Reading KARFE A WUTA Chapter 5 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

?aya a yanzu ji take yi, ba ta da wani ma?iyi idan ba ita ba.

Har sha biyu da rabi na dare, ba ta samu cikakken abun da take son sani ba, sai ma zarge-zarge da suka din ga ?arsuwa a ranta game da matar.

Saukkowa ta yi daga kan gadonta, ta fice daga ?akin, fita tayi can babban falo, ta nufi kitchen ta samu abun da za ta ci, dan yunwa take ji sosai.

Fridge ta bu?e, ta samu ruwa mai sanyin gaske, da coc ta fito falo tana sha.

Hasken fitila ta hango a baranda, ba a kashe ?wan wurin ba, ga abba kullum sai yayi magana a kan rashin kashe kayan wuta, kafin a kwanta bacci.

Wurin ta nufa, da niyyar ta kashe ?wan, ta na zuwa ta le?a, ta hango nasir a kan kujera, yana ta danna system.

Ta window ta je ta zura hannu, tana ta?a masa kunne. Caraf! Ya ri?e hannun ba tare da ya ?ago ba.

Tayi dariya ta ce "Shi ne ba ka tsorata ba"

"Me ki ke tunanin zai razana ?an sanda?"

Ta ce "Ai dai ?an sanda mutum ne, kuma na san ka ji tsoro mazewa ka yi"

Yayi murmushi ya ce "Tsoro sai lauyoyi"

Ta bu?e ?ofa ta fita ta zagaya in da yake ta ja kujera ta zauna sannan ta ce "Duk tsoron lauya bai kai ?an sanda ba"

Ya ?ago ya kalleta, sanye cikin kayan bacci pink, masu bargo kanta ko ?an kwali babu, tayi parking ?in gashinta"

Murmusawa yayi ya ce "Ke kin san babu tsoro ga wanda yake ri?e makami, yayi ya?i da ?arna"

"Hmm, yi dai a hankali, dan harshe ya fi makami dafi, kar lauyoyi su baka mamaki watarana"

"Ina aiki kin zo zaki dame ni, ina nawa aikin, ina kallabinki?"

"Yana ?aki" tayi maganar tana lashe murfin jarkar lemon hannunta.

"Kalli abun da ki ke yi kamar ?ar ?auye, sai an yi magana ki fara ke barrister ce, ke degree holder " yayi maganar yana mayar da hankali a kan system.

Ta numfasa ta ce "Wai aikin me ka ke yi ne?"

"Wani aiki ne mai wahala, wanda nasara a kansa, na iya sawa na samu cigaba a aikina".

Nabila ta ce "Haba dai, to Allah ya taimaka"

"Amin" ya amsa ba tare da ya kalleta ba.

Shiri ya wanzu na wani ?an lokaci, sannan ta ce "DSP"

"Na'am barrister"

"Sannu da aiki" ya ?ago ya kalleta ya ce "Kin isheni fa, za ki tashi ki bar wurin nan"

"Yi ha?uri, na daina magana"

Ya cigaba da aikinsa, ta na shan lemonta, tana jin yadda iska ke ka?ata.

Duk abun nan, Abba ta ?akinsa ya na hango su, sai dai ba ya jin me suke cewa.

Can ta sake cewa "DSP"

A hasale ya ce "Ke! Meye ne? Tashi ki je ki kwanta dare yayi"

"Ni na kasa bacci, raina ne a ?ace".

"Ai dama kullum cikin ?acin rai ki ke, tun da ke a rayuwarki ta duniya, baki da ha?uri tashi ki bani wuri"

Ta marairaice ta ce "To ka tsaya ka ji me aka yi mini mana, dan Allah kafin na tafi, ka gaya mini me zan yi, wanda zai saka na yi suna, kowa ya sanni" tayi maganar very serious.

