sakkowa Mammee ta mayar, ta ce,
"Kin san ina ran naki yake ne Umaimah? A ina aka dasa maki shi takamaimai?"
"Ah ah" Umaimah ta furta cikin tsananin kuka.
"Kinga kenan, ba naki bane balle ki dauka, Allah shi ya saka maki rai, shi ke da ikon cire maki shi a lokacin da ya ga dama, daukan abinda ba naki ba ya na da hukunci mai tsanani, dan haka kar ki sake wannan tunanin kinji? Dalilin da ya sa kk ga ba a yi haramar kai ki gidan mijin ki ba, ganin ba wani waje bane na daban, sannan tun safe da aka daura aure ba a sake ganin Noor ba, kinga kenan hankali ba a kwance yake ba, amma yanzu zan kai ki da kaina"
Kallon ta Umaimah ta yi da sauri ta ce,
"Mammee dan Allah a raba auren nan,ba na jin akwai kyakkyawan abu da ke jira na a cikin shi"
"Allah ne kadai ya san wannan, ke naki hasashe ne, tunda ba ke kk tsarawa kan ki rayuwa ba ba zaki san me zaki tarar ba sai kin je,oya shiga ki watsa ruwa da sauri, ki alwala ki fito"
Tura ta bayin ta yi, ta rufe qofa, sannan ta ma Aaseeyah fadan kukan da take, ta na tsaka da hada ma Umaimah kayan ta, da fidda mata da wanda za ta saka, 'yan uwan su Ummee su biyu suka shiga, Inna Rakiya da Inna Ubaidah (Sis Ubaidah) su ne suka gyara amarya, suka mata kwalliya mai kyau, ta yi fess kamar ba Umaimah ba, ta na so tai kuka Mammee ta ce in ta sake ta bata kwalliyar ta sai ta rankwashe ta, dariya sukai ta yi, Aaseeyah ta ware ta dinga ba ma Umaimah labaran abun dariya, ba a jima ba ta fara sake ran ta.
"Kar ki damu 'yar uwa ta, ni zan taya ki zama har mijin ki ya dawo,"
"Ban yarda ba, wa ya fada maki yanzu ana al'adar kwana a gidan amarya, wannan ai da ne,"
Aaseeyah na son ta kawo uzirin za a bar Umaimah ita daya, Mammee ta zare mata ido,tura baki ta dan yi gaba,sannan ta nade hannayen ta, laffaya yaluwa da ratsin golden aka nade amarya da ita, Umaimah ta fito sak balarabiya, sai yanzu ta ji lallai bikin ta ake, kallon Mammee kawai take da irin kallon da d'iya ce kawai za ta wa mahaifiyar ta, Ummee ta rasa wannan damar, 'yan uwan su Ummee na kallo Umaimah ta rungume mammee ta na zuba mata kalaman godiya da soyayya kamar ita ta haife ta.
Takaicin Ummee ne ya kama su, me ne ne aibun Mammee da ba ta qaunar ta? Nan suka gano kishin faccaloli ne kawai ke damun ta, Mammee ta fita iya komai, ita bata iya komai ba, kuma ba ta so a yabi Mammeen.
Ba su suka kammala shirya amarya ba sai wajen sha biyu da 'yan mintuna, na dare, kan Umaimah a duqe, Mammee da Inna Ubaidah suka tsaida Umaimah a gaban Ummee, durqusawa ta yi, ta kasa furta komai, dan bata san me zata ce ba, hawaye ne ya gangaro a idanun ta, ya sauka a saman hannun ta da ya sha lalle,Ummee na ganin hawayen Umaimah sai zuciyar ta ta karye, tunanin 'yar uwar ta ya bijiro mata, wani irin kuka ta fashe da shi, sannan ta ja Umaimah jikin ta, ta na furta kalmar,
"Ki yafe ni Umaimah, ki yafe ni domin Allah, ba dan halayya ta ba, in dan hali na ne ba mai yafe min, amma ki dubi Allah ki yafe min, na cutar da ke ba tare da laifin ki ba, ban kula da ke ba, ban kula da zumunci ba,amma ki yafe min domin Allah, ban taba neman gafarar kowa ba bayan Allahn da ya haliccen, amma yau ina neman yafiyar ki, ki yafe min"
Kuka suke sosai, da kyar Umaimah ta furta ta yafe mata saboda kuka,da kan ta ta shiga gaba wajen fita da Umaimah zuwa bangaren Goggo Aysha, wato kakannin su,nan aka gyare masu tass, ya sha kayan zamani, sabbi fill, har bakin gado Ummee da Mammee suka ajiye Umaimah, Aaseeyah na gefe ta na share hawaye, ko ba komai ta ji dadin neman gafarar Umaimah da Ummee ta yi, Mahboob na tsaye daga can wajen parlour, ya na hango shigar su, idanun shi sun taru da hawaye, ya so ya gana da qanwar tashi kafin a shigar da ita, ya san za ta so ganin shi ita ma, amma ba komai, fatan alkhairi ya dinga mata, ya na jin motsin fitar su Ummee ya rabe a gini.
