Reading KARFE A WUTA Chapter 74 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma baya ta tata, ga wannan tsohon ciwon nata da ta fama. Zuwa yaushe Abba zai fuskanci gurbin ido ba ido bane ba, duk wani abu da ya faru a baya, bata san an yi shi ba, ba ta san maman nata ba dama wannan an tabattar mata da bata raye, to mahaifinta fa, komai lalacewarsa zata so ta ga abun ta, kuma komai ya yi wa mahaifiyarta, wani abu ne da ya wuce a baya, da ba ta nan ma aka yi shi, to na menene za a gadar mata da wani abu da ba shi da tushe balle cikakkiyar makama.

Ta zabura ta tashi, ta watso drower littatafanta, ta ?aukko hotunan mahaifiyarta, cikakkiyar bafulatanar yarinya ce ba wata babba ba, fara sol da ita mai dogon hanci, tayi ?auri irin na mutanen da, ta zubo da dogon gashinta ta ?ar?ashin ?an kwalinta, har ka kafa?arta, dukkanin hotunan uku, fuskarta ?auke da murmushi daga yanayin hotunan zaka fahimci ba ta da hayaniya, kuma mai yawan murmushi ce.
Ta da?e tana kallon hotunan tana kuka, ta gaji ta kwanta a kan gado, sai ajiyar zuciya take yi.

Washegari da safe, ta shirya zata tafi wurin aiki, ta shiga wurin Abba ta gaishe shi, amma ya shareta ya?i amsawa, sai gajiya tayi, ta tashi ta fita.

Ko da taje wurin aikin ma, kanta ta kifa a kan teburin office ?in ta.

Barrister Habib har yayi knocking ya shigo, ba ta sani ba, sai da ya daki teburin, sannan ta ?ago.

"Nabila ya dai? Na ji program ?in ki ya ?au hankalin mutane, ki zo a mayar da hankali wurin neman shaidu, kin shigo kuma kin zo nan kina bacci"

Tayi shiru ba ta ce Komai ba.

"Wai meyafaru ne?"

"Ba na jin da?i ne"

"Yasalam, sannu kuma kika fito? Kina da tiral ne yau?"

"A'a, na zo ne dama mu cigaba da aikin shari'ar nan, ai na sha magani, bari na biyoka office ?in"

Tare suke aikin, amma sam hankalinta baya kan aikin, ?arshe ya ce, su bari sai ta samu sau?i tukuna.

***

A wani wurin cin abinci saifu suka ha?u da Abdul, suka zaune saifu ya ce "Mutumina harkar siyasar nan duk ta ?oye mana kai, wurin chilling ?in ma duk ka daina zuwa. Hafsa ta ce tana son ta zo ta ganka, na ce ko ta je asibiti baka zama, ayyuka sun yi maka yawa, asibitin ma ba wani zama kake yi ba"

Yayi murmushin ?arfin hali ya ce "Ya jikin nata?"

"Da sau?i sosai Alhamdilillah, likitanta ma sun sallameta, sun ce ta warke, ina ga wani abun ne yake damunta, ta ce kafi dubata sosai, na rasa wani siddabarun kake yi wa patient suke li?e maka"

"Saif, mu bar wannan maganar, akwai damuwa fa"

"Ta me?"

"Haryanzu babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi kuma ta matsa mini, kullum cikin kuka take"

Saifu ya ce "Ai fa Abdul ka yi mugun ganganci abun da ka aikata, ka mayar da ita wurin iyayenta, tun kafin asirinka ya tonu, sunanka ya ?aci"

"Saif, ni fa ba ta sunana ya ?aci nake yi ko akasin haka ba, ni wallahi burina kawai na cigaba da ratuwata da ita, wani irin abu nake ji a kanta, da rabani da ita tamkar rabani da rayuwata ne"

"Kai Abdul, ba ka gama ?ibar abun da kake so ba, ko haryanzu bai isheka ba?"

"Ba wannan nake yi wa ba, ita nake so, tun bayan da na ?aukota take bani tausayi, ka san ban ta?a raping ba, sai a kanta, wallahi son rahama nake yi, so mai tsanani".

