Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata a can Abuja, yar gidan IG of police mai suna Firdaus, tun da ta ji labarin Aliyyu bai taba aure ba, ta maqale mishi, firdaus irin matan nan ne masu aji, da kamewa,baqa ce kyakkyawa,ta na da qaramin jiki, amma ta na da shekaru, dan ta kai a qalla talatin da biyu ba aure, Aliyyu kuwa shekarun ta su ne daidai shi, kuma tsarin tarbiyyar ta ya mishi, dan haka ta na furta masa kalmar so bai watsa mata qasa a ido ba ya yi na'am da tayin da ta masa. Sai da su Aaseeyah suka sha biki, sannan Mahboob ya raka ta har cn yola, da kuka da alqawurran kiyaye soyayya da mutuncin su suka rabu. Aaseeyah ta maida hankali wajen karatun ta, da kiyaye dik abinda aka koyar da ita, a yanzu ta cire kan ta daga layin marasa qoqari da fahimtar boko kamar yanda ta jefa kan ta a baya. Wasu daga mazan da take haduwa da su sun zaci budurwa ce, irin masu kamun kan nan, sai da ta musu bayani ita matar aure ce sannan ta samu sauqin damun ta da suke. Ta shekara d'aya a yola ta dawo ta tafi service din ta, a Jigawa State, zaman ta a jiqawa zama.ne mai dadi domin karamci da mutuncin mutanen garin,ga shi ta na samun mutumin ta wato Nonon shanu,kullum da shi ta ke karyawa, da dare shi take sha kan ta kwanta, dan qaramin gida Abee ya kama mata,take zaune a ciki, ta na da maqota, fulani, a wajen su ta fara sanin ashe fullanci kala kala ne,dan haka sai da ta yi qoqari ta koyi nasu fullancin, da girkin gargajiya, ta na kyautata masu da sauke haqqin maqotaka,suma su na kyautata mata da sauke haqqin maqotaka. Shekarar ta daya ta tattara duk wani abu da ta mallaka ta bawa diyar mutan gidan wadda ake shirin yi wa aure bana. Tun kan ta tafi suka fara kewar juna, ranar da Mahboob ya je daukan ta kuwa da kuka suka rabu, suka mata tsaraba daidai da arziqin su. ************************** Aaseeyah ce ke sauka daga jirgin da ya dakko ta daga Abuja zuwa Kano, ita da Mammee Mahboob da Umaimah, a yau ne Aaseeyah Ibrahim Abdul mudalleeb Jordan ta zama cikakkiyar lauya, kowa ka gani cike yake da farin ciki,Ummee da su Yesmeen da Ummu Suleim na gida su na hada hadar bikin da Aaseeyah bata da masaniya akai. Ko da suka isa qofar gidan su gani ta yi akwai motoci da yawa, motar mutane kadan ta gane, ciki har da ta Amatullah, tunanin ta ne ya bata wataqila walima aka hada saboda kammalawar karatun ta da samun nasarar zama cikakkiyar lauya me lasisi a qasar Nigeria. Murmushi ta yi ta maqale hannun Mammee a nata, Mammeen ma murmushi ta yi dan ta fahimci Aaseeyah bata san komai ba. Ta na saka qafar ta cikin gidan 'yan uwan su na Yola suka rangada gud'a, kamar za su tsage mata kwanya, waqa suka dauka ta fullanci da ake ma amare. Gane.me ke faruwa da tai ne ya sanya ta kuka, har da shessheqa, bangaren Umaimah 'yan matan suka.wuce da ita, Yesmeen na ta tsokanar ta da cewar. "Kukan munahinci take yi, bakin su daya ita da angon ta, na tabbata ya sanar da ita komai" Da sauri Aaseeyah ta kalli Yesmeen, "Dama ya san da wannan abun shi ne bai fadan ba?" "Ke wa zaki yi wa bariki, halin