Bayan sun koma ne ya kula Mammee ba ta fita ba ita da Aaseeyah, dan haka ya fada da sauri, Umaimah na ganin shi ta nufe shi da dan gudun ta ta fada jikin shi, kyakkyawar tarba ya mata, kamar zai tsaga qirjin shi ta shige, lallashin ta ya dinga yi, sannan ya mata nasiha, da nuna mata mahimmancin hakuri,a qarshe ya ce duk abinda za ta yi ta dinga hango cewa da ita ce Mammee ya zata yanke hukunci akan abu? Mammee ta ji dadi sosai da ta zama madubin da za a duba nagari, abun ya sa zuciyar ta nauyi, dan haka ta fita ta na share kwalla, Aaseeyah na ganin Mammee ta tafi ta nufi hanyar fita ita ma, dan bin bayan ta, da sauri Mahboob ya ma Umaimah sallama ya bi bayan Aaseeyah, dan ya tabbata a tsorace take, banda bangaren Ummee da ke da mutane gidan ya dau shiru, sakamakon da dama ana gama daurin aure yawanci suka koma, manyan kawai aka bari, suma ba su wuce mutum bakwai ba.
Kanta take leqawa waje, saboda tsoron fita ita daya take, kafin ta isa Mammee ta bace ma ganin ta.
Motsin shi a bayan ta ne ya tsora ta ta, qiris ta kwalla qara, ya damqe bakin ta, su na tsaye a haka, su na kallon kwayar idon junan su, suka ji bude gate, sake mata baki ya yi, suka fita a tare, Noor ne ya shiga, ya na sand'a, a bakin qofa suka tsaya, Aaseeyah na jin kamar ta je ta shaqo shi ta wurga shi gaban Umaimah, ta tilasta masa sai ya bata hakuri.
Baya ya ja a tsorace da ya kula da su a wajen,
"Daga ina ka ke?"
In ina ya fara, can ya ce,
"Daga wajen abokai na"
"Shi ne ka manta yau aka daura auren ka ka na da matar da ya kamata ka dawo gida da wuri domin ta ko?"
"Ba haka bane Yah Mahboob, ban san me nake tunani ba, ban san me nake ji ba, farin ciki ne ko baqin ciki ne, zuciya ta na cikin rudani,"
"Yah Noor wannan ba hujja bace, duk wani rudani kai ka saka kan ka, Umaimah bata da wata illa a rayuwar ta bayan wadda ka mata, kai ne sanadin shigar ta dik wani hali da take, in baka lallashe ta ka ririta ta ba, bai kamata ka guje ta ba, da baka lalata rayuwar ta ba, kai ka yi kadan ka zama mijin ta, sai mijin da ta zaba,Yah Noor baka da 'yanci ko damar cewa zuciyar ka na cikin rudani, kai ne ka bata komai, kai ne ka lalata komai, komai laifin ka ne,"
Mahboob ne ya riqe Aaseeyah da ke masifa kamar za ta daki Noor, da kyar ya ja ta gefe, ya raka ta har qofar su, sannan ya koma wa Noor,
"Ina ledar da ango ke kaiwa Amarya? Ba wani abu da ka tanadar mata? Noor ka ji tsoron Allah, ina tausaya maka in ba ka tallafi qanwata yanda kowanne miji ya kamata ya wa matar shi ba, saboda...saboda.." fuskar su kamar zata hadu da ta juna,saboda yanda Mahboob ya kusanta jikin shi da na Noor, cikin murya mai tsoratarwa yake magana. "Saboda in baka kula da ita ba, sai na karairaya qashin ka, na zubar, ka kiyaye,ba zan maka da sauqi ba Noor, in ka quntata ma Umaimah"
Gyada kai Noor ya dinga yi, a ran shi ya na ayyana ba dan masu gashin kaji sun tashi ba da ya je ya siyo mata, amma ta bishi bashi zuwa gobe.