Cikin mamaki Abdul ya ce "Ta??ijan, aurenka ne fa yake gabatowa, yanzu yaya kenan, gashi ana ta fitina a kan ainihin wanda ya yi mata fya?en, wata lauya ta kafe, sai an fito da ita ta bayar da shaida a kotu. Ina ga fa dolenka ka gaya wa mahaifinka gaskiya, ya ?auki matakin da yakamata a rufe abun nan".

"Ina son gaya masa, amma ina tsoron abun da zai iya yi, ba zai ?auki maganar da sau?i ba"

"To ai kuwa ko da yaya zai ?auki maganar, haka ne kawai mafitar"

Abdul ya yi shiru yana zancen zuci.

***
Viper yana zaune, ya tsurawa hoton jauhar ido, yana hararo kamannin Nabila a cikin kansa.

Walid ya dafa shi, ya ?aga kai ya kalle shi.

"Ya ake ciki ne? Mutuniyar kwana biyu, yakamata ace fa shirye-shirye sun yi nisa a kan shari'ar ka, ta ina za a fara?"

Viper ya ce "Fushi take yi "

Walid ya ce "Fushin me? Wani abun ya faru ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Akwai magana a bakinta da yakamata na saurara, wata?ila zai haska mini abun da kake gaya mini, sai dai ta bijiro da abun da dole na taka mata burki"

"Wane abu ne?"

Ya ?an yi shiru sannan ya ce "Bakomai"

"Mai zamani, yakamata ka din ga bin komai a sannu, mata fa dukkansu ba irin jauhar bane, jauhar one in million ce, ba kowace mace ce zata iya juriyar da ta yi ba, kar ka yi treating ?in Nabila yadda kake treating ?in Jauhar, suna da banbanci"

Yayi shiru, ya cigaba da kallon hoton hannunsa.

"Allah ya jaddada rahama a gareki, ya kyautata makwancinki my wife " yayi maganar yana shafa ha?oranta na jikin hoton da yake da shi da ita ne, fuskarsa da ?uruciya sosai lokacin.

Walid ya ce "Amin" ya kar?e hoton, ya ajiye shi a wani wurin.

Yayi shiru yana tunanin ko me Nabila take son ta gaya masa? Ko yanzu tana wani hali? Da gaske son shi take yi, ko kuwa dai still da wasa take yi? Kukan da tayi ya tabattar mata ba wasa take yi ba.
To su mata babu wuya sun fara son mutum kenan? Ya ga damuwa sosai da sosai a cikin idanunta da suka ha?u, ya so ya ji menene damuwarta, amma ta zo da lamari mai girman gaske, son da take yi masa wahalar da kanta kawai zata yi, yana cikin wannan halin na ?oye-?oye, idan ta fara son shi yaya zata yi, tun da ba aurenta zai yi ba, kuma shi ba ma wannan ne a gabansa ba gaba ?aya.

***

Kusan kwanaki hu?u, amma Abba baya saurar Nabila, fushi yake yi da ita sosai, gajiya tayi da fushin da yake yi da ita, ga habaici da yar da magana da ake yi mata a gidan.

Ta shirya tafiya aiki, ta shiga ?akinsa, ya na karyawa.

"Abba ina kwana" yayi mata shiru ya cigaba da karyawa.

Ta tashi ta je gabansa ta zauna cikin kuka ta ce "Dan Allah Abba ka yi ha?uri ka yafe mini, dan Allah ka yi ha?uri ka yafe mini, in sha Allah ba zan sake maganar babana ba, idan raina ne ya ?aci aka yi mini gori, duk sai na ji babu da?i amma dan Allah ka yi ha?uri ka yafe mini ba zan sake ba" da fari yayi mata shiru, amma daga baya ya numfasa ya shafa kanta ya ce "Kukan ya isa haka, na ji na yafe miki, duk da kin sha yi mini wannan al?awarin amma ba kya cikawa, yau da mahaifinki wani abun kirki ya tsinanawa mahaifiyarki, rabuwar arziki aka yi, babu yadda za ayi na nesanta ki da shi har haka, na yanke duk wata ala?a tsakaninki da shi. Ki yi ha?uri na san kina ha?uri da abun da ake yi miki, da zarar kin yi aure shikenan kin wuce wurin, ki yi ha?uri ki cire maganar mahaifinki a zuciyarki"

Nabila ta jinjina kai, amma ?asan zuciyarta ba ta ji zata iya daina maganar mahaifinta ba.

