fatan ba zai sake aikata wannan zunubin ba,kuma ka yi irin shi,indai bawa ya yi haka baya buqatar sanar da kowa....yanzu dole ne ka tabbatar da cewar rayuwar Aemana bata lalace ba bayan tafiyar ka,dole ne ka bibiyi bayan rabuwar ku,dole ne k nemi yafiyar ta,kafin Allah ya amshi naka tuba, bayan haka ni na yafe maka dik abinda ka ke ganin ka min,nima ina fatan Allah ya yafen dik abinda na aikata ba daidai ba,kuma ina fatan har abada ba zaka sake aikata kwatankwacin irin wannan laifin ba"
Baki sake yake sauraron qaramar yarinyar dake a matsayin matar shi a yanzu,cikin sauqi haka ta yafe masa?
"Da gaske ki ke kin yafe min, za ki iya zama da mutum kama ta? Aaseeyah da gaske komai ya wuce cikin sauqi haka? Kece fa mai kishin nan, anyaa kin hakura da gaske kuwa?"
"Yah mahboob lokacin wasa daban, lokacin da ba na wasa ba ma daban,ina son ka, ina jin qaunar ka a cikin jini na ta na yawo, abinda ya faru ya riga ya faru,ba zan iya sauya hakan ba,"
Zubewa ya yi a bisa guiwowin shi dika biyu ya riqe hannayen ta, ya fara zuba godiya tare da alqawuran da ya ke ji har qasan ran shi zai komai dan cika mata su,murmushi kawai take zubawa, qarshe ta sa hannun ta a saman kan shi ta na shafawa, shi kuma ya kwantar da kan nashi a jikin cinyar ta,yana shaqar qamshin jikin ta, a hankali ya fara goga hancin shi a jikin cinyoyin ta, ya fara saukar mata da kasalar da ta sanya ta zama a kusa da shi, tare da manna kan ta a qirjin shi cikin jin kunya,hannu ya sa ya tallabe ta ya matsa ta da qirjin shi,
"Aaseeyah ji nake kamar na tsaga qirji na biyu, na sanya ki a ciki na rufe,saboda ki zauna a cikin jiki na har abada, Aaseeyah ban san irin son da nake maki ba,ni dai abinda na sani shine ke ce rayuwa ta, ba zan iya rayuwa ba ke ba,in na ce ba zan iya rayuwa ba ke ba ina nufin hakan,duk sanda aka ce ba ke yau ki tabbata ko kwana na bai qare ba to rayuwa ta ba ta da amfani"
"Yah Mahboob iya abinda ka ke ji ka ke fada,abinda na ke ji zuciya ta ta kasa fassara shi a cikin kwakwalwa ta, ballantana labbana su furta shi,kai ne jinin jiki na,soyayyar ka ce zuciya ta, in ba jini a zuciya ba rayuwa kenan," daga kan ta ta yi ta kalle shi, idanun su na cikin na juna ta ci gaba da cewa, "Yah Mahboob ba zan iya rayuwa da kowa ba a matsayin miji in ba kai ba, ba zan iya ci gaba da numfasawa a duniya ba dik sanda baka cikin ta"
A hankali Mahboob ya hada goshin shi da nata, hancin su na gogar na junan su,wani irin dumi fuskokin su ke fitar wa,zuqatan su na dokawa a tare,labban shi ya goga a nata, da sauri ta maida leben ta na qasa cikin bakin ta ta saki murmushi, sannan ta sauke kan ta qasa cikin jin kunyar shi.
A hankali ta sauka daga jikin shi ta koma saman gado,binta ya yi ya rungume ta, ya dora kan shi a kafadar ta,
"Haka amarya ya kamata ta yi wa angon da take tsananin so? Gaskiya ki ajiye kunyar ki a gefe mu raya wannan daren,saboda ya zama a cikin tarihin rayuwar mu,yanda ko mun shekara dari in mun tuna za mu ji nishadi"
Juyar da ita ya yi, ya hade fuskar su,ya jima ya na kissing din ta, sai da ta ji iska na neman mata kadan sannan ta tura shi baya ta miqe, ji ta yi kamar zata fadi qafafun ta sun sake.
Kwabe fuska ta yi cike da shagwaba ta ce,
"Yah Mahboob yunwa nake ji"
Da rawar jiki ya miqe ya fita parlour,ya dakko ledar da suka zo da ita, suka ci kajin da ya siyo suka sha juice,suka shiga a tare suka wanke baki tare da daura alwala.
Sallar nafila ya ja suka yi,bayan nan ya dafa kan ta ya fara zubo addu'a da yaren da ya girma ya yi wayo a cikin shi.
