komai ba, dan har yanzu bai saba da ita ba yanda ya saba da Mammee ba.
Shirun ya yi yawa, gashi ya shirya dan fita,ita kuma ba ta ce komai ba, cikin rusunar da muryar shi, ya ce,
"Ummee akwai abinda ki ke buqata na maki ne?"
"Ah ah, kawai dai na ji ina son na zauna da kai ne,a matsayi n na uwa a gare ka, na kula dik wata kulawar ka da ya kamata ka bani saboda matsayi na a wajen ka,ka tattare ka bawa Subai'a, ni ce qanwar mahaifiyar ka,ba fa ita ba,komai naka ya tashi can ka ke tafiya,hakan sai ya qara jawon raini da gori a tsakanin mu,"
Dan tsuke fuska ya dan yi sannan ya kalle ta ya ce,
"Ammmm..Ummee tunda ki ke da Mammee ta taba yi maki gorin da kk fadi za tamaki?..ko ta taba maki wani gani gani da ya ke nuna ni din ban da wata alaqa da ke? In har ki ka furta ta taba maki wani wulaqanci akai na, tsakanin ki da Allah, ni kuma na maki alqawarin ko hanyar da tabi ba zan sake bi ba"
Shiru ta yi,ta na kame kame, shi kuwa ya baza mata idanun shi da ke rikita ta,gyada kai kawai ta yi alamar Ah ah, sai ya saki fuskar shi, sannan ya riqe hannun ta guda daya, a cikin nashi biyun, sannan ya ce,
"Ummee ki yi hakuri da yanda na ke janye jiki na daga gare ki, ban haka da wata mummunar manufa ba, inshaa Allahu zan gyara, shaquwar da ke tsakani na da Mammee ko da Mahaifiya ta ban samu ba, ita ce ci na, sha na, da yi min duk wani abu da na ke so in baki manta ba,tun ina da yarinta, har na girma,har ina Jordan kullum sai mun yi waya ta ji lafiya ta, in zaki iya tunawa sai mu kusan wata ba mu gaisa ba ni da ke,ko muna gaisawa da su Yesmeen ba amsa kk ba,dan haka ki qara hakuri,inshaa Allah a hankali komai zai yi daidai,b a gina shaquwa a dare d'aya, amma in tai qarfi mutuwa ce kawai ke yanke ta"
"Haka ne Mahboob,Allah ya muku albarka dika, na fahimce ka,kuma zan jira har lokacin da za ka bani matsayi na na Uwa a wajen ka"
Murmushi sika yi, ta janyo masa naman, da sauri ya zaro ido, ya na dariya qasa qasa,
"Ummee kin manta yanda muka sha fama da toilete ko?"
Itan ma dariya ta yi, tace,
"Ai ka na iya aje wa, ko gobe ka ci, abinda an yi kwana hudu kenan rabon ka da zawon, na tabbata yanzu komai zai daidai"
"To na gode,bari na ajiye, inna dawo zan ci"
"Ina zuwa haka ma sha gayu kana zuba qamshi?"
Dan kallon ta ya yi ya sunkuyar da kai ba ya son yin qarya, amma dole ya yanko ta, kafin ya yi magana ta tare shi,domin in hasashen ta ya zama gaskiya wajen mace zashi.
