Reading KARFE A WUTA Chapter 106 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum ya tuba, ko a kashe ne ko kuma a kashe shi"

"Walid, Abba ba zai iya daba ba, ina ganin shaye-shaye kawai yake yi, wane irin kisan zalunci ne wannan da rashin imani? A sassara mutum a zuba a buhu aje a zubar?"

Liti ya ce "Ni ku matsa mini, na yi sujudar godiya ga Allah, gabasa ake kallo ko daga nan Arewa ma zan iya yin ta? Da?ina da kai wasu lokutan kana da wani ?oyayyen rauni, da ya kan kusa cutar da kai Viper. Matar da ta rufe muku ?ofa, aka hallaka ?an uwanka, shekarun da suka gabata, sharrin da ta aika ne, ya dawo mata kanta a kan ?anta ita ma, cin amanar da ta yi, ita ma Allah ya ?an?ana mata, Allah Allah ne, dan haka babu ruwanka".

"Liti kai mahaukaci ne? Ko kaza aka kashe wa mutum bisa zalunci, abin tashin hankali ne, mai rai a sassara shi, a saka a buhu, a kai a yar fa"

Walid ya ce "Yanzu idan ka je gidan me zaka yi musu? Salon ta ce kai ne ma ka saka aka kashe shi, ka san halinta ai, babu in da zaka je, taje Allah ne ya kamata".

Fafur suka hana Viper fita, ya koma cikin ?aki, ya ?aukki wayarsa ya kira Nabila.

Ta ?aga tayi sallama ta ce "Vi ya ne?"

"Amm ki tambayi ?awar nan taki Sumayya, ko labarin kisan da aka yi wa wani yaro Abba a unguwarmu, ya je mata dan Allah ina son a ?an bikcika".

Ta ce "Subhanallah, ban sani ba, bari na kirata na ji"

"Yauwwa yi sauri, dan Allah idan gaske ne, Joseph ya kai ku station ?in da case ?in yake hannunsu, ku jiyo mini ya ake ciki?"

Ta ce "An gama ranka ya da?e, amma ya sunan wanda aka kashe ?in?"

"?an matar Abbu ne, sunansa Abba idan ya kama ku je gidanmu, ku ?ara tabattar mini".

Mamki ya cika Nabila, amma ta ?oye mamakin nata ta ce "In sha Allah zamu je" ya katse wayar cikin matsanancin jimami.

Walid ya ce "To wai meye amfanin hakan da ka yi? Meye naka a ciki Viper?"

Al'amin ya girgiza kai ya ce "Yaya ku ke abu kamar ba tsoffin 'yan hannu ba? Yanzu fa?an ?aukar fansa zai ?arke a tsakanin unguwannin, kuma ina gudun abin da ya faru da ni, ya sake faruwa a kan wani, ina son na bibiyi abin a kama wa?anda suka kashe shi, na tabattar da an hukunta su, domin ya zama izina. Kuma ko ba komai, musulmi ne, kuma mahaifina ne ya ri?e shi, an yi masa kisa mai muni, abin da ta?a zuciya"

Sai kuma suka yi shiru, liti ya ce "Haka ne, maganarka dutse, amma gaskiya ba zaka je ba, ba ruwanka daga nan kayi masa addu'a, idan komai ya lafa sai a san abin yi"

Viper ya ja tsaki, tare da girgiza kai.

Walid ya ce "Menene kuma?"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Walid, babu wani alfanu ko jin da?i a rayuwar daba da shaye-shaye, duk kalle mu dai, babu wanda wannan rayuwar ta amfana da komai, face tabon ba?in ciki da tsantsar nadama. Akwai tarin ?alubale, muddin za a ci gaba da tafiya a haka"

Walid ya ce "Haka ne, sai fatan Ubangiji Allah ya yafe mana ya shiryar da mu baki ?aya".

Kamar yadda Viper ya bu?ata, Nabila tare da Sumayya, suka tafi binciken da ya ce, jami'an tsaro suka tabbatar da faruwar Al'amarin.
Sumayya ta je har gidan su Viper, kamar sai dai ba su tafi tare da Nabila ba.

