Noor bai koma ba, sai da ya gama da ita, da ta ke ta qoqarin nuna masa abinda ya aikata, sannan ya juya kan Noor, ya tsaya a saman shi, tare da kama qugun shi...........
Hummmmmm yau a nan za mu tsaya inshaa Allah, if ur comments sweet meee anjima zan qara, innaji ba sugar , zan lafe sai gobe a qara ko jibi, ko gata..ko masoro..ko citta...ko barkono..uhummm ko kimba...uhummm na manta sauran ku qarasa.
TAUBASHI
PAGE 29
HAERMEEBRAERH
Ruwa Aaseeyah ta dawo da shi a cup, ta sheqawa Noor, bai motsa ba, sallamar Mammee ce ta karade parlourn, ta na kula da Noor a qasa ta buga salati, da sauri ta qarasa gaban su, ta na tambayar me ya faru, cikin Kuka Aaseeyah ta mata bayani, hankalin Mammee ya tashi matuqa,su na tsaka da magana Noor ya bude ido, tare da sauke doguwar ajiyar zuciya, dishi-dishi ya ke gani, baya gane me suke fadi.
Mammee ke ta masifa, abinda ba halin ta ba, ta dau wayar ta ta fara danna layin Abee, Aaseeyah ce ta riqe hannun ta ta ce,
"Mammee kin hana ni fada ma Abee maganar tashin hankali in ya na wajen aiki, ki hakuri su dawo, kinga yanzu ba su jimawa kamar da, hudu na yi sike dawowa, yau kuma juma'a, na san su na tafe"
"Aaseeyah ban had'a safety din ki da komai ba, ke ce kadai zan daga na bugi qirji na ce dangi na ba dan ke d'aya na haifa ba, sai dan kusancin da ke tsakanina da ke, in wani abu ya same ki fa?"
Cikin cijewar haqurra Mahboob ya qanqance ido ya kalli Noor ya ce,
"Ba abinda zai same ta sai alkhairi, in kuma wani mai halin bunsurayen ya ce zai sake gwada kusantar b'ata rayuwar ta, yanzu suma kawai ya yi, a shirye na ke na masa dukan mutuwa, in ya so a yanken hukuncin kisa"
Yawu Noor ya hadiya mai kauri, ya na dafe da kan shi, ya na bin bango, kunyar duniya ta gama lullube shi, gashi dumu-dumu ya na qoqarin aikata zina da macen da ya ke ikirarin ya na so, guduwa ya so yi, sai ya ji qarar bude gate da shigar motoci, to in ya fita ta ina zai buya ba tare da sun hadu da su Abee ba?
Mahboob ne ya kula da qoqarin fitar da yake, ya cafko wuyan rigar shi ya jijjiga shi, sannan ya ce,
"Noor ba ka da kunya fa ko,ina za ka?...ke Aaseeyah je ki kira Ummee,"
Mammee ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta matsu Abee ya shigo, ta na jin sallamar shi kuwa ta nifi wajen shi, su na hada ido kwallar da ta riqe ta gangaro mata, Abee na ganin hawaye a idon sarauniyar zuciyar shi ya ji tashin hankali ya shige shi, dafa kafadar ta ya yi,tare da goge mata hawayen ta da hannu daya.
"Bani labarin abinda ya sami Sarauniyar mata,bugun zuciya ta, fada min matsalar ki yanzunnan ta zama babu da izinin Allah,"
"Ku san matakin da za ku dauka akan Noor, in ba haka ba ni zan dauka, dan kuwa zan damqa shi ga hukuma a yau ba sai gobe ba"
Cikin damuwa Abee ya ce,
"Me Noor din ya yi?"
"Lafiya? Lafiya wannan kodaddiyar ta je ta na min rashin kunya, ta tsaya min a ka ta na fadan ki na nema na? Wata tsiyar ki ka aje a wajen ki da kike kira na ki goga min?"
