zata, ita da kan ta kuma sai ta ji dad'in ruwan.
Ko da suka fito idanun Aaseeyah sun yi jawur sun kumbura,fatar ta ma ta yi ja, a bakin gado ta zauna, Ummee ta fiddo mata da kaya, atampa riga da zani, da kyar ta same su, ta dinga fad'a kuwa , kamar kayan ta aka dinke da skirt din.
Aaseeyah dai ba baki, dan kuwa da gaske bakin nata ya gasu, daidai da kwayar zarra bata yi tunanin ramako ba, (hummm ba a yabon dan kuturu, ba zan yarda ba sai an gama wankan jego ba ki wa Ummee komai ba)
Man habbatussauda,man zaitun,kadanya,da man za'afaran, aka hade mata,shi ta shafe jikin ta da shi, sannan Ummee ta ce,
"Kinga wannan man da na had'a na waccan gorar?"
"Eh na gani,"
"To shi sai jini ya dauke, kin zauna a ruwan nan na bagaruwa da kaninfari da gishiri, sai ki dinga dangwala a audiga, ki na matsawa a jikin ki, in ya dan yi kamar minti talatin, sai ki cire audigar ki yar, inshaa Allahu zaki ji dad'in jikin ki sosai"
"Ummee man meye da meye a ciki"
"Ban sani ba, wato gani muguwa ko? Man gelo ne to, na ce man gelo ne"
"Ummeena ba fa haka nake nufi ba, kawai dai ina son sanin man meye"
Yanayin yanda tai magana da qasqan da kai, ba halin ta bane, Ummee ta gamsu tambaya kawai take, dan haka sai ta dan bata rai kadan san ta ce,
"Tun da kin matsa se kin ji man meye, kafin ki aiki da shi, to man tafarnuwa ne, man zaitun, man habbatussauda sai turaren musk,ko da magana?"
"Babu"
"Da kyau"
Ta na gama shirya Aaseeyah ta fita, ko bi ta kan Umaimah batai ba ta amshi yaran, ta nufi dakin da su, miqawa Aaseeyah su ta yi, ta ce ta basu su sha,yau fa ake yin ta, ba bu wanda ya taba zaton Aaseeyah na da kunya har haka sai ranar.
An kad'a an raya ta basu mama,ta qi, qarshe ta saka kuka,yaran ma kukan suke, dan kuwa yunwa suke ji,da kyar Mahboob ya lallashe ta ta basu, bayan kowa ya fita, Yesmeen ce da za su fita ta ce,
"Aikin kawai, gobe a gaban idon mu za a sake su waje, ku muje"
Ummee kuwa ta ce,
"Yo in ba a basu a gaban mu ba ai an bayar agaban namiji,garjejen qato"
Ita dai Aaseeyah kan ta na qasa har suka fita.
Su na ta mata dariya kuwa suka fita, dan kuwa har su Ummee ta basu kunya,garjejen qato ai mijin ta ne, daga ita sai Mahboob, ya sha tsiya da masifa wajen Ummee, dan ta ce in ta sake ganin shi ana ma Aaseeyah wanka, shi ma sai ta masa wankan jegon, dariya wajen su Ummu Suleim da ita kan ta Ummeen ba a magana.
'Yan biyun Aaseeyah sun qara kawo farin ciki a cikin ahalin Abdul mudalleeb Jordan, kowa ka gani dauke yake da murmushi, da annashuwa,Mammee kuwa farin cikin ta ba ya misaltuwa, ji take kamar yaran ne jikokin ta na farko , roqon Allah ta fara tun a yanzu akan ya bata ikon yin adalci a tsakanin jikokin ta, kamar yanda ta yi a tsakanin yaran ta.
