bace, su ji tsoron Allah da sauran wa’azi irin na masana Allah, ga shi lokaci d’aya Aaseeyah ta tona shi gaban qannen shi.
Hussein kuwa ba shi da niyyar nuna wa Noor ya san komai, dan kuwa shi ma ba ya son a daga nashi maganar.
Haka suka ci gaba da rayuwar su a boye, har sai da ta kai Hussein zai dau Ummu suleim su je wani dakin na abokin shi, abun nasu dai bai wuce wasanni, har a fidda sha’awa, kullum a haka suke, Umaimah da Noor kuwa, ya riga da ya gama lalata ta tun ta na qaramar ta, a haka ya ke ci gaba da lalata ta a boye, ya sake sabon taku ta yanda ko Umaimahn ba a cika ganin su tare ba a cikin gida, da kan ta take fita ta bishi har d’akin shi cikin dare, in sun gama abinda za su yi ta koma nasu d’akin, ba tare da kowa ya sani ba.
A daidai lokacin da kowanne bawa na gari mai neman rahamar Allah yake tashi dan yin sallar dare, su kuma a wannan lokacin suke aikata sabon su.
Mahaifan su maza basu da wani katabus a harkar tarbiyyar yaran su, domin kuwa in suka fita tun safe sai dare, sai weekends ne suke a gida, shi ma sun fi bada hankali wajen tasu hutawar da matan su, matan kuwa a ganin su su na matuqar qoqari wajen tarbiyyar yaran su, dan haka kowa gani yake d’an shi kamili ne.
Kamar abun wasa Aemana ta daina zuwa aiki, tun abun baya damun Mahboob har ya tambayi wani co-worker din su ko ya san me ya hana Aemana zuwa? Mamaki ne ma ya sa wancan din kallon shi.
“Yanzu kai da za a tambaya Aemana kai ke tambaya ta ita?”
“Basshi kawai”
Shi ne abinda Mahboob ya ce ya koma bakin aikin shi, ya yi qoqarin share ta, tunda ai shi ya ce ba ya son ganin ta again, amma ya kasa, yanzu kusan wata hudu da rabuwar su, ko duriyar ta bai sake ji ba, a hankali ya fara neman adireshin ta a boye har watarana ya yi dace ya samu ya adana.
Wata ranar juma’a sun taso daga masallaci, kawai dai ya nufi gidan su Aemana, ya jima ya na danna qararrawa kafin khadeematul manzil din ta bude mishi qofa, cikin harshen laranci Mahboob ya tambaye ta ko Aemana na nan, saurin kallon inda ta ji taku ta yi, ta matsa mishi, tare da alamar ya shiga.
Ko da ya shiga abinda ya gani ya firgita shi,da sauri ya isa gare ta ya tare ta,anya Aemana ce kuwa? Ko dai ta na da wata ‘yar uwar ne?
“Madha hadath laki ya Aemana?”
(Me ya same ki Aemana)
Dariya ta mishi irin ta ‘yan kwaya, sannan ta kwantar da jikin ta a nashi, daga baya ta yi sauri ta ture shi ta fara kuka mara sauti, a hankali muryar ta ke fita, ta fara ihu ta na korar shi ya tafi ya bar masu gida.
Tashin hankalin da Mahboob ya shiga ba kadan bane, mahaifiyar ta ce ta fito cikin shigar mutunci, doguwar riga baqa da rolling din mayafi kalar ja, kyakkyawar mace yanda ka san Aemana qanwar ta ce ba diyar ta ba, rungume Aemana ta yi ta na lallashin ta, inda Aemana take kalla ta na magana itama matar ta kalla, ganin Mahboob ya sanya zuciyar ta a qunci, wanda har ta kasa boyewa, kalaman ta sun sake jefa Mahboob cikin tashin hankali da dimuwa.
“Sawf yamta’ik Allah”
(Allah ya hukunta ka)
Hawaye ne suka zubar mishi, tabbas shi ne sanadin komawar Aemana haka, hakuri ya dinga bama mahaifiyar ta, ta na sake zuba masa kalaman da suke jaddada masa sun bar shi da Allah akan abinda ya yi ma ‘yar su, alqawarin auren Aemana ya yi masu amma firrr suka qi, da suka ga ba shi da niyyar fita musu a gida sai ta fara qoqarin kiran ‘yan sanda, domin ba su buqatar mutumin da soyayyar shi zata gusar ma da diyar su hankali ta fara sabon Allah ta hanyar shaye-shaye, sun samu wai a haka ta fara ragewa kenan, gashi ya zo zai sake sanya mata damuwa.
