Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sissiyar na daga abinda ta bari. Abbu ya ce za su kira masana ilimin rabon gado, a raba dukiyar domin duk mai haqqi a ciki a bashi, nan suka mata addu'a tare da sauran magabatan su, hira ta barke kuma, kowa na tambayar shi abubuwa kala kala. Duk abinda ake Umaimah na manne da qafafun shi, kamar zai gudu, shi kuwa ana hira sai ya dora hannu akan ta, cikin qauna irin ta yaya da qanwar shi, ji take kamar su dawwama a wannan yanayi, saboda qaunar shi dake sake huda jinin jikin ta, bata taba zaton ta na kewar shi ba sai da ta gan shi,kamar daga sama ta ji ya ce, "Yauwaa Umaimah irin tarbar da kk min d'azu kenan ko?" Rantsuwa ta dinga yi, ta na masa bayani ba ita bace, ya na sane ya qi amincewa, ya ce ba komai ya yafe mata, amma kar ta sake, abun ya mata zafi ya qi yarda ba ita bace, ta yi iya qoqarin fahimtar da shi Aaseeyah ce amma ya ce ba komai ya yafe mata kar ta sake kawai, Aaseeyah ta sa fuskar tausayi ta nuna ita sam ba ita ba ce, murmushin gefen baki ya yi irin nata in ta na son yin mugunta, Aaseeyah ta gane irin murmushin, nan fa murna ta kama ta, a zaton ta akan Umaimah murmushin yake. Iyayen su maza ne suka fara tashi domin zuwa masallaci, Mammee kuwa da Ummee yau ce kusan rana ta farko bayan shekaru da dama suka zauna waje guda, suke hira cikin kwanciyar hankali da jin d'adi, abinda Mammee ta so matuqa a yi tun farkon zuwan ta gidan amma bai samu ba. Sai da suka ji kiran sallah kowa ya tafi dan gabatar da sallah. Ta chat ya ce ma Aaseeyah ta kawo mishi ruwan shayi, ba ya son kwanciya ba tare da ya sha ba, ta fad'awa Mammee, kitchen suka shiga ta dora shayin mai cike da kayan qamshi, ta juye a flask ta ba Aaseeyah ta kai mishi, tare da sanar da ita ta tambaye shi ko akwai abinda yake so. Aaseeyah na dosar dakin ta ji wari warin da ba ta taba ji a cikin gidan nasu ba, cikin son dauke numfashin ta ta shiga parlourn, ya na zaune ya mimmiqe qafa, ya na zuqar sigarin shi abin shi,hankalin shi kwance, sauran kad'an ta yarda flask din, cikin nuna tashin hankali ta ke bin shi da kallo, shi din ma miqewa ya yi ya na mata kallon me ya faru? "Shaye shaye ka ke dama baka taba fada min ba?" "Shaye shaye kuma? Me na sha?" "Gashi nan ka na shan sigari, irin na yan daba,innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Yah Mahboob ka gaggauta kashe sigarin nan, kuma kar ka qara sha dan kuwa in Abbu ya gan ka kashin ka ya bushe, Abbu ya tsani duk wani dan shaye shaye,in ya ga masu shaye shaye damqa su yake wajen hukuma nan take" Da sauri ta hau rurrufe windon parlourn, ta re da rufe qofar a qoqarin ta na hana hayaqin fita waje, room freshner da aka ajiye a bangaren ta shiga cikin daki da sauri ta dakko ta hau fesawa a ko ina,kallon ta kawai yake ya na jin wani yanayi na shigar shi game da ita, lallai Aaseeyah na da wani boyayyan lamari a tattare da ita, wanda ke jan zuciyar mazaje a gare ta, abinda ya ke ji bai taba jin irin shi game da wata mace ba, kallon yanda ta ke qoqarin rufa masa asiri akan abinda bai ma dauke shi laifi ba, shaye shaye da take magana daban da shan sigari a wajen shi, shan sigari kamar wata al'ada ce da ta bi jikin shi, kuma ba ya jin zai iya barin ta kai tsaye, amma dole ne zai kiyaye shan ta a cikin gida, saboda kiyaye abin da Aaseeyah ke gudu. "Shukran lake ya Bint al-3m" Yanda ya ke kallon ta da yi mata