Reading KARFE A WUTA Chapter 120 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta razana jin motsi a bayanta.

"Me ki ke yi da wannan hoton, ki kula kar ki fasa mini hoto"

A sanyaye ta ce "Kallonta kawai nake yi"

"Ki na sonta ne" da sauri ta kalleshi ta ce "So kai, wallahi har cikin zuciyata nake jin matsananciyar ?aunarta, haryanzu ina jin zafi da ?acin rashin saninta a rayuwata, da tare muka tashi babu lallai na zama masifaffiya ko?" Tayi maganar tana kallonsa.

Dariya ya yi ya ce "Ai ke fa?a da tsiwa a jininki yake, ita kuma wannan ha?uri da kawaici ne a jininta, amma da ni da ita wa ki ka fi so?"

Ta nuna masa hoton jauhar, ya saka hannu ya kar?i hoton ya ce "Nima ita na fi so"

A sanyaye ta ce "Ko baka fa?a ba na sani, amma Vi dan Allah ba cin amana ne abin nan ba, haryanzu na kasa samun nutsuwa da auren nan, idan ina tuna wahalar da ta sha, sai na ga kamar na ci amanarta, da na fara sonka har na aureka" ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.

Ya rungumota jikinsa ya ce "Idan mafarkin da nayi gaskiya ne, to Jauhar tana murna da aurena da ke, kuma ta ji da?in ganinki cikin farinciki"

"Vi"

"Mmm"

"Na san ba zan iya zama jauhar ba, ba kuma zan ta?a kamota ba, ba zan ta?a ha?a matsayina da nata a wurnka ba, amma dan Allah ko babu yawa ka sama mini space a zuciyarka, kar maraicin yayi mini yawa"

Wani irin tausayinta ya mamaye zuciyar sa ya ce "Ki na da naki space ?in, ba zan bari maraici ya ci gaba da damunki ba, zan yi occupying spaces ?in da suke cikin rayuwarki in sha Allah my abla"

A hankali ta yi ajiyar zuciya ta ce "Na gode sosai da sosai Vi, Allah ya bamu zaman lafiya"

Ya ce "Amin, yauwwa yakamata na yi comment akan fankar jiya, ita ma sanyinta ya yi, ba mai cutarwa ba ne ba"

?wacewa ta yi daga jikinsa ta ce "Kai ka san wata fanka, dama abin da ka ke nufi kenan, ka ke gaya mini zafi ka ke ji kwanaki, ko?" ?aga mata gira ?aya ya yi yana murmushi.

Ta ce "Bari na duba girki"

Ya jinjina mata kai, ya sake ?aga hoton Jauhar yana kallo, daga bisani ya mayar da shi in da yake.

Suna karyawa yana tsokanarta, wai a ina ta iya girki har haka, shi ya zata ba ta iya komai ba, kawai ajebo ce.

Dariya ta yi ta ce "Haba dai, boarding fa nayi har high institution, ace ban iya girki ba, girki yana cikin abubuwan da sukan sakani nisha?i, da kuma kwalliya.
Abba ne baya son make up, girki kuma sai na ga ina so nake yi, Abba ya hana sakani girki, idan ba ni na yi ra'ayi nayi ba"

"Yar gatan Abba, gaskiya yana ji da ke sosai, dama har Jauhar shi ne ya ri?eta"

"Shi kansa ya yi wannan nadamar ai"

Ua jinjina kai ya ce "Maybe da shi ne ya ri?eta, da ba zan santa ba, Allah dai ya riga ya gama tsara komai, hakan ma mun gode masa"

Wayarsa ta fara ringing, ya ?aga ganin lambar Abbu.

Suka gaisa, Abbu ya ce "Ina zamu yi, idan mun shigo Abuja?"

"Wai zuwa za ku yi?"