"Ahiiirr din ka da zuwa waje budurwa ka na daure da auren 'yar Subai'a, na haneee kaaaa, yarinyar nan bata da mutunci, in ka ji labarin irin azabar da ta ke gana ma mutane sai ka ce qarya nake, ni kaina nan,azabar ta da nasha ba ta da iya ka, komai akai mata sai ta rama,yanda kasan yaro me koyon magana komai ka fada yace zai maimaita, to haka take"
Yanda Ummee tai maganar ne ya sanya shi dariya, sai ya ji ya na son sanin me Aaseeyah ta taba yi wa Ummee,
"Ummee ki ce kema kin sha azabar Aaseeyah,"
"Habbbaaa mana, wannan taqadarar, yarinya kamar mai aiki da aljanu, wataranafa nake fada maka,ta fito dakin Noor na gan ta boye da chaculates, Noor baya nan, duk da ya basu damar diba, amma sai na ji haushin boyewa yarana da take kar su sha,shegiyar rowa ne da ita kamar me,ta zuba wajen takalma ta qasan labule takoma suka ci gaba da hira, na kuwa faki idon ta na kwashe, ashe jikin ta ya bata ni na diba ko kuma gani na tai,oho,da yarinyar nan ta dinga min sata sai da na zaci aljanu ne suka tsane ni, ba su so na ci abu me dadi, da na girka abu in ka ga na ci sai dai na ci nan take ban matsa a wajen ba, na kuskura na matsa daga abincin har tukunyar ba zan gani ba, abun kwalama inna aje a fridge sai dai na ga wayam,duk Abbun ku ya ji labarin abu ya qare da wuri, ya azamin cin mutunci, ya ce ban iya nema ba, sai shegen ci,watarana ta zumdume min robar da na gama soya nama na tsane, ta je ta baya ta na durewa a leda sai gani, ko tsayawa batai ba ta karkata ledar wasu suka shiga wasu suka zube a qasa, kan in isa ta keta da shegen gudu, ina a rufe gate haka me gadi ya qi, dan ya san halin ta shi ma, ya rufe ta dawo kan shi, qarshe sai hakura na yi ban magana ba, da kan ta ta daina,kaiiii wannan yarinya sai godiya"
Mahboob dariya kawai yake, ya na hango ta,hira suka sha kamar ba Ummee ba, ya kuma ji dad'in hakan sosai, bata bar wajen shi ba sai da ta ji ana kiran sallar azahar,alwala ya yi ya nufi masallaci, ya na dawowa ya duba no Eliza a wayar shi ya rasa,murmushi kawai ya yi, dan ya san wanda zai goge No Saratu awayar shi.
Motar shi ya nufa ya bude ya tada ta,Aaseeyah na fita daga bangaren shi ta kai masa abinci, shi kuma bai kula da ita ba a wajen, ya fita cike da murmushin kishin Aaseeyah, ita kuma nan da nan ta d'arsawa ran ta, duk inda za shi ya na murna da zuwa wajen,
'Ko dai gidan su Saratu za shi?'
Wata iriyar faduwar gaba ne ya same ta, ji ta yi hankalin ta ya tashi,ina ma ta san gidan da ta je ta lallasa Saratun ta mata warning ta bar mata mijin ta,in ta qi ji ta kai ta ga hukuma. (Kishi kumallon Aarce)
Ko da ya fita sai ya duba katin da ta masa rubutun adireshin ta, har da no ta saka, a hankali ya ke tuqin, ya loda Numbers din,sannan ya kira, bayan sallama da gaisuwa, ya sanar da Eliza zuwan shi, bata nuna tsananin murnar da ta ke ciki ba, sai kawai ta masa fatan isa lafiya.
*********************
Murna ta dinga yi ta na shewa, Alh. Munkaila ba ya gida a lokacin, ta waya ta sanar da shi,komai yake ya dawo gida surukin shi zai zo,nan ta shiga kitchen ta fara bawa masu aikin gidan da ke jin haushin ta umarnin girka abubuwa masu dad'i,domin za ta yi baqo, ciki ciki dattijuwar ta amsa mata, Allah-Allah take ta samu hutu taje qauye ta sanar ma da maman Alha. Munkaila zaman Eliza a gidan shi, duk da ya masu qayar taimakon ta ya yi,amma zaman yarinyar bai mata ba,
"Tunanin me ki ke? Ke na ga fa ki na min wani kallo, kin san ko ni wacece kuwa? Kar ki yi fatan ki siga black list dina,daga ke har dangin ki kaf zan iya badda su adoron qasa,ki kiyaye ni"
Cikin mazari dattijuwar ta ke daga kai,ta yi matuqar tsorata da yanayin Eliza matuqa da gaske.
Atampa ta sanya riga da zani, ta daura dankwalin atampar, sannan ta saka mayafi kalar kayan, turare kuwa ta yi barnar su kamar ba za ta daina fesawa ba.
Sai murmushi take,qarfe 3:11pm Mahboob ya isa gidan, parlourn baqi aka sauke shi, yanda Eliza ke taimaka wa Iya dattijuwa mai aikin girki, ya burge Mahboob,dan yara 'yan gata irin Saratu basu yi kama da wanda za su na taimakon masu aiki ba, ita kuwa dattijuwar mamaki take, dan ba ta jima da mata warning ba.
Bayan sun gaisa, Eliza tace,
"Ni fa ban zaci da gaske ka ke ba"
"To gashi sai ki dai na kokonto akan xuwa na"
Murmushi ta yi sannan ta ce,
"To Malam..."
"Mahboob,"
"Malam Mahboob ga ka a gidan mu, me ke tafe da kai?"