A rumfar zaman makoki, ta hangi Abbu, ta ?arasa tayi musu gaisuwa, Abbu ya taso, suka sake gaisawa, ya ce "Sumayya ya aka yi ne?"

"Nabila ce ta kirani, Viper ya ce lallai mu zo a tabattar da abin da ya faru, ban san dai dalilinsa na yin hakan ba"

Ya ?an yi shiru ya ce "Shi da kansa?"

Ta ce "Eh" nan ya sake yi mata bayanin abin da ya faru, maganar da yake yi mata ma, mahaifiyarsa na Asibiti allurar bacci kawai ake yi mata, tamkar zata haukace, saboda yadda aka kawo gawar Baba, jikinsa ya fara zagwanyewa, jikinsa ko ina sara, hannunsa ma daban aka kawo shi.

Sumayya ta tattara rahoton abin da ta samu, ta sanarwa Nabila, kuma ta samu na sanarwa a gidan rediyo.

Sosai batun ya ?auki hankalin jama'a, Duk ita kanta Nabila, sai da ta ce Alhakin Viper ne, amma ta ka?u matu?a jin irin kisan tozarcin da aka yi wa Abban duk a silar ?waya. Kamar yadda ta wallafa a shafinta, suna nan suna zuba ido, su ga matakin da jami'an tsaro za su ?auka, wurin cafke wa?anda suka aikata laifin.

****
Rahila dai abin da ya samu Abba ya zame mata masifa, ta daina magana ta daina cin abinci, ba ta gane kowa sai kuka, idan aka jima kuma ta yi ta kurma ihu, tana kururwa tana kiran ?ana Abba, Abba bai mutu ba, sai dai a daddaneta ayi ta yi mata allurar bacci.

Haka Shahida zata rungumeta, tayi ta kuka, ga Amira ta shilla ta yi nata wuri, tun da Abbu ya ce ba zai kar?eta a gidansa ba.

*****

Yau da yamma Viper ya je barrack wurin Nabila, sai dai tun kafin yayi magana, ta fuskanci matsananciyar damuwa a tattare da shi.

Ta ce "Vi meyafaru ne?"

"Abin da ya faru da yaron nan Abba ne ya yi bala'in tsaya mini Abla"

"To yaya za ayi, sai addu'a, amma in ganin kamar har da hakkinka abin da ya same su"

Viper ya girgiza kai ya ce "Ba na tunanin haka, haka kurum abin ya tsaye mini. Shikenan dai makomar ?an shaye-shaye ko ?an daba. Ko ka kashe ko a kasheka, ko a kashe maka wani makusancinka, da zai bar maka mummunan tabo a zuciya, babu riba sam a wannan harkar".

Ta gya?a kai ta ce "wannan haka yake, amma ka godewa Allah da ya sanya ka farga da wuri, har ka ke ta ?o?arin tuba ga Allah, ina fatan Allah ya kar?i tubanka"

Ya amsa da "Amin ya Allah, kuma kema ina yi miki godiya sosai Abla, kema kin bayar da gudummawa sosai da sosai a cikin rayuwata, kamar yadda sisternki jauhar ta yi mini, Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"

Tayi murmushi ta amsa da Amin, duk wannan basar da abubuwan da yake yi, ashe yane sane da duk alkhairin da ake yi masa.

"Amm ya maganarmu ta zuwa asibiti, me ka yanke a kai?"

Ya jinjina kai ya ce "Zani in sha Allah"

Fa?a?a murmushinta ta yi, ta ce "Alhamdilillah ala kulli halin, amma na yi murna na ji da?i sosai da sosai, Allah ya tabattar da alkhairi"

"Amin"

"To menene next, idan an kammala shari'a, sannan ya zamu yi da batun indabo? Shi Shikenan ya ci bulus kenan, idan aka hukunta su madaki shikenan?"

Al'amin ya ha?iyi yawu, ya ce "Shi wannan iya jarrabawar da yake ciki ta ishe shi, ko iya yanzu ya san tasa ta ?are, akwai jarrabawa a rashin mulki, tarwatsewar iyali kamar yadda na fuskanta. Bore daga magoya baya ga karayar arziki an kama kayansa a ?asar waje da yaransa, ga tuhuma da yake fuskanta a cikin gida da sauransu, bana bu?atar wani ya hukunta indabo ni ne zan hukunta shi"

Ta waro ido ta ce "Dan girman Allah mun kusa zuwa ga?ar ?arshe, kar ka mayar da mu baya ka ?allo mana wani babban aikin dan Allah".