Zamani sauyawa yake, a duk sanda yaran ka ko jikokin ka suka kula ka fi karkata ga wani bangare,to fa hassada,kyashi,da ganin ido zai shige su, duk da cewar wannan ba sabon abu bane, in muka yi duba da qissar Annabi yusuf da 'yan uwan shi,amma wannan generation da muke ciki, illar hakan ta fara bayyana ainun,d'an uwa zai kashe d'an uwan shi, ko ya raunata shi,ko ya illata shi saboda an fifita d'an uwan shi akan shi, wanda da zai hakuri ya kula da ya fuskanci ko an fifita wancan da son rai ne kawai ba bisa cancanta ba, ko kuma an fifita wancan ne bisa cancanta ba bisa son rai ba,koma dai da mene ne, mu na sanyawa zuqatan mu hakuri, juriya, da kauda kai ga barin hassada, hassada ciwo ne babba da kafin ka farga in baka nemi waraka ba, ka rusa kan ka da kan ka.
*************************
Bayan kwana tara da suna, Aaseeyah da 'yan uwan ta ne zaune suna ta hira, mutanen da suka zo masu suna dik sun tafi,sai su ya su, sai debating suke akan sunan da za su sanya wa yaran ya zama inkiya,tunda an saka ma Hassana sunan Maman Mahboob, wato Zainab, sannan an sakawa Hussaina sunan Ummee, wato Fatima, wannan zabin Mammee ce da kan ta ta roqi azziqin, wanda a zuciyar Aaseeyah ta so a sanya sunan Mammee ne, amma Mammeen ta roqi a sawa Ummee takwara.
Hakan da ta yi kuwa ya qara mata qima, daraja, d mutunci a idon Ummee, Abee,Abbu, da yaran su dika, tare da sauran dangin su na kusa ma.
Hira suke ta yi, kowa na kawo sunan da ya ke ganin shi ya fi dacewa a yi ma yaran laqani da shi, ana cewa ah ah.
Noor ne ya miqe ya ce,
"A matsayi na na uban yaran nan, na sa musu inkiya da Asifa da Azma, Zainab ita ce Asifa,(wadda ake girmamawa) Fatima kumaa Azma, (kyautar Allah) "
"Masha Allah, Masha Allah, gaskiya suna yayi, Yah Noor ashe ka iya zaben suna haka"
Hararar Ummu Suleim ya yi da wasa, sannan ya ce,
"Me ki ka maida ni?"
Dariya sukai baki dayan su, can Aaseeyah ta ce,
"Ni fa ba dan kar a ce na ce ba, da sai na ce har yanzu ba na gane wace ce wacce, a tsakanin su, kamannin su ya yi yawa"
"Ke kenan ma da ki ka haife su, balle mu, ni kai na na kasa gane su"
"Amatullah ce kawai uwar bin diddigi take iya gane su"
"Ai Amatullah da ma ba harkar lauyanci take ba, da ma detective ta zama (Almuhaqaq)"
"Aikuwa dai"
Haka suka yi ta hira abun su gwanin sha'awa,Ummu Suleim na jin kamar kar ta koma gidan ta, ta ci gaba da zama da 'yan uwan ta.
****************************
Bayan arba'in Aaseeyah ta koma gidan ta, cike da gyara da kuma kayan da zata gyara da kan ta, daga taskar hajiya Ummee, wani irin mutunci da shaquwa ce a tsakanin su mai ban mamaki, dik da cewa Mammee ba irin iyayen nan ne masu tsananin kunyar da take hana su magana da yaran su ba, amma akwai wasu abubuwan da Aaseeyah kan ji nauyin maganar da Mammee dan haka wajen Ummee ta ke neman sani kan ta tsaye.
Ummee na son takwarar yayar ta sosai, dan yanda ta ke kula da ita daban ne, har kowa ya fuskanci hakan, ba dan ba ta son takwarar ta ba, sai dan son da take ma yayar ta da ta maida shi kan me sunan ta.
A washegarin ranar da Aaseeyah ta koma gidan ta, a ranar suka samu baquwar da ta bawa kowa mamaki..........
Assalamu alaikum my kyawawan makaranta,ina fatan labarin Aaseeyah ya na kai maku kooo ina na kunnuwa da zuqatan ku?