"Kin manta na fada maki ina son sanin ke wace ce, meye damuwar ki, ko zan iya taimakawa"
"Kai kuwa za ka iya taimakawa in har ka na son taimakawar, domin ba zan maka dole ba"
"Kar ki damu, inshaa Allahu zan taimaka mki, domin ganin inda kk da zama kawai ya qaran kwadayin son sanin damuwar ki"
Gyara zaman ta tayi, tare da rufe qirjin ta wanda ta na sane ta matso su suke bayyana ta saman rigar ta a duk sanda ta motsa.
Mahboob bai bar kallon ta ba har ta gama abinda take ta fara bashi labarin qaryar da ta tsara kamar hak,
"Suna na Saratu kamar yanda na sanar da kai, kuma ni ce diya d'aya tal a wajen Alh. Munkaila,da Haj. Bilkisu, Allah ya jiqan Mama na, (idon ta ta share kamar mai kuka) tun tasowa ta mahaifa na ke nuna min gata matuqa,gatan da ko 'yar gidan shugaban qasa iyakar shi za ta samu,daga primary har tatiary institute ba a qasar nan na yi ba, amma dik inda na ke son zuwa karatu mahaifiya ta na tare da ni, mahaifi na in ya samu lokaci zai kai mana ziyara,ana haka na kammala karatu na muka dawo gida Nigeria, dangin mahaifi na suka kyalla ido suka gan ni, sai suka ce na girma ya kamata amin aure, ni kuma na so na yi aiki, saboda lokacin shekaru na ashirin da biyar kawai,kakata kullum zarya take daga qauye zuwa nan,dan jaddada ma iyaye na su ban dama na fidda miji, ko kuma ta nema min a dangi, mahaifiya ta ta dage sai na fidda miji da kai na kafin a min aure ba mai min auren dole, in taqaice maka magana, akan aure na, kakata ta sa Abba na sakin Mama na, sannan ta sa ya aura min wani cousin dina, mutumin qauye,damuwar da na shiga ne ya sanya mahifiya ta shiga damuwa,har ta kamu da ciwon hawan jini, da ya ga ba zai samu kaina ba, ya sake ni ya ce banda tarbiyya ba abinda zai da ni, kakata ta zo ta zage mahaifiya ta, sannan ta ce sai ta bar gidan,dik da cewar bata gama idda ba,baqin cikin wannan ne sanadin mahaifiya ta"
Kuka sosai Eliza ta ke yi, na tuna asalin labarin ta, wanda Mahboob ya yi zaton tunawa da mahaifiyar ta ne ya sa ta kuka, tissue ya dauka ya je kujerar da ta ke ya fara goge mata hawaye,kafe junan su sukai da idanu,Eliza ta yi matuqar sake fadawa soyayyar Mahboob, ganin kyakkyawan balaraben a gaban ta.
Ganin kusancin da ke tsakanin su ne ya sa shi saurin tashi daga kusa da ita,ya hau kame kame, dake yar duniya ce, sai ta ci gaba da labarin ta,
"Bayan rasuwar mahaifiya ta yanzu da shekara uku, kakata ta sawa mahaifi na dokar in bai aurar da ni ba nan da wata d'aya za ta tsine masa, ta yafe shi daga cikin yaran ta, tunda a cewar ta ya ga ya yi kudi, ya haifi wadda ta fi ta a wajen shi, shi ya sa ya ke qin bin umarnin ta, yanzu sauran sati d'aya lokaci ya cika, kuma ni banda wanda zan aura, na rasa yanda zan bullowa lamarin, kamar ana korar maza daga waje na, ba mai son aure na"
Kuka ta fashe da shi sosai, sannan ta ce,
"Mahaifi na na matuqar son mahaifiyar shi, yanzu in ban samu wanda zai aure ni ba kafin lokaci ya cika zai rabu da mahaifiyar shi, ba na son na rasa mahaifi n kamar ynda n rasa mahaifiya ta"
Kukan ta ya shigi zuciyar shi matuqa, nan take tausayin ta mai girma ya shige shi.
"Kar ki damu, matsalar ki ta zo qarshe da izinin Allah, na sanar da ke zan taimaka maki ai ko? To alqawari na na nan, share hawayen ki, karbi wannan, goge idon ki"
Wani irin farin ciki ne ya baibaye ta, goge hawayen ta ta fara, Mahboob ya miqe dan tafiya, duba da lokacin sallah da ya yi, Eliza ta so Alh. Munkaila ya dawo su gaisa, amma gashi har zai tafi basu hadu ba.
