Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baku nan da kwana biyu a binciko ko wane ne ke da hannu a kan fitar firsunonin, nan da sati daya ina son a kamo su dik inda suke" Wayar shi ce ta yi ringing, ya katse ya dauka dan ganin mai kiran nashi, "Maza maza ku bi su, kar ku sake su bace muku, ku kamo su, ku na daidai ina ne yanzu?.....ok gani nan zuwa da kaina" Cikin wasu mintuna da ba su wuce biyu ba Aliyyu ya ba ma wasu jami'an tsaro umarnin bin shi zasu wani waje,Aliyyu ne zaune a gefen driver, yanayin yanda ya fito kawai ya bama drivern tabbacin cewa akawai inda za su na gaggawa, unguwar da za su je Aliyyu ya sanar da drivern, da gudu kuwa ya bar hedikwatar. ****************************** Aaseeyah ta gama lectures din ta, ta na tsaye jiran Mahboob, zafi duk ya dame ta,ta gaji liqis, amma taqi tafiya, ta na gudun kar ta tafi ya zo, tunda neman sulhu take dole ta jira shi. Ta na tsaye ta ga wata mata da niqab ta tsaya a gefen ta,mamakin qirar matar take, saboda tafi kama da namiji ko kuma mata maza, bata gama mamaki ba ta ga matar ta saka hannu a jakar ta da ta rataya, dan juyar da kai ta yi sabida yanda ta qura ma matar ido sai ta ga bai dace ba. Juyawar nan da za tai kuwa matar ta fesa mata wani turare, nan da nan kuwa hankalin ta ya gushe daga jikin ta, a hannun matar ta fadi, mota ta tsaya a gaban su, suka danna Aaseeyah ciki suka cilla motar saman kwalta. Masu bawa Aaseeyah tsaro na ganin abinda ya faru suka sanar da Aliyyu, sannan ya basu umarni suka rufa masu baya. Gudu suke sosai a cikin gari,motoci na basu hanya,wasu na zagin tuqin gangancin da suke a cikin gari,sun tsorata matuqa, sai bawa juna laifi suke,ganin motar 'yan sanda har biyu na biye da su, basu taba zaton 'yan sandan na ganin su ba, cike da tsoro da tashin hankali suke zuba gudu a saman titin, cikin rashin nasara suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, gudu suke sai tada qura suke, mutanen unguwar kuwa sai darewa suke suna ba motar hanya, wata yar qaramar yarinya ce ta ke kuka ta gigice sakamakon ihu da qarar abun hawan da ya iske su tun kan motar ta qarasa, mai tuqa motar ne ya ce, "Oga ga yarinya nan a gaban mu fa," Cikin tsawa wanda aka kira da ogan ya ce, "Bi ta kan ta mana, uban me za ka jira," Kamar zai bi takan yarinyar, amma ya ji ba zai iya bi ba, wani irin burki ya taka, sai da suka buga kawunan su a jikin motar, yarinyar kuwa faduwa ta yi a wajen tare da tsanyara sabon kuka na jin tsoro, a guje mahaifiyar ta ta je ta dauke ta suka bar wajen,qoqarin sake tada motar yake, 'yan sanda suka zagaye su da bindigogi. A take a wajen aka tattare su sai ofishin 'yan sanda. Aaseeyah kuwa gida Aliyyu ya sa aka maida ta, suka shiga bincike. Duk wata wahala matasan nan sun shata amma sun qi fadin wanda ya sa su sace Aaseeyah. Abu daya suke maimaitawa shi ne "Ba wanda ya aike mu, kawai gari ne ba kudi shi ne muka gan ta a tsaye muka sace ta" Bangaren su Hon. Mamman Accu kuwa hankalin shi in ya yi dubu ya tashi,yanzu ta ya zai tunkari Sanata Kabiru da wannan zancen? Ba shi da zabin da ya wuce ya sanar da su kuwa, haduwar gaggawa yakira, cikin abinda bai fi awa daya da rabi ba suka hallara a gidan shi. Ya na gama labarta musu mummunan labarin Eliza ta miqe, tare da maida gashin ta da ya sha qari bayan kunnen ta ta dau wayoyin ta za ta fita,ASP shalele kuwa zufa ce ke yanko masa ta ko ina, jikin shi rawa ya ke ya na fadin, "Shi kenan tawa ta qare, mutuwar su Garzali ba