Reading KARFE A WUTA Chapter 71 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama Viper.
Gefe guda ga fargabar abin da Nabila za ta janyo musu, tun da ita ba ta so a zauna lafiya, yana matu?ar fargabar Indabo ya yi mata wani abun.

Gaba ?aya ta daina walwala, ko fitowa ta daina yi, sai idan fita zata yi, sai dai a kai mata abinci ?aki a ajiye.

Ganin ta takura kanta da yawa, Nasir ya sameta yana rarrashinta, da bata baki a kan ta jure ta kar?i ?addara.

"Ba wata ?addara da zan kar?a" tayi maganar tana hura hanci.

"Ke sa?o zaki yi kenan?"

Nabila ta ce "DSP, abun da Allah ya hukunta shi ne ?addara, ba abun da mutum ya ga dama yayi da son rai ko son zuciya ba, ko da me matar nan take yawo, sai na tona mata asiri wallahi, gara ma ka ?yale ni da wannan nasihar"

"Na ?yale ki, amma idan kin ?i ji, ai ba kya ?i gani ba, tun gashi yanzu kin fara ganin ma, amma ba wannan ba, wai haryanzu babu wani news da ki ka samo a kan Viper ne? Na ga duk kin yi sanyi, kin daina taimaka mini"

Ta kalleshi ta ce "Ba dole na yi sanyi ba, ai dama ka ce na daina saka kaina a abun da babu ruwana, dan haka wannan ma babu ruwana da shi"

Yayi murmushi ya ce "Haryanzu a fusace ki ke arfa, to ba ni ne dai Naja'atu Bunkure nan ba, amma yakamata idan da wani hints a taimaka mini"

Ta kalleshi ta ce "Babu wani hints, ban san komai ba"

"To shikenan, idan kin huce sai mu cigaba da maganar" ta harare bayansa har ya fice.

Kasa samun nutsuwa ta yi, ta sake ?aukar wayarta ta yi posting, "Idan har mahaifiyar ramma ba ?ata tayi ba, kuma da gaske Bunkure foundation na kula da ramma ne, to tana ina, al'umma yakamata su samu update a kan halin da take ciki, kuma shin suna da masaniya a kan ?atan mahaifiyarta? Idan eh to ina tafi? Tana tare da 'yarta ne ko kuwa?" Tayi posting ta nemi wuri ta zauna, lissafi da tunani daban-daban suka din ga kaiwa suna komowa a cikin ?wa?walwar Nabila.

***
"Indabo, yakamata fa ka sake matsa Abdul, ya gaya maka in da yarinyar nan take, hankali ya fara dawowa kanmu, yarinyar nan fa ta matsa, kuma ban ga alamar, zaka ?auki wani muhimmin mataki a kan ta ba"

"Ya ce mini ya kasheta"

Bunkure ta ce "Ya kashe ta ta yaya? A binciken da na yi, an tabattar mini uwar yarinyar ba ta garin nan, tafiya ta yi babu shiri, kuma Abdul ya je gidan fiye da sau ?aya, bayan ya ?auke yarinyar, me ya je yi, ni fa ba na son a din ga gaba ana baya, kar asirinmu ya tonu fa"

Indabo ya numfasa ya ce "Abubuwa sun fara caza mini kai Naja, ga takarar Abdul da nake ta fafutuka, ga auren nan da ake shirin yi na shi. Ga ?angaren ki taki matsalar, duk is a minus case, bababr damuwata yanzu Viper, aiken da ya yi mini ya tayar mini da hankali, idan ba a kama shi an kashe ba, hankalina ba zai ta?a kwanciya ba, ga ?an adawa sun sako mu a gaba, ga tunanin jafar da yake tsare na rasa wane tunanin ma yakamata na yi"

"Ai wanda ya fi muhimmanci shi zaka yi, wallahi idan aka cigaba da ?yale yarinyar nan, muna raina abun da take yi zata bamu mamaki fa"

Ya jinjina kai ya ce "Na ga alama, kuma ba zan ta?a bari hakan ta faru ba".