Abbu da ya biyo bayan ta na shirin mata fadan kalaman ta sai mamaki ya hana shi magana, domin tunda yake tun zainab na da rai Mammee bata taba daga murya ya na kusa ba.
"Dalla malama yi mana shiru, tsiya ta wuce wadda kk haifa? Kin haifi yara baki san tarbiyyar su ba, sai cika bakin ke me haihuwa ce, ki na ina yaron ki ya ke neman ya yi ma yarinya ta fyade? Wato ya yi ma Umaimah, ya lalata rayuwar ta, ke a ganin ki matsalar ta wuce, ba za ki tsaya ki ja masa kunne ya nutsu ya daina lalata yaran mutane ba, ah ah masifa da cin mutunci ki ka iya, FATEEMA b fa tsoron ki nake ji ba, ina raga maki ne saboda Yayah da kuma miji na, sai zuri'ar da ke tsakanin mu,....ga shi nan Yayah, ku dau tsattsauran mataki akan shi, in ba haka ba hukuma ce za ta raba ni da shi, Aaseeyah ita kadai ce dangi na, ita ce kadai nake kalla ta mayen gurbin rashin uwa da uba, yayu da qanne da ban da su,ba zan taba yafewa kaina da duk wanda ya nemi ya keta mutuncin ta ba"
Kowa ya yi shiru kamar ruwa ya ci su, kunsan wanda bai saba masifa ba, duk sanda ya yi sai ya ba kowa mamaki.
Kallon da Abbu da Abee suke ma Noor kadai ne ya sanya shi durqusawa a qasqance, ya na jin shi a muzance, Ummee kuwa baki ta bude, ta na kallon Mammee, sannan ta maida idon ta ga Noor dan gasgata abinda ya faru, tabbas da dikkan alama wannan magana gaskiya ne, duba da shatin yatsu biyar da ke kwance a gefen fuskar Aaseeyah, idanun ta sun yi jawur saboda kuka, ga bakin ta a fashe, Mahboob ne ya yi ma su Abbu bayanin iya abinda ya gani, Aaseeyah ta fada masu kaff abinda ya faru.
Abbu qarasa shiga parlourn ya yi, su Umaimah da Yesmeen suna labe a waje dan jin me ke faruwa, gaba daya Noor yanzu tsoro yake basu, ya sauya hali kamar ba shi ba, (dama baku san komai ba).
"Inaaaa Noor,"
Cikin shaqaqqiyar murya ya amsa, tare da matsewa a jikin bango"
"KA BUDE BAKI KA AMSA NI DA KYAU INA MAKA MAGANA!"
"Na'am Abbu, gani"
"Yanzu Noor tsakanin ka da Allah halayyar da ka dakko mai kyau ce? Ka na ganin halin mutanen kirki ne fyade? Ashe Noor gaba daya halayen ka kyawawa ka rufe mu ne kana da munana a boye wanda mu iyayen ka da muka haife ka ba mu san ka na da su ba? Ka lalata Umaimah, yanzu ka dawo kan Aaseeyah, in ka ce baka son Umaimah, me zai sa ka lalata macen da ka ke ikirarin so? Noor me ka nema ka rasa daga wajen mu? Soyayya ce, ko ilimi ne na arabi da boko? Me ka nema ka rasa da ka zama mazinaci,in baka bani amsa ba Noor na maka alqawari da sai na tsine maka, sai na cire ka daga zuri'ar mu ta Abdul Mudalleb Jordan,domin zuri'ar mu mai tsafta ce, ba lalatacciya ba ce irin wannan"
Cikin kuka da dana sani,da nadama Noor ya bude baki ya fara magana, iyakar gaskiyar shi ya ke son sanar da iyayen nashi, domin ba amfanin boyewa, alqawarin da Abbu ya dauka da alama zai cika shi in har bai fadi gaskiya ba.
