Reading KARFE A WUTA Chapter 25 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai, kamar an ciro shi daga kwata, yayi ba kyan gani.

Tuni ta suma a wurin, dan kuwa hannunta ta ?ora a kansa ba ta sani ba.

Maimakon ya tashi, sai ya zuba mata ido, cikin takaici, abu ka?an sai ta suma, ko ta hau ihu.

Kamar ba zai tashi ba, sai kuma ya mi?e.
Ya saka hannu ya ?auketa ya kwantar da ita a kan kujera, sai dai jikinta ya yi zafi sosai, sai yanzu yake tunanin zazza?i take yi kenan?.

Ya duba ledar magungunan da ta sayo, maganin ?aya mai hoton sauro, ?aya kuma pcm ne.

Ya kama gefen hannunta, ya ji bugun zuciyar ta yana bugawa da sauri, ya saki hannun nata yana kallonta, ita a rayuwata komai ma tsoro yake ba ta kenan.

A hankali ta fara motsawa, ta yin?ura za ta tashi, ya ce "Koma ki kwanta" ta ?aga idonta a hankali ta kalleshi.

"Tsoro nake ji" ta fa?a muryarta na rawa cikin tsoro.

Ya sake kama hannunta, yana jin bugun zuciyar ta, ya saki ya ce "Tashi" ta yin?ura ta tashi a hankali, kanta na sara mata ga jiri saboda yunwar da take ji.

Tana daga kan kujerar a kwance, ya ?age ?aya kujerar da ?adangaren yake ?ar?ashin ta, kawai ya saka hannu ya dan?i ?adangaren ya jefa shi waje.

"Na shiga uku master, ?adangaren ka ke kamawa da hannunka"

Tsaki yayi, ya wuce ?akinsa, jikinta ya din ga rawa, tsigar jikinta ta din ga tashi. Ya dawo ya dire mata leda, ya ce "Ki ci ki sha magani" ya jefa mata wani kwali sannan ya fita.

Kwalin ne ya fara ?aukar hankalinta, ta ?auka da sauri tana dubawa, sabuwar mp ce kar 'yar ?arama mai kyau.

Ba ta san lokacin da ta yi murmushi ba, ta hau kukkunata tana dubawa, sai da ta gama, ta ajiye ta bu?e ledar.

Irin meatpie ?in nan ne oasis manya kusan biyar, da ?atuwar robar fura da nono.

Kasancewar a yunwace take kuwa ta hau ci, ta ji babu da?i kwana biyu tana ciwo, amma bai iya yi mata sannu ba, dama magani ba ta saka ran ya saya mata ba, mutumin da bai ba ta abinci ba wane magani zai bata, ashe yana sane, sannu ce ko ya jiki ba zai iya ce mata ba.
Sai dai da tuna yadda ya ?auki ?adangare da hannunsa, sai tsigar jikinta ta tashi.

Ana yin sallar isha'i ya dawo, mp ?in ta har da fitila.

Ta tashi tana yi masa sannu da zuwa, ya wani maze ya bata wata ledar, sannan ya zauna ya ce "Ki nemi wata ma'aikaciyar idan akwai a nan kusa, tayi miki, idan ki ka je wurin wancan ?an iskan na bakin hanya kuma ni da ke ne"

Ta saka hannu biyu ta kar?a, allurar zazza?i ce mai tsada ya sayo ya kawo mata, amma bai iya cewa ya jiki ba.

"To godiya nake master, Allah ya ?ara arziki ya sa a fi haka, na ga sa?o ma na gode sosai da sosai Allah ya sa afi haka".

"Amin".

Ta ce "Ga naka na ajiye maka"

Ya ce "Idan zan ci ba sai kin ce na ci ba, ki daina kuma wannan mugun tsoron, komai ya baki tsoro, idan ba haka ba ki kashe kanki a banza"

Jauhar ta rausayar da kai ta ce "Nima ban san ina jin tsoron ba ne. Amma kai ba ka jin tsoron sa ka ri?e shi da hannu?"

"Ban sani ba? Rannan kwa?o yau ?adangare, meye abun tsoro a jikinsu, har da suma saboda ?adangare" tayi shiru ta sunkuyar da kai.

