ta.
Watan Mahmood d'aya, a gidan, ya saba da su sosai, kuma ya na waya da Aemana ba tare da nuna ya tsani inda ya ke ba, sai dai kawai ya na fada mata ya yi kewar ta.
A cikin wata na biyu aka sanya shi a makaranta, Aaseeyah ta koma aiki, tare take shirya su, su tafi, in ta ajiye shi a makaranta sai ta wuce office, yaran ta kuwa a gida take barin su wajen su Yesmeen, duk bayan awa uku ta na komawa ta shayar da su ta koma, sau biyu ta ke komawa gida, kafin ta tashi office, a zuwa na biyun ta ke komawa da Mahmood gida, in ta gama shayar da 'yan biyu, ta bashi abinci shima, ta watsa masa ruwa sai ta masa wanka, ta hada shi da kayan wasan shi, su je can su yi wasa da su Humairah.
Da weekend kuwa su je gidan Mammee, islamiyyar da su Aaseeyah suka yi, ita aka sanya Mahmood da su Aysha, an sake zamanantar da makarantar, daliban da suka sauke qur'ani, a makarantar maza su ke koyarwa.
In an tashe su, su dawo gida, da kan su, in sun ci abincin dare su koma gidan su.
Mahmood yaro ne me tsananin son qannen shi, ba shi da mugun hali, ba shi da hayaniya, hakan ne ya bawa Aaseeyah damar bashi tarbiyya mai kyau irin wadda take fatan bawa yaran ta.
Ta nuna masa mahimmancin ibada, girmama iyaye da na gaba, ta nuna masa mahimmancin girmama mace da mutunta ta, ta yanda kallon al'aurar mace ko da yarinya ce ya na daga cikin rashin girmama mace, dan haka ko sauya ma 'yan biyu pampas za tai sai ya juya, shi a dole ba ya son ya kalla.
Mahboob abun na su tun ya na bashi dariya, har ya fuskanci ma'anar hakan, tabbas su ma da sun samu irin wannan tarbiyyar da sun girmama mace, ba su haike mata ba ba tare da aure ba.
Mahmood yaro ne mai shiga rai, daga makaranta har gida, yara na son abota da shi, saboda balarabe ne, wasu saboda qoqarin shi, wasu saboda kyaun shi, wasu haka nan suke jin su na son shi.
Duk abinda ya ke so iyayen shi na mishi, Aemana ma ba a barta a baya ba wajen yi ma jikokin gidan gaba daya hidima, in ta tashi yi wa Mahmood gaba daya kowa da sunan shi take yo aike.
****************************
Ba abinda ya ke da mahimmanci a rayuwar d'an Adam sama da lokaci, in ba ka tsaya ka amfana ko ka amfanar da mutane ba a lokacin da ya dace, to fa lokacin zai wuce, ya zama ba ka da sauran dama a rayuwar ka, sai dai ya bar ka da dana sani.
Shekaru ne masu dan dama,wadan da za su kai goma sha shida, a wannan rana Mahmood ke kammala first degree din shi a bangaren Engineering, ya na fatan taimaka wa kakannin shi da sana'ar su, dan kuwa tsufa ya kama su Abbu sosai, su na buqatar mataimaki.
Aaseeyah ta na nan ta bude ta ta chamber mai zaman kan ta,inda ta ke riqe da lauyoyi masu tarin yawa a qarqashin ta, 'yan biyu suna a JSS 2 a yanzu,duk wanda ya gan su sai sun bashi sha'awa, ba wai dan kyawawa bane kadai, ah ah, nutsuwar su, da kamewar kai, tare da sanin ya kamatan su ne babban abin burgewa.
Tunda Aaseeyah ta haifi mai sunan Abee, wato Ibrahim Khaleel, bata sake haihuwa ba, yanzu ya na da shekaru bakwai.
Umaimah ta sake haihuwa, ta na da yara hudu, Yesmeen ma na da hudu, Ummu Suleim na da shida, ciki har da 'yan biyu,Tasneem na da uku.
