Reading KARFE A WUTA Chapter 82 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne, amma haryanzu mamaki nake yi, yadda aka yi ki ka tako da kanki, ki ka zo har in da nake"

Ta numfasa ta ce "Ka san komai dalili ne yake kawo shi"

"Haka ne, bari na saka a kawo miki abu mai sanyi"

Ta ce "A'a, Alhamdilillah tambayoyi ne nake da su a gareka Yalla?ai"

"To gimbiyata ina jinki"

"Case ?in da nake yi, na yarinya da aka yi raping, ashe a gidanka aka yi. Na sake komawa na lura da sunan street ?in sunanka ne, kuma na tambaya aka nuna mini gidan aka ce naka ne. Abun ya ?aure mini kai, sai dai na jajje amma ban samu abun da nake so ba, matar gidan ta koreni, kusan sau biyu ma, yaya aka yi haka yalla?ai?"

Yayi murmushi ya ce "Waye ya ce miki gidana ne?"

"Sir gidanka ne mana, Mu'azzam wada kankarofi street, kuma aka nuna mini gidan aka ce gidanka ne, sir ban yi tsammanin haka daga gareka ba, ?oye mai laifi a ?orawa wanda bai ji ba bai gani ba mai gadinka?"

"Nabila, ina iyakar ?o?arina, am even supporting you, baban yaron nan abokin adawata ne, matata kuma akwai yara a tsakanin mu, bai kamata na tona mata asiri haka anyhow ba"

"Amma yarinyar mutane da aka zalunta fa? Maigadinka da aka rufe ba da laifinsa ba fa? Wannan ba hujja ba ce ba, what if ?anka aka yi wa haka? Haba yalla?ai"

"Nabila, lamarin ?asar nan ya wuce duk in da ki ke zato? Dole sai mutum yana lissafi, amma in tambaye ki mana? Waye ya ajiye miki tarihin Bunkure a Office ?in ki? Waye ya tura miki message ?in babar ramma? Duk kina tunanin wannan, ko kuwa kawai sabgarki ki ke yi?" Waro ido ta yi tana kallonsa.

"Mayar da idanun madam"

Cikin mamaki ta ce "But how?"

"Through barrister Habib my dear. Ba zan tona wa yaron asiri kai tsaye ba, saboda ubansa ne tushen lalata shi, ba kuma nayi haka ne dan na ?oye laifinsa ba, ina jan ?afa a lamarin ne, saboda ki gano komai a sannu, yadda babu mai zargina, duk da akwai ji?a??iya tsakanina da ubansa.
Mahaifiyar ramma na tare da ni, ni na saka aka ?auketa, tun kan a illata ta saboda case ?in nan. Zan ha?a ki da ita, zata yi miki bayanin komai, amma ki daina zargina a kan ?oye mai laifi, am supporting you, program ?in ma da ki ke yi am supponsoring the program sweetheart, ki daina zargina please, tabbas a gidana aka aikata laifin, kuma ina iya ?o?arina a kai madam. Ki je ki cigaba da aikinki, zan cigaba da ?o?arina in taimaka miki"

Saroro tayi tana kallon kankarofi kamar sokuwa.

"Akwai alamar gajiya a tare da ke, ki je zan saka Habib ya kai ki in da take"

"Amma duk tsawon wannan lokacin, kuka rufe ni ka ke yi mini yawo da hankali?"

"Akwai dalili ne, amma ki yi ha?uri dan Allah, a dalilin haka aka saka miki wuta a office, aka kusa taka ki da mota, duk dan ina tsayawa ina tsawatar wa ne, akwai hatsari a abun da ki ke yi nesa ba kusa ba, shiyasa nake taimaka miki ta ?ar?ashin ?asa, amma kiyi ha?uri" ba ta ce masa uffan ba, ta ?auki jakarta za ta fita.

"Ina ba?onki kuwa? Idan kun sake ha?uwa ki ce ina gaishe shi" ta tsaya ta waiwayo ta ce "Wane ba?on kuma?"

"Viper" ya amsa mata kai tsaye.

"Ka san Viper?"

Kankarofi ya ce "Na san shi, akwai labari mai sar?a?iya ne, amma kar ki matsa, ki bi a hankali, zai kawo ?arshen labarin, kamar yadda ya fa?a, a sauka lafiya abar ?aunata" ba ta iya magana ba, ta mur?a ?ofar ta fice.
Tun a hanya ta kira barrister Habib, take yi masa masifa, a kan abun da ya yi mata, ya din ga yi mata yawo da hankali da nuna bai san komai ba.

