daban, dan Allah janye jikin ka a mota ta na wuce gida, an kusan sallar la'asar"
"Yi hakuri Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumussalam, ko kai fa" ta fadi cike da murmushin ta mai sanyi.
Ji ya yi ta burge shi, da alama ta na da son addini.
"In ba za ki damu ba zan iya sanin sunan ki?"
"Su na na Saratu Munkailah Mai Yadi"
"Masha Allah, Malama saratu,ina so na sanki sosai, amma da alama sauri ki ke, ya za a yi?"
"Kar ka damu da sanin ko ni wace ce, domin ba zai amfane ka ba, kuma ba zai rage ka da komai ba,so ina ga barin sani na shi ne ya fi maka alkhairi"
"Me ya sa za ki ce haka? To in ba ki son na san ki, ke ba ki son sanin ko ni waye?"
"Ba na buqata, saboda wataqila yau ne rana ta qarshe da za ka ganni, domin kuwa zan koma in da na fi wayo,nan qasar in banda baqin ciki da tarin damuwa ba abinda nake samu a cikin ta"
Saurin maida kwallar qaryar da ta fara tarawa a idanun ta ta yi, tare da tada motar ta, wannan abun da ta yi ya sake sanya Mahboob son sanin ko ita wace ce, da sauri ya zira hannu ya dau wayar ta da ta sanya a saman jakar ta da ke kan cinyar ta, danna no shi ya yi, ya kira, nan da nan ta ta no ta shiga wayar shi, ya yi saving da sunan da ta sanar da shi, ya na gamawa matsawa baya ya yi ya daga mata hannu, cike da mamaki ta kalle shi.
"Bawan Allah me ye haka? Ba ka nemi izini na va fa"
"Sai kin ji kira na"
Shi ne abinda Mahboob ya ce mata, ya wuce, ita ma ya na barin wajen ta bar wajen, cike da tsananin farin ciki, da nishadi, ranar ta sha barasa ya fi kwalba daya, saboda murna.
Bangaren Aaseeyah kuwa ta ga jimawar Mahboob ta yi yawa, ga baqon watan ta ya zo, ba tare da ta shirya masa ba,adaidaita sahu ta haye ta nufi gida, cike da takaicin rashin zuwan Mahboob da wuri.
Bayan ya samu tabbacin tafiyar ta ne wajen abokan karatun ta, ya juya motar shi ya wuce gida.
Ko da ya isa direct bangaren Mammee ya shiga, nan ya tadda Umaimah na taya Mammee girki, ta na sake koya itama, domin Noor na son girkin ta, ya na yabawa,shi ya sa take qoqarin koyan sabbin dabarun girki a kullum.
Bayan sun gaisa ne ya tambayi ina Aaseeyah, nan Umaimah ke sanar da shi cewar,
"Yah Mahboob yau kana cikin damuwa,domin Aaseeyah da fushin ka ta dawo gida"
"Na sani my dear, yanzu haka lallashi zani"
Ko da ya shiga ta gama sanya dankunnen ta kenan, ta na bare sweet za ta sha, da sauri ya sanya hannun ta a bakin shi ya fara tsotsar sweet din, takaici ya hana ta magana kawai sai ga hawaye sun fara zuba, ganin haka ne ya sa shi saurin ciro sweet din daga baki, ya miqa mata nata vakin, ya na mai bata hakuri, cike da shagwaba ta bude ya sanya mata, ta yi gum da bakin ta kamar ba ita ta fara kuka ba.
Dariya ya dan yi kadan ya zauna gefen gadon shima, sannan ya fara bata hakuri,
"Ni dai ka tafi kawai, na sanar da kai yau da wuri za mu tashi, amma shi ne ka qi zuwa da wuri, wa ya sani ma ko wajen wata ka je ka bar ni ni wato ga yar wahala na yi ta jiran ka ko?"
Gaban shi ne ya yi mummunar faduwa, shin ko Aaseeyah na da aljanu ne da suke sanar da ita komai? Kame kame ya fara, nan da nan kuwa Aaseeyah ta juya sosai ta fara kallon shi, cike da tashin hankali ta ce,
"Da gaske ne? Wajen wata ka tsaya?wace ce ita? Ka na son ta? Auren ta za ka yi ita ma?"
Kuka ne ya ci qarfin ta ta fita da gudu, ta bar mishi dakin, binta ya yi ya na bata hakuri amma inaa, dakin Abee ta fada ta san nan ne kawai baya shiga, a qasa ta zauna ta na kuka, tabbas wajen wata ya tsaya, tunda ya fara kame kame.