Familyn Abdul Mudalleb Jordan ya zama babba, kuma cikakken Family, Mahmood na matuqar son Aysha Humairah, diyar Yesmeen kenan, hakuri da kau da kan da yake ya qare yau, tunda Abban shi da kan shi ya masa maganar fitar da matar aure tunda ya kammala karatun shi, in ma zai ci gaba, to fa sai da aure.
Sai a wannan lokacin ne ya ke sanar da Abban nashi cewar Ayshaa yake so,kowa ya yi mamaki, saboda ba ya wani kula ta, ita ma haka, ashe ta ciki na ciki ne, ita kan ta soyayyar shi ta gama nakasa zuciyar ta , ba tare da ta shirya ba.
Ko da iyaye suka sanya baki ma ba su wani sakewa da juna, in zai magana da ita Asma'u diyar Tasneem ce 'yar kai saqo a tsakanin su, in kuma kyauta ze bata 'yan biyu yake aika ko Khaleel su kai mata.
Wannan tarbiyyar ya same ta ne a wajen Ummeen shi Aaseeyah, ta koya masa azumin litinin da alkhamis, ta koya masa yawan tilawar qur'ani, bata masa tarbiyyar yawan kallon films ba,dan haka ba shi da wata wayewa akan rayuwar auratayya, sai da aka sanya ranar auren su, in ta zauna ta na masa wasu maganganun akan aure, pillow yake sawa ya toshe kunnen shi,ko ya bar mata wajen, shi din mai kunya ne sosai.
Watarana ta sa Mahboob a gaba ta na masa surutu, akan ya fara koyar da yaron shi yanayin rayuwar zaman aure, ba mace kadai ake koyarwa zaman gidan miji ba, maza da mata suna da 'yancin koyon rayuwar zaman aure,saboda ta haka ake samun daidaito a zaman lafiya a gidan aure.
Tun Mahboob na jin kunya har ya ware, Mahmood ya ce, wato Ummee ce ta aika shi ko? A wasa da dariya Mahboob ya ke nuna masa mahimmancin mata, da kula da su.
***************************
Bayan bikin Mahmood da Aysha, wanda suka dage su dai a tsohon bangaren da iyayen su suka yi zama anan za su zauna, in su khaleel suka taso a gina masu nasu gidan, rashin girman kan Mahmood na burge kowa, dan haka Mahboob ya zuba dukiya sosai dan gyara masu wajen, da qawata shi, ba me cewa ginin ya yi shekara da shekaru.
Ango da amarya na zaune lafiya, cikin so da qaunar juna.
Asma'un Hussein tunda miji be zo ba, an sama mata makarantar gaba da sakandire ta ci gaba,ana fatan in miji ya zo a aje karatun a yi aure, sannan a ci gaba.
*****************************
Aaseeyah sun samu ziyarar Umaimah, da Ummu suleim sai yaran su, gidan gwanin sha'awa ya cika, Ayshaa tun da ta je gidan ta qunshe a daki, ita a dole kunya take ji, dan ta na dauke da cikin wata biyu, ba kowa ne ma zai gane ba, amma tun da ta san ta na da ciki ba ta son kowa ya gan ta.
Hajiya Aaseeyah na zaune tsakiyar 'yan uwan ta,sun gama waya da Aemana kenan ta ajiye, suna ci gaba da hira wata wayar ta katse mata hira.
Dagawa ta yi ta yi sallama, kuka ta ji ana yi a wayar,dan tashi tai daga tsakiyar 'yan uwan ta ta koma gefen Umaimah, ta juya baya ta na amsa wayar.
'Hello, ki na ji na kuwa?'
