nan kana karada unguwa, sai yunwa ta kora ka ka je gida, ba za a zauna uwale da ubale su amfana da haihuwa ba, sai dai mutan unguwa su bada taro da sisi su mora, zo to na saka aiki, ga dari biyar"
Ya na jin kudi ya manta da baqar maganar da ta watsa masa,
"Aikin me zan miki, bur.....ub.... yau akwai cin soyayyar indomie yasin"
"Bera zaka samo min manya guda uku, kai ko daya aka samu ka kawon, in ka kwo ka kwankwasa ka ce ma mai gadi waje na kazo"
"To an gama, dakin babar mu ai nan ne dandalin su,yanzu kuwa ko biyat kk so an gama"
Kusan warce kudin ya yi, ya sa kai, sai gidan su.
Ya na zuwa gida kuwa ya samu ramin berayen su ya saka musu hayaqin barkono, ya riqe buhu, nan fa da hayaqi ya ishe su suka dinga fitowa a guje, sai da ya ji sun shiga da dan yawa, ya damqe vakin buhun shi, ya fita ya kashe su ya nufi gidan su Aaseeyah, an kusan sallame sallar magrib ya kai mata.
Godiya ta yi ta nufi bangaren Mahboob, ba wanda ya gan ta ta shige ta aje masa berayen nan a daki, bandaki da parlour,ta fice.
"Ni za a wa iskanci, duk wanda ya batan rai yasin sai nashi ya baci,"
Sallar ta ta je ta yi, ta na azkar ya dawo, bata fita ba da ta gama ma sai ta dau littafan ta na boko ta hau dubawa,dan ta san kan ta baya ja sosai, sai ta na bita.
Ya jima zaune bai gan ta ba, ba kunya ya ce ma Mammee, bari ya duba Aaseeyah,ta ce ya duba dakin ta,ita ma tin kan Magrib rabon ta da su hadu.
Ko da ya shiga ya gan ta ta kafe littafin ta da ido ta na karatu, kamar ba abinda ke damun ta, nan kuwa ta na karatun ne zuciyar ta na gare shi, su na hada ido ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ya yi, tare da cewa,
"Aaseeyahn Mammee case kenan,da dikkan alamu kin yi kewa ta, amma na kira ya fi ba iyaka kin qi dagawa, wai dan Allah me ne ne matsalar ki ne? Ina son sani, ko me ne ne na maki alqawari zan gyara, ko kuma kin daina so na ne?"
Da sauri ta kalle shi, sai kuma ta turo baki, ta maida kan ta gefe, ta na motsa labban ta,ita kan ta bata san me take fada ba,gane hakan ne ya sa Mahboob zama a kan gadon nata daf da ita, sannan ya ja ta jikin shi ya kwantar da ita duk da qoqarin guduwar da tai ta yi,qarshe dole ta hakura, ta na kwance saman qirjin shi ta n jin bugun zuciyar shi, ya sauke ajiyar zuciya mai qarfi sannan ya ce,
"Aaseeyah ba ki tambaye ni ya muka yi da Sarah ba yau?"
Ta sakankance ta na jin vibration din muryar shi ta ji ya na maganar Saratu, wani tuquqin baqin ciki ne ya kama zuciyar ta, ta miqe daga jikin shi ta koma gefe,idanun ta sun kada sun yi jawur, bata ce komai ba, baya jin zata fada din, dan haka ya ce,
"Na san zaki ta tambayar kan ki wace ce Saratu a waje na? Meye matsayin ta? To yau zan sanar da ke wace ce saratu, Saratu dai wata baiwar Allah ce mai tsananin tsoron Allah, da taimakon talakawa, amma damuwa ta ma rayuwar ta yawa, haduwar mu da ita ne ya sanya ni daukan alqawarin sai na kawar mata da damuwar da take cikin rayuwar ta...."
"Sannu dan agajin hisba,wato kai rayuwar ka ta taimakon mata ce ko?"
"Aaseeyah kenan, ki bari mana na gama baki labari in ya so kin katse ni,"
Hararar shi ta yi, sannan ta goge hawayen da ke mata zarya a kunci, haushin shi take ji kamar ta samu kulki tai ta rotsa masa ta yi jinyar shi daga baya.
"To cikin ikon Allah sai abun ya zo mana a daidai, domin kuwa Aliyyu ma na buqatar irin taimakon da Sarah ke buqata, dan haka a yau Allah ya bani iko na hada aikin alkhairi,n kai Aliyyu wajen Sarah, sun daidaita, kuma sun aminta da juna, za su auri juna"
Sakatooo Aaseeyah ta yi da baki,
"Dama ba budurwar ka ba ce?"