"Eh zuwa za mu yi, tun da kai ba ka ga ya dace ka sanar mana abin da ya faru ba"

"Abbu ka yi ha?uri, na yi hakan ne dan kar na ?aga muku hankali"

"Koma menene gamu a hanya dai"

"To bari na turo maka adress ?in"

Ya sauke wayar ya ce "Wai su Abbu su na hanya, ko wa ya gaya musu abin da ya faru, gashi an ta so su, next week na so mu koma gida fa"

Nabila ta ce "Sai a ?ora girki, kafin su ?araso, amma sai an yi cefane"

"Zaki iya kuwa, na ga jikin naki sai a hankali"

Murmushi kawai ta yi ta tashi tsaye, ta ce "Zan iya mana"


*****
Wani irin gumi ne yake tsatsafowa Indabo, cikin hasala ya ce "Wai wace irin Naja'atu kuma, ina ruwana da wata naja an kaita prison, iya ruwa fid da kai kawai a wannan ga?ar.
Nan na ?oyeta, na saka ake yi mata visa a ?oye, ta bar ?asar amma abun bai yiwu ba, wannan jarabben yaron maye, ya kawo mana farmaki, gashi gidan jaridar da aka bawa kwangilar ya?a labarin, an maka su a kotu kuma tara za a caje su mai yawan gaske. Ko dai mu biya musu, ko su tona mana asiri.
Gashi ba ni da tabbacin rundunar soja, za su ?i fa?ar ainihin abin da ya faru, dan su wanke Viper, gashi ministan tsaro ?an uwan kankarofi ne, balle a sasanta komai yayi magana da su"

"Ka kwantar da hankalinka, zuwa jibi war haka, ka bar ?asar nan, kujerar sanatan ka ha?ura, ace ka tafi neman lafiya, idan Allah ya sa komai ya lafa sai ka dawo, koma ka yi zamanka a can".

Ayshercool
08081012143
*MASU JIRAN ?ARFE A WUTA COMPLETE DOCUMENT, ZA KU IYA PAYMENT A YANZU, A CIKIN SATIN NAN ZAI KAMMALA 1K VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143


Yakice gumi Indabo ya yi, yana jinjina kai cike da gamsuwa.

Zakiyya kuwa, hankalinta ya kwanta bayan ganin hafsa ta koma gidan Alhaji mu'azzam, babu irin hu?ubar tsiyar da ba ta yi mata ba kafin auren. Ta koma ta sakankance, hafsa zata din ga dumbuzo abin da ta samu ta din ga kai mata, domin kuwa har ta fara tsara irin rayuwar da za ta yi, a matsayinta na surukar ?aramin minista a Nigeria.
Babu irin hu?uba da dabarun ha'inci, da ba ta koyar da hafsa ba, haka ba ta fasa shige-shige ba, cike da fatan a karon farko hafsa ta haifo ?a namiji, domin idan kankarofi ya mutu su samu dukiya, domin kuwa yaransa mata ne. Amma tun da hafsa ta bar gidan, wata kusan shida, ko Kanon ma ba ta tako ba, sisi ba ta turawa Zakiyya ba.
Ta din ga kiranta a waya, a kan ta aiko da ku?i, a sake bi mata malamai ayi maganin uwargidansa, kuma a kama mata shi, amma ta ce ita baya bata ko sisi.

Hafsa ta sanya wa ranta, a wannan karon ba zata yi asarar ku?inta ba, babu wani mushiriki da zai sake cin sisinta, saboda ta mallake Alhaji mu'azzam.

Ta yi amfani da shawarar Jauhar, da ta bata tun tana raye, ta kama addu'a, da mi?awa Ubangiji lamarinta, tare da yi masa biyayya dai-dai iyawarta, sai kuma uwa uba gyara da take yi, yadda yakamata ba tare da ta yi abin da zai cutar da lafiyarta ko imaninta ba.

Sai dai mai rai ba a rasa shi da motsi, duk da irin kula da tattalin da Alhaji mu'zzam yake yi mata, ba shi da isashshen lokacinta, kuma har zuwa yanzu ya kan bi abin da matarsa uwargidansa take so, bai fiye son ?ata mata ba, gashi kusan kowane lokaci cikin aiki yake ba shi da lokaci.