Mahboob na kuka shabe shabe ya shiga motar shi ya koma gida, sun tabbatar mishi in ya koma za su had’a shi da hukuma ne kawai.
Hankalin shi ya yi gida Nija, ya na ganin kiran su Umaimah bai daga ba, tashin hankalin da ya shiga ba kadan bane, gajiya suka yi da kiran shi dikan su suka hakura, domin duk su na tare, su na son su gaishe shi, suna kewar shi sosai, duk sanin waya suka mishi, duk cikin su ba wacce ta san shi sosai da sosai.
Bayan watanni biyar Aemana ta sauya wajen aiki, ta ci gaba da rayuwar ta kamar da, sai dai ba walwala, ba bu annuri a cikin rayuwar ta, ta zama shiru-shiru, ta koma rufe jikin ta, domin kuwa har da niqabi take sanyawa, maza da dama sun nemi auren ta taqi, ta na gudun ranar da za tai aure mijin ta ya gane ta taba lalata a baya, iyayen ta sun yi iya qoqarin su taqi amincewa da aure, har gargadi ta musu in suka matsa mata za ta gudu, dole suka kyale ta,suke sanya ta a addu’a,domin da addu’ar dama Allah ya shirya masu ita, sun yi imani da Allah da addu’ar za ta amince ta yi aure wata rana.
Mahboob kuwa ya koma garin Ar-ramtha,ya siyar da gonar qanwar mahaifin shi da ta riqe shi, da gidan ta, da duk wata kadara ta ta, ya hade kan kudin tass ya yi ma maqota, da sauran ‘yan uwan mahaifin shi sallama akan zai koma Nigeria da zama, nan suka dinga bashi saqonnin gaisuwa wajen iyayen nashi, da abubuwan alkhairi,da dare kuwa aka hada masa liyafa ta ban girma na abinci irin nasu na larabawa, irin su Mansaf,Falafel,Maqluba, sai shayin su masu dad’I da kala kalan qamshi, ga kuma madara mai kyau,Mahboob ya yi farin ciki sosai, sannan ya na jin kewar rabuwa da su, da su ya saba,kuma su ma sun saba da shi sosai, cikin kewa suka rabu wajen qarfe biyu na dare.
Da safe ya koma cikin garin Irbed,ya ci gaba da shirin shi na dawo wa Nija, hankalin shi, rushin shi, da gangar jikin shi, sun tattaro sun yo Nigeria.
Mutan Nigeria kuwa na ta shirin zuwan shalele Mahboob,su Umaimah kuwa har da sabbin dinkuna suka sha, dan tarbar gwarzon yayan nasu Mahboob………….
Da wa da wa za a tarbon Mahboobbbbbb?????? Ni dai zan tsaya a kitchen dan na san akwai harka a ta wajen aradu.
TAUBASHI
PAGE 14
Ya kammala tura duk wani kayan shi da ya ke da buqatar turawa zuwa gida Nigeria, Mahboob na cikin tsananin murnar komawar shi qasar shi ta haihuwa,tsaraba kuwa ya yi ta har ya na tunanin an ya bai yi almubazzaranci ba? Duba da cewa bai ma gama tabbatar da girman qannen na shi ba, dan ba a yarda da hoto,tayu sun fi yanda yake zata girma, sannan ta yu ba su kai yanda yake zata ba, haka dai ya gama tsarabar shi, ya yi sallama da dukkan wanda ya kamata, tare da sallama da wajen aikin shi, a daren da zai bar qasar ne suka mishi tasu liyafar, sun ci sun sha a wani wajen cin abinci mai suna Yasin Alfawal.
A gajiye ya koma gida, bai samu rintsawa ba sai da ya had'a komai a qaramin akwatin da zai dauka, sai jakar shi mai dauke da laptop din shi da wasu mahimman takardun shi,ganin komai ya kammala ne ya sanya shi fad'awa bayi domin yin wanka, ruwa mai zafi ya sakarwa kan shi dan huce gajiyar da ya ke tattare da ita, ya ji dad'in wankan sosai, ya fito daure da towel a qugun shi,ya na shafa gashin kan shi da ya gyara, inda ya ajiye kayan baccin shi ya nufa ya dauka ya sanya rigar, ya zame towel ya na qoqarin sanya wandon shi ya ga kamar gilmawar mutum ta wajen qofar dakin,da sauri ya kammala sawa ya bi hanyar fita, tare da tambayar waye? Ko da ya fita sai ya ga qofar parlour a bude, alamar tabbas an shigo, da gudu gudu ya fita dan ganin wanda ya shiga masa gida duk da cewar ya kulle gidan, bai ga kowa ba, dole ya hakura ya koma, mai gadin wajen ma ya ce bai ga shigar kowa ba,lallai ko waye ya shiga ya san kan wajen sosai, tunani ya ke waye ya san wajen, abokan aikin shi ma ba zuwa suke ba.