"Haba akwai bambanci tsakanin Al'amin ?an daba da kuma jami'in tsaro, na san abin da nake yi, ki kwantar da hankalinki"

Nabila ta ce "Anya kwanciyar hankalin nan kuwa?"

"Trust me mana" yayi maganar yana murmushi.

Ranar Litinin, Nabila da Viper da rakiyar Sumayya, suka kai Viper Asibitin ?wa?walwa, domin ya ga likita.
Ba su wani sha wahala ba, ya samu dukkanin kulawar da yake bu?ata, hatta history na yadda ya fara shaye-shaye, sai da suka yi wa likitan bayani, aka tura shi yin wasu gwaje-gwaje.

****
Kwanaki suka ci gaba da shu?ewa, wasu da?i wasu akasin haka, ana tsaka da alhinin mummunan kisan gillar da aka yi wa Abba, Rahila ba ta gama dawowa dai-dai ba, aka sake sanar da ita, an kama Nazifi a Lagos, tare da manyan 'yan fashi, hakan ya ?ara tunzura nutsuwar ?wa?walwarta.

Kwanci tashi asarar mai rai, aka sake shafe watanni guda curr, Ramma kullum cikin lissafi take, yaushe Abdul zai fito daga tsaren da yake.

Yau kotu ta fi ko yaushe cika, ana jiran hukuncin da kotun zata yanke.

?arar su Viper ce ta uku da aka kira, bayan dogon rubuce-rubuce da Al?ali ya yi, da bayanai ya shiga karanto hukuncin da za a yanke wa su Lakwari.

Shekarun ?aurin rai da rai, kowannensu, sannan kotu ta yi umarnin a cigaba da binciken in da sauran wa?anda su ka tafka ta'asar tare suke.

Wata irin ajiyar zuciya Nabila ta sauke, hawaye suka din ga zuba daga idanunta, ba zata ta?a manta wannan rana ba, domin kuwa wannan ita ce mafi ?ololuwar nasara da ta samu.

Viper ma sunkuyar da kansa ya yi a wurin, hawaye ya kasa barin idanunsa, duk da Madaki yana can gadon Asibiti, bai san ma waye a kansa ba.

Ana gama yanke hukuncin ta yi waje, da Sumayya ta fara arba, suka rungume juna, Nabilan sai kukan farinciki take yi.

'yan jarida ne suka baibaiye ta, suna yi mata tambayoyi, amma Sumayya ta ce su ?yaleta ba ta cikin nutsuwarta.

Walid ne ya fito tare da Viper, yana ta rufe fuska da handkerchief, babu abin da yake iya sanya shi hawaye a take, sai tuna jauhar, 'yan jarida shi ma suka yo kansa, amma ya rufe fuskarsa, Liti ya ce "Ko me zaku tambaya ku tambayeni, ba zai iya magana ba"

"A'a da shi muke son yin magana"

"To ba zai yi ba, munafukai kamar baku ku ka din ga zuzuta lamarin baz da fa?ar ?arya da gaskiya, wallahi idan ba ku bi a hankali ba, sai aikin nan ya kai ku wuta, saboda ya?a fasadi da sharrin da k...

"Kai liti wai waye ya tambayeka ne?" Walid ya dakatar da shi.

Baba yana tsaka da rarrashin Nabila, ta daina kukan da take yi, ya ga Viper ya fito, ya nufe shi, yana zuwa ya rungume shi ya na "Ina tayaka murna Aminullahi, Ubangiji Allah ya wankeka yau, ni dama na fa?a ba zaka iya kashe mini jauhar ba, Allah ya yi maka albarka".

Abbu yayi tsuru daga gefe, yana son yin magana, amma ya kasa wata irin kunya ta mamaye shi.

Alhaji mu'azzam ma gefe ya koma yana murmushi, amma bai tunkari in da Viper yake ba.