ki ba wanda ban sani ba yarinya, sha kurimin ki, yau dai ba zaki kwana ma Mammee a gida ba, sai gidan ki, bawan Allah ai ya yi hakuri, hakan na nuna shi din waliyyin Allah ne indai ta wannan wajen ne" Ni kuwa na ce lallai yara baku san komai ba, ba ku san wane ne Mahboob ba. PAGE 52 Amarya da ango sun sha gayu na ban mamaki, ita kan ta Aaseeyah Mamakin yanda akai aka mata dinki cif-cif jikin ta ba tare da an gwada ta ba take yi, Mammee ce ta sanar da ita kayan ta aka bayar akai amfani da su. Bayan la’asar kuwa qawayen ta da ma wanda ba qawayen ta ba gaisawa kawai ake na makaranta har da na unguwa duk sun sha ankon da bata san sanda aka fidda shi ba, wasu sun saka abaya a saman atampar wasu hijabs, gwanin ban sha’awa, Amatullah ta kalla cikin hararar wasa ta ce, “Maman biyu na san wannan aikin ki ne,ki na can ki na karatun lauya a gefe guda ki na lauya yanda za a hada wannan gagarumar walima haka” Murmushi Amatullah ta yi, sannan ta zaro wayar ta ta nuna ma Aaseeyah ta ce, “Indai da wannan cikin qanqanin lokaci komai zai daidai da ikon Allah, ta waya duk na gayyaci qawayen mu na skul,kuma wa ya ce maki biyu zan haifa malama?” “Inshaa Allah” “Da kyau matar Shuwayya Shuwayya dole a maqale murya mana” Ummee ce ta shiga a hanzarce, ba a saba da saka hijabi ba, tsagun dinkin ya karkace gefe, ta wuyan duk ya yi zufa, daurin ya karkace, leqa kai ta yi ta kalli su Yesmeen ta ce, “To uwayen yara ana nan ana musu tawai, kun manta ma me ya kawo ku ko? Waccan siririyar me kama da bulalar in ba uzzura mata kukai ta yi ta gama shiri da wuri ba kun san har sai Malama Lubabatu Ahmad Usman ta tafi batai wa’azin ba” Aaseeyah ce ta kalli Ummee ta ga shin da wa take? Suna had’a ido Ummee ta kau da kai, sannan ta ce, “Ni dai ban kama suna ba, duk jarabar mutum kuwa dole yau d’aya dai ya d’aga qafa,maza mana ku fito kowa ya hallara,an gayyato Shaikh Sa’eed Sanusi Ahmad domin yi ma maza wa’azi shima” Murmushi Aaseeyah ta yi, mutan dakin da suka san takun saqar dake tsakanin Ummee da Aaseeyah suka fashe da dariya, itan ma kan ta tafi sai da tai ta dariya ta na tsokanar Aaseeyah, ta sake gyara mata sanya hijabin ta, sai da ta na gyara hijabin Aaseeyah ne Aaseeyahn ta kula da sanya hijabin Ummee, da ta fara dariya sai da ta ji haushi ta dungure mata kai ta fita. Amatullah,Umaimah,Yesmeen,Ummu Suleim,Tasneem,da Zahrah,(cousin) din su Aaseeyah,sune sika sanya ta a tsakiya suka fidda ta farfajiyar gidan da aka fidda dika motoci,sai a ranar suka ga girman gidan nasu sosai, idanun mutane kuwa akan su, Amarya ko a ina take daban take, ballantana wadda ta sha ado na musamman, hijabin ta mai cike da ado da kwalliya ya na sheqi da daukan ido,ya kai mata har guiwar ta, fuskar ta ta sha sassauqar kwalliya mai daukan hankalin mai kallo, Mahboob na zaune a kujerar dake kusa da inda su Amatullah suka zaunar da ita, ya na waya da Aliyyu, Aliyyun na bashi hakurin rashin samun damar halartar bikin,saboda ayyuka da suka masa yawa,shi kuma Mahboob na sanar da shi ba komai, in ya samu dama ya shigo kano suna