magana ya sanya ta rusunar da idanun ta qasa, cikin jin nauyin shi, ta mishi sai da safe ta fita. Bayan fitar ta Noor da 'yan biyu suka shiga, nan sukai ta hirar su irin ta samari, ya na sake karantar qannen nashi. Anan ya fuskanci Noor na da ibada, akwai son kiran Allah a komai na shi, ga ilimin addini da na zamani ya hada, su kuwa 'yan biyu ba su da wani ilimin addini sosai, amma akwai wayo da wayewar boko. Nan suka kwana wajen Mahboob, cike da jin dadin dawowar yayan nasu. Washegari da safe kuwa, Ummee na can na nata girkin dan yi masa abin karyawa ita da Umaimah, a cikin 'yan matan nata Umaimah tafi kowa qaunar shiga kitchen, dan haka ta fi su kwarewa wajen girki, dan ma wataran ta na shan fad'a da hantara wajen Ummee, watarana kuwa in 'yan mutuncin na kusa lafiya qalou za su yi komai su gama. Aaseeyah ce ta fito kan ta ba dan kwali kamar kullum, gashin ta a daure a bayan ta, rigar bacci ce jikin ta mai siririn hannu da gajeran wando, (a haka take yawo gaban yayun ta maza masu son matan tsiya ba mai hana ta, ko da ke iyayen su ba su san me yaran nasu ke ciki ba) Kitchen ta nufa inda ta ke jiyo qamshi, ta na zuwa ta tsaya a gefen Mammeen ta, tare da miqa hannu ta dauki soyayyan bread din da ya sha kwai a ruwan kwan ta daka nama ta sanya su tattaruhu da albasa garlic da curry, sai dan gishiri kadan. Lumshe ido Aaseeyah ta yi sannan ta ce, "Kaiiii Mammee na ko a qasar waje ba za a samu gwanin girki kamar ki ba" "Ke kuwa ga shi har yau kin kasa zama gwana, in kin dafa abinci sai an qara gishiri ko maggi, watarana sai an saka yaji ya ciyu," Dariya suka yi, sannan Aaseeyah ta ce, "Ai Allah Allah nake mu gama WAEC na samu na maida hankali akan girki," "In kuma ki na gamawa aure ya zo ba ki iya girki ba fa?" Wata kunya ce ta kama ta, nan da nan ta ayyano Yah Noor a ran ta,murmushi ta sake saki, sannan ta ce, "Mammee ai mijina zai bar ni na iya girki kafin ai aure" "Auuu haka kuka yi da shiii?" "Ah ah amma zan tambaye shi" Juyawa Mammee ta yi ta na kallon ta, "Waye mijin naki?" Aaseeyah na shirin fadin sunan mijin Abeen ta ya shiga kitchen din, ya na shaqar qamshin girkin Mammee, ya na lumshe ido. "Me ake dafa mana ne duk gidan ko in ce unguwar ta cika da qamshi" "Ba wani abu ba ne ba fa, abun kari na ke yi, na ma gama," Farfesun naman kazar da ya sha kayan lambu da dankalin turawa ta buda, nan qamshi ya sake dukan hancin su, ya ji albasa da garlic, yawu Aaseeyah ta hadiya, ta ce, "Mammee ni dai ki yi ki gama ki zuban nawa, bari na je na yi wanka" Da gudu ta fice,Abeen ta na maganar gudun da har yanzu ta qi dainawa a matsayin ta na budurwa. Hakuri ta bashi daidai sanda ta bude dakin ta ta fada. Wanka ta yi ta sha gayu da riga da skirt na atampa, mai kalar pink da blue a jiki, dinkin ya zauna das a jikin ta kamar a jikin ta aka dinka shi, ta yafa qaramin mayafi ba tare da ta daura dankwalin kayan ba, qamshin ta mai sanyi na shiga qofofin hancin duk wanda ya zauna kusa da ita. Abinci Mammee ta bata dan ta kai bangaren Mahboob, ta na shiga da sallama tai karo da manyan mazubin abinci daga wajen Ummee, ajiye na hannun ta tayi, Hussein sai miqa ya ke ya na hamma,tare da kwala ma sauran kira akan su zo su ci abinci yunwa yake ji. Dikkanin su ba su yi wanka ba, Mahboob ne kawai ya yi wanka, ya sanya jallabiyya fara, ya taje kan nan luf ya na sheqi, gemun shi sai daukan ido yake, sakatooo