ko dai sauya halin rashin jin nata bai burge kowa ba ne, wataqila za ta dawo kamar da, hakan shi ne zai sa Yah Noor ya dawo da kulawa da ita kamar da.
Fita tayi ta fara neman shi dan ta bashi hakuri, sannan ta ce masa ta daina saka dan iskan dinki, Umaimah ta gani ta nufe ta da saurin ta, gani ta yi umaimar na barin wajen a lokacin da suka hada ido, ta nufi tsohon bangaren su Mahboob da ke a rufe, ita ma bin ta tayi, ko da ta isa bata ga Umaimah ba ta hau kiran sunan ta ta na neman ta,
"Me ne ne wai,ki ke neman qarar min da suna?"
Cikin mamaki da zaro ido Aaseeyah ta kalli Umaimah wadda ba ta ji nadamar masifar da ta ke ba,sai ma jin wani sabon kishi da tsanar Aaseeyah da ke taso mata,
"Umaimah lafiya kuwa? Me ya yi zafi haka kk min magana kamar wata na maki laifi? In na maki wani abu ne ai sai ki fada min amma ba ki dinga magana kamar wata kububuwa ba"
"Ko ba kububuwa ba? Dalla malama ki daina abu kamar ba ki san me kika aikata ba, to ki bude kunnen ki da kyau ki ji me zan sanar da ke Aaseeyah,ki yi gaggawar nesanta kan ki da Yah Noor, domin Yah Noor nawa ne, ni kadai ba zan iya raba shi da kowa ba, ki san matsayin ki, ki kama kan ki a matsayin qanwar shi, ki daina naniqewa ki na neman kulawar shi dom...."
"Ke dalla malama dakata, shin Yah Noor din kud'i ne shi ko abinci ne shi da kk maganar kaso? Ni ba ni da masaniya akan abinda kk magana akai, in zaki fito fili ki magana ki fito, ki daina min wani kwana, dan kin san sarai magana cikin magana ba gane ta nake ba"
"Kin gane me nake nufi sarai, amma in ba ki gane ba bari na miki gwari gwari, ina son Yah Noor sama da yanda nake son kai na, ina son ki janye ki daina naniqe masa ki na neman kulawar shi, ina fatan yanzu kin gane ina na dosa ko?"
Shiru Aaseeyah ta yi ta na kallon Umaimah, wadda ta ke kallon ta itama tare da jiran jin amsar ta, dariya Aaseeyah ta kece da ita, har da duqawa, sannan ta kalli Umaimah da ta qulu,
"Yanzu ke dan Allah yayan ki kike so? Yayan ki ki ke kishi kamar wata baki san me kk ba? To kwantar da hankalin ki, Jubeir na ke so, in bayan na san ba za a amince min da tarayyar mu ba da har gidannan zai dinga zuwa, ke shaida ce ina son shi, Yah Noor yaya na ne, matsayin shi kenan, in ki na da matsala da hakan kuma sai na ji, haba Umaimah, ina soyayyar da ke a tsakanin mu ta 'yan uwantaka har da za ki daga hankalin ki ki na fadan magana a tsaitsaye "
Cikin dan jin nauyin Aaseeyah Umaimah ta sunkuyar da kai, sai a yanzu ta kula da wautar ta, ta manta cewar Aaseyah bata da masaniya akan komai, ita din a duhu take, dan haka sai ta wayance ta hau bata hakuri, har suka daidata kan su,kallon bangaren ta yi cikin baqin ciki da kewa, sannan ta kama hannun Aaseeyah dan komawa parlourn.
Alhaji Muhammad da Alhaji Ibraheem da matan su na zaune a table din da ya fi dukkan sauran tables din qayatuwa su na zaune su na cin abinci suma tare da hira, kowannen su ya sha ado na alfarma, matan su kuwa kamar za su gasar sarauniyar kyau, kwacce ta na ba wance bace ni ce,daya daga cikin samarin da ake kira da Uwais ne ke magana ta abin magana,ya na fadin sunan shi, da na mahaifan shi, da garin su, da kuma yi musu barka da sallah, haka suke ta tashi daya bayan daya, in wannan ya je sai wannan ya dawo.