"Ina jin ki"
'Dama na samu lambar wayar ki ne a hannun wata qawata lauya,ta ce ta na aiki ne a qarqashin ki, ni ina so na bada qarar wani cousin dina ne,dan yayar mahaifiya ta,da ya lalata rayuwa ta, kuma yanzu yake son ya auri qawa ta, a cewar shi ni ragowar maza ce, kuma ni na rantse ban taba kwana da kowanne namiji ba in ba shi ba, tun ban san kaina ba, ya ke lalata da ni, har na girma,amma yanzu ze guje ni, kuma ina son shi, ki temaka min'
Cikin kuka yarinyar ta qarasa magana, lallashin ta Aaseeyah ta yi sosai, sannan ta mata tambayoyi ta bata amsa; daga baya ta ce gobe ta je ta same ta a office,sannan suka yi sallama.
Ta na zama ta kula kowa a wajen ya yi shiru ne ya na saurarar wayar ta da wannan yarinyar,domin kuwa volume din ya na da qarfi duk da ba a speaker ta saka ba.
Umaimah ce ta sunkuyar da kan ta qasa, cike da wani irin yanayi mara fassaruwa.
Aaseeyah ce ta dafa ta, sannan ta ce,
"Dan Allah kar ki bata ran ki a banza, akan abinda ya riga ya zama tarihi"
"Kwarai kuwa, shi abin tarihi abun tunawa ne, dik yanda ka so kauce masa watarana ko kai,ko yaran ka,ko jikokin ka, sai sun tuna shi, domin an aje masu tarihi, ba zan maki qarya ba, ina son Yah Noor,ya na so na, kuma ya na bani dikkan kulawa, amma ki sani, har yanzu akwai wata daraja da qima da na rasa,wanda ni a cikin zuciya ta ina jin wannan emptiness din, ko kun san cewar Yah Noor aure yake nema? Ban fada maku bane saboda abun bai tabbata ba, amma ya na nan ya na neman auren wata yarinya sa'ar su Asma'u, ko za ta girme su da kadan ne"
Dikkanin su jikin su ya mace, ba aya ko hadisin da ya hana qarin aure, sai ma umarnin qarawa, amma kishiya na da tashin hankali, amma in an hakuri komai zai zo da sauqi, nan da nan kuwa suka dinga kwantar mata da hankali, tare da bata shawarwari, duk iya qoqarin Aaseeyah na ganin ta cike mata gurbin wannan abinda ta ke ji a ran ta ta rasa da kalaman ta masu matuqar tasiri a rai, ta kasa.
Duk macen da ta je gidan miji ba a cikakkiyar mace ba, wallahi, wallahi, har abada sai ta dinga tuna ya asalin ta yake a gidan miji, kuma in ta tuna ba zata ji dadi a ran ta ba, mata a kiyaye, tabbas an cuci mata da wannan karin maganar, domin zai iya zama gaskiya, 'duk abinda d'a namiji ya yi ado ne'.
Bayan sun gama maganar Umaimah ne, Aaseeyah ke fadawa 'yan uwan nata, yanda take karbar case akan cousins, a kullum sama da uku ko hudu.
Anan take sanar da su labarin yarinyar da ta kira, fadin sunan yarinyar da unguwar su ne ya sanya Tasneem sake tambayar Aaseeyah sunan,ta maimaita mata.
"Subhanallahi, Aaseeyah, wannan ai kamar Shakuraa, ko baki gane sunan bane wai, Shakuraa ce fa,"
"Shakuraa dai Shakuraa? Yarinyar da ko yatsa ki ka sa mata a baki ba zata gatsa ba, habaa, wataqila suna ne ya zo daya"
"Ina zuwa bari na kira ta yanzu"...........
Ni ma ina zuwa aradu hannu na ya gaji, mu hadu zuwa gobe, inshaa Allah, ina saka ran mu kammala TAUBASHI a yau ko gobe inshaa Allahu.
TAUBASHI
PAGE 65
Tasneem ta jima ta na kiran wayar Shakuraa amma bata daga ba, sai da ta hakura da kira sannan shakuraa ta kira ta, muryar ta a shaqe alamar kuka, ta yi sallama.
"Aunty Tasnee barka da war haka"
"Barka dai shakuraa, ki na lfy kuwa? Na ji muryar ki a shaqe kamar kin yi kuka?"