Kwankwasa qofar ya yi ta yi ta qi fita, sai da Mammee ta ji bugun ya qi qarewa ta je ta wuce shi, ta kulle qofar, ni dai ban ji me ya faru ba na dai ga Mammee ta koma kitchen Aaseeyah ta fito ta na zumbura baki, tare da matso hawaye na dole dole sai sun fito.
Da sauri ya kama hannun ta daya,ta fizge,
"Ok ba zan sake riqe maki hannu ba,amma ki saurare ni, ni ba wajen wacce na tsaya, me ya sa kk zargi na ne wai? Ko kin taba jin wani mummunan labari akai na ne?"
Cikin shagwaba ta ce,
"Ban taba ba, amma na rasa me ya sa nake yawan tunanin wata a rayuwar ka, zuciya ta ta kasa nutsuwa, ji nake kamar akwai wani al'amari mai girma dake tunkarar mu, zuciya ta na bani akwai wani abu, amma ba zan iya cewa ga shi ba"
"Kuma ita zuciyar taki, sai ta maqale maki akan dole dole wata macen nake so ko nake zuwa gani ko?"
Tura baki ta yi, shi dariya ma ta bashi, cikin shagwava irin na ta ya kama ciki, tare da kiran,
"Washhh Allah na, ciki na"
Da sauri ta dafa kafadar shi, tare da duqawa ta na kallon cikin idanun shi, da ke dauke da tsantsanr soyayyar ta, ta ce,
"Me ya sami cikin ka?"
"To to ba yunwa nake ji ba, na dawo mata ta bata ban abinci ba, amma ta na zargi na"
"Dan Allah ka daina cewa zargi, ni fa ba zargin kana aikata wani abu nake ba, da na tambaye ka ne na ga ka tsaya kame kame, kuma ni wasa nake,ban ma san me ya sani fadin han ba,shi ya sa kawai na zaci ko da gaske wajen wata ka tsaya"
"Na gaji da maganar wata, ni dai yunwa nake ji"
Abinci ta je ta hada masa, ya ci ya qoshi, ya yi hamadala, sannan ya miqe a kujerar, tare da kafe ta da ido, cike da gajiya, ya na ayyana da ba dan kar a ga rashin kunyar shi ba da ta raka shi sashen shi, ta taya shi ko da cire kaya ne, ya gaji matuqa.
Wayar shi ce ta fara qara, miqawa Aaseeyah hannu ya yi, dan ta fi shi kusa da wayar, dan haka hannu ta sa ta daga wayar, kamar an ce ta duba, sai ta ga suna kamar haka,
'SARATU MUNKAILA MAI YADI'
Da sauri ta daga ta kara a kunnen ta, tai shiru,
"Hello?"
Ita ce kalmar da Eliza ta furta cikin muryar ta da ta kashe ta zaqaqa ta dan salon sace zuciyar Mahboob, a qasa Aaseeyah ta sake wayar, ta na kafe shi da idanun ta da suka kada suka yi jawur, ko hawayen ma ya qi zuba, duk saurin kukan ta.
Ganin haka ne ya sa Mahboob saurin daukan wayar shi da ke qasa a yashe, ya na jiyo muryar Eliza, na fadin,
"Waye me No dinnan ne? Na ga an kira, kuma na biyo kira ba a magana,....hello? Waye ne?"
Wani yawu Mahboob ya hadiya, ya kalli Aaseeyah cike da tashin hankali.
'Ohhh shi ne ma ya nemi No ta ya kira ta ko?'
Hummmmmmmm Mahboob ka fara kuka kawai, shawarata kenan,ku fa? Meye shawarar ku?
PAGE 38
Idanun ta sun kad'a sun yi jawur saboda kishi, Mahboob kuwa ya gaji da kallon da take bin shi da shi, dan haka bayani ya bude baki ya fara,
"Kin ga,ba abinda ki ke tunani ba ne, a...."
Hannu ta daga masa a zafafe, ta tsallake table din tsakiyar wajen ta shige dakin ta ta kulle qofar ta, kwantawa ta yi a gadon ta,sunan Saratu na sake yawo cikin idanun ta,ta saba yin kukan ba gaira ba dalili, dan ita ta yi awa biyu ta na kukan banza ba damuwar ta bane,amma wannan kukan jin shi ta ke daga qasan zuciyar ta,har maqoshi zuwa idanun ta, zuciyar ta na suya da quna,ashe dama ba son ta yake ba? Kalaman shi qarya ne, yaudara ne? Tun kafin su tare har ya fara yin 'yan mata,yaushe ma har ta yi sake tayi sanyin da za a wulaqanta ta haka, ba zata taba barin Mahboob ya yi nasarar wulaqanta ta ba,tun kafin ta tare a gidan shi ya fara hulda da wasu matan, ai ba tai lalacewa har haka ba.
