band, ya kwanta a kafadun ta, ta dage qafafun ta sama riqe da waya ta na chatting da Yah Mahboob, ta na jiyo motsin qofar dakin Mammeen ta ta yi wurgi da wayar ta ta hau gyare-gyaren qarya, ko da Mammee ta shiga ta ga dakin kaca-kaca, fad’a ta fara,
“Yau da qazama nake da ban da takaicin haifar qazama, ke wai ko kunya ba ki ji, ki shiga bangaren su Yesmeen ki gan shi fess, duk da qazantar uwar su, dan Allah dibi yanda kk fito wanka ki ka tattaka dakin duk ya yi shatin datti, kalli pant din ki a qasan gado, kalli rigar ki a can, haka ki ke so ki girma cikin qazanta? Ina maki hani da zama qazama, ba namijin da ke son qazama , ko ba a samu mace mai tsananim tsafta ba, ana son a gan ta da tsafta daidai misali, amma ke ko ta sisin kobo ba ki da ita, toilete din ki har bana son leqawa, saboda datti, baki san in mijin ki mai tsafta bane sai ya tsane ki son ki ya ragu a ran shi saboda qazantar bayi ba ko?”
Dariya sosai Aaseeyah ta kece da ita, cikin dariyar ta ce,
“Dan shi ne sarkin masu kashin Nigeria ko Mammee,kan bandaki zai tsanen, ashe ma dama ba so na yake ba”
“Lallai ki na raina qazantar bayan gida, to bari ki ji, qazantar bayan gida ta kashe ma mata da dama aure, sannan ta sa an juya wa wasun su baya, domin in su na da kishiya mai tsafta sama da su, su na ji su na gani za a fada bayan gidan kishiya wanka ko kashi, su yi ta zargin cin amanar su ake”
Shiru Aaseeyah ta yi, dan bata gane cin amanar ba can ta ce,
“Mammee ni fa dik wadannan abubuwan ba su damen ba,dan ni ba auren da zan yi, na tsani abinda zai raba ni da ku”
Ta yi maganar ne cikin fadin iyakar gaskiyar ta, ganin haka ne ya sa Mammeen ta rungume ta, sannan ta shafa kafadar ta ta dama, ta ce,
“Aure babbar Sunnah ce wadda kusan mutane suka Maida shi dole,duk wanda kk ga ba su yi ba lokacin su ne bai ba, ko kuma Allah bai hukunta su na daga cikin wanda za su yi ba, Aure rahama ne, Aure ibada ne, Aaseeyah ko kin yi aure ba rabuwa mukai ba ai, duk sanda muka so ganin ki za mu je, in kin so ganin mu za ki zo, ballanta na ma a yanda na san ki, in kk samu wanda ya sace zuciyar ki sai mun neme ki Aaseeyah”
Dariya suka fara yi, nan Mammee ta taya ta gyara dakin, ta nuna mata duk abinda ya kamata ta na yi na gyara daki da bayin ta, su na gamawa Aaseeyah ta shiga wanka, ta wanke bakin ta, akwai tsaftar jiki Aaseeyah amma ta muhalli kam sai a hankali, ita a ganin ta ta na qoqari, tsaftar Mammeen ta ta wuce misali shi ya sa take ganin kamar Aaseeyah qazama ce.
Ko da ta fito uniform din islamiyya kawai ta saka,ta fita, abinci ta ci sannan ta ma Mammee sallama, bangaren su Umaimah ta nufa, ta gaishe da Ummee, ta amsa a dage, tare da cewa,
“Wai mutum za shi makaranta amma ya ci uban ado, kamar mai zuwa neman mijin aure”
Har ta wuce ta koma baya, ta ce,
“Ummee kenan, yanzu fa na girma inji Mammee na,Mammee na na cewa da a qauye nake da tuni an min aure”
Ta na fadin haka ta rufe fuskar ta wai ita ta ji kunya, da gudu ta fada dakin su Yesmeen, ta bar Ummee na zagin ta, ta na tsinewa rashin kunyar ta.