Cikin gatse ya ce "Ki nemo in da Aminu Viper yake, ki taimaka mini na kama shi, kin ga sai ki yi suna, ni na samu cigaba a aiki"

Ta fuskance shi sosai ta ce "Waye shi, a ina yake? Kamar na ta?a jin sunansa"

Ya kalleta ya ce "Shi nake ta aiki a kansa, galibin aikin ta'addancin da ?an daba suke yi, a wasu shiyyoyin da saka hannunsa, yaransa ne. An ce lallai na kamo shi, tun da yankin da ake ?arnar ?ar?ashin kulawata yake akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison"

"Dan Allah idan na nemo maka shi, zan yi suna, kowa ya sanni?"

Kallon baki da hankali yayi mata, ya cigaba da abun da yake yi.

"Ka ga riba biyu kenan, na yi suna, kuma ka samu cigaba a wurin aiki, yes! Amma na ji ka ce akwai zarge-zarge a kan guduwa yayi daga prison how? Kun tabattar da hakan ko kuwa? Ka bani hints mana, laifin me ya yi a ka kai shi prison ?in?".

Takalminsa ya ?auka ya mi?e tsaye ya ce "Tashi ki bar wurin nan, tashi maza"

Da haka ya koreta, ta tafi ?akinsu. Sai dai da ga koma ?akinta, ta dinga sintiri a cikin ?akin, sosai ta ji maganar Yaya Nasir ta shiga ranta, ina ma hakan ta tabatta.

"In taimaka masa ya kama ?an ta'adda, in nemo ha?i?anin dalilin barinsa daga gidan yari, idan guduwa yayi me ma'aikatan suke yi, idan sakinsa aka yi laifin me yayi, aka sake shi duk da hatsarinsa, na banka?o ainihin identity ?in Naja'atu Bunkure, na gyara career ta, wai ma menene dalilin da ya sa ban zama ?ar sanda ba?, na zama wata lauya yau ka kare mai gaskiya gobe mara gaskiya.
Ta yi wani irin shu'umin murmushi ta ce "Accepted DSP Nasir, zan nemo maka Aminu Viper, na bibiyi laifin da ya aikata, da yadda aka yi ya bar prison.

Ayshercool.
08081012143


*?ARFE A WUTA*


AISHA ADAM (AYSHERCOOL)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

BRIGHT PENS SECOND BATCH.



5




Wurin shiru, ba ka jin motsin komai, hantsi yayi, yana zaune a kan wani dutse, yana jin yadda ?umin ranar ke ratsa shi, dan ba ta riga ta yi zafi ba, hannunsa ?aya ?auke da taba sigari, yana ta zu?a yana busawa, idonsa yayi jawur.

"Viper" matashin ya kira sunansa, yana ta sauke haki.

"Ina jinka" yayi maganar ba tare da waiwayawa, ya kalli matashin ba.

"An kama ?an mama da kayanmu fa jiya da daddare, a chamber yamma da gari, yana tsaka da raba kayan ga mutane, kuma wadda aka kama da yawa"

Ya saka yatsansa ya ?an daki jikin sigarin, tokar jiki ta zube, ya ja numfashi ya ce "Wace hukumar ce?"

"Masu ?waya ne"

Ya mi?e tsaye ya ce "Shikenan, kar ka damu, ku bar shi a hannunsu"

Ya waro ido ya ce "A bar shi, Ka manta a halin da ake ciki? Idan wani abu ya faru fa?"

Cikin takunsa na ?a??arfan namiji, ya ?arasa gaban matashin, ya ri?e kwalarsa a hankali sannan ya ce "Ba na butulci walid, ?an mama ni yake yi wa aiki, dole na fito da shi. Ni ba zan kamu ba, da zan kamu da basu bari na fito ba. Kuma ko a yanzu suna sane suka bar guzuma, suke harbin karsana. Ni na shirya a kama shi, sannan ina son ku je dabar Madaki, ko wurin da yaransa suke, ku tayar da hayaniya, ku zubar da jini, kar ku raga musu ko ka?an, ko da kuwa hakan yana nufin jami'an tsaro su kama ku"

Yayi shiru yana kallon viper.

Ya shafi sumar walid, da tayi cibiri-cibiri ya ce "Ya ka ke kallona kamar kana tantama a kaina?"