"Aemanah"
Shi ne sunan da ya fita daga bakin shi, duba gidan ya fara da kyau, dan bai yarda da ita ba, kar ta je ta masa wani mummunan abun, ganin bai ga komai ba ne ya sanya shi rufe gidan har da sakata, ya koma daki dan hutawa, qarfe biyu na dare ta yi lokacin, alarm ya sanya kafin ya kwanta.
Aemana kuwa ita ta karbi hayar wajen da Mahboob ya siyar a hannun wani balarabe, ta qudirta bayan tafiyar Mahboob za ta dinga zuwa ta shiga, dan debe kewar Mahboob din.
Da misalin biyar na safiyar ranar ya farka ya sake wanka ya wanke bakin shi, ya yi sallah, shiri ya yi mai daukan hankalin mai kallo, da farar jallabiyya mai matuqar kyau, fara tass, da dan mayafin nan da larabawa ke sanyawa, masha Allah, Mahboob ba dan ya na da sirki da mutanen Nigeria ba, ba mai cewa ba baralabe zalla bane, wanda ya san asalin shi ne kawai zai san ruwa biyu ne shi (kar ku ce fa an zuzuta kyaun mijin novel mai kyau duk inda yake dole a hwadi ah toh) baqin takalmi da baqin eye glass sai baqin agogo masu kyau da tsada ne sanye a jikin shi.
Sai qamshi yake zabgawa, kallon dakin ya juya ya na yi, cike da tunano abubuwa da dama da suka faru a cikin dakin,hamdala ya yi wa Allah da ya bashi ikon barin wannan gida lafiya, tare da addu'ar Allah ya bashi ikon isa Nigeria lafiya.
Ya na rufe qofar shi wayar shi ta dau qara, cike da murna suke hada baki wajen gaishe shi, da alama su na a tare ne baki dayan su, amsa wa ya yi cikin farin ciki da dokin son ganin qannen na shi, lallai zai zama mafi farin ciki a wannan ranar, Huseein ne ke tambayar shi ya fito ne? Nan ya ke basu amsa da cewar yanzu ya ke fita, zai tafi Amman daga nan sai Nija, fatan isa lafiya suka mishi, Noor ya yi gyaran murya sannan ya ce,
"Ka na isowa za ka tadda ni ina jiran ka a Airport, ka dai gane hoto na ko?"
Murmushi ya yi mai sauti,sannan ya ce,
"Habaa Noor, in ban gane kowa ba ai ba zan kasa gane ka ba,ko ka manta komai ne inna zo na maka tuni?"
Taxi ya tsayar ya shiga ya na waya da su, daga baya suka yi sallama, daga Irbed City ya wuce Amman City,bayan kammala duk wani abu da ya kamata a filin jirgin, ya zauna jira har aka kira pasinjojin da za su taso daga Amman din qasar Jordan zuwa Nigeria.
