Reading KARFE A WUTA Chapter 4 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

harar Nabila, amma ko a jikinta, ita kanta sumayya sai da haushi ya kamata abun da Nabilan take yi.

Nabila ta ce "Yalla?ai, ko zaka saka mini lambarka, idan wani abu ya kama na aiki, zan iya taimakawa i am barrister Nabila Yusuf"

Ya ce "Wow, what a very young and beautiful barrister, kin zama lawyer da ?ananan shekaru, ya kar?i wayar Nabila, ya saka mata lambarsa, ta tashi ta yi musu sallama.

Sumayya kamar ta yi bindiga, su na fita ta din ga ?urawa Nabila ashar, a kan abun da ta yi, tare da gaya mata ala?ar Lawisa da kuma MD.

Nabila ta ce "Sumayya, dan Allah kar ki ?oye mini, idan yana da ku?i na ci rabona, na ga zai yi son mata"

Ganin Nabila na neman mayar da ita mahaukaciya, sai ta canza maganar.

"Ke kin san menene? wai ni zan kai rahoto har kashi biyu, sakaryar matar nan ta ce ba za a saka ba, wai ba sa bu?atar irin wannan labarin, MD ya tambayi me nake yi a reception ba na aiki, wai ta ce masa ban iya aiki ba, na rasa uban da na tsare mata ta tsane ni, dama ni na samu damar da ake baki, a wurin aiki, in yi wata shida ina aiki a wurin, wai ban iya aiki ba, da yake kwanan nan ya dawo daga ?aro karatu, tun da aka ?aukemu ya tafi".

Maimakon Nabila ta tausaya mata, sai ta hau dariya, "Ai kawai ki fara soyyaya da MD ko ta bala'i, shi ne zaki rama".

Sai da ta ga Sumayya ta yi fushi sannan ta ce "Sorry my sumy, maganar gaskiya babu da?i, kuma kishi take da ke kuma tana ?o?arin kare abun da take so, shikenan"

Idon sumayya ya tara hawaye ta ce "Sai kuma ta din ga da?ile ni a harkar aikina? Ta yi mini adalci kenan?"

Nan ta ba wa Nabila labarin abun da ya faru, daga fitowarta daga gida, zuwa yanzu.

Nabila ta ce "Na shiga uku, sumayya me ?asarmu ke son zama ne? A zahiri an nunawa mutane ana neman mai laifi, a ba?ini kuma hukuma na ?oye shi? Duk yadda ake fama da ?an daba da masu ?wace a garin nan, tir?ashi ana maganin ?aba kai yana da?a kumbura, ke ba ki san sunan wanda ya yi laifin ba?".

Sumayya ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, bai fa?a ba, korata ma suka yi".

"Mu ?arasa titi mu tari napep mu je asibitin, mu tattauna da shi mutumin, ni kin san ba na tsoron a mutu ko a yi rai. Sannan zan je na samu Yaya Nasir na yi masa maganar wannan ai abun kunya ne"

Sumayya ta girgiza kai ta ce "A'a, na tsorata da kashedin da aka yi mana, a bar zancen kawai, ban san suwaye mutanen ba".

Nabila ta ce "Wallahi sai mun je, akwai wata shashasha da ta isa ta hana ki cigaba a rayuwa, idan ma ba a saka radiyo ba, sai mu kwatsa a media ina da mabiya sosai a social media, sai ayi duk wadda za ayi.!!!"

Ayshercool
08081012142
??*?ARFE A WUTA ??


*AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g





Page 4

"No Nabila, abun da ki ke yi is too risky, mutanen nan da gaske suke, they mean what they said, kar ki jefamu a matsala"

Nabila ta ce"Karatunki ya tashi a banza kenan sumayya? Idonki har da hawaye saboda takaici. Wasu lokutan kin fiye sokwanci sumayya, da ni ce da tuni na ci buhun ubanta".