Sai da ya gama sannan ta ce "Ka yi ha?uri to, ban san ya ake yi nake jin tsoron ba".

"Idan ma kina sane ki cigaba da yi mini ihu a gida kamar gyare".

Sai da ta yi murmushi ta ce "Zan koyi jarumta, zan daina jin tsoro in sha Allah. Yauwwa master yaushe zamu je ka kai ni na gaida su mama? Ba su ta?a ganina ba, ban ta?a ganinsu ba, su hajiya kawai na ta?a gani, yakamata ka kaini na gaishe su. Sai ayi girki mu je mu gaishe su, na ga haka ake yi".

Shiru yayi, yana tuna Ummansa, tana yawan cewa Allah ya raya mini babana na ga aurenka, in ga mai sa'ar da zata auri ?an autan mazana

Jauhar ta ce "Ka yi ha?uri idan na ?ata maka rai ne maganar da na yi"

Ya tashi tsam ya ce "Yauwwa, Ina sake jaddada miki, idan ba zaki iya zama ba, ko kin gaji zaki iya komawa gida, babu takura, na ga shekaranjiya kina ta koke-koke, idan da takura you are free to go" daga haka ya nufi ?akinsa.

Gabanta ya fa?i ta fara tunanin, me ta ce da zai ?ata masa rai har haka?.

Haka nan ta ji ba ta fatan abun da zai sake mayar da ita gida yanzu, da sunan zawarci ko ace ta kasa zama, saboda ta san dama mugunta ce ta saka aka aura mata shi.

A ranta ta ce 'Zan jure, in sha Allah zan bawa mara ?a kunya, in sha Allah, Allah ba zai kunyata ni ba, ba zan tagayyara ba"

Lokaci-lokaci yake le?owa falo, sai ya hangota tana aikin stone ?in ta, tana jin radio a mp. Yana so yayi mata maganar ta je ayi mata allura, amma ya fasa.

Bacci ta fara, ji ta tafi ta je ta kwanta, har ta fara bacci aka kawo wuta, hasken lantarki ya hasketa, ba shiri ta tashi, sai a yanzu ta tuna ba ta kashe ?wayayen ba, ta fita falo dan ta kashe, taga Al'amin ya fito daga ?akinsa, yana soke wu?a a ?ugunsa.

Ta tsura masa ido tana kallonsa, bai san tana falon ba, yana ?aga ido, suka yi ido hu?u, ?aure fuska yayi ya zo zai fice.

Ta ce "Master ina zaka je a daren nan, kuma?"

Ai ko sake kallonta bai yi ba, ya nufi ?ofar fita.

"Dan Allah kar ka je in da za a illataka, zuciyata ba ta yi mini da?i in ga kana zubar da jini".

Bai tsaya ba, sai da ya dangana da tsakar gida, ya kama katanga ya dira, ita kuma ta zauna a wurin ta fashe da kuka mai ta?a zuciya.

Ko da ya fita titi, liti ya zo a kan babur ya ?auke shi, suka tafi.

Unguwar shiru, kowa ya shige gida, suka ma?ale a wani wuri su na shaye-shaye.

Can sai ga wanda suke hari, ya kwararo layin a kan babur, Al'amin ne ya fita da sauri, ya daki tayar gaban babur ?in, aikuwa ya fa?i ?asa da shi da babur ?in.

Suka rirri?e shi, Al'amin ya zagaya dai-dai kunnensa ya ce "Tijjani Faruk ko? Garga?i aka ce ayi maka, a kan rubuce-rubucen da ka ke yi a dandalin sa da zumunta, da wa?anda ka ke suka, da Switzerland na so na yi maka warning ?in, amma a yadda ka ke ?in nan, zaka iya ?ayewa idan nayi maka da ita, ko ira?i na saka maka a jiki ba zaka shura ba.
Liti, duba bayana, ka ciro Russia ka yi masa rijiya a cinya, ka yi masa eleven da ira?i a gadon bayansa".