Kuka ta ci ta godewa Allah, ta na ji Umaimaih na buga mata qofa, ta na mata sallama zata koma sashen su, tai banza da ita, tare da murgud'awa qofar baki kamar Umaimah na ganin ta,
"Sai na yi maganin yayan ki, zai san Aaseeyah ba wadda za a ciwa mutunci bace ta kyale"
Kwafa ta yi ta maida kan ta jikin pillow ta bare baki ta n kuka, sai da tai mai isar ta ta yi brush, ta daura alwala ta fita, a parlour suka hadu da shi, da alama bai koma ma sashen shi b dan hutawa ko sauya kaya.
Mammee na ta kallon ikon Allah, ya zauna yarinya qarama na qoqarin juya shi, ta so shiga lamarin amma sai ta miqe ta shige wajen mijin ta da ya dawo ba da jimawa ba.
Mahboob da sauri ya miqe ya bi Aaseeyah kitchen ya na mata bayani,
"Kin san Allah, ni ba wani abu dake tsakanin mu, dama kawai mun hadu ne a hanya sai na amshi lambarta,"
'Kuuuutt, na ma zaci ya ce irin abokiyar aikin shi ce, ashe ma amsar lambr ta ya yi? Daga yau ko lambar Mammee aka ce ka yi saving sai ka yi tunani'
Ba wanda ya isa karanta yanayin da take ciki, saboda boye dik wani yanayi da zuciyar ta ke ciki da ta yi, qoqari ya ke ya fahimci shin ta yarda da shi ko kuwa?
Ta na gama yanka fruits ta dauka ta shige dakin ta, qafa ya sa ya tokare qofar, zai shiga, wani irin kallo ta sakar mishi, da ya sashi saurin janye qafar shi kamar qaramin yaron da ke laifi ya jiyo motsin maman shi.
Danna qofar ta tayi ta rufe,kwankwasa mata ya fara,ya ji qofar Mammee na budewa, da gudu-gudu ya bar wajen,sashen shi ya nufa, ya watsar da jakar shi da rigar shi ta saman, ya fada kujera a ruf da ciki, qara ya saki a cikin kujerar, sannan ya sake hannun shi qasa, jikin shi a sake ya ke magana,
"Ni fa ban ce ina son kowa ba bayan ke Aaseeyah,ke ce farin ciki na, ke ce macen da zan iya rayuwa da ita cikin so da qauna da aminci, me ya sa zaki fushi da ni bayan ba ki ji na ce ina son ta ba?ni fa kawai burge ni take,kuma ina son jin me ne ne labarin ta da ke sata kuka da damuwa, a matsayin ta na wadda ta ke cikin daula"
"Aaseeyah plsss ki daina fushi da yayan ki kuma mijin ki"
Ya na fadar mijin ki na qarshe dabara ta fado masa, murmushi ya yi ya miqe ya na rangajin gajiya,ya shiga wanka.
Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya ma Mammee waya, ya maqale murya,
"Mammee dan Allah ina son tea da dan maganin ciwon kai, zan shigo na dauka,"
"Subhanallahi, kan ne ke ciwo haka? Anya ba zazzabi? na ji muryar ka na fita da kyar,"
"Eh a d'an kwai zazzabin ma Mammee, bari n zo na dauka, jiri na ke dan ji"
"Subhanallahi, to ko za a je asibiti ne?"
Da d'an qarfi ya ce,
"Ah ah ba sai an je ba,...maganin kawai ya isa"
Bayan sun gama magana da Mammee, ta hada masa Tea mai kyau, ta dora a dan faranti ta saka maganin a gefe,dakin Aaseeyah ta shiga ta baza littatafai ta na karatu,
"Maza taso ki kai ma Mahboob bashi da lfy,yi sauri"
Tunawa da messages din shi na dazu, da ya yi ta turo mata ta yi ,nan da nan kuwa haushin shi ya sake kama ta, message ya dinga mata akan ta je wajen mijin ta ko Allah da mala'iku su yi fushi da ita, ita kuma ta qi reply, wato shi ne ya bullo ta nan, ba komai, za ta yi maganin shi.