Ko da ya dawo daga duniyar tunanin shi sai ya ga ba kowa a wajen sai shi kadai, a hankali ya shiga ciki, ta na kwance ta na bacci, zama ya yi a gaban ta, ya ji yanda cikin ta ke qugi, da alama ta na jin yunwa tai bacci.
Kitchen ya shiga, ya bude manyan drums na roba, wanda aka zuba kayan gara ciki, tun daga Yola aka kawo su mota guda, har su Ummu suleim duk an kai masu nasu.
Diba ya yi har da soyayyan nama, ya dauki ruwan roba ya shiga dakin, tada ita ya yi, ya na kame kame, dan bai son su hada ido,tausayi take bashi, miqa mata ya yi, sannan ya shiga bathroom.
Jikin sink ya tsaya ya na maida numfashi, tun fari kunyar Umaimah ce ta hana shi dawowa, sai yanzu ya ke jin tsanar rayuwar shi, tun ta na qarama ba ta san kan ta ba ya ke lalata ta, gashi yanzu za su yi zaman aure, a zaton shi auren kawai wasu igiyoyi ne da ake daurawa ma'aurata kawai marasa tasiri, sai yanzu ya ji qarfin igiyoyin sun dabaibaye shi, har ba ya iya numfasawa, jin su yake kamar igiyoyin qarfe, wanda ba zai iya motsi a cikin su ba.
Ashe yanda ya dauki aure da sauqi ba haka bane, aure daraja ne da shi, qima ne da shi, sannan ya na da daukaka, dole ya yi fada da mummunar zuciyar shi da ke ayyana masa tsanar Umaimah, tare da bijiro masa da soyayyar Aaseeyah, dole ya amshi wannan auren da hannu biyu, amma ta ina zai fara? Ya zai ya ba ma Umaimah hakuri? Domin kalaman bakin shi sun yi kadan, ba ya jin ya na da ajiyayyar kalmar da zata haqurqurtar da zuciyar ta,'yar qara ya sake tare da ture shower gel da ke saman sink din, sannan ya dafe fuskar shi da hannayen shi dika biyun.
"Da me zan baki hakuri Umaimah? Kalamai na sun yi kadan wajen furta maki kalmar hakuri"
"Ka gwada furtan kalmar hakurin ka gani,"
Da sauri ya juya, ya gan ta tsaye, kallon qasa ya yi inda take kallo, ya ga ya yarda shower gel din da ke wajen, ba tare da ya sani ba ma, qarar shi ta ji ta bude qofar dan ganin me yake yi, a tsorace ta bude, amma da ta ji kalaman shi, sai ta ji duk wani haushin shi ya kau a ran ta. *
(Abinda ka ke sooo)
Da guiwowin shi ya durqusa gaban ta ya na kuka, ya kasa furta kalmar hakurin ma, kama fuskar shi ta yi a hannayen ta biyu, ta na qoqarin hada ido da shi, yaqi bude idon shi,
"Na..naa..yafee..maka, ba sai ka furta ba..na yafe maka"
Idon shi na zubar hawaye, ya bude a hankali, ya na kallon ta, murmushi take yi mishi mai hade da kuka, ido cikin ido suke kallon junan su, cike da kulawa, Umaimah ce ke qoqarin miqewa tsaye, Noor ya riga ta, ya daga ta gaba dayan ta a hannayen shi ya rungume ta, tare da kissing duk inda bakin shi ya kai a jikin ta, ya na yi ya na furta kalmar,
"I am sorry my wife, i am truely sorry, ba zan taba iya wanke baqin cikin da na dasa maki ba, amma na maki alqawari, zan kula da zuciyar ki, da jiki da ruhin ki, ba zan bari hawaye ya zuba a idon ki ba, sai na farin ciki, zan shayar da ke zumar farin ciki, har sai kin ce Yah Noor ya isa haka,ban sa me na aikata mai kyau ba da Allah ya mallaka min ke, na godewa Allah da ya sa ni ne mijin ki ba wani ba, dan haka daga yanzu zan fara baki kulawa ta musamman, har sai na ji kin ce, ina son ka Yah Noor"
Dariyaa ta yi, saboda yanda ya kwaikwayi muryar ta a qarshe.
Dire ta ya yi, suka daura alwala, suka wanke bakin su, sannan suka koma dakin, sallah ya ja su suka yi, sannan ya ja masu kayan garar da ya debar masu, suka ci, suka qoshi, sannan suka sha ruwa, soyayya mai tsananin zafi Noor ya fara zabgawa Umaimah, wadda ta sanya ni fita a guje na fada dakin Aaseeyah gwauruwaaa.........
