Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jin an ce Mahboob na daf da zuwa inda ta ke, ta bude motar ta fita,cikin kyankyami ta ke miqawa almajiran kudi,motar Mahboob na gilmawa har wani durqusawa ta ke wajen bda sadakar, kamar mutuniyar kirki. Abun ba qaramin burge Mahboob ya yi ba,kamar an ce ya kalle ta ta mirror, ita ma kallon mirrorn shi ta yi, bai san sanda ya sakar mata kyakkyawan murmushi ba, dauke kan ta tayi da sauri, ta miqawa mutum na qarshe kudin hannun ta dika, da sauri ta fada mota, ta dauki wani abu a roba ta shafa a hannun ta, tare da sake fesa turaruka a jikin ta, Mahboob ya yi nisa sosai da barin wajen, ta na daina hango motar shi ta tada ta ta, a guje ta dauki hanyar gidan ta, domin ta na buqatar wanka, ta taba hannayen almajirai. Tun daga babban parlourn nata da ya sha kayan alatu ta fara tuge dankwalin ta, wanda mai kwalliya ta musamman aka gayyato ta daura shi,mayafin ma a qasa ta yar, ta na zubarwa mai aikin ta na kwashewa. Ta na isa daki ta zame skirt da rigar ta zubar a qasa, ta fada bayin ta mai tsananin ado da kyau. Kwamin wanka ta fada, ya sha kayan qamshi da na wanka, ta kwanta tare da lumshe idanun ta, fuskar Mahboob kawai take hangowa, cikar kyau da kyaun surar jikin shi sun tafi da ita. "Woww, lallai na yi mijin aure,wannan shekarar zan karya alqawari na na qin yin aure, a yanzu na samu mijin da ya dace da komai nawa" Miqewa ta yi a cikin ruwan ta jima sannan ta daqo, ta na shafa fuskar ta cikin murmushi. Bayan ta gama shiri cikin qaramin wando da ya wuce mazaunan ta da kadan, da wata bingilar riga mai dogon hannu, ta isa balcony din dakin ta, ta tsaya riqe da sigarin ta a hannu, waya ta kara a kunne ta yi ma Alh. Munkaila bayanin duk tsare tsaren ta. Wata muguwar dariya ya saki, ya mata kirari, ya na ci gaba da ziga ta ta katse wayar shi, tare da yin tsaki, "Men are alllll the same," Kujerar da ke wajen ta fada ta zauna, cike da tunanin Mahboob a ran ta. *************************** Sun kusan sati biyu Mahboob na haduwa da Eliza a wurare mabanbanta da ita, watarana ya tashi aiki, ya biya siyan fruits ya wuce da shi gida, sai ya ga irin motar da ya ke ganin yarinyar nan mai yawan sadaka, ko da ya leqa sai ya gan ta ta na ta rizgar kuka, cike da mamaki Mahboob ya parker motar shi a gefen ta ta, ya isa cikin yi mata sallama, bata amsa shi ba sai ma cewa da ta yi "Dan Allah ko waye ya yi hakuri kudin hannu na sun qare zuwa gobe inna fito zan baku sadaka" Cikin sauri Mahboob ya ce, "Baiwar Allah ba sadaka na ke nema ba, na zo ne na ji me ye ya saka kykkyawar mace mai taimakon mutane kuka a bakin titi haka, Allah ya sa lafiya ki ke" Murmushi ta yi mai hade da hawaye, ta sa hannu ta fara goge hawayen sannan ta ce, "Yi hakuri, ka san banda labarin kyawawan mata ba su da 'yancin nuna damuwar su a fili, in su na cikin tashin hankali irin nawa,ka yi hakuri," Hawaye ne suka zuba mata, cikin sauri ta tada motar ta ta bar wajen, Mahboob gaba daya sai ya ji ya tsani kan shi, dama bai kula ta ba, me ya sa zai fadi abinda ya fada ba yan bai san matsalar ta ba, ko dake ita ce bata fahimce shi ba. Tunani ya dinga yi mai zurfi har ya isa gida, sai ya bama kan shi laifi,sai kuma ya warware ya ce ba shi da laifin komai. Har dare bai je ya amshi abincin shi ba, da ya je masallaci ya yi sallah zai koma wajen shi. 