Har ta amsa, zata fita sai ta ce,
"Mammee ki je kawai, bari na saka hijab babba,"
"To ki sauri ya na jin jiki daga jin muryar shi, in ta kama ma ki kwana ki kula da shi ba komai, in kuma za a asibiti ki kira ni,zan sanar da Abeen ku,hanzarta, ki masa sannu in ji ni"
"To Mammee"
Hijabi ta saka a saman rigar baccin ta, ta dau farantin ta bi ta kitchen,inda suke ajiye magunguna ta je ta bude, wani magani ta dauka, guda biyu ta jefa a tea din, ta juya,sannan ta yi murmushin mugunta ta fita, ya na tsaye bakin qofar shi ya hango ta tafe, da gani a tsorace take, murna ya fara ya gudu dakin shi ya kwanta akan akan gado ya duqunqune da bargo,sallama ta yi ta ji shiru, dakin ta nufa.
Da ganin shi ta gane ciwon qarya yake,
'Yanzu za kai na gaske bawan Allah'
Ajiye farantin ta yi ta balli maganin ta miqa masa da tea din,ya bude baki alamar ta sa mishi, ba musu, ta kuwa saka masa, ta bashi tea din, ya dan kurba ya kauda kai, ba ta ce komai ba ta sake miqa masa tea din,shi kuwa sai ya ji zuciyar shi wasai, Aaseeyah na shayar da shi tea, har wani lumshe ido ya ke,duk da yanayin sauyawar d'and'anon da ya ji,amma haka ya zuqe tass.
Qoqarin tafiya ta yi ya ja ta ta fada jikin shi, bata hana shi duk abinda ya yi niyyar yi ba dan ta san mintuna uku sun yi yawa maganin zai fara aiki.
Sunsunar fuskar ta ya ke ya na shaqar qashin iskar baki da hancin ta da take fiddawa, qamshin kamar na sweet, a koda yaushe haka qamshin bakin ta ya ke,ya na mamaki kamar wadda ke ajiyar sweet kullum a ciki, tunawa ya yi shi sai da ya yi brush sannan ya dan sha sweet dan kar ta ji warin bakin shi, amma ita a kowanne lokaci bakin ta qamshi yake, lumshe idanun ta tayi, dan in ta ce bata ji komai ba tayi qarya, ya na gaf da dora lips din shi akan nata cikin shi ya bada wani irin sauti mai qara,da sauri ya bude idon shi, ya damqe cikin, a kunyace ya juya baya, ji ya yi kamar zai tusa, dan haka ya ce ma Aaseeyah ,
"Uhmm...je ki ciki ko, ina ga maganin ki ya yi aiki,kan nawa ya yi sauqi,sai da safe,"
Kallon shi ta yi cikin dakewa ta ce,
"Mammee ta ce na zauna n kwana anan, in kuma ka na so na koma ta ce na qi bin umarnin ta to muje ka raka ni"
Inaaa abinda ya ke ji, ai in ba bayi ya fada ba ko taku uku bazai yi ba zuwa waje zai fito, walau tusar walau gudawar.
A guje ya tsallake ta ita da cup din tea din ya fada bayi, rufewa ya yi ya dan buda qafar shi dan ya yi tusa ba tare da ta ji ba, sai ya ji abu suuuu ya fita, ajiyar zuciya ya sauke, can kuma ya ware ido daya ji dumi na bin qafar shi, ko da ya bude ya duba sai ga gudawa, mai shegen wari, ga shi cikin shi na sake murdawa,a gaggauce ya cire wandon shi ya haye saman shadda, ba abinda ka ke ji sai qarar tusoshi da zawo,
"Buuuuurrrrr barrrrrr"
Aaseeyah kuwa me za ta yi in banda dariya, har ta na fadowa qasa ta na hawaye,Mahboob sai da ya gama ya wanke wandon shi, ya yi wanka, ya daura tawul ya fito ya na dafe gini, ya ga Aaseeyah zaune kamar ba ita ta gama sheqa dariya ba, wata jarida ta dauka ta na dubawa.
Wata iriyar kunya ce ta lullube shi, kamar qasa ta bude ya shige, shi a rayuwar shi ma gaba daya zai iya tuna sanda ya yi gudawa? Sam ba zai iya tunawa ba, ya na da ciki mai kyau, komai ci yake lafiya qlou.
Ya na tsaka da tunani, dajin kunya cikin shi ya murda sai da ya duqa,wani qara cikin ya yi, a guje ya koma bayin, ya na fadawa Aaseeyah na zubewa a qasa dan dariya.