Ina mai tallata maku sabuwar Channel di na da ke YouTube,mai suna TASKAR HAMIBRAH, kindly subsribe to my new Channel dan samun wasu labarai masu ilimantarwa,fadakarwa da ma nishad'antarwa inshaa Allahu, a gwadan soyayya irin ta Ummee da Aaseeyah pls😂
https://youtube.com/channel/UC0NWMTHsARvoeI0CTnclFig
TAUBASHI
PGE 63
Kowa ya yi mamakin ganin baquwar banda Aaseeyah, dan yaron dake tare da ita ya fi daukan hankalin su Yesmeen, tsaye yake mannee da balarabiyar matar da ke ta zabga murmushi.
Hussein ne ya shigo dauke da akwatunan su,shi ma ya na murmushi, kaya ne lodi guda, dan kuwa akwatuna ne guda hudu,sai da ya gama ajiye su ya samu waje a kujera ya zauna, ya na huce gajiyar shi.
"Yah Hussein wa ce ce wannan?"
Yesmeen ta tambaya,
"Lallai ma Yesmeen, yanzu baki gane ta ba? Baki gane Aemana ba? Maman Mahmood little?"
Cike da fara'a Yesmeen ta zamo daga kujera, ta na kallon Aemana da Aaseeyah da ke rungume da juna kamar ba za su saki junan su ba, jin soyayyar junan su suke kamar ciki daya suka fito.
Mahmood Aaseeyah ta durqusa ta dauka da kyar, yaron ba dai nauyi ba.
Shi dai bai nuna alamar ya gane Aaseeyah ba, kuma bai qi yarda ta taba shi ba.
Yesmeen na tsaye ta na washe baki, ta ji Aemana ta kai mata runguma itama, nan fa Yesmeen ta sake, da sai d'ari-d'ari take.
Tasneem da ta shigo dauke da abincin da Hussein ya sa ta dafawa ce ta tsaya baki sake, nauyin abincin ne ya sa ta saurin qarasa kan dinning ta ajiye,
"Ina muka samu balarabiya haka?"
"Maman Mahmood ce,"
Ita ma dan rungumar juna sukai irin na larabawa, sannan suka bata waje ta zauna, nan fa harshe ya juye, Tasneem ba bihim sai ido.
Komawa ta yi debo sauran abincin,ta jera, ta shiga kitchen din Aaseeyah ta debo plates sabbi da serving spoons, da cups, da duk wani abu da za a buqata dai.
Su na nan su na hira Aaseeyah ta ja Aemana ciki dan ta dan watsa ruwa ta huta, sai yaba yanayin gidan ta ke, dik da ba wani hamshaqin gida bane, amma tsarin abun burgewa ne matuqa.
Sai da ta fara wanka, ta sauya kaya, ta shirya Mahmood, sannan suka shiga taga twins,ta musu addu'a,ta na ta yaba kyaun su.
Hussein ya tafi masallaci, su Yesmeen dake sallah suma suka je sukai sallah, basu dawo ba sai can yamma sun tabbatar da baqin nasu sun huta,sun ci abinci, sannan suka koma.
Aemana na ta jin dadin hira da su, sun yi vedio call da mahaifan ta, da mijin ta, wanda ya dinga yi ma Mahmood wasa, qarshe hawaye suka fara zuba masa dole ya kashe, Yaron ma kuka ya dinga yi, da kyar ta lallashe shi.
Sai qarfe biyar Mahboob ya dawo daga aiki, ya yi mamaki da kidima matuqa da ganin Aemana a gidan, Aaseeyah ce ta masa bayanin komai, cikin fara'a da kallon shi ko za ta ga murnar shi.
"Yah Mahboob ta waya muka tsara komai na zuwan ta, Yah Hussein ne ya dakko ta, ta zo ne da mahimmin abu,ina ganin ka ci abinci ka yi wanka, in ya so sai mu tattauna, ba zama zatai ba, jibi za ta koma"
"Mene? Wai me ki ke fada ne? Ni fa ban fahimci komi ba,me ne ne mahimmi? Bayan ita ta ce na bar mata shi? Ta zo ne dan ta tonan asiri a idon duniya ko me?"