Ta tashi ta fita ta tafi aiki, ita ma ta fita daga harkar Nasir gaba ?aya.

Yau ba ta da shari'ar da zata halatta, dan haka tana office tana ta nazarin shaidunta, da za su yi appeal.

Wayarta ce tayi vibrating, ta ?aga ta duba "Mu ha?u a restaurant ?in da ki ka je, zamu yi magana mai muhimmanci" ta zubawa wayar ido tana kallonta, ta ajiye wayar. Har mamakin kanta take yi, yadda take abu babu tsoro take wannan kasadar haka.

Ta ajiye wayar ta kifa kanta, can ta mi?e, ta tattara system ?in ta da kayanta, ta tashi ta fito, suka yi karo da barrister Habib.

Ya ce "Yauwwa wurinki zan zo dama, ina son mu je unguwar da abun nan ya faru ne, ko da wani abu da zamu kuma samu, da bamu haske a kan shari'ar"

Ta ce "Amm ganin likita zan je ne, ko mu bari sai gobe in Allah ya kaimu?"

Ya ce "Subhanallah, jikin ne dai?"

"A'a ba wani abun damuwa ne sosai ba, zan dai je na ga likita ne, yau yakamata na koma dama"

"Ok, to Allah ya ?ara afuwa"

Ta amsa da Amin.

Ta je wurin cin abincin, ta kira wayarsa ya ?aga.

"Gani na zo ina wurin"

"Ki mi?e sosai ciki, ki tambayi Vip 2" ta ?arasa ta tambaya, aka nuna mata, ta bu?e ta shiga.

Yana zaune, ya ?ora ?afafuwansa a kan tebur, yana sanye da facemask da facing cap ya rufe fuskarsa.

Fuskarta babu annuri, ta ?arasa ta ja kujera ta zauna, ta ajiye jakarta da wayarta, da mukullin motarta, amma ba ta ce komai ba.

A yanayin yadda ta tafi wancan karon, bai zaci da ya ce ta zo zata kuma zuwa ba.

Tayi masa shiru, tana danna ?aramar wayarta.

Ya ?an daki teburin ya ce "Attention, magana zamu yi"

Ta ajiye wayar ta ce "Ina ji"

Ya ja babbar wayarta, ya bu?e ya ?aukko tab ?in sa, ya fara daddanawa.

Mai kawo abinci yayi knocking, ya kawo ruwa da lemo.

Ya sauke facemask ?in sa ya ce "Yaya ake ciki da maganar wancan case ?in, zuwa yaushe zaku yi appeal ?in? Sonake ki kammala da wancan shari'ar, sannan ki mayar da hankali a kan tawa, already ina da shaidu guda biyu a ?asa" har yayi maganar ya gama, bata ?ago ta kalleshi ba, wasa kawai take yi da zobunan hannunta.

"Magana fa nake yi"

"Ina ji ai"

"Ba jin nake bu?ata ba, hankalinki zaki bani" iya idanunta ta ?aga ta kalleshi tana yi masa wani irin kallo.

"Ina magana a kan yaushe zaki yi appeal, ki zo ki fara processing tawa, ina da shaidu biyu a ?asa" still ba ta ce komai ba ta cigaba da kallonsa.

Zubawa sarautar Allah ido yayi, ya saka mata nasa idon shi ma, ta gyara zamanta, ta kwantar da hannunta a kan teburin, ta ?ora kanta ta kwanta ta yi masa shiru.

?asa yayi da muryarsa ya ?an matsa ya ce "Meyake damunki ne?"

Kawai ta fashe da kuka, yayi mata shiru, tayi iya yin ta, ta ?ago ta share hawayenta ta ?auki jakarta, ta ?auke wayarta daga gabansa, ta juya za ta fita.

