Reading KARFE A WUTA Chapter 3 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shekara ashirin da hu?u amma tana abu kamar yarinya ?arama. Tsaki yayi, ya tashi shi ma ya fice, ya ?yale ta, ta ci uban kukanta, ta kwanta a kusa da flask ?in Abincinta ta hau baccin gajiya.

A tsanake Nasir yake duba file ?in da aka bashi, a kan Aminu viper, da aka ce lallai ya kamo.
A record ?in da ya duba, ya gano zuwan Aminun gidan yari, ba sau ?aya bane ba, a kan mabanbanta laifuffuka da suke da ala?a da harkar daba, da ta'amalli da miyagun ?wayoyi.
Sai dai abun da ya ?aure masa kai, ba a shigar da dalilin da ya sanya, aka kai shi prison na ?arshe ba, an dai nuna ya aikata wani babban laifi ne, da ga cikin manyan laifuka da bai kamata daga lokacin faruwar abun zuwa yanzu ace an sake shi ba, haka zalika an cire wasu abubuwa masu muhimmanci da yakamata ace ya gani a cikin file ?in, sannan ga shi solomon Wada ya yi masa umarni da ya yi amfani da iya abun da aka bashi.

"To menene dalilin haka?" Ya tambayi kansa, a lokacin da kan na sa ya ?ara ?aurewa.

Sake duba file ?in yayi yana tunani, kamar ya ta?a duba wani case, makamancin record ?in da yake cikin file ?in, sai dai kamar sunan ba haka yake ba.

"Aminu Viper" ya sake maimaitawa.

Ayshercool.
08081012143
??*?ARFE A WUTA ??


AISHA ADAM AYSHERCOOL




3



Sama-sama Nabila ta ke jin hayaniya a kanta. Amma ta ?i motsawa.

"Ke Arfa" yayi maganar yana ri?e hannunta.

Tashi ta yi zaune tana bu?e idonta a kan Abba, a sanyaye ta ce "Abba ka dawo?"

"Na dawo, tun da na tafi ki ke kwance a nan, ko abincin ba ki ci ba?"

"Abba Yaya ne ya ce kana fushi da ni, dan Allah ka yi ha?uri ba zan sake ba"

Major ya ce "Eh ya kira ni ya gaya mini, na ha?ura tashi ki wanke fusarki ki zo ki ci abincinki" ta tashi ta shiga ban?akin falon, ta wanke fuskarta, ta zo ta zauna ta saka spoon ta fara cin abincin.

Ya numfasa ya ce "Rashin ji ne, ya yi miki yawa arfa, duk yadda na so na yi ha?uri sai kin ?ure ni, ban bi da?in abun da kunnuwana suka jiye mini ba, kina i?rarin zaki yi zaman kanki"

"Abba ka ce fa ka ha?ura, ba zan sake ba"

"To shikenan na ji, ci abincin"

Umma tayi sallama da flask ?in shayi, matarsa ta biyu, kasancewar yau girkinta ne.

Ta zauna a kusa da shi, ta ha?a masa tea, ya kar?a yana sha ya na yi wa Nabila hira, kamar bai yi fushi da ita ba, har ta ?an ware.

Kiran sallar magariba ne, ya sanya ta tashi ta bar ?akin, dan umma ta ji haushin zaman da Nabila ta yi, ita kanta Nabila ta so ba su wuri, amma Abba ya cigaba da jan ta da hira.

Da ya dawo daga sallar magariba, kai tsaye ?angaren mama ya wuce, tana zaune a falonta, da Sauda su na kallon tv.

Gyaran murya yayi, sannan yayi sallama, suka amsa suna yi masa sannu da zuwa.

Ba tare da ya amsa ba ya kalli Sauda ya ce "Sauda nan gidan waye?" Ta ?an yi turus tana kallonsa.

"Ki amsa mini"

"Gidanka ne Abba"

Ya ce "Masha Allah, idan ba zaki iya zama da ni, da tsarina ba, ko ki koma gidan tsohon mijinki, ko kuma ki fitar da miji ki yi wani auren"

Cikin damuwa Mama ta ce "Major me yayi zafi haka?"