Mahboob na tafe ya na tunanin ta ya zai taimake ta ta fita daga wannan musiba da take ciki?
"Koma ta halin yaya ne zan taimaka wa wannan baiwar Allah, na yi alqawari"
Hummmmmm, sannu marigayi Shuwayya-Shuwayya.
PAGE 40
Wani masallaci ya gani a hanya za su shiga sallah, tsayawa ya yi aka yi la'asar da shi, bayan ya idar da sallah ne, ya zauna a wajen ya na tunanin yanda zai maganin matsalar Saratu.
Ya na nan zaune har lokacin magrib ya yi, sallah ya sake bi ya na azkar wata shawara ta fado masa, sujjada ya yi dan godiya ga Allah, sannan ya fita cikin sauri ya na murmushi, waya ya zaro a aljihun shi ya kira Eliza cike da murna da No da ta rubuta masa a jikin katin da ta rubuta address d'in gidan su.
"Sarah, albishir na kira na miki,"
Ajiye sigarin ta ta yi a dan qaramin kwanon da take zuba tokar ta, cike da murna ta bar jikin windown da take fesa hayaqin, tunda Alh. Munkaila ya hana ta shan sigari saboda masu aiki kar su ji.
Gado ta fad'a ta na murna,
"Wanne irin albishir ne wannan?"
"Na samo maki mijin aure, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata na fara warware tukunna"
Ta b'ata wajen saurarar muryar shi, da yanayin yanda murmushin shi ke fita cikin sauti mai ratsa zuciyar mai sauraro, ta ji muryar shi na fad'in,
"Ki na ji na kuwa Sarah?"
'Ohhh how i wish cewa har yanzu ana kira na da wannan suna, ya san yanda zai kira shi a labban shi su yi dadin saurara'
"Pls call my name again"
"Uhum? Lafiya kk kuwa?"
Hawayen ta ta share, nan da nan zuciyar ta ta quntata, ta matse waje guda saboda yanda take jin wani irin qunci domin tuna baya da ta yi,ta yi alqawarin ba mai sake kiran ta da sunan da mahaifin ta ya rad'a mata, sai gashi ta na nema ido rufe Mahboob ya furta mata"
"Sarahhh"
Shi kan shi da ya fada sai da ya ji wani yanayi a tattare da shi,
"Uhumm, ina jin ka"
Cikin murya mai sanyi ya ce,
"Cewa na yi na sama maki mijin aure,amma ban ji ki na murna da hakan ba, ko baki so"
"Ina son dik abinda ka zaba min ko da kuwa ba zan gan shi ba har ranar aure"
Murmushin jin dad'i ya yi, sannan suka dan taba hira kadan sukai sallama, ranar kulle daki Eliza ta yi ta kunna kid'a, da ta ga ta na son mafiyin haka, gida ba nata ba, a daren ta binjima jallabiyyar ta ta isa gidan ta,tun kan ta isa gate ta fara horn,ta na zuwa mai gadin ta ya tabbata nan ne,wangale mata gate ya yi,ta shige a guje, kida na tashi a motar, bata qarasa rufewa ba ta shige gidan, a bakin qofa ta sake rigar ta fadi qasa,daga ita sai wata bingilar riga da dan kamfai,masu aikin ta na ganin ta cikin murna haka sun san me ya kamata, nan da nan kuwa suka kawo mata glass cup da qanqara, da mutuniyar ta ta, barasa, suka ajiye suka bar wajen, har za su tafi ta daga musu hannu, dika su biyun maza ne, kuma ba musulmai bane, gayyatar su ta yi suka zauna jugum jugum su na kallon juna.
"Celebrate with me, na samu mijin aure, balarabe, kyakkyawa, mai arziqi, dan babban gida,mijin fita kunya,lets drink guys hoooohoooooo"
Nan da nan suka washe baki, suka dakko cups, suka dinga shan barasar nan, har sai da suka bugu,a nan suka yi bacci.
*******************************
Mahboob ya isa gida bayan ya yi sallar isha'i, parlourn Mammee ya shiga da sallama, ya tarar Mammee na ta aikin lallashi, Aaseeyah ido ya mata jawur saboda kuka, jikin nan ya yi zafi rauuu, ta qi ci ta qi sha, kuma ta qi fadin abinda ke damun ta.