A haka har aka zo kan su Aaseeyah ita ma ta gabatar da kan ta,akai- akai ta fadi sunan iyayen ta taqi sai dai ta ce 'Mammee na da Abee na' ai kuwa wajen sai dariya ake mata, ita kuwa ko a jikin ta, budar vakin Ummee sai cewa tai,
"Ai da yake sakara ce gani take dan ta ce Subai'a ko Ibraheem ta yi ba daidai ba"
Ran Mammee ya baci ta so mayar mata da magana amma dake ta sha roqo wajen mijin ta kafin su zo wajen sai ta hakura ta danne.
Noor bai dawo daga wajen budurwar shi ba sai da kowa ya gama gabatar da kan shi har an fara watsewa ya dawo.
Aaseeyah kuwa tun da ta gan shi ta fara qoqarin kaucewa duk wata hanya da zata hada su ko da da wasa ne, hakan ba qaramin sanyaya ran Umaimah ya yi ba, ta tabbatar da cewa Aaseeyah ba ta son Noor, dan haka wannan ce damar ta da za ta kafa soyayyar ta a zuciyar Noor din........
Toooo sai na ce Umaimah mu je zuwa mu ga ni ko akwai nasara?????
TAUBASHI (COUSINS)
BY HAERMEEBRAERH
Page 8:
Shagalin sallahn wannan shekarar daban yake da sauran shekarun da suka gabata a cikin wannan ahalin, domin kuwa an samu zumunci ya qullu a tsakanin wasu bangarorin, wasu daga cikin matasan sun samu abokan rayuwar su, har magabatan su sun san hakan, dukkan bangarorin na cike da farin ciki da murna, sai bangarori biyu da aka sha fama kafin su sake zuqatan su su taya ‘yan uwan nasu farin ciki, amma a so samun su, kar alaqar jini ta qullu a tsakanin su, wannan bangare biyun ba kowa bane face Ummee da Mammee.
Bangaren Umaimah kuwa a qoqarin ta na ganin ta cusa soyayyar ta a zuciyar Yah Noor, ta maida hankali wajen kyautata masa, wanda kusan kowa ya kula da yanda ta ke masa hidima, hatta da kayan shi sai ta kwasa ta ce za ta wanke, ana bikin sallah kowa na gayu da farin ciki ita kuma ta na bautar soyayya,Yesmeen da Aaseeyah kuwa dariya suke mata in suka ga yanda take dagewa wajen yi mishi guga da gyaran daki.
Yau ma dauke take da tsintsiya da parker za ta shiga dakin Yah Noor bayan sun fita shi da su Yah Uwais, Aaseeyah da ke zaune a kujerar da ke kusa da kitchen ce ta kalle ta ta kwashe da dariya, Yesmeen ma ta dauka, Ummu suleim da ke taya Najwah daurin d’ankwali ce ta tsaya da abinda take ta ce,
“Wai me ya sa in ba ku yi tsokana ba ba ku jin dad’I ne? Ina ruwan ku da ita, tsabar neman ayi rigima ne ya sa ku ke mata dariya, kun san dariya na da cin rai ko”
“To ai da ta na ci mata rai da tai magana, ‘yar wahala qatti su zauna su b’ata daki ki na tafe da tsintsiya da parker kullum a hannu kamar an sanya ta”
Wata dariyar suka kwashe da ita, ko kula su batai ba, ta fad’a dakin ta rufe qofar, kaya ne a baje wasu a qasa wasu a saman gado, cumb da vest duk a qasa, ga shatin ruwa nan dik a qasa alamar an fito ana digar ruwa ko tsanewa ba ai ba.
Ko haushin hakan Umaimah ba ta ji, fadi take a ran ta,
‘Kwana nawa ne za su tafi komai ya koma normal, daga jibi fa shi kenan, ba zan bari maganar yaran can ta bata raina ba nai wasa da dama ta,’
Kafin qanqanin lokaci ta gama, ta goge d’akin ya yi fess room freshner ta fesa ko ina ta sake labulayen da suka dage, ta na qoqarin fita Yah Noor ya dawo cikin sauri, ya yi mantuwa da makullun motar shi, sun jima a babban parlour ana hira, sai da suka shirya fita cikin gari ne ya duba ya ji ba key din a jikin shi, ko da ya shiga sai ya coge a bakin qofa ya na fada ma Aaseeyah ta je ta dakko masa,budar bakin ta sai cewa tai,
“Umaimahn ka na ciki ta na gyara dakin,wataqila ta san inda yake,”
Qasa qasa Yesmeen ke dariyar maganar Aaseeyah wai umaimahn ka.
