, kamar in gudu wallahi".

"Wai Nabila ba zaki daina wannan i?irarin ba?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zaki gane ba, fa?a muka yi da Siyama, har da Abba ayi mini fa?a, sau?inta ?aya ta ci duka da tukunya na din ga dukanta"

"Haba Nabila, wannan ai yawa ne, degree holder da dambe?"

"To yaya ki ke so in yi? In zuba mata ido ta yi mini duka? Ga uwarsu ta addabi rayuwata, ba ta san yadda ta tsane ni, nima haka na tsaneta ba, kawaici kawai nake yi mata ba.
Duk uban ?an matan gidan nan har da zaurawa, babu wanda duka sanyawa ido sai ni, da na motsa ayi ta janyo mini jafa'in karuwanci" ta ?arasa maganar hawaye na cika mata ido.

Sumayya ta ce "No dear, dan Allah ki ?ara jurewa, lokaci ne da kin yi aure zai wuce"

"Yaushe zan yi auren? Dan Allah ni mummuna ce Sumy? Duk saurayin da ya zo, sai za a fara maganar aure, sai ya gudu kamar wata ja?a"

"Nabila kina da matsala, Babu wata halittar Ubangiji mummuna. Ga ki fara, ga gayu da ilimin addini da na zamani, kina da kwarjinin da ki ke bawa maza tsoro ne, ai ke kalar manya ce tawan, ba duk kai ba"

Cikin takaici Nabila ta ce "Ba wasu manya, manyan da suka din ga yaudarata Allah ya isa da ba su aure ni ba suka ?ata mini lokaci, ni yanzu kowaye ma zan aura na bar musu gidan, ko ba na son shi. Idan ba haka ba wallahi wataran sai na gudu"

Sumayya ga tausayin Nabila ga dariya, tabbas Nabila akwai farijinin samari, masu kashe mata ku?i ma kuwa, sai dai Nabila ta fiye za?e-za?e, kuma ba ta fiye ba wa masu sonta da gaskiya muhimmanci ba.

"Ki gudu ki je gidan uban wa? Gaki ga Abba nan maza ki gudu kar ki fasa"

Sai kuma ta koma rarrashinta, har bayan azahar suna tare, sai da sumayya ta tashi suka fito tare.

A reception suka tarar da wani mutum, ana ta yi masa fadanci, yana hura hanci cikin manyan kaya na alfarma, reception ?in ko ina security.

Sumayya ta risuna ta gaishe shi ya amsa, amma Nabila ko kallonsa ba ta yi ba, ta sunkuyar da kai, kamar alla-alla take yi, ta yi ta bar reception ?in.

?an rikicewa yayi, ya ?ura mata ido, amma ta basar ba ta gaishe shi ba, sai so yake yi ta ?ago su ha?a ido, dan ya tabattar da abun da yake tunani, amma ta?i ta mayar da kanta gefe.

Mamaki ya shiga yi, yana tunanin ko dai gizo idonsa yake yi masa? Sai dai ya rasa abun yi kafin ya yi wani yin?uri, sun bar reception ?in.

?aya daga cikin ma'aikatan ya kalla ya ce "Wannan mai hijjabin ma'aikaciyar ku ce ita ma?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a sir, she's just a guest here"

Ya ce "She looks familiar to me, anyway shikenan dai" yayi gaba.

Cike da takaici Sumayya ta ce "Kina kallon babban mutum ki ka basar ba ki gaishe shi ba, sai kallonki yake yi, ki ka sani ko shi ne mijin a dace a daidaita ko ?yasawa yayi? Da irin wannan halin naki, ki ke korar samarinki na kirki wallahi".

"Kin fi kowa sanin bani da ba?in hali, wasu lokutan ma cewa ki ke yi na fiye za?ewa"

"Haka ne, amma baki kyauta ba, ko dan kallon da yake yi miki, ai kya kula shi".

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban ta?a jin na tsani wata halitta a kallon farko da na yi mata a rayuwata ba, sai wannan mutumin. Gaba ?aya ya canza mini mood lokaci guda"

Sumayya ta waro ido ta ce "Meyasa kun ta?a ha?uwa ne? Me yayi miki?"

"No, ina ganin shi a poster dai, ba ?an majalisa bane? Ban ta?a jin komai idan na ganshi a poster ba, sai yau da na ganshi ido da ido, bana fatan Allah ya sa na sake sanya shi a idona. Kin san me? ji nake kamar ya ta?a cutar da ni, cuta mai muni"

"Arfa, kina hayyacinki kuwa? Tayaya mutumin da ki ka fara gani yau kawai, ki ce kin tsane shi, ya cutar da ke how?"

