Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bar gidan ta nufo unguwar su Aaseeyah, Noor kuwa wani irin mummunan kallo ya ke bin Aaseeyah da shi, kallo ne na tsana, kallo ne na kin ci amana ta kin karya min qudiri na. Tunawa ya yi sanda suka dawo daga yawon bude ido, ya ajiye 'yan uwan na shi, ya parker motar shi, sun fito su na ta hira sai ya hango 'yan matan gidan kaf din su, ana zaune a babbar tabarma ana hira, gefe ga 'yan biyu can,da wasu daga sauran 'yan uwan nasu maza, su na ta hira, yawo ya dinga yi da idanun shi bai ga Aaseeyah ba, nan ya tambaya aka ce tunda ta raka qawar ta ba ta dawo ba, bangaren su Aaseeyah ya shiga da dabara ya duba tare da tambaya aka tabbatar tun azahar da ta bar wajen bata koma ba, nan fa hankalin shi ya fara tashi, bai sake komawa wajen 'yan uwan nashi ba, bangaren su ya shiga ya duba bai gan ta ba, har Ummee ta na fadin 'Aaseeyahn allura ce da za a nema a rasa' bai ce komai ba ya nufi gate, nan mai gadi ya ke sanar da shi inda ya ga sun nufa dan sai da ya leqa, kuma ya na qara leqawa akai akai, ya tabbatar su na wajen har lokacin, ya tabbatar ma da Noor ya ga sanda qawar ta ta ta wuce ita kadai bayan sunyi baya ita da Aaseeyahn sun je wajen Jubeir, kuma har awannan lokacin bai ga Aaseeyh ta koma gida ba, sannan motar Jubeir ba ta bar wajen ba. Cike da tashin hankali da qunar rai ya bar wajen, ya na isa bakin motar ya ga yanda Aaseeyah ke kuka Jubeir na magana da bacin rai ya ga sanda Jubeir din ya ja mayafin Aaseeyah, nan da nan ya fara dube dube, ya hango wani qaton dutse, bai tunanin komai ba ya buge glass din da shi...... Sun isa gida kowa fuska a daure, Aaseeyah na jin qafar ta a cikin gida, ta diba da gudu sai bangaren su, ta na shiga ta tadda Mammeen ta na kwashe abincin dare, qananan 'yan mata daidai shekarun ta guda biyu su na fita da shi,daya mai suna Surayyah ce ta kalle ta cike da mamaki, ganin yanda ta rungume Mammeen na ta ta na kuka,Mammee cikin tsananin damuwa ta juya tare da banbare riqon da Aaseeyah ta mata, fuskar ta ta daga ta na kallon ta, tare da share mata hawayen ta, "Aaseeyah me ne ne? Wa ya taba ki? Me aka miki, sanar dani, ki dai na d'aga min hankali da kukan ki" "Mammee..Ki yafe min, ba san sake tsallake magabar ki ba...zan dinga jin maganar ki," "Me ya faru, zaki fadan me ya faru ko sai na bige ki," Ran ta ya fara baci, ga wani irin tsoro da ta ji ya shige ta, me ya sami d'iyar ta sha lelen ta. Kallon 'yan matan Aaaseeyah ta yi sai ta nufi dakin Mammeen na ta ta kwanta a gado ta na kuka,ita ma bin ta tayi bayan ta basu umarnin daukan abincin da ya rage su tafi,ta na shiga ta ga Aaseeyah kwance ta na kuka, tsayawa ta yi a bakin qofa ta na kallon ta, cikin kuka Aaseeyah ta bata labarin duk abinda ya faru bata boye mata komai ba,da dukan da Noor ya ma Jubeir din, ta qarasa maganar ta da cewa, "Mammee dan Allah ki yafe min, ban taba zatan abinda kk hana ni inna aikata zai zamar min wannan matsalar ba,ba dan Yah Noor ya je ba da ban san me zai min ba, Mammee na ki yafe min, na miki alqawarin ba zan sake qin jin maganar ki ba" Lallashin Aaseeyah Mammee ta fara, dan kukan da take ya wuce hankali, ta tsorata matuqa, nasiha ta sake mata akan kula da kan ta a tsakanin maza, maza ba ruwan su, za su lalata mace ne cikin kwanciyar hankali, ba tare da tabon abinda suka