"Come on eat ur food, ki daina kukan haka,"
"Mammee na qoshiii, ba na jin yunwa,"
"Aaseeyah raina ya fara baci, Umaimah tun la'asar take lallashin ki, Noor ya zo duk sun baki baki, amma kin qi sanar da kowa damuwar ki,in baki maida hankali kin ci ba tashi zan na barki,"
Sallamar Mahboob ce ta katse ma Mammee maganar ta, ta miqe tare da cewa,
"Yauwaaa, gwanda da Allah ya kawo ka, ban sani ba ko dan yau baka shigo bane ya sa take kuka, domin taqi fadin meke damun ta"
Cike da fushi ta miqe za ta bar wajen,jiri ya debe ta, da sauri shi da mammi suka kai hannun su, nashi hannu ya tare ta, Mammee na ganin haka ta basu waje, ta yi daki, kuka sosai Aaseeyah ke yi, ta na ture shi, za ta tafi dakin ta, amma ya qi sakin ta, kyakkyawar runguma ya mata a jikin shi, ya na shafa bayan ta, ta jima ta na kuka kafin ta fara ajiyar zuciya,zama suka yi a manne da juna, sannan ya daga kan ta ya na kallon fuskar ta, idanun ta sun kumbura sun yi ja ta sama, lips din ta sun yi jawur, sun kumbura, sai hancin ta da ya yi ja shima, idanun ta kulle, ta ji ya jima da fuskar ta a hannun shi, ta na bude idanun ta ta ga fuskar shi daf da ta ta, da sauri ta janye fuskar ta a hannun shi, ta na haki kamar ta yi gudu, harara ta watsa masa, sannan ta miqe ta na son tafiya dakin ta,
"Mahboobatee ina zaki? Na dawo ina jin yunwa, ki zauna mu ci abinci"
Harara ta sake watsa mishi, sannan ta daddafa ta na son barin wajen, tashi ya yi ya kamo ta ya dora ta saman cinyar shi, ya ce,
"Ko ki tsaya mu ci abinci, ko na biki dakin ki mu kwana, kuma ni ma ba zan ci abincin ba, yau yini na yi ban ci komai ba"
Hararar shi ta sake yi sannan ta ce,
"Inda ka je din ba ta baka abinci ka ci ba kenan"
"Ta kawon abinci ban dai ci bane, lemo kawai na sha"
Kallon shi ta yi baki sake, wani irin abu mai maqaqi da zafi na taso mata a zuciya,ji ta yi numfashi na mata wahalar shaqa, idanun ta har wani juyewa suke, bata gani sosai,
"Wajen wa ka je?"
"Wajen sarah"
Tafiya ta yi luuuu, jiri ya debe ta, da sauri ya tare ta, ji ya yi jikin ta na wata iriyar rawa,cikin tsoro ya dauki juice din da ke gefen wajen ya miqa mata vakin ta, ta sa hannu ta doke cup din ya fadi qasa,kamar wadda ke amfani da batiri haka ta miqe, da sassarfa ta na jin jirin amma ta daure, dakin ta ta shiga, bata samu damar rufe qofar ta va ya shiga,
"Ka fita min a daki,Yah Mahboob kar ka sa na aikata abinda za mu yi dana sani da ni da kai, ka ci amana ta, ba zan taba yafe maka ba, ban san me ne ne so ba, bayan soyayyar iyaye na da 'yan uwa na, kai ka koyar da ni yanda mace zata so namiji, akan ka n fara so,ban taba vawa wani abu mahimmanci a rayuwa ta ba sama da yanda na baka,amma shi ne ka ke cin amana ta tun kafin na tare da kai? Ashe kai ba mutumin kirki bane? Ka sani Yah Mahboob, a yau ka ciren son da na ke maka, na tsane ka, na tsane ka, da ace laifi kawai kamin, da na hukunta ka a iya hukunci irin nawa,amma wannan rayuwa ta ka yi wasa da ita, idan na mutu alhaki na kan ka"
Ta na kaiwa nan, bata bashi damar magana ba ta tura shi waje,ta rufe qofar ta, a wajen ta zube, ta na kuka mai ban tausayi, me ye a cikin so banda azaba da qunci? Me ye dad'in soyayya da wasu ke makancewa akan ta? Ashe soyayya azaba ce, qunci ce? Wahala ce, izaya ce,
"Wayyoo Allah na qirji na, wayyoo Mammee na,wayyoo Allah Abee na zan mutu, wayyoo Yah...."
Shiru ta yi ta kasa qarasawa, kukan ta mai matuqar ban tausayi ya karade dakin, Mahboob na tsaye ya saka goshin shi a jikin qofar dakin,ya na jin kukan ta kamar saukar wutar dalma a jikin shi.