P.A ne ya kaste su, ta hanyar yin sallama, suka amsa duk suka ?ago suna kallonsa.

Ya kalli indabo ya ce "Akwai matsala fa"

"Again?"

"?warai kuwa, madaki ne ya yi aike, wai ya samu rauni a ?afarsa, yanzu haka ko iya tafiya ba ya yi, ?azu ya turo yaronsa har ya bu?aci a bashi ku?i ya je asibiti, amma wai duk wani abu da yakamata, yana da yaran da za su iya yi maka"

Indabo ya buga tsaki ya ce "Maganar banza kenan, zuwa yaushe zan cigaba da rarraba sirrina, wannan yayi mini aiki wancan yayi mini, kalli yadda haryanzu jarabar ?an tahaliki ?aya take ta ?awainiya da rayuwata. Na gaji ya je Allah ya kyauta, na nemi wata mafutar"

"Amma kana ganin watsi da shi, ba zai zame mana wata ?arakar ba ko barazanar ba?"

"Babu abun da zai zame mana sai wahala, tun da ba shi da wani amfani yanzu, Viper da na bari ya ci karensa babu babbaka, saboda yaron dodo ne, ina matu?ar jin tsoron abun da ya sani a kaina, kuma kamar yadda na yi tsammani, ya san abubuwan da idan yayi magana kashinmu ya bushe, dole fa a nemo Viper akwai matsala wallahi" yayi maganar yana zazzaro ido cikin tashin hankali.

Sai da aka kusa sati da yanke hukunci, sannan Nabila ta tafi wurin iyalan dattijon nan, tare da sake rarrashin su, a kan su yi ha?uri su ?ara mata lokaci, zata ?ara shiryawa sosai a appeal ?in da za su yi, tana saka ran za su yi nasara in sha Allah.

Suka yi ta yi mata godiya, sai da zata tafi, ?aninsa ya ke?e da ita, ya ?ara yi mata godiya, sannan ya ce "Dan Allah ki ?ara bincikar ?an uwana, kamar fa ya san wanda ya yi laifin, barazana aka yi masa Shiyasa ya kasa gaya miki komai"

"Barazana kuma, wace irin barazana?"

Ya ce "Eh, akwai ziyara da na kai masa, ya gaya mini amma ya nemi kar na gaya wa kowa, ya san sunan wanda yayi laifin, da ala?arsa da matar gidan, amma bai san ?an waye ba"

Ta ce "Ya salam, to amma meyasa ni bai gaya mini ba, babu yadda ban yi da shi ba a kan idan ya san wani abu, ya sanar mini, amma ya ce mini babu abun da ya sani, sunansa ma bai sani ba, kawai dai ya san ?an yayan matar gidan ne".

Ta ce "Subhanallah, shikenan zan san abun yi, a cigaba da yi mana addu'a"

Ya ce "In sha Allah, kullum cikin yi muku ake, Allah ya ji?an magabata mun gode sosai da sosai".

Tana kan hanya sa?on Viper ya shiga wayarta, a kan yana son su ha?u.

Ji tayi kamar ta maze ta?i zuwa, amma ina, ba ta ji alamar zuciyarta zata bari ta aikata hakan ba.

Garden ?in da suke ha?uwa, a can ta same shi, ta tsaya tana kallonsa ya rage sumar kansa, yayi kyau sosai.

Wata tab ta gani a hannunsa, cikin basarwa ta ce "Ina wuni?"

"Wayarki zaki bani"

Ta kalleshi ta ce "Wai baka san meya same ni bane? Baka jajanta mini rashin nasara da nayi ba, abu duk ya dame ni"

"Yanzu ki ka fara, idan har rashin nasara ba zai saka ki ?ara jajircewa ba, sai dai ki yi kuka"

Nabila ta ce "To idan ban yi kuka ba ya zan yi?"

Ya kalleta ya ce "Babu"

"Waye ya sai maka waya?" Yayi mata shiru.

Ta sake cewa "Haryanzu fa ina da tarin tambayoyin da baka amsa mini ba"

"Wanne daga ciki?"