Viper ne da kansa ya tunkari in da yake tsaye, ya je gabansa ya mi?a masa hannun sa.
Sai da Alhaji mu'zzam ya waiwaya, ko ba shi yake mi?owa hannun ba.

Ya ga dai shi yake bawa hannu, ya mi?a masa hannu suka yi musabaha.

Viper ya rungume shi, ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gode, ina sane da dukkanin gwagwarmaya da ka yi a kaina, duk dan saboda soyyayar da ka ke yi wa jauhar, da kuma ?o?arin ?aukar fansa ta hanyata. Ka yi amfani da ni, ka cimma burinka, ba butulu ba ne ni, da na rintse idanuna daga kallon abin da ka ke yi mini, ina matu?ar kishin matata ne.
A karo na babu adadi, ina mai sake baka ha?uri, ka yi ha?uri da Nabila kamar yadda jauhar ba ta kasance taka ba, Nabila ma haka, mussaman da ake barin halak dan kunya, a wannan karon ma ita ma ?in tawa ce. Na gode sosai da gudunmuwar ka".

Alhaji mu'azzam kawai ya yi murmushi ya ?an daddaki bayan Viper ya ce "Ina tayaka murna, maganar Nabila kuma, ba a sanin ma ci tuwo, sai miya ta ?are".

Nabila kuwa hankalinta ne ya kai kan Naja'atu Bunkure da take yi wa 'yan jarida bayanin cewa, za su ?aukaka ?ara.

Ta gama bayanin ta nufi motarta, Nabila ta nufi in fa take, Sumayya ta ri?e ta, amma ta fizge ta nufi Bunkure.

Ayshercool
08081012143
Tsayawa Bunkure ta yi cak, tana jiran Nabila ta ?araso, Nabila ta ?arasa gabanta tana wani irin huci, kamar fusatacciyar damusa. 'yan jarida na ganin haka, abin nema ya samu, yuuuu suka ?iba suka nufe su, da abin magana da camerori.

"Ina fatan yanzu kin tabattar da jinin 'yar uwata ba zai ta?a tafiya a banza ba? Kuma matsayin da ki ke ta?ama da shi, ki ka ce ba zan ta?a taka shi ba, ashe ba matsayin ba na arziki bane ba, na gode Allah da ki ka haska mini ko ke wacece, ban ci gaba da yi miki makauniyar soyyaya ba. Abin alfahari shi ne kayi amfani da damar da Allah ya baka, wurin kyautata wa mutane, yadda ko bayan ranka zaka yi alfahari da hakan, ba yin mugunyar shuka ba, da sharrinta zai ta bibiyarka har bayan ranka ba.
Na ji ki na i?irarin ?aukaka ?ara, to baki da wannan lokacin, ga copyn ?orafin da zan shigar a kanki nan, ga hukumar shari'a, kuma ina fatan ta soke lasisinki da na ?ungiyar ki, ta ?watowa al'umma hakkinsu da ki ke dannewa, ta hanyar rufe kura da fatar akuya, ki na kare yaran masu ku?i, kina tozarta masu ?aramin ?arfi. Bakk da lokacin ?aukaka ?ara, zai fi kyau ki mayar da hankali a kan yadda zaki karenki" Nabila ta dangwara mata wani file, tare da yi mata kallon banza.

Tabbas tarihi ya maimaita kansa, domin kuwa sowa aka ?auka da tafawa Nabila, yayin da ta bar Bunkure baki bu?e ta rasa abin cewa, ?an?anwar bayanta, da da auren wuri tayi, da ta kusa haifar Nabila, duk yadda ake girmamata kamar wata abar bauta, ita yau Nabila ta dizga kuma ta kayar a shari'a, wani malolon takaici ya ?uleta, ta watsar da File ?in, za ta shige cikin mota. Wani abokin aikinta ya ce "Kul, kar ki yar ki tafi da shi ki je ki duba, ki ga ta ina zaki ?ullowa lamarin".

