Reading KARFE A WUTA Chapter 20 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ri?e shi ya ce "Umarni nake baka, ba shawararka ko ra'ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai ku?in aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ?a ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke"

A fusace ya ce "Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka da?e da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ?acewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke bu?ata, amma ba zan iya ba.
Ka sani ina ta'amalli da miyagun ?wayoyi, da gaske zan iya kashe ?ar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ?ara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ?auki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan ra?ar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ?aya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi al?awarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ?auki nauyin zunubin".

Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya ri?e masa riga, ya saka kai ya fice.

Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu.

Gaba ?aya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fi?e sai farar fata da idanuwa.

Ma?wabciyar su ta din ga cewa "Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari ma?erin budurci ya gama ?ere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamsha?in ya dace"

Anty ta ce "Wannan ma hamsha?in ne".

A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwa?e-kwa?e suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki.

Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matu?ar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ?oye mata.

Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ?asa ce, cikin ?akuna babu floor, sai dai an yi plasta a ?akunan, falo ?aya da ?akuna uku a ciki, kowanne da ban?aki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma.

An yi wearing ?in wutar lantarki, a gidan.

Sai buhunhuna, aka shimfi?a a ?asa, sannan cikin ?akunan aka saka leda, falo kuma aka shimfi?a carfet, saboda duk tur?aya ne.

Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci.

Sai kujerunta, ?an gida masu kyau, ?aki ?aya an saka furnitures, ?aya kuma sai aka saka ?atuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau.

Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai ta?a ganinta ba, kuma ba ta ta?a ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta.

Dogon gashinta ba?i, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da ba?i.

Haka kurum take tuna Alhaji mu'azzam, a ha?uwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure.

Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba.

Su liti suka lura da shirun Al'amin ya ?ara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci.

Walid ya ce "Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa" tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba.

Ya karkace ya ?aukko invitation a aljihunsa, ya mi?a wa walid.

Wani irin ihu walid yayi, ha?i da kururwa, yayi katantanwa a ?asa ya kuza uwar ashariya.

Sannan ya ce "Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa".

Sauran matasan da ke wurin suka mi?e suna tambayar Walid ko lafiya?.

Ya mi?a musu invitation ?in, take suka hau shewa suma, suna dara.

Kawai ya dafe kansa, yayi shiru.

Walid ya ce "Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka ta?a kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci"

"Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban ta?a yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shai?aniyar matar ?ar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai ha?ani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ?aya"

Walid ya zauna kusa da shi ya ce "A'a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke ri?e da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin da?i, idan yayi maka baki ?ara watsewa zaka yi.
Duk da lokaci ya ?ure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka haya?i, abun farin ciki ya same mu" ya ?arasa maganar suna shewa, ban da Al'amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga.

Hatta kayan da Al'amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al'amin, dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa.

?arfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye.

Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu ala?arsa da Abbu za ta ?ara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba.

Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka za?i a aura masa oho.

Ana tsaka da walimar haya?in, fa?an daba ya kaure, Al'amin kuma ya koma gefe ya ?i magana, ?an sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ?an unguwar suka kai wa jami'an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ?aurin auren da bai san wacece matar ba.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



Hanyar da ta bi ya bi da kallo, yana tunanin a ina ya ta?a ganin fuskarta.

A ransa ya ce "Mahaukaciya ce kenan, Shiyasa aka aura mini ita, haukana ya fi naki" ya fito daga falon ya saka takalmansa ya fice.

Jauhar kuwa dur?ushewa tayi, ta ?ora hannunta a ka ta ce "Na shiga uku" a take ta fashe da kuka ta ce "Allah ka sanya mafarki ne ba gaske ba, Allah ka sa ba wannan ne mijin nawa ba? A gabana ya kashe wani, Allah Ubangiji ka rufa mini asiri ka dube ni, ya Allah ka dubi maraicina da ?angin da na baro, ka sassauta mini a nan, ya Allah ka sa ba shi ne mijina ba". Ta cigaba da addu'ar tana kuka, ta kasa fitowa sai ma ?ara sakata da ta yi a ?akin tana kuka.