Aaseeyah ta tsaya ta na kallon shi, Noor ne ya fito ya na sanya T shirt din shi yai ido hudu da Aaseeyah da ke kallon Mahboob kamar doluwa, Mahboob din shi ma ita ya ke kallo, ya na ganin yanda atampar ta bi dik wani lungu da saqo na jikin Aaseeyah ta kwanta, kamar a jiki aka dinka,ta mishi kyau sosai kamar babyn roba. Tsaki mai qarfi Noor ya ja, cikin tsawa ya ce ma Aaseeyah, "Keee! Ina hijabin kin? Ban hana ki yawo ba babban hijabi ko mayafi ba, gida dik maza ki dinga yawo tsirara, dalla bar nan" Hussein ne ya murmusa, dan ya gano kishi ne kawai ke damun Noor, tunda dai ya san komai, kar ta san kar ne. Hassan ne ya ce, "Dan Allah Yah Noor, Yah mahboob ku zauna mu ci abinci, yunwa zata yi kisa anan, qarfe fa tara yanzu" Da sauri Aaseeyah ta juya ta koma bangaren su, ta na tura baki, "Shi Yah Noora nan sai ya dinga ma mutane fada, kamar ni kadai ke saka irin kayan nan, naga dai duk abinda na ke da shi kusan su Yesmeen ma na da shi, amma bai taba hana su sawa ba sai ni marainiyar wayon shi" Ta na qunquni ta gama dibar abincin ta ta koma parlour ta zauna ta na ci, ta manta da tea din d za ta kai musu Mammee da ta shiga ta ga ba a kai ba ta kira ta, ta bata akan ta kai, ko komawa ta dau siririn mayafin batai ba, dan ba ta san ma ya fadi ba. Ko da ta isa cikin bata fuska ta ajiye za ta juya, Noor ne ya miqe da sauri ya bi ta, kafin ta yi maganar me ya sa yake bin ta ta ji qozo mai mugun zafi akan ta, ihu ta saki ta fadi a qasa ta na shura qafar ta, tare da dafe kan ta, Mahboob ne ya isa gaban su da sauri, ya na qoqarin d'aga ta, Noor ya riga shi kama hannun nata, cikin zare ido ya ce, "Kin min shiru ko sai na qara miki, saboda kin raina ni da na maki magana shi ne ki ka ma cire tayani gantalin kk zo a haka ko? Ke ga kajol ta india sarkin gashi ko," Sai a sannan ta san ma laifin da tai, cikin kuka ta ke bayanin ita ba ta san ya fadi ba, Mammee ce ta bata tea ta kawo musu, "Mammeen ce ta ce ki fito gaban maza qansan qansan haka" Kada kai ta yi alamar ah ah, "Bar nan wajen sokuwa kawai, ki sake fitowa tsirara ki gani" Mamaki ne fal cikin Mahboob, wannan wanne irin fada Noor yake kamar ta je gaban garadan unguwa ta tsaya ba kaya, 'yan biyu kuwa kamar ba sa wajen, abincin su suke loda. Dafa kafadar Noor Mahboob ya yi, tare da fada masa, "Ka yi hakuri, ka dinga bin qannen ka da sanyin hali, in ka na musu zafi haka za su raina ka, za su tsane ka" Wani kallo ya zuba ma Mahboob din, daga baya kuma ya sauke idon shi, tare da masa godiya, ya ce zai gyara, abincin da bai qarasa ci ba kenan, duk da dadin da ya mishi, tsallake abincin ya yi ya koma daki ya dau wayar shi ya bar bangaren nasu. Da fushi ya shiga dakin shi, wani irin zafi qirjin shi yake mishi, ba ya so sam ya ga Mahboob na ma Aaseeyah kallon nan.mai sanyi, ya sani sarai Mahboob gaba yake da shi, kuma ya fi shi kyau da komai, shi ya sa ya ke jin tsoron kadaicewar Aaaseeyah da Mahboob, a baya ya zaci sha'awa ce kawai ya ke ma ta, amma yanzu ya fuskanci akwai soyayyar ta a ran shi, ba kuwa zai bari daga zuwan wani sama ta ka ya janye ta ba. Ya na nan ya na saqe saqe Umaimah ta shiga dauke da tray din da ta saka kayan abinci a kai, Ummee ta ce ta kai mishi abincin shi, dan bata san bai ma kwana a wajen su ba. Ta na shiga ta gan shi kwance ido a lumshe, rufe qofar ta yi ta ajiye abinci a gefe, sannan ta kwanta a gefen shi, ta raba