Kanta har sarawa yake tsabar dariyar mugunta, ya jima yana zazzage gudawar da ta taso masa ya sake fitowa cike da jin kunyar ta,
"Aaseeyah dan Allah ko za ki amson maganin wannan ciwn cikin? "
"Na kawo maka iya abinda zan iya, ba zan fita ba a wannan daren, tsoro nake ji, sai dai ka wa Saratu waya ta kawo maka daga gidan su"
Rigar shi jallabiyya ya zaro zai saka, ya bude baki ya ce,
"Aaseeyah ni fa ba budurwata bace,kawai..."
Kululululuuuu, shi ne qarar da cikin shi ya yi, wata zuface ta karyo masa, da sauri ya zira rigar, duk sai ya ji ba shi da kwari a jikin shi,bayin ya koma, ya sake fesa wata gudawar ya fito, Aaseeyah na goge idon ta ya xauna kusa da ita, cikin yanayi na ban tausai ya ce,
"Dan Allah muje na raka ki ki duban ko akwai,sai mu dawo,dan ba zan iya kwana a hka ni kadai ba, sai na ke ji kamar zan mutu kafin safi..."
Da sauri ta rufe masa bakin shi da dogayen yatsun ta, ta kada masa kai,sai kuma ta ji nadama ta fara shigar ta, dama bata zuba maganin da yawa haka ba, amma ai shi ya jawo, shi ya takale ta rigima, ita kuwa rigima ma ba da ita ake ba shiga take balle an tabo ta, dama ta jima batai tsiya ba.
Tashi ta yi ta ce ya jira ta, a tsorace ta koma wajen su, ta duba kaff gidan ba maganin tsaida zawo,salati ta hau yi,ta koma, ta na shiga ta ji ya na sake fesa wani zawon, yanzu ba abinda ke fita sai manyan tusa da ruwa.
Ga dariya ga tausayi, komawa tayi ta hado masa ruwan gishiri da sugar, cikin jug ta dawo.
Kwance ya ke a gadon ya yi ruf da ciki, ga bacci ya na ji, ga shi ba damar yi, tsiyaya masa ta yi ta ce,
"Tashi ka sha wannan, jikin ka zai kwari, na duba kaff ba maganin zawon,sha wannan kafin safiya a je asibiti"
Ai kuwa kafa kai ya yi ya shanye.
Kusan a haka suka kwana, ba su rintsa ba, Mahboob ya shiga bayi ya fi sau a qirga, tun ya na shiga shi kadai har sai da ta fara rakashi bakin qofa, duk jikin shi ya sake, a wannan lokaci kuwa ta yi nadamar abinda ta yi ya fi sau a qirga,amma fa da ya fara zawon za ta kafa dariya, saboda qarar fitar shi.
Da assuba ta sanar da halin da suka kwana, likita Abbu ya ma waya,sun yi sa'ar samun shi a waya, nan ya zo ya masa allurai, aka qara masa ruwa, aka bashi magani, rubdugu aka masa ya samu kuwa nan da nan bacci ya dauke shi, su na zaune ana tattauna rashin lafiyar tashi Aaseeyah ta yi bacci a kujerar da take zaune a dakin, Abbu ne ya ce, kowa ya fita a bar su su huta, jiya da gani ba su rintsa ba.
Mammee sai da ta rufe ta sannan ta tafi, Aaseeyah kuwa bacci ta yi mai kyau da mafarkin zawon Mahboob, a mafarkin ta dinga kyalkyala dariya, ta na masa gargadin ya kiyaye ta, in ba haka ba gaba sai ta masa mafiyin wannan.
Baccin awa uku ta yi ta miqe a tsorace, dubawa ta yi ta ga Mahboob na baccin shi kamar wani jariri, cikin nutsuwa, duk idon shi ya fada,wayar shi ta dauka ta goge no Eliza, sannan ta ajiye ta fice abun ta.
Shiri ta yi ta wuce makaranta, Mammee na ta mata fadan ta tsaya ta karya, ruwan tea kawai ta kurba ta fice.
(Sabo da wanke baki akai akai na maganin warin baki, ba dole sai sau uku a rana ba, duk sanda kk ji bakin ki na buqatar wanki wanke shi,ba za ki dawwama shan sweet ba ai, zaqn ma illa ne in ya yi yawa,saba da dan tauna kaninfari ko d'aya ne in kin wanke bakin, ki saba da kin gama cin abinci ki kurkure bakin tasss har sai kin ji ba komai, sannan ki sha ruwa,inshaa Allah za a rage warin baki,yin dunkummm da baki ba ko da tasbihi ne ya na sa bkin ya yi gumuss, a dinga barin iska ta na shiga ta nafita.)