'Wace matsala kyakkyawa kamar ta take ciki?da dikkan alama mai kudi ce ita' Mammee ce ta sa Aaseeyah shiryawa dan kai ma mijin ta abinci, tare da duba lafiyar shi............. Tooooooooo....makaranta a dinga hamfuli, duk da na ji dad'in yanda wasu suka min qorafi ta Whatsapp kuma privately, ba tare da hayaniya ba,da kyakkyawan lafazi, amma ku sani, yanda muke zaton komai ya tafi a rayuwa va lallai ne ya zama haka ba,wataqila kai hasashen za ai ruwan sama saboda ganin gagarumin hadari, amma in Allah ya so sai ya tafi da hadarin nan rana ta maye gurbin shi, so na san yanda kuke zato Aaseeyah ta gama makaranta ta kai Gazaa kotu a yanke masa hukuncin kisa bla bla bla... to kenan ma labarin ya qare ba wani armashi ba sugar?? Ku qara hakuri ku ji ya qarshen zai qare, this is my tory ni na qirqire shi duk da na gina tubalin shi ne akan labarin gaskiya,amma ku qara hakuri ku ga ya zan qarqare shi plss, so inshaa Allah ba za ku yi danasani ba TAUBASHI PGE 36 Washegari Mahboob ya shirya zai wuce wajen aikin shi, Aaseeyah ta fito cikin shirin makaranta ita ma, har za su fita ta kula da yanayin idanun shi, kamar wanda ya yi kuka ko ya rasa bacci, ba ta yi magana ba sai da suka zauna a mota,ya tada ta suka bar gidan tukunna ta kasa hakuri, ta ce, "Yah Mahboob, yanzu har tunani na ya fara hana ka bacci?...bari na san me zan yi akan hakan, ina ganin zan dinga taya ka hira, har sai ka yi bacci sai na tafi," Dariya suka dan yi, dan ya san tsokanar shi take yi, tare da son jin damuwar shi, shiru ya dan yi ya na nazari, shin ya sanar da ita ne ko kuwa? Inaaa ba zai iya sanar da ita maganar wata ba, in ta yi zargin wani abu na cin amanar ta fa? To amma ai ba amanar ta ta yake ci ba, ko dai ya sanar da ita ne?" "Yah Mahboob koma me ne ne damuwar ka, ba na fatan ka sanar da ni abinda ba kai niyya ba, ba wai ina matsa maka sai na sani bane, kawai ina son ka sani duk abinda ya dami bawa Allah shi ne magani, Mammee ta ce idan mutum na cikin damuwa,ya fawwalawa Allah lamuran shi,ya yawaita ambaton Allah, da roqon shi taimako akan lamuran shi, inshaa Allah zan taya ka addu'a, a matsayi na na matar ka, na san da izinin Allah za ta karbu" Wani irin sanyi ne ya wanke mishi zuciyar shi, daga murmushin shi ya tabbatar ma da Aaseeyah maganganun ta sun yi tasiri, dan haka ita ma murmushin ta dinga yi, ba ta yi zato ba ko tsammani ta ji ya ce, "Ana uhibbuki jiddan, ya Mahboobatee" Da sauri ta sanya takaddun hannun ta a fuskar ta, ta na murmushin jin dad'i, cikin yin qasa da muryar ta ta ce mishi, "Ni ma ina son ka da yawa Yah Mahboob dina" "Ki na nufin ni naki ne ke kadai? Ba zaki samma kowa ba?" Dan bata rai ta yi, kuma har zuciyar ta bata ji dad'in b'ata masu moment din da ya yi da wannan maganar ba, tura baki ta yi ta qi amsa shi, ta juyar da kan ta ta na kallon waje, murmushi ya yi mai sauti, sai da Adam's Apple din shi ya motsa, hannu ya sa ya kama nata, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta maida idanun ta kan na shi, cike da tura baki irin yanda ta ke yi, da shagwaba ya ce, "I am sorry Aaseeyahn Mammee da Yah Mahboob wasa nake miki," "Ah toh, dan kai ba alewa bane ko biredi da za a gutsurarwa wani ko wata," Yanayin yanda ta yi maganar kawai ya sa shi dariya kamar zai suqe, har suka isa makaranta shiririta kawai take zuba masa, shi kuwa ya na dariya, kwata kwata a wannan lokacin ya manta da wata wai ita Eliza da ya taba gani, zuciyar shi cike take fam dam da soyayya da qaunar