Tijjani yana ihu, yana kururuwa, yana komai, liti ya caka masa wu?a a cinyarsa, ya yage masa riga, ya yanke shi sau biyu a baya, ya watsar da shi a wurin yana kururuwa.

Can gida mama tana ta sintiri, har sha biyu saura, ba ta ji an ce Tijjani ya shigo gida ya ?auki abinci ba, ta din ga kiran lambar wayarsa amma a kashe.

Tana ta mita, aka kira baba a waya, aka sanar musu, an tsinto tijjani a hanyar dawowa gida, an yanke shi da makami, an tafi kai shi asibitin cikin gari, sashen bayar da agajin gaggawa.

?ora hannu ta yi a ka, tana ihu tana ta shiga uku an kashe mata ?a.

Baba ya ce 'Ba cewa aka yi ya mutu ba, an yanke shi aka ce, ?ila masu ?wacen waya ne ki bari mu je mu gani mana"

Ya fita ya kira ma?wabcinsa, ya ce ya raka shi asibiti, domin su ga a halin da Tijjani yake ciki.

Ala'amin bayan ya koma gida, a falo ya tarar da jauhar, sauro yayi dandazo a kanta yana cizo, sai ajiyar zuciya take yi ta ci uban kuka.

Tsayawa yayi yana kallonta, tare da jinjinawa taurin kanta.

Kamar ya tsallaketa ya wuce, ya dur?usa ya kwasheta kamar tsuma ya nufi ?akinta da ita, yana zuwa ya kwantar da ita a kan gadon, ta bu?e idonta tare da ?ura masa ido.

Tsaki yayi ya fita, ta mayar da kanta ta kwantar a kan pillow.

Al'amin sawun keke ne, Allah ka?ai ya san in da ya dosa, ?azu ya gama cewa idan ba zata iya zama ba, ta tafi gida, amma yanzu ya tsinto ta a falo ya kawota ?aki.

Da safe ta dafa tea, ta kawo masa da sauran meatpie ?in da ya so jiya, yau bai yi rejecting ba ya kar?a ya fara ci.

"Master"

"Mmmm"

"Na iya irin wannan meatpie ?in fa, idan ka na so ka sayo mini kayan, na iya sosai mai da?i".

Ya ce "To".

Da tana jin kunyar cin abu a gabansa, amma zuwa yanzu ta saba, ta gama cin nata, ta je ta kwaso kayansa da suka bushe, tana ninkewa ta saka zare da allura, tana ?inke masa wa?anda suka yage.

Yana kallonta tana yi, shi kuma ya karkace zai kunna sigari.

"Master, shan sigari yana cutar da lafiya fa, ka din ga ragewa dan Allah, kar ka yi rashin lafiya".

"Kin je an yi miki allurar?"

"Zan sha magani, ba na son allura ne tsoro nake ji"

Tashi ya yi zaune ya ce "?adangare, kwa?o yanzu kuma allura, sannu 'yar madara. Sai ki biyani ku?in allurar da na saya" yayi maganar yana barsawa yana gyara gefen rigarsa.

Tayi dariya, jin yau ya kulata, har ya ?an yi doguwar magana da ita.

"To nawa ne, sai na tara da ka?an-ka?an na biya ka" yayi shiru yana cigaba da sakin haya?i.

Ta sake gyara zamanta ta ce "Master Mp nan fa tayi kyau sosai, Allah ya ?ara maka bu?i"

Ya jinjina mata kai.

Tijjani kuwa ba ma ya hayyacinsa, saboda ya zubar da jini sosai da sosai saran da su Viper suka yi masa, da ?yar aka samu ya farfa?o.
Cinyarsa sun yi masa rami da ?an buda, likitoci sai ?o?arin ceto ransa yake yi.

"Sai oga"

"Yaya na ji shiru fa, haryanzu kuna tsare da yarona".

"Na sani, trape ?in muke setting, idan muka yi gaggawa aikinmu zai kwa?e"

"Ok ina saurarenku".

Jauhar sai murna take yi, zata je registration makarantar su, dama tun da aka kawota ba ta je unguwar ba.

