Reading KARFE A WUTA Chapter 65 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce "Kai bana son nu?u-nu?u, wanene ya biya ku?in?"

"Nima ban sani ba, management ne suka turo mini receipt, aka ce kar mu kar?i ku?inku, an yi settling bills ?in"

Nabila ta ce "Suwaye management ?in?" Yayi shiru yana kallonta.

"Malam kayi mini magana, ka tsare ni da ido, suwaye management ?in? Suwaye suka biya ku?in?"

Liti ya ce "Ki yi magana a hankali, kar ki janyo hankalin mutane kanmu"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ana bibiyarmu, wanda yake wannan abubuwan ya san duk wani motsi da muke yi"

Liti ya jinjina kai ya ce "Nima nayi wannan tunanin"

Nabila ta ce "Mu koma wurinsa, kafin mu san abun yi" suka koma in da suka baro Al'amin da walid da ?an mama.

Walid na ganin su ya ce "Yaya? Nawa ne ku?in?"

Nabila ta ce "Kar ka damu, an biya"

Tayi maganar tana zama a gefen Viper, ta tsurawa fuskarsa ido, kawai tuno yadda ya din ga kuka ta din ga yi, gaba ?aya jikinta ya ?ara sanyi.

Walid ya ce "Ba zaki ga likita ba, wurin da ya caka miki allura?"

Ta girgiza kai ta ce "Bakomai, ni yanzu ta lafiyarsa nake yi"

"Amma yakamata ki koma wurin aiki fa, ai muna tare muna kula da shi"

"No, ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba, ba zan iya aikin ba, bari na jira naga abun da hali zai yi"

Likita ya sake shigowa, yana duba Al'amin.

Ya ce "Alhamdilillah, ina ga ya samu bacci, dan ya farfa?o daga suman"

Nabila ta ce "Masha Allah" ji tayi ya ta?a hannunta, ta kalli hannunsa, ya yi mata alama ta matso.

Ta matsa ta kai kunnenta saitin bakinsa, a hankali ya ce "Ki gaya masa a cire mini wannan abun na hancina bana so".

"Haba master, baka ga yadda kake numfashi da kyar bane ba? Dan ya taimaka maka aka saka maka shi, dan Allah ka yi ha?uri ka ji, Allah ya baka lafiya"

Ya sake cewa "Ki ce musu bana iya bacci, yayi mini abun da zan yi bacci, kaina zai tarwatse"ta ?ago ta kalli likitan ta ce "Doctor, ya ce dan Allah ayi masa allurar bacci, so yake yayi bacci baya iya bacci"

Likitan ya ce "Ai mun yi masa, kuma da jinin ya sauka zak yi bacci mai yawa mai da?i in sha Allah"

Ta sake sunkuyawa, zata yi masa magana ya ce "Bana son baccin, ba na son jinin ya sauka, bani da rabon sake yin su, Allah ya nuna mini ranar da zan bi matata"

Babu wanda yake iya jin abun da yake fa?a, sai ita, muryarta na rawa take yi masa magana a hankali cikin nutsuwa.

"Haba Al'amin, mai babban suna, shikenan bawa ba zai yi imani da ?addara ba, tun da ka fuskanci kurakuran da ka yi a baya, ba sai mu nutsu mu nemi mafita ba, yanzu idan ka mutu ma?iyanka sun ci galaba a kanka kenan fa.
Dan Allah ina ro?onka ka janye wannan fatan da ka ke yi, kuma in dai muna tare in sha Allah zaka yi bacci mai da?i mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali trust me.
Wallahi i feel your pain, bani na tsinci kaina a halin da ka ke ciki ba, but ina jin zafi a zuciyata, in sha Allah you won't cry alone, an cutar da kai, in sha Allah kuma sai in da ?arfina ya ?are a kan ?wato maka hakkinka, in sha Allah sai nayi sanadin dawo da farincikin ka.
Amma sai ka yi ha?uri, ka yi ha?uri, kayi ha?uri na san da wahala, da ciwo, an yi maka illa, amma ina ro?onka a wannan karon kar ka jinkirta tuba, mu yi ta addu'a, Allah ya taimake mu, ka kwantar da hankalinka ka yi ha?uri, Allah da kansa ya rarrashi masu ha?uri a cikin Alqur'ani"

Yayi shiru yana sauraren Nabila, hawaye yana bin gefen fuskarsa.