Aaseeyah, ba ya jin akwai inda ya yi saura bai cika ba da son ta,ko ina na jikin shi amsa sunan ta yake a matsayin mata kuma abar son shi. Har za ta fita a motar ya marairaice kamar wani baby, fuskar shi abun tausayi ya ce, "Allah sarki Mahboob, yanzu matar ka za ta shiga makaranta maza da mata babba da yaro, duk sai sun kalle ta, gashi ko dan kiss ba ta maka ba a matsayin lallashi, ba komai, bari na tafi, matan Nigeria dama ba su kula da mazan su, ina ga dai zan je Jordan na qaro ta biyu," Wata wawura Aaseeyah ta kai mishi, tuni ta manta da tunanin da ta fara na akwai mutane a wajen, sai da ta bashi mamaki, ta na kai lips din ta kuncin shi ta wara haqoran ta ta kafta masa cizo, da gudu ya bude idon shi daga lumshewar da ya yi, ya kalle ta, ya na sosa wajen, ba makawa sai ya yi tabo, Allah ya sa ma ya na aje gemu wataqila fatar shi ta so dayowa, "Aaseeyah har abada na yafe kiss din, ni zan dinga miki," "Ai baka ga komai ba,sai mun hadu a gida, ba 'yar Jordan za ka aura ba wadda gidan su ke maqotaka da masallacin makka zaka aura, ni ka ke had'awa da wata ko?" Nan da nan idon ta ya kawo ruwa, kallon agogon hannun ta tayi, ta ga ta na latti, da gudu gudu sauri sauri ta bar wajen, tun cizon da ta kafta masa mutane da dama ke kallon su,da ganin su wa su sun san dai wannan ba saurayin ta bane, ko dai yayan ta, ko mijin ta, dariya suka bama wasu, wasu kuma na kallon su da birgewa da sha'awa, wasu kuma 'yan baqin cikin unguwa qarqashin layi,sai zunden su suke, har ya fara qoqarin bin ta, ya hakura, dan da alama ba zata saurare shi ba. Murmushi ya yi ya shiga motar shi, tare da kallon madubi ya kalli inda ta kafta haqoran ta ya yi ja, amma in ba mai qurilla ba ba zai gani ba, saboda cikin sajen shi ne. Tada motar shi ya yi,ya wuce nashi wajen aiki. ******************************* "Sire, akwai wata mota da na kula yau ta na biye da ta su Aaseeyah, amma mace ce a ciki, da dikkan alamu su take bi,dan Mijin Aaseeyah na ajiye ta motar ta bi ta mijin Mahboob din" 'Ok ku tabbatar kun yi bincike kun gano wace ce wannan, ba na son matsala, ina so ku yi aikin ku da kyau,' 'Yes sire,inshaa Allahu za mu maida hankali akan aikin mu' 'If u need anything ku min magana,komai qanqantar lamari ina so ku sanar da ni me ke faruwa' "Yes Sire" Katse wayar suka yi, su na nan su na jiran a tashi su Aaseeyah. Eliza kuwa karkata kan motar ta tayi zuwa gida, dan bata so ya san ta na biye da shi, a tsarin abun nasu, ya kamata a ce ta yi sati ba su ga juna ba, amma ba zata iya jure sati bata gan shi ba, shi ne dalilin da ya sa ta bi su, sai dai abinda ta gani na faruwa tsakanin shi da Aaseeyah ya mugun d'aga hankalin ta, baqin cikin Aaseeyah ne ya bi ya mamaye zuciyar ta, 'Anya ba zan watsa mata acid a kyakkyawar fuskar da take taqama da ita ba? Ko kawai na sauqaqa mata wahalar da na ke mata tanadi na kashe ta tun yanzu ne? What am I going to do to her???' Sai kaiwa da kawowa take cikin parlourn ta, cikin riga da wandon ta matsattsu, kamar ta duqa su tsage, ga wani kitso dogo har saman mazaunan ta baqiqirin ta sha, ta yi mugun kyau, qarar takalmin ta mai tsini kawai ke tashi, jin damuwar ta masu aikin gidan suke a iska su na shaqa, dan in ranta ya na bace komai ka yi baka yi daidai ba ne, sai ran kowa ya baci. Kukun ta guda biyu su na tsaye, su na shawara, daya ya na a kai mata giyar ta, dayan ya na lemo ko ruwa, in kuma ba a kai ba nan ma masifa