"Meyasa Indabo ya ce zai yi maka tarko da ni ya kama ka? Ni meye ha?ina da kai?"

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Wata?ila ya san kina zuwa wurina"

"To amma ya aka yi haryanzu bai kama ka ?in ba? Kuma ni haryanzu kana ?oye mini wasu abubuwa"

Ya saka ?aramar wayarsa a kunnensa, ya ce "?an mama ya ake ciki?"

"Oga Viper, mun ?wamuso Lakwari fa, yanzu duk in da madaki yake, dole ya bayyana, tun da babu mai taimaka masa ko ya kula da shi"

Viper ya ce "Good job, zan gaya muku what next"

Cikin zaro ido Nabila ta ce "Viper kidnapping?"

"Eh ina son na sau?a?a miki aiki ne, shaidu na fara tattara miki, kafin a fara shari'ata, Madaki yayi jigatar da ba zai iya musa laifin da ya aikata ba"

"Amma ka gaya mini me ka ke yi da wayoyi? Ka daina yi mini ?oye-?oye. Sai kin zo kan shari'ata zaki ji koma me ki ke bu?atar ji"

Kamar shashasha haka take kallonsa, gaba ?aya ta ma rasa me za ta ce masa.

Ya mi?a mata wayarta ya ce "Angry bird"

"Am confused"

"Sorry"

Kamar ta sake fashewa da kuka ta ce "Zuciyata kamar a kurku, haka nake jin ta, mai laifi daban yana can yana rayuwarsa, mai kar?ar hukunci daban, wane irin abu ne wannan?"

Viper ya gya?a kai ya ce "Kamar dai ni a kwanakin baya, idan aka kama mai laifi, sai ayi musanye a saki wancan saboda ?an gata ne, ni kuma a tsare ni a matsayin mai laifin"

Ta ce "Kuma dai? Wani yayi laifi kai kuma a tsareka?"

"Mmm, a saka matata tayi ta yawo tana wahala ba, wata Shari'a sai a lahira, duk rintsi kar ki yadda ayi amfani da ke ki ci amana, ba kowa ne yake da zuciyar yafiya ba"

Jiki a sanyaye ta jinjina kai, ya ce "You can leave".

Kusan a tsukin lokacin, Nabila ta zama topic of discussion a social media, sai dai ba ta karaya ba, wurin cigaba da posting a kan bunkure foundation.

***
"Abdul tun muna shaida juna, ka gaya mini ina yarinyar nan take? Ka kashetan ko kuwa? Sannan uban me ya sake mayar da kai gidansu, bayan ka je ka ?auki yarinyar, kuma saboda hauka maimakon ka saka ayi? Kawai sai ka wanke ?afa ka tafi da kanka ka je ka ?auki yarinyar, kamar baka san matsayinka ba? Idan ka san uwar yarinyar nan ma, tana tare da kai, ka gaya mini, na san matakin da zan ?auka a kai"

Ya girgiza kai ya ce "Ni ban ?auki uwar yarinyar ba, ban san in da take ba"

"Da ka kashe yarinyar yaya ka yi da gawarta?"

Abdul ya ?an yi jimm sannan ya ce "Ruwa na jefa ta"

Indabo ya ja guntun tsaki ya tashi, maganganun da bokansa ya gaya masa ne suke ta yi masa kai komo a zuciyarsa, wai dutsen da ya gaya masa zai ci karo da shi, lokaci yayi da shi bai san ya za ayi ba, dole ayi ?ayan biyu, ko dutsen yayi nasara a kansa, ko kuma su yi mutuwar kasko, amma babu yadda za ayi, ya iya maganin dutsen nan da kansa.

Nabila fa ta sake jajircewa, da cigaba da ?o?arin gano bakin zaren matsalolin da take tunkara.

Bayan shari'ar ramma, akwai shari'oi da dama a gabanta, amma wannan c ta fi ci mata tuwo a ?warya, sai kuma ta Viper da zata fuskanta.