Ko da ta shiga ko shiryawa ba su yi ba, masifa ta fara musu, ta na neman huce haushin Ummee akan su, nan fa suka balbale ta da nasu masifar akan ta raina su, gaba suke da ita,
“To sannu wanda suka yankewa qasa cibi, dalla ku yi sauri, na tafi samo chaculate, na kwan biyu ban je da abun kwadai makaranta ba”
Umaimah ce ta dalla mata harara,
“To Yah Noor din ma baya nan dai,”
“To sai na ce maki wajen shi dama zani? Ko ya taba fita ya sa kwado ko makulli ya rufe dakin shi? Ni abinda na je diba daban abinda kk min magana akai daban”
Dan murmushin yaqe Umaimah ta yi ta fara shirin makaranta, Aaseeyah kuwa ta shiga dakin Noor, kwance ya ke riqe da wayar shi,ya na kallo, saurin kife wayar ya yi ya juya, ba wani kallo bane mara kyau, kawai yanda ta fada dakin ba sallama ne ya firgita shi, ita kuwa an bata tabbacin baya nan, a firgice ta juya zata gudu,cikin takun da bai fi uku ba ya isa gaban ta ya fizgi hannun ta tare da maida qofar ya rufe, jikin shi ta fada, shi kuwa ya mata kyakkyawar runguma,hancin shi ya manna a jikin kan ta, ya na shaqar qamshin shampoo din ta, ya na lumshe ido, abinda ba ya ji a wajen Umaimah kenan, Umaimah ga ta bata san tsaftar baki ba, ya na son ya dinga mata kiss amma wataran da ya ji bakin na wari sai dai ya hakura ya tsaya a lalubar qirjin ta, Aaseeyah kuwa bakin ta kullum na tsinka mishi da jinin jikin shi, ya na jin zaquwa da son kissing din ta, hakan ne ya sa yanzu ma ya ji ya na mararin jin lips din ta a nashi, har ya kai bakin shi saitin nata, ta bude idon ta, ganin me ya ke shirin yi ne ya sanya ta saurin kwace jikin ta,
“Yah Noor yau laifin me na yi da ka ke qoqarin kissing di na? In a baya ka sumbace ni da niyyar yi min abinda na so yi da Jubeir in ji ka fa amma, yau kuma fa?”
“Ni ki ka ga zan sumbace ki? Ta ina? Sai ka ce ban san me nake ba, me ki ka shigo ma yi min daki ba sallama ba kwankwasawa?”
Inda inda ta fara, ta na zaro ido,
“Immm…damaa.. na zo na ce ka sammin chocolate ne”
“Shi ne za ki shigo ba sallama?”
Daidai nan Umaimah ta shiga itama ba sallama,a qoqarin ta na ganin me sike yi,sai ta gan su tsaye, ta ji kuma ana ma Aaseeyah magana da fada, murmushi ne ya kwace mata, yanzu ta gamsu ba wata alaqa dake tsakanin su da ta wuce ta yan uwantaka.
“Daga yau kar ki sake shigo min ba sallama, debi ki tafi,”
“Ni fa?”
“Debar maku dika har su Yesmeen”
“Mun gode”
“Banzaye ku na abu kamar wasu qananan yara, dukkannin ku kun girma amma kamar jarirai”
Ba su kula fadan da yake ba suka fice, shi kuwa ya san ba halin shi bane fadan rashin dalili, sai dai ya tabbata kore kunya da hauka ya yi yau, lallai kafin ya samu biyan buqata a wajen Aaseeyah zai wahala da dikkan alamu, kenan kwanaki da ya yi kissing din ta ta yi shiru dan ta tabbata ta yi laifi ne ko?
Aaseeyah sun isa makaranta sun tarar har an fara karatu, zama sukai suma aka fara karatu da su, haddar ta ta bayar, ta koma gefe, su Ummu suleim kuwa sai da aka masu dukan rashin iya hadda dika, ta na cikin musu dariya ta ji an zuba mata dundu a bayan ta, sai da tari ya sarqe ta, yarinyar da ta zabga mata dundun kuwa ba da niyya ta yi ba, jakar ta take ta qoqarin cirowa ta maqale saboda zama a saman hijabin ta da tai, sai hannun ta ya kwace ta dirkawa Aaseeyah dundu, kusan mazauna bayan Aaseeyah duk sun shaida hakan, amma Aaseeyah fuskar ta ba ta nuna gamsuwa da wanan hadadden dundun da ta sha ba, dan haka ta qullaci yari yar akan sai ta rama.