Ya na shiga ciki suka tafa, tare da fadin,
“Sai kace irin matar shin nan,” inji Yesmeen.
“Kuka sani? In Allah ya yi shi ne mijin ta fa?” cewar Ummu Suleim.
Aseeyah kallon ta tayi da irin kallon nan na baki da hankali ne? Amma sai bata ce komai ba ta ci gaba da chatting din ta da qawar ta Rahmah da ta ke sanar da ita za ta zo kawo mata ziyarar sallah anjima, bayan sun gama sallamar Jubeir ta gani, nan da nan zuciyar ta ta fara zillo dan murna, ta zaci ya yi fushi da ita, rabon su da magana tun da Yah Noor ya mata fad'an saka matsattsun kaya, wanda a da kuwa kusan ko me take suna maqale a waya ko su na chatting.
Ko da Yah Noor ya shiga ganin ta ya yi a tsaye da alama fita za ta yi, hannu ta miqa masa, ya kalla, sai ya ga makullin motar shi ne, da mamaki ya kalle ta,
“Ya akai kk san shi nazo dauka?”
“Na ji ka na fada ma Aaseeyah ta dako maka sanda zan fito,”
“Ok, thanks Durling,gaskiya ina jinjina ma qoqarin da kk min, Allah ya miki albarka yar qanwa ta,”
Murmushi ta yi tare da sanya yatsanta a baki ta na kallon shi, tana juya jikin ta, har zai fita ya koma ya rufe qofar, ya jata jikin shi,bakin shi ya kai kunnen ta sannan ya rada mata cewar,
“Anjima da dare ki shirya, za ki raka ni wani waje, daga ni sai ke, za ki je?”
Cikin kasala ta ke daga kan ta, tare da cije lips din ta, kallon bakin na ta ya yi, ya sumbace shi kadan sannan ya fita,tare da sake furta mata
“Na gode Umaimah Durling”
“Umaimah durling????”
Su Yesmeen da Najwah suka hada baki wajen fada,daga baya suka qunshe dariya, ya na fita suka fada dakin da gudu su na tsokanar ta da Umaimah durling, ita kuwa ba abinda take sai dariya da jin kunya, ita kadai ta san irin yawan soyayyar Yah Noor da ta kwaso a zuciyar ta, dan ji take kamar ta yi zari ta debo da yawa.
Da misalin qarfe biyar na yamma, Rahmah ta iso gidan su Aaseeyah, nan fa suka shiga ciki, inda ‘yan matan gidan suka taru ana hira, Rahmah sai rarraba ido take dan ganin zuri’ar kyawawa, wani iri take ji a ranta na dama a ce ita ma a wannan ahali take, mata ne sun kai tara kowacce da kalar kyaun ta, wasu baqaqe masu kyau, wasu farare tass ga kyau, wasu sirara wasu masu qiba, wasu matsakaita, duk da cewa itama Allah ya azurta ta da daidai nata, sai ta ji ta raina, ta na son qari,lemo da snaks da soyayyan nama Aaseeyah ta aje mata, ta dauka ta kurbi kadan,Aaseeyah ta ce,
“Rahmah ni fa na manta yaushe za a koma school, tsabar na tsani boko,”
“Ai ke dai Aaseeyah ki na buqatar addu’a, ace mutum.ba ya son karatu, ni na tabbata da ki na maida hankali da ke za ki na mana na daya, amma tunda kike ba ki taba na hudu bama”
“To ‘yar rainin hankali tonan asiri gaban dangi na, naji din, tunda na iya na muhammadiyya ku riqe na su Obama na bar maku”
Fairoozah ce ta kalli Rahmah ta ce,
“Wannan makarantar ku daya da ita kenan ko Aaseeyah?”
“Eh Aunty Fairoo,ajin mu daya tun da na shiga makarantar, ita ma ta na cikin kayan gadona na makarantar in na tashi fita, har da ita zan hada”
“Ban gane ba?”