Ya risuna ya ce "Tuba nake mai gida, duk abun da ka ce dole ayi shi, umarninka muke yi wa biyayya"

"Good. Idan aka kama ku, ko da mutum ?aya ne daga cikinku, ku ambaci sunana, ku ce ni ku ke yi wa aiki, ni ne na saka ku. Ina sake jaddada maka, kar ku ragawa kowa a cikin su. Amma ku kiyaye ?a'idar aikina. Babu kisan kai, babu ta?a wanda babu ruwansa mata ko kuma ?anan yara"

Walid ya ce "An gama maigida"

" ?ace " ya furta a hankali.

Yau Nabila ko karyawa ba ta tsaya yi ba, haka zalika ko sumayya ba ta jira ba, ta tafi aiki.

Daga office ?in ta, tana hangen harabar chamber, ta ga isowar motar Barrister Bashir. Bayan mintuna talatin ta bishi office ?in sa, suka gaisa ya dube ta ya ce "?ar ?walisa ya jiki?"

Ta ce "Jiki kuma, ba ni da lafiya ne?"

Ya ce "Ranar da muka dawo daga court, kina ta tari har ki ka tafi gida, ko kin manta?"

Ta ce "A'a na tuna, na ji sau?i ai"

"Wai meyafaru ne a kotun, bayan na je na ga abokina, da na dawo na tarar da ke gaba ?aya ranki a ?ace, na tambayeki kin ce ba komai"

Nabila ta ce "Da ma fa dan bana jin da?i ne, ai ni ba zan manta da ranar ba, na ga masoyiyata kuma mudubina"

Barrister ya ce "Wa kenan?"

"Barrister Naja'atu, ina son matar nan sosai "

Yayi murmushi ya ce "Bunkure ki ke nufi?, mace mai hatsari kenan"

Ta waro ido ta ce "Hatsari kamar yaya?"

"No, kin san ba ta da wasa da aiki, duk shari'ar da ta saka gaba, sai ta ga bayanta, ke kuma gashi ba haka ki ke ba, ba kya mayar da hankali a kan aikin".

"Ai in gaya maka ganinta kawai da na yi, na ji wata irin ?warin gwiwa, na ji sonake na nutsu na mayar da hankali sosai a kan aikina. Sonake na bi footsteps ?in ta, nima na yi nasara kamar ita. Amma me ka sani a kanta da zaka iya gaya mini?"

Yayi murmushi ya ce "Nothing much, ki tambayi barrister Habib, ya santa sosai " sai da ta ji wani dummm! Yadda suke fa?a da barrister Habib, amma hausawa su ka ce ranar biyan bu?ata, rai ba a bakin komai yake ba, dan haka ta ce "To shikenan, na gode sosai ayi aiki lafiya". Ta juya ta fita tana nanata "Dangerous woman, zamu gani ai".

Ba ta zame ko ina ba, sai ofishin barrister Habib, ta tarar da shi da wasu client suna tattaunawa, ya ?ago ya kalleta ya ce "Meye?" A ?an hasale dan a ?ule yake da ita.

Ba tare da ta yi fushi ba, ta yi masa murmushi sannan ta ce "Wurinka na zo, amma bari na jira ka gama".

"Idan na gama ina da abun yi" ya fa?a a ta?aice.

"Dan Allah yaya habib ko mintuna goma ne"

"Na gaya miki ina da abun yi, fita ki bani wuri" tsayawa ta yi tana kallonsa, tare da tura baki, babu alamar ma za ta fita ?in.

"Ba magana nake yi ba?"

A shagwa?e ta ce "Dan Allah"

?aya daga client ?in ya ce "Barrister a taimaka mana, kar ta yi kuka"

Ya ce "Ta da?e ba ta yi ba, ba zaki fita ba?"

Nabila ta ce "Ya ka ke korata kamar wata kare ne? Na san ina yin laifi, ka yi ha?uri na shiryu ai"

Tsaki yayi, ya cigaba da rubuce-rubuce.