yi ya manne masu a jiki ba a zahirance, mata kuwa tabon da suke dauka baida iyaka, nasiha sosai da qoqarin sake dasa mata tsoron kusantar maza Mammee ta mata, da kyar ta bata abinci ta karba ta ci, ba ta wani qoshi ba ta ture,wanka ta tafi dakin ta ta yi, sannan ta yi alwala tai sallolin da batai ba, magrib da isha'i, qin fita ta yi ta kwanta, ba dan bacci take ba, sai dai tunanin abinda ya faru dazu shi ke damun ta, 'Shin an samu wanda ya taimaka wa Jubeir kuwa? Ko dai sun tafi sun bar shi ya mutu a wajen? To ko zuwa za ta yi ta gani?' Tuna nin kar ya mutu alhakin mutuwar shi ya rataya akan su, ne ya zaburar da ita ta dau hijabi dogo ta sanya a kan rigar baccin ta ta fita riqe da wayar ta, ko da ta fita ba kowa tsakar gidan duk su na babban parlour ana cin abinci, Noor ne ya shiga gidan, cikin sauri, ganin Aaseeyah tsaye ta na danna waya cike da damuwa ne ya sa shi isa gaban ta, a nata wautar kiran wayar Jubeir zata yi, in an d'aga ta tambaya ta ji an dauke shi ko yaya? Hannun ta ya fizga ya yi lungun bangaren su Aaseeyan da ita, kwace wayar ya yi tare da kafe ta da idanun shi a cikin hasken da ba shi da wani yawa. "Wanne dan iskan kuma ki ke kira ku hadu yanzu a cikin daren nan?" Da sauri ta bude baki za ta yi magana, ya bige bakin nata da bayan hannun shi, yar qara ta saki, ya sa hannun shi a lips din shi tare da fadin, "Shhhh, stupid,wajen uban wa zaki na ce a daren nan?" Kallon qasan hijabin ta ya yi inda ta dage hannu ta sa a baki ta na hawaye,rigar baccin da ya gani iya guiwar ta ya sake tunzura shi, me ke damun yarinyar nan kuma, wajen wa zata da kayan bacci, lallai abun nata ya ta'azzara, ya kori wancan ta fito gun wani d'an iskan ko? "Wato iskancin naki yanzu ya koma har ki saka kayan bacci ki fito kiran wani qaton? Kowa na can na cin abinci ke kin fito ba wanda ya sani ko? Ok, idan iskancin ki ke so, bari ki gani," Kafin ta furta kalmar da ke bakin ta ya manna ta da jikin shi, abubuwan da Noor ya ke mata ba dan a tsorace take ba da ta yi maraba da su, a gigice ta ke shaqar numfashi, cike da tsoro ta tura shi baya,ta na son magana amma numfashin ta na mata wahalar fita, ganin haka ne ya sa Noor shiga hankalin shi ya tallabe ta, ta sake tura shi bata, kan ta a sama, numfashin ta na mata wahala,da sassarfa ta shige gidan su, dakin ta ta shiga ta kwanta a gadon ta, ta na maida numfashin da ya qi daidaituwa mata, ta kai a qalla minti takwas kafin ta samu damar fashewa da kuka mai tsanani, hannu ta sa ta toshe bakin ta, ta qanqame jikin ta, 'Yah Noor kallon 'yar iska ya ke min, bai tsaya ya ji uziri na ba ya yanke min hukunci, ta ya zan fahimtar da shi abinda ya ke zato ba gaskiya bane, ba zan taba iya abinda yake zargi na da shi ba? Shin zan iya sanar da Mammee abinda ya min ne ko na yu shiru? Shi da Jubeir wa ne ke son lalata rayuwa ta? Abinda Yah Noor ya min Jubeir bai min shi ba, wane ne ne bad guy a tsakanin su? Na tabbata laifi na Yah Noor ke gani shi ya sa ya ke min abinda ya ke min a matsayin hukunci, haka ake hukunta mai laifi???' (Yoh ina nissani? Wannan shi ne matsalar Cousin,zai aikata abu amma ana tsoron a fadi me suka yi, ko kuma ana ganin ma kwata kwata ba za a iya fada din ba, wata ma ba ta jin ya mata laifi, wata ma so take cousin din ya so ta ya taba ta, za ta iya mallaka masa jikin ta, cousin ba ya