"Ba?ar a?idar ki, da ta ara ta yafa, ba zan lamunta ba. Kun sani ba na ?aukar duk wani abu da ya shafi Nabila da sau?i, yadda na yi mata shamaki, da wanda ya zama katangar rayuwarta, dole na tsaya tsayin daka, na kula da ita kamar yadda na yi al?awari. Ba zan lamunci a cigaba da wula?anta mini ?a ba, har ta fara i?irarin za ta yi zaman kanta. Babu wani ?a da ya fi Nabila a cikin gidan nan, idan ki ka sake ce mata agola, to zaki fita ki bar mini gida ki nemi wani uban".

Cikin takaici mama ta a ce "Amma da kunnenka ka ji ta fa?a mata haka? Ka san dai makirci irin na yarinyar nan ko?".

"Kunnena ne ya jiye mini, ko zan yi mata ?arya ne?"

Suka yi tsur-tsur baki daya.

Ya ja guntun tsaki ya bar falon.

Yana fita sauda ta ce "Mama dan Allah sai yaushe Abba zai daina fifita yarinyar nan a kanmu, tun da aurena ya mutu bai ta?a yi mini gori ba sai yau, saboda ita?"

"Ba ke ka?ai ba, ni kaina yadda ki ka san na yi mata kucciya, duk ita ce matsalar gidan nan, amma zan kawo ?arshen komai da kaina, ki bar ni da su".

Nabila kuwa na ?akinta, itaka?ai, tana duba document ?in shari'ar da director ya saka aka ba ta, sai dai gaba ?aya ba ta da intrest a kan shari'ar, da ta gaji ma, ajiyewa ta yi ta hau waya da saurayi.

Wata matashiyar budurwa ce ta shigo ?akin ta ce "Wallahi Nabila abun da ki ke yi ba kya kyautawa"

Nabila ta ?an kalli Asiya, ta katse wayar ta ce "Da na yi me?".

"Kin saka Abba ya yi wa mama da Anty sauda kaca-kaca saboda ke, sai da Anty sauda ta yi kuka".

"To ai cewa zaki yi, Abba bai kyauta ba ni meye nawa a ciki?"

"Amma ke ki ka gaya masa ta ce miki Agola, bayan yayi musu mu ma ya iskemu a babban falo, ya yi ta yi mana fa?a".

Nabila ta ce "Ashsha, ai kin san ni bana kai ?ara, ko dai na ?auki mataki, ko kuma Allah ya saka mini da gaggawa"

Asiya ta ce "Ai shikenan, kowa yayi na gari kansa".

Nabila ta ce "Allah ya yaye miki Aisya, ke ma fa matar nan idan ta tashi karta miki wula?anci, ba saurara miki take yi ba, daga ke har umman, amma ku yi ta bin ta kamar wata shugaba, ni dai ba mai takani ban ?aga ?afar na karya ba"

"A'a ai ke ki ka ce, ke ki na da ma dogara"

Nabila ta yi tsaki, tare da furta "Allah ka aurar da ni na huta da wannan kacaniyar gidan, Ya Allah dogo mai gemu" ta fita daga ?akin tana addu'a.

Bayan kwanaki takwas.

A tsaye yake ?yam, kamar ?ofa, kasancewar in da yake a tsayen ba a iya ganinsa sosai saboda duhu, sai dai inuwarsa ta nuna dogon mutum, kakkaura.

Ya ?auki ?ankwali, ya ?aure kansa da shi, tare da na?o ?ankwalin ya rufe fuskarsa sai idanunsa kawai ya bari a waje.

Ya laluba hannunsa, ya ?aukko wata irin doguwar wu?a, ?angare ?aya zarto, ?aya kuma kaifi, ga ta da uban tsini, a ?alla za ta yi kamu uku, ya ?aga rigarsa ya soketa.
Ya sake ?aukar wata ya soke a jikin wandonsa.

Yanayin takun da yake kawai, ya isa ya tabbatar da?a?arfa ne, saboda yadda ?asa ke amsa takun nasa.