"Madam ya kuma kike kuka, mu da muke son hankalinsa ya kwanta, jininsa ya sauka?"

Liti ya ce "Rabu da shi doctor, kukan shi ne samun afuwarsa, mun gode sosai da ?o?arin ku.

Cikin kalaman hikima, da tausasawa, ta cigaba da yi wa Viper nasiha, tare da bashi ?warin gwiwa, a kan cigaba da ha?uri, da kuma Addu'a.

Har bayan azahar, Viper bai gama frafa?owa ba, haka Nabila ta ha?ura ta tafi gida, bayan ta ajiye musu abincin da ta zo da shi.

Sai magariba ta isa gida, Allah ya sa Abba baya nan, balle ta sha tuhuma.

Message ne ya shigo wayarta, ta ?auka ta duba.

"Arfa dan Allah kar ki yi mini mummunar fassara, ki tsaya ki saurare ni mu yi magana, kin ?i ?aga wayata, hankalina a tashe yake, amma ki bani dama nayi miki bayani, dan girman Allah"

Har jikin Nabila yayi sanyi, kamar ta yarda da maganar Sumayya, sai kuma ta fasa, tayi mata reply da "No peace for wicked person, kar ki sake tunanin zan yarda da maganarki" ta saka lambar a busy, ta cigaba da sabgar gabanta.

Ta idar da sallar isha'i, tana zaune tana cin abinci, kawai Nasir ya fa?o ?akin, babu ko sallama. Ta ?aga kai ta kalle shi, amma bata ce masa uffan ba.

"Arfa"

"Na'am yaya"

"Ina ki ka je yau?" Ta ?aga ido ta kalleshi ta ce "Meyasa kake tambayata?"

"Ki bani amsa kawai"

Cikin ko in kula ta ce "Wurin aiki"

"?arya ki ke yi, me ya kai motarki hanyar ungoggo?"

Ta ajiye cokalin ta ce "Haba DSP, mutum nawa ne suke da vibe a birnin kano?"

"Ya ina magana kina nema ki raina mini hankali, wurin aikinki an ce baki je ba"

"Amma yaya ka san aikina ba na zama wuri ?aya bane ba, yaya ka ke yi mini tmbaya kamar ka ritsa ?ar ta'adda ne? Wata?ila harkar aiki ne ta kaini wurin, bibiyata kake yi kenan? Ko kuwa meyafaru ko rashin yadda ya shiga tsakaninmu ne?"

Ya sauke numfashi ya ce "Gaba ?aya kwanan nan kin canza Arfa, na je Division ?in ungoggo kan wani case, a hanya na ga motarki, dan lambar motarki ce"

"Abokin aikina ne ya ari motar, suka fita, ta sa ta samu matsala. Sannan kuma ni ban canza ba, kai ne dai ka canza mini kwanan nan, ni ban san me nayi maka ba, duk ka tsane ni, ka daina goyon bayan gaskiya, ni na fara tsoron ko kaima ka fara kar?ar cin hanci" tayi maganar tana ?a?alo kukan kissa.

Sai kuma ya kwantar da murya ya ce "No ki fahimce ni, ke ?in ce yanzu dole sai ana saka miki ido, kar wani abun cutarwa ya samar mini ke, ki yi ha?uri ki daina kuka" a haka ya ?uge da rarrashin ta, ta nuna masa komai ya wuce, yana fita tayi masa gwalo, tare da ajiyar zuciya.

Ta ?aukko wayarta ta ce "Bari na kira na ji ya jikin ?an marayan zakina" sai dai wayarsa a kashe, haka ta ha?ura.