laifi a wajen qannen shi cousins, komai ya yi daidai ne, nadama sai ranar da aka kai mace dakin miji, ta ga bata kai darajar ta ba, sai ta hau kuka ta tuna cousin ya sa mata albarka kan aure na so ace Aaseeyah ta dau mataki tun yanzu) A haka bacci ya dauke ta, Noor ma dakin shi ya nufa, ya kwanta tare da yin ruf da ciki, ya na tuno santsi da laushin fatar Aaseeyah,ta na girma jikin ta na gogewa, 'Ba zan bari yarinyar nan ta rabawa gayu jikin ta ba, ina zaune gida d'aya da ita ban mori komai ba' Miqewa ya yi da nufin ya shiga bayi qofar dakin shi ta bude, kallon ta ya yi ya dauke kai, bai aje ta a wani matsayi ba da ya wuce abar hutawar shi, yau kuwa ba ya jin sha'awar komai da kowa in ba Aaseeyah ba. "Me kk zo yi Umaimah kin san fa yanzu akwai mutane gidan sosai ko" "Yah Noor kusan tun rana da ka fita ban sake ganin ka ba yau, shi ya sa na zo na maka sai da safe," "Ok, sai da safe kenan?" Shiru ta d'an yi dan ba haka suka saba ba, taku ta yi d'aya zuwa biyu, ya d'aga mata hannu, "Kinga Umaimah ki dinga abu da tunani mana, yanzu in wani ya shigo fa? Ki je kawai sai da safe zan zaga" Ba haka ta so ba, amma ba yanda za ta yi,yau a yayan ya fito ba a masoyi ba, jiki ba kwari ta ja masa qofa ta fita. Ta na fita ya saki siririn tsaki, "Yarinyar nan sai na mata sabon karatu, na ga alama ba ta san privecy ba,sabbin balaga sai a hankali," (Kai kuji min d'anneman Yah Noor d'innan wai sabbin balaga, to sannu tsohon balaga) **************************** Rana ta uku a cikin shagalin bikin sallar da suke rana ce da suke fita, gaba dayan su, a shiga gari, a je gidan Zoo, da dai wurare masu tarihi da mahimmanci da kyau, duk dan nishadi, da kuma cika shagalin bikin sallar su. Har qarfe sha d'aya Aaseeyah bata bar gado ba tun bayan da tai sallar asuba ta koma,kowa ya shirya, ban da ita, duk an firfita,motoci sun cika,kowannen su ya sha ado, na ban mamaki, daga mazan har matan,wad'an da ba za su ba su na can a babban parlour, Noor duk ya duba bai ga Aaseeyah ba, ya tambayi su Yesmeen sun tabbatar masa ba su gan ta ba a ranar baki d'aya, wayar shi ya sa ya hau kiran ta, a kashe wayar ta take nutsuwa ce ta gagare shi, hannu ya sanya a goshin shi, daga baya ya bude motar ya fita, bangaren su Aaseeyah ya shiga, ba kowa shiru, sallama ya yi ta dokawa daga can d'akin Mammee ya ji muryar Mammen ta na amsa masa, ba ta fito ba ta na daga d'akin ta ke tambayar, "Noor ne?" "Eh Mammee, barka da safiya" "Barka dai, ka na buqatar wani abu ne?" "Ah ah Mammee na leqo ne kawai mu gaisa" "Ina godiya, na fito wanka ne, shi ya sa ban fito ba, na gode da gaisuwa" "Ba komai Mammee, Abee fa?" "Ya fita shi da Abbun ku," "Ok to sai an jima" "To sai anjima na gode" Dakin Aaseeyah ya bude ya fad'a, ta na kwance ta na bacci, rigar baccin ta na da kauri dan haka ba abinda ya ke iya gani, sai qafafun ta da tudun qirjin ta, gashin ta na nade cikin hular da ta sanya kalar rigar ta,fuskar ta fess ba kwalliya sai tsananin kyau daga Allah,sunkuyawa ya yi a hankali cikn sand'a ya sumbaci kuncin ta,ya sumbaci lips din ta, ya saki murmushi, nutsuwa ce ta sauka masa da ya gan ta, ya kuma taba ta, a hankali ya miqe tsaye, ya zira hannun shi d'aya a aljihu, ya daure fuska, sannan ya tashe ta, ta na farkawa ta gan shi, ta hau neman abun rufa, ko da ta samu abun rufa har kan ta ta rufe, tare