Kasancewar da sassafe ta je wurin aikin, duk babu mutane, ta shiga office ?in ta, ta ajiye jakarta, ta yi addu'a ta zauna, ta bu?e computer ta fara aiki.

?aurin wayar wutar lantarki ta fara ji, ta ?aga kanta, ba ta ga komai ba, ta sunkuyar ta cigaba da aikinta.

Wata irin ?ara wearing ?in office ?in ta yayi, ya fara ci da wuta, a razane ta tashi cikin tashin hankali, ta nufi ?ofa zata bu?e, ta ji an kulleta ta waje, ta jijjiga iya ?arfin ta, amma a ?ofar a kulle gam, ga wuyar wuta sai cigaba da ?ara take yi wuta na kamawa tana tarwatsi.

Da ?yar ta iya ?aukko jakarta, ta ciro wayarta, tuni ta fara gani dishi-dishi, saboda haya?i, tari ya turnu?eta.

Hannunta na rawa, lambar Viper kawai ta iya gani, ta danna.

Ya ?aga wayar sautin tarinta ya fara ji, tana ta yi ha?e da haki, da ?yar ya iya fahimtar ta ce "Wuta" daga nan ya ji ?if

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Cikin rashin fahimta, yake bin ta da ido, sai dai tamkar soko, har tayi maganar ta gama, bai iya tofa mata uffan ba, har tayi ta gama ta kar?i wayoyinta da system tayi tafiyarta ?aki.

?akin ta rufe, ta shiga duba call logs ?in ta, amma kaf ba ta ga kiran Viper ba, wani irin takaci ne ya turnu?e ta, wato duk sira?in nan da ta tsallake da kyar, bai kirata ba, balle ya ji a wane hali take ciki.

'To idan kuma bai san abun da ya faru ba fa?' ta tambayi kanta. Ta basar ta ce bari ta jira zuwa gobe, taga ko zai kira wayar.

?asan zuciyarta kuma ta din ga hamdala da Allah ya sa bai kira ?in ba, dan da ya kira Nasir zai ?aga ne, kuma ba abun da yayi masa zafi, zai iya gaya masa waye, idan ya tambayi waye.

***

"Naja wai ko ke ki ka saka aka yi wa yarinyar nan wani abu ne?"

"Wace yarinyar?"

"Barrister nan? Karofi ya kira ni yana yi mini kashedi, ina tsoron Allah ina tsoron shu'umancin mutumin nan"

Naja ta ce "Eh, ni na saka aka yi mata haka, dan so nayi ma ta mutu, na ga kai ka ?i mayar da hankali ka yi abun da yakamata, ba zai yiwu ta tona mini asiri a banza ba, mutuncina ya zube a idon duniya ba. Ba a ta?a samun wanda ya yi yin?urin kawo mini tangar?a ba, ka ?yale shi ka ke jan ?afa a kansa ba, sai a kan wannan yarinyar"

A fusace Indabo ya ce "wai meyasa ki ke haka ne Naja? Duk iya ?o?arin da nake yi a kan lamarin nan? Na gaya miki zata iya zama tarkon da zan kama Viper, kuma ina amfani da ita wurin yi wa yayanta barazana yake yi wa umarnina biyyaya, lokaci ?aya karofi ya bijiro, yake yi mini garga?i a kanta, wai sonta yake yi, wata?ila ma yi yake yi dan kawai ya muzanta ni. Amma gaba ga?i babu shawara, kin je kin aikata abu, kin saka yana ta kiran wayata yana nema ya tozarta ni"

"Nifa ban yi danasanin abun da nayi ba, kuma zan cigaba da bibiyarta sai na ga bayanta, ban damu da abun da zai biyo baya ba muddin zan tsira, kar ka manta kai ka koyar da ni hakan" ta kaste wayar tana jan guntun tsaki.

***
A gurguje Abdul ya yi breakfast a wurin ramma, yayi mata sallama ya fice.
Bayan fitarsa ta da?e tana kuka, kamar zuciyarta ta fashe haka take ji, saboda damuwa da tashin hankali, tun tana lissafin adadin kwanakinta a wurin Abdul, har ta karaya lissafi ya ?wace mata, tana matu?ar son sanin halin da mahafiyarta ke ciki. Ta sha attempting ta saka wu?a ta kashe Abdul, amma sai ta kasa, ita kanta ta sha yin?urin kashe kanta, amma tuna makomarta sai ya sanya ta fasa.