"Abbu dan Allah ku yafe min, na aikata babban laifi, na zama lalatacce a cikin wannan zuri'ar,"
"Yi min shiru, ka fadan dalilin ka shi kadai na nema, domin ni dai i am not ready to forgive u yet,ban sani ba ko sauran iyayen ka,"
Nan take rayuwar shi ta Jordan ta fara gilma masa daya bayan daya, ido Mahboob ya rintse ya na tuno kukan Aemana,istigifari ya fara a zuciyar shi har ya sauka a labban shi,muryar Noor ce ta katse shi, cikin dakiya ya fara bayani,
"Abbu, ba abinda na rasa na gata daga wajen ku da soyayya, sai dai ma na ce soyayyar taku ce ta min yawa har ta kai ni ga lalacewa,"
"Whatt?? Me ka ke nufi da hakan?" In ji Abee.
Noor Kallon Ummee ya yi, ya ci gaba da magana, duk sai ta ji ta tsargu, dan kuwa kowa ita ya ke kallo,
"Ummee in baki manta ba, kin taso da ni cikin gata, da shagwaba, ke ce mace ta farko da ta fara koyar dani zama mai fuska biyu, mai boye laifi na na fadi qarya a matsayin gaskiya ta, sannan ke ki ka koyan kafewa akan wannan qaryar da na yi, ko za a kashe ni, na sha yin laifi ki koyan yanda zan kare kai na, a dora ma Mahboob, na sha na saci abun wasan Mahboob kin san sarai baki sai min ba, amma ki dage ki ce ina da irin shi, Ummee ke kika koyan ko banda abu, dole na san yanda zan na mallake shi indai ina so,ke ki ka koyan gasa, da yin abinda wani ya yi, ko da ban da halin yi din,Ummee ke ce ki...."
"Kai ka ci uban ka, dan uban ka ni kadai na haife ka, komai sai ka ce ni, ni, ni kadai ce mahaifiyar ka, shi uban naka bai taka rawa wajen lalacewar ka bane,"
"FATEEMA KAR KI BARI NAI MUMMUNAN FUSHI AKAN KI, ZAN HUKUNTA KI HUKUNCIN DA BA KI TABA ZATON ZAN MAKI SHI BA!"
Tsuke baki Ummee ta yi, zuciyar ta na quna da quncin tozarcin da ake mata, meye laifin uwa dan ta kare d'an ta, ta so shi, ta ririta shi? (Ba haka ne so ba)
Noor ne ya kalli Abbun su, sannan ya ce,
"Abbu,ka sani, iyayen ku sun baku tarbiyya, nagartacciya, domin su mutane ne nagartattu, ba dan baku da nagarta ba, amma Abbu kun saki hanya daga tarbiyyar da aka baku, ba ita kuka bamu ba, Abbu, sanda na balaga ba ka sani ba, ballanta na samu shawarwari daga gare ka, a matsayin ka na namiji, kuma uba na, Abbu sanda na fara jin matsananciyar sha'awa irin ta sabbin balaga,ba ka koyar dani yanda zan kula da kare kaina daga zina ba, hasali ma ka wadatani da kudi, ba na neman su na rasa, ka mallakan waya mai kyau, da layi da komai, Abbu ka mallakan computer, ka mallakan TV a daki na, Abbu, tunda na ke baka taba zama da ni na awa biyu ba mun yi magana, ka ji damuwa ta, ka ban shawara, haka na taso daga islamiyya sai boko, sai gida, duk wani yanda zan nemi qananan yara ba tare da an gane ba, a internet na koya, yawan shiga internet da nake ne ya sa sha'awa ta taqi kwantawa, kuma ba ni kadai ba har 'yan biyu ku diba wayoyin su, za ku sha mamakin abubuwan da ke ciki, saboda ba ku bamu kulawar ku ba, ta tarbiyya, kun zaci islamiyya da boko, da waya za su bamu tarbiyya da nishadi, sam ba haka abun yake ba.....Abbu wadannan su ne dalilan lalacewa ta, amma a yanzu na gane kure na, dan Allah Abbu ku gafarta min, kar ku hada ni da hukuma, dan Allah,"