***
Gaba ?aya ramma ta fita daga harkar Abdul, abun duniya ya addabe shi, gashi ya kasa gano in da mahaifiyar ta take, babban tashin hankalinsa kar ta gano cewar mahafiyarta ta ?ata. Dan bai san wane irin kalar bori zata yi masa ba.
Ga Indabo ya uzzura masa, dan har an kai masa ku?in aure, ga shirye shiryen takararsa na ta ?ara yin nisa, amma gaba ?aya hankalinsa baya kan takarar. Abokansa sai mita suke yi masa a kan duk ya canza, ga aurensa an saka su fara shiri, amma ya kasa mayar da hankali a kai, sun kasa gane kansa gaba ?aya.
Babu wanda ya tsaya saurara da bashi amsa a kan surutun da yake yi.

Yana zaune yana kallo, amma hankalinsa ba a kan kallon yake ba, tunani kawai yake yi.

Ramma ta ?araso kansa ta tsaya, ya ?aga kai ya kalleta, ya tashi zaune sosai ya ce "Rahama, ya aka yi ne?"

Ta ?araso ta dur?usa a kan gwiwoyinta, hawaye na bin fuskarta ta ce "Abdul yasar, dan son da kake yi wa Allah da annabinsa, ka mayar da ni gaban mahaifiyata, naga message a notification ?in ka, wai aure zaka yi, dan girman Allah ka mayar da ni wurin uwata da ?an uwana, na yadda zan ?arasa rayuwata, a rushen zan tattara ta na rayu, ba ma na saka ran zan zan yi aure, na yarda na rayu a haka"

Ya kalli ramma ya ce "Daga ganin message sai ki ce aure zan yi? Bincike ki ke yi mini kenan? To ni ba wani aure da zan yi ".

Cikin kuka ta ce "Ka daina yaudarata Abdul, ka rabu da ni, idan kana son iyayenka, na gaji, na gaji na gaji da ha?uri, da fatan zaka mayar da ni gida, ka ?yaleni dan girman Allah, ai ka gama morar abun da kake so zuwa yanzu, kowace irin ?ishirwa ce ka kasheta zuwa yanzu ka rabu da ni dan Allah " tayi maganar cikin ?aga murya.

Abdul ya kalleta a tsanake ya ce "Kin manta al?awarin da ki ka yi mini ne?"

"Babu wani al?awari da nayi maka, ni ban san wani al?awari ba, ka mayar da ni gida"

"Wallahi ?arya ki ke yi ki rusa maganar da muka yi da ke, da al?awarin da ki ka yi mini"

"Ka yi mini duk abun da ka ga dama, amma ni dai ka sakeni na koma gida, idan duk matan duniya ne ka je ka aura, ban damu ba, amma a yanzu tun da dai ka gama da rayuwata dan Allah ka rabu da ni"

Abdul ya tsura mata ido, yadda take kuka wiwi har da majina.

Ya saukko daga kan kujerar, ya zauna a gabanta ya ce "Rahama kishina fa ki ke yi"

Kamar zata kai masa mari ta ce "?arya ne, Allah ya kiyayeni ya tsare ni da kishin ?azamar halitta mara tsoron Allah kamar ka, ni kishin rayuwata nake yi"

Ya sauke numfashi ya ce "Zan mayar da ke, amma sai kin cika mini al?awarina, sannan kin haifa mini ?a sannan zaki koma gida, kin ga idan kika haihu duk duniya babu wanda ya isa ya raba ni da ke" yayi maganar yana share mata hawaye.

"Abdul ba zan ta?a yafe maka ba, na bar ka da Allah"

"Duk cikin kishina ne, matsayin matar da zan aura daban, naki ma daban, you are like my guest house, wurin hutawa ta da nisha?ina"

Jiki a sanyaye ta ce "Ka cuce ni Abdul, duk saboda ina 'yar talakan ?auye, mara gata mara galihu"

Ya girgiza mata kai, ya ha?e bakinsa sa nata, wata irin ajiyar zuciya take yi, a hankali ya cire bakinsa daga nata, ya kalli idanunta ya ce "Iya wuya rahama, ina tare da ke, ban ga wanda ya isa ya raba ni da ke ba. A lokacin da maza da yawa suke gudun matan da suka lalata, ni a dai-dai lokacin soyayyar yarinyar da na lalatawa rayuwa ta yi mini kamun kazar kuku".