Gashi yanzu sam ba ta iya bujirewa bu?atar sa, rayuwa suke yi tamkar ma'aurata, ta yi kuka tayi istigfari amma da ya zo ya kalallameta da zance, sai ta bayar da kai bori ya hau, wasu lokutan idan ta kalli hidimar da take yi masa, ta gyaran gida, kula da abincin sa, yin wani abu da zai saka shi farinciki sai ta yi sai ta ji haushin kanta ya isheta.

Abdul kuwa Asibitin su doctor AK ya wuce, ofishin sa ya je suka gaisa ya ce "Kai ne zaka yi morning kenan?"

Ak ya ce "Eh ni ne your excellency kai fa zuwa yanzu ya ci ace ka ajiye Lab coat, tun da ana ta ?ishin-?ishin kai ne zaka zama lamba biyun garin nan, zaka koma field ?in dadynka"

Abdul ya ce "Nifa Ak ko lamba ?ayan ?asar nan na zama, ba zan iya daina aikin likita ba, ina gudanar da office ina consultation" suka tafa tare da kwashewa da dariya tare.

Ak ya ce "Sannu doctor excellency, ina ?anwar ka da kuka zo tare kuwa? Baka wani tsaya mun gaisa da ita ba, ko dan kar na ?yasa ka bani ita, ai ban ta?a sanin kana da ?anwa ba, na zata kai ne ?arami"

Abdul ya tsuke fuska ya ce "A wane room patient ?in take ne?"

"Ai ta uzzura sai da aka sallameta, amma Alhamdilillah jikinta yayi kyau sosai, sai dai ka yi mana ward round idan da abun da za a taimaka mana ayi mana" ya jinjina kai ya juya ya fice daga office ?in.

***
Tun bayan da ?an mama ya tabattarwa Viper an sallami Nabila daga asibiti, yake kallon wayarsa yake jiran kiran wayarta, amma shiru ba ta kira shi ba, har ya fara tunanin ko ?arya ?an maman ya yi masa da ya ce ta warke an sallame ta.

Shigowar Walid ce ta dawo da shi hayyacinsa, ya ?aga kai ya kalle shi, Walid ya ciro wu?arsa ya zareta daga cikin gidanta, ya kalli Viper ya ce "Lakwari da gaske yake, na iske madaki, ?afarsa ba ta takuwa, raunin da ka yi masa ya zama gyambo a ?afarsa, ga shaida harafin sunanka na zana masa a gadon bayansa, yadda shi ma ba za a kammala na sa labarin ba, dole sai an ambaceka"

Viper yayi kamar zai yi murmushi ya ce "Mai laya"

Walid ya ce "Na kiyayi mai zamani, Allah ya kiyaye mini kai ?an amanata"

Viper ya ce "Ina kewar wancan kwanakin, kwanakin da aka yi rashin ji da gaske, yanzu girma ya fara zuwa duk an daina wasu abubuwan"

Walid ya yi murmushi ya ce "Rashin jin ai duk ba na da?i bane ?an uwa, duk da kai ?ar madara ta fara saita mana kai, Allah ya kar?i kayarsa, amma duk da haka ba zan gushe ba ina jinjinawa Nabila, dan ita tayi abun da muka kasa, albarkacinta mun sake ganin walwala a tare da kai, duk da ba ta kai ta wancan lokacin ba"

"That angry bird, masifaffiya" ya furta yana kallon liti ya ji me zai ce.

Aikuwa kamar mai jiran ?iris hya e "Ba wata tsiya da ta tsinana masa, sai shegen naci da taurin kan tsiya, mara kunya da ita sai kayan ?aton kai kamar injin marka?e da ?wala-?walan idanuwa kamar an soya aya, ai wallahi 'yar madara duniya ce, ga kunya da girmama mutane, wannan tsagerar kuwa, tana zazzarewa mutane ido, ni har mamakin mai zamani nake yi wallahi".