Kalaman Noor sun shiga jikin gaba daya mutanen wajen, musamman Abbu da Abee,sai Mahboob da ya ke tuna shi da ya qarasa rayuwar shi a Jordan ba uwa ba uba, mariqiya ta rasu,wa zai koyar da shi daidai da ba daidai ba? (Shin makaranta dan Allah ku ban amsar tambayar nan, dole sai iyaye ne za su sa mutum baligi a hanya sannan ya shiryu? Mu tattauna dan warware wasu matsalolin ko da ta whatsapp ne pls)
Gyaran murya Abee ya yi, sannan yace,
"Noor na yafe maka na tabbata Mammen ku ma ta yafe maka, ka kalli fuskar ta da kyau ka gani, ita din mace ce mai yafiya, da kauda kai, amma da sharadin ban yarda mu gan ka anywhere around Aaseeyah ba again, ba zamu raba ku ba kwata-kwata a matsayin ku na 'yan uwa, amma ba kebancewa, ka na ji na ko? Sannan ina mai maka nasiha da ka ji tsoron Allah, ka ji tsoron Allah, ka sani ya na kallon ka a dik inda ka ke, a komai ka ke aikatawa,a boye ko a bayyane, Allah baruwan shi da girman ka ko rashin girman ka, indai ka balaga, to hukunci ya hau kan k,maganar su Hussein kuwa, ba na fatan Allah ya mana hisabi da su, amma daidai misali ina koyar da su abinda ya dace da wanda bai dace ba, sai dai na san ban yi masu kamar yanda aka mana ba,dan haka mu na sake neman gafarar ku kuma, inshaa Allahu za mu sauya"
"Allah ya sa" shi ne abinda wasu a wajen suka amsa banda Ummee da har yanzu ta ke jin ita ba a mata daidai ba, da Noor ya ce ta na da hannu wajen lalacewar shi, bayan duk soyayyar da ta nuna masa.
"Tabbas abinda ka fada ya yi daidai Ibraheem, amma fa dole ne a hukunta Noor, domin kuwa ko bayan auren shi a cikin gidan nan za su ci gaba da zama,ban yarda da zaman su waje guda da su Mahboob ba, sanda na gama aminta da halayyar shi ta gyaru ya koma can da iyalin shi"
Mammee ce tai saurin cewa,
"Yauwa Yayah, hakan ma ya yi daidai"
"Eh kin ce haka mana, tunda gidan zai zama yaran ki ne kawai a ciki, ai ni da an bi ta tawa kowa da unguwar shi, kuma kowa da gidan shi za a yi, duba dacewar tun fari an yi zaman faccalolin nan ba ji dad'in shi ba"
"A hakn dai za a zauna, ai dama ba rayuwar da za ta tabbata ba sa'in sa, qarshen kusanci miji da mata kenan, to su ma sukan samu sabani, kin ga dai Subai'a ko a ina zan yabe ta, amma akwai sanda muke samun sab'ani, mun rabu? Ah ah, hakan sai ya ke qara mana kusanci, dan haka su ma a haka za su zauna, dole akwai amfani a zaman tare kamar yanda kuma akwai rashin amfanin a zaman taren, so dan Allah ki ma bar maganar raba masu gida"
"Ibraheem ina fada maka ka daina min shisshigi a magana ta, kai ba miji na bane,"
"Sannu mai ladabi da biyya wacce dole qanin miji ya girmama ta,....ku kuma in kun gama laben ku shigo, in kuma qafafun ku ba su gaji da tsaiwa ba ku bada himma ku yi ta tsayuwa a wajen"
'Yan biyu da suka shigo suka ji ana case din, su Umaimah suka labarta musu me Noor ya ce akan su, tuni suka shiga wayoyin su suka hau goge komai, duk wasu hotuna da video da chats da 'yan mata sun goge, sun bi sahun matan sun maqale agini su na jin me ake tattaunawa akai, su na jin an yi magana da su, suka zabura a guje, kowa ya yi nashi wajen boyo.