Dake ranar ranar laraba ce, ana masu wa’azi, dan haka ko da a ka tashi duhu ya fara,su Umaimah na ta neman Aaseyah, sun rasa, gidan su yarinyar baida nisa da Islamiyyah, Aaseeyah ta cire abun hannun jakar ta, na fata ne akwai dan qarfe a jikin shi, nannade shi ta yi a hannun ta, ta na cikin soron su yarinyar a labe,ta kashe fitila, ko da yarinyar ta shiga ta ga duhu, sai tai tunanin an manta ba a kunna bane, ta na tafe ta na neman makunnin ta ji an zabga mata bulala aka, ihu ta bude baki zata yi, Aaseeyah da ta dade cikin duhun ta na kallon ta, bakin yarinyar ta damqe, ta juya ta ta durma mata dundu, sannan ta cukuikuye mata kai da hijabi, ta fita da gudu waje, sai ga ta a hanyar gidan su, ta na tafe ta na gyara jakar ta,ta na waige, can baya ta hango su Umaimah su na jajen ina take, tsayawa ta yi su tafi tare,tare da daidaita numfashin ta kan su iso.
Ko da suka iso ta hau masifa, ta na fadin, sai neman su take bata gan su ba, ita ko ta taho abinta,hakuri suka bata suka sanar da ita ai su ma neman ta suka tsaya yi, bayan sun fara tafiya ta waiga gidan su yarnyar, ta yi murushin ramuwar da tai, hankalin ta kwance duk da ta gano ba da gangan ta dake ta ba,suka ci gaba da hira har suka isa gida,Ummu Suleim ce ta ce,
“Dazu da yarinyar nan ta durma maki dundu, wata dariya da ta kufcen sai da na karya alwala ta da na riqe,”
“Ai ni ban zaci Aaseeyahn za ta hakura b ma, dan n san halin ki komai akai maki sai kin rama”
“Gani zawo sarkin rashin hakuri ko? Ai komai rashin hakuri na tunda ba da sanin ta bane dole n hakura ai,da ban hakura ba ai da ina can gidan su ina ramako, kuma ku ne ‘yan rakiya ta kun sani”
Dariya sukai ta yi su na tuna yanda abun ya faru kamar da gayya yarinyar tai dundun, nan kuwa ba da sanen ta bane, ita kuma ta na dariyar dukan da tai wa yarinyar a soron gidan su.
Kowa bangaren su ta nufa,ta na zuwa ta yi alwala ta tada sallah, ta na ruku’un raka’ar farko ta ji ana sallama kamar da tashin hankali, Mammee ce ta je dan ganin mai Sallamar, ko da taje sai ta ga yarinya kamar shekarun su Aaseeyah na ta kuka da shessheqa, goshin ta ya kumbura kamar an jefe ta da dutse, ga yayan ta nan murd’add’e ya na jijjiga ya na masifar a fito masa da Aaseeyah sai ya rama wa qanwar shi abinda ta mata,Aaseeyah na jin abinda aka ce ta tsawaita ruku’un.
Nan fa sallar waliyyai ta motsa, tun Mammee na leqawa ta ga ko ta idar, har ta gaji ta koma ta basu hakuri, tare da basu dubu uku a saiwa yarinyar magani, shi kuwa yayan ya amshe sannan ya ce idon shi idon Aaseeyah, yanda ta kumburawa qanwar shi goshi sai ya rama mata shi ma.
Ko da Mammee ta koma ciki, da bulala ta tsaya ta na jiran Aaseeyah ta idar, ita kuwa cikin sallar ta ke addu’ar Allah ya kwace ta, ya sa kar a dake ta.
Ta na yin sallama, ta fara bismillah xata yi karatun qur’ani, ita ga waliyyiya, kafin ta kai bismillar ta ji shimfidar bulala a bayan ta, tsalle ta sa ta dale gado ta na gantsarewa tare da ware murya ta na ihu, ‘yan biyu ne suka shiga gidan da gudu jin ihun Aaseyah, sun dawo daga masallaci.
Ko da suka shiga suka ga Mammee na qoqarin sake lafta mata daya, sai suka riqe bulalar su na bata hakuri, tare da tambayar me ya faru, Aaeeyah na ganin an riqe bulalar farin ciki ya kama ta, amma sai ta kwanta ta na kuka mai ban tausayi, ita a dole she is innocent.
“Barni Hassan na ci qaniyar ta, tun da ba ta san ta girma ba, ka dubi yarinyar nan kamar ta wai a ce har yanzu ta na fad’a a waje, har da kumbura ma yarinyar mutane goshi,wane irin iskanci kenan, so take ta dore da dambe har gidan auren ta,”
“Mammee wacce yarinya na daka?”
Cikin kuka mai tsanani take tambayar Mammeen.