kusan rabin jikin ta a nashi, ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi, sannan ya bude idon shi akan fuskar ta, "Umaimah baki da hankali ne, in wani ya shigo fa?" "Ai na rufe qofar" Tashi ya yi ya na dan tsaki, sannan ya kula da me ta kawo, jan abincin ya yi, ya fara cin dankalin turawan da aka soya cikin kwai, bayan an cusa nama a tsakiyar shi, tea ta hada masa ta miqa mishi, godiya ya yi, ya na ci ya na zurfafa tunanin shi, Umaimah ta sha mamakin yanda ya nuna halin ko in kula da kasantuwar ta a dakin, duba da yanda yake luguiguita ta in ta je gare shi, sai ya samu biyan buqata da ita yake barin ta ta bar dakin shi, amma yau ko ta kan ta bai bi ba,har ma fada ya mata wai in aka gan su fa, yaushe ya fara damuwa da hakan? Fita ta yi zuciyar ta na quna, da niyyar za ta bashi lokaci ta san zai neme ta ne. 'Yan biyu ne suka koma da kwanukan da suka ci abincin, suna ta tsokanar Aaseeyah da ke kukan ciwon kai, Mammee na bata hakuri da lallashin ta. Barin parlourn ta yi ta koma dakin ta dan sai su sa ta kukan da ya fi na yanzun dan tsokana. Wayar ta ta gani ta na ringing alama ce na ta jima ta na ringing din, dauka ta yi ta amsa, "Ki zo ina neman ki" "To" Kashewa ta yi ta fara neman hijabi domin zuwa kiran da ake mata........ Toooo sai in ce Aaseeyah a sa hijabi har qasa duk da ban san me kiran ba dai😛😜 TAUBASHI PAGE 16 Hijabi ta nema kalar pink mai laushi, ta sanya, sannan ta fita, ta na tura baki,ta na shiga wajen ta ji shi shiru, kamar ba kowa, ta jiyo hayaniya a bangaren Mahboob,wataqila su na can, "Ohh ba za su bar bawan Allahn nan ya huta ba, tun da ya dawo ba na jin ya samu lokacin kan shi shi kad'ai ba tare da wani ya dame shi ba" Tura qofar ta yi dauke da sallama ta shiga, kwance ya ke kamar mai bacci, fuskar shi na kallon sama,hannun shi a saman kan shi, ya na kad'a qafar shi, "Gani Yah Noor" Ta fad'a cike da tura baki, dan fushi take da shi sosai. Bude idanun shi ya yi fess akan ta, hijab din ma sai ya ga qara mata kyau ya yi ba ragewa ba, tsaki ya dan ja kafin ya miqe zuwa gaban ta,jijiyar kan shi har harbawa take tsabar kishi, yaushe ya fara jin wannan zazzafan kishin akan ta ne? Ko dan da ba shi da abokin takara, yanzu kuwa ya samu, wanda a qiftawar ido zai iya juyawa da Aaseeyah tunani, tun da ya sani ba wai wata hamshaqiyar soyayya take masa ba, ya dai riga ya dasa mata cewar shi din shi zai aure ta kar ta kula kowa, kuma a wautar ta ta yarda da hakan,dole ya qara mata da soyayyar shi, amma zai iya sanya budurwa kamar Aaseeyah fad'awa tarkon so kuwa? Bari ya jaraba ya gani. Hijabin ta ya riqe a hankali, cikin sanyin murya ya ce, "Dubi wai a haka kin rufe jikin ki kenan, amma kowanne lungu da saqo na jikin ki, gashi nan a bayyane ana gani, kalli nan, dubi can" Ya na magana ya na kai hannun shi hips din ta da qirjin ta, cikin salon da ya sanya Aaseeyah taune lips din ta na qasa, janye hannun shi ta yi daga saman qirjin ta,sannan ta ce, "Yah Noor ni haka Allah ya yi ni, ai ka ce na saka hijabi, kuma na saka, tunda ka ga jiki na bai boye a ciki ba to haka Allah ya yi ni" Murguda baki tai a hankali, karaf a idon shi, "Ban hana ki murguda min baki ba? Baki da kunya ko?" Hannu ya sa ya riqe mata leben ta na qasa ya dan ja, lumshe ido ta yi, ta bude a saman nashi,kafin ta kwace ta ja baya, "Gaskiya ni Yah Noor ka daina,zan fada wa Mammee ka na cin zali na" Da