Sai da suka ha?u, yayi ta bata ha?uri, yana ?ara yi mata bayani, kankarofi yayi mata kwarjinin da bata tsigale masa ba, amma ta yi wa Habib ta tas.

****

Nabila tana tafe tana kallon hotunan hannunta, ta kira Viper ya ?aga ta ce "V ina wuni?"

"Lafiya ?alau, ya ake ciki?"

"Ina hanya zuwa zan yi"

"To, Allah ya kawo ki lafiya"

****
Ramma ta tsurawa Abdul ido, ya ce kunun gya?a yake so, yana sha yana waya, ya ajiye kofin kunun ya ce "Daddy ni dai dan Allah ka yi ha?uri, wallahi ba zan iya fito maka da rahama ba"

Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce "Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a fa?i cikakke waye kai ba, ga maganar ku?i na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?"

"Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma....

Wata ashar ?in indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya dafe kai.

"Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ?oye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata dining ?in.

***
"Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai ka?i gaya mini wacece?"

"Yaya shari'ar ta kasance?"

"Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah"

"Mhmm, a ina aka ganta?"

"Ta gudu ne wani wuri ta ?uya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota"

Viper ya jinjina kai ya ce "ya nawa, ni ya ake ciki?"

"Shiyasa na zo ai"

"Ok"

"Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina bu?atar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu su bayar da shaida"

"Wane bugaggen?"

"Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi ha?uri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi exposing ?in su a kotu"

"Rashin ji kamar yaya?"

Ta kalleshi ta ce "Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ?ulla wiwi black market duk da ka yi"

Ha?e rai yayi ya ce "Amma ba prison zan koma ba ko?"

"Idan ta kama ai dole ka koma"

Ya ce "What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?"

Ta zum?ura baki ta ce "Ni na ?aureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda zamu yi da su, sai anjima"

*****

Nabila ta tafi ?akin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ?auke da addu'a, ta shiga ?akin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ?ace.

Ta je ta dur?usa ta ce "Abba gani"

"Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila? Sai kin tozarta ahalin nan gaba ?aya ko Nabila?"

Ta girgiza kai ta ce "Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan ta?a aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah kar abun da zan nema ya ?ata maka rai"

Ta mi?a wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce "Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan.

Abba ya saka hannu, ya kar?i hotunan yana dubawa.

Ya gama ?arewa hotunan kallo, ya ce "A ina ki ka samu hotunan nan?"


Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa



https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*


Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*?ARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*


Ta ?an yi shiru sannan ta ce "A office ?ina na gansu"

A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce "A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka ?aci ba, dan Allah Abba ko sau ?aya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba" ?arasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin ?acin rai ya ce "Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa yanzu shi ya nemi in da ki ke".

Anty ta ce "Haba major, dan Allah ka yi ha?uri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan ta, kayi ha?uri dan Allah " gaba ?aya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka.

Cikin tsawa Abba ya ce "Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana"

Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yin?ura ta tashi da kyar, ta bar ?akin, ta koma ?akinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role ?in uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido bane ba.

Baba magajiya ce tayi sallama, ta ?arasa kan gadon, ta dafa kafa?arta ta ce "Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya ha?uri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki ha?ura ba, shekara nawa ana abu ?aya kin ?i ki gane ki ha?ura".

Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce "Baba magajiya"

"Na'am arfa"

"Kema laifina ki ke gani?"

Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta.

"Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau ?aya? Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina ?aya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau ?aya na je na ganshi na dawo dan Allah"

Baba magajiya ta girgiza kai ta ce "Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki"

Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce "Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi babana, zan neme shi kuwa in sha Allah "

Baba magajiya ta waro ido ta ce "Baki san gatse ba Arfa?"

Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta.

Baba magajiya ta ce "Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai ro?ona da ke, ki yi ha?uri idan da rabo zaki ha?u da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu sa?ani da maitama"

Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki.

Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta.

****
Duk da Nabila bata jin da?in komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba.

Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin yaransa, bisa zargin kisan matar Viper, shekaru shida da suka gabata.

Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ?urarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba.

Nabila tayi iya ?o?arin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program.

Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce "Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren ?an ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan sanda, take nemansa ruwa a jallo?"

Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program ?in su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa.

Tayi wani irin murmushi ta ce "Ba ?an ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma ?an ?asa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane ?an ?asa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya ?uge da gyangya?i, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar".

"Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka, ki kare mai laifi?"

"Sam, dokar da aka wula?anta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya al?ali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ?a'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani ?aurin ?oye da yakamata a warware? " Tayi maganar tana ?ure sumayya da ido.

Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin.

Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta ?aga wayar suka gaisa, ya ce "T ladan, meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?"

"Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon, maciya amana mai fuska biyu "

"Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa ?an adam ne? Ba a ta?a iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba ?aya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan zai ?ara mata ?aimi"

Sumayya ta ce "Ok sir, na gode" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta ha?ura da batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba.

Abbu kuwa a zabure ya mi?e tsaye, jin program ?in da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ?ayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi.
Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a ki?ime, tare da ?aukar radion ya fito tsakar gida.

Rahila ta ce "Ya dai na ganka a firgice haka?"

"Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan radiyon zan je, wata?ila su sun san in da yake"

Ta kwa?e baki ta ce "Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari"

Ya ?ura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice.

****

Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a ma?ogwaronta, kukan ma gaba ?aya ta kasa saboda ba?in ciki da ?acin rai.

Katafaren gate ?in aka bu?e mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan.

A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da zuwa.

Nabila ta zauna cikin ya?e, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta ha?iyeta, ita dai ban da an yi mata garga?i, da tuni ta fa?i abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an garga?eta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta tsuke.

"Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da ha?uri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ?ara miki zaman lafiya da mijinki"

Nabila ta ce "Ai ba mijina bane mama"

"A'a ba Alhajin ba, Aminu"

Cikin mamaki Nabila ta ce "Aminu kuma? Nifa ban ta?a aure ba, ba ni da aure" tayi maganar tana murmushi.

Babar ramma ta ?oye mamakinta, kar kwa?arta tayi ruwa ta ce "Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke ta ?o?ari a kanmu"

Nabila ta ce "Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a rayuwarmu"

Maman ramma ta ce "In sha Allah, addu'a yanzu aka fara"

Nabila ta ce "Na gode sosai" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa.

Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba.

A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi.

"Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an ri?a a gida babu aure, abun bai yi miki yawa ba kuwa Nabila" Sauda tayi maganar tana dariya.

Ta sake cewa "
An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda ba?in naci, kin li?e mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da ba?in cikin ki a banza ba"

Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta ya?a mata magana.

"Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ?i karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ?ayan ma sai na tsinketa, sai ku ji da?in zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki bayar nonsense"

Sauda ta tashi a ?ufule, Nabila ta ce "Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki ka zauna"

Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta.

****
Cikin mamaki Abdul ya ?ago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwa?a masa.

"Ina na kai mini ku?i Abdul?"

Abdul ya yi shiru ya?i magana.

"Ka gaya mini in da ka kai mini ku?i, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ?acin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai watsa mini ?asa a ido ba, ina ka kai mini ku?i?"

Mahaifiyar Abdul ta ce "Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina ku?in da ya zuba a account ?in ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?"

Abdul ya numfasa ya ce "Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a" ya fa?a kai tsaye.

Salallami suka hau yi, da tafa hannu.

Indabo ya ce "Abdul, ku?in ka kwasa ka ?arar a kan garin yar matsiyata da karuwa?"

Ya girgiza kai ya ce "Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fya?e nayi mata, nayi hakan ne, dan na goge laifina"

A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ?iba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar P.A ya janye shi daga jikinsa.

"?arya ma kake yi, ka fito mini da ku?ina, sai na yi seazing ?in asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita".

"Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta"

Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, ku?in da suka yi sama da fa?i da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da ku?in da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama ku?in mutane ne na wasu hukumomi a ?asa, ga balli na neman tashi, kuma Abdul ya yi masa hauka.

P. A ya ce "Kayi ha?uri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara kashe case ?in can na gaban kotu tukuna".

"Na fara tunanin anya Abdul ?a na ne? ?iri?iri ya za?i mace a kaina, ni zai tozarta?"

P.A ya ce "Jarabta ce da kuma ?uruciya ke damunsa"

"A shekara talatin da shidan ne ?uruciya?" P.A ya din ga bashi ha?uri yana lala?a shi, Abdul kuwa tunu yayi ficewarsa.



*****

Madaki na zaune a cikin ?aki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ?ofar gidan da yake.

Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce "Madaki, yan ?ofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta fama da su, sai ?o?ari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka"

Madaki ya tashi ya ?walalo ido, sai dai kan yayi magana, sun fa?o gidan, sun kai su bakwai, suka zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na fa?a da yaran madaki.

Duk da akwai ?arfin zuciya, yana ta ?o?arin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ?wari, suka din ga saransa, ?arshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ?asa tamkar abun banza, duk da iya ?o?arin da yaransa suka yi, su ?wace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon ?aukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da sa?o, daga ?arshe da

Please Login or Register in order to submit comment