Bayan wasu awanni, duhun dare ya ?ara yi, sahu ya ?auke, sai haushin karnuka ko ina.

A ?ofar wani gida ya tsaya, ya din ga waige-waige, ya tabattar da babu kowa. Tamkar ?an biri, haka ya cafke katangar gidan ya dira ciki.

Ya saka mukulli, ya bu?e wata ?ofa a cikin gidan da duk ta yi ?ura, ya bu?e ta ya kutsa kai ya shiga ciki.

Tsayawa yayi ya kunna fitilar wayarsa, yana haske ?akin, take ya ji wani abu mai tsananin ?aci ya fara kaiwa da komowa a ?irjinsa, ya ji numfashin sa na barazanar barin ?irjinsa.

Jikinsa ne ya fara rawa, ya ji tamkar hankalinsa zai gushe, ya dur?usa a wurin yana wani irin haki, cike da wani yanayi na mai shirin fita hayyaci.

Hayaniya ya fara jiyowa a waje, hakan ya saka shi mi?ewa tsaye babu shiri.

Cikin sauri ya fito daga ?akin, ya kama katanga, ya le?a, sai dai yana le?awa ya ga ?an ?ato da gora da miyagun makamai, sun fara taruwa a kewayen gidan, kasancewar akwai hasken farin wata, kuma akwai hasken ?wayayen solar hakan ya bashi damar ganin makaman da suke hannun su.

Babu tsoron komai, ya haye katangar, ya hau saman roofing gidan, ya dira ta wani ?angaren, jin sautin dirarsa, ya sanya suka rufa masa baya, ta in da suke jiyo sautin gudunsa har da karnuka su na kururuwar a tare.

Sai dai duk da wannan ?ira da Allah ya yi masa, ta siffar ?arfi ba ya jin nauyin jikinsa, ya din ga dukan ?asar da dukkanin nauyin jikinsa, ba su ankara ba, ya ?ace musu ?at kamar wal?iya.

A bakin titi suka tsaitsaya suna haki, su na mayar da yadda aka yi.

?aya daga cikin su ya ce "Anya yaron nan, ba da layar zana yake amfani ba?"

"Ba wata layar zana, tsohon hatsabibi ne kawai, ni na yi mamaki ma da ya gudu ai, da da ne fa, wallahi sai ya illata ku kan ya gudun. Ai kamar yadda na gaya muku ne, da na ji alamun ya zo, zan kira ku a waya na sanar muku, ai ba zan sake sukuni ba sai ya je hannu, na za ta ma zaku kira ?an sanda ne"

?aya daga cikin jami'an sintirin, ya ce "Ko zamu kira ?an sanda, mu yakamata mu fara hu??asa mu kama shi, sai mu mi?a musu shi, wannan gudun nasa yaushe muka kira ?an sanda ma"

"Amma duk da haka, yakamata su san yana zuwa ai"

Shugaban su ya ce"Muddin suka sani, canza taku zai yi, ba zai sake zuwa ba".

Malam lawan da gidan sa ne a jikin gidan da yake zuwa ya ce "In ji wa? Ba zai ta?a iya daina zuwa gidan nan ba, yadda ka san ya binne asiri a ciki, kodayeke sai ta yiwu ma asirin ya binne, wannan hatsabibancin nasa akwai lamarin sihiri a ciki, amma zan cigaba da saka ido, da ya zo zan kuma kiranku"

"To shikenan malam lawan mun gode, yanzu ka koma gida, bari mu koma bakin aiki, ko kuma a raka ka ne?"

"Ahha haba, kamar ba namiji ba, ba wani abu bari na koma, ai ya riga ya gudu" Suka yi sallama ya nufi layinsu.

Sai dai yana daf da ?arasawa gidansa, kawai ya ji an yi ball da shi, kasancewar sa ?an ?aramin mutum, sai jin sa yayi, ya yi sama ya dawo ?asa kamar wani karmami. Ya tashi a gigice yana zaton ko gamo yayi da aljani, ya hau waige-waige.