A wannan karon ba ta yi yin?urin yin fito na fito da uwargidansa ba, dan taga alamar baya son hakan, kuma ita rayuwa yar siyasa ce, a gabansa babu abin da ya yi mata zafi, da ko sako zancen matar, a bayan idonsa kuwa ba ta jurewa idan ta kira ko ta yi yin?urin ci mata mutunci.

Kuma dai-dai gwargwado kankarofi yana sakar mata ku?i tayi yadda take so, ko kyauta zata yi a gidansu, Baba take aikawa ku?i, ta san koba komai kowa zai amfana a kan ace Anty kawai take bawa, dan ta san ?arshen ku?in a yawon bin bokaye zai ?are.

Daf da azahar su Abbu suka iso gidan su Nabila, kafin nan tuni ta kammala abincin kar?ar su.

Abbu ne da Baba da kuma Major suka zo tare.

Nabila ta yi farin cikin zuwansu sosai da sosai, sai dai Major yayi ta fa?a a kan yadda ba su fa?i abin da ya faru ba.

Major kawai kallon Nabila yake yi, yadda ta fututtuke da ba ta son auren, amma tayi ?alau da ita.

Sun da?e a gidan, sai da Major ya zaga a cikin barrack ?in, suk sai juniors ?in sa a aiki, duk sun yi retire.

Daga nan suka je gidan Alhaji mu'azzam, suka wurin hafsa, ita ma kamar ta taka dan murna, iyaye akwai da?i.

Sai dai ba su da?e a gidan hafsa ba, saboda yamma suka kama hanyar kano.

Nabila na kitchen tana ta ?o?arin yin wanke-wanke, Viper ya shiga kitchen ?in ya tarar da ita.

"Sannu"

Ta kalleshi ta ce "Yauwwa"

"Ki na iya aikin a haka?"

Ta ce "Eh mana, me ka gani?" Yayi murmushi ya ce "Bakomai, dama dai shekaranjiya suka zo, yau na so nima na yi zaman jinya, anyway sannu Abla, na so na yi appreciating iskar fankar jiya unfortunately....

Katse shi ta yi da "Ni dai na ga ta kaina da wannan fankar"

Ya jingina da jikin bango, ya ce "Na yi ?o?ari fa Abla, shekara ta nawa ina zaune haka, kodaye ba na gane komai sai 'yan kwanakin nan"

"Dan Allah vi ka ?yale ni da zancen fankar nan"

Dariya ya yi ya ?arasa kusa da ita, ya saka hannunsa a sink ?in, yana tayata wanke kwanukan.

****

Abdul shi yake kai Ramma makaranta, haka idan an tashi, idan kuma yana da ayuuka da yawa da kanta take tafiya.

Mama sam ba ta son kaita makarantar nan da yake yi, tafi so ta tare, saboda gudun abin da aka iya faruwa, dan haka ta ya tan kunnen ramma, a kan lallai gara ta tare, can su ?arata kar su ?aukko mata magana a titi.

Allah ya taimaki Abdul, hankalin Indabo ba ya jikinsa, hatta ita mahaifiyarsa ba ta cikin hayyacinta, amma shi sam hakan bai dame shi ba, yadda zai gina rayuwarsa da ta rahama yake yi.

Surutun abin da ya faru da Bunkure kuwa, ya ci gaba da zaga wa lungu da sa?o, gaba ?aya mutane suka din ga Allah wadai da yadda ta da?e tana cutar jama'a.

Viper kuwa bai bari Nabila ta yi girki ba, ordern abinci ya kuma yi musu, yana ta lalla?ata.

Bayan sallar isha'i, ya kira Walid, yayi sa'a kuwa ya ?aga.

"Mai laya"

"Mai zamani, ya gida ya ?anwata?"

Viper ya ce "Lafiya ?alau, tun ?azu nake kiranka, su Abbu sun zo fa yau, har da sirikaina"

Walid ya ce "Kash, amma wallahi da na san za su zo, biyo su zan yi"

"Ai gara da baka sani ?in ba, ka zauna ka kula mini da ?anwata, tun la'asar na kiraka ai baka ?aga ba"

"Sai magariba na ga missed call ?in naka, muna asibiti ne, Shahida ba ta jin da?i tun asuba muke can, sai magariba muka dawo"

Viper ya ce "What? Muhsin haka muka yi da kai? Daga aura maka yarnya ka ha?ata da aiki, wane irin abu ne haka?"