“Kai sakar min bulala ta ni za ki mayar ban san ki ba? Ni fa na haife ki, za ki fadan me ya had’a ki da yarinyar mutane har ki ka dake ta ko sai na balla ki, yayan ta ya ce ta dake ki bata sani ba, ta baki hakuri, amma sai da kk dake ta har soron gidan su, wai ke mara kunya “
“Laaaahhhhh Mammeee wai wannan ‘yar ajin namu, sai Allah ya saka min kuwa tunda suka sa aka sake duka na, ga dundun da ta min ga dukan da ta ja min”
Kuka sosai Aaseeyah take kamar mai gaskiya,ganin haka ne ya sa jikin Mammeen ya yi sanyi, ta fara lallashin ta, da neman sanin jin me ya faru,
“Mamme me zan ce maki, bayan kin yarda da su, har kin daken, da ni na kumbura mata goshi zan riga su Umaimah tahowa ne? Ni da nake can ina neman su, har na yo gaba suka tadda ni a hanya, ki kira su ki tambayi me ya faru wataqila kin fi yarda da su, tunda ni ba ki yarda dani ba”
Miqewa ta yi da gudu ta fada bathroom, Mammee na cike da tsananin nadamar bulalar da ta shaud’a mata, ita kuwa ta na shiga ta fashe da dariya qasa qasa, tare da toshe bakin ta, kallon kan ta tayi a madubi ta ga yanda ta had’a zufa kashirba,
“Wato yin qaryar nan ma ba sauqi bane, a rayuwa gwanda kai gaskiya ka huta, bala’ii, ji yanda riga ta ta jiqe,”
Tube rigar tayi ta cire kayan ta tass ta fara wanka, daure da towel ta fita, fuskar nan kamar ta wadda aka cuta, ganin abincin da aka ajiye mata ne da juice? Sai taji yunwa ta motsa mata, kaya ta saka ta bar bangaren nasu, ta na zuwa su Yesmeen za su ci abinci kuwa,nan ta sa hannu su ka ci su ka qaro, tai nak, sannan ta fada masu me ya faru, nan suka tabbatar da ita ta daki yarinyar, ta dage akan ba ita bace, cikin fushi ta miqe za tabar dakin, dole suka amince ba ita bace, dan bata laifi ta qi yarda ba itan bace.
Dalilin qin bari a san ita ce kuwa shi ne, ta tabbatar daga hirar yarinyar da qawayen ta bayan an tashi ba da gangan bane, amma kuma Aaseeyah ta rantse tun a aji sai ta rama,ita kuwa da ta karya rantsuwar ta gwanda ta dake tan,shi yasa ma ba ta ji komai ba na nadama sanda ta na dukan.
Nan ta sha hira da su Umaimah, dan kuwa Ummu Suleim su na tsaka da hira ta fita.
Qarfe tara da rabi ta yi hamma tare da yi musu sai da safe, ta fita ta na sosa gefen fuskar ta, ta ga gilmawar mutane, an yi bayan lungun su da sauri, lallabawa ta yi ta bi ta daya bangaren, ta na tafe cikin sand’a ta isa gaban su, su na manne da juna, bakin shi cikin nata, hannayen shi na ta yawo a cikin rigar Ummu Suleim.
Salati ta saka, cikin gigita suka saki junan su, wani irin tashin hankali ne ya kama su, kamar qasa ta bude su shige ciki,
“Me ku ke yi anan da daren nan? Me ka ke yi da hannun ka a cikin rigar ta? Me ya sa ka ke sumbatar vakin ta? Laifin me ta yi?”
‘Laifi?’
Shi ne tunanin da ya shiga kan su a tare,
“Ba za ku fadan laifin da tai ba ka ke hukunta ta sai na fada ma Ummee ko Abee?”
Ta na magana kuwa qarar motar iyayen nasu maza na kunno kai, saurin barin wajen ta ke qoqarin yi Hussein ya ja hannun ta,
“Dan Allah kar ki fad’a wa kowa, in Abee ya ji zai kashe ni,”
“Me ya sa zai kashe ka, bayan hukunta ta ka ke,waye saurayin ki ke Ummu suleim da ki ke son aikata irn haka da shi Yah Hussein ya gan ki?”