Haske shi ya yi da fitila, sannan ya ce "Kwana da yawa malam lawan, tsohon butulu, da na ?yale ka ban yi maka komai ba, shi ne ka cigaba da yi mini bita da ?ulli?"

Cikin kwakwazo, da tsananin razani ya ce "Na tuba, na bi Allah na kuma bi ka, dan Allah" kan ya ?arasa, ya karya shi ?aras, ta hanyar saka ?afa, ya yi masa wani irin duka a ?afarsa ?aya.

Malam lawan ya a kurma ihu, cikin tsananin zafin nama, ya cire hular kan malam lawan,, ya tura masa a baki, sannan ya ciro wu?ar ?ugunsa ya yanke shi a damtsensa, aikuwa jini ya ?alle.

Ya dur?usa a gaban sa ya ce "Yanzu ai ka ji da?in bayar da rahoton zuwana, ragon maza kawai" ya tashi tsaye ya ja da baya ya ?ace a cikin duhu, ya bar shi a mawuyacin hali, ga karaya ga yanka, gashi kuma ya toshe masa baki.

Ko da ya koma gidansa da yake zaune, ciro wu?ar da ya yanki malam lawan yayi, yayi jifa da ita. Ya tsaya yana haki, abun da ya yi al?awarin dainawa, yau ya yi, ya zubarwa da wani jini.

Ya dafe kansa yana huci cikin tsananin damuwa.

**
Yau sumayya ba ta ha?a tafiya da Nabila ba, dan da wuri sosai ta fita, za ta shiga asibitin murtala ta duba wata yayar babansu da aka kwantar a emergency, za ta kai musu abinci.

Su na tafe da mai adaidaita sahu, ta hango mutane na ta shiga su na fita a wani layi, duk da lokacin gari bai gama hasken da za ace, mutane suna wannan tururuwar ba.

Da sauri ta tsayar da mai baburin, ta biya shi ku?insa, ta sauka, ta nufi layin da mutane ke shiga su na fita.

Wurin duk babu mata, sai maza, amma hakan bai hanata kutsawa da son gano abun da yake faruwa ba.

Tsayawa ta yi ta tambayi wani magidanci, abun da yake faruwa. Ya sanar da ita, gawar wani yaro aka tsinta, a bayan ma?abartar unguwar, an yanke masa al'aura da wasu sassa na jikinsa.

Jikinta na tsuma ta cigaba da kutsawa tana fa?in "Ku matsa, ni ?ar jarida ce" tare da nuna musu id card ?in ta.

Ta ?a??auki hotunan yaron, sannan ta tsaya tattaunawa da mutanen da suka fara zuwa su ka tarar da abun.

Sai kiranta ake yi a waya, ana jiran ta kai abinci, amma sai da rana ta ?aga sosai, aka gama komai ?an sanda suka zo, sannan ta yi shirin tafiya, shi ma sai da ta kar?i lambar wayar wani ?an sanda, da zimmar zai din ga ba ta update na sakamakon binciken da za su yi, a kan gawar.

Ko da ta je asibiti ta sha fa?a,na rashin kai musu abinci da wuri, ko a jikinta, saboda ta samu rahoto, dan haka tana ajiye musu abincin, ta yi waje.

Sai dai ba ta fito daga emergency ba, ta din ga jin ihun wani babban mutum, kamar mara gaskiya, haka ta koma tana le?awa ta ga abun da yake faruwa.

Magidanci ne, ake yi masa ?inkin wani uban yanka a damtsensa, jikinsa yayi kaca-kaca da jini, duk da ana ta yi masa allaurar kashe zafi, amma sai ihu yake yi.