A take komai ya dawo mata fes, yadda ta ganshi, ya yi kisan kai, hannunsa ri?e da mutum da wu?a a gefen cikinsa.

"Na shiga uku, ko biyoni yayi ya kasheni, me na yi masa wallahi ban gayawa kowa yayi kisa ba" tayi maganar ?asa-?asa tana kuka.

Ko da wasa ba ta yi yin?urin, sake bu?e ?ofar nan, a ban?akik nan tayi alwalar magariba da ta isha'i, ta kasa addu'a komai, sai fatan Allah ya sa ba wannan ne mijinta ba.

Ba ta sake fitowa ba, har garin Allah ya waye.

Zaman ?akin ya isheta, fitowa kuma ta gagareta, sai da ta le?a ta ga babu kowa a falon, bakinta ?auke da addu'a ta fito.

Ba kowa, ta le?a tsakar gida, ya rufe mata ?ofar, babu taklmansa kuma a wurin.

Ta dawo falon, ya cinye taliya da man da da ta zuba masa tas, ya ajiye komai a wurin, hatta wadda ta ?an zube a ?asa bai kwashe ba, jug ?in ma daban kofin jug ?in daban.

Ta kwashe komai ta fitar tsakar gida, ga sauran kwanukan da ta fara wankewa ta bar su a wurin, komai yana nan.

Sai zuciyarta ta fara raya mata, ai ba shi ne mijin nata ba, ya shigo ne kawai ya tsorata ta, sai ta cigaba da addu'a Allah ya ?ara nesanta ta da shi.

Ta yi 'yan gyare-gyaren ta na gida, yaran da suke shigo mata, yau ba kowa duk sun tafi makaranta, ga tsakar gidan wasu irin manyan ?adangaru suna bin bango, dan haka fitowa tsakar gidanma wahala yake bata, saboda tsoro.

Ta datse gidan, yadda babu wanda zai shigo sai ya bubbuga.

A jere ta sake jera kwana biyu ba ta sake saka shi a idonta ba, akwai ranar da bai kwana a gidan ba. Bai sake dawowa da rana ba, sai cikin daren nan, idan ya tarar da abinci ya zauna ya cinye abun sa, kafin ta tashi ya fice.

Abun ya fara damunta, ga tsoron gidan take ji, sosai da sosai.

Wajen la'asar ta ji ana buga ?ofa, ta din ga tambayar waye, amma ta ji shiru.

Har zata ha?ura da bu?e ?ofar, ta zata ba kowa, aka kuma buga gate ?in maimakon ?ofar da ?arfin gaske.

A tsorace ta bu?e, aikuwa ya hanka?o ?ofar, ta kuma kurma ihu, ta kwasa da gudu, ta shiga kitchen ta rufe ?ofa.

Sororo ya tsaya yana tunanin, ihun me take yi dan ta ganshi? Ya basar ya shiga ya yi abun da zai yi ya fice.

Sai a yanzu ta fara gazgata lallai wannan ne mai gidan, shi ne mijin da aka aura mata.

Cikin kuka ta ce "Allah komai ka yi dai-dai ne, Allah ka sanya shi ne mafi alkhairin da nake ta fata". Ta sanya wa zuciyarta za ta yi ?o?arin, danne tsoronsa da take ji, amma abun da ba ta gane na shi ne, ba iya abun da ya faru waccan ranar ne kawai yake ba ta tsoro ba, tsananin kwarjinin sa ne ke ?ara rikita ta.

Suna dabarsu, Al'amin yana ta shan sigari, Walid ya ce "Maza, gaskiya abun da ka ke yi baya dacewa, an kai maka mata, amma kullum kana nan kana cakewa, akwai matsala ne?".

Al'amin ya rausayar da kai ya ce "Yarinyar Mahaukaciya ce ashe"

Cikin rashin fahimta ya ce "Mahaukaciya kamar yaya?".