Hade gira ya dan yi cikin mamaki, tare da kallon ta da kyau, sai a sannan komai ya ding dawo masa a kwanyar shi, Aaseeyah dama kishi ne ya sanya ta take ta mishi fushi? Wani dad'i ne ya kama shi, zuciyar shi wasai, ya tabbta dari bisa dari ta na son shi.
Da rarrafe ya isa gaban ta cike da murna, ya daga ta zuwa qirjin shi ya rungume ta tsam tsam, itan ma for the first time rungume shi ta yi ta na dariya, zuciyar ta wasai,ba abinda ke damun ta.
"Aaseeyah ashe ki na so na haka, ashe dik fushin da kk saboda ki na zargin ina neman wata ne,Aaseeyah ina son ki nima, ina qaunar ki,Aaseeyah ban ma san iyakar abinda na ke ji game da ke ba,ke kadai ce macen da na mallakawa zuciya ta da ruhi na, ba wata bayan ke a raina,kuma bana jin akwai wadda zata zo ta fiki a raina"
Kalaman shi sun sanya ta kuka sosai, a hankali jikin ta ke girgiza saboda kukan da take a jikin shi, qara rungume shi ta yi, ta na fadin,
"Ina son ka nima Yah Mahboob dina, ina son ka, ka yafe min dik abinda na maka, ba zan iya bude ido na gan ka da wata ba, zuciya ta ji nake kamar ana hura wuta a cikin ta, abinda nake ji ba shi da misali,dan Allah kar ka ci amana ta, komai za ka aikata ko dan gaba ka dinga sanar da ni, kai ko da aure za ka qara, ka na fada min me ke faruwa, ta yanda ba zan yi zargin komai akan ka ba"
"Inshaa Allahu zan kiyaye, ki yi hakuri ban kyauta ba da ban sanar da ke komai ba tunanin sanar dake din bai zo min ba"
Daga kai ta yi, alamar ta hakura, murmushi suka fara yi, ta zame jikin ta a nashi ta zauna, shima zama ya yi, ya dauki littafin ta ya na dubawa, nan ya ga yanda karatun nasu yake, ta zauna ta na masa bayani, sai ta ji ma da ta na bayanin tafi fahimta,
"Kaga da ina maka bayanin abubuwan nan, sai na ji na fi ganewa"
"To kuwa daga yau zamu dinga samun lokaci ki na koyar dani nima, dan ba ke kadai ba ce ke koya, nima ina ganewa"
Haka dai suka yi karatun su,tare da soyayyar su, har tara na dare, Mahboob bai yi sallar isha'i ba, sallama ya mata ya ce zai je ya yi wanka ya yi sallah, ya huta.
Aaseeyah na ta doka murmushi, ta qanqame hannayen ta a qirjin ta, kan ta na jingine da allon gadon ta, idanun ta lumshe, duk wanda ya kalle ta a wannan yanayi shi ma sai ya murmusa kafin ya tambayi dalilin kasancewar ta cikin nisha'd'i.
Kamar wadda aka mintsina ta bude ido, tare da wara su sosai, a guje ta miqe ta fice daga dakin ta, ihu da kururuwa ta jiyo a tsakar gida na Mahboob, Ummee kan ta ba ko dankwali zani a hannu ta fito a guje a gigice,
"Su waye? Barayi ne suka shigo da farkon daren nan? Mahboob lafiya?"
Dikkan wata tsoka ta jikin shi rawa take, cike da tashin hankali ya ke kiran,
"Bera,Bera" yau ba larabcin.
Aaseeyah da ta qaraso ta ga an tattaru a tsakar gida, har Abbu, sai ta yi qoqarin zamewa ta koma ciki, Mammee da Abee ne a tsaye a bayan ta, kallo suka bi ta da shi, dan in ba su manta ba zuwan shi na farko ita ta saka masa bera, lokacin ma ba wanda ya san ya na tsoron bera sai ita kadai.
Dariyar yaqe ta yi, har cikin ran ta a tsorace take, dan Mammee dama ta mata warning, kallon hanyar bangaren su Umaimah ta yi ta keta da gudu,Mammee na kwala mata kira ko waige batai ba,murda qofar ta yi ta ji ta a rufe, da alama sun ma kwanta ba su san me ake ciki ba, da sauri ta nufi wajen Mahboob din, ta shige ta kulle qofa, Abee na dariya ya dafa kafadar Mahboob ya ce,
"A ido dai ga ka ingarman namiji,amma a zuciya sam baka da wani katabus,mace ta juya ka, bera ya razana ka, Allah ya kyauta, to yanzu ina ka yi? Wajen mu zaka ko kuma ina?"