gayyatar shi gidan su. Bai ji qarshen maganar da Aliyyu ke masa ba, saboda ya tattare hankalin shi kan amaryar shi,zuqatan su na bugawa a tare, tun kallon farko da ta masa bata sake kallon shi ba, amma hoton fuskar shi na zane a zuciyar ta, ta tabbata har abada ba zai goge ba. Ya fito a sak balaraben shi, dik mazan shigar farar jallabiyya suka yi da dan abun nan na larabawa, (mi suna nai ma? Lols) sai dogon wando fari. Mahboob ma irin shigar ce a jikin shi, amma tashi daban ce, kowa ya kalla sai ya kuma, baqin takalmin da ya sanya ya fito da dogayen yatsun qafar shi, wanda a wannan lokaci idon Aaseeyah ke kan su,hannun shi ya sha tsadadden baqin agogo da zoben zallan azurfa mai baqin dutse mai kyalli, maida idanun ta ta yi saman hannin nashi guda daya da ya dora a saman cinyar shi ta na kallo, kamar daga sama ta ji an dan daki kafadar ta, sannan ta ji muryar Yesmeen na cewa, “Dan Allah ki bar kallon shi haka, kowa na kallon amarya na qarewa ango kallo kamar ba tare za ku kwan ba yau, shi kuwa kamar ya cinye ki da ido,ohh wadannan jarababbun ma’aurata ba za su bar mu ma shiga bangaren su ba da alama” Murmushi kawai Aaseeyah ta yi ta sauke idanun ta qasa, ba da jimawa ba kuwa malaman nan biyu suka fara kwaroro addu’o’I daya bayan daya, tare da wa’azi a kan zamantakewar aure, da zama da maqota, dangin miji, tarbiyyar yara,da kyautata d’abi’a,kyautata zuciya,da ruhi dika. Sun tabo mahimman abubuwan da suka girgiza Mahboob,suka tsorata shi suka sanya shi tuna rayuwar shi ta baya,akan abinda ya yi wa Aemana,nan da nan kuwa tashin hankali ya shige shi,zuciyar shi ta quntata,idanun shi suka fara zubar da hawayen nadama da dana sani, shin a wanne hali take? Ta yafe masa kuwa? In ya haihu shima kenan sai an yi ma na shi yaran abinda ya yi wa Aemana? “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un” Ita ce kalma daya da Mahboob ke maimaitawa, maza da mata da dama a wajen sun koka saboda wa’azin da suka ji, zuqata sun raunana, wanda suke zunubai irin wanda akai wa’azi akai da wanda ma ba su yi,jiki ya mutu murus,sai kwadayin rahamar Allah kowa yake. Kiran magrib ne ya sanya aka yi addu’a aka tashi taro, alwala kowa ya yi aka yi sallah a wajen gwanin ban sha’awa, sahun mata na bayan na maza, bayan an gama aka dinga kawo abinci kala kala,da abin sha kala kala, mutane sun ci sun sha sun kuma yi guzuri da abinci,da har ‘yan gajen hakuri sun fara cewa da sun idar da sallah za su tafi, an gayyace su walima ko ruwa ba a basu ba,ga daga masu hankali da akai da wa’azi ,suna ganin dha’ami suka baje, suka dinga kwasar girki. Wajejen tara na dare wasu sun tattafi,Mahboob na ta son kebewa da Shaikh Sa’eed, amma bai samu dama ba, ganin ya na tare da su Abbu suna cin abinci, ya kasa saka komai a cikin shii ya na son ya masa tambaya,wayar shi ce ta fara qara, kira ne daga manager’n branch din kamfanin DANGOTE da yake aiki ya kira shi, dan yi masa murna, ya tafi amsa wayar shi kenan Shaikh Sa’eed na wucewa da tawagar shi da suka yo masa rakiya, Malama Lubabatu Ahmad Usman,dake ita ta fara