"Ina miki magana zaki tafi? Ina zaki je ina yi miki magana?" Yayi maganar cikin tsawa da sai da ta firgita, ta ja da baya tana kuka.

"Talk" yana mata tsawa tana ?ara sautin kukan nata.

"Meyake damunki? Kin san haka zaki yi mini, ki ka yi mini tayin dawowa normal rayuwata? Ki ka ce zaki taimaka mini"

"Ina amfanin tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani kuma yake so? Ba cewa kai baka so na ba? Rashin amsa tayina bai yi mini ciwo ba, irin halin ko in kula da ka nu na wa rayuwata, hakan na nufin duk da risk ?in da na saka rayuwata baka damu ba ko da zan rasa rayuwata. Saboda kana ganina a haka do you know what am going through ne? To an fasa taimakon naka, i destroy the deal and i am out of it, ka je kayi duk abun da ka ga dama"

Murmushi ya yi, sai da ha?oransa suka fito, abun da ba ta ta?a gani ba.

"Angry bird, always angry for no reason, duk saboda na ce bana sonki, ki ke wannan abun? Ba zan ta?a sonki ba, zuciyata ta jauhar ce itaka?ai"

"Ai baka burgeni ba, da aka zauna baka bi ta lahira ba"

Viper ya ce "Ai nayi niyyar bin nata, ki ka hanani, wannan deal ?in sai an kai ?arshensa da ke"

"Komai zaka yi, ba zan sake zuwa in da kake in dai ni yar halak ce, babu amfani tarayya da mutumin da kansa kawai ya sani" ta ra?a shi ta wuce ta bar wurin.

Ajiyar zuciya yayi, ya koma ciki ya zauna.

Gida ta tafi, abun duniya duk ya dameta, tana ganin kiran sumayya, amma ta share ba ta ?agawa, gaba ?aya ta zama so silent.

***

Abdul ne yake kallon ramma, yadda take ya shiri, ya ce wai shirin me ki ke yi haka ne?

"Asibitin ka zaka tafi da ni, ni dai mu je ka duba ni na tabattar"

"Rahama haryanzu tunaniki ?arya nake yi kenan?"

"To wa ya sani, tun da haryanzu ban ji na warke ba, amai ya?i tsayawa, muje idan ma shi ne kawai ka zubar da shi"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ni ba na zubar da ciki gaskiya"

Ta kalleshi she?e?e ta ce "Yaushe ka fara tsoron Allah, har ka ke cewa ba ka zubar da ciki?"

"Ai lokacin da zan kama aiki, rantsuwa nayi, ba zan ci amanar aikina ba"

"Kai har wata darajar rantsuwa ka sani? Ni ka daina yi mini wasan kwaikwayon nan, kawai mu tafi"

"Rahama mutuwa fa aka yi a wurin zubar da cikin nan"

"Na ji, bakomai, Allah ya yi mini rahama".

Ya sauke numfashi ya ce "Na ji, zamu je, amma wallahi ki ka takura mini ba zamu je ba, kuma kar ki dame ni"

Ta ha?e rai ta ce "Zan baka nan da sati ?aya, idan na ji shiru zan kuma magana" ta cire mayafinta, ta bar ?akin.

***
Unguwar gidan aikin ramma take son sake zuwa, kamar yadda barrister Habib ya bu?ata, take ta yi masa yawo da hankali.

Tana daf da shiga mota, ta tsaya tana amsa kiran waya.

"Salamu alaikum, Barrister, walid ne"

Ta ce "Oga walid, ya kake?"

"Lafiya ?alau, mutumin ne babu lafiya fa, ko zamu ha?u a wani wurin mu kai shi asibiti a motarki, saboda yanayin tsaro"

Gabanta ya fa?i ta ce "Subhanallah, wani abun ya je ya sha?"