ne, qundunbala sukai, kowa ya dauki abinda ya ke ganin ya dace akai mata a wannan lokacin, su na shiga, su ka tsaya a gaban ta tare da fadin, "Ma'am, ga ruwa/ ga wine din ki" A fusace ta kalle su, ta miqa hannu ta qasan farantin ta kifa masu a jikin su, "Na aiki wani shege kawo min ruwa ko wani abu? Ku bace min daga nan" A gurguje suka fara qoqarin tsugunnawa debe glasses din da ke tarwatse a qasa, ball ta yi da wata kwalba ta daki qafar kujerar dake wajen, ta ce, "Na ce ku bar nan ko bakwa ji ne kurame ne ku?" Hannayen su na rawa suka bar wajen,ba dan su na jin dad'in ta ba sanda take nishad'i, kuma su na samun alkhairi sosai a wajen ta, da ba za su zauna qanwar bayan su na wulaqanta su haka ba, amma neman kudi suke,sannan Anne shi bai gaji zuciya akan nera ba, ah toh. Zama ta yi a daya daga kujerun ta, gefe akwai kwalin sigari da makunin wuta,da mazubin tokar ta, dauka ta yi ta kunna ta hade qafa daya kan daya ta na busa hayaqi kamar a injin niqan qari. Sai da ta sha kara biyu, ta na na ukun wayar ta ta hau qara, ko da ta duba sai ta ga Sanata Kabiru ne, kamar ba za ta dauka ba ta daga, ta kara ba tare da ta ce komai ba. "Hello, Eliza ki na ji na ko? Dama muna ta jiran ki mun ji shiru, lafiya dai ko? Dan ba halin ki bane tsayar da mu jira" "Ku yi taron bani, i can't make it today, i have a lil headache" "Subhanallahi, sannu, Allah ya sawaqe, sai na shigo du..." "I want to be alone,pls ba sai ka zo ba, thanks" Kashewa ta yi, shi kuwa Sanata da bai saba jin wannan lamarin ba abun ya sa shi shiga damuwa, ko da ya basu labari nan kowa ya shiga damuwa, shalele ne ya ce, "Ina kyautata zaton wannan tsohon dan kwayar ta ke tunawa, ko kun manta me ya same shi ne, ko kun manta komai ne? Ai ba abun mamaki bane a ce ta na can a make ita ma saboda tuna shi" "Shalele ka iya bakin ka ka san halin Eliza, ta ja harsashi ta sake shi a kwanyar ka ba matsala bane a wajen ta, dan ta bar harkar makamai ba shi ne yake nufin ta manta riqe su ba, na hane ka da sakin baki" Alh. Munkaila ne ya yi ma ASP Shalele kashedi, sai zaro jajayeb idon shi yake, ya na gyara zaman shi, qaton tumbin shi na rawa, ya tsorata da ya ji an ce za a fasa kwanyar shi. "Yanzu sai mu hakura da taron,tunda ita ce dama za ta bamu bayani akan yanda shirin nata ke tafiya" "Ni fa ina ganin mu daina jiran feedback daga wajen ta, mu tsara namu plan daga gefe, saboda kowa ya san halin Eliza akan maza, ina zargin kar ta kamu da son d'aya daga cikin mazajen ta lalata mana aiki," in ji cewar Hon. Mamman Accu. "Gaskiya ba na jin hakan za ta kasance,kar ku manta fa har da masoyin ta Sam a cikin wanda Aaseeyah ta kashe, ba ku ganin daukan fansa shi ne babban burin ta?" "Kai ma ka ce wani abu Alhaji." In ji shalele. Taron na su dai haka ya tashi ba wani abun azziqi da suka tattauna akai,sai hira kawai da suka sha suka tafi. Daga bacci Eliza ta tashi da misalin qarfe uku na rana,cikin hanzari ta fada wanka, ta fito, rigar ta kalar orange ta saka, tare da takalmi black mai tsinin gaske, riga ce wadda dikan ta ba ta kai guiwa ba, hannun shimi gare ta, ta yi kwalliya da baqin jan baki, idan ta ya sha kwalli, ta yi kyau sosai, sai tashin qamshi take, sun glasses ta saka kalar rigar ta, ta dau jakar ta siririya ta rataya,tare da kwasar wayoyin ta da makullun motar ta. Drivern ta ya kula ta daina ma neman shi, shi dai indai za a biya shi kudin shi a wata, ta yi ta fita