wa’azin ta riga kowa tafiya, dan mace ce mai iyali. Ya na dawowa ya hau dubawa ya ga bai ga inda Shaikh Sa’eed yake ba, tashin hankalin cikin zuciyar shi ne ya bayyana a fili, Abee ya rankwafa kunnen Noor ya masa rad’a, d’ag kai Noor ya yi daga cin abincin da ya maida hankali ya na yi, ya kalli inda Abee ke masa nuni, ganin tashin hankali a fuskar Mahboob ne ya sanya shi tsame hannun shi a abincin, abokan aikin shi na masa sallama da kai kawai yake amsa su, wasu na tambayar shi ko lafiya? Sai dai ya ce masu “Lafiya qlou” Noor ne ya dafa shi,ya na juyawa suka hada ido sai ya ji idanun shi sun kad’a sun sake jawur dama kuka ya yi da wataqila zai ji dadin zuciyar shi. “Yau ce rana mafi mahimmanci da farin ciki a gare ka brother,me ya ke damun ka da ya qi boyuwa a zuciyar ka har ya bayyana a saman fuskar ka haka?” “Haka ne ya kamata ya kasance Noor, amma a yanzu haka ina cikin tashin hankalin haqqin mutum akai na Noor, wa’azin da akai ya farkar da ni daga baccin da nake,Noor ina wannan malami da ya fadakar da mu yau game da haqqin mutum akan d’an uwan shi mutum?” Cikin tsananin damuwa Noor ya dan ja Mahboob gefe, inda ba mutane, “Kar dai ka ce min….ko..ka taba…kashe wani?” “Subhanallah lala, ban taba kashe kowa ba,subhanallah, Noor lokaci na tafiya ka sanar da ni inda malamin nan yake” “Kwantar da hankalin ka, ni na kawo shi, aboki na ne, wajen shi na yi karatu ai,gobe ma sai na kai ka wajen shi” “Dan Allah ka kai ni yau mana, tambaya kawai nake so na masa” “Haba ba zai yu na kai ka yau ba, unguwar su da nisa, kafin muje dare ya yi sosai, kuma yau dole a gidan ka za ka kwana, ango ka ke, ba wani maganar zuwa ko ina,” Cikin wasa Noor ya qarasa maganar shi,amma Mahboob ya ja rigar shi cikin tsawa ya ce, “Me ya sa ba zaka gane ba ne, ina buqaar ganin shi yanzu!” Cikin daga gira da qimtse baki Noor ya dakatar da Mahboob ya amshe wuyan rigar shi, sannan ya zaro wayar shi, ya dinga kiran Shaikh Sa’eed ana fada masa network Busy, sun jima a haka,Noor ya ce, “You see, he is a very busy man, ka bari gobe na kai ka” “Ok Allah ya kai mu,dan Allah kar ka karya alqawari,” “Inshaa Allah” Har Noor ya tafi ya na mamakin yayn na shi. Bayan kammala walima,’yan uwa da abokan azziqi da dama an shirya dan yi wa amarya rakiya gidan ta, masu mota sun tafi marasa mota an kai su, wasu daga can za su wuce gidajen su,wasu nan za su dawo su kwana washe gari kuma kowa ya kama hanyar garin su. Amarya na ta sheqa kuka, tun Ummee na tsokanar ta ita ma sai da ta fara kuka, tare da fada mata za ta yi kewar abokiyar fadan ta. Mammee mace mai dauriya, addu’a kawai take a ran ta, tare da kiran sunayen Allah tsarkaka kyawawa,ta na neman Allah ya taimake ta, kar ta yi kuka,domin Aaseeyah ta bama kowa tausayi,tunda take in ba dan da ta girma ba harkar service da zuwa law school bata taba zuwa gidan kowa hutun kwana biyu ba ballantana sati d’aya, ko da yaushe ta na gida,sai gashi yau za ta bar gidan, dama bata bari an sake mata wata kwalliyar ba balle ta bata, kaya ne dai aka sauya mata na alfarma, masu ji