Sumayya ta ce "Ni ce sokuwa ko? na gode amma ni ba zan iya kasadar da ki ke yi ba, na rasa aikina, but wait mu je na rakaki in da aka aike ki mana"

Nabila ta ce "Wa? Ta? tuni na kira MD na bashi uzuri, dama barrister Habib ne ya aike ni, yadda wannan matar ta wurin aikinku take, lawashi ko lotion take, haka yake yi mini, ba ya ?aunata"

"A'a, naki ya sha banban da nawa Nabila, shi taimakonki yake yi ai"

Nabila ta kwa?e fuska ta ce "Ke, idan fa kin ga ina zu?ewa a aikin nan, wanda za a kare ba shi da gaskiya ne, MD zan saka ya canza mini team daga na su Barrister Habib, na Barrister Bashir nake so, wata zazzafar shari'a za su kara, shari'ar manya ce, a kan ku?i, zuwa zan yi na sha kallo, kuma an ce akwai yiwuwar na ha?u da masoyiyyata kwanan nan"

Sunayya ta ce "Wa kenan?"

"Anty Naja'atu Bunkure mana, kin san am die hard fan of that woman, Barrister Naja'atu duniya ce, ga gayu malam, harshenta akwai turanci, kamar wadda aka haifa royal palace ?in Elizabeth"

Sumayya ta yi tsaki ta ce "Aikin banza ?ar wahala, ita ta zama abun da ta zama a harkar aiki, har tana burgeki, ke kuma kina zaune kina shashanci, wallahi ?arshe ki koma ?ar ?aukar jakarta"

Nabila ta ce "Kan uba, degree holder in yi dakon jaka, Kin ci mutuncina fa,

Sumayya ta girgiza kai, haryanzu Nabila shirirta da yarinta na damunta.

Ko da Nabila ta je gida, tun a tsakar falo take tambayar magajiya, ina DSP.

"Bai dawo daga aiki ba, na ji ?azu yana cewa ko za su je ringin"

Nabila ta ce "Aikuwa ya yi ya dawo, sun bayar da maza, in mun zauna ya yi ta cewa police ya fi lawyer, yau zai sha kunya idan ya ji me suka yi. Yau zazzafan debate ne tsakanina da shi, har lemo zan yi mana aji da?in yin musu"

Anty ta ce "Ka ji mashirirciya, musun da za ku yi za ki ha?awa lemo?".

"Eh mana, ?an sanda sharri, lawyer kuma musu" tayi maganar tana dariya.

Wani mugun kallo mama ta yi mata, yaran gidan nan har take suke yi wa Nasir da discipline master, saboda yadda suke jin tsoron sa, amma tsakaninsa da Nabila sam ba haka bane ba, suna good time sosai da Nasir, kuma duk gidan bayan Abba ba ta da abokin hira ko shawara sai shi.

Nabila ta share mugun kallon da maman ke yi mata, ta tafi ?aki.

Misalin ?arfe hu?u na yamma, Sumayya ta ga kiran lawisa, kawai ta basar ta cigaba da kallon tv, ta kira ya kai sau hu?u sannan ta ?aga.

"Ki na ji ina kiran waya ki ka ?i ?agawa?"

"A silent take, bacci nayi ne".

"Ki tura mini recodings ?in nan, su murtala ba su sami wani samo rahotanni masu muhimmanci ba, kuma na ga su Mikiya radiyo duk sun wallafa labarin yaron nan, ki turo mini mu ga wanda za a iya tacewa a saka" Sumayya ta ta?e baki ta ce "To"

Ta kashe wayar, ta ce "Allah ya ?ara, da mu muka fara sanar da labarin, kuma mu ka saka a internet, ai da ya fi, tun da ni ce ?ar jarida ta farko da ta fara zuwa wurin, amma ki ka ?i"

Ta lalubo lambar Nabila ta kirata, ta gaya mata abun da ya faru. Nabila ta ce "Amma baki da wayo sumy, ke yanzu sai ki tura mata, saboda ba ki da zuciya?"

"To yaya zan yi mata?"

"To amma kin san ko kin tura mata, sunanta za ta fa?a a mai rahoton ko wanda ya karanta ba ke ba ko?"