Jiki babu ?wari ta cw "A hakan? Wace irin soyyaya ce zaka yanke mini farincikina ba tare da wani dalili ba, bana sonka Abdul ko ka?an"

"Ki saurari zuciyarki, kina jin zafin abun da nayi miki ne kawai, amma kina so na rahama, nima kuma ina matu?ar sonki"

"Da ban yi wa kaina, da mahaifiyata adalci ba, idan na fara sonka Abdul yasar"

"Zuciyar ki, cike da ?uruciya, kina ?o?arin sakawa kanki ?iyayyata ne ta ?arfin tsiya ne".

"Wallahi wannan ba so bane, ka gama lalata ni, ka samu abun da kake so, kuma ka ce sona kake, me yayi saura?"

"Kin san abun da na ?auko ki ki yi mini, kuma na daina kamar yadda ki ka bu?ata. Wuri ?aya nake kwana da ke nake tashi, amma na daure, ban sake yi miki ba, kuma na lazumci istigfari kamar yadda ki ka gaya mini. Kar ki sa?a al?awarinmu mana. Wa ki ka ta?a ganin ya lalata yarinya ya bita kuma yana so? Ke kin san waye ni a garin nan da ?asar nan. Na fiki shekaru, da ilimi da tarin dukiya, amma gaba ?aya na bar abun da yake gabana na tattara hankalina a kanki, ki yafe mini mana sweetheart, ki yarda ki so ni, zan goge laifukana zan kuma mayar da ke wurin mama in sha Allah"

"To yaushe?"

"Very soon, da zarar kin yafe mini, kuma kin cika mini al?awari"

Ramma ta share hawayenta ta ce "Abdul ta yaya zan haihu da kai, in kalli duniya in ce musu me? Baga mata nan zaka aura ba, ba sai ku haihu ba?"

"Naki nake so please" yayi maganar yana sumbatar goshinta, cikin tsananin so da shau?inta.

***

Yau ma uban sammako Nabila ta yi, ta tafi asibitin da Viper yake, sai dai ba ta ?auki motarta ba.

Yanzu ma ?an mama ta tarar, yana ta sharar uban bacci, babu liti babu Walid.

Viper kuma yana zaune, ya jingina da bango idanunsa a lumshe.

Murmushi tayi, tare da farin cikin ganinsa a zaune.

Ta ?arasa ta zauna ta ce "Yalla?ai, good morning, ya jiki? Alhamdilillah na ji da?in ganinka a zaune" sai dai kamar mai bacci, bai bu?e idonsa ba.

Hannunsa ta kalla, ?aya da drip, ?aya kuma kamar lazumi yake yi. Wani irin farinciki ya kama Nabila.

Wani ba?in abu ta hanga, a gefen pillown sa, ta saka hannu ta janyo, ta ce "Menene wannan, ko kayan da zaka canza ne?" Tayi maganar tana bu?ewa.

"Wannan rigarka ce?" Bu?e idonsa yayi ya kalleta, cikin wani irin zafin nama ya fizge rigar daga hannunta, ya hau waige-waige.

Ta ce "Menene? Meyafaru?"

Ya kalli in da ?an mama ya saki baki yana bacci, ya kalli taga babu hanyar shiga ko fita ta tagar, ya sake ?aga rigar.

Ba?ar riga ce shirt, mai ?auke da hoton tambarin dragon a gefen rigar, bayanta kuma an rubuta wasu alphabets, da bai bar Nabila ta karanta ba. Duk da jikinsa babu ?wari haka ya saka ?arfin sa, ya yayyaga rigar, yana cigaba da waige-waige.

Cikin rashin fahimta ta ce "Wai me yake faruwa ne?" Ya girgiza mata kai, ya sake jingina.

Nabila ta kalle shi ta ce "Akwai damuwa fa, jiya an yi settling bills ?in ka, sai dai bamu san waye ba, an ?i gaya mana ko wanene" ya ?ura mata ido, ta jinjina masa kai, alamar da gaske take.

"Dan Allah ka gaya mini, menene yake faruwa ne, bai kamata ka ?oye mini komai ba, tare fa zamu yi gwagwarmayar nan" Sai ya lumshe idanunsa ma, ya?i kulata.

"Haba master, yar suganka ce fa, talk mana" a hankali ya fara ka?a ?afa, amma bai yi magana ba.