Ummee ce tai zirif ta ce,
"Ai wannan 'yar vanzar yarinyar ba zata bar mu mu huta ba sai sanda ta haihu, sannan ta yi hankali wataqil, kai Mahboob ka je dakin Noor ka kwana,gobe zan shiga ni da Umaimah a fidda kayan dakin dika,a gyare in ma akwai beran dik a fitar"
A tsorace ya bi bayan su, Abee na ta dariya, Mammee kuwa takaicin Aaseeyah duk ya dami zuciyar ta, she is not getting any younger,amma rashin ji ba abinda ya ragu a tare da ita, dole ta dau mataki akan Aaseeyah, lokacin yarinta ya wuce a wajen ta.
Aaseeyah kuwa na can ta tattare berayen dika ta saka a leda ta daure ta bude window ta bayan dakin ta wurga su, da niyyar gobe ta zubar dika.
Leqawa ta yi ta ga ba kowa a tsakar gidan, sanda ta yi ta fita, ta je qofar su ta murda knob din, ta ji shi a kulle, tura baki ta yi, wato da batai dabarar fidda berayen ba nufin Mammee ta kwana a can da su ko? Ai dai ta tabbata Abeen ta ba zai ce a barta ta kwana a can ba, gashi tsoro take ji,ko giyar wake ta sha ba ta je wajen Ummee ba, ba abinda za su tsaya yi sai cacar baki.
Bangaren su Umaimah ta je ta dinga bugawa, cikin bacci Noor ya ji ana bugawa.
Noor ne ya sanya jallabiyya ya fita, Aaseeyah ya gani, cikin mamaki ya tambaye ta lfy?
"Yah Noor dan Allah zan kwana wajen ku"
"Lafiya dai ko? "
"Lafiya qlou,"
Bata hanya ya yi ta wuce ciki, dayan dakin ya nuna mata ta masa godiya ta shige,sukai sai da safe, mamakin me ya kawo ta da dare haka yake, Umaimah na can na bacci bata san meke faruwa ba.
Washegari.........
TAUBASHI
PAGE 43
Umaimah ce ke tsaye a kitchen ta na girki ta na sheqa dariya har da hawaye, sakamakon labarin da Aaseeyah ta gama basu,Aaseeyah kuwa duk fuskar ta ba wata walwala,da alama bata samu bacci mai kyau ba, Noor sai murmushi ya ke,ganin yanda Aaseeyah ke cike da damuwa,for the first time ta yi abinda take danasani akai.
"Umaimah wannan ba abin dariya bane, da ace laifin da ya min gaskiya ne, abinda ya fi bera ma inna saka mishi haka ta faru ko kwarzane ba zan damu ba, amma yanzu da wanne ido zan kalle shi ya gama zaman shi a daki na ya fita ban sanar da shi ba,a dayan bangaren Mammee jira na take yanzu na san ta ci qaniya ta,"
Wata dariyar Umaimah ta kwashe da ita har ta na kada kai,
"Banni haka Aaseeyah, dariyar ta min yawa,dan Allah gobe ma in halin ki ne rashin ji ki qara, kar ki fasa, d'an bawan Allah yayana, ya na can ya na taimakon al'umma su yi aure ki na nan ki na hada masa shege"
"Ai aikin agajin shi ne ya jawo masa, da bai shiga aikin agajin hadin aure ba ai da haka dik be faru ba"
Noor ne ya fashe da dariya,
"Wai aikin agaji,Aaseeyah Allah ya shirya mana ke....to sweetheart ni zan fita"
"Allah ya kiyaye ya bada sa'a, Allah ya tsare, Allah ya dawon da kai lfy"
"Ameeen,Allah ya kare min ke ya kulamin da ke har sai na dawo,"
"Ameee,"
Cike da sha'awar yanda suke bawa junan su kulawa Aaseeyah ke kallon su, ta shagala sosai ta ji Noor ya ce,
"Bangane kin koma gefe ba, haka zan tafi ba wani dan rakiya, ba wani komai?"