Sumayya ta ?an yi shiru ta ce "Kuma fa haka ne"

"To tun wuri ki ce mata kin goge kawai, gobe ba za ta ?ara yi miki wula?anci ba".

Sunayya ta ce "Haka za ayi, na gode sosai" cikin hanzari ta kira Lawisa, ta sanar mata da cewa ba ta ga recordings ?in ba.

Aikuwa ta hau ta da bala'i, Sumayya ta danna recording tana dariya ?asa-?asa da niyyar ta turawa Nabila.

Bayan sun gama wayar, ta turawa Nabila, suka din ga dariya, Nabila na ?ara bata ?warin gwiwar, kar ta sake ta ?auki raini ko wula?anci daga wurin lawisa.

Ta kuma cigaba da lalla?a sumayya, a kan lallai ta koma asibiti, ta sake tattaunawa da mutumin nan, ko iya sunan mai laifin ta samo.

Barrister Habib ne ya shiga office ?in MD, ya zauna suka gaisa, cikin takaici Habib ya fara magana, "Barrister, ni fa na gaji da iskanci yarinyar nan, idan a team ?i na za ta zauna, ta zauna, kuma dole ta yi biyayya ga abun da na sakata, idan wurin Bashir za ta koma, ta koma na gaji da iskanci da rashin mutuncin da take aikatawa, ba ta san aiki ba ko ka?an"

MD ya ce "Calm down Habib, na sani wallahi, na san ku na ha?uri da ita, wallahi nima nauyin mahaifinta nake ji ne, abun da yayi mini a rayuwa idan na kore ta ban yi wa kaina adalci ba, shi ma yana yawan bani ha?uri a kanta, marainiya ce kuma ba ta da cikakkiyar lafiya."

"Mu ma duk marayun ne ai, waye yake iskancin da take yi? Ta zo lokacin da ta ga dama ta tafi lokacin da ta so, she's not serious at all"

"Na sani, kuma nima ina gani, ka rabu da ita, duk wani abu da za ku yi ku daina sakata a ciki, ?yaleta da bashir ?in, shi ne daidai da ita, ku yi ha?uri dan Allah" MD ya din ga lalla?a Habib, dan ba zai so rasa gogaggen lawyer kamar Habib a law firm ?in sa ba, a kan Nabila da ba aikin ne a gabanta ba.

Yau weekends ne, gaba ?aya iyalan major na babbn falo, kowa ya ja nasa wuri yana karyawa, Nabila ce kawai babu a wurin.

Tun yana jurewa ya kasa, yayi gyaran murya ya ce "Ina arfa ne?"

Anty ta ce "Bacci take yi"

Ya kalli walida ya ce "Tasota, ta fito ta karya, sai an cinye an bar ta, ta cikawa mutane kunne da kuka"

Kusan mintuna goma da taso ta, sannan ta fito, kayan bacci ne a jikinta, dogon wando da rigarsa har gwiwa, kanta babu ?an kwali.

Nasir ya tsura mata ido, ko ?iftawa ba ya yi.

Abba ya ce "Ina kallabinki? Ki ka fito da wannan gashin ba kyan gani, kamar totuwar masara?"

Ta saka hular hannunta ta ce "Haba Abba, dan daga bacci na tashi ne fa"

"Tafi can ?azama, kullum kai babu kitso, ba za a rasa kwarkwata a wannan gashin ba" dariya aka hau yi mata.

Ko a jikinta, ta zauna kusa da Abba, ta kalli Nasir ta ce "DSP, yaushe ka dawo ba labari, ya hanya?"

Ya jinjina kai ya ce "Alhamdilillah"

Major da kansa, ya taya Nabila ha?a shayi, ga soyayyen dankali, ga bredin ta, amma tana bu?e bredin ta ce ba za ta ci ba, kwantai ne.