Walid ya ce "Innalillahi me zamani meye haka wai? Fura ta sha ta ?ata mata ciki, take ta amai da gudawa muka tafi asibiti fa"

"Ba wani nan, laulayi ne, matsalar aurawa tuzuru yarinya kenan, gamo da kasawa sai wannan al'amari, to ni dai idan namji ne ayi mini takwara"

Kashe wayar Walid ya yi, jin abin da Viper yake yi masa.

Nabila kuwa sai kallon Viper take yi, dama haka yake da tsokana har haka, kuma yana yi yana wani mazewa, kamar ba daga bakinsa suke fitowa ba.

Shahida kuwa dariya take yi wa Walid, yadda ya dage yana yi wa Viper rantse-rantse.

"Wallahi my kana bani dariya, ya san kunya ka ke ji, shiyasa yake yi maka wasu abubuwan, ka fiye kunya, ni har dariya ka ke bani"

Yayi murmushi ya ce "Ai na fuskanci tsokanar ta wa yake yi kawai"

"My ka san sai yanzu na san Yaya Al'amin yana wasa da dariya, wallahi da ko kallona ba ya yi, ban ta?a zaton yana wasa da dariya ba"

Walid ya yi murmushi, yana shafa gefen fuskarta, ya ce "Ki daina tuna bayan nan, amma Viper mussaman lokacin marigayiyya, bayan ta fara saita mu, yana wasa da dariya, kin san rayuwar ta mu ce, duk sai a hankali sai godiyar Allah. To ya ki ke jin jikin naki yanzu?"

"Da sau?i, amma ba zaka yi mini wayo ba, ni duk ka daina jin kunyar tawa yanzu"

"Ai mai zamani gaskiya ya fa?a, da ya ce matsalar a ba wa tuzuru aure kenan, bai iya cin ?wan makauniya ba"

Tare suka yi dariya, cike da nisha?i da jin da?i.

Nabila kuwa ta ?auka, yau za ta sake, ta samu isasshen bacci, dan tun da ta fara jinyar Viper, ba ta samun bacci, ta zata ya samu abin da yake so, zai bari yau ta yi bacci.

Amma sai ta riski abin da ba tayi tsammani ba, dan kusan gara jiya da yau, dan jiyan ?yaleta kawai ya yi, yadda yake nanata zancen fankar nan, sai da ya tabattar mata da gaske tsawon lokacin da ya ?auka, yana zaune haka ya dame shi, dan ta gazgata yadda yake ba wa fanka muhimmanci.

?angaren Abdallah Liti, barkwancinsa ya sanya yake da mutane sosai a kasuwa, amma hakan bai hana shi yin fa?a da muzurai wasu lokutan a kasuwar, dan ma idon Abbu yana hana shi yin wani abun.

Sai dai Abbu yana jin da?in aiki da su sosai da sosai, ba su da ?yuya ko ka?an, kuma ya sha jarraba amanar su, ba tare da sun sani ba, amma ko kusa ko da wasa babu wanda ya ta?a yin?urin cin amana.

Sai da ya ?ara dana sanin ?aukar su Abba ya ?ora su a kan harkokin sa, suka din ga ?urka masa sata, suna cutarsa. Da su Al'amin ya ri?e, da yanzu dukkanin su, sun tsaya da ?afrsu.

Sai dai ya yanke shawarar zai tallafa musu sosai da sosai, su tsaya da ?afafuwan su, dan ya san bai isa ya biya su, wahalar da suka yi da ?an sa ba.

Samunsu a kasuwar, ya sanya wasu lokutan ko zuwa baya yi, sai ya zauna a gida ya ?an huta, ko yaje wasu sha'anunnunkan, za su kular masa da komai babu cuta ko cutarwa.