Walid ya ce "Ai ita ce daidai da ku, daga kai har mai zamanin, mu da muka kasa iya masa, ita ai gata nan yana saurarenta"

"Ba wani nan, ni haryanzu ba gama yarda nayi da ita ba, yar le?en asiri ce"

Walid ya ce "To tayi le?en asirin, ai ba asirinka ta le?a ba ko?"

"Ware, ban da naga kuna ta tata, da sai na saka tsumagiya na ji?a mata jikinta, sai na yi mata mazinacin dukan da ba zata iya tashi ba, na rama muguntar da yayanta yayi mini a station"

Viper yana gefe yana jin su, wasu lokutan fa?an Walid da liti nisha?i yake saka shi, kamar sako da sako.

Nabila wuni tayi da waya a hannu, amma shiru babu kiran Viper, shi ma haka ne, wuni yayi yana kallon wayar ta sa yana sauraren kiran wayarta, amma ba ta kira ba.

***

Nasir ne zaune a ?akinsa, yayi zurfi sosai a cikin tunani, yana ta tuna wasu abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan sosai yake jin yana zargin Arfa tana aikata wani rashin gaskiya, da take ?oyewa, mussman da ya ji ta ambaci viper lokacin da ta farfa?o, ba zai yiwu a ce magagi ne kawai ba, kuma a yan kwanakin nan tayi watsi da lamarin cewa zata taimaka masa a kan nemansa balle ya ce tsananin saka abun a ranta ne ya sanya ta farko da sunansa, amma haryanzu yana son sanin dalilin da ya sanya Indabo ya ce zai yi tarko da Nabila ya kama Viper, menene ha?inta da shi?.

Nabila tana zaune a kan gado, tana waya da Alhaji Wada, sai kashe murya take yi, wai ita haryanzu ba ta warke ba, ya biye mata sai sangarta take yi, kamar ba babban mutum ba yana lalla?ata, tun da ya ce zai kuma zuwa gida dubiya ta ce masa ai ta warke ba sai ya zo ba.

Sallamar baba magajiya ce ta sanya tayi masa sallama, ta ?ago ta kalleta da murmushi.

"Yauwwa yar gari, ai dama zuwa nayi na tashe ki, ki samu ki karya ki sanya wani abun a cikinki, ashe ma kin tashi "

"Eh hajjaju, ina kwana"

"Lafiya lau, ya ?arfin jiki kuma?"

Nabila ta ce "Alhamdilillah da sau?i"

"To Allah ya ?ara kiyayewa, ki cigaba da addu'a Allah ya ?ara tsarewa, dama mu ma addu'a cikin yin ta muke babu dare babu rana, Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ki yawata fa?arta babu adadi, da yardar Allah ba dai mutum ba sai dai Allah"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Kin fa?a kin nanata mini, na da?e da haddacewa ai"

"Kya ci ?aniyarki da kin da?e da haddacewa, zamanin nan na yanzu waya ce miki ana zama haka? Kana da ido ba na ganin gari ba, Addu'a kake tu?uru iya yinka, baka san waye ma?iyin fili da na ?oye ba"

Sosai Nabila take dariya ta ce "Aikuwa ma?iyina yana ruwa, dan ni kaina ba wani cikakken saiti ne da ni ba in ji Abba"

"Ke ki yi addu'a kawai yar nan, tashi ki je ki samu abun da zaki ci" ta saukko daga kan gadon, ta fice falo tana mi?a, wayarta take kallo lokaci lokaci, duk kiran Viper take jira, amma shiru.

Sauda ta kalleta ta ce "'yar asara an fito"

Nabila ta ce "Wallahi kuwa, Allah ya nufa barka da safiya, bazawara uwar son banza ga gadonki ga na asara"

"Arfa, me ki ka ce?"