PAGE 31
A washegarin biki Aaseeyah ta koma makaranta, ta tarar qawar ta da ko gama sanin sunan ta batai ba ta tara mata dikkan note din da aka musu, ta na son mata godiya amma ta kasa tuna sunan ta, mazaunin su na kusa da na juna, ta kula matar na son qawance da ita sosai, duk da cewa ita din matar aure ce, irin sabon auren nan.
Aaseeyah da ta ga ta kasa tuna sunan ta kawai sai ta ce,
"Na gode sosai sister, Allah ya saka da alkhairi, kin taimake ni sosai, fashin kwana uku ba abu ne mai sauqi ba, dan ma na samu ina zuwa duk da hidimar da ta min yawa"
"Babu komai, kar ki damu, ai zaman taren kenan,ya hidimar bikin to?"
"Alhamdu lilLAAH, an yi biki lafiya, amare da angwaye kowa ya na gidan shi, hankali ya kwanta"
Dariya suka dan yi, matar ta ce,
"Allah sarki, dama haka rayuwa take, yanzu sauran naki kema,"
Aaseeyah ta dan ji kunya, dik da cewa matar ba ta wani girme ta sosai ba, amma ta ji nauyin ta sosai,ganin haka ne ya sa matar ta sauya akalar zancen nata,
"Kinga ni mutane na ganin kamar ba zan iya karatun lauya ba, duba da cewa na yi aure, ba su sani ba cewar aure ba ya hana karatu, kowanne irin karatu ne mai aure ta na iya shi, me yara ma na iya shi, sa kai ne abun, da kuma son abun,tare da irin niyyar da mutum ke da ita akan abu"
"Haka ne, Allah ya sa mu dace,"
"Ba ki nuna min hotunan biki ba,"
Nan fa Aaseeyah cikin fara'a ta zaro wayar ta, ta bude password,ta shiga Gallery ta hau nunawa matar hotunan biki, matar ta rude da ganin zuri'ar kyawawa, a hankali ta dinga tambayar Aaseeyah abubuwan da ya shafi zuri'ar su ta na gaya mata ita kuma ba wayo.
Daga qarshe matar ta amshi wayar Aaseeyah, ta na ta hilatar ta ta loda hotunan Aaseeyah a wayar ta,sannan ta bi cikin Xender din, wajen da akai sending abu ta goge duk abinda ta tura, Aaseeyah ta nutsu wajen duba karatun ta.
Ta na gamawa ta wa Aaseeyah murmushi ta bata wayar ta, tare da fatan alkhairi.
Ko da aka tashi mijin matar ne ya zo daukan ta, Aaseeyah ta gan shi da kayan 'yan sanda, nan take tunanin CP Aliyyu ya fado ga ran ta,kwatakwata ta manta da shi, bai kamata ba kuwa a ce ta manta da shi, by now ya kamata a ce ta qulla abota da shi, wadda zata sa kowacce alfarma ta nema a wajen shi ba zai qi ba.
******************************
"Yaya ga shi, ga alqawarin da na maka, ina fatan ta zama wadda ka ke jira, har yau ba kai aure ba,"
"Amatullah ki na da surutu, abinda na saka ki daban abinda kk min daban, ni na fada maki ina son ta ne?"
Dariya wadda aka kira da Amatullah ta yi, sannan ta miqa hannu ta dauki spring roll daya ta fara ci, ta ce,
"Yayah Aliyyu ba yanda za ai ka sa qananan yan sanda su na bi maka ita, dan su ga wa da wa take hulda da su, meye shige da ficen ta, sannan ka ce ba son ta ka ke ba, ni dai fatan alkhairi na maku, ba komai ba,...by the way, she is kind and beautiful i like her, i will keep her as my friend, dama bani da qawa....Yah Aliyy ba ka ganin it is very wrong ka sa a dinga bin ta kamar wat me laifi? In ta gane fa? Ta na da 'yancin maka ka a kotu, saboda sawa da kai a bita ba tare da wani laifi ba, bar ganin kana da muqami babba, itama 'yar qasa ce, kuma ni nan zan tsaya mata mu kada kai a kotu, tunda dai ba haka ake soyayya ba, kamar ka na jin tsoron ta kar ta kore ka ta ce ba ta yi, ka mata tsufaaa"
"Kin ji da shi dai, thanks anyway"
"No problemo Sire"
Alama ta yi da hannun ta ta sara mishi ta fice daga parlourn da ya yi matuqar qayatuwa.