Idan yana cikinsu, sai ka ?auka shi ne ya haife su, har shawara ya kan yi da su a kan harkar kasuwanci, bai yi da abokan sana'arsa ba, saboda su ba za su cuce shi ba ko su yi masa hassada ba.

Abbun ne yake tsokanar liti ya ce "Abdallah, kai haryanzu babu wadda ku ka daidaita ne? Su sun yi aure sun bar mini kai a haka fisabilillahi, yakamata ka motsa kai ma na aurar da kai"

Liti ya ce "Ai abbu wadda nake so ?in kamar tafi ?arfina, gani nake kamar ba za a bani ba" yayi maganar cikin damuwa.

Walid sai hararsa yake yi, yadda yake sakin jiki yayi hira da Abbu shi ba ya iyawa.

Abbu ya ce "Haba dai, ni da ina da wata 'yar ai da na baka, amma meyasa ka ce ta fi ?arfinka?"

Jiki a sanyaye ya ce "To ai ana ganin ni ba mutumin kirki bane ba, ba kowa zai iya jihadin da ka yi ba Abbu"

"In ji waye ya ce maka ba mutumin kirki ba? Wannan wani abu ne da aka yi shi ya wuce, kuma yanzu Alhamdilillah, babu abin da za mu cewa Allah sai godiya. Kuma gaka da sana'a ka shiryu yanzu ba kamar da ba, in sha Allah za a baka, yar gidan waye idan ma baban naka ba zai tambayar maka ba, ni sai na wuce maka gaba"

Liti ya ?an yi shiru ya ce "?anwar matar mai zamani ce, wata Walida a gidan su take, 'yar major ce"

Abbu ya ce "Au to ashe ma 'yar gida ce, shi ne ka ke ta damuwa"

"Ina jin tsoro ne, gani nake kamar ba zai bani ba, kuma Walid ma cewa ya yi na nemi wata, ba lallai a bani wannan"

"Ita yarinyar kun daidaita? Kana zuwa wurinta ne?"

Ya jinjina masa kai alamar eh.

"An gama, ka fara tarin abin da ya sauwwa?a ba zai gagara ba in sha Allah" washe baki liti yayi cikin matsanancin farinciki, Walid kuwa kamar ya mare shi, saboda ba ya jin kunya ko ka?an yake wannan maganganun da Abbu.

Shahida ta je har gida gaida Abbu, ta yi masa farfesun kaza, taje gaishe shi, sai da ta tuna masa da jauhar, lokacin azumi ta saka Al'amin a gaba suka zo musu sannu da shan ruwa.

Rahila kuwa, ko kallon kirki ba ta yi wa Shahida ba, duk yadda shahidan ta din ga ra?arta, amma ta din ga hantararta, tana ?arewa auren zagi.

****
Viper har tausayin Nabila yake ji, domin yanzu zaman ?ari-?ari takeda shi, saboda yadda ya addabeta, har ta fara yi masa zancen, tun da ya ji sau?i, zata koma Kano, hutunta ya kusa ?arewa, ya ce ba za ta koma ba, shi ma an kusa sallamar shi, zai je hutu, sai su tafi tare.

Har murna take yi idan ya ?an fita baya nan, ta samu ta ?an sake.

Da ya dawo kuwa ta shiga fargaba da tashin hankali.

Da safe wurin ?arfe tara da mintuna, Viper ya zuba wa Nabila ido da ta kasa tashi, take ta lumshe ido, alamar bacci bai isheta ba.

"Abla yau ba zamu karya bane ba? Yunwa nake ji fa"

Ta bu?e idonta da kyar, ta ce "Tun wurin 8 fa na tashi, na yi niyyar ?ora breakfast ?in, kai ka hana ni, kuma ga wani irin bacci da nake ji" tayi maganar tana ci gaba da lumshe idanunta.