Aaseeyah na tsaye ta na jiran ta ga Umaimah ta takawa Noor zuwa bakin qofa kawai ta ga Noor ya ja Umaimah ya hade fuskar su waje daya, qara ta saka ta rufe idon ta,tare da juya baya, ta na fadin,
"Wayyooo Mammee, da na sani ban zo gidan ku kwana ba, Allah na tuba ni dai ba leqen su nai ba su suke yi a gabana"
Noor bai kula ta ba sai da ya yi kissing matar shi son ran shi sannan ya ce,
"Kin ji da shi, ku Allah kadai ya san me za ku yi in aka baku waje; idon Yah Mahboob a tsaye yake kuma a soye"
Umaimah ce ta wurga masa harara sannan ta kai masa dukan wasa, da gudu gudu ya bar gidan ya na dariya,
"Za ka dawo ne ka min bayanin soyewar idon yayana"
"Ohhh i would love to sweetheart,kin san ina son yin bayani dalla dalla, kar ki damu bye, love u"
Gaba dayan su Murmushi ne kwance a saman fuskar su, musaman Umaimah da ke jin rayuwar ta ta gama cika da farin ciki, a baya tayi zaton asirin ta ba shi kadai ne zai tonu ba har Noor ma ba zata same shi ba, sai gashi ta samu wanda zuciyar ta ta girma da son shi, kuma ta samu shiriya daga wajen Allah.
(Kar ki ga rayuwar Umaimah ta kyautatu, ke kuma ki sake ma cousin din ki jiki, ya yi yanda ya so dake, wallahi wallahi ba kowa ke samun dacewa ba, in baku manta ba ita kan ta ta samu tonuwar asirin abinda suka jima suna yi, ko da wannana aka bar ki tashin hankali ne, ballantana cousins din yanzu su za su sauke sha'awar su da va a nuna masu ya za su yi maganin ta ba akan ki, kuma su guje ki, in da hali ma su sanar da wasu cewar ke yar iska ce a dangi, musamman qannen su, su kuma qannen su su yayata ki cewar ke yar iska ce, magana har ta fita waje, manema auren ki a hankali za su samu wannan labari, in ma basu samu ba an kai ki gidan miji ya same ki fanko, me zaki ce? Ki kiyayi cousins, ki kiyayi cousins ki kiyayi cousins sharrin cousins ya fi alkhairin su yawa a cikin gida)
Aaseeyah ce ta zagaye Umaimah ta dauki mug dan hada tea, juya kwayar idon ta tayi cikin salon wasa ta ce,
"Ba sai kin fada min ba, fuskar ki ta nuna halin da kk ciki, ni yau ma zan bar maku gidan ku"
Murmushin Umaimah ne ya qaru ta ce,
"Ki tafi din mana, ai kin san sauran, mu ne dai muka baki mafaka sanda kika dakko yaqin basasa akan ki"
Haka suka yi ta hira cikin nishad'i, su na tsaye suka ji motsi a qofar Mahboob, da gudu Aaseeyah ta leqa ta jikin bular key,Ummee ta hango Mahboob na bayan ta, wanda bai san me ke faruwa ba da ya kalle shi zai ga cikakken namiji, tsayanne mara tsoro, nan kuwa qasan ran shi cike ya ke da tsoron kar ana bude qofar beran ya daka tsalle ya dale shi, ya na nan tsaye hade da hannun shi a qirji Ummee ta shiga ciki, dan yin bincike ta ga akwai ko babu.
Har Aaseeyah ta juya zata koma wajen Umaimah, ta sake komawa cike da dariyar qeta, bude qofar ta yi a hankali ta sa bakin ta ta waje, tai irin yar qarar nan da beraye ke yi,wata zabura Mahboob ya saka ya fada bangaren nashi gaba daya tsabar tsoro, a wajen Aaseeyah ta zube ta na dariya.
Karo sukai da Ummee ta ce,
"Lafiya? Me ne ne? "
"Ummee aljaradh na waje, ya fita waje,na ji qarar shi"
"Ohhh ni Fatima yau ina kallon abinda ya fi qarfin lissafi na,wato yau ka tuna sunan shi da larabcin ko? Ina ce jiya mantawa kai, Mahboob ka daina wannan abun da ka ke dan Allah, ka na nan cikakken namiji mai izza meye bera fisabilillahi? Ita kuma yar banzar ta na can ta na shaqar bacci kai ta hana ka baccin azziqi, kaiii wannan yarinya Allah kawo ranar gama karatun ta ta d'aga tai gaba ko ma huta"
"Ummee ina jin ki, kuma ko na gama karatun ba inda zani anan zamu zauna kamar Yah Noor,na ga ta rabuwa da ni, in ke ba ki so na Mammee na na so na, na san ba za ta so nesa da ni ba ehe"
Nan take Mahboob ya gane ita ta yi kukan beran, daure fuska ya yi tamau.