"Ban san tayaya ba, amma haka nake ji a raina, kuma da gaske nake jin hakan"

"Ki daina irin wannan wasan, kar ki saka a din ga yi miki mummunar fassara"

"Forget, ba zaki gane ba" tayi maganar a daidai lokacin da suka ?araso titi.

Tun ba ayi sallar magariba ba, walid ya riga ya gama tatara gayyar matasa zauna gari banza, wanda suka yi bankwana da fatan samun ingantacciyar rayuwa, suka kama makamai da ta'amalli da miyagun ?wayoyi.

Kasancewar ba a cikakken hankalinsu suke ba, haka suka raraka kowa da kowa gida.

Yaran madaki, na ta shirin shiga ?aya unguwar sare-saren ?aukar fansa. Labari ya iske su cewar, yaran Aminu sun rigasu yin dirar mikiya.

Ba su yi zaton gayya guda, yaran aminun suka ?aukko ba, dan haka suka fita domin su far musu.

Kamar ba jikin ?an Adam ba, haka suka din ga sara da sukar junansu, mutanen unguwa duk suka shiga gida suka rufe.

Aka yi rashin sa'a madaki baya nan, ?aya daga cikin yaransa, ya kira shi ya sanar da shi halin da ake ciki.

Nasir yana zaune ya idar da sallar magariba yana lazumi, so yake ya tambayi ina arfa, ya ga ya jikinta, amma mama na babban falo, ya san da ya yi hakan, za ta yi masa fa?a, tare da sake garga?insa a kan Nabila.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya shafa addu'ar, ya ?aga tare da yin sallama.

Da sauri ya tashi tsaye, yana fa?in gashi nan zuwa.

Da sauri ya ?auki mukullin motarsa, ya fito daga sashin mama, zuwa falo.

Mama ta kalleshi ta ce "Ya dai? Ya na ganka a birkice?"

Dai-dai lokacin Nabila ta fito daga ?angaren ?akinsu, hannunta ri?e da kofi, hakan ya sanya ya kasa ba ta amsa.

Zuciyar sa ta tsananta bugawa da sauri, doguwar rigar material ce a jikinta, kanta babu ?ankwali, tayi parking ?in gashinta.
Wani irin kyau ta ?ara yi masa.

"DSP yaushe ka dawo?" Tayi maganar tana kallonsa.

"Da magaribar nan, yanzu nake shirin nemanki, in ga ya jikin naki? Wayarki ba ta shiga"

Anty ta ce "Jiki yayi kyau, har fita tayi"

"Fita kuma, ki ka je ina? Kuma da iznin wa?"

"Dan ubanka ina yi maka magana ka shareni, maganarta ta fi tawa muhimmanci ne ko yaya?"

A ?an rikice ya ce "A'a mama, yi ha?uri kiran gaggawa aka yi mini, fa?an daba ya ?ara ?arkewa, ?an daba sun rufe unguwar babu shiga babu fita, yaran Aminu Viper ne da wani madaki, wai ?an sandan da aka tura, sun kasa kwantar da rigimar, kin san am incharge of his case, shi ne zan je na ga abun yi"

"To ka kula da kyau, ni wannan aikin ya isheni, shikenan kai ba hutu, ni hankali a tashe".

Ya jinjina kai ya nufi ?ofar fita.

Jin an ambaci Aminu, ya sanya jikin Nabila ya hau tsuma, ya bishi da gudu ta ri?o rigarsa ta ce "DSP, amma ba kai ka?ai zaka je ba ko?"

"Eh, na yi waya za a ?aro mini ?an sanda"

"Ko mu je tare?"

Ya zaro ido ya ce "Ki yi me?"

Sai kuma ta rasa me za ta ce "Kawai dai ko zan iya taimakawa"

Murmushi ya yi ya ce "Ba fa kotu ba ce madam"

"Zaki sake shi ya tafi ko kuwa? Wane irin iskanci ne haka, Meye haka ne Nasir?"

Nabila ta saki rigarsa ta ?an ?aga murya ta ce "Take care, ka tsaya daga nesa nesa dan Allah, kar wani abu ya same ka, kar mu yi asarar ?an ?asa na gari"

Dariya ya yi, ya fita da sauri.