"A'a, ai rabon da ya sha wani abu, an kwana biyu, ciwon ciki yake yi, tun yana yi sama-sama, tsakanin jiya da yau har suma yake yi"

A rikice ta ce "Ya salam, a ina zamu ha?u to? Ina wurin aiki gani nan"

Da gudu gudu, ta ?arasa ta hau motar, ta ja, tana tafe tana waya da su, har suka ha?u, sun ?aukko shi a adaidaita sahu.

A sume suka saka shi a motarta, hankalinta yayi mummunan tashi ta ce "Oga walid yana numfashi?"

"Eh yana yi, Suma dai yake ta yi"

"Yanzu wane asibitin zamu nufa? Ka ga wancan ga matsalar da aka samu"

Suka tattauna suka yanke shawarar kai shi wani asibitin daban.

Asibitin shi ma a wajen gari yake, amma yayi kyau ya tsaru, ko ina tsab da shi.

Nan da nan aka shiga da shi emergency, aka fara yi musu tambayoyi a kan meyasame shi.

Su walid suka yi musu bayani, aka tafi da shi wurin yin scanic.

Nabila ta fita da sauri, dan ta je ta ji ya tsarin Asibitin yake, da biyan ku?in, taga ?an mama yana ?o?arin komawa in da ya baro su.

Ta ce "Sannu ?an mama"

Ya ce "Yauwwa, an gano meyake damun nasa?"

Tayi murmushi ta ce "Suna ?o?arin yin hakan dai, wannan karon ma ka je ka sanar da su ne su zo su biya bills ?in asibitin nasa?"

Yayi turus yana kallonta, ya ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda wancan karon kayi, kai ka yi waya aka biya bill ?in Viper, dan babu wanda ya san mun je asibiti, yanke muka din ga yi, mu ?addara ma wani ya sani yana bibiyarmu, ana tsaka da treating ?in sa hankalinmu yana kansa, ka zame ka fice. Kana kawo masa miyagun ?wayoyi a duk lokacin da ya bu?ata, abubuwa da yawa idan ba na kusa da shi ba babu yadda za ayi a san su, wa ka ke yi wa aiki?"

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



?an mama yayi murmushi, ya ?ara taku biyu gabanta, ya kalleta ya ce "You better count yourself out of this. Ba ni da niyyar cutar da Viper, da cutar da shi zan yi, da tuni na yi so bakinki ?anin ?afarki" daga haka ya mi?e ya nufi in da suka baro su walid.

Aka fito da Viper a kan gado, aka ce za a ba su ?aki, za a turawa likita result ?in.

Kamar yadda Nabila ta yi tsammani, an biya bills ?in, ta din ga yi wa ?an mama kallon tuhuma, shi kuwa da sun ha?a ido, sai yayi mata murmushi, hakan ya ?ara jefata cikin tunani.

Likita ya shigo da file a hannunsa, suka sake gaisawa, ya tatta?a cikin Viper, sai dai duk da an yi masa allurai ya samu bacci, da ya ta?a cikinsa ?angaren dama, sai da ya zabura ya motsa.

Ya duba scanic ?in hannunsa, ya ce "Hantarsa ce ta kumbura gaskiya, amma ?odojinsa da sauran abubuwa lafiya ?alau, amma duk da haka zaku yi x-ray na cikin, mu sake tabattarwa ko da wani abun"

A tsorace Nabila ta ce "Likita hantarsa ta kumbura kuma?"

"Eh, amma karki damu babu wani abu in sha Allah, idan aka yi x-ray ?in, akwai likitanmu da zai zo ya duba shi, ba wani abun tayar hankali bane ba, zai samu sau?i in sha Allah"

Walid ya ce "Allah ya sa"

?an mama ya ?urawa wayarsa ido, sannan ya kalli Nabila, yayi mata alama da su ha?u a waje.

Ya tashi ya fara fita sannan ta bi bayansa.

Ya ce "Ana bibiyarki, yanzu aka turo mini sa?o, zaki bani mukullin motarki, zan kawo miki ita gida a matsayin bakanike"

"Nifa ban fahimci duk wannan abun ba"

"Tsayawa dogon bayani, ba zai haifar da ?a mai ido ba, ki ga gaggauta muje na raka ki, na ?ulla da ke wata hanyar ki hau napep ki tafi gida, zan kawo miki motar gida".