ita kadai bai damu ba. Hanyar da ta san dole sai ya bi kafin ya wuce gida ta bi, ta samu nesa da idon mutane ta tsayar da motar ta, ta na zaune a ciki, ta na taunar chewingum,hankalin ta na kan motocin da ke wucewa. Ta fi minti sha biyar a wajen sai tsaki take, kafin ta ga motar Mahboob ya wuce, shi da Aaseeyah, su na hira,Aaseeyah na buga masa takardun ta a kafadar shi, ta na shagwaba, haushin yarinyar take ji over,ji take kamar ta fizgo ta ta take ta da motar ta, bata kula da motar police din dake kula da Aaseeyah ba, amma su sun gano ta, sai da su Mahboob suka isa gida, ta juya za ta koma,ta ga mota na bin ta, qara gudu ta yi, su ma suka qara gudu, ganin haka ne ya sanya ta take motar ta a guje, dan bata san su waje ba, su din ma ba su tsaya wasa ba, suka rufa mata baya da tsere............. Toooo wa zai kama wani a cikin su? TAUBASHI PAGE 37 Da gudu take wuce motoci da baburan da ke gaban ta, tare da yin fatali da duk wani kayan masu sana'a da ake kasawa a saman hanya da suka shiga gaban ta, ta samu nasarar ba su rata sosai, har ta samu wani layi ta fada, ta dinga sharara gudu, ta bulla ta wata unguwar da ko sunan ta ba ta sani ba, sai waige waige take cike da tashin hankali, wayar ta ta zara ta ga missed calls din abokan harkar ta,sai da ta samu daidaituwar numfashin ta sannan ta kira ASP Shalele, ta masa bayanin komai, tambayoyi ya mata, ta sanar da shi ina da ina ta bi har ta kai inda take a yanzun, sanar da ita ya yi ga shi nan zuwa, zai zo ya fitar da ita daga wajen,dan ya gane wajen. Ta fi awa biyu a wajen ta na jiran Shalele, tun mutanen wajen ba su damu da tsayuwar ta ba har suka fara bin ta da kallo, har su ka fara qus qus ana kallon ta, qoqarin barin wajen take saboda tsoron kar a kira 'yan sanda wayar Shalele ta katse ta daga qoqarin kunna motar, cikin fada ta dauka ta ce mishi, "Ka kuskura wani abu ya same ni a nan ka kuka da kan ka" "Ga ni nan na iso, na kuma hango ki, bani mintuna biyu zan iso inda kk" Kashewa ta yi bayan ta ja dogon tsaki, ko da ya kusan isa tana hango shi, kafin ya fito a motar ta ja ta ta, dan ba ta buqatar sake second daya a wajen, da gudu ya koma motar shi shima, ya bi bayan ta, daga baya ya shige gaba dan mata jagora, mutane dai na ta kallon ikon Allah. Direct gidan Alhaji Munkaila suka je,gida ne mai kyau irin na Alhazawan nan, masu ji da Nera, daga shi sai masu aiki, tunda matar shi ta rasu bai sake wani auren ba,gashi babu rabo tsakanin su, dan haka sai dai ya fita kasuwancin shi, da dare ya je wajen sharholiyar shi ya dawo gida ya kwanta, tunda yake bai taba kawo mace gidan ba, dan haka masu aikin gidan sun yi mamakin ganin mace mai irin shigar Eliza a gidan. Cike da bacin rai ta zube a kujera ta na maida numfashi, zuciyar ta ke tafarfasa, bacin rai, rashin nasara, da kuma kishi, su ke damun ta, ga uwa uba gajiya. Ta so zuqar sigari amma Alh. Ya hana, ya ce sai dai in ta koma gidan ta,ba zata zubar masa da mutunci gaban masu aikin shi ba. Bayan an gama gabatar da abinci da abin sha a dinning table ne, Alhaji ya gayyace su cin abinci, wanu mugun kallo Eliza ta watsa musu dika, sannan ta ce, "I want to go home,ina da abubuwan yi" "Dole ki jira in ma ba zaki ci abincin ba su Hon. Mamman Accu su zo, domin mu bamu gane me kk yi ba, in ba zaki iya handling issue dinnan ba zamu iya da kan mu, muna baki girman ki ne a matsayin ki na wadda ta ke kawo mana harkoki na