“Ban gane ba”
“Eh mana, Yah Noor ya tabbatar min da yin hakan ma qanne hukunci ne, saboda ya na zargin ni da Jubeir abinda muke yi kenan,”
Sai a lokacin Hussein ya fahimci komai,
“Ba ki san saurayin nata ba, ba dan unguwar nan bane, kar ki fada ma kowa, in aka sani a gida duka za a mata, kinji ko”
“To na ji, ba zan fada ba, amma kai ma ka daina, tunda ai bata aikata komai ba, kullum mu na tare, ku sai ku dinga yanke ma mutum hukunci bayan ba ku ga ya yi komai da wani ba,yanzu rannan da Yah Noor ya kama ya dinga sumbata ta, zargin mu yake, ni da Jubeir ba mu yi komai ba,amma ya hukunta ni”
Zaro ido Ummu Suleim da Hussein sukai, ashe Yah Noor shiru shiru ustazu ustazu shi ma ya na qoqarin lalube Aaseeyah ne, lallai kuwa zai sa asirin su ya tonu, duk sanda Aaseeyah ta gano komai, sun bonu.
Jin muryar iyayen nasu na ma juna sai da safe ne ya sa suka yi shiru, sai da suka shige ciki suka sake dambalar da Aaseeyah sannan suka rabu.
Hankalin Ummu suleim ba a kwance yake ba, dan ta san Aaseyah na iya daga magar a ko ina, kuma a gaban kowa, ya za ta yi da ita, ko dai fahimtar da ita asalin me ke faruwa za ta yi ta roqe ta ta rufa musu asiri, ko kuma bari zatai har ta tona masu asiri baki daya?
Mammee ta ji ba da’di da ta ga Aaseeyh bata ci abinci ba, amma ta san gobe za ta ware ne, ai fishin ta dama haka yake, ko da ta shiga ta ma Abeen ta barka da dawowa daki ta wuce, ta kwanta tunanin abinda ta gani tsakamin Ummu suleim da Hussein na bijiro mata, ta zurfafa cikin tunanin ta ne kawai ta zaro wayar ta, data ta kunna ta shiga internet ta rubuta ‘MENE NE SUMBA’
Nan fa ta dinga ganin bayanai akan sumba, da yanda ake yin ta, har ma da wasu bayanan da bata tambaya ba, hankalin ta ne ya tashi, kenan raina mata wayo ake a gidan,yayun nata neman lalata su suke,ranta taji ya baci ainun,screen shoot ta yi na bayani akan sumba ta tura ma kowannen su ta whatsapp, sannan ta kashe data, ranta na matuqar zafi, akan sabon ilimin da ta samo akan sumbaaaa…….
Tirqashi, Aaseeyahn ku fa ta gano alfanun Sumbaaaaa..
TAUBASHI
PAGE 13
Hussein da ke ta tattuna yanda za su bullo wa lamarin shi da Ummu suleim ne suka ga message daga Aaseeyah, cikin hanzari kuwa suka buda, ganin abinda ta tura masu ne ya sake d’aga hankalin su, musamman Ummu Suleim,har kuka ta fara.
Kiran wayar Aaseeyah ta fara, Aaseeyah na gani ta dinga rejecting,Ummu suleim ji ta yi kamar ta fita ta je ta same ta a daren,Hussein ne ya kwantar mata da hankali, ya ce zai je ya mata magana,hawaye ta dinga zubarwa, ta na tunanin in asirin su ya tonu sun shiga uku.
Cikin sand’a Hussein ya murd’a dakin Aaseeyah, a tsorace ta miqe zaune, ko da ta gan shi sai ta ja tsaki ta koma ta kwanta.
“Me kazo min d’aki na? Ko ka zo ne nima ka min abinda ka ke ma Ummu Suleim?”
“A’uzubillahi, ta ya zan miki abinda na ke ma wata, ke fa qanwata ce,”
“Ita kuma ba qanwar ka ba ce?”
“Qanwa ta ce amma..”
“Amma me?”
Tashi ta yi ta zauna sosai, ta ce,
“Na karanta cewar irin kiss din da kuke, da rungumar da ka ke mata miji ne kawai ke wa matar shi haka,an maku aure ne ban sani ba?”
Dafe goshin shi ya yi, duk yanda ya ke tunanin abun ba haka bane, ta zurfafa a binciken ta.
“Aaseeyah mun yi nadamar abinda muka aikata, da ni da Ummu Suleim yanzu muka gama chatting na ce bari na zo na baki hakuri, dan Allah ki rufa mana asiri, ba za mu sake ba, in kk fada sai su Mammee su tsine mana ai, ko ki na so iyayen mu su tsine mana?”
Kad’a kai ta yi cikin tura bakin ta, tare da kallon shi ta gefen ido,wuyan ta da ta karya ya kalla,ajiyar zuciya ya sauke, da alama nasara ta fara samuwa.