"Kamar yadda na gaya maka, ihu take yi itaka?ai"

Walid ya ce "Ko dai tsorata ta ka ke yi? Ki tsaya kun yi magana kun gaisa?"

Aminu ya ce "Da wa?"

"Da amaryar mana" ya ja tsaki, yana mayar da sigari bakinsa.

"Wallahi Aminu da ni aka yi wa auren gatan da aka yi maka da na more, haba baka kyautawa gaskiya "

Yayi masa shiru, ya?i ko kallonsa, dan ko zancen auren ba ya son ji, haka kurum ji yake yi kamar an yi masa dabaibayi.

Saifu kuwa yanzu ban da gaisuwa, babu abin da yake ha?a shi da da mama da Baba, dama Babar su hafsa Zakkyya ba shiri suke yi ba, ko kallo ba ta ishe shi ba.

Sai dai sun fara zancen a kawo 'yar aiki, dan duk yawan 'yan matan gidan nan, ba sa iya aikin gidan, girki sai dai a jagwalgwala, wani ya ciwu wani ba zai ciwu ba, gidan nan kuwa wasu lokutan kamar fadar mahaukaciya, dama jauhar ce ana ?atawa tana gyarawa, yara na cire kaya suna zubarwa tana kwashewa, amma yanzu bata nan babu mai gyarawa.

Baba kuwa ?asan zuciyarsa yana nadamar auren da ya yi wa jauhar, amma ba zai iya nuna hakan ba, ya du?ufa yana yi mata addu'ar samun kwanciyar hankali a gidan aurenta.

Cikin dare da ya dawo, ya ji gidan a rufe, bai tsaya jiran komai ba, ya kama katanga ya dira kamar ?arawo.

Gaba ?aya jauhar a zatonta, itaka?ai ta kwana a gidan, saboda ba ta ji bugun ?ofa ba, ta fito tana ta share-sharenta, ta ?ora ruwan zafin dafa makaroni, saboda su yaya saifu ya sayo mata, taliya makaroni, mai maggi sugar da sauransu.
Ta fara bin ?akunan tana gyarawa. Sai dai ta din ga jin warin taba, ta rasa daga ina take jin warin.

Kawai ta nufi ?akin da yake ciki, ba tare da ta san yana ciki ba, ta afka, a zatonta ita ka?aice a gidan.

Yana kashingi?e yana zaune yana ka?a ?afa yana shan tabarsa, ya zazzage kayansa a kan katifar ?akin, ghana must go ?in, ya cillar da ita a tsakar ?akin. Har da takalma a kan katifar, soson wanka da brush duk suna kan katifar.

Ba wannan ba kawai, har da ledoji da kwalayen taba, ga tokar maganin sauro ko ina.

Kamar mahaukaciya haka ta juya, ta ?iba da gudu, sai dai a wannan karon, rufa mata baya ya yi, ya cimmata, tana ?o?arin rufe ?ofar ?akin da ta shiga, ya hanka?a ?ofar ta fa?i jikinta na wata irin tsuma.

Ya zuba mata ido, wanda ya haddasa mata tsuma da karkarwa cikin razani da matsanancin tsoro.

Bai ce mata komai ba, sai cigaba da kallonta da yake yi.

"Dan Allah ka yi ha?uri, wallahi ban gayawa kowa ka kashe shi ba, dan Allah ka yi ha?uri, ni matar aure ce, ka daina shigo mini gida" tayi maganar wani irin gumi na tsatstsafowa daga fuskarta.

Ya sunkuyo saitinta, warin sigarin da ya sha, tana dukan hancinta, sai a lokacin ya gane ta, ya gene a in da ya ta?a ganinta.

"Kin ganni na kashe shi?"

Ta jinjina kai alamar eh.

"Mahaukaciya ce ke? Ki na da ta?un hankali ne?" Ta girgiza masa kai alamar a'a, tana ja da baya.