Tafiyar awanni Biyar da minti arba'in da bakwai 5hrs 47mnts ne ya kawo su Nigeria, sakkowa ya ke ta matattakalar jirgin ya na wara idanun shi akan mutane da komai ma da ke gaban shi, ba ya son missing din kallon komai, fuskar shi dauke da wani irin yanayin da na kasa ban-bance shi tsakanin farin ciki, da baqin ciki,tafe ya ke ya na jan akwatin shi, ya na rarraba idanu ta inda zai ga d'an uwan na shi, ta gaban Noor ya gifta, Noor na ta kallon shi, daga baya ya dauke kai, ya ci gaba da leqen inda zai ga Mahboob din, 'Yan biyu na tsaye gefe da gefen shi, su na kallon shi, tare da kallon mutanen da ke wajen, Mahboob na tsaye a bayan su ya na murmushi,
"Da alama fa mutanen da suka sauka yanzu sun gama fitowa, amma ba Yah Mahboob a cikin su,kuma ka ce za ka gane shi, ga dai shi har yanzu ba ka nuna kowa a matsayin shi ba"
Dan hade gira Noor ya yi,
"Ka na nufin qarya na ke yi Hussein? Dama na san sai ka qarya ta ni, ka gama ganin kowa na cikin Airport din ne? Ta ya ka san kowa ya gama fita, in za ka qara hakuri ka qara, in ba za ka qara ba ka tafi gida, dama ku kuka matsa sai kun zo, ban niyyar zuwa da kowa ba"
"Look, calm down, ni fa ba da wani manufa na fada ba, mu dan sake ko 10mnts ne haka,"
Ta baya ya dafa kafadun su, cikin gurbatacciyar hausar shi ya ce,
"Ba zan iya qara minti goma a nan ba, ba tare da na je gida ba,"
Da sauri suka juya tare da rungume junan su, nan fa Noor ya fara bayani, shi dai ya ga wucewar shi, ya ga kamar shi, kamar kuma ba shi ba,
"Amma kai ma ba ka gane ni ba shi ya sa ka wuce"
"Lala ni na wuce ne dan kawai na ga ni a fuskar ka ba ka gane ni ba, har na so maka magana, kawai sai na kalli gaba, na wuce ku"
"Ohhh Yah Noor ke nan mai gane mutane"
Kallon Hassan ya yi da gefen ido, cikin had'e gira, nan suka kama hanya zuwa wajen da suka aje mota, sai gida.
Su Umaimah ana can an sha ado da dogayen riguna baqaqe da mayafai kala kala, kowa da kalar mayafin ta, wanda ya dace da adon jikin rigunan su, Aaseeyah ce kawai bata cab'a kwalliya irin ta su ba, smokey eyes ta yi sai man lebe mai haske da ta shafa, qamshi ne mai sanyi ke tashi a jikin ta, komai na ta baya baya take yin shi, duk wani murna da suka dinga yi, 'Yan biyu na ce masu ga su nan a hanya bugun zuciyar ta ya sauya, hannayen ta na ta zufa, kowa ya kula da sauyin da Aaseeyah ta samu na rashin walwala kamar da, sun tambaye ta dalili, ta ce ba komai.
Bangaren da ya jima a kulle suka bude, suka shigar da kayan abinci, da abin sha, sun gyara shi kamar bai yi shekaru a rufe ba,sai tashin qamshin turaren wuta yake,
"Aaseeyah ina suprise din da kk ce za ki ma Yah Mahboob komai ya zama ready ko?"
Sai a sannan ta dan murmusa tunawa da abinda ta qulla masa da tai, cikin gyada kai da rufe bakin ta ta ce,
"Na aje komai yanda ya dace,"
"Muje ki nuna mana me kk aje masa dan Allah"
"Kin ga bar had'a ni da Allah ki cucen, ina ruwan ku da me na aje masa? Wannan abun tsakanin mu ne, dan ba ku san sanda ya ce min duk duniya ya fi son abun ba, balle na nuna maku, ku bari in ya iso ya shiga daki ya gani,sai kuma ku gani,ni kai na ma sara min yake, zuciya ta na tsinkewa ku barni na je na dan kwanta na huta kan su iso"
Fita ta yi zuwa bangaren su, ta samu waje a parlour ta kwanta, wani indi'an film ake mai su na Dil, ta na kwance ta na kallo, fad'uwar gaban ta na qaruwa, dafe qirjin ta ta yi, tare da kiran sunayen Allah, bata tsaya ba sai da ta dire a guda casa'in da tara, sannan ta daga hannayen ta dika biyu zuwa sama, ta hau addu'a,
"Ya Allah ka kawon sauqin wannan sabon yanayi da na ke ji a zuciya ta da jiki na, ban san me ne ba amma ka sani ya Allah, Allah ka sa ya zama alkhairi, ya Allah dukkan sharrin da ke tinkaro ni ka kauda shi daga gare ni"
"Ameen, me ki ke ji a zuciyar ta ki haka, da ya sanya ki addu'a?"
Kallon Mammee ta yi sannan ta miqe ta kwantar da kan ta a qirjin ta, tare da rungume ta da hannayen ta dika biyun, hannu daya Mammee ta sanya a bayan Aaseeyah tare da shafa bayan na ta,ita kuwa a hankali take sauke ajiyar zuciya mai sanyi, nan da nan nutsuwa ta fara shigar ta, ba ta bar kiran sunan Allah ba har sai da taji kwanciyar hankali ya samu matsugunni a zuciyar ta.
"Ba ki ban labarin damuwar ki ba Aaseeyah"
"Mammee b..."