sauri ya zaro ido, 'Wannan yarinya an yi sokuwa, sam bata da sirri kamar Umaimah.' "Me zaki ce na miki?" "Abinda ka min yanzu mana, ka dora hannun ka anan da can da nan, ka jaa min baki na" "Wa ya ce miki in miji ya wa mata abu ta na zuwa ta fad'a a gida?" "Ana fad'a mana, akwai 'yar ajin mu a islamiyya, da mijin yayarta ke cin zalin ta, ai kuwa ta fad'a a gida, baban su da yayun ta suka je suka masa shegen duka shima," Dariya sosai Noor yake yanda ta ke bashi labarin da nunawa kamar da ita aka je akai dukan, ita ma dariyar ta dinga yi, har suka zauna, ta na fuskantar shi a kujera, ita kuma ta na saman table din dake gaban kujerar. "Yah Noor in tambaye ka dan Allah" "Ina jin ki," "Kafin mu yi aure, za ka barni na koyi girki? Ka ga ban gama kwarewa ba, Mammee ta ce maza sun fi son mace kwararriya wajen girki," "Ke kuma ki na so in so ki shi ya sa kk son koyon girki ko?" Cikin jin kunya ta d'aga kai, Murya can qasa ya kama hannun ta ya na shafawa sannan ya ce, "Aaseeyah zuciya ta ta sauya akalar soyayyar ki, daga wani bigire da ni na barwa kai na sani, ta koma sabon bigiren da ban san sanda hakan ta faru ba,ba na jin zan iya auren wata mace mu zauna lafiya bayan ke, ba zan taba son kowa ba in ba ke ba, ina fatan kema za ki min so irin wanda nake miki, amma fa ba na son ki fad'a ma kowa ni zaki aura, kin san akwai 'yan sa ido, masu mugun baki, sai su sa mana baki abun ya lalace" Lumshe idon ta kawai take, ta na sauraren shi, a zaton shi hannun ta da ya riqe ne, nan kuwa bacci take ji, nan da nan ta kuwa sake hamma mai tsaho, sannan ta ce, "Yah Noor ni ma ina son ka zama miji na, ba kuma zan fad'awa kowa ba, zan jira har mu kammala makaranta kafin na fara koyon girki sosai, ina so na burge ka ka qara so na, bari na je na dan kwanta, na tsani bacci a aji, Malam Salisu Tumbi in ya kama mutum ya na bacci a aji, bulalar shi me shegen wari ya ke turawa mutum a baki" Dariya sukai, nan fa bacci ya gudu, ta dinga bashi labarin Malam Salisu tumbi, irin azabar da take gana masa, da wadda yake ramawa, Noor ya yi dariya har ya ji ba dad'i. Bata bar d'akin Noor ba sai ana kiran azahar. Mahboob kuwa hira kawai yake, amma hankalin shi na qofa, ya na jiran ya ji shigowar ta, ya mata magana ta whatsapp ya ji ta shiru ba ta hau ba, Umaimah ce ma ke dauke hankalin shi da labaran ta,in ya kalle ta mahaifiyar su take tuna masa, ba abinda ta bari na mahaifiyar su, sai dai fuskar ta da ke cike da yarinta. Murmushi ya yi, ya sa hannu ya kama kumatun ta ya girgiza, ita kuma ta sa dariya kamar wata mitsitsiyar yarinya, ta na jin dad'in kulawar da yayan ta ke bata. Aaseeyah kuwa na zuwa ta ga Mammee har ta gama abincin rana, gaskiya aikin ya fara mata yawa ita kadai, "Mammee aiki na maki yawa gaskiya,kin qi yarda a kawo mai aiki gidannan," "Mu na da manyan 'yan mata kamar ku a gidannan, me masu aiki za su mana? Me ye amfanin ku? Ku ci ku sha ku yi makaranta,ku dawo ku yi bacci ko kallo ko? Lala ba haka ake rayuwa ba, rayuwa tsara ta ake ta yanda zaka morar kuma a san an more ka din, ba wai ka zauna lalaci ba, sa'o'in ka na can ana morar su kai ka na nan kana aikin banza, yanzu daga ina kike, ba irin kiran da ban maki ba, har wajen Mahboob na je amma ban gan ki ba, gidan uban wa ki ka tafi?" "Mammee dan Allah ki hakuri, Yah Noor ne ya kira ni, dazu duka na ya yi dan na saka qaramin mayafi, shi ne yanzu wai