Ta tura baki ta fice, a zuciyarta ta ce "Ai ko da me ka ke yawo, sai na samu abun da nake son ji a wurinka"

Ta je ta samu MD, suka gaisa, sannan ta ce "MD, ka ga Barrister Habib ko, na je na bashi ha?uri, amma ya kore ni a gaban mutane".

Ya yi murmushi ya gyara gilashin fuskarsa ya ce "Anya ba wani laifin ki ka yi masa ba?"

"Ba laifi na yi masa ba, ha?uri na je ba shi fa, amma ya kore ni a gaban mutane"

MD yayi murmushi ya ce "Ai ke ?in ce ba kya ji, ya so ya koya miki aiki yadda yakamata, mussman yadda ki ke da faran-faran da mutane, amma ki ka ?i ba kya so, idan ya saka ki aiki ki ?i yi, dole ku din ga fa?a ai"

Nabila ta ce "Na daina fa, so nake na zama ?wararriya a kan aikina, ko dan farincikin Abbana, ku yi ha?uri"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan, Allah ya sa, ki je ki bashi ha?uri"

Ya ce "Bayan ya kore ni, yauwwa sir dan Allah ka san barrister Naja'atu Bunkure?"

Ya jinjina kai ya ce "Yes, she's famous a tsakanin lauyoyi, har ma da jama'ar gari ma, ai sananniya ce sosai"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Wow ina yin matar nan sosai da sosai, yadda take gudanar da aikinta, ya ?ara jan hankalina a kan aiki, ai mun ganta kotu a lokacin da mu ka je kotu last, ni da barrister Bashir, ?ar gayu da ita"

"Nabila, ke dai ki na son harkar gayu, amma ba gayun ba, ki mayar da hankali sosai a kan aiki, ki yi ?o?ari ki kamo ta, ko ma ki fi ta".

"In sha Allah, na yi maka wannan al?awarin but i need your support"

Ya murmusa ya ce "Kin samu, ?ari bisa ?ari, ?ar gidan major"

"Yauwwa to ka bawa barrister Habib ha?uri, zan koma team ?in sa dan Allah kar ya sake korata, mussaman a gaban mutane"

"To za a bashi in sha Allah"

Ta mi?e tsaye tare da fa?in "Godiya nake" ta fice ta bar office ?in cikin nisha?i.

"Bunkure na ki zai zo mini da sau?i, saura kuma Aminu Viper"

***
Major ya ?an tsurawa Uwargidan sa mama da ta tattare kwanukan da ya kammala cin abinci.

Ta ?ago su ka ha?a ido, ta ce "Ya dai?"

"Nasir"

"Me yayi?"

"Ki ja masa kunne, hawainiyarsa ta kiyayi ramata, na da?e da gane in da ya dosa, amma tun da kin da?ile abun, to ya ?ara nesanta kansa da ?a ta, kar ya kuskura in ji ko in ga wani abu da zai sosa zuciyata, kuma kar ya kuskura ya saka ta fara son shi, tun da ba ki amince ba, balle a jefa ta cikin yanayi mara da?i".

Cikin rashin fahimta ta ce "Amma major, wani abun ya yi ne?"

"Bai yi komai ba,gugar zana dai nake yi, idan ma yana shirin yin, to ya shiga hankalinsa" cikin mamaki take bin sa da kallo, tabbas idan aka ji major yana magana da kurman ba?i, akwai abun da ya gani, kuma ko me za ayi, ba zai fito yayi bayanin abun da yake nufi ?in ba.

****
Kamar ?arawo haka yake zagaye tilon matsakaicin gidan, wanda can nesa da gidan, kamfanunnunka ne, sai gonaki.

Cikin ?asaita yake tafiyar, yana yi yana duba ?aramar wayarsa mai madannai.

Kamar korarre, haka wani matashi ya ?araso in da yake tsaye.

Ya ?aga kai ya kalle shi ya ce "Menene labari, yaya aka yi ka fito?" Cak matashin ya tsaya, ya ce "Wai dama ba kai ne ka fito da ni ba?"

"Me zan tambaya idan na san komai?" Yayi maganar a ?an hasale.

"Wallahi master....