“Eh mana, makarantar fa muke zuwa tun daga nursary har yanzu muna senior secondary school ba a sauya mana ba, makaranta kamar gidan gado,”
Dariya kowa yake saboda yanda Aaseeyah ke maganar ma kan shi abun dariya ne,
“Ke dai ki maida hankali a karatun ki, ki aje shirirtar wani baki son karatun boko, karatu na da mahimmanci a wajen al’ummar musulmi baki daya, bayan taimakon kai”
“Inshaa Allahu aunty zan dage, daga wannan term din za ku sha mamaki”
“Allah ya sa”
“Ameen”
Kowa hirar shi ya kama, inda Rahmah ke ta duba wayar ta, ta na maida saqon da ake tura mata, can ta ce ma Aaseeyah,
“Aaseeyah zo mu dan je waje ki ji”
Kallon Rahmah Aaseeyah ta yi ta ga yanda ta ke qasa da murya kuma take kallon mutanen wajen, da alama bata son a ji ko a ga fitar su, dan haka Aaseeyah itama ta tashi a hankali dan kar a kula da fitar su.
Magrib ta yi dan kuwa kiran sallar ma ake ta yi, a bakin gate Aaseeyah ta tsaya ita da Rahmah, cikin wayewa da kwarewa irin ta Rahmah ta ce,
“Qarar ki fa aka kawo min Aarce”
Gaban Aaseeyah ne ya dan fadi kadan, dan ta san mutum daya ke kiran ta da wannan sunan,Jubeir.
“Qarata kuma? Wa ya kawo qara ta wajen ki, a duk mutanen duniya a rasa wajen wa za a kai qara ta sai ke, ke da kin ci kuma kin sha duka na ba sau daya ba ba sau biyu ba”
Tunawa da hakan ne ya sa Rahmah dan maida confidence din ta da da ta ke da shi, ta sassauta murya ta ce,
“Dallah ba wani abu bane ba fa, dama Jubeir din ki ne duk ya susuce ya damu, akan rashin ganin ki da bai ba na kwanaki, jiya har qara masa ruwa sai da akai, ba shi da lafiya,dazu ma shi ya kawo ni, ya so ya gan ki, yanzu ma shi zai zo dauka ta dan Allah ko leqawa ne ki je ya gan ki,”
Wani kishi ne ya takure zuciyar Aaseeyah waje d’aya, ta kalli Rahmah a kaikaice ta ce,
“Ke kuma a wa da zai kawo ki nan, sannan ya zo ya maida ki gida? Wace ce ke a wajen shi? Ina ce dazu ma mun yi chatting da shi a whatsapp, wata sabuwar gulma ce hakan ko me”
“Kinga Aaseeyah kar ki mana mummunar fahimta, na zo ne musamman saboda roqo na da ya yi, ya na tunanin ni zan zama masa tsani na ganin ki, na yi haka ne dan sanin kema ki na son ganin shi, da yayan ki bai tsananta maki da tsaro ba, da ban tausaya maki na zo ba, sai anjima”
Cikin bata fuska ta yi qoqarin fita, Aaseeyah ta yarda da kalaman ta, dan haka ta riqe mata hannu ta na bata hakuri, tare da nuna mata ta amince da abinda ta ce su je ta gan shi ya gan ta sai ta dawo,Rahmah cikin murmushin da ita ta bar ma kan ta sanin me ke zuciyar ta suka fita daga gate din, Aaseeyah ta ce ma baba mai gadin su zata raka qawar ta ne, dan Yah Noor ya bada dokar kar su fita sai da vabban dalili, kuna in za su fita su fada masa inda za su, saboda ko baya nan ya dawo a fada masa.
Jubeir ya sha shadda kalar toka ya yi kyau sosai, idanun shi sanye cikin farin gilashin shi mai qara qarfin gani, ya zuba ma hanyar ido cike da murmushi,Aaseeyah ma murmushi take da ta hango shi, kafin su isa ya bude motar shi ya fada, ya ci gaba da kallon takun ta.
Ko da suka isa Aaseyah ta zaga ta gefen mai zaman banza ta kura masa ido, Rahmah na daga waje ta na jiran su,
“Ka ga kyaun da kai kuwa? Ban taba zaton manyan kaya za su karbe ka haka ba, a gaskiya ba na biyun ka My Jubeir”
“In ana maganar kyau da an gan ki ai an dasa aya Aarce,I missed u so much,yanzu haka za mu zauna ba zamu dau mataki ba akan raba mu da yayan ki ke shirin yi ba?”
“Jubeir ni kai na ba na jin dad’in hakan, amma a gaskiya ba zan ma yayana musu ba, domin gaba yake da ni ya san me ne ne yake daidai me ne ne ba daidai ba,”
“Ki na nufin za ki iya rabuwa da ni in aka ce ki rabu dani kwata kwata?”