ci gaba, ba dan haka ba da tuni mun aika an sheqe mana su, iyaka a sanar kashe su akai,mu bamu san meye shirin ki ba, kuma kin qi fadi" Cikin karyewar zuciyar da bata taba zata zata shiga irin shi ba akan namiji ta kalle su, idanun ta sun kawo ruwa, za ta yi magana ta fasa, ta koma ta zauna, domin jiran sauran. Har suka gama cin abinci ba su zo ba, cike da bacin rai ta fita, ba tare da ta kula kowa ba, ta zira key kenan mai gadi ya wangale gate, motoci suka shigo, sakin hannun ta tayi cikin gajiya da abubuwan da suka faru a yau din, ta fita ta koma parlourn, Bayan duk Alh. Munkaila ya kaisu wani parlour da ya ke na shi shi da marigayiya, sai da ya tabbata ba wanda ya ke iya jin maganar da suke a masu aikin shi suka fara gudanar da zaman nasu.Sanata Kabeeru ne ya kalli Eliza ya ce, "Uhumm? Muna jiran jin abinda ke faruwa ta bangaren ki," "Abinda ke faruwa shi ne na fara gudanar da duk wani salo da na san Mahboob zai fada tarko na, kuma na kula akwai alamar nasara, sai dai matsalar da aka samu wadda ita ce ta kawo min tsaiko shi ne, akwai jami'an tsaron da AIG Aliyyu ya sa suna kula da lafiyar Mahboob da Aaseeyah, yau da kyar na sha, su ne za su ban matsala wajen gudanar da qudiri na, yanzu shawara za mu tsayar akan yanda za a dakatar da wadannan jami'ai, ko kuma a dauke hankalin su gaba daya" "To yanzu me ye plan din ki na gaba?" "Plan dina shi ne na auri Mahboob, Aaseeyah ta rasa shi a kan idanun ta, kamar yanda na rasa masoyi na, sannan na kashe ta da hannu na dan daukan fansa,shi kuma Aliyyu na tabbata mutuwar Aaseeyah sai ta girgiza shi, domin shi din ya mace akan son ta,da raunin da ya yi da shi za mu yi amfani wajen ganin bayan shi," "Da kyau kyakkyawa mai kyakkyawan tunani, amma ya kamata ki gaggauta qaddamar da wannan qudiri naki, dan ni na matsu a gama da su mu samu wadan da za su maye gurbin su Gazaa da Sam, kar abokan gabar mu su yi ta kwashe garabasar kudade, mu muna nan zaune ba wata harka da ke shiga kuma ta fita" in ji Alhaji Munkaila. "Wannan gaskiya ne, ki sanar da mu akwai taimakon da kk buqata ne?" "Ba wani taimako, kawai dai kai Alhaji Munkaila kai zaka tsaya min a matsayin uba, daga gobe zan dawo nan gidan da zama, saboda cikar burin mu" "Allah ya kaimu,amma ni fa ba na son ki zo ki na shaye shaye masu aiki na na gani, rabin masu aiki na garin su daya da iyaye na, da kuma iyayen margayiya, ba na son abin da zai ja min magana a can qauye" Tsaki ta ja ta zari makullin motar ta ta fice, "Ya kamata mu takawa yarinyar nan burki akan tafiya ba tare da an sallame ta ba, "ASP shalele ya fada ya na mai bin qugun ta da kallo ya na lashe busasshen leben shi mai dauke da farin busasshen yawu gefe da gefen bakin shi. Ba wanda ya kula shi, dan kusan dik hankulan su na kan ta,sun jarabtu da qaunar kasancewa da Eliza amma ita sam ba sa gaban ta. ************************** Sadaka take ta bayarwa kamar kullum cikin shigar hijabi irin mai rufe sama da qasan fuska dinna, riga da skirt ne na leshi mai laushi a jikin ta, kalar makuba, ta yi kyau matuqa, ta na kammala bayarwa Mahboob na Parker motar shi a jikin ta ta, shiga ta yi ta na qoqarin tada wa ya tsaya gefen inda take zaune. "Baiwar Allah, ina da tarin tambayoyi dake kai na game da ke, amma gashi na ga alama ke din ba mai son kula mutane bace," "Haba malam, wanne irin mutum ne kai ba sallama ba komai zaka hau min wata maganar ta

Chapter 24 of 41