Hannu Ummee ta daga zata make Aaseeyah ta zaci zata gudu, sai ta ga ta na bin ta da kallon tabani ki gani,maida hannun ta tayi ta hau masifa, ta na zagin Aaseeyah,
"'Yar banza kalar duka, amma ba wanda ya isa ya daka ya zauna lafiya; uwar ki Subai'a ce kawai maganin ki, to ta kasa, shi ya sa kk gagari kowa,"
"Ai kuwa in ba a godewa Mammee ba ba a kushe ta va, dan dik dangi ba mai tarbiyyar ta ehe"
"Ni ki ke fadawa magana? Wato ni banda tarbiyya ko,"
"Ba daga vaki na ta fito va"
Mahboob da ya gama zagaye parlourn da idanun shi dan tabbatarwa ko ba bera ne ya ce,
"Dan Allah ku dan zauna anan ku ci gaba da hirar bari na je n shirya"
Ummee ce ta kyabe baki ta kalli Aaseehah sheqeqe, sannan ta kalli Mahboob ta ce,
"Dawa zan hirar? Mutane sun qare agari ne? Maza je ka kai wankan ka,ina nan,tunda ta dage sai ta cutar da kai, Allah ba zai bata nasara ba"
Murguda baki Aaseeyah ta dan yi, in ba mutum.ya kula ba ba zai gane ba,
"Wannan dai tsakanin miji da mata ne, kuma ba wanda ya isa ya shiga, dan tsabar ki hada mu fada kike kiran wai ni zan cutar da shi"
Sun ci gaba da ce ce kuce din su Mahboob ya shiga a gaggauce ya shirya, ko da ya fito gani sukai kawai ya nifi hanyar waje,dan ba shi da lokacin rabon fad'a ya makara.
Da gudu Aaseeyah ta bi shi,
"Yah Mahboob ka raka ni na shiga wajen mu dan Allah, in Mammee ba ta gan mu tare ba zata min fada,ni kuma na tsani fada"
Bai ce mata komai ba har suka tsaya a bakin qofar su Aaseeyah, ya sa hannu ya kwankwasa, Ummee na ta masifa daga nesa ta n fada wa Mahboob kar ya sake ya sakar wa Aaseeyah fuska tunda ba ta da mutunci.
Mammee ce ta bude qofar sanye da mayafi a jikin ta,da doguwar riga, yawaci hka take zama a gidan, komawa ta yi ciki,Mahboob da Aasseyah suka shiga,abinci ta aje wa Mahboob kamar yanda ta saba.
Aaseeyah ta gudu dakin ta ta shiga wanka, ta na fitowa ta hau shirin makaranta, ta makara amma ya zatai, ita ta jawa kan ta.
Koda ta fito gani ta yi ba Mahboob a parlour, da sauri ta fice ta hango shi a mota a zaune,murmushi ta yi
"Dama na san ba zai iya tafiya ya barni ba,"
Takawa ta yi zuwa motar, ta na tafe ta na tsara yanda za ta bashi hakuri.
Hannu ta sanya dan bude motar ta ji ta a kulle,kallon shi ta yi da murmushi tare da masa alamar motar a rufe take, ji ta yi ya tada motar shi, sannan ya juya ya kalli baya,ya danna horn mai gadi ya bude ya sa kai ya fice, Aaseeyah daskarewa ta yi a wajen, nan da nan kuwa hawaye suka taru mata,
'Ni Yah Mahboob zai wulaqanta haka?'
Dariyar Ummee ce ta katse mata tunani,
"Dan albarka da ya yi gadon arziqi, ai ya min daidai, in...."
Wani tsaki Aaseeyah ta ja ta bargidan cikin fushi,
"Kar ya dauken din mana, nima daga yau ba zan sake shiga motar shi ba,ya je ya ci motar shi,in fushi ne na fishi iyawa"
Ta na tafe ta na sambatu ta manta me ta masa, ita a ganin ta ita aka wa ba daidai ba.
***************************
Alh. Munkaila da sauran 'yan qungiyar su ne zaune a wani sabon wajen taro da suka kama, wara ido na ke dan hango Eliza na ga wanne irin shiga yau tayi sarauniyar gayu, sai na ga wajen kaff maza ne ba mace ko guda daya, wasu matasa ne,wanda kallo daya za ka musu ka ji tsoro ya kama zuciyar ka su biyar ke tsaye a bayan Hon. Mamman Accu.