Shiru ta yi idanun ta na kawo hawaye, dan kuwa ta san za ta iya hakuri da shi din indai da za a ce ta barshi, duk rashin jin ta ta san daidai.
Hannun shi ya sa ya ja nata da take wasa da shi a saman cinyar ta, da sauri ta daga kai ta kalle shi, murza yatsan ta mai zoben zinare ya fara yi a hankali sannan ya yi yunqurin hade fuskar su waje daya, har ya samu nasarar fara tsotsan lips din ta na qasa ta kula da hasken wayar Rahmah, da alama daukan su hoto take ko video,da sauri ta tura shi baya, ta na qoqarin bude murfin qofar ta fita, gam ta ji motar a kulle, kallon jubeir ta yi, sannan ta kalli Rahma wadda da fari ta tsorata ta zaci Aaseeyah za ta samu damar fita, sai kuma ta ga ta kasa bude qofar da alama ya rufe, murmushi ya yi na mugunta sannan ya ce,
“Well, a ina muka tsaya my dear Aarce”
Wani kallon ka ci amana ta Aaseeyah ta mishi, sannan ta kada kai, ta daga hannun ta daya ta ce,
“Ko za ka iya min bayanin abinda ke faruwa?”
“Kwarai da gaske, amma fa labarin mai tsaho ne, ki na da lokacin saurarar shi?”
Kallon shi ta yi cikin takaici, ba ta ce komai ba,ta na tunanin irin cin amanar da suka mata a yanzun.
Rahmah ce ta duqa ta miqa masa wayar shi da ta musu video, sannan ya miqa mata kudi ‘yan dubu dubu, ta ce ma Aaseeyah,
“To qawa sai mun hadu a school in an koma, ki sani, ni Rahmah ban taba qaunar ki ba, kin dasan qiyayyar ki a rai na tun mu na yara, bayan fi na kyau, da dogon gashi da kika yi,cimar ki ta fi tawa, sannan motar da ake kawo ku sama take da tawa, ga uwa uba mugunta da kk min, har zuwa girman mu ba ki daina cin zali na ba, da frank din ki ya tashi akai na yake qarewa, shiru nake kawai, sau nawa ki na ja min duka ke ba a dake ki ba? Sau nawa ki na sawa a sa suna na a masu surutu ke ki tsira ba sunan ki? Wannan ita ce hanya mafi sauqi da zan rama me kk min, Jubeir ya kawo min buqatar shi na in taimake shi dan ya na son kauda kwadayin shi akan ki, wanda ya jima ya na dakon shi, ni kuwa ko da bai min alqawarin dubu goma ba da zan taimaka masa, ballan tana ga kudi kuma ga biyan buqatar bata ran ki da zai yi, na barku lafiya masoyan asali”
Ta na kaiwa nan ta sa kai ta bar wajen cikin jin dad’I, da ta san abinda ta aikata me zai jawo ma Aaseeyah da bata aikata shi ba.
Jubeir kuwa cikin murmushin samun nasara ya kalli Aaseeyah da idanun ta ke zubar da hawaye,saboda mamaki, a rayuwar ta kaff bata bama Rahmah wani mahimmanci ba da har za ta ma zaci ita Rahman ta tsane ta haka, ba wani qawancen qut da qut suke ba, saboda akwai yara da yawa da ke son hulda da ita saboda kyaun ta, zuwa da abinci mai dad’I da kuma azziqin su, duk da yaran yawancin su yaran masu kudi ne, amma wani yafi wani.
“Ina maki magana kin wani tafi duniyar tunani,”
Jan hancin ta tayi, ta goge hawayen ta, sannan ta kalle shi, da alamar ba ta ji shi ba.
“Na ce ya ya kenan yanzu? Ki na ganin za ki iya bijire ma yayan ki akai na, ko kuma za ki biye mishi ki rabu dani, ni kuma na tura masa wannan videon, kinga ina da No shi ma”
Shiru ta yi ta na jin hawayen tsanar shi na zubar mata, da ta san haka yake da bata sanya soyayyar shi a ran ta ba tun farko, da bata amince shi din mai son ta bane, da haka bata faru ba, da ta ji nasihar Mammeen ta akan kula maza, yansu ya zata yi?????
Mutuniyar ku na neman shawara faaaaa a kawo dauki…..