Da hausa suke maganar, Aemana ta san fushin Mahboob sama da yanda Aaseeyah ta san shi, tunda a haka tai zama da shi,dan haka ta gane fada yake,sai ta ji zuciyar ta ta matse, da ta na da yanda za ta yi da ba zata dawo da yaron nan ba.
Nan da nan idanun ta suka kad'a suka yi jawur, jan hannun yaron da ya qura ma Mahboob ido, ya na son tuna inda ya san shi ta yi,suka shiga dakin da Aaseeyah ta sauke su.
"Ka gani ko? Meye amfanin haka yanzu? Ta fahimci fada kake, gaskiyar magana baka kyauta ba,ba ka da dalilin yin fada,"
"Saboda me ya sa ki ka ce banda dalilin yin fada?"
"Saboda baka tsaya ka ji dalilin zuwan ta ba, sannan abun nan ya riga ya faru,ba wanda ya isa sauya shi , Allah ma ya san me kuka aikata balle mutum? Shi ne fa kuka sabawa, kuma wajen shi kuke neman gafara, to meye dan mutum ya san halin da ka ke ciki?, kuma babban abin da ya batan rai yanzu Zaujee baka ji me ya kawo ta ba fa,"
Aaseeyah barin wajen ta yi cikin bacin rai, ta nufi dakin su ta dauki Azma da ke kuka,ta hau bata mama, Mahboob na tsaye a parlour, kan shi ya kulle, ya na son ya bawa kan shi laifi amma ya kasa, ga shi dai ya san ya na da laifin amma ya qi danganta kan shi da laifin.
"Me ya kawo ta?"
Gajiya ya yi da tunani ya kalli jakar shi da Aaseeyah ta bar masa abar shi a wajen, tunda akai auren su bai taba kai jakar shi d'aki da kan shi ba.
Jiki a sake ya shiga, sallama ya yi ta amsa da labban ta, dan kuwa ba sauti,ya na zama ta miqe tare da ajiye Azma, ta fita, abun ma dariya ha bashi, meye abun fushi.
Dakin da Aemana take, Aaseeyah ta shiga,zaune ta gan ta ta zuba tagumi, ta na kallon wayar ta, ta na ganin Aaseeyah ta shiga, ta miqe, ta na jera mata tambayoyi akan abubuwan da ta kula Mahboob ya yi da ya gan ta.
Aaseeyah nuna mata ta yi mamaki ya ke da ganin su, ta ce, inaa sai dai in bai ji dadin zuwan ta ba, Aaseeyah shiru ta yi, bata boye mata komai ba ta sanar da ita, ji ta yi jikin ta ya yi sanyi,to ya za ta yi da ran ta? A tunanin ta kawo shi nan shi ne zai sama masa 'yancin shi, amma kuma da alama ta yi kuskure.
Hawayen da ba ta zata ba taji Aaseeyah na share mata, fashewa ta yi da kuka sosai, ta sanar da Aaseeyah cewar, da ta sani ta bi shawarar mahaifan ta,da suka ce za su riqe mata Mahmood, amma ta qi.
Mahboob ne ya yi sallama, da sauri Aemana ta goge hawayen ta, ta dora mayafi a saman kan ta.
Sallama ya mata, ta amsa cikin sanyin murya, Mahmood ya miqawa hannu, ya isa gare shi, ya rungume yaron, ya yi kissing din shi, sannan ya dora shi a cinyar shi.
Hakuri ya bawa Aemana, har sai da ya tabbatar komai ya wuce, sannan ya bata izinin gabatar musu da dalilin zuwan ta.