abinda ta janyo mana sai asara da tonuwar asiri, wannan yarinya Hasiya Allah ya tsine mata albarka, tunda lamarin mu ya gauraya da nata muke ganin tijara da tashin hankali kala kala,....ke kuma ina zaki? Ko baki ji tashin hankalin da ya same mu bane?" "Ya same ku dai, da zaku hada wannan plan din wani ya yi shawara da ni? Ku manya masu hankali ko? Kun fi ni hangen nesa,to ai ga aikin gaggawa nan me ya jawo muku, so long friends, ni na yi nan" Qarar takalman ta ne kawai ke tashi, yau dik cikin su ba wanda ya damu da wani kallon tafiyar ta, damuwa da tashin hankalin da suke ciki ya ishe su. "Ku kwantar da hankalin ku, ni da kai na zan yi magana da IG of police din,yau yau dinnan za a sake su," "Ya kamata ka samu ganin shi a yau yau dinnan" "Zuwa Abuja ya kama ni yanzu yanzun nan" "Amma Sanata ka na ganin wannan yaron Aliyyu zai bar maganar nan kuwa? Dama fa da haushin mu a wajen shi, neman mu suke ruwa a jallo, in suka samu labarin mu muka aika yaran nan zai iya komai dan ganin bayan mu" "Ahafff ai shi ma ya na da na gaba da shi, duk maitar shi da son kama mu umarni kawai za a bashi daga sama zai janye komai," "Sanata ka manta me ya faru ne? Nan nan ka sa a kai shi Abuja ya bar kano mu sakata mu wala yaron nan ya qi,sai da ya bi duk wata hanya da za ta hana a kai shi Abuja, ka na ganin zai saki wannan lamarin ya wuce cikin sauqi kuwa?" "Da wannan surutu da tattaunawar da kuke a gaggauta a dau mata ki mana, ni fa hankali na ba a kwance yake ba, gani na ke any minute yaran nan da sun ji wahala za su bayyana mu" "Gaskiya ne Shalele, Alh. Munkaila ka sa ido a kan waccan yarinyar, dan da alama ta san me ta taka, hankalin ta a kwance ya ke ba wata damuwa da ta nuna" "Ba komi zan kula da Eliza" A ranar Sanata Kabiru ya tafi Abuja dan ganawa da IG, tun kan ya isa ya ke waya dan samun izinin ganin shi amma abun ya ci tura, ji yake kamar ya tsala ihu, nan take ya fara danasanin harkar da suke,ya na da hanyoyin samun kudi kala kala, amma ya tsayawa fashi da makami, da girman shi yanzu a ji ya na da hannu a taimkawa manyan masu fashi da makami na qasa ai mutuncin shi da qimar shi sun zube a cikin al'umma. Har ya isa Abuja bai samu izinin ganin IG ba. **************************** Aliyyu kusan a wajen ya kwana, kwararru masu bincike aka samar, kuma Alhamdu lilLAAHi sun yi aikin su, dan kuwa sun bayyana ta.hannun wanda suka samu aikin sace Aaseeyah, wato yaran Hon. Mamman Accu da suka samu guduwa daga prison. Nan da nan kuwa aka bazama neman su, wajejen da suka sanar ana iya samun su anje duk ba a gan su ba. Abu fa ya yi tsanani, ga 'yan jarida sun matsa suna ta son daukan rahoto, Aliyyu ya gargadi duk wasu 'yan jarida kar su kuskura su yada wani magana da ta danganci wannan case din lokaci na zuwa da za su bada izinin sakin labaran a ko ina suke so. Washegarin ranar ya yi ta kiran Eliza dan ya dan yi magana da ita ko zai ji sauqin gajiyar da yake ji a tattare da shi, amma ya kasa samun ta a waya. Eliza kuwa na can mafakar ta a wani qauye,ta kashe wayoyin ta da duk wani abu da zai sa a gano ta. Gida ya nufa domin ya yi wanka ya ci abinci,in so samu ne ma ya huta kafin a koma bakin aiki. Ya na tsaka da cin abinci ya ga wayar IG, cike da girmamawa ya amsa, tare da bashi girma irin nasu na masu uniform. Umarni IG ya bashi na son tsananta bincike akan case din da suke yi a yanzu, mamaki ne ya kama Aliyyu ta yanda akai IG ya san maganar. "Aliyyu na san za ka yi mamakin jin na san