Qarshe dai sai da Abbu ya tattara dika iyalan ya musu nasiha, mai ratsa zuciya, sannan daga baya Noor ya ba ma Aaseeyah hakuri,kowa ya fita, aka bar Mammee da jinyar vakin Aaseeyah, Ummee na ta masifar rashin dalili, sai ta kama waccan masifa ta ga bata da gaskiya, sai ta saki ta kama waccan.
****************************
Yau sauran kwanaki biyar a daura auren yaran gidan Jordan,wasu daga cikin dangi sun hallara musamman 'yan mata, da samari, sai manyan mutane mata su ma ba wasu da yawa ba, Matar Kaka Auwal sai ana gobe daurin aure za ta zo.
Su Aaseeyah ne cike a mota guda biyu, Mahboob da Hussein na tuqa su zuwa kasuwa, dan siyan mayafai,takalma, sarqa da abun hannu da suka dace da ankon su, sai hira suke a hanyar su ta zuwa kasuwar.
Aaseeyah na gaban mota, amma hankalin ta da jikin ta duk su na baya, ji ta yi ta gaji da juyawar, sai ta koma ta zauna su na ci gaba da hira, ta mirrow ta kula da wata mota da ta kwan biyu indai ta fita sai ta ga motar na bin ta, shiru ta yi dan ta tantance shin motar su take bi ko kuwa, Fada ma Mahboob ta yi ya bi ta d'ayar hanyar saboda ba cunkoson abun hawa sosai,za su yi saurin isa, su na shiga titin motar ma ta shiga, da ganin haka jikin Aaseeyah ya yi sanyi qalaou, gashi ba ta son fad'a da qarfi kar sauran su tsorata, gashi ba ta ga fuskar masu bin nasu a baya ba.
Su na isa kasuwa Mahboob ya samu wajen parking, suka firfita, ta na son sanar da Mahboob Yesmeen ta ja hannun ta,
"Muje mara kunyar amarya, a kasuwar ma sai kin nuna rashin ta ido dad'in abun ma, ba ke a wannan ruguntsimin bajimin bikin,ke daya za ai naki"
Sauran na dariya suka ja ta suka bar wajen, gani ta yi wani ya fito daga motar da ke bin su,kafin ta tabbatar d waye,Ummu Suleim ta ja hannun ta sun fada tsakiyar kasuwa tsundummmmmmmmmm
Hyekace rijiya😂
TAUBASHI
TAUBASHI
PAGE 30
HAERMEEBRAERH
Har suka kammala siyayya Aaseeyah ba ta daina tunanin mai bin su a mota ba,kusan su Yesmeen ne suka zabar mata komai,sai tsokanar ta suke ko dan ba da ita za a hada auren ba ne ya sa jikin ta sanyi? Sai dai tai musu yaqe kawai,ko da suka gama suka koma tai ta waige waige ba ta ga motar ba.
Har suka isa gida ta na kallon bayan su ta madubi ko za ta ga ana bin su ba ta gani ba.
Gida ya kacame da hayaniya, wannan taron ba laifi kusan matasan dik sun shiga taitayin su akan soyayyar ba gaira ba dalilin nan, sai qalilan masu taurin kai.
Kwana biyu kafin daura aure suka fara gudanar da events din bikin, kamar su kamu,sai walima inda aka yi ma mata har da mazan ma wa'azi sosai,a ranar daurin aure kuma iyaye mata sukai yini a cikin gida, mutanen unguwa da dama sun sun hallara, har da wanda ba a gayyata ba sai da dare akai dinner, a daren kuma aka kai Yesmeen gidan su, wanda ke a cort road, ta so a ce gaba dayan su ne aka kai a tare kamar yanda iyayen su suka tsara tun farko,domin ba ta saba da matar Hussein ba, duk da Mammee ta kwantar mata da hankali, tace mata sabo dama ba a dare daya ake yin shi ba, a hankali za su saba ne, su na shiga ta ga girman gidan, sai ta ji tsoro ya kama ta, duk fadin gidan ace su biyu kawai za su zauna.