Nan take, ta fara sanar da su,dalilin zuwan ta, cikin harshen larabci,
"Na dawo da Mahmood ne wajen ka, saboda ba na so ya zauna a wulaqance, da gorin ta yanda aka haife shi har qarshen rayuwar shi, mun saka shi a makaranta, tambayoyi da bincike ya sanya aka gano ko shi waye, makaranta ta gagare shi zuwa, kullum da kuka yake dawowa,ana haka miji na ya kawo yaran matar shi guda biyu, sun rabu ta tafi da yaran, mukai aure, kwatsam ta dawo da su, wai aure za ta yi,Mahmood na fuskantar tsangwama sosai a wajen yaran,suna masa gori akan mahaifin su, abun na qona zuciya ta, ganin ka auri mace mai kirki shi ya sa na yanke shawarar kawo shi nan, sannan na ga jarirai da kuka samu,mahaifa na sun so na basu shi,na yi nazarin ba inda zai samu gata sama da nan, shi ya sa muka shirya yanda zan taho,a zaton matar ka, za ka yi farin ciki da hakan, sai kuma muka ga sabanin hakan, ......kayi hakuri, za mu koma tare,zan maida shi hannun mahaifana"
"Ya salam, Aemana ki gafarta min akan abinda na maki,ban san abinda ke faruwa ba kenan, ba zaki koma da Mahmood ba,ya zo gida kenan, mu na qaunar shi, iyaye na da dika 'yan uwa na, mu na son shi,da fari na ji tsoro ne na ganin ku, amma ba yana nufin ba na son shi ba"
Yaro dai sai raba ido yake, tunda da hankalin shi, kuma da bakin shi, ya na ji, kuma ya na ganin me ke faruwa.
Murmushin kwanciyar hankali ne ya bayyana a fuskar Aemana,daga nan, suka hau hira, kusan rabi akan abinda Mahmood ke so ne, da wanda ba ya so, Aaseeyah ko daidai da kwayar zarra bata ji haushin bayanan Aemana ba, sai ma qayatarwa da abun ya mata,ta samu wasu tips din itama na kula da yaran ta, cikin qoshin lafiya.
Da daddare Mahboob ya dauki Aemana da Mahmood,da izinin Aaseeyah ya kai ta gidan su Ummee,su Ummee sun yi farin cikin ganin Mahmood ido da ido, ba hoto ba, sun kuma yi na'am da dawo da shi din,har Mammee da Ummee na rige-rigen fadin a bar shi a hannun su, tunda Aaseeyah na da danyen jego, kula da shi zai mata wahala.
Mahboob ba kunya ba tsoro ya ce,
"Tabb ai Ummee ku daina ma wannan maganar, Aaseeyah ba yarda za ta yi ba"
"To in bata yarda ba, ba se ta zo ta sa duka ba"
"Ummee ba haka..."
"Kai yi min shiru,ka duba ka ga yanda yaro ya lafe jikin subai'a,kamar sun jima a tare,wace matsala zai samu anan din? Ai ba wai dindindin zamu riqe maku shi ba masu d'a,kafin nan kafin yara su qara kwari ne ai, ga aikin office, aiki yawa zai mata"
"To Ummee dik yanda kuka ce"
Aemana dai na zaune, ta kalli Ummeee ta kalli Mahboob,sannan ta kalli nune nunen da suke da hannu da baki.
Bayan sun gama magana Mahboob ya wa Aemana bayanin me ya faru,murmushi kawai ta yi, ta nuna ai duk yanda suka yi daidai ne.
Ta ji matuqar jin dadin yanda iyayen Mahboob maza da mata suka nuna qauna a gare ta da yaron ta.
A daren suka koma har da Mahmood, Aaseeyah ta sake gyare gidan ya yi tsaf,sai qamshi ke tashi, ga sassauqan abinci Yesmeen da Tasneem sun dafa domin baqi.
Ko da suka dawo suka sanar da Aaseeyah me su Ummee suka ce, tsalle tai ta dire har da shagwaba sai da kyar Mahboob ya lallashe ta, ta sa shi yi mata alqawarin ba me amshe Mahmood a hannun ta, alqawari ya mata, cikin murna ta dauki yaron ta na kissing kuncin shi, dariya shi ma ya yi,ya mayar mata da martanin abun da ta masa.
Aemana bata sake cin wani abinci ba, ita da Mahmood sai madara,suka yi masu sallama, suka shiga dakin su,brush su ka yi ,suka yi alwala sukai sallah a tare, sannan suka kwanta.
Babban abinda ya ban mamaki shi ne, yanda Aemana ke ma qaramin yaron bayanin barin shi za ta yi anan, ya na kuma fahimtar ta, sannan ya na mata alqawuran zama yaron kirki.