Cikin dakewa Shakuraa ta maida kwallar da ke barazanar zuba mata, ta ce,
"Lafiya qlou Aunty Tasnee, ina qanwa ta Asma'u, kwana biyu ba mu hadu ba"
"Ta na lfy qlou,ya aunty na?"
"Lafiyan ta qalou,"
"Shakuraa kin san dai ni auntyn ki ce, in akwai abinda ke damun ki, ki sanar da ni,"
Kuka Shakuraa ta saka, sannan ta katse wayar, zuciyar ta ta quntata da d'acin rashin masoyi, da wulaqancin da ya shuka mata, dama soyayya na zama qiyayya?
(Soyayyar gaskiya ba ta taba zama qiyayya, in kin ga masoyi na gudun masoyi to ba a gina soyayyar kan gaskiya da amana ba, ba a gina soyayyar dan Allah ba, an gina soyayyar domin sha'awa ne, an gina ta ne dan wani qudiri da cikar wani buri a zuciya, daga sanda aka samu wannan burin to shikenan soyayyar ta qare, amma in ba a same shi ba, ko shekara dari za ai wannan soyayyar zata ci gaba da wanzuwa)
Hankalin Tasneem ya tashi ainun, dan haka suka yanke shawarar ranar Monday in Aaseeyah za ta tafi Office ta bita, anan ne za ta ga wace yarinya ce, shakuraan ta ce ko kuma wata?
Haka kuwa suka yi, ranar Monday da izinin Hussein Tasneem ta bi Aaseeyah, ko da duka shiga saune take a bakin qofar shiga Office din ta rufe fuska da Niqabi,ta na ganin Tasneem ta yi kamar za ta wuce su, ba tare da ta ce komai ba,
"Shakuraa?"
Tsayawa ta yi cak, ta kasa gaba ta kasa baya, asirin ta ya tonu, Tasneem kuwa gaban ta taje, ta daga Niqab din, ta ga yanda hawaye ke bin 'yar kulullubar fuskar diyar yayan nata.
Rungume ta tayi, ba shiri kuwa ta fashe da kuka,da ganin idon ta, ka san ba ta samu baccin azziqi ba.
Cikin office Aaseeyah ta musu izinim shiga, bayan sun zauna, Aaseeyah ta nemi qarin bayani wajen Shakuraa.
"......to shi ne na ce bari na kai shi qara kotu, wataqila za a saka shi aure na dole,tunda shi ya lalata min rayuwa, amma yanzu yake son ya guje ni, ya auri wata,kuma gaskiya ni....niii...inaaa son shi"
Kuka ta sanya daga qarshe, ta re da dafe kan ta da ke mata tsananin ciwo.
"To Shakuraa na ji bayanan ki, kuma.na gamsu da ko kotu aka maka shi ba laifi bane, amma wannan magana ina ga iyaye ne ya kamata su shiga ciki ko? In ya qi still sai a kawo shi nan,a yanke masa hukuncin da ya dace da shi"
"Wannan gaskiya ne Aaseeyah, yanzu ina ganin in kin samu time, ki taimaka mu je gidan Yaya,ki masu bayani da kan ki, zai fi, sannan a yi wa Mudassir din barazana, in be aure ta ba za a kai shi gidan yari, sannan in ya aure ta ya wulaqanta ta nan ma kotu za ta dau mataki"
"Kin kawo shawara, yanzu zan iya bada awa daya a lokaci na, mu je yanzu mu dawo tunda kusa ne"
Babu bata lokaci kuwa suka isa gidan, Yah Inuwa na shirin fita, dan har ya shiga mota suka shiga gidan, Tasneem bata fuska ta yi, dan sai yanzu haushin shi ya taso mata, dalilin abinda ya aikata mata ne ya sanya aka lalata innocent yarinya da bata ji ba, bata gani ba, laifin uban ta ya ja mata.