Nabila kuwa wurin Barrister Habib ta waiwaya, da ya kammala wata Shari'a ya fito, yana ta yashe mata baki, "Congratulations our legit barrister"

Cikin murmushi mai ha?e da farinciki, ta ce "Na gode barrister, Allah ya saka da mafificin alkhairi. Har duniya ta na?e ba zan manta da kai ba, a lokacin da yan uwa abokan aiki suke yi mini kallon mara hankali, na ?aukko dala babu gammo, ka tsaya tare da ni, tare da bani ?warin gwiwa da gudunmawa ta kowacce fuska"

Yayi murmushi ya ce "Honorable Mu'azzam Wada kankarofi shi ya dace ki yi wa wannan yabon, duk ?o?arin sa ne ya kawo haka"

Ta dubi Alhaji mu'azzam ta ce "Honorable, ban san me zan ce maka ba, sai dai ina fatan idan kujerar sanata alkhairi ce a gareka, Allah ya baka, ina kyautata maka zato, halacci da taimakon da ka yi mana, Ubangiji Allah ya shaida ya kuma biyaka, bamu da baki, ko wani kalami da zamu yi amfani da shi, da zamu yi gamshashshiyar godiyar da za ta wadaci hidimar da ka yi mana, mun gode sosai da sosai"

"Babu komai Nabila, yi wa kai ne, kun cancanci hakan ne, daga ke har Al'amin"

Walid ya ce "Shikenan Alhamdilillah, zaman rami ya ?are, mun yi 'yanci, kumurcin cikin rami zai yi yawonsa freely a gari, Allah ya sa kuma kar ya addabi al'umma da sara" murmushi Viper ya yi.

"Yaya" suka ji an fa?a daga nesa, suna juyawa Shahida ce ta taho da gudu, ta ru?un?ume Viper tana kuka.

"Yaya dama zan sake ganinka? Yaushe rabon da na ganka a rayuwata, ashe zan sake ha?uwa da kai?"

Wani irin sanyi ne ya ratsa Viper, duk da ba wani good time yake yi da Shahida ba, amma atleast yar uwassa ce ta jini, kuma duk da irin cin kashin da aka din ga yi masa a gidan su, sosai take nuna masa tausayi da jin ?ai"

Rungumeta ya yi, sai dai ya rasa mai ze ce mata.

Ta ?ago tana kuma ?are masa kallo, ta ce "Na je prison ban san adadi ba, ba a bari na ganka, ina yawan yin kuka, idan na tuna halin da ka ke ciki, ?azu na ga text ?in Abbu, wai na taho kotu an wankeka daga zargin da ake yi maka, ni ban san yana ganinka kuna ha?uwa ba, na yi kewarka sosai yayana"

Ya ri?e hannayenta ya ce "Kin yi saurin girma Shahida, ?arama ce ke fa, lokacin da aka tsare ni"

Zata yi magana ta ha?iyeta ta ?arfin tsiya, sakamakon arba da ta yi da Nabila, cakumar rigar Viper ta yi, tana nuna masa Nabila.
Ya ce "Menene?"

"Ba ta mutu ba?"

Ya ce "Eh, amma ta dawo ne ta halarci taron kotu, ta ga yadda za a hukunta wa?anda suka kasheta, yanzu zata koma"

Nabila ta ce "Kaiiii"

Ki?imewa Shahida tayi cikin matsanancin tsoro, Walid ya ce "Viper kai fa ka iya wasan banza wasu lokutan, ba fa ta san ainihin abin da ya faru ba, sai ka saka ta suma ai"

Baba ya ce "Na ga alama ai, Shahida wannan ba Jauhar ba ce ba, twins sister ?in ta ce Nabila" tayi ?uri da ido, tana kallon Nabila.

Liti ya ce "Ke kin ta?a ganin wanda ya mutu ya dawo ne?"

Ganin Nabila ta samu nutsuwa, 'yan jarida suka cigaba da addabarta a kan tayi magana, tambayar da ta fi ?aukar hankalinta, har ta ji zata iya amsata ita ce "Wane irin farinciki ki ke ciki a yau, ganin kin yi nasara a wannan shari'ar?"

Tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, nayi farinciki sosai da sosai, dan wannan ce nasara mafi girma da na samu, tun bayan zamana cikakkiyar lauya mai zaman kanta, kuma in sha Allah yanzu aka fara.
Sai dai na sadaukar da wannan nasara tawa kacokan, ga babana maganin kukana, abin alafharina baya goya marayu ginshikin da na jingina da shi, ya zame mini tsananin da na taka na cimma wannan nasara. Mutumin da ya saita ni a kan wani buri da ban ta?a tunanin ina da shi ba, kuma zan ci karo da shi ba, yau gashi wannan burin ya cika wato Major Yusuf maitama mai ritaya, ina alfahari da kai dattijon arziki matu?a gaya. Ina fatan al'umma za su ci gaba da bamu goyon baya ?ari bisa ?ari wurin kawo gagarumin gyara da sauyi, a fannin shari'a da kuma harkar tsaro. Kuma ina fatan matasanmu maza da mata zamu nisanci shaye-shaye da ta'amalli da miyagun ?wayoyi".

Yanayin yadda Nabila take magana, ya sanya Viper ya kalli Shahida ya ce "Jauhar zata iya magana haka doguwa a gaban mutane cike da ?warin gwiwa ba tare da tsoro ba?" Shahida ta girgiza kai ta ce "A'a"

"To Nabila daban jauhar ma daban, wannan 'yar biyunta ce"

"But how, ban ta?a sanin tana da sister ba ai"

Viper ya ce "Is a long story"

Abbu abin har mamaki ya bashi, yadda a wannan karon, Viper ya sake da Shahida, duk da a baya, duk da irin shishishigi da take yi masa, baya saurarar ta.

Viper ya gabatarwa da Nabila Shahida, Nabila ta ce "Ai naga kamar haryanzu tsorona take ji, bari idan ta sake ta ?ara tabattar da ba jauhar ba ce, sai mu yi magana"

Wata ?atuwar helux ta shigo harabar kotun, ba?a ?irin sai ?yalli take yi.

Ta yi parking a gaban su Nabila, da Abbu, wasu zaratan ?arti ne suka saukko, su na sanye da riguna ba?a?e da tambarin dragon, bayan rigar kuma hoton maciji ne da sunan Viper.

Murmushi ne ya su?ucewa Viper, suka jeru suka din ga gaisawa sa shi ?aya bayan ?aya, suna yi masa congratulations da rungumarsa, yana amsawa cikin sakin fuska.

Suka gaggaisa da su Abba, sai dai girmamawa ta musamman suka yi wa Alhaji mu'azzam.

Viper ya ?alle rigar jikinsa, rigarsa ta ciki irin ta su ce.

?aya daga cikin su, ya ce "Oga yana son ganinka, shi ya ce mu zo mu tafi da kai we need to celebrate with you"

Ya jinjina kai ya ce "Ok to" ya kalli Baba ya ce "Baba bari na tafi, Nabila za a mayar da ita gida, idan na nutsu za ayi maganar in da yafi security ta koma, idan kuma za ta ci gaba da zama da madam shikenan. Shahida, zan zo gida zan yi miki gaisuwa ban in sha Allah.
T ladan ina godiya sosai da sosai" ya ?arasa maganar yana jinjina musu hannu, ya ce "Mai laya zamu yi magana, mu ha?e a chamber" yayi maganar yana dan?ar kwalar ?an mama ta ?eya ya tura shi cikin motar"

Liti ya ce "Wai yaushe zaku daina munafurtarmu daga kai har ?an maman, wa?an nan jibga-jibgan kamar kai su kuma suwaye, menene ala?arka da su?"

"Tambaye su mana" Viper ya yi maganar yana nuna masa su.

Ya kalli Nabila, yayi mata alama da hannunsa na zai kirata a waya, tare da kashe mata ido ?aya. Murmushi ta yi ta ?aga masa hannu, a daidai lokacin ya rufe motar suka ja, suka bar wurin.

Nabila ta kalli Abbu jikinsa duk a sanyaye, Baba yana ta bashi ha?uri, ta ce "Baba da kai da honorable, yakamata ku shiga cikin lamarin nan mussman kai, a sasanta Viper da Abbu, wallahi nayi nayi da shi ya?i, da na fara maganar yake ha?e rai"

Abbu ya ce "Na san kin yi iya ?o?arin ki Nabila, ki daina matsa masa, kin san mur?a??en mutum ne, mai taurin kai, amma mai raguwar zuciya, duk wannan abin da yake yi, zai saukko, zan ci gaba da ha?uri, har zuwa lokacin da Allah zai sanya ya saukko".