Major ya mi?a mata nasa ya ce "Duba zaki iya cin wannan? Dankali kawai ba zai ri?e miki ciki ba" ta duba buredin Abban ta ce "Eh wannan sabo ne, Abba ka ?ara mini ?wan, ni ba na son dankalin ma"

Ya ce "To shikenan, ?auki nawa da ma ni yanzu ?wai bai dace da ni ba, a shekaruna"
Idan da sabo, sun saba da ganin irin wannan fifikon da major yake nunawa, duk da mutum ne mai ?aunar yaransa sosai da sosai, amma son da yake yi wa Nabila na musamman ne, amma fa hakan ba ya hana idan suka yi laifi, ya hukunta su kamar ba ?a?an cikin sa ba.

Anty ta ce "Arfa ba zaki bari Major yayi ?iba ba, kalli yadda ki ke tara mazaunai, saboda ci"

Yayi murmushi ya ce "Tafi kowa girma a gidan nan"

Nabila ta ce "Abba, Allah ya ?ara arziki, ka yi ta sayowa mu na ci"

"Amin arfan Abba"

Nasir ma ya juye mata nasa ?wan, ta tattare tana dariya, dan ta na son ?wai sosai.

Mama kuwa kamar za ta yi bindiga, saboda ba?in ciki.

Bayan an kammala cin abinci, su walida ne suka kwashe kwanukan da aka ci, Nabila kuma ta hau labartawa Nasir, abun da ya faru da sumayya da ta je Asibiti.

Fafur Nasir ya ce ?arya take yi.

Ta ha?e rai ta ce "Yaya, wai meyasa a duniya jami'an tsaro ba kwa yadda kun yi laifi, ko wani ne daga cikinku yayi, sai kun ?aryata, kun kare mutum"

"Wa ya gaya miki hukuma tana laifi?"

"Ba mutane ne hukunar ba? Ai mutane na laifi, kuma hukuma ma suna yi, wallahi da gaske nake, ka bincika ka ji kuma, koma na kira maka sumayyan"

Ya ce "A'a ai ?arya ki ke yi, ni zaki zauna kawai dan ki ?ure"

Duk yadda ta so, ta fahimtar da shi, amma ya ?i fafur.

Abba dai kallonsu kawai yake yi yana dariya, ganin ba zai yarda ba, ya sanya ta ?yale shi, ta koma wurin Abba.

"Abbana" tayi maganar tana ?an murmushi.

Abba ya ce "Ku?i zaki tambaya kenan?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, abu zan tambaye ka"

"Ina jin ki"

"Abba dama, wata amarya ce, suka kira ni a waya, zan je gida na yi musu make up, ita da ?annenta na biki, za su biyani, VIP ne har gida"

Ha?e rai yayi sosai sannan ya ce "Me na gaya miki a kan wannan she?ancin? Kin san na hana ki sabgar banzar nan, ban da kalen she?anu jikinku, me wannan shashancin zai amafana miki, na fuskanci kin fi fifita wannan kwalliyar a kan aikinki, to babu in da za ki je".

"Dan Allah Abba, wallahi zan samu ku?i fiye da salaryna, dan Allah"

"Ba in da zaki, tun da babu abun da ki ka rasa a gidan ubanki, ba matar da zaki bi gida ki na shafawa hoda, idan ta matsu tayi da kanta mana, banda shashanci ace mace ta zauna sai an bita gida shafa mata hoda da gazar"

"Abba!"

"Shut up" yayi mata tsawa, hakan ya tilasata mata yin shiru.

Walida kuwa fa?an Abban dariya ya bata, wai idan sun matsu su yi da kansu, ba wadda za aje gida shafawa hoda.

Nabila ta din ga jin ko a ?oye sai ta je, tana son sana'arta ta kwalliya, Abba kuma ba ya so, wai shashanci ne da fatan aljanu, ita kanta idan tayi a fuskarta wasu lokutan, ya din ga fa?a kenan.