Da safe tana ta shiri, ya fito zai fita ya ajiye mata dubu ?aya ya ce "Ki hau mota"

"Na gode sosai da sosai, Allah ya sa a fi haka, ya ?ara bu?i, ya tsare mini kai" ba shiri ya kalleta, ya ga ba shi take kallo ba, sai jujjuya dubun take yi tana murmushi.

"Da ina da wata ba zan kasheta ba, ina son sabon ku?i sosai" tayi maganar tana ?ara fa?a?a murmushin ta.

"Sai ki ?inka ta ki saka tun da riga ce"

"Kuma zata yi mini kyau fa, adawo lafiya, Allah ya tsareka"

Ya amsa da "Amin"

Jauhar ta ?arasa shirinta, ta tafi makaranta, kamar yadda Baba ya ce mata ta je tayi registration, a nan ta ha?u da 'yan makarantar su, ta din ga murna sun ha?u da 'yan makarantar su, da malaman makarantar ma.

Ta din ga yi wa ?awayenta mitar ba su je gidanta ba.

"Jauhar wa zai zo gidanki kina auren ?an daba? Ba ma za a bar mu mu zo ba"

Jauhar ta yi murmushi ta ce "Ku daina fakewa da haka, ni da muke tare, ya aka yi bai yi mini komai ba?"

"A'a ai ke matarsa ce, mu kuwa fa"

Duk da ba ta gaya masa ba, haka kawai ta ji tana son ta je gida.

Ganin ko ta fita ba hanata yake yi ba, ya sanya ta nufi hanyar gida.

Gaba ?aya sun yi mamakin ganinta, Anty ta ce "Yaya, ya na ganki yanzu meyafaru?"

Jauhar ta yi murmushi ta ce "Lafiya lau anty, registration na zo na ce bari na biyo, tun da kun ?i zuwa".

Kallon jauhar suke yi, su ga ko akwai wani abu na tashin hankali a tare da ita, ko alamar duka ko makamancin haka, amma ba su gani ba, sai ma wata nutsuwa ta mussaman da suka gani a tare da ita.

Mama ta ce 'm"Jauhar kin kyauta, wato miji da?i, ki ka kasa zuwa ki duba ?an uwanki, ya kusa mutuwa"

Cikin tashin hankali jauhar ta ce "Subhanallah, mama ban sani ba ba shi da lafiya ne?"

"Ina fa, ya dawo daga aiki, aka samu wasu suka sassare shi".

Abun ya ?agawa jauhar hankali, ta ce musu ba ta sani ba.

Al'amin yana can wurin su Walid, kansa yana yi masa ciwo, ga yana jin yanayin jikinsa kamar zazza?i yana son kama shi.

Yana jin wayarsa na ta vibrating yayi banza.

"Viper wayarka fa ta cika mini kunne, dan Allah ka ?aga"

"?yale ni, kamar zazza?i ne zai kama ni"

"To ka kashe wayar mana".

"Ba zan kashe ba"

"Ka duba mana ko beb ?in ka ce take nemanka, yarinyar nan ta na kula mana da kai yasin".

Viper yayi tsaki, ya sake gyara kwanciyar sa.

Walid ya mi?a hannu, ya ?auki wayar ya ?aga ya ce "Ya aka yi?"

"Ka gaya wa uban gidanka, na ga cikarsa ta shigo mana arear, duk da kashedin da na yi kar ta sake zuwa, tun da ya kwasheta. Yayi ganganci mafi girma da muni, tun tun da ya bari ta shigo, ya zo ya ?auki gawarta a dabata!.

Ayshercool
08081012143
???500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa


Walid ya kalli Al'amin, ya lumshe idanunsa, wasu irin jijiyoyi suka fito ra?a-ra?a a goshinsa.

Yayi shiru ya ?i ko motsawa.

"Mai zamani, ba ka ji me ya ce ba ne, matarka fa yake maganar ka je ka ?auki gawarta"

"Na aiketa ne?"

"Ban gane ka aiketa ba? Kai kut....." Ya ?ura masa ashar.

"Idan da gaske ya kasheta fa?"

Al'amin ya tashi zaune, ya ?auki wayarsa, ya danna ya kira wata lamba.