abinda ke faruwa, duk da ba ku sanar da mu ba, akwai wasu hatsabiban mutane a cikin qasar nan da ke neman lalata matasan cikin ta,tahanyar amfani da su wajen fashi da makami, ko kuma harkokin siyasar su, ba jimawa Sanata Kabiru ya kawon qorafi akan su na so na san yanda nai aka maido ka Abuja ka bar kano, sannan ya na so na baka umarni akan cewar na sa ka saki yaran da aka kama, to Aliyyu ina so ku sake yaran, mu yi amfani da kwarewar mu, wajen samun shaida akan su, domin gurfanar da su ga shari'a, na yi alqawarin tsayawa akan gaskiya, domin kawar da azzaluman mutanen nan, da ke hana talakawa zaman lafiya a qasar su" Godiya sosai Aliyyu ya dinga zubawa dan samun goyon bayan shugaban shi. Mama ya roqa da ta mishi addu'a da sanya mishi albarka dan samun nasarar wannan case din, addu'a kuwa t ding kwarara masa, tare da tura masa abincin dan bata son ya fita ba tare da ya ci ya qoshi ba (uwa kenan). Da yamma ya samu komawa wajen masu laifin, cikin kwarewar aiki, ya ce a sake su, da alama gaskiya suka fada ba wanda ya sa su, talauci ne ya sanya su sace ta, dan haka ba abinda ya kamata ayi da ya fi a sake su, tare da ja musu kunnen kar su qara hakan. Wasu daga cikin 'yan sandan sun so su nuna masa cewar qarya suke, amma ya nuna a rabu da su, a aje su kawai har 'yan uwan su su zo su yi belin su. A cikin satin Hon. Ya tura wasu yaran shi suka yi belin su. Party suka had'a na murnar dawowar su, da kuma gayyatar Eliza domin bata hakuri akan nuna mata rashin mahimmancin ta da suka yi, sun yi iya yanda za su yi dan su same ta a gidan ta da wayoyin ta ba su samu ba. Ta je shago siyen bread da safe a cikin qauyen ta tadda mai shagon na sauraron maimaicin shirin inda ranka, a gidan redion ta ke jin labarin sakin yaran da AIG Aliyyu ya sa a yi tare da yi ma matasa gargadi su kiyayi harkar garkuwa da mutane. Jin hakan ya sanyaya zuciyar Eliza, duk da dai ta na ji a jikin ta akwai wani mummunan abu da ke tunkarar rayuwar ta. Cikin gari ta dawo da dare, direct gidan Alh. Munkaila ta dira, ta samu baya nan, waya ta mishi, ya sanar da ita dama neman ta suke dan su bata hakuri, nuna mashi ta yi ba komai,ba sai ta je ba, a gajiye take, sun hadu washegari........... Nima dai na gaji bari na bari mu hadu washegarin inshaa Allah, mu ji Aarceen Mammee ta farfado ko kuwa???? TAUBASHI PGE 45 Aaseeyah bata farfado ba sai cikin dare, bude ido ta fara yi a hankali, ta na kallon d'akin nata, a kwance take amma ji take kan ta na juyawa kad'an kad'an, yunqurin tashi ta yi, ta ji wani zafi a kan ta, da sauri ta dafe kan nata tare da fad'in, "Washhhh Allah na, wayyoo kaina" Gefen ta ta duba inda ta ke jin saukar numfashi a hankali, Mahboob ne zaune a qasan gadon ta, ya dora kan shi a jikin gadon ya na bacci,zai wahala bai tashi da ciwon wuya ba a yanayin yanda ya kwanta din, komawa ta yi ta kwanta, ta na tuna me ya faru. A hankali komai ya dinga dawo mata, da sauri ta sake miqewa, "Su waye ke qoqarin sace ni to? Ya akai na dawo gida? Me ya faru?" Mahboob ne ya bude idon shi da suka yi jawur,ya kalle ta, ganin ta a zaune cikin fuskar rudani ne ya sanya shi tashi da sauri, ya kama kafadun ta, "Alhamdu lilLAAH laqad ustaiqazatu, sannu, wani waje na miki ciwo ne? Ko za ki sha ruwa? Abinci za ki ci na kawo miki?" Sauka ya ke qoqarin yi dan kawo mata abinci da ruwa ta riqe hannun shi, idanun ta da kwalla labbanta na rawa alamun son yin kuka, ta dan tura bakin ta gaba irin na shagwabar nan sannan ta