Babu neman izni, ta afka ciki ta ce "Sannu bawan Allah, ka yi ha?uri Allah ya baka lafiya, ka daure"

Duk sauka waiwayo su na kallonta, har da ma'aikatan, mutumin ya ce "Na gode sosai"

Ta ?ara matsawa ta ce "Amma hatsari ka yi ne? Kodayeke wannan ai yankan makami ne ba hatsari ba"

Ya ce "A'a wani ?an daba ne, ya sare ni jiya cikin dare, dama hukuma ta da?e ta na neman sa"

Sumayya ta gyara tsayuwarta ta ce "Subhanallah, bawan Allah a wace unguwa ce haka? Ko rigima ku ka yi da shi ne?" ?anin malam lawan da yake tsaye a wurin, a fusace ya kalli sumayya ya ce "Dalla malama fita, mutum yana fama da kansa, kin zo ki na yi masa wasu surutan banza"

Ta ce "A'a Allah ya baka ha?uri, ka sani ko akwai wani taimako da zan iya yi masa. Kalli saran da aka yi masa fa, idan ba za ka damu ba, zan na?i muryarka, mu saka a radio, ko Allah zai saka, hukuma su bi maka ha??inka, barin su da ake yi suna cin bulus ya sanya suke cigaba da ?arna".

Malam lawan ya ce "Ke rufawa kanki asiri, hatsabibanci da ta'addanci yaron, ya wuce tunanin ki"

Sumayya ta zaro wayarta, za ta yi magana, sai ga wasu mutane guda biyu sun shigo da wani kaki a jikinsu, da ba ta san na menene ba, suka mayar da ?ofar ?akin suka rufe.

Malam lawan ya kalle su, ba su ne ?an sandan da aka kirawo suka tsaya masa, likitoci suka zo kansa ba ne.

Sumayya ta yi tsilli-tsilli da ido, ?aya ya ?irga mutanen da suke cikin ?akin, da likita ?aya, nurse ?aya, sai ?anin malam lawan da sumayya. Dan duk ma?wabtan da suka kawo shi, sun tafi wurin sana'oin su. ya ce "Ku biyar ne a ?akin nan, idan ka sake mu ka ji labarin sunan wanda ya yi maka wannan raunin, to za ka maye gurbinsa da ya bari na gidan yari, dan haka ka ja bakinka ka yi shiru".

Sumayya ta ce"Ban gane ba Yalla?ai, mutum mai laifi kuma ace kar a fa?i waye? Ba ka ga irin illar da aka yi masa ba ne, ga karaya ga rauni, da ya kashe shi fa?"

Ya ba ta amsa da "Da ya kashe shi, bakinki zai iya sakawa, ki ?auki hukuncin da za ayi masa na kisan" daga nan suka juya suka fice.

Mamaki ya mamaye sumayya, ta ce "Kai kuwa bawan Allah, waye wannan shi kuwa, da har jami'an tsaro masu kaki, za su hana bayyana laifinsa, ana sane aka ?i kama shi kenan?"

Malam lawan ya ce "Ba zaki ja mini masifa ba, ki fita ki bar wurin nan, na ji da masifa ?aya, bayan ?inkin nan a karye nake wallahi"

Cikin tsananin naci, da son samun rahoto, ta kwantar da murya za ta lalla?a shi, ta samu labari, amma da likitan da ?aninsa suka koreta daga ?akin.

Fitowa ta yi, tana ta mamakin abun da ya faru, yaya za ayi hukuma ta bawa mai laifi kariya, wane irin abu ne haka?.

Ba ?aramar makara ta yi ba, amma tunanin abun da ya faru, ya fi ?aure mata kai.

***
Sannu a hankali yake yi wa kansa allura, yana yi yana fatan samun abun da yake so, a hankali ya gama ?urawa jijiyarsa ruwan allurar da yake fari tas a cikin sirinji, bayan ya kammala tsaf ya fara jin kansa yana yi masa nauyi.

Take idanunsa suka yi mitsi-mitsi, ya soma lan?wasa kansa, yana jin idanunsa kamar za su fito waje, suna yi masa yaji, a haka ya kunna sigari, ya kashingi?a, ya na bawa sama haya?i,yana jin yadda jikinsa ke son bijirewa aikin allurar.

Wayarsa ce ta fara vibrating, ya mi?a hannu, ya ?aukkota ya duba, yana zaton ko a cikin yaransa ne, sai dai ya ga private number ce.

Har zai ?i ?agawa, sai kuma ya ?aga ya saka a kunnensa, amma bai yi magana ba.