"To ga dai yaran da na alqawarta zan samo,kowannen su za ku ga irin taqadirancin da ya aikata har aka kulle shi a gidan yari in kun duba files din da ke gabn ku,kwararru ne akn aikin su, dan haka na masu bayanin komai, yanzu umarni kawai suke jira su ji ta ina za su fara aiki"
"Ban katsi numfashin ka ba, amma ni fa sabuwar shawarar da Sanata Kabiru ya kawo bata kwanta min ba, kuna nufin cin amanar Eliza zamu yi?ya kamata ta san da wannan taron,ko ba haka ba?"
"Shalele in ba za ka iya shiru ba sai ka sanar da ita sai mu dau mataki"
"Ahhhh Ahhh me ya yi zafiii?"
Kame labban shi n sama da qasa ya yi ya gintse cikin bakin shi, sannan ya jingina da kujera ya nade hannayen shi a qirji, tumbin nan ya yi himmm a gaba, sai muzurai ya ke dan su yarda sa shi ba zai fada mata ba.
"Shalele ka na abu kamar wani mara aikin yi, da girman mu mun tsaya wani game din yara, in muna son kawar da mutum ko wane ne a ranar muke aika shi, amma mun tsaya wani shiririta, ni dama tun fari na biye maku ne kawai,amma har yaushe za mu tsaya wasa? Gashi Alhaji Munkaila na fadin jibi abokin kasuwacin shi Usama Bege zai shigo da kayan shi daga dubai, qaramar sarqa a cikin kayan ita ce sarqar million bakwai, to shiriritar me za mu tsaya yi? A aika su lahira kawai har shi Mahboob din a gama komai"
"Kwarai da gaske, dan in muka rasa wannan dukiyar mun yi a sara babba, Kai C boy ya kamata ku karkasa kan ku a yau dinnan, kowan nen ku ya kira yaran shi, a aiwatar da abinda ya kamata"
"Ranka ya dade, yaran mu na nan na aikin su,dan kafin mu shigo dakin taron nan ma,sun min waya, sun sanar da ni Aaseeyah ita kadai ta tafi makaranta, kuma sun duba ba kwalawan da ke biye da ita yau"
"Da kyau"
Ci gaba da qulla yanda za su yi dan cikar burin su sukai,ni kuma na garxaya.gidan AIG Aliyyu dan ganin wainar da suke soyawa......
TAUBASHI
PAGE 44
Mahaifan Aliyyu na cike da farin cikin samun matar aure da gudan jinin su ya yi, komai na duniya lokaci gare shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba,Mama ta ce dole sai an yi bincike kamar yanda shari'a ta tanadar, Aliyyu ya so ya tabbatar masu da ba matsala ai mahaifin ta sananne ne, amma Mama ta ce sam sai an yi bincike.
Amatullah ma da ta samu labarin ta waya ta yi farin ciki sosai, tare da alqawarin zata zo jibi.
Suna tsaka da hira Aliyyu ya samu waya daga babbar hedikwatar 'yan sanda ta kano ana da buqatar shi,sallama ya yi wa su mama ya fita.
A mota kan ya isa ya kira Eliza su ka gaisa, qasan ranta kuwa haushin shi take ji, dan ba shi take so ba, ai ko za a yi daukan fansa ta auri wanda zata mora ko na daren farko ne ko?
Ya na isa ya kashe wayar shi ya shiga dakin da suke taro,nan da nan aka gabatar masa da qorafi akan b'atan wasu firsinoni, guda biyar,file din su da duk wani abu da zai bada shaidar su din masu laifin ne an nema an rasa, cikin kwarewa kan aikin shi ya amshi takaddun da aka miqa masa, duba wa ya yi a nutse ya ga komai a rubuce, sunayen wanda suka batan da duk wani bayani da ya kamata ya sani, shiru ya dan yi na wasu lokuta, sannan ya ce,
"A gaskiyar magana wannan abun ya na buqatar bincike na cikin gida, domin babu yanda za a yi firsinoni guda biyar su bata, ba tare da sanin hukumar gidan yarin ba,koda mutum daya ne sun samu taimakon shi,sannan za su gudu, wannan mutumin za mu nemo,ko kuma na ce mutanen,, ko su wane ne hukuma za ta hukunta su kuwa, na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 41