Bayan sun gaisa, suka sanar da shi wajen shi suka zo,Shakuraa da ya gani ta na kuka ne ya sanya hankalin shi tashi, a hanzarce suka shiga ciki, suka zayyana masa komai,shi da matar shi, mamakin wai har shakura ta san ta kai qara kotu suke dikan su.
"Yah ka yi shiru, ka ga rayuwa ko? Dik abinda bawa ya yi, ya sani za a masa makamancin shi, ko sama da shi, ko wanda bai kai shi ba,yanzu ka duba ka ji wannan mummunan labari,yarinyar da ko sha takwas batai ba an lalata ta,kuma ana neman a gudu a barta, ba tare da an aure ta ba, ka na ganin in Mudassir ya qi auren ta, wani zai aure ta kuma tai daraja ne? Ba kowanne namiji bane ke hakuri in ya samu mace haka, ba kowanne miji bane irin Hussein, inni na samu kamar Hussein ita fa?"
Kuka ne ya kwacewa Tasneem, tabbas lalata mace ya na da ciwo, ba abinda zai goge wannan tabon har tsufan ta, har mutuwar ta, in ita ya lalata ta, Allah ya dube ta ya bata Hussein Shakura fa? In batai sa'ar miji ba fa? In kuma shi Mudassir ne ya aure ta ya wulaqanta ta fa? Dik da shi ya fara lalata ta, dik wannan laifin waye?
Kukan ta ya qi tsayawa, tashi ta yi ta fita daga dakin, sai a sannan jikin Yah Inuwa ya hau makarkata ya na tina baya kamar a film, ya na tuna yanda ya maida ita kamar matar shi ta aure, bai riqe zumunci ba, ya lalata yarinyar da ya kamata ya kare da rayuwar shi,ya lalata yarinyar da ya kamata ya zama mata uwa,uba, da dikkan wani dangi.
Maman shakuraa ce da shakuraan suke kallon shi, zufar da ke fita masa ce ta sake tona asirin shi.
"Ko za ka iya mana bayanin me Tasneem ke nufi?"
Har zai magana Aaseeyah ta katse shi, domin magana ta wuce, dawo da ita ba shi da wani amfani sai rusa zumunci,wataqila ma har da auren shi sai maganar ta taba.
"Yah Inuwa ina son a kai ni gidan su yaron, bani da lokaci mai yawa, dole mu zauna da iyayen shi, da shi kan shi, a gindaya masa dikkan sharruddan da suka dace, domin ba zamu bari ya wulaqanta Shakuraa ba, bayan shi ne sanadin lalacewar ta"
Cike da jin kunya ya tashi, ya ma matar shi umarnin ta sako hijabi aje gidan yayan ta.
A jikin motar Aaseeyah suka tadda Tasneem wadda ta duqar da kai, ta na kukan baqin ciki, Yah inuwa ne ya taka zuwa inda take, Aaseeyah na ganin haka ta tsaida su Shakuraa, tare da musu qaryar,
"Mu basu lokaci, kun san abun Yaya da qanwa, ballantana abinda aka yi wa Shakuraa ya taba zuciyar ta sosai, ta na qaunar shakuraa matuqa"
Hakan ya sanya shakura zubar da hawaye, da jin son Auntyn nata sosai a ran ta.
Tsaye yake a gefen ta, ita kuma ta na ta share hawayen da ya qi tsayawa, juyar da kan ta tayi, ta na kallon gate,
"Tasneem, dan Allah, da son Annabi ki yafe min, na so kaina da yawa, ke ba ma son kai bane, ni kai na ban ma kaina adalci ba, domin na aikata abinda yake halaka ce ga kan kaina,cutarwa a gare ki qanwa ta, kuma cutarwa ga zumuncin mu,ina roqon ki ba dan ni ba, ki duba girman Allah ki yafe min"
Ya jima ya na roqon gafara, da kyar ta samu kuka ta ya tsaya, cikin murya mai rawa ta ce,
"Na yafe maka, Allah ya yafe mana baki daya, abinda ya sani kuka shi ne, tunda na ke ban taba jin danasani, nadama, da tausayin kaina ba, akan abinda ka min sai yau da haka ta sami shakuraa,Allah ya sa kar ta wulaqanta akan abinda muka aikata a baya"
"Ameen Tasneeem, a gaskiya ke ta daban ce, dik da abinda na miki, kin damu da jini na, ba ki son wata damuwa ta rabe mu, na gode na gode Tasneem, Allah ya qara maki hakuri akan na da"
"Ameen"
Ganin Tasneem na murmushi ne ya sanya su Asseyah isa, nan suka shiga mota, Shakuraa na tare da auntyn ta Tasneem.