Akwai ranar da za ta je biki, ta yi kwalliya ta saka eyelashes, ya kirata dan ya ga meya samu idonta, gashin idonta yayi tsawo haka, tun da ta ce masa sawa tayi, ba ta ankara ba, ya saka hannu, ya fige shi sai da ya ha?a da gashin idonta, ya ce ya kuma ganinta da shi sai ya zaneta.

Har a gaban saurayi, ya ta?a korata gida, wai ta je ta wanke fuskarta, ba za ta cuci ?an mutane ba, duk ta damalmala fuska da hauka, ta zama kamar wata bebin roba.

Ta rasa meyasa Abba yake adawa da sana'ar nan tata.

Nabila tun a weekend, take cigaba da zuzutawa Sumayya trial ?in da za su je, kotu ranar laraba, farincikin ta ya kasa ?oyuwa, wanda hakan ya samo asali ne, da yadda ta ga Barrister Habib ya ?yale ta, ta koma team ?in Bashir, kuma ta samu labarin barrister Naja'atu ma tana da shari'a ranar a kotun, dan haka za ta ha?u da ita.

Nabila uniform ?in ta, tamkar su yi magana, saboda ?aukar guga, ita kanta a bar kallo ce a cikin kayan, ba fara ce tas ba, amma haskenta mai kyau ne da ?aukar hankali, domin kuwa jikinta kamar ?wai, dan tana kashewa Jikinta ku?i ba ka?an ba, ba ta da wata damuwa, ba abun da take yi da ku?i, ban da sayen kayan gyaran jiki, ta samu ku?i a aikinta, major ya bata, Nasir ma ya bata, ga wanda take tatsar samari, ga ?an sana'ointa, dan haka ku?i sam ba matsalarta bane ba.

Barrister Naja'atu Bunkure matashiyar lawyer, mai dakawa maza gumba a hannu, karo da ita sai lawyern da yake jin kansa ya isa, dan abu ne mawuyaci case ya shiga hannunta ba ta yi wining ba. Ana yawan sanar da ayyukan alkhairin ta, a gidajen rediyo na taimako da tsayawa marasa galihu a kan shario'i daban-daban.

Bakin Nabila ya ?i rufuwa, ganin yau ga ta ga Barrister Naja bunkure, wata ?ar gayu da ita, yadda ta gabatarwa da kotu kanta kawai, ya isa ka tabattar da ta san me take yi, ga yaren nasara a harshenta wato turanci.

Gaba ?aya hankalin Nabila ba ya kan shari'ar, yana kan bunkure, da yadda take magana.

Murna kamar nabila ta taka rawa, yau ga ta ga mentor ?in ta.

Sumayya ta samu damar editing news yau da kanta, kasancewar MD yana ta mitar, ta daina ware kanta, ta din ga shiga ana aiki da ita a haka za ta goge.

Kiran Nabila ta gani, dan haka ta ?aga ta ce "Kiran me ki ke yi mini ina aiki?"

Sama-sama ta din ga jiyo numfashin Nabila, muryarta ?asa-?asa ta ce "Kin tashi daga aiki ne?"

"A'a menene meyafaru?"

A galabaice ta ce "Na dawo chamber ne, na ?auki kayana, ina hanyar komawa gida, ji nake kamar ciwona ne zai tashi, ina titi dan Allah Sumy ki zo"

"Subhanallah, gani nan zuwa amma babu wani a wurin da zai kai ki gida?"

"Ni ba na son damun kowa, dan Allah besty ki zo, kar na mutu a titi"

Ganin ta gama abun da take yi, ya sanya a gurguje ta ?auki jakarta, ta fita, ba ta tsaya ko ina ba, sai hanyar wurin aikin su Nabila, tana ta rarraba ido a titi tana kiran wayarta.

A kan wani tudu ta hango Nabila, idanunta sun yi jawur, da alama tayi kuka sosai da sosai.

Ta ce "Mai napep, bari na ?auketa ka kaimu gadon ?aya dan Allah, ba ta da lafiya"

Ya ce "To shikenan" ta sauka ta rungumo Nabila, ta taimaka mata, ta shiga napep ?in, sai dai babu baki, sai numfashi take sama-sama.