"Idan ki ka kuma ganina, ki ka gudu kina ihu" ya zaro wu?a a ?ugunsa, ya nuna mata. Sannan ya ce "Sai na yi miki abun da ki ka ga na yi wa wancan mutumin, wato in kashe ki"

Ta girgiza kai ta ce "In sha Allah ba zan sake ba" ya mi?e, ya mayar da wu?arsa ya fita ya bar ta.

Wani irin numfashi ta din ga saukewa, cike da tsoro, ta ?ara gazgata cewar, shi ?in ne dai mijinta ba wani ba.

Ta jima a wurin tana kuka, sannan ta tashi a hankali, ta sake komawa ?akin da ta gano shi.

?akin yana nan, kamar mahaukaciya ta bu?e dealer, ya watsar da komai, sai warin sigari ?akin yake yi.

Ta ?a??aga labulaye, ta zo ta dur?usa ta fara ware kayansa, wankakku da masu datti, ta kwashe takalmansa, ta jera masa a bayan ?ofa, wankakkun kayansa, ta shirya su a cikin wardrobe, marasa wankin ta fita da su, ta share ?akin tsaf, ta ?auki brush ?in sa da toothpaste, ta kai masa ban?akin cikin ?akin, da bokiti da buta.

Kayanta akwai turarukan wuta, da aka bata na gudunmuwa, sai dai ba ta da gawayi, dan haka ta kunna na tsinke, ta sassaka a ko ina, saboda korar warin sigarin nan. A cikin kayan sa ta ga wata Mp, ta ?auki mp ta kunna ta ji tana yi, ta kunna radion jiki, ta ji tana yi, ta fita tsakar gida da ita, tana ta aikace-aikace, da zummar kan ya dawo ta kashe ta ajiye masa, ta ?an ?ebe mata kewa, ta manta ko sallama baya yi kafin ya bayyana.

Gidan su jauhar, akwai ma?wabciyar su Anty lubabatu, tana tausayinta sosai, suna mutunci da juahar, dan idan ta haihu, jauhar ta yi ta zuwa gidanta, dan ta ?auki yaranta, ita ce ta ha?ata da 'yan gidan su, take kar?ar shirin dutse tana yi.

Tun washegarin kai jauhar, ta shiga gidan ta ce wa su mama, a bata mutum ?aya ya rakata gidan jauhar, amma suka ce ba wanda ma ya san gidan.

Jauhar kuwa, ta gama aikinta tayi wanka, gidan babu komai na abinci, sai taliyar nan da macaroni da yaya saifu ya saya mata, gashi sun isheta, sai dai babban abun da yake yi mata da?i, tana da damar ta dafa ta ci yadda take so, sa?anin idan a gida ta girka, sai ta gama wahalar a sanmata.

Tunani take yi, idan ta dafa taliya yau ma ko zai ci, tana tunanin ko shi ma sun fara isar shi. "Karfa ya ce ko ban iya girki bane, shiyasa kullum nake dafa taliya. To ai gidan bakomai sai su"

Ta ?an yi shiru, tana tunanin yau bari ta aika a sayo mata kayan miya, tayi da miya, so take ma ta nuna masa ku?in da kakarshi ta ba ta, amma tsoronsa take ji.

Tana ta tunani, ta ji ana buga ?ofa, cikin murna ta tashi, ta san ba?i tayi sa ?ebe mata kewa.

Anty lubabtu ta gani, ma?wabciyar su, da ?anwarta wadda take kar?ar shirin dutse a gidanta, cikin murna tayi musu maraba.

Allah ya sa tana da ruwan pure water, ta basu.

Ta ce "Anty lubabatu shi ne sai yau zaku zo ko? An barni nika?ai, ba wanda yake le?o ni".

"Ki yi ha?uri jauhar, tun washegarin kawo ki, nake sintirin neman mai rako ni a gidanku, wallahi fafur 'yan gidanku da 'yan tsukin nan aka rasa masu zuwa su rako mu, wai tsoro suke ji, 'yan gidanku ma wai ba za su rakomu ba, mijinki ?an daba ne, ni kuwa na ce ko menene zamu zo, sai kwatance suka yi mana".