💅🏻 TAUBASHI (COUSIN) 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
Page 9:
Fuskar Jubeir ta faranuna alamar rashin hakuri da jiran amsar Aaseeyah, cikin cijewar haqori da zare mata manyan idanun shi ya ce,
"I don't have all day to wait for ur answer kin kuma san haka ko?"
"Jubeir yanzu hukunci ya rage naka, ka na da damar da zaka yi duk abinda ka ke so da ni ba zan hana ka ba, indai soyayyar da na ke maka ita ce laifi na a rayuwa in buqatar hukunci,.....kabani mamaki Jubeir, na sha jin tarihin sahabban Annabi, Sahabin da ke da sunan ka mutumin kirki ne, ya na daya daga dalilin da ya sa ka shiga rai na, sannan a baya ina maka kalon ka gaji mai sunan ka, ashe.....ashee...ban san ka ba...ban san wane ne kai ba Jubeir....ka aikata duk abinda kk so Jubeir,in ka gama ka buden qofa na shiga gidan mu....in ya so sai na qarasa nuna ma kowa abinda ka min...ka ga na hutar da kai asarar data, na hutar da kai cikar memoryn waya, Jubeir kai nake jira, i don't have all night to wait for ur fake love"
Cikin tsananin tsawa ta qarasa maganar ta, idanun ta na zubda hawaye ba tare da ta san suna zuba din ba, jikin ta na fidda zufa saboda damuwar d take ciki, ta san ba mai fidda ta sai Allah, ita ta jawa kan ta, da ta bi maganar Mammeen ta ta ji fadan Yah Noor da ba ta so Jubeir ba, da bai qoqarin bata rayuwar ta ba.
Ba qaramin sanyi jikin shi ya yi ba, amma shaidaniyar zuciyar shi na tunzura shi, hannun shi na rawa ya fizge dan qaramin mayafin ta, rintse idanun ta tayi, tare da cije leben ta na qasa ta na jiran ta ji me zai faru, wata qara taji ta tarwatsewar abu, da sauri ta qanqame jikin ta saboda tsorata da tayi, a daidai lokacin Jubeir ya saki qara shima, hannu Noor ya sa ta daidai inda ya fasa glass din window n motar Jubeir, bude qofar motar ya yi, ya fizgo Jubeir dake digar jini ta goshin shi da kuncin shi, sai dokin wuyan shi, tartsatsin da glass din ya yi ne ya ji masa wannan ciwon, Noor bai kula da jinin da ke zuba ba ya hau naushin Jubeir, ko ta ina, wannan damar Aaseeyah ta samu ta fita daga motar da gudu, tare da zagayawa kusa da Noor ta na fadin,
"Yah Noor ka amshi wayar shi, kar ka barshi ya tafi da ita plsss,"
Noor bai tsaya ba bai kuma yi alamar ya ji ta ba, sai da ya jibgi Jubeir sannan ya fara laluba aljihun shi, ya na samun wayar Jubeir ya sake shi ya zube a qasa, ya na maida numfashin wahala,kuka ya ke son yi amma ya kasa tsabar dakuwar da ya yi,Noor jujjuya wayar ya dinga yi a hannun shi, ya rasa password, tambayar Jubeir ya dinga yi password amma ba halin magana,
Amsar wayar Aaseeyah ta yi ta rubuta 'Aarceeee'
Sai ga waya ta bude, kwasa tai da gudu dan bata son Noor ya ga me ye ta ke son gani a wayar, kwala mata kira ya dinga yi amma taqi tsayawa, dan banzan gudu gare ta, ya san hakan shi ya sa bai ma yi yunqurin bin ta ba, dan ba zai kamo ta ba, ta na gudu ta na duba videon, daf qofar gate din maqotan su ta tsaya, ta samu videon kuwa duk ta goge,ta shiga chats din su ta goge komai, da hotunan ta da ta sha tura masa wanda ya dace da wanda bai dace ba, ta na yi ta na kuka,tare da danasanin abinda ta aikata, sai da ta gama tasss ta koma ta wurga masa wayar a fuska,ya na nan kwance ya na fadin,
"Ku kai ni asibiti.....zan...zan mutu"
Wayar tashi Noor ya dauka, ya kira mahaifiyar shi, ya sanar da ita inda d'an ta yake,tare da yi mata kashedin gaba gawar shi za ta dauka in bata jawa d'an ta kunne ba akan iskancin da yake, cike da tashin hankali ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 41