ce, "Yah Mahboob ka yafe min dik abinda na maka? Na maka alqawari ba zan sake duk wani rashin ji ba, i promise to be a good gurl daga yanzun nan ma ba sai gobe ba, ba zan sake fad'a da kowa ba, ba zan sake ma kowa rashin kunya ba, na daina tsokana, ba zan sake fad'a da Ummee ba, ba zaka sake ganin bera ba a rayuwar ka indai har ni zan saka maka shi, Yah Mahboob da ace ban dawo ba fa? Wataqila kashe ni....." Da kuka ta qarasa maganar ta, "Shiiiiii, it's ok,kar ki sake damun kan ki, na yafe maki, and ana sa'eedun jiddan al'an da kk yi alqawarin daina duk wani rashin ji" (I am very happy now) Ya qarasa cikin murmushi tare da goge mata hawayen ta,rungume ta ya yi a gefen jikin shi, ta lumshe ido, ba ta fatan abinda zai raba su, ji take kamar su dawwama a hakan, sake sanya hannun ta tayi ta bayan shi ta rungume shi, murmushi mai sauti ya saki, ya qara rungume ta, kallon saman fuskar ta yake, ya na kallon yanda gashin idon ta ya kwanta,hancin ta madaidaici mai kyau ya tafi saitin labban ta masu dan tudu,da alama ta sake turo su gaba ne saboda shagwaba da ta yi wa Aaseeyah yawa, murmushi mai sauti ya sake yi, wanda ya sanya ta daga idanun ta ta kalle shi,itan ma murmushin ta saki, ta maida laben ta na qasa cikin bakin ta, cike da kunya ta sake shi ta juya baya. "Me ya sa za ki saki mijin ki ki juya masa baya?" "To ba kai bane komai na yi sai ka nuna min, da ka yi shiru ba shikenan ba, ga jikin ka nan na fasa rungumar" Dariya ya yi sosai sannan ya rankwafar da kan shi saitin kunnen ta, iskar bakin shi na dukan kunnen ta sannan ya ce, "Anya Aaseeyahn Mammee za ta iya cika alqawarin daina rashin kunya kuwa?" Da sauri ta juya, fuskokin su na daf da na juna ta ce, "Zan iya mana, ai kai din ne" Kallon da ya ke bin fuskar ta ne da shi, ya sanya fuskar ta ta daukan wani irin dumi,cikin sauri ta ce, "Yahmahboobyunwanakejizanciabincidaruwa" (Yah Mahboob yunwa nake ji,zan ci abinci da ruwa)" Direwa ta yi ta tsaya kyam da qafafun ta, jikin ta na dan shaking kadan, kusancin nasu ya yi yawa, ya sanya ta shiga yanayin da bata taba shiga ba, "Matsoraciya,zauna ki jira ni" "To" Fita ya yi ya je kitchen, Mammee da dama idon ta biyu ta na jiran ta ji ko Aaseeyah ta farfado, ta na jin motsi a kitchen ta bude qofar su ta fita, Mahboob ta gani ya na diban abincin da dama dan ita aka ajiye shi,taya shi ta shi suka hada komai, ya na bata labarin tashin Aaseeyahn. A tare suka shiga ta na ganin Mammee ta miqe ta je ta rungume ta,ta kai minti uku a jikin Mammeen daga baya Mammee ta janye ta, "Aaseeyah zauna ki ci abinci" "Mammee ba na son barin jikin ki,sau biyu kenan ina shiga mugun hannu, Mammee ki yafe min ban sani ba watarana in aka sace ni zan dawo ko kuma na tafi kenan" "Kar ki sake fadan haka, inshaa Allahu ba abinda zai sake samun ki da izinin Allah,Allah ya muku albarka, ya kare mana ku daga dikkan sharri" Sallamar Abee ce ta sa su maida hankali qofar,zuwa ya yi ya dafa kan Aaseeyah cikin murmushin yaqe, "Aaseeyah ina mai baki hakuri akan rashin kulawa ta a gare ki, zan iya kiran wannan a matsayin laifi na, da na kula dake, na sama maki mai kai ki da dakko ki da haka bata faru ba, tunda shi ma ya na da nashi aiki, ba lallai ace sanda kk gama lectures shi ya gama aikin shi ba, inshaa Allahu zan sama maki driver na ki ke kadai" "Ah ah Abee, ni dai gaskiya ba wanda zai n tuqamin mata, ina nn da raina da lafiya ta zan na aje dik abinda nake yi na kai ta na dakko ta, har Allah ya sa ta