da fadin, "Yaaah Noor, me ka ke yi a daki na?" "Me kuwa zan yi a dakin ki, dalla ki tashi ki shirya mu tafi Zoo" "Banda lfy kai na ciwo yake ba zan je ba" "Allah ya sawaqe to, ki tashi ki wanka ki ci abinci ki sha magani yanzun nan, kar na dawo baki yi hakan ba, da na kai su zan dawo nima" "Ni dai kar ka wani dawo" "Ki ka ce me ne," Turo baki ta yi ta sauke abun rufar daga fuskar ta, ta na kallon gefe ta ce, "Ni ban ce komai ba, ku dawo lfy" "Ok, sai na dawo" Fita ya yi ya ja mata qofar a hankali, ita kuwa dira ta yi qasa ta na qunqunin ya fa fara takurawa rayuwar ta, ba kuma ta son hakan. Ko da ya fita su Yesmeen sun suqe dan haushi, Ummu suleim da ta bi su Hussein tuni sun kusan isa, su suna nan jiran Aaseeyah, babban abinda ya ba Umaimah takaici ba ta ga Aaseeyahn na biye da shi ba duk dad'ewar da ya yi,kuma bai masu bayanin komai ba ya tada motar suka tafi. Tunda suka isa Umaimah ta kula Noor sai shisshigewa wata Cousin din su ta bangaren Ummee Noor yake mai suna Zuhrah, Zuhrah ta girmi su Umaimah, gata mai manyan gabbai, ko ta ina a cike ya ke, ta fi su Umaimah wayewa da sanin duniya, ta na matuqar son Noor, ta so ita ma ya na mata irin son da take mishi, ita ma da kan ta koma da iyaye sun san da tarayyar su, amma tsaf ta gane waye Noor, d'an a sha soyayyar minti ne, dan haka ta ke biye masa, ba ta son damar ta ta wuce ta, wataqila a hakan ta samu damar sace zuciyar shi kafin su koma gobe. Ice cream suke sha, ita da shi, ta miqawa Umaimah wayar ta akan ta masu hoto, kwafa Umaimah ta yi a hankali kafin ta amshi wayar, ranta baqiqqirin, Noor kuwa kamar bai san Umaimah ba, haka yake nunawa, abun na mata zafi matuqa, in ba kowa har sunaye masu dad'i yake kiran ta da su na masoya, amma in da mutane kashi ma ya fi ta. Hoton ta dinga dauka a wulaqance, duk ba wanda ya yi kyau, ta na gamawa ta miqa mata wayar ta bar wajen su, wajen su Sumayyah ta nufa dan sune suke kusan sa'anni, ta na hango yanda Yah Noor ke shige ma Zuhrah, kamar ta je ta shaqe su su dika biyun ta ke ji, tunani ta yi dama ita ma zaman ta tayi a gida kamar Aaseeyah. ******************************* Da kallo ya ke bin ta,har ta isa saman gadon ita ma ta zauna ta na tura baki da shagwaba, pillow ta dauka qarami ta hau buga mishi a qirjin shi da ke bude sakamakon rashin rigar da ya zame mishi jiki in ya na gida, hannun shi na dama na riqe da abokiyar shi sigari, ya na busawa, gefen gadon d'an qarfen da yake saka toka ne, riqe pillown ya yi da hannu daya, ya ja ta jikin shi nan da nan Aemana ta kwanta a jikin shi ta na hawaye, bai ce mata komai ba har ta gama kukan ta ta fara gwada masa yanda ta yi kewar shi, biye mata ya yi, suka fada duniyar da malam ya hana ni fada.... Sai da komai ya lafa, ta na kwance a jikin shi, ta d'aga kai ta kalle shi, cikin harshen larabci ta ke masa magana, "Hal tahabanee?...madha ilay an af'al laka tahabanee?" (Shin ka na so na? Me zan aikata ka so ni?) Shiru ya yi, daga qarshe ya janye abun rufan da suka rufa da shi ya nad'e jikin shi ya fada bathroom domin yin wanka,Aemana kuwa rintse ido ta yi a daidai sanda ya rufe qofa, ta na jin wata zazzafar qaunar shi na sake shigar ta, ta dauka in ta yi fushi da shi, ta dauke qafa ya rasa wadda zai dinga rage ma kan shi sha'awar da ta kula ya na da yawan ta, zai neme ta, zai kewar ta, amma