da kyau da tsada,kaya irin na larabawa, sai ta fito sak balarabiyar,qamshin jikin ta kamar manna shi akai a jikin nata, ko taba ta mutum ya yi sai hannun shi ya yi qamshi. Ta na cikin mota ta na waigen Mammeen ta ta na sake zillo da kuka,Umaimah sai kare dogon cikin ta take kar a naushe mata shi, sai da motar ta bar gidan ta daina juyawa, suna tafiya Mammee ta shige bangaren ta ba wanda ya kula, ta fada dakin ta ta rufe, bakin gado ta zauna ta fara rera kuka mara sauti. Ranar da take ta tsoro ta zo,ranar rabuwar ta da Aaseeyahn ta, wadda ta fi so da qauna sama da dikkan yaran ta, jin Aaseeyah take kamar wata dangin ta kwalli daya da ta rage mata a duniya, maraici ne ta ji ya lullube ta,qanqame jikin ta waje guda ta yi, ta na zaune ta na kuka aka bude qofar, da sauri ta juya ta na qoqarin goge hawayen ta, ta bayan Abee ya rungume ta, dan motar su Aaseeyah na fita, ya isa gaban matan da suka rage basu je ba, ya ga bata wajen, tausayin ta ya tsarga zuciyar shi, shi ne dalilin da ya sa ya shiga dan ya lallashe ta. “Shiiiiii, kar ki kuka akan abun farin ciki,ki godewa Allah, ya bamu dama mun aurar da ita lafiya ba tare da ta jawo mana magana ba, ki sanya musu albarka, da fatan samun jikoki nagartattu” Wani irin kuka mai maqaqi ne ya tokare ta, ta juya da sauri ta rungume shi sosai, bai hana ta ba sai da ta yi mai isar ta sannan ta goge hawayen ta ya na taya ta, murmushi sukai a tare suka zauna bakin gado, sannan ta ce, “Ka tuna sanda ta fara takawa, ta na sanye da wani pant kalar blue,hancin ta duk majina ina son in share mata,kawai ta bamu.mamaki ta miqe ta na takawa” Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar ta da hannu daya, ya sake maqale dayan hannun nata cikin nashi, “Kwarai na tuna, har ki kai ta tsalle garin murna ki ka zubar da kunun ta muka fadi gaba dayan mu ba, ina tuna sanda ta fara zuwa bangaren Fateema,ta ajiye meye masunan abun nan na kwalamar ku na mata,kanti… “Kantin gana ake cewa,ta dakko ta gudo Fateema ta biyo ta a guje, ita ma ta kwasa a guje, sun jima suna zagaye gidannan, kafin ta kama Aaseeyah Aaseeyah ta cinye tass,ta na kama ta sai ta ce, ‘na dai cinne daci abinci’ “(na dai cinye daki abinki) Dariya sosai suka yi, haka sukai ta tunawa da quruciyar ta wani su yi dariya, wani su yi salati da jinjina rashin ji irin nata, cikin murya mai sanyi Mammee ta ce, “Ka na ganin da a ce Zainab da Yayah na da rai za su yarda da wanan hadin auren kuwa?” “Me zai hana? Zainab fa na da kyakkyawan hali, kishi ne kawai da hangen abinda wani ke da shi shine matsalar su dika su biyun, na tabbata in da Yaya na da rai arziqin mu zai bunqasa sama da haka, dan ya fimu nasibin kasuwanci,ga Mahboob d’anta ne babba na tabbata in ta ga ita ce a sama zata sakko komai ya yi daidai, balle ma yaya sai ya fi kowa farin cikin hadin nan” “Koh?” “Kwarai, dan haka ki daina saka damuwar komai, ki ta ma kowa addu’ar nan taki ta alkhairi da kk saba kin ji? Bari na je wajen Yaya” “To inshaa Allahu, nima bari nai isha’I na je waje, ban sallah ba” “Sai na dawo, yau muma gidan