Gidan ba wani mugun hadadde bane, kadaran kadahan kamar na iyayen su, dan kusan fasalin ginin daya aka masu, iyaka an sake zamanantar da wannan, kayan daki da kujeru kowa da kalar nata, daidai misali, gwanin sha'awa.
Ummu Suleim dangin mijin ta suka zo tafiya da ita, ta yi kuka ta gode Allah, Ummee kuka Ummu Suleim kuka, sai da suka bawa dangi tausayi, haushin Hussein ya sa ta dinga roqon Allah ya sa sai ta tafi za a kawo matar shi, dan ba ma ta son ganin matar tashi a wannan daren, har yanzu ta na jin son shi a ran ta, kawai ta amince da auren ne domin ta na saka ran watarana za ta manta da ta tab'a son wani wai shi Hussein, tunda shi ma ba ya son ta, ya yi amfani da ita ne dan biyan buqatar shi.
Ana fita da Ummu Suleim motar kawo amaryar Hussein na shiga gidan, kan ta a qasa, ta shige motar da Musa ya aiko dan daukan ta, Innonin ta na tsokanar ta ta matsu ta tafi dakin miji,ba ta kula da abinda suke fada ba,ta zauna ta lumshe idon ta,zuciyar ta na quna,hawaye na zuba a idon ta, har motar ta fara tafiya bata waiga ba, su na fita ta fara kuka sosai, rayuwar ta tun ta yarinta ce ke bijiro mata, haka rayuwa take,kowacce macce akwai lokacin ta na barin gidan su, komai dadewar ta a gaban iyayen ta,indai Allah ya hukunta za ta yi aure to fa wata rana za ta bar gidan su.
Sai da aka kai Tasneem dakin Mammee suka gaisa, ta mata addu'a da fatan alkhairi, tare da samun zuri'a mai albarka, kyautar turaren wuta da humra ta bata cikin wanda ta sa aka yi wa su Ummu Sulem,domin kuwa Ummee ba ma tayi wannan tunanin ba, ita kan ta.ba wai ta damu da qamshin bane balle ta wa yaran ta.
Bangaren Ummee aka wuce da ita, ta na zaune cikin quncin tafiyar yaran ta, ga Noor tun da aka daura aure ba wanda ya sake ganin shi, har 'yan daurin aure da cousins din su Noor din suka tafi tai waya ko ya bisu ne, suka tabbatar da bai bi su ba,ko da tai ido hudu da matar Hussein yi ta yi kamar ba ta ganta ba, sai da 'yan uwan ta su ka taba ta, sanan ta amsa sallamar su, tare da gaisuwar ciki-ciki, wasu daga dangin Tasneem, sun zaci ko kishiyar babar Hussein ce ita.
Tunda ta amsa ta ja bakin ta ta tsuke, sai 'yan uwan ta ne suka ma amarya nasiha,sannan suka raka su har bakin mota,Hussein suka tarar a motar dan haka aka danna amarya gefen angon ta, sauran matan suka duru a mota biyu da ta rage, wasu kan wasu, kamar dole, haka suka isa gidan amarya da misalin 11:13pm,ba su wani jima ba aka kwashe su zuwa gida,'yan biyu ba wasu masu kwashe-kwashen abokai bane, kusan su ne abokan junan su, dan haka dikkan su su kadai suka shiga dakin amaren su.