"Yeah maza"

Ya ce "Ina aikin da na saku?"

"Ai ta gama ta tafi ma"

Ya ce "Ba tafiya a ta yi ba, gidansu ta tafi, ba ka kira ni ka gaya mini ba. Wancan garan ya ce in je in ?auki gawarta a dabarsa, wallahi ya kashe 'yar mutane sai na kasheka kai ma"

"Haba maza, cewa ka yi mu saka ido, ta shiga ta gama abun da take yi ta tafi, kuma min bi ta ba ta sani ba, ta gama ta tafi ba ka ce mu bi ta mu ga ina zata tafi ba"

"Wallahi liti ka bari muka ha?u sai na saka maka ?arfe, ka ji na rantse. Ya ajjye wayar ya yin?ura, Walid ya ce "Ina zaka je, ka ce ba ka jin da?i, ka zauna bari ni na je"

"In zauna sai ya kasheta, sannan zan je?" Yayi maganar a zafafe.

Walid ya bi shi da kallo, yana son gano ha?i?anin in da ya dosa, amma bai gane ba, Al'amin ya sake birkicewa ya ce "Ya kasheta ko ya bar ta da rai, ba shi ne a gabana ba, tun da ba ni na gayyato ta rayuwata ba, abu mafi muni shi ne ace madaki ya kuma yi mini illa, idan haka ta kasance, kan mai uwa da wabi, zan ?auki matakin da ya dace".

Ya fita da sauri, Walid ya bi bayansa, bai ma san ina ne gidan na su ba, sai da walid ya yi masa jagora, yaran madaki suna ganin Al'amin ya shigo musu unguwa da rana tsaka, amma aka rasa mai tunkararsa, dan ba su fiye galaba a kansa ba, sai sun yi masa taron dangi.

Suna tafe a hanya, liti ya kira Walid ya ce masa "Ka ce ya kwantar da hankalinsa, na yi waya tana lafiya tana cikin gidan su, zamu fito da ita lafiya in sha Allah"

Walid yana gaya wa Viper, ya ce "Ka ce masa bana so" ya yi maganar yana ?ara sauri.

Jauhar kuwa na can, har ta ?ora musu girki, sai zungurarta suke yi, su ji a wani hali take ciki a gidanta, da irin zaman da take yi da Al'amin, amma ta dinga waskewa, ta?i gaya musu komai.

Hafsa har da tambayarta, wai wuri ?aya suke kwana?.

Jauhar ta kwashe da dariya ta ce "To zai kwana a waje ne yana da mata?".

Surayya ta ce "Iyee zama da ma?aukin kanwa, wato har bakinki ma ya bu?e haka?"

Jauhar ta yi dariya ta ce "Kai Anty surayya tambayata fa tayi, bari na ?arasa na je gida ma na yi girki, kar ya dawo".

A tunaninsu za su ga jauhar cikin mawuyacin hali, amma sam ba su ga alamar hakan ba.

Ta shiga suka gaisa da anty lubabatu,ta din ga murna yadda ta ga jauhar, babu alamar wahala a tare da ita, ta aika 'ya'yan anty lubabatu su je gidan kakannin su, su kar?o mata shirin dutse a wurin ?anwar anty lubabatu. Da yake duk a unguwar ne.

Anty lubabtu har da harha?awa jauhar 'yan kayan gyaran aure na mata, ita dai ba ta ce komai ba, ta kar?a ta ce ta gode.

Da ta fito daga gidan, ta lura da wasu matasa da ba ta san suwaye ba, a layin amma ba ta damu ba ta shige gida.

Walida ta tare ta ta ce "Me Anty lubabatun ta baki?" Suka kar?i ledar hannunta, suka ga kayan mata da turarukan wuta da humra masu kyau da ?amshi.

Suka din ga yi mata dariya cikin izgilanci surayya ta ce "Wai nan ba ki yadda ba ke matar aure ko jauhar? Dan Allah ya ki ke yi ke kuwa da shi, ga 'yan shaye-shaye da ?azanta, kuma har kiss ku ke yi?"