Ta ?an rausayar da kai ta ce "Shikenan bakomai, yaya saifu ma ya zo, daga ni sai yaran ma?wabta, ni ka?ai nake wuni".

Samira ta ce 'Allah sarki, mma dai jauhar ba wata matsala dai ko?"

Tayi murmushi ta ce "Babu anty samira, ya shiri kin zo mini da shi?"

"Ta? kina amarya, kawai sai na kawo miki shiri?"

Jauhar ta ce "Eh mana, zai din ga ?ebe mini kewa ai, dan Allah idan an samu mai zuwa, ki bayar da yawa a kawo mini, na din ga yi"

Anty lubabtu ta ce "Jauhar iyayen neman ku?i".

Samira ta ce "Bar ta ta nema, rayuwar nan ba a zama haka"

Miya lubabatu ta soyawa jauhar, mai yawa ta sha naman kaji, da shinkafa da 'yan kayan bu?atu.

Jauhar ta ji da?in hakan sosai da sosai, ta din ga murna, suka wuni tare har la'asar, sannan suka tafi.

Suna tafiya ta aiki almajiri, ya sayo mata salak da kayan ha?in sa, ta zauna ta shirya salak ?in nan, ta juye miyar a tukunya, ta ?ara soyata tayi mata gyare-gyare ta ?ara mata su maggi da kayan ?amshi ta kammala komai.

Ta ?ebarwa yaran da suke shigo mata abincin ta basu, ta ?ebe wani ta rufe, dan abincin da yawa, ta sake turara shinkafar ta zuba a wani flask mai kyau kamar a lokacin ta dafa ta.

Tana aikinta, tana jin radiyo a mp.

Ta bawa yara ku?i, suka sayo mata ruwa da lemo mai sanyi.

Ta gama aikin, ta share kitchen ?in, ta kwaso sharar abun da ta ?ata, ta fito kawai ta ga Al'amin a tsakar gida, aikuwa ta razana ta saki abun kwashe sharar tana ihu, ta zubar da sharar a wurin, har zata gudu sai kuma ta tuna kashedin da yayi mata, ta tsaya jikinta yana rawa ta ce "Yi ha?uri, tsorata nayi, ban san ka shigo ba" tayi maganar tana kare jikinta, saboda babu hijjabi a jikinta, bai jira ta gama maganar ba ma, ya shige falo.

Ta da?e a tsakar gida, ta kasa shiga falon ma, ta lalla?a ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, gaba ?aya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi.

Ba ya falo, ta shiga ?aki ta sako hijjabi ta fito, sai dai ta kasa zuwa ?akin da yake.

Wanka yayi ya fito, ya tarar ta ajiye masa sabulun wanka, a cikin wanda ta zo da shi, ban?akin ta kai mas bokiti da ruwa, ga buta ita ma cike da ruwa.
Ya gama wankan, ya ?ora soson a kan sabulun yayi fitowarsa, da zai canza kaya kuwa, duddubawa ya din ga yi, da ya gan su a cikin wardrobe, sai da ya watso su gaba ?aya ?asa, sannan ya za?i wanda zai saka, ya bar su a wurin ba tare da ya gyara ba.

'yar siririyar muryata ya ji a bakin ?ofar ?akinsa, tana ta sallama.

A fusace ya ce "Meye ne?".

Ta razana ta ?an shigo daga bakin ?ofa ta tsuguna, ta ce "Dama tun washegarin kawo ni, wasu sun zo, da kakarka hajiya da wasu, suna nemanka na ce baka nan, suka bani kaya da ku?i dubu goma, amma na sai maggi da ashana da omo, a ciki baka zama a gida, ban nuna maka ba, shi ne na kawo maka"

?an shiru ya yi, jin ta ce hajiya ta zo, ya ji babu da?i da bai ha?u da hajiyar ba, dan rabon da yaje ya ganta har ya manta.

"Ga ku?in" muryarta ta dawo da shi daga tunanin da yake yi.