"Sweetheart" ta fa?a tana dariya ?asa-?asa.

"Sweetheart magana nake fa" sai ya kwanta ya juya mata baya baki ?aya.

"Am sorry wasa fa nake yi maka, ya ?arfin jikinka to, ina fatan akwai progress, kana samun sau?i?"

Ya girgiza kansa alamar "A'a"

Ta ce "Ohh ni Nabila ina ganin mulki yau, Allah dai ya jaddada rahama da Fatima jauhar, ta yi ?o?ari sosai"

Ya ce "Amin" tausayin sa ne ya sake kama ta, ta ce "To tashi ka karya, na san yanzu za a zo yi maka allurai, kuma na san kana jin yunwa"

Bai yi magana ba liti ya shigo da leda a hannunsa, ya kalli ?an mama da yake ta bacci, ya dake shi da ?afarsa ya ce "Tashi, ?an asara, idan ma sace shi za ayi, kana kwance ka shanya baki kamar fatarin mata kana bacci" ?an mama ya tashi yana mutsutsuka ido.

Jauhar ta kalleshi ta ce "Ina kwana?"

Ciki ciki ya amsa, ya dafa Viper ya ce "Maza ya ne, ya jikin?"

"Alhamdilillah"

"To masha Allah, ga brush ?in da toothpaste, ka wanke bakin, yanzu Walid zai kawo abinci, sai ka yi wanka ka canza kaya"

Ya yin?ura ya tashi zaune, ya ?urawa ?an mama ido, sannan ya ce "Kai waye ya shigo ?akin nan jiya da daddare?"

"Likita ne, sai mai bada magani Nurse, sukenan"

"?arya kake yi"

?an mama ya ce "Wallahi suka?ai na gani"

Liti ya ce "Dama ya kwanta yana ta uban bacci, ya za ayi ya san me ake yi? Ina fatan ba wani abun ne ya faru ba?"

"Babu komai"

Da Al'amin ya shiga ban?aki, sai Nabila ta fita tana waya da barrister Habib, ya ce lallai yana son ganinta, Sumayya T ladan ta turo wasu mata, kuma zasu taimakawa aikinta a kan bunkure.

Nabila ta yamutsa fuska ta ce "Ka sallame su kawai, babu bu?atar na gansu"

"Kamar yaya, abu mai muhimmanci da ki ke nema, ki ce a sallame su"

"To ai nayi nisa ne, yaushe na bar abun da nake yi na zo"

"Ki bari koma menene ki taho yanzun nan" to kawai ta ce masa, ta ajiye wayar.

Ta cikin ni?abinta, take ?arewa asibitin kallo, wurin cashier ta sake zuwa, sai dai yau wata mace ce. Suka gaisa Nabila tayi mata bayanin abun da ya faru jiya, ta bu?aci ta dubo receipt ?in da aka turo musu na biyan ku?in, ta ciro ta bata.

Ta shiga computer ta duba, ta kalli Nabila ta ce "Ban ga receipt ba, kawai an saka bill settled"

"Ina ne ofishin MD, ko admin na asibitin nan, dole fa a nemo wanda ya biya ku?in nan"

Ta ce "Ba sa shigowa da wuri, amma maybe zuwa anjima"

Nabila ta juya ta koma ?akin Viper.

Ya canza kaya ya zauna a kan gadonsa.

Har walid ma ya zo, ya bu?e masa wainar shinkafa ta sha ?uli-?uli, yana lalla?a shi ya ci.

"Barrister har kin zo ashe?"

Ta ce "Eh oga Walid, na zo tun ?azu, naje likita ya duba ni, allurar da master ya caka mini jiya, hannuna ya sage" da sauri Viper ya kalleta.

Walid ya ce "Subhanallah, Allah ya sauwwa?e ya ?ara afuwa"

Ta kalli wainar gaban Viper, ta ce "Oga walid ?auke wainarka, na dafo masa abinci.

Ta janyo ledar viva daga ?ar?ashin gadonsa, ta bu?e food plask, ta ?aukko mini tea flask ?in ta, ta ha?a masa tea.