Jauhar ta yi wani irin murmushi ta ce "Yaya surayya kenan"

"Gaya mana man"

"To ni me zan ce? Annabi ya hana fa?a, sirrinmu ne ai"

Surayya ta ce "Lallai, yau na ga illar ?ani ya rigaka aure, ni ki ke gaya wa ba?ar magana jauhar?

"A'a ki yi ha?uri, ba ba?ar magana ba ce"

Ta kar?e kayanta, ta saka a jakarta, ta cigaba da aikinta.

Ta zauna tana yanka salak, sai mita take yi ba ta ha?u da yaya saifu ba, kuma baba ma baya nan"

Tijjani ya fito yana ?an tattakawa, ta din ga yi masa sannu.

Tun da ya shigo layin yake ganin yaran madaki tsilla-tsilla, alla-alla yake yi ya ?arasa ya tabattar da abun da madaki ya fa?a gaske ne ko akasin haka, idan gaske ne bai san iya adadin haukan da zai yi masa ba.

Walid ya ce "Ga gidan nan" dai-dai lokacin ?an gidan anty lubabatu ya zo zai shiga gidan su jauhar, hannunsa ri?e da ledar viva, an zubo mata dutsen shiri da kayan yi kala-kala, babar anty lubabatu ta ce a bata kyauta a matsayin jari, shi ne gudunmawarta na biki.

"Kai shiga nan gidan ka ce.... Sai kuma ya yi shiru dan ya manta sunanta, sai Fatima yake iya tunawa.

Walid ya ce "Ka fa?a masa sunan"

Tsaki yayi ya ce "Na manta sunan, sunan wani iri ne dai haka kamar Angela"

Walid ya ce "Amma kuwa ka yi asara"

Al'amin ya ce "Ka ce 'yar madara ta zo in ji Master"

Walid na son yin magana, ya maze ya ce "Na san ?arya fa madaki dama yake yi bai kasheta ba".

Yaron ya shiga ya fara ba ta sa?on hajiya kakarsa, na bata kyautar dutse, ta kar?a tana murna da godiya, sannan ya ce "Wani a waje ya ce wai 'yar madara ta zo" take gaban Jauhar ya fa?i.

Walida ta ce "Wace wata 'yar madara, babu ita a gidan nan, in ji wa ya ce maka?"

Yaron ya ce "Wai in ji Master "

Jauhar ta ce "Na shiga uku, master ne, ban gaya masa zan zo nan ba, waye ya gaya masa?".

Ta ce "Bari na ?aukko jakata"

Anty ta fito ta ce "wannan aikin kuma wa zai ?arasa shi? Ai sai yayi ha?uri ta gama, kai je ka ka ce masa aiki take yi, ya dawo an jima"

Bu?e baki jauhar ta yi ta ce "A'a anty kar ya gaya masa haka, kaga haidar ka ce masa...

Anty ta katse ta ta ce "Fita ka je ka gaya masa haka, waye shi ba gidan sirikansa ba ne ba".

Gaban Jauhar ya tsananta fa?uwa, ba ta san me hakan ka iya haifarwa ba.

Mama ma fitowa ta yi ta ce "Ba zaki zauna ki cigaba da aikin ba"

Viper kuwa wani marurun takaici ne ya ?ule masa a wuya, jin irin sa?on da aka aiko masa da shi, kamar shi za a aikowa da wannan banzar maganar. kawai ya sai kai zai shiga gidan, walid ya ri?e shi ya ce "Mai zamani gidan sirikanka ne fa, dan Allah kar yi wani abu mara da?i, ka zubar mata da mutunci"

"Tun da suka za?i su aura mini ita, sai na tabattar musu da maganata ce gaba da ta su a yanzu" kawai ya saka kai cikin gidan.

Cak ta tsaya, jikinta yana tsuma, ganinsa ya shigo yana wannan takun nasa, ya ?ureta da ido, tun kafin ya ?araso.

Tsit suka yi suna kallon ikon Allah, ya ?araso, ta wutsiyar ido ya kalli yaya tijjani da ke zaune a kan farar kujera, ya sauke idonsa a kan mama, su surayya sannan Anty Zakiyya ta ?arshe.