ta tabbatar a yanzu bai damu da ita ba, in ta na nan zai kwana da ita, in ba ta nan zai rayuwar shi ko ba ita, ta tsinewa ranar da ta fara haduwa da shi a makarantar su ta Jordan University of Science and Technology, da ta san haka yake kamar dutse da bata fada ma zazzafar soyayyar shi ba. Ta samu manema auren ta tun bayan da ta kammala karatun ta amma ta qi basu hadin kai, har ta fara aiki a ma'aikata d'aya da Mahboob sabida ta dinga ganin shi kullum, a rana in ta samu ya mata magana bai fi sau biyar ba, shi ma in ta takura masa ne zai mata fada akan ta bar abinda take mishi,ta sha gwada kuka ko zai tausaya mata amma inaa, ya na abu ne kamar ba zuciya a qirjin shi, gaba daya ta rasa dalilin da ya sa zuciyar shi take a kulle ba ya son ya bar kowa ya shiga, ta sani da dukkan alama akwai abinda ke damun shi, ta na ta qoqarin ta shiga rayuwar shi dan ta taimaka masa da quncin da yake ciki ya toshe duk wata kafa da zata samu shiga rayuwar shi. Wayar shi ce ta dau qara,kamar an saka ta, ta dauka, suna ta gani a jiki an rubuta Abee, hannu na qaiqayi ta dannan tare da kara wayar a kunnen ta, sallama Abee ya yi cikin muryar shi mai cike da Izza.......... 💅🏻 TAUBASHI (COUSIN) 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 10 Hannun shi da ke jiqe da ruwa ya miqa tare da amshe wayar ya kafe ta da kyawawan idanun shi masu cikakken gashin ido, girar shi baqa qirin ya hade waje daya saboda bacin rai, Sallama ya amsa wadda da dikkan alamu d'an uwan mahaifin nashi ya jima ya na masa sallama, cikin harshen larabci suke magana,daga baya Mahboob ya koma hausa. "Ina nan tafe inshaa Allahu qarshen shekara mai zuwa, so nake na kammala wasu abubuwa anan,akwai kadarorin Khaalah Lila da suke ajiye ina so na koma Ar-ramtha na siyar da komai na taho da dukiyar tunda ba ta da kowa,in ya so an raba gadon su anan din, don so nake inna dawo na dawo kenan, ba komowa nan" "Masha Allah, haka nake son ji, zaman ka anan kai kad'ai ya na damun mu dika, ba mu da kowa da zai kular mana da kai, ga 'yan uwan ka kowa na kewar ka, dan Allah ka yi maza ka kammala komai ka dawo gare mu" "Inshaa Allah 3am Ibraheem, jazakallahu bi khair, ina miqa gaisuwar barka da sallah zuwa ga kowa da kowa anan gida Nigeria," "Kowa da kowa zai ji, ga 3am Muhammad din ka ma za ku gaisa" "To ba ni shi" Ko da ya karbi wayar dan gaisawa da 3am Muhammad din shi ji ya yi an rungume shi ta baya, cikin ajiyar zuciyar da bai shirya ba, ya qanqame wayar, tare da amsa sallamar, sun gama gaisawa ya kashe wayar ya juya cikin matsanancin fushi ya wurga ta gefe ta fadi qasa cike da tsoro, nuna ta ya yi da yatsan hannun shi manuni, sannan ya bude baki zai magana, me ya tuna kuma kawai ya wuce ta ya koma bathroom dan yin wanka, ta so ace ya mata fada, dan ta san me ye a ran shi, ta so a ce ko zagin ta ne ya yi dan ta san haushin ta yake ji ko tsanar ta ya ke yi, ta kasa gane inda ya dosa, in ya na waya da yaren da bata sani ba ji take kamar da ta samu abinda zai mata tafinta dan ta san me yake fada ko za ta gane wani abu dangane da rayuwar shi,a kalaman shi ta ji ya kira Nigeria, ta na jin sunan qasar Nigeria, me ye had'in shi da Nigeria? Shekarar su kusan uku tare amma har yanzu ya qi ya bude mata zuciyar shi, wannan wanne irin tarayya ce mara suna, mara al'qibla? Janye mayafin rufar dake jikin