"Kamar wani abun kake shiryawa a kaina" ya mi?a mata wayarsa, ta kar?a ta duba, message aka turo masa aka yi masa bayanin kar ta tafi a motarta, akwai yiwuwar a kamata, ko kuma ayi mata wani abu.

Bai bari ta yi wa su liti sallama ba, ya fitar da ita daga asibitin, ya tare mata abun hawa ta hau ta tafi tana mamaki.

Ta koma gida, duk a gajiye, abubuwa duk sun dame ta, tana ta tunanin ciwon Viper, tayi ta addu'a Allah ya bashi lafiya, sai ta ji ba ta kyauta ba maganganun da ta gaya masa, ha?uwarsu ta ?arshe.

"Allah ka bashi lafiya, ka bani ikon cika masa al?awarin da nayi masa"

"Arfa"

"Na'am" ta amsa tana daga zaune.

"Ina motarki?" Nasir yayi maganar yana shigowa cikin ?akinta.

"Lalacewa ta yi, na bawa bakanike"

"Wane bakaniken?"

"Bakanike dai mai gyara mota"

"An ce an ganki da wasu maza a motar, a can ring road, sai dai ba a san in da ku ka yi ba, na saka jami'ai a arear in da ake tunanin kin bi, aka kama wani da motar yanzu haka yana tsare a wurina"

Ta mi?e tsaye ta ce "Wai dan Allah yaya me kake nufi da ni ne? Motata ta lalace zan yi gammo na ?auketa a kaina ne, na kira masu gyara su tafi da ita sai ya zama laifi, na menene zaka saka a din ga bibiyata ma?"

"Saboda baki da gaskiya arfa, gaba ?aya kin canza, kuma ba kya tsoron salwantar da rayuwarki"

"Kalli, kamar da gaske ka damu da rayuwar tawa, ba ta rayuwata kake yi ba, mafitar ka kawai kake nema Yaya Nasir, amma ai ramin ?arya ?urarre ne ka cigaba da bibiyata. Na ro?e ka ka saki bawan Allah, gyaran mota kawai na bashi, abun arziki bai kamata ya zama na tsiya ba" ta fita daga ?akin gaba ?aya ta bar shi.

Da daddare ta kira walid, ta ji ya jikinsa, ya tabattar mata jiki da sau?i sosai, ya farka ma.

Nabila ta ce "Oga walid, shaye-shayen nan ne fa ya fara ta?a shi, ya janyo masa wannan matsalar"

"Ai bama sai kin fa?a ba, shi ne ba wani abun ba"

"Dan Allah oga walid ku daina wannan rayuwar, idan ba haka ba da ?uruciyarku haka zaku rasa lafiyarku ku mutu, dan Allah" yayi murmushi ya ce"Karki damu, za a daina in sha Allah"

"Allah ya sa, ayi masa sannu dan Allah"

Ya ce "Zai ji in sha Allah" bayan ya kashe wayar, ya fita yana mitar ina ?an mama ya tafi har wannan lokacin bai dawo ba.

A harabar Asibitin ya ha?u da ?an mama, kamar ya kwa?e shi, dan haushin abun da yayi, shi kuma bai gaya masa ainihin abun da ya faru ba, ya ce masa wani wuri yaje.

"Ka wuce ka je ka zauna da shi, liti ya je nemo wani magani, ni kuma zan je gida".

"Kar ka je gidan nan oga Walid, hanya babu kyau, cinnakun nan sun ?ana mana, akwai wani abu a ?asa ka ?ad da sahu, ka lafe a wani wurin, akwaisu sosai a hanyar gidan nan"

Walid ya ce "Na fahimta, muddin kaga wani abu da baka yarda da shi ba, ka kira sanar mini" ya jinjina masa kai.

Nasir yana zaune ya gama cin abincin dare, aka kira shi a waya.

Ya ?aga a take, ganin daga office ?in su ne.

"Yalla?ai yaron nan fa, wasu sun zo sun yi belinsa"

"Wane yaron?"