Faten dankalin turawa ne, ya sha ganye sosai da nama, sai ?amshi yake yi duk ya cika ?akin da ?amshi.

Ta mi?a masa shayin ta ce "Bisimillah ranka ya da?e, kaga tea ne, da ?uminsa sai ka samu cikinka ya warware, kaga tun jiya baka ci komai ba, ina fatan Allah ya baka lafiya da wuri, mu cigaba da aiki muna addu'a, in sha Allah sai mun dangana da nasara"

Ya ?aga kai yayi mata wani irin kallo, ta ce "Ba danni ba, dan Allah idan baka ci ba ba zan ji da?i ba, dan kai na girko na kawo maka. Lafiyarka na da matu?ar muhimmanci a wurina please mana, ka kar?a" ya mi?o mata hannu, ta saka masa kofin tana kallonsa tana murmushi.

"To yi bisimillah ka fara sha".

?an mama ne yake ta ?o?arin yin dariya, amma yana jin tsoro, ganin yadda aka bar Walid da busashshiyar wainarsa. Liti kuwa ?ya?yatawa ya din ga yi ya ce "Walid, mi?o mana wainar nan, mu ?addamar mata"

"Sannu maye, aikuwa ba zaku ci ba, ku ci kanku"

Nabila murmushi ta yi, ta cigaba da yi wa Viper hira, cike da tausayawa, da bashi ?warin gwiwa a kan ha?uri da ?addara.

Sannu a hankali yake cin abincin, har ya cinye tas, ya shanye shayinsa.

Wani murmushin ta sake yi masa, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin. Allah ya ?ara maka sutura da ingantacciyar lafiya, ya baka tsawon rai ya bamu nasarar ?aukar fansar abun da aka yi mana. Har cikin raina nake jin zafin abun da ya faru da kai, but before then. Please promise me ka daina z1y ły2ubar da hawayenka, wanda ka yi ya isa. Kuma kayi mini al?awarin ba zaka sake shan ?wayoyin da za su illata mini kai ba"

Liti ya tashi ya ce "Nikam nayi waje, wannan wace irin fitsara ce?"

"Ka kalleni mana dan Allah" ya ?aga kansa ya kalleta.

Duk da idanunsa sun yi mata nauyi, amma ta ce "Ka ce Nabila, nayi miki al?awari ba zan sake shan miyagun ?wayoyi ba, ba zan sake yi wa kaina allura ba, zan baki cikakken goyon baya in ?auki fansata ta hanyar da ta dace"

"Tashi zan kwanta" ya fa?a a ta?aice.

Duk wannan zubar da ta gama yi, ba su ne a gabansa ba, kawai ta tashi zai kwanta.

Ta fuskanci aiki ne jawur a gabanta, ba ta sare ba ta?i tashi, ta kuma ?i magana.

Ya ture ta, ya ra?a ya kwanta ya juya mata baya.

"Allah ya baka lafiya ya jaddada rahamarsa ga marigayyiya jauhar".

"Amin ya Allah, na gode" yayi maganar idanunsa a lumshe.

Tayi murmushi jin ya amsa, ba ya wasa da duk abun da ya shafi Jauhar.

Walid ne ya rakota, take ce masa "Ku yi ha?uri da wasu abubuwan da zaku ga ina yi, ina yi ne saboda sama wa ?wa?walwarsa nutsuwa, idan ba haka ba zai iya rasa hankalinsa baki ?aya"

Walid ya ce "Karki damu na fahimce ki, ki rabu da liti, ba kan gado ya cika ba dama".

***
Ramma na kwance a jikin Abdul, yana waya da mahaifiyarsa, tana yi masa magana a kan ha?a lefensa, ya ce su yi duk abun da yakamata, yau zai je asibiti ne, zai yi tiyata cikin dare, dan haka yayi busy. Ya kashe wayar, ramma ta motsa tana ?o?arin tashi ya ri?e ta ya ce "Beb, ina zaki kuma?"

Rai a ha?e ta ce "Na gaji da kwanciyar tashi zan yi"

Ya tashi zaune ya ce "Haba rahama, nifa duk wani motsinki ina gane me kike nufi, ai na baki ha?uri, kin san dalilin auren nan.....