Cikin wata irin razananiyar tsawa ya ce "Kar ka sake kirana da wannan sunan"

Cikin tsuma ya ce "Tuba nake oga, su?utar baki ce, ban san waye ya fito da ni ba, kawai cewa aka yi na tafi"

Ya ?an yi shiru sannan ya ce "Kuma ka tabattar da ka gaya musu sunana, cewar ni ne me kayan?"

"Wallahi na fa?a musu"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan"

Ya ?aga rigarsa ya zaro wata shar?e?iyar wu?a, ya dan?a masa ya ce "Maza ka fasa cikin gari, unguwarmu, su walid sun tafi yaran Madaki zaku farwa babu sani babu sabo, idan an yi ram da wani daga cikin ku, ku ambaci sunana, ku ce ni ne jagoran aika-aikar, amma ku kiyaye ?a'idar aikina"

?an mama ya risuna ya ce "Umarninka ne abun biyayya a gare ni, an gama za ayi yadda ka ce" ya soke wu?ar ya juya, ya tafi da sauri yana ha?a hanya..

Cikin ?aramin gidan ya shiga, ya nufi ?akin kwanansa, ya kunna fitilar wayarsa, ya kunna ?wan solar, haske ya gauraye ?akin.

Ya saka mukulli ya rufe ?akin, sannan ya zauna yayi shiru tsawon mintuna, daga bisani kuma ya ?aukko wiwi ya na?a ta, ya kunna ya fara zu?a.

Madadin ya ji ?unci, da zafin da zuciyarsa ke yi masa, yana raguwa, sai ma wani irin ba?in ciki da matsananciyar damuwa da suka kawo masa ziyara.

Wani abu mai tsananin ?aci yake ?o?arin ha?iyewa, amma abu ya gagara.

Ya ?aga wiwin yana kallonta cike da ba?in ciki da takaici, yayi watsi da ita yana sauke numfashi.

Kamar mahaukaci ya zabura ya bu?e wata akwati, ya ?aukko kwalaben allura, ya farfasa ya ha?a, ya yi wa kansa, ya nemi wuri ya kwanta.

Bai fi mintuna goma ba, kansa ya fara barazanar tsagewa, ya fara kakari yana rirri?e kansa.

Duk yadda ya kai ga ?ara yawan doses ?in abun da yake sha, ba sa ?aukarsa, su mantar da shi damuwarsa, sai dai su wahalar da shi, shi a yanzu babban fatansa ya samu abun da zai yi amfani da shi, da zai goge masa komai na ?wa?walwarsa ya yi bacci mai nisan gaske.

***
Nabila ce tsaye a kitchen tana ta ciye-ciye, tana yi wa magajiya surutu.

Baba magajiya ta ce "Dan Allah Arfa ki yi mini shiru na ji radiyona, wai ni ya aka yi, ki ka tashi da sassafen nan ma"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Baba magajiya kin gane mai muryar nan kuwa?"

Baba magajiya ta yi dariya ta ce "Sumayya ce mana"

"Ashe za ki gane ta"

"Ka ji ?a, yau na sanku da ke da ita, da zan kasa gane muryarta"

"Ai in gaya miki baba magajiya, wata mata ce ta takura wa aminiyata, a wurin aiki, da iskanci kala-kala ga sumayya da son aiki, amma matar nan tayi ta ta?iyeta, ni kuwa na ce ta daina saurara mata wallahi,shi ne ma fa ake ba ta karanta rahotanni wasu lokutan, da experience ?in ta da komai, wata sokuwa ta cuceta, ta hana ta cigaba"

Baba magajiya ta ce "Ohh Arfa, ai maha?urci mawadaci, yawan fa?a ba shi da amfani"

Nabila ta ce "A'a fa baba magajiya, ni ma ba fa?a ne da ni ba, wula?anci ne ba na so, duk wanda ya wula?anta ni, sai mun yi fito na fito da shi".

Baba magajiya ta ce "A dai din ga ha?uri, tun da.... ba ta gama magana ba, Nabila ta yi wani irin tsalle ta ?auki radiyon, tayi waje da gudu.