************************
Kwana biyu Eliza bata ga Mahboob ba, hankalin ta ya tashi da na Alh. Munkaila, dan kuwa hauka ta dinga masa a gida, da kyar ya lallaba ta tare da mata alqawarin ta fita yau, kwana na uku kenan, za ta gan shi, kamar ba zata ji maganr shi b dai ta shirya cikin doguwar abaya, ta sha turarukan ta masu qamshi, ta yane kan ta da mayafin kayan, ta saka takalmin ta mai tsini kamar yanda ta saba, ta dau makullin motar ta da wayar ta, ta fice.
Ta na tsayuwa ya na wucewa, a hanzarce ta sake tada motar ta, ta sha gaban shi, sun je daidai danja, an tsaida su, kawai ta jingina kan ta da kunjera, ta fada duniyar tunanin yanda lamura ke neman cabe mata, horn ya dinga mata, na bayan shi na mi shi shima.
Kewaye ta ya yi,ya kalli gefen da take zaune,dan ganin mamallakin motar,nan take ya gane ta, magana ya mata da qarfi ya ce,
"Malama Saratu in tunani za ki yi, ki na samun waje ki zauna a gida, ko ki tsaya a gefen titi,"
Muryar shi ce ta dawo da ita daga duniyar da ta fada, su na hada ido ta sake mishi murmushi, gaba ya yi, ya samu waje nesa da Titi ya tsaya, bin shi ta yi cike da farin ciki, yau dai ba maganar jan aji, komai za a yi shi ya qare a yau.
Ya na tsaye jikin motar shi, ta fito daga ta ta,kallon juna sukai suka yi murmushi,
"Malama Saratu ya kamata ki samu ki sanar da wani damuwar ki, ko da mahaifan ki ne, wataqila kin rage tunani"
Hawayen kewar shi da suka taru mata ne suka gangaro a kuncin ta,da sauri ta fara share su, shi kuwa cikin tausayi ya kalle ta ya ce.
"In kin amince da ni,kin yarda zaki iya fadan damuwar ki, na miki alqawarin zan taimaka maki wajen maganin ta,ban san meye dalilin da ya sa na damu da sanin ke wace ce ba, amma koma dai meye ina fatan ya zama alkhairi"
"In har ka shirya jin labari na ina gayyatar ka gidan iyaye na,saboda ba labari bane n kan hanya"
Kati ta duqa cikin motar ta ta zaro, na wani biki da ta je, biro ta amsa a wajen shi ta rubuta masa adireshin gidan Alh. Munkaila.
Amsa ya yi ya mata alqawarin zuwa a week-end,sallama suka ma juna suka tafi.
Eliza na ta murna, ta na ayyana irin qaryar da zata zabga masa, dan ba zata taba bashi tarihin rayuwar ta na asali ba.........
Ina sake baku hakurin ji na shiru, inshaa Allahu daga yanzu da izinin Allah za mu ci gaba sai an gama mu tsaya.
PAGE 39
Mahboob ne shirye cikin qananan kayan da suka yi mashi matuqar kyau, kasancewar week-end ne, ya qudurta ziyartar Eliza, ba bu wanda ya nasarwa, dan ko cikin gida ranar bai shiga ba, a bangaren shi ya karya, Ummee da taji shiru be je gaishe ta ba sai ta sanya mayafi da kan ta, ta debi soyyyan nama a mazubi madaidaici, ta je bangaren na shi da kan ta, a tunanin ta ko zawon ne bai yi sauqi ba, ko da ta shiga sai ta ji parlourn ya game da wani sihirtaccen qamshin turarukan shi, irin wanda ya saba amfani da su tun a Jordan.
Sallama ta rangada masa, tare da ajiye dan madaidaicin kwanon da ta kawo masa soyayyan nama, ko da ya fito murmushi ta sake, shi din ma murmushin ya mayar mata da shi, sannan ya dan duqa ya gaishe ta, ta amsa cike da qaunar shi a ran ta.
"Da ace mace ne kai tabbas da ka fi Umaimah dakko kamannin Zainab, Allah ya jiqan 'yar uwa ta"
Goge 'yar kwallar da ta taru mata ta yi, shi dai bai ce
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 41