gama" Murmushi suka yi, Aaseeyah kuwa ta sunkuyar da kai, ita a dole ta ji kunya. "To maza taho ki ci abinci," "Bari na wanke baki na," Bayi ta shiga, kafin ta fito iyayen nata sun tafi, Mahboob ma bayin ta ya shiga ya wanke hannayen shi da bakin shi, a tare suk ci abincin, su na hirar su. Bayan ya gama ci ya ce ta kwanta ta huta shi zai je dakin su Hussein na da ya kwanta, "Ai ni ba zan iya komawa bacci b yanzu,karatu zan dan taba wataqila ya deben kewar shirun da zan yi" "Ok amma kar ki jima baki koma bacci ba" "Ni da na shaqi na bacci ko ka mnt ne, tun la'asar nake bacci gashi yanzu kusan biyu na dare" "Haka ne kin sha bacci ba laifi, sai da safe Mar'atee," "Sai da safe Zaujee" Kallon ta ya tsaya ya na yi na wasu mintuna sannan ya fita. Lumshe ido ta yi ta na hango kwayar idon shi a nata wadda ke cike da dimbin soyayyar ta a cikin su. "Allah ka dawwamar ma na da zaman lfy, Ameen" Littattafan ta ta bude ta fara dubawa, a haka bacci mai dad'i ya dauke ta. Da safe kuwa Ummee ta sha mamakin yanda Aaseeyah ke gaishe ta cike da ladabi da girmamawa, a ranta dariya ta yi ta ce, 'Shegiyar yarinya ta jiyo qamshin mutuwa shi ya sa yanzu ta rusuna kafin ta balle da iya shegen nata' Hassan da Hussein su yesmeen har ma Ummu Suleim sun samu zuwa ganin ta,gida ya cika gwanin sha'awa, Ummu Suleim ma na dauke da ciki, amma ko da hira bata taba sanar da kowa ba, sai ranar suka gani. Umaimah na ta taya su murna, a ranta ta na fatan itama watarana ta samu nata. ************************ Bincike ya yi tsanani, ta yanda Aliyyu ba shi da lokacin kan shi ballantana ya samu zuwa wajen budurwar shi Saratu,da dama ta waya suke yin hira,har suka dan samu shaquwa da kusanci,yanzu ta daina jin haushin shi sosai ta fara sakewa da shi,nisan da ke tsakanin su na damun shi,ya na son ganin ta kwarai, duk yanda suke zaton samun sauqin lamarin abun ba haka bane, duk wata hanya da zata yi linking din su C boy da ogannin su sun toshe hanyar. Su kan su ganin su na neman yi wa jami'an tsaron wahala. Wannan rashin lokaci na Aliyyu ne ya sanya ya dakatar da zuwan iyayen shi neman auren Saratu, ya na son komai ya daidaita kafin ya aure ta,mahaifin shi da Alh. Munkaila ne kawai suka samu ganawa. Watarana Aliyyu ya samu kammala abubuwan da ya ke da misalin qarfe sha biyu na dare,sai ya ji ya na son ya ga Saratun shi, in ma ba zai gan ta ba ko qofar gidan su ne ya je ya tsaya wataqila hakan zai sanyaya ran shi. Da kan shi ya ke tuqi,har gidan su Elizabeth, wato Saratu a wajen shi,nesa kadan da gidan Alh. Munkaila ya kashe motar shi, ya danna lambobin wayar ta, 'Anya za a same ta ido biyu ma yanzu kuwa? Let me try calling her,i missed her so much' Kamar da wasa kuwa ya na kira ta d'aga, gaisawa sukai, cikin mayaudariyar shagwaba ta ke magana, "Assalamu alaikum dear, ki na lafiya? Ina fatan ban tashe ki bacci ba ko?" "Haba yallabai na kawai sai ka manta da ni? Haka za a yi auren ba na samun kulawar ka? Ba ka da lokaci na sai na aikin ka" Zai yi magana kenan ya ga gate din gidan su na budewa, daga can nesa ya hango ta ta na daga ma wata mota da ke son barin gidan hannu, alamar na cikin motar ya/ta je kawai,wasu matsiyatan kaya ne a jikin ta gashin nan sake a bayan ta, sake leqawa da kan shi ya yi sosai, ya na kallon matar da ke shiga cikin gidan, anya Sarah ce ya gani kuwa. Bai gama mamaki ba ya ga motar da ta fita daga gidan ta gilma ta gaban shi, biyu daga matasan da suke nema ruwa a jallo ya gani,saurin katse