zai zama mu biyu kawai” Dan kashe mata ido ya yi, ita kuma cikin jin kunya ta ce, “Da saura dai, ka manta akwai baqi?” “Kashhh” Zai magana ta fada bayi ta na murmushi, mijin ta sam baya tsufa indai wajen soyayya ne. A gidan Amarya Aaseeyah kuwa…….. Sai hannu na ya gaji a daidai nan TAUBASHI PAGE 53 Yesmeen da Tasneem sun gama sake gyara gidan amarya bayan kowa ya tafi, dik da qarfin aikin Yesmeen ce,Tasneem sai shegen qiwa da lalaci, Aaseeyah na hankalce da ita, dan guntun tsaki ta yi, a ranta ta ce, 'Banda lokacin ki yanzu, ta kaina nake,amma zamu hadu ne,sai na gyara maki zama matar nan' Banda zubar da shara da karkade kujeru ba abinda ta yi amma fadi take ta na kuma wa, ita ta gaji. A hanyar ta ta zubar da shara ta biya kitchen ta debo lemo da snaks na cikin garar da aka kawo wa Aaseeyah, ta zauna yaraf ta na ci,haihuwa d'aya duk ta lalace, an san ba kowa ke da jiki mai kyau ba,wata da ta haihu shikenan duk wani kyaun surar ta yake komawa baya, amma in mace na gyara ana samun sassauci,Tasneem ba wannan gyaran, in ka zauna kusa da ita sai ka yi hakuri, daga nesa kam lafiya lafiya, amma da ka matsa warin baki ko na hammata zai tashe ka, amma a haka take da shegen son a ci soyayya. Yanzun ma ba abinda take bayan zuba surutu akan yanda Aaseeyah ya kamata ta na sarrafa Mahboob,tun Aaseeyah na sauraron ta har ta bata rai,ta kasa jure shirmen Tasneem, Yesmeen na kula da haka ta fara jan Tasneem akan su tafi dare ya yi,dan in ta qara minti d'aya Aaseeyah ta fashe ba zata ji da dad'i ba,ba dan ta so ba,suka yi wa Aaseeyah sallama suka tafi, har za su fita Aaseeyah ta kira sunan Yesmeen a shagwabe, tare da tura lips din ta na qasa gaba, idanun ta sun kawo ruwa, "Yanzu tafiya za ki yi ki barni?" "Ki yi hakuri dear sis,gobe zan dawo," "Nima zan shigo goben kinji" Tasneem tai katsalandam a maganar su, "Ni kar ki wani shigo min,ki tsaya ki ji da mijin ki" Dan yaqe Tasneem ta yi, bata ji dad'in gwale ta da Aaseeyah ta yi ba,hakan kuwa ashe ba qaramin bata ran ta ya yi ba, cikin yaqe ta bar gidan ta wuce nasu. Da kyar Yesmeen ta samu ta lallaba Aaseeyah ta wuce itama,fitar ta da minti biyar Mahboob da su Noor,Hassan,Hussein,da wani abokin shi Suhaib da ke wajen aikin su suka rako shi. Suna tafe suna dariyar yayu za su siyan bakin qanwar su,Mahboob dai murmushi kawai yake, daga baya Noor ya dinga jan shi da hira da tsokana, a qoqarin shi na kawar masa da koma meke damun shi a zuciya, wannan daren ya na da mahimmanci a wajen kowanne mutum,ba ya son ganin yayan nashi sukuku haka,ya kuwa samu nasarar sanya shi nishad'i,dan har fadi ya ke, "Ba mai shiga min gida, duk a bakin qofa za ku tsaya,a rabu anan, inna shiga na siyo bakin ta ko nawa ne na leqo ku ban kudin na kai mata" Dariya sosai suka dinga yi har suka isa gidan. A parlour suka zauna, Mahboob ba shi da niyyar kiran amaryar shi,sun yi duk tsokanar da za su yi sun gama amma ya qi kiran amaryar shi, ledar da suka taya shi riqowa suka bashi, Noor ya ajiye kudi kimanin dubu ashirin,ya ce gashi ya sai bakin qanwar shi,raka su