Daga cikin wayar aka ce, "Meyasa ba ka gajiya da neman magana ne? A wannan karon ma sai da ka saka na yi abun da na goge ?arnar da ka yi, yakamata ka nutsu Aminu"

Ya saki haya?i, tare da ?an ka?e tokar da sigarin ta tara, sannan ya ce "Waye kai? Sannan waye ya saka?"
Mutumin yayi dariya, ya ce "Mutum mai ba ka kariya, domin cimma nasa muradin, yakamata ka sau?a?a mini aiki, ka daina aikata abubuwan da za su din ga barin trace a kan ka".

"Ka yi muguwar kasadar ?o?arin cimma burinka da mutum irina, kar ka manta viper ake yi mini la?abi da shi, macijin da ya fi kowanne hatsari, idan ka bari na sare ka, ka gama yawo" yana gama maganar ya cillar da wayar, ya ?ata fusaka kamar ya fashe da kuka.

Cikin fusata ya ce "Ni again? wani ya kuma amfani da ni? Impossible zan watsa dafina a in da ya dace da in da bai dace ba, sai na tabattar da danganawa ga kunyar ?arshe, ko da kuwa za ayi mutuwar kasko" ya yin?ura da nufin ya tashi tsaye, amma ya kasa sarrafa gangar jikinsa, hakan ya tilasta masa komawa ya nemi wuri ya kwanta.

Duk da irin fa?an da sumayya ta sha a wurin aiki a kan makara, bai dame ta ba, jikinta sai tsuma yake saboda ta zo da rahotanni masu muhimmanci da ?aukar da hankali.

Ofishin head of news ta je, ta shiga da sallama.

Matar ta ?ago ta amsa mata da ?yar, ta ?arewa sumayya kallo, ta ce "Yanzu ne lokacin shigowa aiki ko? Gaba ?aya yaran yanzu ba kwa ?aukar aiki da muhimmanci, kodayeke karatun ma ba wani na kirki ku ka yi ba, duk da satar amsa ku ke gamawa. Ki shiga hankalinki kafin na kai maganar nan wurin MD"

Sumayya ta risuna ta ce "Afuwan anty, in sha Allah ba zan sake ba, na samu wasu rahotanni ne masu muhimmanci, da ya san na tsaya a hanya, shiyasa na makara na kawo miki a tantance ne ko za a saka su a news"

A yamutse matar ta ce "Na menene" cikin farinciki da jin ?warin gwiwar ta yi abun arziki ta fara da gaya mata abun da ya faru a asibiti.

Amma matar sai cewa ta yi"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya zamu saka wannan shirmen a news?"

"Anty ai a rahotanni, ko a janyo hankalin hukuma.... "Dalla yi mini shiru, business mu ke yi a nan mu, ke fa iyayinki da rawar kanki yayi miki yawa sumayya. Meye hujjarmu idan aka tsutsiye mu, cewar hukuma na ?oye mai laifi?"

Sumayya ta ce "Wallahi a gabana aka yi, mutumin yana nan a emergency"

"Kin ga idan ba ki da abun fa?a, fita ina da abun yi"

Sumayya ta yi iya ?o?arin ta, ta danne abun da yake taso mata na fushi ta ce "To shikenan, sai kuma akwai abun da na gani, ina kan hanyar tahowa nan, a nan wajen gari, an tsinci gawar yaro an cire masa wasu sassan jikinsa".

"Almara kenan, wa zai yadda da wannan zancen?"

"Ba zance ba ne ba, na yi recoding ?in maganar wasu daga mutanen da suka fara cin karo da abun".

"Sumayya, ba irin wannan labaran mu ke bu?ata ba dan Allah, je ki su murtala sun fita neman rahotanni, ki din ga kawo sensitive abubuwa"

Summaya ji tayi wata irin ashar na kai komo a wuyanta, da take ?o?arin narkawa matar nan, ta rasa abun da ta yi mata, haka kurum ta tsane ta. Ta yi ta kyararta ba ta son ta ga tayi wani abu na cigaba.

Sumayya ta fice daga office ?in kamar ta yi kuka, ta koma reception ta nemi wuri ta zauna.