"Arfa, meyafaru an ?ata miki rai ne?" Ta girgiza kai alamar a'a.

"To menene? Haka kurum ciwon ya tashi" bu?e baki ta yi, da nufin yi wa sumayya masifar ta ?yaleta, amma ta ji numfashin ta, zai gudu ya bar huhunta, hakan ya sakata yin shiru.

Can kuma a hankali ta ce "Sumayya mu je gidanku, wurin umma"

Sumayya ta jinjina mata kai, haka aka yi.

umman sumayya na ganinsu hankalinta ya tashi, Nabila ta samu wuri ta kwanta.

Umma ta ce "Sumayya, me aka yi mata ne?"

"Wallahi umma ban sani ba, kawai kirana ta yi a waya, ciwonta ya tashi"

Cikin kuka Nabila ta ce "Umma dan Allah ki yi mini addu'a, ki ?yale sumayya"

Umma ta ce "To shikenan" ta din ga tofa mata addu'a, har aka samu ta yi bacci.

Bayan awa ?aya da rabi, ta farka, har ta samu ta ci abinci ta yi salla, umma ta din ga tambayarta, ko wani abun aka yi mata, amma ta ce a'a.

Ganin ta ware, ya sanya umman basu wuri, Sumayya ta sake kallonta ta ce "Ke, wallahi wani abu aka yi miki, yanayinki ya nuna mini, kin ga idonki kuwa, ki gaya mini menene?"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Sumy, ashe haka ake ji, idan aka wula?anta mutum mussman a gaban jama'a, a dizaga ka"

"Menene? Waye ya wula?anta ki?"

Ta ?an yi shiru sannan ta ce "Kin san Naja'atu Bunkure?"

"Ba dole na santa ba, a wurinki na santa ai"

"Ashe matar nan tsinanniya ce"

Da sauri sumayya ta ce "A'uzubillahi, me yayi zafi, mentor ?in taki?"

Nabila ta ce "Zilwajahiani ce, abun da muke ji a kanta daban, yadda take daban. Yau muka ha?u a kotu, kin san ina cikin team ?in barrister Bashir, tare muka je court yau.
Bayan an fito, jiki na tsuma na bita, ?an jarida sun baibayeta, na yi mata magana kin ga wula?antaccen kallon da tayi mini? Ba shi ne ya dame ni ba, duk da uniform ne a jikina, na cire girman kai na gabatar mata da kaina, a matsayin lawyer mai koyi da ita, amma still ban isheta kallon kirki ba. Abunka da zuciya da abun da take so, na matsa tare da mi?a mata wayata, a kan ta bani lambarta, sai ce mini ta yi ba za ta bayar ba, kar na isheta da kira. Na ce mata bakomai, a matsayina na mai koyi da ita, kuma mai ?aunarta, dan Allah ko mintuna uku ta bani, na da?e ina burin ha?uwa da ita. Ina son ta bani shawara a matsayina na lawyer mai tasowa, kuma ta bani tips da zan bi, na zama kamarta a rayuwa, dan ina son ta da irin ayyukan da take yi. Ta ?are mini kallon baki isa ba, sannan ta ce 'Ki zama kamar ni kuma? Taka matsayin da na taka? Never! Don't even give a try, ba zaki ta?a zama ba, and leave my way please, ina da abun yi"
Haka fa ta ce mini, a gaban mutane da masu yi mini dariya, da masu yi mini Allah ya ?ara wai neman suna da gidin zama ne ya janyo mini, wasu kuma su ka bani ha?uri wai haka halinta yake. Sumayya yau na tozarta, an wula?anta ni, duk yadda nake ganin ina da class, soyayya ta rufe mini ido, saboda ina ?aunar matar nan fisabilillahi, wallahi da ?yar na ?arasa chamber, nan da nan na fara jiri, numfashina ya fara sama, kin ga dariyar da aka yi mini, wallahi na muzanta fiye da tunaninki"

Sumayya ta ce "Nabila jikina yayi sanyi, ban ta?a zaton matar nan za ta aikata haka ba, wai meyasa mu mata, galibin mu ?an ba?in ciki ne? Wato ba zaki zama kamarta ba, sai ka ce wayo da dabararta ne suka ba ta matsayin da take kai".