Viper ne a tsaye a wani katafaren office, wani narkeken mutum ya mi?e, ya ?arasa wurin Viper, suka yi musabaha, ya rungume Viper ya ce "Congratulations my man"
Viper ya ce "Thank you Sir"

"Congratulations once again Al'amin"

"Thank you very much sir"

"Yarinyar nan fa ta bamu mamaki sosai da sosai, bamu ta?a zaton za ayi wining case ?in ba, saboda case ne mai hatsari da sar?a?iya, amma thank God, Congratulations once again"

Ya kalli ?an mama ya ce "Anas" ?an mama ya ?an ?ago yana risunawa.

"Yaushe zaka tafi training ne?"

"Dan Allah sir ka yi ha?uri, ni ba sai na yi training ?in nan ba, a bar ni kawai"

Yayi murmushi ya ce "Viper ka ji abin da ya ce?".

Viper ya ce "Bai isa ba sir, dole ya tafi"

"To kai Anas, ko Viper bai fa?a ba, dolenka Anas, ai ka riga ka yi aiki da mu, you can leave, zan ganka" ?an mama ya fice.

Ya mayar da idonsa kan Viper ya ce "Viper, komai ya zo ?arshe, yaushe zaka koma bakin aiki gaba ?aya?"

Viper ya ce "Ina son a ?an ?ara mini lokaci, tun da ina gudanar da aikina daga nan, ina da abin da nake son ?arasawa ne"

Ya ?araso ya dafa kafa?ar Viper ya ce "Kamar haryanzu kana cikin pain Viper, amma yakamata ka tattara hankalinka wuri guda, a baka abin da za a baka ka cigaba da rayuwarka, amma duk abin da ka yanke shikenan, ina yi maka fatan alkhairi, zamu cigaba da baka dukkanin gudunmuwar da ka ke bu?ata"

Suka sake gaisawa da Viper ya fita.
*****
Bayan Nabila ta koma gidan madam Halimaz tayu wanka ta canza kaya, madam sai murna take tayata saboda nasarar da suka samu, kai tsaye gidan Abba ta tafi, ta nufi benensa cikin matsanancin farinciki da murna, suna tare da Nasir, da wasu daga cikin yaran gidan da matansa.
Gaban Abba taje ta zauna, tana ta murmushi bakinta ya?i rufuwa, gaba ?aya suka tattara hankalinsu a kanta.

Dogon skirt ne a jikinta, da over size t-shirt ta Viper, tayi rolling da veil, ta ?arasa gaban Abba ta dur?usa ta ce "Major Abba, na samu nasarar da ban yi zato ba, Alhamdilillah kotu ta wanke babban mai laifin da nake karewa, bayan da aka gano ba shi da laifin da ake zarginsa"

Fuskar Major babu yabo babu fallasa ya ce "Na tayaki murna"

"Abin da nake ta gaya maka kenan Abba, tun farko ba ka tsaya ka fahimce ni, nayi maka bayani ba"

Ya girgiza kai ya ce "Nabila, ni fa duk wani abu da ya shafi mahaifinki ba ?aunarsa nake yi ba. Da bai aura mata ?an daba ba, da duk haka bata faru ba, ai yana da wasu yaran, meya hana su ya aura musu shi, sai ita, saboda ba ta da galihu, ni fa mutuwar yarinyar nan, ?ara mini ?iyayyar mahaifinki ta yi, and na baki za?i idan zaki zauna a nan ne ki zauna, idan kuma wurin mahaifinki zaki koma, ki sauka lafiya ki yi abin da ki ke so, you are allowed to make decision"

Jiki a sanyaye Nabila ta saki hannunsa, ta kalleshi ta ce "Abin har ya kai ga haka Abba? Ban ta?a tunanin akwai ranar da za ta so, ka sanya na ji wani abu a raina, mai kama da ba kai ne

Please Login or Register in order to submit comment