Ba uwar da ta tsinana a aikin yau, tun da head of news department ta yi mata wula?anci.

Kasancewar a makare ta je, ya sanya lokaci yayi gudu, Lawisa, wato head of news ?in, ta din ga shiga tana fita, ta na kaiwa tana komowa, idan ta kalli in da Sumayya take sai ta ha?e rai.

Wannan karon bayan ta fita, a tare suka shigo da managern director, sai karairaya take yi masa, tun da ya shigo ma'aikatan suke ta gaishe shi.

Ban da sumayya da ?acin rai ya saka ta cika ta batse.

Sai da yayi gyaran murya ya ce "Wannan ba sabuwar staff ?in mu ba ce? Ya na ganki a nan? Wane department aka kai ta ne?"

Lawisa ta yi caraf ta ce "Sir ba ta da ?warewar aiki ne haryanzu, ana ?an nunnuna mata aiki ne, kafin ta gama gogewa".

Ya ce "Ok, babu laifi" sumayya kamar ta kwa?awa lawisa mari, a fusakarta da ta sha uban bleaching, duk tayi taruwar jini.

Ta daure ga gaida MD, sannan suka wuce gaba.

Tsaki Sumayya ta ja, tana duba wayarta.

Sai dai jin sallamar Nabila a reception ya sanya ta ?ago da sauri tare da amsa mata.

"Ya na ganki a nan?"

Nabila ta ce "Ke baki iya karrama ba?o ba ko?" Ta tsaya suka gaisa da admin ?in da ke reception, sannan ta ?arasa kusa da Sumayya ta zauna.

"Arfa, ya na ganki yanzu ne? Lokacin tashi daga aiki bai yi ba?"

"Kema ya na ganki a nan kamar mara galihu, ke baki da office ?in da zaki zauna ne? Ki zo chambermu ki ga ofishin da aka bani hajiya, kamar wata sarauniya"

Sumayya ta ce "Eh ofishin da baki damu da aiki ba ko, sai sun dawo da ke gadin chamber tukuna".

Nabila ta yi dariya ta ce "Kin san wani abu, wai nan aikena aka yi, zan je na lalla?a na zo da wata mata, ko in tattauna da ita, sannan in je shagari firm, zan ha?u da wani lawyer, kuma ni wallahi kaina ciwo yake yi"

Sumayya ta kalleta ta ce "Ba zaki ba kenan?"

"Ai fa?a ma ?ata baki ne, sumayya wurin nan naku mai kyau, tashi ki rakani na zaga" duk da ran sumayya babu da?i, amma ganin Nabila ya sanya ta jin sanyi a zuciyarta.

Suka shiga zazzagawa, ta kaita news room, sai dai su na bu?ewa suka tarar da MD da lawisa a ciki, suna aiki.

Sumayya ta risuna ta ce "Am sorry sir, ban san ku na ciki ba, Arfa mu je ki ga....

"A'a tsaya mana na ga nan ?in, Nabila ta shiga cikin fara'a ta ce "Yalla?ai ina wuni?"

Shima cikin fara'ar ya ce "Lafiya ?alau, ya ki ke?"

"Lafiya lau sir, ina fatan ba zan takura muku ba, ina son sanin abubuwan da ban sani ba a rayuwata, mussaman wanda ba field ?ina ba, sister ina wuni?" Tayi maganar tana kallon lawisa da ta yi bala'in ha?e rai.

Lawisa ta takurawa Sumayya ne, saboda tana ganin ?ar gayu ce, ga ta ba?a amma ba?inta mai kyau ga ?wazo, tana gudun ta ?wace mata matsayin ta, kuma ita bazawara ce, a da a wurin babu wanda ya kaita gayu a wurin, amma yanzu sumayya ta fita.
Yanzu kuma ga Nabila, ita da take da hasken fata ma sosai.

Nabila ba ta san lawisa ta amsa ko ba ta amsa ba, ta ja kujera ta zauna, tana yi wa MD tambayoyi, a kan abubuwan da suke cikin news room ?in.

Lawisa ta ?ulu,ta din ga

Please Login or Register in order to submit comment