Yana ganinta ya ?ara tabattar da Rahila ce ta saka aka yi masa aure, bai ga alamar akwai mahaifiyar jauhar a cikin su ba.

Ya kalli Jauhar ya ce "Ni na aiko ki zo ki ka ce mini ba zaki zo ba?"

Ta ce "Dan Allah Master ka yi ha?uri"

"Shut up!" Yayi maganar cikin ?araji, tare da ball da bokitin da aka kawo marka?e, da kwanon salak ?in duk suka tarwatse a wurin, ta zabura ta ?an?ame jikinta. Ai ba ita ba, har sauran matan gidan da 'yan matan.

Tijjani kuwa ?imaucewa yayi, dan kuwa ba zai manta muryar nan ba, duk da yana tantama amma kamar muryar wanda suka yi ma aika-aika.

"Dama mun yi da ke zaki zo nan? Kin zata ?arya suke yi da suka ce za su saraki idan suka kuma ganinki a unguwar nan?" ?ago ido ta yi cikin tsoro tana kallonsa.

Ganin yadda duk ta rikice ya sanya ya saki muryarsa ya ce "Zo ki wuce mu tafi"

Ta ce "Bari na ?akko hijjabina"

Mayar da idonsa yayi kan Anty Zakiyya, ko ?iftawa ba ya yi, babu shiri ta juya da sauri ta shige ?aki.

Jauhar ta fito, da jakarta da ledojinta, ya dan?i hannunta, suka yi waje.

Suna fita Surayya ta ce "Bala'i dama wannan ne mai dogon zamanin? Jaraba jauhara na cikin bala'i".

Hafsa ta ce "Ni kuma abun da na gani daban, kut wallahi na ?auka zan ga wani gardin mummuna, ji mutum hanci har baka, kai amma yayi kalar tsoro da yawa, haka yake yi mata wannan tijara"

Mama ta ce "Dalla ku yi mana shiru, kalli asarar da ya yi mana, abincin ranarmu ya mayar da mu baya" mama tayi maganar a ?ule.

"To mama aikin gama ai ya riga ya gama, ni wallahi na zata dukanta zai yi ma. Anty har an gudu ?aki, bayan ita ta bayar da sa?on da aka gaya masa"

Daga ?aki ta ce "Haka kurum in tsaya ya kasheni a banza, kin ga wani huci da yake yi kamar kumurci, gashi sai kallona yake yi, ya ?ara girma fiye da yadda na san shi".

Jauhar kuwa suna fita, walid ya rufa musu baya, Viper ya din ga jan ta, gashi saurinsa ya ninka nata, kamar ta hantsila, Alla-Alla yake yi su ?arasa titi ya saka ta a abun hawa, sai dai suka yi karo da madaki da yaransa.

Wata irin muguwar dariya madaki yayi, wadda ta ?ara fito da ainihin muninsa, ba?i ne wuluk kuma gabjeje, yana da jajayen idanuwa, wanda yake ramba?a musu farin kwalli, ga wani ?aton sara a fuskarsa a kaikaice da ya raba fuskar in to two equal parts.

Sai ta ga Al'amin ?in ta nutsatstse ne mai kyan gani, a kan madaki, ta san gidansu ta san sunansa a unguwar su, amma ba ta sanshi a fuska ba.

Jikinta ya hau tsuma, Al'amin ya sakata a bayansa, ya tsaya yana fuskantar madaki, Walid ya tsaya a gefensa.

"Tun da aka gaya mini matarka ta shigo unguwar nan, na ce bari in auna adadin son da ka ke yi mata. Ka san bikin ma bana nan aka yi, labari na samu ban ha?u da kai na yi maka Allah ya sanya alkhairi ba. ?arfin halinka ya kai, tun da ka iya ratso cikin unguwarmu ka auri 'ya. Shiyasa na so ka zama ?aya daga yarana tun a wancan lokacin amma ka ?i.

Ya le?a ya kalli fuskar jauhar ya ce "Ashe 'yar gidan Alhaji faruku ce, rabona da ita tun

Please Login or Register in order to submit comment