Sashin mama ta fa?a, dan ta san tun da Nasir yana gari, lallai zai shiga sashen ta ya karya kafin ya fita.

Aikuwa a sashen ta tarar da shi, yana karyawa, su na hira da mama, da kuma sauda.

?aro volume ?in radiyon tayi, ta na yi masa nuni da ya saurara.

Rahoto ne a kan rikicin fa?an daba, da ya gudana a cikin ?aya daga manyan unguwannin kano, wanda tun goma na dare ake rikicin, har ?arfe sha biyu ana rigimar, ?an sandan sun yi nasarar cafke wasu daga cikin matasan, in da ?aya daga wanda aka kama, ya ce Aminu Viper ne ya aka su

Sai da suka kammala ji, Nabila cikin rawar jiki ta ce "Yaya Nasir, ba wannan ne wanda ka ke nema ba?"

Ya jinjina mata kai ya ce "Shi ne"

"Ka yi sauri ka tashi, ka je division ?in da aka tsare ?an daban, a baka su ka zurafafa bincike, gidan radiyon su sumayya ne, sai na biya can na sake samo rahoto".

"Ke!" Mama ta daka mata tsawa, har sai da ta ?an razana.

"Tashi ki bani wuri, yaya ina magana da shi, ba sallama ba gaisuwa babu neman izini, kawai ki zauna ki na surutun banza" Nabila ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Sauda ta ce "Dama mama yaushe za ta gaishe ki, tana abu kamar mahaukaciya"

Ta kalle su, ta kalli Nasir da yake wurin, ta ha?iye wani abu ta tashi, za ta fita.

Nasir ya ri?o hannun ta ya tashi ya tsaya, ya ce "Sorry barrister, na gode sosai da wannan gudunmawa, zan je division ?in, ki samo mini bayani a wurin sumayyan".

Ya kalli mama ya ce "Haba mama, kin san tana gaishe ki, tsananin zumu?in ta kawo mini labari ne fa ya sa ta manta, thank you Arfa ki shirya ki tafi aiki kar ki makara"

A ?ule mama ta ce "Wai kai har abada ba zaka yi hankali ba, dan ubanka ya zauna yana cewa in ja maka kunne, a kan shishshigin da ka ke yi mata, amma ina magana kana dizagani a gabanta" Nabila ta yi gaba ta fice a fusace, dan idan ta cigaba da tsayuwa, za ta iya aikata abun da zai hana kowa wuni cikin farin ciki.

Ya ce "Ni ?in kuma mama?"

"Kai ?in fa, ko ka shiga hankalinka, ko kuma duk abun da ya biyo baya kai ka so".

Sam sai ya ji maganar kamar maman ce, ta shirya kayarta dan ta saba, dan haka ya yi musu sallama ya fice.

A gurguje ta tsaya ta gaisa da Abba, ta fice cikin zumu?i, gidan radiyon su sumayya ta fara tsayawa.

Sumayya ta yi mamakin ganinta, ta ce "Hajiya lafiya ki ka zo mana wurin aiki da sassafe? Talla ki ka kawo ko cigaya?"

"?aniyarki na kawo" Nabila ta ba ta amsa.

Sumayya ta ce "Ai na san ke ungulu ce, ba kya jewar banza, ya aka yi uwar makara"

Nabila ta ce "Yau da safe kan na fito, na ji baba magajiya na jin program ?in ku na labaran ?arfe shida, bayan kin karanto naki, na ji wani rahoto na fa?an ?an daba, jiya a kano"

Sumayya ta ce "Eh meyafaru?"

"Kin je wurin ne?"

Sumayya ta zaro ido ta ce "In je in yi me?"

"Na ji an ce wai yaran Aminu Viper ne"

Sumayya ta ce "Eh to, ni ma haka na ji"

"Dan Allah ki tashi mu je asibiti, an ce an kama wasu, wasu kuma da aka yi musu miyagun raunuka suna asibitin koyarwa na cikin gari"

Sumayya ta ce "To wai ke duk menene ha?inki da hakan?"