Daren ranar Aemana kwana ta yi ta na kukan rabuwa da yaron ta.
Washegari kuwa, Mahboob ya dauke ta, ita da su Aaseeyah suka shiga gari.
Aemana ta ga Nigeria, ta yaba matuqa,ta yi santin ganin albarkar da Allah ya azurta mu da shi,Aaseeyah ta mata tsaraba, irin tamu, wanda za ta iya amfani da su, har da kayan fulani, ta mata bayani cewar yaren kakar su ne mace,sannan ta yi mata yaren fullancin, duk da ba ji taje ba,ta ji yaren ya mata dadi,hotuna ta dinga nuna mata na fulani kyawawa da kayan a jikin su,abun ya burge Aemana sosai.
Ta sai mata atampopi an bayar a dinka mata, ta sa an dinka mata hijabbai irin namu guda biyar.
Aemana na ta jin dadi, tare da nishadi, ta dauki hotunan dik wani abu da ta ga ya burge ta,bakin ta ya kasa rufewa.
Daga nan gidan su Mammee suka je, anan aka sha darga, Aaseeyah har da kuka ba me dauke Mahmood, da kyar Ummee ta hakura ta sakar wa Aaseeyah.
Bayan sun dawo gida Aemana ke sanar da Aaseeyah cewar akwai kaya da ta sako ta jirgi za su zo na Mahmood ne, da tsarabar jarirai,
"Hidimar ta yi yawa, ga akwatuna biyu da kika kawo na jarirai, kuma ki ce akwai wasu a hanya?"
"Inda ban da shi sai dai na zo haka kawai, amma tunda akwai ki min addu'a kawai"
"To muna godiya sosai,Allah ya saka da alkhair"
"Ameen"
Ranar Aemana a qirji ta dora Mahmood ya yi bacci, idanun ta kamar za su fadi dan kuka,ji take kamar ta fasa barin yaron ta gudu ba tare da kowa ya sani ba.
********************
Washegari da safe da misalin qarfe tara suka je suka amshi dinkin ta, daga nan suka wuce Airport,Mahmood na gidan su Ummee, domin dabara suka masa, suka tafi, Aaseeyah ta tausayawa Aemana matuqa, musamman da ta san irin shaquwar da ke tsakanin su.
Har suka raka ta Airport ta gama dik shirye-shiryen tafiya,bata dena kuka ba.
Haka suka koma gida Aaseeyah na ayyanawa a ran ta, zata riqe Mahmood kamar yaron ta na cikin ta.
Ta gidan Ummee suka bi suka dauke shi, abinda ya ba su Aaseeyahn mamaki shi ne tambayar da yaron ya musu, na cewar,
"Hal dhahabat?" (Ta tafi?)
"Na'am laqad dhahabat" (Eh ta tafi)
Hawaye ya fara, masu gudu da dumi, a hankali ya fara shessheqar kuka,
"Yah Mahboob stop the car,"
Tsaida motar ya yi,ta bude baya,ta zauna ta dauki yaron ta na lallashi, ita kan ta daurewa take, amma tausayin shi ya addabi zuciyar ta.
Wata iriyar soyyyar Aaseeyah ke ninkuwa a zuciyar Mahboob, wata tambaya ce ta shiga zuciyar shi.
'Shin da ita ce,ta aikata zina, ta samu ciki ta haihu, zan aminta in karbe ta, da d'an ta?'
Hummmmmm haka rayuwar nan ta zama, maza can do anything, ina nufin anything su zauna lafiya mata su karbe su,mata kuwa komai qanqantar abu in suka yi, su na cikin kyara, tsangwama...
Ina son jin ra'ayoyin ku makaranta akan wannan tambaya ta Shuwayya-shuwayya....
Kindly subscribe to my channel,on YouTube https://youtube.com/channel/UC0NWMTHsARvoeI0CTnclFig
TAUBASHI
PGE 64
Har suka isa gida Mahboob na ta maimaita tunani guda daya.