ya yi har bakin qofa, Hussein ne ya dan leqa cikin parlourn ta qasan hannun Mahboob ya ce, "Ko kallo daya yanzu ba zamu ma qanwar mu ba" "Mata ta ce, tafi wajen taka, sai da safen ku" Rufe qofa ya yi,Noor da Suhaib suka tafi, a motar Noor din. *************************** Bacci ya dauke ta ko da ya shiga, tsayawa ya yi ya na qare mata kallo kamar a ranar ya fara ganin ta, fuskar ta ta yi ja musamman ta hancin ta, saman idon ta,da lips din ta, alamu ne da ke nuna ta sha kuka,murmushi ya yi ya zauna a kusa da ita, tare da riqe hannun ta,zoben da ke sanye a hannun ta ya fara murzawa,tun a sannan ta farka,amma tai luf, idanun shi na bin zanen ja da baqin lallen da ke dogayen yatsun ta, bakin shi ya kai yatsan ta manuni ya sumbata, cikin sanyin murya ya fara magana,cike da dana sani da tausayin kan shi. "Da na san ke ce zaki zama mata a gare ni da ban bata rayuwa ta da ta wata ba a baya,da na jira ki,baki cancanci miji kamata ba, kin cancanci mutumin kirki kamar ki, wanda bai taba aikata laifi irin nawa ba ki...." Bai zato ba bai tsammani ba ya ji muryar ta da ta dusashe saboda kuka ta ce, "Me ka aikata a rayuwar ka har ka ke ganin ban cancanci auren ka ba?" Da sauri ya saki hannun ta zai tashi ta kama nashi hannun ta miqe,tsayawa ta yi a gaban shi, fuskokin su na daf da na juna, qoqari take su hada idanu amma yaqi yarda ya kalli idanun ta,kauda kai ya yi sannan ya taka zuwa bakin window,ita ma tsayawa ta yi a bayan shi, hawaye suka fara sauka mata,shessheqar kukan ta ya ji, ya juya cikin damuwa, lallashin duniya ta qi shiru, ga kan ta ya dau zafi saboda kukan da ta ke ta yi, ita dai sai ya sanar da ita me ya aikata,ba bata lokaci ya fara bata labarin rayuwar shi a Jordan,ta ji tashin hankalin da bata taba zaton zata ji irin shi ba all her life. Wanne laifi ta taba aikatawa Allah ya jarabce ta da auren miji wanda ya taba aikata zina? Wanda ya lalata rayuwar mace 'yar uwar ta? Hakan kenan na nuni da Allah na iya jarabtar bawan shi da abinda bai aikata ba domin ya gwada imanin shi?Jin tashin hankalin ya yi yawa, kawai sai ta fara tasbihi da roqon Allah sauqi a zuciyar ta, Ganin ta shiga cikin dimuwa da tashin hankali ne ya sake jefa shi cikin damuwa da danasanin bai sanar da ita ba, "Aaseeyah na rantse maki bayan Aemana ban taba aikata zina ba,kuma akan ta na gama aikata zina, na tuba tuba na gaskiya,amma na san hakan ba yana nufin ni din mara laifi bane,gani a gaban ki duk hukuncin da ya dace dani ki min" Sakamakon kiran sunayen Allah da ta dinga yi, sai ta ji sauqin bacin ran da ya taso mata,sai ya bata tausayi, yanda ta ga ya na kuka,jikin shi na rawa damuwa ko ta ina ta bayyana a tattare da shi,cikin gajiya da kukan ta fara magana. "Irin wannan laifin Yah Mahboob ba abun alfahari bane da bawa zai aikata ya dinga fada,duk da na san ni na matsa maka ka sanar dani,amma da ka ke fadin zaka samu Sheikh Sa'eed akan maganar ba dole bane, babban abinda ake buqata in bawa ya aikata zunubi ya fahimci laifin da yake aikatawa haramun ne, sai ya tuba, tuban da yake

Chapter 33 of 41