Har gidan su Mudassir, ga lefe nan da za a kai gidan budurwar shi, baja baja, an kashe dukiya ainun, tattare kayan Maman shi ta yi, Baban shi kuwa ya na murnar ganin Inuwa, domin sun jima ba su hadu ba.
Mudassir kuwa bata rai ya yi, da ya ga Shakuraa na kallon shi, ciki. So da qauna, tare da kewar shi.
Har zai fita, Tasneem ta ce,
"Ina ga ai ka dawo ka zauna domin zuwan naka ne"
"Ni kuma?"
"Kwarai kai,"
Labari shakura ta fara bayarwa tiryan tiryan, tun daga sanda ya fara neman ta, har wa yanzu da yake son auren wata ba ita ba,
Yanayin shi kadai ya bayyana gaskiya, amma ya hau rantse-rantse ya na cewa shi bai taba kama ko da hannun ta bane, iyayen shi kuwa suka amince,nan suka bawa Shakuraa rashin gaskiya, cikin bacin rai kuwa Aaseeyah ta miqe,
"Yah Inuwa, ku tashi mu tafi, dole wannan case din sai an shigar da qara kotu, a da na zaci abun zai zo da sauqi in aka tattauna a cikin gida, ba tare da kowa ya sani ba, musamman duba da cewa mahaifin yaron nan ya na siyasa, ba wanda zai so sunan shi ya baci, amma tinda haka ne, kawai muje sai an shiga kotu dole,"
Ai su na jin kotu, hankalin su ya tashi, musamman Mudassir, dan ya san ya aikata, in aka gano shi a kotu ga hukunci, ga kunya.
"Na amince zan aure ta, amma dai ni ban taba taba ta ba, zan rufa mata asiri tunda qanwata ce,"
"Yah Mudassir ni zaka rufawa asiri? Ka manta sanda ka ke kiran na rufa maka asiri kar wani ya san me ya faru tsakanin mu? Da na san haka ka ke, da ban amince da kai ba, Aunty na hakura da shi, ba zan aure shi ba,ko son shi zai kashe ni, gwanda na mutu da son shi, banga amfanin son dan iska irin shi ba, wanda ba zai iya tsaya min ba, bayan kai ne sanadin bata rayuwa ta,"
Kukan Shakuraa har tsokar zuciyar Mahaifiyar ta, ta kalli Yayar ta ta ce,
"Yaya na gode da irin kalar qaunar da kika nuna min, ban taba banbancewa tsakanin yaran nan ba, amma a gaban ki yaron nan ke qarya, ki ke biye masa,ni kaina ba zan bari ki aure shi ba shakura, kuma na muku alqawarin dik inda ya je neman aure ba zai samu ba, ke kin san ko ni wace ce,"
Cikin fushi ta kama hannun shakuraa suka bar parlourn, iyayen Mudassir hankulan su sun tashi, har yanzu Maman shakuraa bata dena biye biyen malaman tsubbu da bokaye ba,tsoro ne fal ran maman mudassir, kar ta wa yaron ta asirin da zai tarwatsa rayuwar shi.
Ko da suka koma gida, Aaseeyah ta basu shawarwari,dan ta tabbata wannan barazanar da suka yi, zai sa su Mudassir su kawo lefen nan gidan su shakura.
Sallama ta musu ta bar Tasneem anan, in Hussein ya tashi daga aiki, zai biya ya dauke ta.