Kamar Nabila za ta yi kuka ta ce "Sumy ban gaya miki ba? Yaya Nasir ne incharge ?in bincike a kan mutumin nan, kusan kullum sai an fa?i mugun aikinsa, ya tabattar mini da in dai na gano masa in da yake, ko na taimakasa ya gano zan yi suna sosai"

Cikin matsanancin takaici Sumayya ta ce "Tashi ki tafi ko na ?ura miki ashar, ?ar wahala, shi yaya Nasir ?in ne ya gaya miki haka? ?ar sanda ce ke? Su ma ya suka ?arke da su balle ke ki na mace, wallahi ba zan kai kaina ga halaka ba"

"Sumy ki gane, this can all help our career ki zo mu je mana"

"Wallahi ba zan shiga shirgin ?an daba su kashe ni ba, idan kin yi sunan uban me zai ?ara miki, za a binneki da shaharar ne idan kin mutu?"

Cikin ?o?arin son fahimtar da sumayya ta ce "Ba za a binne ni da shahara ba, amma atleast zan samu chances da zan iya fuskantar Naja bunkure"

Wata uwar ashar sumayya ta yi wa Nabila, ta tashi ta ce "Mahaukaciya, ai sai ki yi, ke da bunkuren ?an wahala"

Nabila ta tashi a fusace, ta ?auki jakarta ba tare da ta sake cewa sumayya komai ba, ta tashi.

Sumayya ta girgiza kai ta ce "Arfa Allah ya taro ki ya shirye ki, ya yaye miki ba?in taurin kai"

"Tun da kin ce ba zaki je ba, kar ki sake yi mini magana, kuma na gode"

"Eh ba zani ba, haka kurum a kashe ni a banza, mutanen da ba tsoron Allah ne da su ba, mutanen da suke shan ?waya tana gaya musu gaibu, su ?antarani biyu a banza ba da ni ba"

Nabila ta yi mata shiru ta fice.

Nabila ba ta yi tunanin komai ba, ta garzaya asibitin koyarwa, na cikin gari.

Ba ta wani sha wahala ba, saboda tana zuwa, ta tarar jami'an tsaro sun kewaye sashen emergency, ba wanda yake shiga ko ya fita.

Zagaye harabar wurin ta fara yi,tana neman hanyar shiga, da son tabattar da abun da yake faruwa a wurin, ta samu wata cleaner, ko meyafaru a in da ?an sandan suke.

Nan ta sanar mata da cewa, yaran da aka illata a wurin fa?an daba a daren jiya, aka kawo an hana kowa shiga ko fita.

Nabila ta yi mata godiya, ta yi mata alheri, ta nufi wurin da aka hana shigar da fita..

Ta ?arasa ta samu ?aya daga cikin jami'an tsaro suka gaisa, sannan ta nemi shiga, suka ce ba za ta shiga ba.

ID card ta nuna musu, amma ?aya daga cikin su ya ce "Madam nan ba prison bane, kuma ba police station ba ne ba, nan Asibiti ne, ki bari idan aka kai su can, sai ki je ki yi aikin ki".

Ta kwantar da murya ta ce "Dan Allah yalla?ai, ku bar ni na shiga, Ma'aikaciya ce nima"

"Get out from here" yayi mata tsawa.

Aikuwa ta hasala ta ce "A beg, don't shout at me, aikinka ka ke yi, nima nawa nake son yi, a kan me za ka yi mini tsawa?" Hankalin mutane ya fara dawowa wurin.

Sake hayayya?owa Nabila yayi, amma cikin dakiya da taurin kai, take mayar masa da martani.

Da ?yar aka rarrashi police ?in, dan cewa yayi sai sun tafi da ita station, wata?ila ma ?ar ?unar ba?in wake ce, ko ta na da ala?a da masu laifin.

Nabila ta ce "Ni za ka yi wa sharri, ki in ?unar ba?in waken zan kai, zan tsaya saurarku ne, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba".

Ana ta ?o?arin sasanta magana, amma Nabila ta ?i yin shiru.

Ta ciro wayarta, ta kira Nasir

Please Login or Register in order to submit comment