"Wallahi sumayya, ko zan rasa raina, ko da kasada, sai na tabattar da na yi suna nima, sai dai idan Allah ya ?addara na mutu. Amma ina ro?on Allah, in sha Allah tana raye, sai na ?aukaka fiye da tunaninta, kuma bibiyarta zan din ga yi, da bibiyar duk wani abu da ya shafe ta, sai na rama abun da ta yi mini. I will do a background check on her"

"Ke fa baki iya ?aukar abubuwa da sau?i ba, ki ?yaleta mana kanta ta yi wa, ni na ce me?, abun da nima ake yi mini, ni kusan kullum ake yi mini, ke yau ne kawai, kuma arfa matsayi na duniya ba na kiyama ba"

Nabila ta girgiza kai ta ce "Wannan ke ki ka ga zaki iya, kuma ?aramar alhaki ce ta wurin aikinku, wannan kuwa dizgin da ta yi mini, in sha Allah rabbi, sai na rama shi, dole na ajiye shirme, na mayar da hankali a kan aikina, ko dan fansar nan, kut wallahi matar nan ta gama cuta ta, kuma ba zan huce ba har sai na rama wallahi. Rakani titi in tafi gida" ta ?arasa maganar tana ?o?arin tashi tsaye.

Sumayya ta dan?ota ta ce "Nabila ki din ga sanyawa zuciyarki salama mana, kin fiye zafin rai, ki bi komai a hankali, kalli yadda ki ka kusa kashe kanki a banza. Idan Allah ya yi nufin ?aukakaki fiye da ita, ita ?in banza ta hana, dan Allah ki manta da ita, ki cigaba da rayuwarki".

Ta kalli sumayya cikin takaici ta ce "Lallai ma sumayya, dan ba ki ga abun da ta yi mini ba, a gaban mutane har da masu yi mini dariya. Ni gaba ?aya ma ji na yi ban yarda da ita ba, abun da ake fa?a a kanta daban, abun da na gani yau a kanta daban, akwai wani abu a ?asa, and i will run a background check on her, for the first place ma, wacece ita? Idan ta kama har bunkuren zan je mahaifarta, meyasa abun da ake fa?a a kanta daban, ita kuma halinta daban".

Sumayya ta ce "Na shiga uku, Nabila" kafin ta yi magana, Nabila ta yi waje, ta tarar da umman sumayya na salla, ta ce Umma na tafi, ta fice daga gidan.

Sosai abun da ya faru ya tsayewa Nabila,da ta tuno abun sai wani irin takaici yakamata.

Yau ba kowa ya san ma ta koma gida ba, dan yau babu surutu da hayaniya.

Abu kamar wasa, har dare Nabila ta kasa walwala, ko fitowa daga ?aki ta?i yi, gani take kowa yana kallonta zai gane an dizgata yau, duk iyayin na ta da jan ajin.
Nabila irin mutanen nan ce masu saka abu a ran su, dan haka ko ta yi niyyar manta abun da ya faru, sai ta kasa.

Ta ?aukko wayarta, ta kunna data, ta tarar da messages ?in sumayya, ta na ta yi mata fa?an ta yi ha?uri ta manta da abun da ya faru.

Nabila ta yi mata reply da "You are not serious, ki saka ido ki yi kallo"

Social media ta hau, ta shiga searching ?in sunan barrister Naja'atu Bunkure, nan da nan sai ga hotunanta, da wasu daga cikin ayyukanta na jin ?ai, sai dai ba ta samu wani cikakken bayani da take son samu a kanta ba.

Tsaki ta yi, bayan tuna yadda take mutuwar son matar nan a baya, har hotonta take sakawa a dp ?in ta, saboda yadda take ?aunarta, amma lokaci

Please Login or Register in order to submit comment