Horn din motar Noor ne ya katse mata abinda ta yi niyyar furtawa, da sauri ta saki Mammeen ta ta yi hanyar waje,Mammeen ma ba zama ta yi ba bin bayan ta tayi, Ummee da su Umaimah duk sun fita, Abee da Abbu, ma ba a barsu a baya ba, domin yau ba su je aiki ba saboda tarbar Mahboob.
Zuciyar shi ce ya ji ta matse a qirjin shi, sakamakon tunawa da abubuwan da suka faru a baya, idanun shi sun kad'a daga launin fari zuwa ja, hawaye ba su da niyyar zuba a idanun shi, amma kukan da zuciyar shi ke yi ba kadan bane.
Ganin haka ne ya sanya iyayen na shi maza rungumar shi, tare da fad'in,
"Barka da zuwa d'an d'an uwan mu,marhabun marhabun,"
Cikin yaqe Mahboob shi ma ya maida masu da martanin murnar da suke na komawar shi, nan fa ya ga kyawawan qannen nashi sun isa gaban shi su na mishi barka da zuwa, a hankali Aaseeyah ma ta isa gaban shi, kan ta a qasa, ta rasa dalilin da ya sa zuciyar ta bugawa da qarfi sanda ta dora idon ta da farko a kan shi,ga shi yanzu ta kasa kallon shi.
Qura masu ido ya yi, ya na murmushin dole, ya nuna Yesmeen ya ce,
"Ummu Suleim ko?"
Ya nuna Ummu Suleim ya ce,
"Yesmeen ko?
"Ummm Aaseeyah ko?
"Ke kuma Umaimah ko?"
Dariya suka dinga yi masa saboda yanda ya juya sunayen su,ya tabbatar masu da cewa bai gane su ba.
Ganin dariyar da suke ne ya sanya shi farin ciki, Aaseeyah na murmushi ta kalle shi, da zummar masa bayani idanun su ya hadu cikin na juna, kallon seconds a qalla goma suka wa juna, Noor ya tsaya a tsakanin su,ya ce,
"To to sarakan surutu ku bashi waje ya shiga ciki ya huta, a hankali zai gane kowa"
Hannu Mahboob ya sa ya janye Noor da ya masa katanga da Aaseeyah,wadda ta ji kamar qafafun ta rawa suke, amma a zahiri tsaye take kyam.
Da hannu ya ke nuna kowaccen su ya na fadin sunan ta na asali, sannan ya dire akan Aaseeyah,murya can qasa, ba tare da ya yi niyyar hakan ba ya furta sunan ta cikin salo,
"Aaseeeyahh"
Da hanzari ta d'aga kai ta kalle shi, kunya kuma ta kama ta, ta rufe idanun ta, ta ja baya,
"To yallabai, in ka gama da qannen naka, ka shiga ka huta, dan wadannan ba su gajiya da shiririta su"
Kallon Ummee ya yi, ya murmusa, sannan ya gaishe su, ita da Mammee, amsawa sukai, tare da yi masa barka da dawowa, cike da murna, wanda hakan ya sake jefa shi tunanin baya.
Ko da ya shiga bangaren nasu b wanda ya bishi sai Noor da ya aje masa jakar shi,ya mishi sallama ya fita, ya ce nan da awa uku za su dawo, ya huta ya ci abinci, in ya gama komai za su shiga a yi hira.
Godiya ya mishi sannan ya samu kujera ya zauna, ido ya qura ma daidai qofar wani d'aki, hoton wani qaramin yaro da ba zai wuce shekara bakwai ba ya hango, ya na gudu,wata mata mai matsakaicin tsaho da jiki, tare da kyaun sura ta fito daga dakin ta na dariya, yaron ma dariya yake ya na gewaye kujerun, Mahboob murmushi yake ya na juya kan shi, tare da bin kujerun da kallo kamar a lokacin matar ke bin yaron da gudu, bai san hawaye na zubar mishi ba sai da ya ji gishirin su a bakin shi, da sauri ya share hawayen shi, ya miqe dan shiga cikin d'akin, ya watsa ruwa ya zo ya ci abinci, dan kuwa Tea kawai ya sha a jirgi, yunwa na damin shi sosai.
Bakin qofar shiga suka tsaya, sun lallabe a jikin gini kamar qadangaru, Aaseeyah ce a gaba, ta na ganin shigar shi dakin ta fara qirge da hannayen ta da bakin ta,
"1...2...3....4........."