Ya saka hannunsa, ya shafi fuskarta, ya yi ?asa da muryarsa ya ce "Na sani ki na ha?uri, amma ki ?ara kin ji 'yar sugar na, duk da wasu lokutan ki na yi mini bore, but am appreciating jazakillahu bil janna" ?an ?ara sunkuyar da kai tayi, cike da jin nauyin sa, dan haryanzu tana jin nauyinsa sosai da sosai. Sannan ta jinjinawa ?o?arin sa, irin yadda ta din ga shishishige masa dan ta dawo da shi hanya, da ke?ewar da suka din ga yi, amma ko da wasa bai ta?a yin?urin yi mata abin da bai dace ba, wanda hakan ne ya sanya ta ?ara sakin jiki da shi sosai.

Maganar sa ce ta dawo da ita hayyacinta ya ce "Kin san wani abu kuwa?"

"A'a sai ka fa?a"

"Liti ne ya zo mini da wata magana, wai wata sisternki yake so, na manta sunanta, wadda muka tarar da baba uwani a wurinki a asibiti"

Ta bu?e idonta ta ce "Wai Walida?"

"Yes ita, wai sonta yake yi, amma ki na ganin Abba zai ba shi aurenta kuwa? Tun da kin ga ga tarihin rayuwar mu"

Nabila ta ce "Me zai hana, Walida tana da sau?in kai, kuma ba ta da dogon buri ita da Anty mamanta"

Viper ya ce "Ina fatan ba zaki yi ramuwar gayya abin da yayi miki ba, ki saka a hana shi ita ba"

Nabila ta ce "Haba dai, ai wannan ya wuce, ai in dai tana son shi shikenan, mu dama fatanmu kullum idan aka samu wanda ya tuba ya daina ?arna, al'umma su kar?e shi, a mutunta shi, in sha Allah ba zai gagara ba"

Viper ya ce "Mun gode sosai da sosai my sugar girl"

Dariya ta yi tana tashi zaune ta ce "Wai kun gode, kamar an yi wani abu"

"Bari idan muka karya, zuwa eleven, sai mu je na kai ki gidan hafsa"

Cikin murna ta ce "Amma na ji da?i sosai da sosai, na gode Vi"

"Never mind, mu je ayi wanka, sai mu yi breakfast ?in"

Ta ji da?in zuwanta gidan hafsa, ko ba komai, ta rage zaman ka?aici.

Ta din ga tsokanar hafsa wai anya ba ciki ne da ita ba, saboda yadda ta yi ?iba.

Hafsa ta ce "Wallahi ba wani ciki Nabila, jiya na gama period kwanciyar hankali ce kawai da cin abinci, ni abin ya fara damuna ma,wata shida ko ?atan wata ban yi ba"

"Kai hafsa, me aka yi da maza kwata kwata yaushe aka yi auren? Dan Allah kar ki ?aga hankalinki"

Hafsa ta rausayar da kai ta ce "To, amma ina son yara Nabila, dan Allah ki yi mini addu'a, ka da Allah ya jarrabe ni da rashin haihuwa, ina son yara sosai da sosai"

Nabila ta ce "Dan Allah kar ki damu kanki, komai rabo ne kuma lokaci ne, daga yin auren ai yayi wuri ki fra wannan maganar" tayi ta kwantar mata da hankali, daga nan kuma suka ?uge da hira, wanda galibi hirar ta karkata ga yanayin zamantakewar aure bawa junansu shawarwari, da zancen kayan likitar mata maman dr . Wadda cikin ikon Allah, magungunanta suka ?aga darajarsu a idon mazajensu fiye da yadda suke tunani, ita mace ai yar gyara ce da kwalliya, babu borar mace sai wadda ta so.
(0706 971 1327 da kayan likitar mata, bbau ruwanki da matsalar sanyi, ko fargabar amfani da kayan da baki san da yaya aka ha?a su ba, domin tsoron cutar da lafiyarku. Domin ?aga likkafar taku kimar, ku kasance masu yawan ibada da addu'a, biyayya tare da gyara da ingantattun magunguna na gyara)

Sai da suka kira Sumayya su ka yi video call da ita, domin daga abin da Nabila take missing, har da Sumayya.

Cikin ikon Allah, hutun wata guda Viper ya samu, domin ya ?arasa jinyarsa, dan haka suka nufo Kano.

Nabila cike da murna ta dawo, sai dai gidan su ya sha uwar ?ura, suna zuwa mayafinta kawai ta ajiye ta hau gyara.