wannan hijabin ma bai masa ba, daga baya kuma muka tsaya hira" "Da gaskiyar shi ai, shi ya sa duk yaran gidannan inna cirsle son kai na, Noor ya fi su hankali da nutsuwa, ga riqo da addini, wadanan shashashun yayun na ki, ba abinda suka sa a gaba sai a dau wankan sukari a xaga gari da abokai, jin waqe waqen banza da kallon shirme, in ka hana su su taso maka kamar za su cinye ka" (Da bakin ta take fadin komai bamu matse ta ba, amma ba za su iya daukan mataki akam tarbiyyar yaran su ba) "Mammee ni dai fad'a min me zan taya ki? Da ga yau na janye magana ta, zan fara koyon girki da kyau tun yanzu, ni fa Mammee in ba dan ki na cewa ban iya ba, ban ga abinda ban iya ba din,komai zan iya dafawa, to meye wahala a girkin ne?" "Ki bari daga dare za mu fara darasin koyon girki da ke da kyau, za ki ga banbancin dafa shinkafar ki da tawa" "To Allah ya kai mu" "Ameen" "Maza dauki Na Mahboob ki kai, in kin dawo ki debi naki, sauran ki min dibar yaran nan da kk ki bata komai" "Ba zan bata ba Mammee" "Ki ma bata sai ran ki ya baci kema" Daki ta shiga, ta yi alwala ta yi sallah, sannan ta dubi kan ta a madubi, gani ta yi ba abinda fuskar ta tayi, amma ta na son ta dan gyara ta, ko me ye dalilin hakan oho,abun taje gira ta dauka, ta taje girar ta, sannan ta shafa man lebe, ta yafa mayafi mai dan girma sannan ta fesa turare ta fita. Abincin ta dauka, ta nufi bangaren Mahboob, zaune yake a saman sallaya shi kadai, ta ajiye a gefen shi,kallon ta ya yi,tare da shaqar sassanyan qamshin ta, mara qarfi, amma mai sanya zuciya nutsuwa. "Ga abincin ka Yah Mahboob, in zuba maka? Daga mata kai ya yi, tare da jingina kan a jikin kujera, ya na bin duk wani motsin ta da kallo,ya na sakin tattausan murmushi, tunani ne mai girma a zuciyar shi,dama ta zama mallakin shi. Har ta aje abincin da abun sha a gaban shi bai sani ba, ya na ta tunani a ran shi,kuma idanun shi kafe akan ta,sai ta ji kallon ya mata yawa, domin jin shi take ya na bula dik wata kafa ta gashin jikin ta ya na wucewa tsokar jiki da jinin ta, saukar da idanun ta qasa ta yi, sanan ta ce, "Ga abincin" Yanda jikin ta ke reacting a gaban shi, ya sha banban da yanda yake reacting gaban kowa, ba tare da sanin ta ba jikin ta kan narke ya koma mai sanyi, ta na narkewa tare da bin duk wani salon da a da bata san ta na da shi ba. "Ta'el wa kulun ma'iin" "Na'am? Ka na nufin mu ci tare?" "Eh, ko ba zaki ci da ni ba?" Shiru ta dan yi, ta na nazari, spoon ya kai bakin ta, na shinkafa jelop da ta sha kayan lambu da naman rago,wanda bai sani ba zai dauka soyayyar shinkafa ce saboda wara wara da ta yi ta yi kyau, nan kuwa jelop ce,qamshin ta ma ba zai bar ka juyar da kai ba, dan haka Aaseeyah bude baki ta yi ta amsa, ta fara taunawa, kallon qaramin bakin ta mai dan tudun labba yake yanda ta ke taunawa,gwanin sha'awa, murmushi ya yi, ya kauda duk wani tunani, shi ma ya ci, lumshe ido ya yi, tabbas Mammeen Aaseeyah ba na biyun ta a iya girki. Amsar cokalin ta yi a daidai sanda zai sake bata, ta ci da kan ta,in ta ci sai ta bashi, tun Aaseeyah na jin kunya, ba sai gashi ta baje ba ta fara halin, hira kamar an kunna fanfo, labari take bashi wanda ba ya gane wata hausar in ta yanko masa, saboda sabuwa ce a wajen shi. Ya yi dariya kuwa har ya na hawaye,saboda jin shaqiyanci irin na Aaseeyah, nan ya tuna sanda ta sa masa bera shi ma, duba time ta yi a

Chapter 11 of 41