"Ni cewa nayi na damu da aurenka? Ina ruwana ne ni damuwata na koma gaban iyayena"

Abdul ya ce "Zaki koma, amma sai Allah ya sa kin samu ciki kin haihu, am doing this for your own benefits, saboda ke duk nake haka".

"To bana so, ka daina"

"Haba sayyada, ba fa zina zan yi ba aure zan yi, kin ce in yawaita istigfari Allah zai yafe mini, to ke kuma kin ?i ki yafe mini, ki yi amfani da iliminki mana haba sayyada rahama"

"Ba wata sayyada, sayaddar da ka kafawa ?ahon zu?a sai ta haifi ?an shege ko?"

Kawai ya kama dariya, ya ce "Ke dai ba a iya miki, idan an yi nan sai ki yi can, anjima zan kai ki shan ice cream mu ?an fita mu zagaya".

"Ba zan je ba"

Ya ce "Shikenan huta roro, na ?auki amaryata mu je"
Tayi tsaki, ta sauka daga kan gadon, ta nufi toilet.

***Bunkure ta fito daga shari'a kenan, ta nufi motarta, ta tarar da Nabila a tsaye tana jiran isowarta.

Ta tsaya ta kalli Nabila, Nabila ta kalleta ta ce "Na je office ?in ki sau biyu, an ce ba kya nan, kin yi balaguro, da ki ka dawo kuma, bani da isashshen lokaci.
Ina son sanin in da ramma take, ita wadda aka yi wa fya?en, da shi kansa likitan da yayi documenting ya tabattar da an yi mata rape, ba wai takarda kawai ba.

"Ke, kin fara wuce gona da iri fa, kar ki bari na waiwayeki, nayi yin?urin ?aukar mataki a kanki"

"Wane matakin kenan? Harka ce ta aiki fa, idan kina da gaskiya menene na ?oye-?oye. Nayi mamakin yadda kina mace, once a rape victim, amma ki zama tsanin kare masu laifi. Na san kin ga shaidar da na gabatar a kotu, ta sautin muryar mahaifiyar ramma, kuma ko sama ko ?asa an nemeta an rasata yanzu. Shikenan idan kina ta?ama da kun saye lawyoyi da al?alai, ki shirya motsi na gaba da zan yi.
Sai na banka?o duk wani shu'umanci, da zalunci da ki ke yi, kuma ko a ina kuka ?oye ramma, sai na tona muku asiri, na tonawa wanda yayi mata fya?e asiri. Kar ki manta ?an hakin da ka raina....... Bata sake cewa komai ba ta tafi ta bata wuri.

Wayarta ta ?aukko ta tura wa Indabo message. "Yakamata ka motsa a kan yarinyar nan, ta fara wuce gona da iri"

Kasancewar ta sha zirga-zirga, a gajiye ta ?arasa office ?in su.

Wurin Barrister Habib ta fara nufa, tana zuwa ta tarar da Sumayya da wasu mata su biyu, a Office ?in Barrister Habib suna jiranta.

Suka gaisa da Habib, ta juya ta fice, zai yi magana, Sumayya ta ce "Bari na je na same ta.

Ta iske Nabila a office ?in ta, ta ce "Arfa, tun safe fa bayin Allah nan suna jiranki, har na zo nima, baki zo ba ina ki ka je ne haka?".

"Sumayya wai baki da zuciya ne, ala?a da ke ce bana so, na menene zaki din ga bibiyata kuma?"

"Nabila, dan Allah ki tsaya mu yi magana, mu fuskanci juna dan Allah"

"Babu wani abu da zan fuskanta, ni kin riga kin sire mini, ki fita ki bani wuri, ko ni baki wuri" Sumayya ta tsaya tana kallon Nabila.

Nabila ta zo zata fice, Sumayya ta ri?e ta, ta ce "Ni yakamata na fice na baki wuri, na san nayi kuskure amma yakamata ace ko sau ?aya kin saurare ni.
Tabbas ina bayar da duk wasu bayanai, da aka nema a kanki, amma ni baki san a wani hatsarin rayuwata take ciki ba, domin kare taki. Ni 'yar halak ce, zan daina

Please Login or Register in order to submit comment