kiran ya yi ya dauki no motar a hoto. Mamaki ne cike da zuciyar shi. "Samarin ta ne ko 'yan uwan ta?meye alaqar su?" Kishi ne ya fara kama shi, wayar shi ya ga ta na haske, Eliza na kiran shi, ya na dagawa sai ta ji muryar shi ba karsashin da ta fara ji da farko. "Hello ka na lfy kuwa?" "Lafiya qalou, matsalar network ne, ba na jin ki shi ne na kashe....ki na ina yanzu?" "Ni na yi tafiya, na je gidan kakata,har yanzu gani take kamar qarya nake da na ce na samu mijin aure, tunda ka qi zuwa gaishe ta" 'Qarya' "Ok,yaushe za ki dawo? Na matsu na gan ki, n yi kewar ki sosai" "Bawani kewata da kai, da ka yi kewa ta da ka zo gare ni, amma is like aikin ka ka sa a farko ka ajiye ni a ta uku, dan aikin ka shine farko da na biyu a rayuwar ka na kula" "Ba zaki gane ba Sarah, aiki na ba qaramin aiki bane, na sadaukar da rayuwa ta da komai nawa ma qasa ta, dan haka ban samu lokacin kaina ba, amma yanzu na maki alqawarin tsayar da komai domin ki, ina ganin rufe case din ma da ke gaba na zanyi, yanzu wata kusan hudu amma ba wani ci gaba" Tsallen murna ta yi, sannan ta ce, "Yauwaaa nawa ni kadai,da kuwa ka faranta raina,yaushe za ka zo to?" "Gobe in na je office na kammala komai game da case din,..har yanzu mun kasa samun shaidun da za su yi linking din mu da mutanen da muke nema, gashi kullum fashi da makamin nan ake yi, ana ta kashe bayin Allah, amma dole mu hakura,ni ma ina son inganta rayuwa ta" "Da kyau yallabai na, gaskiya in ka rufe case din nan kuwa za ka samu kwanciyar hankali, gajiyar da kullum ke dawainiya da kai zata ragu, ka ga ko ba komai mun samu lokacin kan mu," "Haka ne, me kike baki bacci ba?" "Ina shan iska ne a balcony,garin ya yi zafi yau" Kamar an ce ya daga kai kuwa ya hango ta, hannun ta riqe da sigari, ta na sanye da wata riga kalar orange me hannun shimi,iyakar ta cinyoyin ta, gaban shi ne ya yanke ya fadi, dama Sarah na shan tava? "Ohhh i see, ki ce min na shirya diyar manyan masu kudi zan aura,anya kuwa account di na na da nauyi? Gidan kakar ku ma irin na 'yan gayu ne ashe har da balcony" A dan firgice ta miqe daga jikin qarfen da ta jingina, ta kashe sigarin tare da fesar da ta vakin ta, "Nooo ka san yanayin wajen nasu dole sai an mata irin wadannan abubuwan ....ummm saboda...umm" "Ok ba komai, bari na barki ki sha iska, zan kwanta, sai da safe," "Bye i love u" Ji ya yi ya kasa maida mata martanin kalmar soyayya da ta ambata, kashe wayar ya yi, ya na hango ta sanda ta daki goshin ta da tafin hannun ta,ya tabbata da ya barta ta ci gaba da qarya ba zata bulle ba, amma ba zai barta ta rasa abun fada ba, zai qarasa mata duk wani labari da ta fara. Ranar Aliyyu bai samu rintsawa ba,hutun da ya so ya samu bai yi gigin tunkarar shi ba balle ya same shi, tunani ne fal zuciyar shi, shin wace ce Saratu? Mahboob ya san ta kuwa da kyau? Me Mahboob ya sani game da Saratu? Mahboob kuwa anya ba abin zargi bane shima???? Wannan tambayoyin bani da amsar su Dan sanda a yau, wataqila sai anjima ko gobe, comments din ku shine zai qaran appetite na rubutu😂 TAUBASHI PAGE 46 Aliyyu ya riqewa zuwa zance wuta,ba dare ba rana duk sanda ya ga ya dace ya je dan samun kwakkwarar shaida akan zargin da ya ke kawai zai tafi. Ganin haka da Alh. Munkaila ya yi ne ya sanya suka daina haduwa a gidan shi,lokuta da dama in ya zo ba ya samun ta sai dai ya jira ta, ta bi ta qofar baya ta shige gidan, ta sauya kaya sannan ta koma ta fita ta shiga ta gate, ya sha tambayar

Chapter 29 of 41