Bangaren Umaimah kuwa qunshe take a d'aki ita da Aaseeyah, da alama ba ma mai shirin kaita na ta d'akin, ta yi kukan maraici ta godewa Allah, tun bayan daura aure, ba wanda ya ji labarin inda Noor ya shiga, balle a ce an gan shi, Ummee kuwa in an tambaye ta shin za a shigar da amarya bangaren ta, sai ta ce,
"Oho ina na sani, tunda dai ko angon ban gani ba nima"
Qanwar mahaifiyar su ce ta same ta Inna Rakiya, cikin fad'a da kuma hawaye a idon ta, ta ce,
"FATEEMA KIN BANI MAMAKI, A ZATO NA KE CE UWA,KUMA KE CE UBAN UMAIMAH,'YAR 'YAR UWAR KI MAI QAUNAR KI,BA DAN ITA BA BANA JIN ZA KI SAMU ZAMA A GIDAN NAN, HAR KI ZUBA ZURI'A, AMMA KE BUTULU CE MAI MANTA ALKHAIRI, KI DUBA YARINYAR CAN, YANDA TAKE KUKA,FUSKAR TA TA YI JAWUR,'DAN UWAN TA TUN DAZU YA KE ZUWA YA TAMBAYA TA DAINA KUKAN? KI GUJI BACIN RAN SHI, DA ALAMA YA NA BAKI GIRMA NE, IN KK BARI GIRMAN KI YA FADI A WAJEN SHI, HUMMM INA TAUSAYA MAKI,WADDA MUKE DAUKA BARE TA FI KI SON YARAN NAKI MA, KI NA NAN KI NA HAUKAN BANZA MARA MA'ANA, DAN NI BAN SAN INDA KK DOSA BA, BAN SAN QUNCIN ME KK BA"
Ita ma cikin fada Ummee ta ce,
"Wannan shi ne baqin ciki na Inna Rakiya,tunda kuka zo bikin nan, ba wanda kuke yabawa sai waccan mayyar, kamar ni ba qoqarin da na yi, duk kulawar da na bawa Umaimah ba wanda ya taba taimakan daidai da sannu ne, amma dan kawai ta yo mata siyayya, ta yo musu turaren wuta da humrah duk kun bi kun rude akai, ni kuma fa? Ban cancanci yabon ku bane?"
Shiru mutanen wajen sukai, ta cancanci yabo ko ma yaya ne, amma alkhairin Mammee ba abun kaudawa ido bane, su na wannan maganar Mammee ta shiga da sallama, domin wajen ta shiru, daga ita sai Mahboob, da ke cike da baqin ciki, ko da d'akin mai gadi za a sa Umaimah,ai ya kamata an shirya ta kamar yanda aka wa su Ummu Suleim an kaita dakin ta, ko da mijin ba zai zo ba,ina ma zai ga Noor da sai ya cire masa haqori a daren nan, Mammee ce tai ta tausar shi, da bashi hakuri.
Da sallama ta shiga, ta gaida kowa, sannan ta ce,
"Ni fa ban ga an kai wa d'ana amaryar shi ba, ko shirya ta ake ne?"
Inna Rakiya na qoqarin amsawa Ummee ta amshe,
"To uwar na'iya, babar d'an masani, sai ki zo ki shirya ta ai ki kai ta,"
"Ba gatse ki kai ba Fateema, zan kai ma Noor amaryar shi yanzu kuwa da ikon Allah"
Bata kula masifar da Ummee ke yi ba, ta shige dakin su Umaimah, Aaseeyah da Umaimah na ganin ta suka tafi da gudu suka rungume ta suna kuka, Aaseeyah kukan tausayin Umaimah ke addabar zuciyar ta, Umaimah kuwa kukan tausayin kan ta take, meye laifin ta? (Bada kan ki ga mijin da ba naki ba, walaqanci da tozarci ne ke biye da wannan jin dad'in na mintoci da ki kai a baya,namiji ya sha in ya lalata mace mace fa?)
"Mammee ya zan yi? Ina zan saka rayuwa ta na ji dad'i, ba dan kashe kai haramun bane a musulunci, da na dau rayuwa ta da hannu na"
Hawayen da ke qoqarin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 41