"Wanda muka kama, kuma sun ?auki motar ma"

Tashi tsaye yayi ya ce "What? Meyasa ku ka bari suka ?auka? Waye ma ya ce a sake shi?"

"Manyanmu ne yalla?ai" mukullin motarsa ya ?aukko ya fito da sauri, kawai ya tarar da motar arfa a gareji.

Bin motar ya din ga yi da kallo, dan ya tabattar ita ce, ko ba ita ce ba. Bai ha?ura ba sai da ya dangana da zuwa ya dudduba ya tabattar dai ita ?in ce.

Bai tsaya ba, ya shiga cikin gidan, ya tarar da ita a falo, suna kallo a falon ita da mutanen gidan.

"Arfa waye ya kawo miki motarki?"

"Ina ga bakanike ne, yaro ne ya kawo mini key ya ce an kawo motar" tayi maganar cikin ko in kula.

Ganin da mutane a wurin, ya sanya bai ja maganar ta yi tsawo ba, ya bar falon.


***
Liti yana zaune yana game a wayarsa, likita ya shigo, ya kalli likitan, likitan ya ce "Sannu ko, ya mai jikin?"

"Da sau?i"

"Masha Allah, naga ya samu bacci ma, shi ne mai hepatitis ko? Yayi maganar yana duba file ?in Al'amin. Kodayeke ma bacci yake yi, bari ba sai an tashe shi ba, idan aka yi x-ray ?in na duba shi, idan ya farka gaba ?aya" yayi maganar yana ta?a cikin Al'amin. Sai dai yayi shiru yana kallon Viper, yana ?o?arin ganin fuskarsa sosai, dan kamar ya san shi, sai dai yanayin kwanciyar da ya yi, bai bashi damar yin hakan ba.

Ya kalli file ?in Al'amin, an rubuta Muhammad Ibrahim. Ya juya zai fita, ya tsaya ya sake waiwayowa ya kalli Al'amin ya ?an yi shiru sannan ya fita.

Yayi iya ?o?arin sa wurin tuna a ina ya san shi, amma ya kasa dan haka dolensa ya ha?ura.

***

"Rahama"

"Na'am"

"Zan fita da ke, zamu je asibiti, wallahi idan ki ka yi misbehaving, ke da ganin mahaifiyarki har abada"

"Idan da zan yi misbehaving, da tuntuni da kake fita da ni da nayi, amma na fara gajiya da ?aryar da kake yi mini, na cewa gwargwadon bin umarninka da nake yi, shi zai sanya ka sada ni da mahaifiyata. Ina tsoron tonuwar asirina na wula?anta a idon duniya, shiyasa bana yi maka ihu, da neman agaji, sonake ka mayar da ni cikin sirri da rufin asiri, yadda ba zan tozarta da yawa ba, amma haryanzu na kasa gane in da ka dosa"

Ya ce "Zaki fahimta ne, muddin ki ka yi yekuwa, to ke zaki kunyata fiye da ni, kuma ni zan iya wanke kaina, ke kuwa zaki tozarta, dan sai kin samu masu ?oraki a social media kowa ya ganki, kin san duk abun da namiji yayi ado ne"

Ta girgiza kai ta ce "Wannan wani banzan tunani ne, na wa?anda ba su san girman Allah ba, babu al'ada a batun sa?on Allah. Allah bai ware wutar mace ba, kuma bai ware ta namiji ba, bai ce zai sassautawa wani ba dan yana wani jinsi idan ya sa?a masa ba, dan haka babu ado da zunubi, idan al'ada ta nuna maka duk abun da ka yi ado ne, addini kuma ya koyar da kai tsoron Allah da tsoron azabarsa"
Wato ramma akwai baki, wasu lokutan duk abun da yake ji da shi, sai ta ?ure shi ta hanyar kafa mishi, hujjoji da addini, dan haka ya ja bakinsa yayi shiru, suka cigaba da shiri.


Tana sanye da ni?ab, a kan dogon hijjabinta, yake nuna mata wurare a cikin asibitin, wai nan ma branch ne na Asibitin, ba

Please Login or Register in order to submit comment