Ai kuwa bayan awa uku da komawar su, Mudassir ya dinga kiran shakura, haka taqi dagawa, message kan message, taqi reply.
Qarshe kashe wayar ta tayi, suka ci gaba da yanda za su wana shi, har sai ta koma da darajar ta da qimar ta a wajen shi da iyayen shi.
*****************************
Bayan kammala yankewa wasu masu garkuwa da mutane, dan a basu kudin fansa hukunci, Aaseeyah ce ke komawa gida a gajiye.
Ta tarar da gidan ana ta murna, Shakuraa ta zo ta basu labarin a ranar za a kai lefen ta daga gidan su Mudassir, Tasneem na can wajen amsar lefe, sun dawo kamar da, sai dai taqi amince masa ya ci gaba da taba ta, har sai an yi aure.
Aaseeyah ta taya su murna sosai, sannan ta sanya wa abun albarka.
Rayuwa ta yi ma familyn Jordan dad'i, kusan kowa zaune yake lafiya da abokin zaman shi, sai abinda ba a rasa ba, na sabanin harshe da haqori.
Maganar Auren Noor ta tashi, dan kuwa Ummee ta yi tsalle ta dire ta ce ba me yiwa diyar ta kishiya, tinda ba ai wa uwar sa kishiya ba, ga ta nan shekarun ta sun ja, amma uban shi bai mata kishiya ba, dan haka shi ma ya lallaba da guda daya.
Noor da ya qi, sai da Ummee ta masa tambayar da ta sanya shi jin kunya sannan ya ce ya sakar mata, ba shi ba qara aure.
**************************
Yau take qaramar sallah,yanzu ba kamar da bane,ahalin Abdul Mudalleb Jordan sun yi yawan da su kadai sun ishi kan su gayya, masu zuwa daga wasu garuruwan kadan ne, hidimar Sallah ake ta faman yi, wannan karon Mammee da Ummee na saune su na bada umarni, 'ya'ya da jikokin su ke aikin abinci, da abun sha.
Su na zaune cikin nishadi da annashuwa,kowa ya ci kwalliya, wannan na wannan bai iya ba ni na fishi.
An yi bikin sallah lafiya, an sada zumunci cikin yalwa da annashuwa.
Bayan sallah da kwana uku, Aaseeyah na gyarawa Mammee gidan ta, ita da 'Yan biyun ta, da Ayshaan Mahmood, wadda ke goye da babyn ta mai sunan Aemana,suna kiran ta da Aemanan ta,domin Aemana da kan ta ta ce kar a boye sunan, amma still Ayshaa bata iya kira, Mamana take ce mata.
Sun yi nisa a gyara gidan, suka ji Mammee ta buga salati daga parlour, rige rigen fita suka yi,dan ganin me ya faru.
Wani dattijon tsoho suka gani, shi da wani matashin saurayi,baqi kyakkyawa.
Matashin ne ya ke riqe da hannun tsohon, su na tsaye Mammee na kallon su, cikin zubar hawaye.
Aaseeyah ce ta iya bude baki, ta ce su zauna, saboda tsohon ta ga alamar ya gaji da tsaiwa, Mammee ta dafa, Mammee na jin hannin Aaseeyah a jikin ta, sai ta fashe da kuka sosai, ita ma ta zauna a qasa, saboda girmamawa ga wannan tsohon.
Cikin yaren nufanci, tsohon ya fara yi wa Mammee magana.
Nan da nan Aaseeyah ta gane tabbas wannan d'an uwan Mammee ne, to ina suke dik tsahon wannan shekarun?
Mammee cikin yaren, da ya fara mata wahalar yi, ta mayar da gaisuwa, tare da saurin tashi, ta je ta kawo masu ruwa,ya na karbar ruwan a hannun ta ya sanya kuka,cikin hausar shi da ke a gurbace ya fara bawa Mammee hakuri,
"Ki yafe mana Subai'a, mun yada zumunci saboda camfin banza,ke ba mayya bace, ke yarinyar kirki ce,gashi nan Muhammadu shi ne silar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 41