Viper ya taimaka mata da abin da zai iya, ya tsallake ya fice, ya tafi wurin 'yan amanarsa.

Tas Nabila ta ?al?ale gidan, ta kira sumayya a waya, ta gaya mata ta dawo, ta ce mata za ta zo.

Ta kuma kira Walida a waya, bayan sun gaisa take yi mata maganar liti.

Da fari nu?u-nu?u ta fara yi, daga baya kuma ta saki jiki ta yi mata bayanin komai.

A fitar da Viper ya yi, har gidan su ramma ya je, yaji da?i da mama ta gaya masa ta koma makaranta, amma ta damu da rashin tarewarta, ta gaji da yadda sai dai ya zo ya ?auketa su na yawo a gari.

Viper ya ce kar ta damu zai yi magana da Abdul ?in.

Bayan ya koma gida yake gaya wa Nabila, da weekends Walid da liti za su zo, dan tun da aka yi bikinsu, Walid ne kawai ya zo.
Ta ce masa to.

Can gidansu Hafsa kuwa, 'ya'yan mama da Anty Zakiyya ta yi wa asiri, da kyar ta samu suka auru, kullum cikin ciwo suke, dan ?aya daga cikinsu kamar zata zare, idan ta fara aljanu kamar zata haukace, hakan ya tsananta wutar ?iyayyar da ke tsakanin su, kuma aka yi rashin sa'a, dukkaninsu babu wadda take jin da?in zaman aurenta, ?aya kishiyoyi sun sakota a gaba, sai da aka yi saki biyu a shakera biyu.
?aya kuma dangin miji da ma?wabta, sun hanata sukuni, ga miji ba ya son haihuwa.

Abin duniya ya isheta, ta rasa abin da yake yi mata da?i, ga Tijjani ya auri wata fitinanniyar yarinya da ba ta da kunya, ba ta ganin mutuncinta ko ka?an, shi kuma ya zama tamkar soko, sai abin da take so shi yake yi, ba ya ji ba ya gani a kan matar nan, bai ?i ya ?ata da kowa ba a kanta, ciki har da maman. Dan idan ta yi masa ?orafi a kan matar, sai ya daina zuwa gaisheta.

Saifu ne dama mai ?an dama dama, shi ma kuma ba ya ji, ya ha?a kai da yaran masu ku?i, yana ta rashin ji, duk da ya rage, ga ku?i yana samu, amma ya fi mayar da hankali a kan shaye-shaye da kashewa 'yan mata ku?i, sam ba ya yi wa rayuwarsa wani tanadi.

Wa?annan tarin matsalolin ne, suka ha?u suka addabi zuciyar mama, ta kasa sukuni da jin da?in rayuwar, duk in da ta motsa ?acin rai da damuwa sun baibiyeta cikin yaranta kowa da halinsa.

Kawai aka wayi gari tana wanka, ta yanke jiki ta fa?i a cikin ban?aki, aka ?auketa aka kaita Asibiti, a nan aka tabattar da ta samu shanyewar ?arin jiki.
Ba ta iya yi wa kanta komai sai dai ayi mata, hatta najasa a kwance take yi, kasancewar jinya ba abu ne na ?an lokaci ba, ya sanya yaran nata suka fara ?osawa suke bata wahala.

Hakan bai zame wa Zakiyya izina ba, dan a iya cewa ita murna ma tayi, yanzu miji ya zama nata itaka?ai.

****

Liti sai ?arewa gidan Viper kallo yake yi, an zuba wa Nabila kaya na alfarma, gidan yayi kyau sosai da sosai.

Nabila ta gabatar musu da kayan ciye-ciye, take cewa Walid "Shi ne yau baka kawo mini Shahida ba"

"Ai ita na kawo ta ma, ke fa baki ta?a zuwa gidanmu ba"

Tayi murmushi ta ce "In sha Allah zan zo, ai ina son zuwa ziyara sosai da sosai, dan ba sai na jira Vi ba, shi sabgoginsa

Please Login or Register in order to submit comment