'Shin me ne ne laifin mace idan ta yi cikin shege? Laifin ta ya fi yawa ne akan na namiji, ko laifin namiji ne ya fi yawa? Wa ya fi dace wa a hukunta in zina ta afku?'
Naga alama ba shi da amsoshin wadannan tambayoyi da suka masa yawa, bari na taimaka masa.
Shi laifi irin na zina ba a ware wa ace wai wane ne me laifi, ko wance ce me laifi, sai dai in fyade akai,domin mace na fara gayyata domin aikata ta, namiji ma na fara gayyata, ko su gayyaci junan su.
Laifin mace kuwa a bangaren nan shi ne, zaqewa, da saurin bada kai, in mace na son namiji, duk kyaun ta, duk ajin ta, duk kwarjinin ta, duk ilimin addinin ta, duk tsoron Allahn ta, ta na iya aje su a gefe,ta sabawa Allahn nan da ta ke matuqar jin tsoro,ta bawa wani kan ta,sai komai ya lafa ta shiga tashin hankali da damuwa, wata kuma daga nan hanya ta bude mata.
Namiji zai iya fin zama mai babban laifi in zina ta afku, domin namiji shugaba ne, uba ne, d'a ne, qani ne,kuma yaya ne,dan haka shi me iya hana a aiwatar da ita ne ta kowanne fanni, amma a wasu lokutan abun takaici shi zai yi kira a aikata ba daidai ba.
Hukuncin zina na duk wani wanda ya aikata ta ne, ba wariya tsakanin namiji ko mace, indai shari'a ta hau kan ka/ki, to tabbas za ka amshi hukunci.
Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya shigar da motar shi cikin farfajiyar gidan.
Ranar sun kwana tausayin Mahmood, domin kuwa zazzabi ne mai zafi ya rufe shi,Aaseeyah har da goya shi ta yi, ko girman shi bata gani, shi bai saba da goyo ba, amma ya ji dadin shi, sai jijjiga shi take sai da ya yi bacci, haka ta jera su a gado, 'yan biyu na gaban ta, shi na bayan ta,in ta juya wajen 'yan biyu, sai ta juya wajen shi, Mahboob kuwa zama ya yi kamar maraya,ya kasa bacci saboda rashin ta a kusa da shi,dakin sai ya masa girma.
Ba abinda ya ke tunawa irin kulawar Aaseeyah a gare shi, in ciwon kai ya ke, ranar a qirjin ta zai kwana, haka za tai ta matsa masa kan sannu a hankula ta na shafawa har ya yi bacci,in kuwa ya farka zai ga kamar a farke ta kwana, sai ta yi kissing goshin shi, ta sake rungumar shi kamar wani qaramin yaro, kafin ta tada shi a jikin ta.
Lumshe ido ya yi tare da murmushi, a haka bacci ya dauke shi cike da tunanin Aaseeyahn Mammee da Ummee.
Da safe sun tashi jikin Mahmood ba zafi, amma ba ya wani walwala,aiki kuwa ya ga Aaseeyah, dan kuwa ba ta bar gefen shi ba, har sai da ta ga ya sake, ko tsoron kar ya kada mata yara batai ba, haka ta dinga bashi su, dan daukar su kadai ke sa shi farin ciki.
Ba su gaisa da Aemana ba sai da daddaren ranar Mahmood ya yi bacci, Aaseeyah ta boye mata halin da ya shiga, gudun tada mata da hankali,ta nuna mata dai ya yi kuka da su na komawa, daga nan bai sake damuwa ba.
Aemana ta ji dadin hakan matuqa, dan da hankalin ta tashe, tun da ta tafi danasanin barin shi take, ta na ganin ba zai saba da mutan gidan ba.
hoton shi ya na bacci Aaseeyah ta dauka ta tura ma Aemana, ta yi ta godiya.
Tun daga wannan rana, sai dare suke gaisawa, har sai da Mahmood ya ware, ya saba da Aaseeya, ya na kiran ta da Ummee,ranar da ya fara kiran ta da Ummee, Mahboob ya ga rawar kai,murna kamar me,har so take ta ji ya ce Ummee, sai wani dadi ya lullube
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 41