Mama ta hayyaya?o mata "Wallahi ki kiyayeni da rashin tarbiyyar ki a kan ?a na, na gaya miki" mama ta yi maganar tana nuna Nabila da yatsa.

Nabila a ranta ta ce 'Ni yanzu ba ke ce a gabana ba, akwai abubuwan da suka fiki muhimmanci a wurina"

Tayi gaba tana kiran lambar sumayya, ta sanar mata da halin da ake ciki, na rikicin fa?an daba.

Sai dai kamar kullum, fa?a suka yi, sumayya ta garga?eta a kan ta fita sabgar harkar fa?an daban nan.

Nabila tayi zuciya ta kashe wayarta, tare da jin da ita ?ar jarida ce, sai ta shiga unguwar nan, ta samo rahoto, tana matu?ar jin haushin yadda sumayya take ?ari-?ari da gudanar da aikinta, sai dai ko ba dan sumayya ba, ya zama dole ta taimakawa Nasir, kuma ta taimaki tata career, dan idan ba ta rama abun da Najar bunkure tayi mata ba, ba zata huce ba dan haka za ta cigaba da bibiya.

Ayshercool
08081012143

*?ARFE A WUTA*


AISHA ADAM (AYSHERCOOL)



https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T



Masu neman book ?in ?ARFE A WUTA daga farko, su bi wannan link ?in, su yi following channel ?in, za su samu previous pages??????.


https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T


9

Har ?arfe goma na dare, Nabila tana kiran wayar Nasir, domin jin ko yana lafiya, amma shiru wayarsa ba ta shiga, abu kamar wasa hankalinta ya fara tashi, zuciyarta ta din ga raya mata wani abun ya same shi.

Da sauri ta tashi ta fita farfajiyar gidan, tana cigaba da kiran wayarsa.

"Ke Arfa, me ki ke yi a wurin nan da daddare haka?" Ta ji muryar Abba babu tsammani.

Cikin damuwa ta ce "Abba Yaya bai dawo ba, kiransa aka yi kwantar da tarzomar fa?an daba, kuma haryanzu bai dawo ba".

Abba ya ce "Yana nan lafiya in sha Allah, da ki ka dawo nan kina sintiri,ai ba bin sa zaki yi ki nemo shi ba, harkar aiki ne yana nan lafiya in sha Allah"

Abba yana rufe bakinsa, sai ga ?arar motar Nasir, yana ta horn ba ?a??aitawa, gaba ?aya suka nufi gate a tare.

Suka tsaye har ya shigo yayi parking ?in motar.

Ya fito yana kallon su da mamaki ya ce "Abba lafiya na ganku a nan tsaye?"

Major ya ce "Arfa ce ta fito tana jiran dawowarka, ya ya aka yi wayarka ba ta shiga gaba ?aya?"

"Tana cikin mota ne abba, ina ga network ne amma a kunne take"

Cikin za?uwa ta ce "Yaya, komai lafiya dai ko?"

Ya ce "Alhamdilillah, an sha artabu dai, yaran sun ninka yawan da muke tunani, mun kama wasu, wasu sun gudu, amma mun kama su da yawa".

Mama ce ta fito ita ma, tare da su sauda, suna yi masa sannu da zuwa yana amsawa.

Arfa ta ce "Amma dai ba su yi maka rauni ba ko?" Yayi murmushi ya ce "Da sun yi mini rauni, ai da baki ganni a haka ba"

Nabila ta ce "To Alhamdilillah, bari na je na kwanta na yi bacci a nutse, tun da kana lafiya"

Ya ce "Ki bar wayarki a kunne, za mu yi magana"

Ta jinjina masa kai ta bar su a wurin ta tafi, mama kuwa kamar ta bi Nabila ta na?a mata duka, ta kalli yadda Nasir yake wani sassanyan murmushi kamar shashasha, shi ma ji ta yi kamar ta kwa?e shi da mari, duk ?o?arin da take yi a kansa na nesanta shi da Nabila, abu ya ci tura.

Ta daure ta ce "Shiga ciki ka ci abinci, ka je ka nemi wuri ka kwanta".

"No na tsaya na ci abinci a hanya ma, sai da safe, gajiye nake kwanciya zan yi"

Major ya ce "To Allah ya tashemu lafiya" suka watse.

A galabaice suka koma mafakarsu, domin kuwa sun

Please Login or Register in order to submit comment