ta tayi ta sake a qasa ita ma ta shiga bathroom din, ya kammala wankan shi ya na gyara gashin kan shi ta shiga, kallo d'aya ya mata ta madubi ya dauke kan shi, dan ya gama kuma da ita a yau, wataqila sai gobe, gani ta yi ba fuska, ba alamar sakewa dan haka wanka ta fara ta na zubar da hawayen qunar da zuciyar ta ke mata na tsananin so da qaunar Mahboob. Ko da ya gama shirin shi, ta fito sanye da bathrobe fara,ta daure kan ta da towel, kallon ta yayi, dan da alama ba ta da niyyar tafiya, kwana ta ke shirin masa a gida, cikin daure fuska ya kalle ta ya ce, "Ke nake kira ki shirya mu tafi cin abinci yunwa nake ji, daga nan ki wuce gida" Lumshe ido ta yi sannan ta ce, "Gida ba kowa, iyaye na sun tafi Saudiyya, ni kadai ce sai masu hidima, tsoro nake ji" "Ya rage naki, ba zaki kwana min anan ba,shirya mu je mu ci abinci ki tafi" "Wai Mahboob me ye matsala ta ne? Me ne ne aibu na dan ina son ka? Ka sanar da ni damuwar ka zan maka maganin ta, a da ka na sake min mu yi hira, amma tun sanda na tambaye ka iyayen ka ka daina min murmushi na jin dad'i, ka daina hira da ni, in iyayen ka ne ba ka so na tambaya na sha maka alqawari akan ba zan sake maganar su ba, ka kuma tabbatar da hakan dan ban sake maganar su ba, to me ye matsalar ne? Ko ni din ce baka so? In ba ka so na me ya sa ka ke kwana da ni?" Kallon ta ya yi na wasu lokuta masu tsaho, kamar ba zai magana ba, can kuma ya ce, "Rayuwar ki ce ki na da damar yin duk wani abu da ki ke ganin shi ne daidai a rayuwar ki, ke kin sani d mutane za su san mu na aikata zina da tuni an kai mu gaban mahukunta, domin qasar nan su na aiki da shari'ar islam, ni ban taba furta miki ina son ki ba,sannan ban taba gayyatar ki ba, ban kuma taba zuwa gidan ku ba, da na san haka kike da naci da ban biye maki ba tun shekaru uku da suka wuce, da na san za ki matsawa rayuwa ta da a ranar da kika min sallama da dauke kai na yi, Aemana ba na son takura, ba na so a matsa min, ki taimake ni da kan ki, ki daga ma rayuwa ta qafa, ki bar ni na ji da abinda ya damen, in kin ga dama daga yau kar na sake ganin ki," Ya na kaiwa nan ya bude qofa ya fice tare da rufe qofar da qarfi, a zuciyar shi ya na matsanancin tausayin ta, saboda shi ne namiji na farko da ya fara saduwa da ita, ya shaida hakan, kuma ya shaida soyayyar shi mara algus da ke ran ta, amma inaa ba zai iya auren wadda ya lalata ba, gida Nija za shi ya samu sabuwa dal a leda ya aura. Aemana yarinya ce da iyayen ta ke da tsananin riqo da addini, kuma suke qoqari wajen bata tarbiyya matuqa, amma matsala daya da aka samu, sun mallaka mata yanar gizo a hannu, ta internet ta san harkar sex, da duk wata shaid'ana ta zamani, mahaddaciyar qur'ani ce da manyan hadisai, amma ko kusa ba ta aiki da abinda ta sani, wanda a ido iyayen ta kallon mumina suke mata, sun bata yardar su da amanar su, za su iya rantsuwa akan ta cewar mutuniyar kirki ce ko hannun namiji bata taba riqewa ba in ba mahaifin ta ba, in za ta fita daga gida shigar mutunci take sosai, ta dora abaya baqa a sama da niqab, amma da ta bar unguwar su, sai ka rantse ta na da nasaba da turawan yamma. Soyayyar Mahboob ce ta sake jefa ta cikin lalatacciyar rayuwa, domin kuwa har sigari ta na busawa in ta zo wajen shi, a zaton ta za ta iya jan ra'ayin shi ya so ta, su yi aure a haka, sai gashi

Chapter 7 of 41