"Bar nan wurin kafin na yi ball da ke, ba ruwanki da shiga sabgata na gaya miki, tashi ki ware" ta tashi ta ce "Ku?in fa" banza ya yi mata, ya tsaya yana kallon fuskarsa a mudubin ?akin.

Ganin ba zai kulata ba, ya sanya ta ajiye masa ku?in, ta tashi za ta tafi, cikin tsawa ya ce "Ke!" A razane ta waiwayo.

"Kwashe ku?in nan ki bar nan" jiki na rawa, ta ?auka ta ce "To bar mini ka yi" mugun kallon da ya yi mata ya sanya, ta juya da sauri ta bar ?akin.

Ta je kitchen, ta shiryo masa kwanukan abinci a kan tray, amma ta tsaya tana wasi-wasi, kar ta kai masa ya kuma korarta, ta shiga falon tana taradaddi.

Ta na shigowa yana fitowa daga ?akin, take hannunta ya hau rawa, ta ji tana neman ta saki farantin da kwanukan, ta ?arasa tsakiyar falon, ta ajiye ta ce "Fita zaka yi, ga abinci" ta juya ta koma kitchen ta ?aukko ruwan roba da lemo, da ta saya masa ta ?ora a kan wani plate ?in ta kawo. Tana zuwa taga ya zauna ya kame zai ci abincin, kasancewar yana girmama cikinsa, Al'amin yana son abinci, dan haka ba kowane tayi yake wucewa ba.

Maimakon ya ?ebi abincin, ya zuba a plate, kawai ya bu?e flask ?in, ya juye salad ?in a ciki, ya ?aga flask ?in miyar ya girgije a kai, ko kallon cokalin bai yi ba, ya zura hannu ya kama kai loma.

Duk da wani irin mugun tsoronsa take ji, amma haka cikin tsoron, ta tsiyaya masa lemo a kofi ?aya, ?aya kuma ta zuba masa ruwa.

Satar kallonta ya yi, yadda take komai a nutse, sai dai hannunta rawa yake yi, saboda tsoro, mamaki yake yadda take wani zuba masa ruwa kamar ya sakata.

Ya din ga tunanin ita kuwa wani zunubi ta aikatawa 'yan gidansu, suka za?a su aurar da ita ga shi? Gaba ?aya yanayinta kalar 'ya'yan hutu ce, irin wanda ba sa son wahalar nan.

Sai dai yadda yake auna loma, yana basarwa ba zaka ce, ita yake satar kallo ba.

Ta koma can gefen kujera ta zauna ta yi tsuru, gabanta na cigaba da fa?uwa da zarar ta kalleshi, sai dai duk da haka, a ranta ta ji tana son yi masa magana a kan kakarsa, da sauran tambayoyi, duk da miskila ce, amma idan ta samu wuri akwai hira. Sai dai ko kusa ko alama, ba ta ga wannan fuskar ba.

Kan ta ankara ta gama zancen zucin, ya kawar da abincin cikin kula 'yar tsakiya, shanye ruwansa da lemo tsaf, ta zuba masa ido, duk da ba abun mamaki bane ba, ta saba ganin maza da shegen cin tsiya, dan tsaf Yaya Saifu zai iya cinye cikin babban flask, dan akwai ranar da suka din ga musu da surayya, ya ce zai iya cinye shinkafa rabin kwano a zama ?aya, dama taliya leda guda yake cinyewa.
Dan haka ba ta yi mamakin yadda ya cinye abincin ba, ya dubi carfet ?in ta, milk mai haske, ya goge hannunsa a kai ya tashi tsam ya bar mata wurin da kwanukanta a wurin.

A hankali ta ce "Na shiga uku, miya a kan carfet ?ina" da sauri ta kwashe kwanukan, ta ?ebo ruwa da omo, ta goge wurin da ya goge mata hannu a carfet, ta koma ?akinsa, ta sake kwashe kayan da ya zubar.

Ya watso su duka gaba ?aya, ya cire na jikinsa duk ya watsar ya ?ara gaba.

Ta sake gyara masa, ta kwaso

Please Login or Register in order to submit comment