"Me ye zai saki kuka haka? Bayan ina son ki, ina maki son da ban taba yi wa wata mace irin shi ba, ke kadai ce macen da na ke hango rayuwa ta ta gaba da ita, Aaseeyah bani da niyyar cin amanar ki, dan Allah kar ki hukunta kan ki da laifin da baki tavvatar da faruwar shi ba, ki zo ki ci abinci pls,ki buden qofar"
Mammee ce ta fito daga dakin ta, muryar shi na rawa yake maganar, ganin hawaye na sauka daga cikin gemun shi zuwa qasa ne ta sake baki,
"Lallai wannan an yi shiriritacce, akan mace yake kuka? Sai kace ba namiji ba?....kai Mahboob, in ba zata ci ba ba sai ka rabu da ita ba, tunda ita taurin kai ne da ita, ka kama hanya ka je ka ci abinci ka kwanta,in yunwa ta ciyo ta cikin dare za ka ji ta fito nema, ai ba yau ta fara wannan shegantakar ba, dan ma ina hana ta da da d'abi'ar fushi da abinci zata tashi, sai sanda yunwa ta ishe ta ta fito diba ta ci komai dare...muje za ta fito ne"
"Mammee wannan karon kukan Aaseeyah daban da na yarintar ta,ba zan iya sanya komai a ciki na ba in har ba ta ci ba"
"Toooo, baka da aikin yi kuwa,nan za ka kwana na tafi daki ko wajen ka za ka tafi na tsaya kulle qofa?"
"Wai hayaniyar me nake juyowa ne?"
"Maganar dai tun ta dazu ce, ga kuma sabon d'an takarar rashin cin abinci mun samu, shi ma wai ba zai ci ba in Aaseeyah ba ta ci ba,kai ka ji"
Murmushi Abee ya yi, sannan ya ce,
"Ina ita Aaseeyahn?"
"Ta na daki Abee ta kulle da key,"
Da kan shi ya je ya buga ya sa ta bude a dole ba dan ta so ba, kan ta a qasa ta na ta ajiyar zuciya da shassheqar kuka, Abee da kan shi ya sa Mammee ta zubo masu abinci, su na zaune a gavan su, suka sa su cin abincin na dole,
"Ko ku fa? 'Yannema masu kan buta, dikkannin ku yunwa kuke ji, Allah kadai ya san rabon ku da abinci,ku maida hankali ku ci abinci kun tsaya shiririta, sai kace qananan yara, ka na namiji za ka bari yarinya qarama ta dinga juya ka, a haka za a yi bikin ku tare? In tai fushi ta na kuka kai ma ka zauna ka na kuka? Kar ka manta dik gidan nan kai ne babba, abinda dik ka yi shi qanannen ka za su gani ya zama masu abin koyi, ka zama cikakken namiji mai tsayawa a gidan shi, ke kuma ki zama mace mai hakuri da sauqin hali, ki duba ki ga mahaifiyar ki, tunda muke kin taba ganin ta yi fushi da ni har wani ya sani? Ni akan kai na ma ba zan iya tuna sanda tai fushi da ni ba balle wani ya gani, komai ya faru tsakanin ku zama za ku yi cikin lumana da kwanciyar hankali, ku tattauna ku warware matsalar ku, ba sai kowa ya ji ba,daga yau kar na sake ganin irin wannan fushin naki, ba na so, kin ji Aaseeyah Abee?"
Daga kai ta yi hawaye na tsiyaya, an cuce ta an hana ta kuka,ba komai,
'Duk wanda ya ci tuwo da ni...'
"Ko ba ki ji ba ne Aaseeyah?"
Daga kai kawai ta yi, dan ba ta jin ko magana ta yi za ta fita,
"Na ce ki je ki kwanta, sai da safe"
Daga kai ta yi, ta rabe gefen Mahboob da ya qura mata ido ta wuce dakin ta, nan fa Abee da Mammee sukai ta ma Mahboob fada, akan me zai tsaya ya na kuka akan qaramar yarinya, so yake ta raina shi? Shawarwari suka bashi na yanda ake tafi da mace kamar Aaseeyah, daga baya suka yi sallama, ya wuce bangaren shi.
A daki kuwa Aaseeyah ta kwanta ne kawai, amma kan ta kamar zai tsage dan ciwo,zuciyar ta na zogin kishi,
'Lemo kawai ya sha, har fadi yake ta kawo abinci amma lemo kawai ya sha, ta tabbata wajen mace ya je, kuma
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 41