Sake marairaicewa ya yi ya dinga lallaba ta,har sai da ya tabbatar maganganun shi sun yi matuqar tasiri a ran ta,kuma ya gamsu ba za ta fad’awa kowa ba.
Cikin sanda ya koma d’akin su ya fada ma Ummu Suleim duk yanda sukai da Aaseeyah, nan fa ta dinga murna, sannan ta ce masa ya kamata su daina, dan watarana iyayen su ne za su gani ba Aaseeyh ba,(suna ta mantawa da Allh a wannan lamari ohh ni hameedah).
Dabara ya dinga mata, tare da nuna mata taku kawai za su sauya, ko su fara had’uwa a waje, shiru ta yi daga baya ta amince, dan kuwa ita ma ta na matuqar jin son abun a ran ta,kuma ta fara sabawa da hakan.
Yah Noor kuwa bai tashi ganin wannan saqon tashin hankalin ba sai da asuba ya dawo daga masallaci, dabas ya zauna a kujera ya karanta tsaf, sannan ya karanta saqon ta na qasa, ji ya yi kamar ba yawu a bakin shi,nan da nan ya goge message din,ya fara qoqarin kiran ta,wayar ta a kashe, dan ba su zuwa da waya boko, kashe ta suke, ta na can ta fara shirin makaranta,har ta ma manta da abinda ya faru daren jiyan.
Da misalin qarfe bakwai da minti goma, ta shirya tsaf, ta fita zuwa wajen su Umaimah dan kiran su, ta tarar su na cin abinci, duk da cewa Ummu Suleim ba ta kai su hayaniya ba, ta sake zama shiru, kunyar had’a ido take da Aaseeyah, Aaseeyah kuwa ta nuna mata ai ba komai,amma duk da haka bata sake ba, dakin Yah Noor ta nufa, ta gan shi ya na ta sintiri, ya leqa kiran ta dan su yi maganar ya ga ta na harkar ta kamar ba abinda ya faru, dawowar shi kenan ya gan ta burum kamar an wurga ta, Ummee na kiran ta kwadayayyiya ko juyawa ba tai ba balle ta kula ta.
A razane ya kalle ta,ita kuwa ta gaishe shi kamar batai komai ba. Bude inda yake aje sweets da chocolates ta yi ta ga wayam ba komai, dan tura bakin ta tayi ta ce,
“Yah Noor ba ka amsa gaisuwa ta ba,kuma ya na ga ba komai, ko ka bawa Umaimah dika ne?”
“Ke ki ka turan saqon jiya?”
“Wanne saqo?”
Kallon ta ya yi kamar zai make ta, dan ja da baya ta yi sannan ta ce ,
“Eh ni ce, na gano abinda ku ke yi kai da Yah Hussein da Ummu Suleim, kai ma so ka ke ka dinga taba ni kamar wani miji na, Allah ni ba zan yarda ba, masu yin haka kan aure yan iska ne, ni kuwa ba yar iska bace, duk rashin ji na ba na iskanci”
“Amma inna aure ki za ki yarda ina taba ki?”
Zaro ido ta yi, sannan ta rufe fuskar ta cike da kunya, sai ta d’an daga kai,alamar eh,
“Da kyau, ki gama secondaryn ki, inshaa Allahu ba ki da miji sai ni, amma ki min alqawarin ba za ki bari kowa ya miki iskancin ba kin ji?”
“Na ji,”
“Sannan ki alqawarin ba za ki fad’awa kowa sirrin mu ba, kinga in kk fada ma wani na tab’a sumbatar ki d’an iska za a ce ma.mijin ki,”
Dan shagwabe fuska ta yi ta ce,
“Ai na fada wa Ummu Suleim da Yah Hussein jiya”
“Damn it! Ki ka ce musu me” cike da matsananciyar damuwa ya ke jiran amsar ta.
“Na fad’a masu kai ma ka taba yi min abinda suke yi, amma ban fad’a masu sau nawa ba ne ai”
“Kar ki sake fad’awa kowa, kin ji? Indai ki na so na aure ki”
“To,”
Kudi ya bata ya ce ta sai chocholate din in ta je makaranta, ta ce rabawa biyu zatai ta sai awara, adashen awara suke yi, bai sake kula ta ba har ta qaraci surutun ta ta fice, saida suka wuce makaranta sannan ya shirya shima dan fita, to ya zai ya kalli Hussein ? Shi da kullum ya ke nuna masu rayuwar da suke ba me kyau
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 41