"Sauda kin sani sarai bana shiru idan aka gaya mini babu da?i, ni yanzu a kan tsini nake, magana ?aya mara da?i ki ka ya?a mini, sai na yi miki goma mai zafi, ba girmata ba Allah ya sa haifata ki ka yi" Sauda za ta yi magana, ta jiyo takun Abba yana saukkowa daga kan bene, dan haka ta ha?iye maganar ta, tana kallon Nabila.

***
Abbu ne zaune a gefen gadonsa, fuskarsa sanye da farin glashi, ya zubawa hoton hannunsa ido. Shi da Zahra'u ne, da sadik, shi kuma hannunsa ri?e da Al'amin, bai fi shekaru biyu ba a lokacin, sai dai fuskar nan ta sa tamau, babu alamar fara'a.
Murmushi Abbu yayi, tun Al'amin yana yaro baya son wargi, ba shi da faa'a, ya tuna yanzu a jikin hoton ba kowa sai Al'amin, shi ma ga yadda ya zama, rabon da ya saka shi a idonsa, tun fitowarsa daga prsion da ya zo masa nan, kusan shekara guda kenan.

"Wai meyafaru ne kamar kuka fa kake yi?"

Ya ?aga kai ya kalli rahila ya ce "Kuka kuma?"

Ta le?a ta kalli hannunsa, ta kwa?e baki ta ce "Kai ta wani abu kamar ?aramin yaro, ka ?auki hoto ka saka a gaba kana kuka, haba kai kuwa?" Yayi mata shiru bai ce komai ba.

"Abbu, dan Allah magana nake so mu yi da kai"

"Ina jinki"

"Dan Allah ka yi ha?uri ka yafewa Abba, ya koma kasuwa, sai raragefe yake yi a gari da shi da Nazifi, ina tsoron kar su fa?a wani mummunan halin, rashin sana'a ga matashi babbar matsala ce".

Ya ?are mata kallo ya ce "Rahila, nawa ?an ma da ya kangare, sallama shi nayi, ba zai yiwu in cigaba da jan ?arayi a jikina suna zalunta ta ba, su yi ta yawo babu sana'ar, ai uban su yana raye, ya nemi abun yi ya ba su"

"Ni kake kallon idona ka ke cewa yarana ?arayi?"

"Na fa?a rahila, ba ?arayin bane ba? Wane irin gata ne ban yi musu ba, ?arshe rashin lafiya na kwanta aka rasa wanda zai zauna da ni a cikin su a asibiti, ?arshe cewa ki ka yi kar na ga laifin su, ba hakkinsu bane ba, amma ni na ri?e su na ciyar da su, na kula da su, ni nawa hakkin ne? Yanzu nake ?ara danasanin biye miki, na wofantar da nawa ?an, kuma ki tattatara su gaba ?aya su bar mini gida, dan ba hakkina bane ba ri?on su"

Cikin takaici ta ce "Wallahi ba zan rabu da 'ya'yana ba, sai dai na tattara da ni da su mu bar maka gidan"

"Allah ya raka taki gona, ya tsare hanya"

Cikin fargaba ta kalleshi ta ce "Au babu ruwanka kenan in tafi baka damu ba?" Tashi yayi, ya ja tsaki ya mayar da takardun gabansa ya bar ?akin.

***
Nabila ta kasa jurewa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abun ne ya samu Viper, duk da bai fiye kiranta ba, sai da ?wa?w?waran dalili, amma shirun yayi yawa. Yau take shirye-shiryen komawa wurin aiki, Barrister Habib ya tabattar mata da an gyara office ?in ta, an canza mata wani.

Har ta shirya ta tsaya, ta kira lambar Viper.

Yana kwance idanunsa a lumshe, yana ?an ka?a ?afa, ya ji ringing ?in wayarsa.

Ganin lambarta sai da ya yi ajiyar zuciya, amma ya zubawa wayar ido, sai da ta kusa katsewa, sannan ya ?aga kuma yayi shiru.

"Hello Viper"

"Salamu alaikum" ya fa?a a nutse.

"Wa'alaikum Salam, kana lafiya?"

"?alau"

Cikin

Please Login or Register in order to submit comment