Wata dattijuwa ce ta fito, baqa mai kyaun sura, da cikar ado, Aliyyu na ganin ta ya miqe ya isa gaban ta, tare da amsar food flask daya da ke hannun ta,ita kuma ta qarasa aje dayan a saman dinning.
"Mama na sha fad'a maki ki dinga hutawa, akwai masu aiki, amma sai ki ta wahal da kan ki,"
"Aliyyu in ban motsa jiki na ba ai sai wata lalurar da ta fi wannan ta samen, ciwon sugar ai na buqatar motsa jiki,kar ka damu, bayan haka, kana jimawa ba ka ci abinci a gida ba,waccan uwar surutun tun dazu ta min sallama sai yanzu ta tafi?"
Murmushi ya yi, ya fara kai lomar abincin da ya zuba a plate bakin shi, sai da ya cinye, ya na lumshe ido sannan, ya kalli Maman su da ke jefa masa tambaya kan tambaya,akan abinda kusan ko da yaushe ya zama mata kamar karatu,
"....imm yanzu ka diba fa tsakani da Allah, abokan ka kaff na da mata, wasu har da yara, ka tasamma talatin da takwas zuwa da tara, amma shiru ba bu ma budurwar balle mata, ba ka da wani buri a duniya ina jin da ya wuce maka aikin ka, ba ka da lokacin kan ka, ballanta na na neman aure, inna ce zan duba maka a dangi kai da mahaifin ku ku yi kamar za ku cinye ni danya, to na...."
"Dan Allah Mama ki bari na ci abincin nan ta d'adin rai, rabo na da abinci yau kwana biyu kenan"
Cikin tsananin damuwa Mama ta ce,
"Subhanallahi, ka ji ko? Ka ji ko? Da na san haka aikin d'an sanda zai maida kai da ban bari ka shiga ba, duk bautar da mahaifin ka ya yi wa qasa, har ya bar aiki bai wasa da cikin shi sam"
Dora hannun shi guda d'aya ya yi akan nata da ta dora a saman dinning din, ya ce,
"Mama, dan Allah ki daina damuwa,aure da mutuwa da haihuwa lokaci ne, dan haka sai sanda Allah ya nufa zan yi nawa, ko da nan da shekara nawa ne, sauri na ko jinkiri na ba shi da amfani, domin Allah ya riga ya tsara min komai, sai dai a wannan karon ina maki albishiri da cewar ni ma na sanya maganar a raina, ba kamar da ba da ko maganar ba na so na ji ki na yi, ki ci gaba da min addu'a Allah ya ban ta gari, ko a ina take"
"Ka yi hakuri da damun ka da nake, na damu na ga ka yi iyalin ka kaima, d'an kulawar nan, da tarairaya kaima ka same su, in ka dawo daga aiki za ka samu wadda zata debe maka kewar damuwar aiki a gida, amma a yanzu rayuwar ka ta zama, ina ka fito aiki,ina zaka aiki, me ka ke yi aiki,"
"Mama ki bar bani hakuri ba ki laifi ba, ke uwa ce, kuma kowacce uwa ta na nema wa d'anta abu mai kyau da inganci, abinda zai taimake shi, duniya da lahira ne, inshaa Allah komai ya zo qarshe"
"Allah ya sa"
"Ni na fita, mu na da wani mahimmin aiki da ya taso mana, akwai wasu masu laifi da aka kama, ana ta musu tambaya kala kala akan su bayyana sunayen wanda suke aiki da su, sun qi, ni har na fara gajiya ma, ina ganin zamu sake su, wataqila ba da wanda suke aiki, su ne dai 'yan iskan kan su"
"To Allah ya tsare, Allah ya bada sa'a, Allah ya yi taimako, ka dawo lafiya"
"Ameen mama"
Daukan wayoyin shi ya yi, ya gyara zanzaron shi, tare da sanya baqin gilashin da ya matuqar daukan fuskar shi mai dogo kuma siririn hanci, Aliyyu ba fari bane, kuma ba za a kira shi baqi wuluk ba, baqin shi na da kyau da sheqi,in ya saka kayan su na 'yan sanda, sai su masa kyau, kamar a jikin shi aka dinka su, basu matse shi ba,kuma ba su sake shi ba.