Ihu suka ji daga cikin dakin da Mahboob ya ke, sannan suka ga ya fito da gudu, Aaseeyah da su Umaimah ma gudun suka diba, ya na fita suka ci karo da Aaseeyah, ta na qoqarin faduwa ya taro ta, kallon idanun ta ya tsaya yi, ita kuwa a zaton ta ko ya gane ita ta dana masa tarko, cikin in ina ta ce,
"Babbba...ni baaa ce ....Umaimah ce"
Sai da ta fad'i hakan ya tuna me ya gani a d'akin, da sauri ya sake ta ya ce,
"Umaimah ce? Ina Umaimahn?"
Ai ta na jin haka ta ruga a guje ta ce da qarfi,
"Ka je neman ta mana, ni ina na san inda ta tafi, tunda ta sa maka mugun abu ta gudu"
Umaimah kuwa ba ta san me Aaseeyah ta yi ba,kuma ta ji an ce ita ta yi, da gudu ta fada dakin su ta shige bayi, ta na ayyana irin walaqancin da za ta wa Aaseeyah, in ba iskanci ba daga zuwan mutum yau yau, ta fara masa mugun wasan ta, to wai me ma ta mishi ne ya sanya qaton namiji kamar shi ihu da gudu?.............
Yo ni ina nissani.
TAUBASHI
PAGE 15
Ya na kallon cikin idanun ta da ke kama masa da launin zuma mai duhu, ya ce,
"Kin tabbatar Umaimah ce ta saka min Aljaradh a d'aki na?"
"To ni ya ma zan iya taba bera da hannu na? Na fada maka ni ma tsoron shi nake ji,ka ma tambayi Mammee na in baka yarda ba"
A hankali ya saki hannayen ta ya tsaya a bakin qofa, ya na tunanin komawa ciki, gashi Aaseeyah ta qi barin wajen, kuma ba ya son ta ga ragontakar shi, juyawa ya yi ya dan ya aike ta kira masa Noor, sai ga Noor din ya fito ya na waya, da alama fita zai yi,da hanzari Mahboob ya kira Noor, nan da nan kuwa ya isa gaban shi, tare da katse wayar da yake, ya na tambayar lafiya?
"Akwai aljaradh a d'aki na, ko za ka cire shi?"
"Ok muje,"
Bin bayan shi ya yi, ya haye kujera ya zauna tare da nad'e qafar shi, Aaseeyah kuwa me zatai banda dariya, jin dariyar ta ne ya bada ita, a yanzu kam ya tabbata ba Umaimah bace, domin bai taba hira da Umaimah akan bera ba, ita din dai ita ta san kusan komai na shi, dan su na yawan chatting, sun san abubuwa da dama game da junan su, murmushi ya yi, ya na ayyana me zai mata domin ramako,beran matacce ne ma har ya fara wari, godiya ya yi wa Noor sannan ya shiga domin yin wanka ya ci abinci ya yi sallah ya huta kuma.
Aaseeyah kuwa bangaren su Umaimah ta nufa ta na ta sheqa dariya,Umaimah ta gaji da zaman bayi ta fito dik ta had'a zufa, suna had'a ido da Aaseeyah ta sake sheqewa da dariyar zufar Umaimah, tare da nuna ta, ta na lakatar zufar,
"Amma dai kin san ba ki kyauta ba ko, me ye na min sharri ki ce ni na saka mishi, kin san da Yah Noor ne ko Yah Hussein wataqila su daken, daga zuwan shi za ki fara gwada masa hali ko"
"Habaa yayata kuma qawalliya rabin duwais, wasa ne fa, ai an cire masa beran ma, wai dan Allah abun bai baki mamaki, ace garjejen basamuden magidancin qato kamar Yah Mahboob ya na jin tsoron bera, bera fa a cikin duk halittun duniya"
"To ba gwanda shi ba akan ki, bera ai abun tsoro ne ko dan cutar lassa"
Habaa me Aaseeyah za tai in ba dariya ba, wannan dai kare Yah Mahboob ne, amma dai abin kunya ya qare akan namiji me tsoron bera.(Walid a kiyaye a daina tsoron bera)
Basu koma hira wajen Mahboob ba sai bayan la'asar liss, gari ya yi sanyi, iskar yamma na kad'awa, gaba dayan su har iyayen ana ta hira, su na ta yi ma Mahboob godiyar tsarabar da ya kawo masu, shi kuwa ya na nuna ba bu komai, daga baya ya dakko dukiyar Khala Lila ya danqa ta hannun Abbu, ya musu bayanin komai akan abubuwan da ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 41