Ya na fita wani d'ansanda da ke qame a jikin qofar shiga, ya isa gaban mota da gudu ya bude masa, driver ya ja shi sai ofishin 'yan sanda..
Tun da ya isa ya zauna, wayar shi ya bude ya na ta kallon hotunan ta, dik da yawanci akwai wasu mutanen, amma ya kula da wani shi d'aya, duk hotunan ya fito, zai girme shi a shekaru, amma na hoton ya fi shi girman jiki, ga shi fari tass balarabe sosai, gemun nan kawai ya isa sace zuciyar duk wata mace, shafa habar shi ya yi, ya ji ba komai, sol, tsaki ya ja, ya ji kamar da ma zai iya aje gemu, tabbas da sai ya aje shi ma,
'Aliyyu kenan, bikin dangi ne fa, what if yayan ta ne fa? Uwa d'aya uba d'aya?'
"Kai anyaa?"
Qarar takun takalmi da qamewar wasu 'yan sanda guda uku da ke tsaye ne a gaban table din shi y dawo da shi daga duniyar tunanin da ya fad'a,a tare su ke tambayar shi ko me yake nufi da abinda ya ce? Basarwa ya yi, ya aje wayar shi, suka fara yin abinda ya kamata, amma ta na maqale a cikin zuciyar shi, ko da lumshe ido ya yi sai ya ga hoton fuskar ta a jikin idon shi ta na turo baki ta na shagwaba.
*******************************
Aaseeyah ta ji d'adi kwana biyu har ta je makaranta ta dawo, ba mai bin ta, ta sake jiki sosai, dan haka ba wanda ta sanar wa, karatun ta take ka'in da na'in.
Yau ta na gida ba ta je ko ina ba, dan haka ta hau gyaran d'akin ta, abinda Mammee ba ta zaci Aaseeyah za ta mayar d'abi'a ba ,wato kwalema, ita da komai ta d'auka a baya sai dai ta yar a duk inda ta ga dama, lallai lokaci ke sauya komai, ta na tsaka da gyaran kayan ta ta ci karo da katin da ta adana, murmushi ta yi, ta dakko shi, da wayar ta, kwantawa ta yi a saman gadon ta da ta gyara, ta daddanna lambobin wayar shi a ta ta wayar, saving ta yi da 'CP friend'.
Murmushi ta yi sannan ta ce,
"Aaseeyah da qarfin hali ki ke, Allah ciyya ciiiii"
Da muryar yarinta, sannan ta dire qasa, ta qarasa aikin ta.
Wanka ta yo, ta zauna shafa mai, ta na gamawa ta mulke jikin ta da humrah, sannan ta sanya turaren ta mai sanyi, ta sanya doguwar riga mara hannu, tare da daure gashin ta ta saka hula.
Fita ta yi riqe da wayar ta, cikin sake baki ta ke kallon su, zaune suke ana hira sama sama, da alamar rashin sabo, Hussein ke ta danna wayar shi, fuskar shi daure, shi ko d'an sauyawar nan ta angwaye bai ba sam.
Da sauri Aaseeyah ta qarasa kusa da shi, ta zauna, tare da riqe hannun shi d'aya,cike da murna ta fara magana,
"Yah Hussein yaushe kuka zo? Yayah Tasneem,amarya barka da yamma,"
"Barka dai, Aaseeyah, ya kk?"
"Lafiya qlou,"
"Yah Hussein ina wuni"
"Lafiya qlou, ai mun shigo na leqa dakin ki na ji qarar ruwa shi ne na dawo, na san wanka ki ke"
"Eh wanka nake, ya su Yesmeen, tare kuka zo? Ko dake ban ga yah Hassan ba"
"Ah ah, su suna gida, ni ce na matsa masa sai ya kawo ni mun gaisa, tunda ke ba ki je ba"
"Ayyaa mun gode sosai da ziyara, ki yi hakuri karatu ne ya yi wahala, kin san mu sabbin shiga, sai mun maida hankali,gashi dama ni kai na ba wani ja yake sosai ba, dole ina buqatar nitsuwa da maida hankali, gashi na dan yi fashi, komai zan koya daga baya ba kamar sanda aka yi a aji bane"
"Haka ne, Allah ya bada sa'a
Cikin daure fuska Hussein ya miqe, ya nufi kitchen inda Mammee take, Aaseeyah na kula da daure fuskar da ya ke in ya kalli matar tashi, basarwa ta yi, dan ganin ita ko a jikin ta.
Sai bayan magrib su Hussein
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 41