Aaseeyah na jin saukar muryar shi a kunnen ta kamar wata busar sarewa mai dadin sauraro,lumshe ido take ta na jin yanda tsigar jikin take miqewa,bata san sanda ta sanya hannayen tata zagaye shi da su ba, murmushi ya yi,bayan ya gama addu'ar ya dauke ta cak,ya dora a saman gado,juyawa ya yi ya kallen ya ce,
"To malama Hameedan Hammaa a je gida Hammaa na kira"
Sumi sumi na fita na koma parlour nima na kahye wuta, nicce ina nan sai swahiya zan tai gida, sai na dau rahoton swahye😂
Ku min addu'a anjima na samu appetite din rubutu,ina jin na fiku matsuwa na kammala wanga novel,thank u so much for all ur du'as,Allah ya baku lada ya qara zumuncin dake tsakanin mu, barakallahu fikum.❤
TAUBASHI
TAUBASHI
PAGE 54
Yesmeen ce tsaye a qofar gidan su Mahboob, ta na jiran a bude mata qofa, ta jima tsaye kamar ta koma, amma ta gyara tsayuwar ta, bude qofa Mahboob ya yi ya leqa kan shi, murmushi suka yi wa juna, ta gaida shi, tare da dan jira ta ga ko zai matsa ta shige ta ga shiru,
"Uhmm dama na zo ne na ga ko Aaseeyah ta tashi,"
"Bacci take, ki dawo anjima"
"Ok,sai anjiman"
"Ok"
Kafin ta tafi ya maida qofa ya rufe, murmushi kawai Yesmeen ta yi,ta tafi, shi kuwa ya na komawa tea din da ya hada ma Gimbiyar shi ya dauka, ta na zaune bakin gado,fuskar nan ta yi jawur, duk ta kumbura,da ganin kayan jikin ta ta yi wanka ta shirya, amma ba walwala a fuskar ta,ajiye dan madaidaicin farantin da ya dora tea din ya yi a side table din dake dakin, sannan ya durqusa a gaban ta,cikin sigar lallashi ya kama hannun ta tare da sassauta muryar shi.
"Mar'atee,ga shayi ki dan sha,zan je na hada maki abun karyawa mai kyau na dawo,kinji?"
Kwalla ce ta cika idanun ta,tunawa da daren jiya,Mahboob bai san tausayi ba, bai san yarinya ba,bai tausaya mata ba ko da da qiftawar ido, dan shan majina ta yi irin na masu kuka sannan ta ce,
"Ni dai na qoshi,ba zan sha ba,"
"Meya sa?"
"Ban yarda da kai ba"
"Ni din? Haba 'yar aljannah inshaa Allahu,farin cikin Mahboob,abar son shi,mace daya tamkar da babu kamar ta a duniyar Mahboob, to na ji baki yarda dani ba, amma ni na yarda dake ai, ki sha dan yardar da nai da ke"
"Ba na shan abun hannun mugaye"
Dariya ya ke yi sosai sai da ya zauna a gaban ta, ita ma a hankali bakin ta ke motsawa da son yin dariya, amma ta dake,
"Dan Allah Hayatee ki sha,kinga har ya yi sanyi"
Dan juyar da kai ta yi ta na tura baki, sannan ta miqa hannu ta amsa,har zata kai bakin ta ta fasa ta kalle shi cikin hararar da ta fi kama da kallon so ta ce,
"Zan sha amma ba dan halin ka na jiya ba,zan sha kawai dan kar ka yi kuka irin na jiya"
Dariya suka kwashe da ita,cikin dariya ya ce,
"To ai dad'in abun ba ni kadai nai kuka ba, kuma ba wanda na kira domin neman taimako daga wajen ki, ke kuma fa? Daga kan Mammee har Ummee jiya sai da kk kira"
Ajiye Tea din ta yi ta fada jikin shi ta na masa dukan wasa, sanan ta ce,
"Dama wa zaka kira tinda ba kai ake cuta ba,ai zan rama ne"
Hannayen ta ya riqe, ya qarasa kwantar da kan shi a qasa, ta na kwance a saman jikin shi, murmushi suke ma junan su mai ratsa zuqata,cikin sanyin ya dora hannun shi daya a bayan ta ya sake manna ta da jikin shi, sannan ya shafi kuncin ta da hannun shi daya, ya ce,
"Zan so ganin ranar da zaki rama abinda na maki jiya"
"Yah mahboobbbb,"
Cike da shagwaba ta fadi hakan, ta daki qirjin shi cikin wasa tare da kwantar da kan ta a qirjin shi.
Sun jima a haka suna sauraran bugun zuqatan junan su,har Aaseeyah ta fara bacci,jin saukar numfashin ta a hankali ne ya sanya shi fahimtar ta yi bacci,a hankali ya fara qoqarin tashi da ita dan ya kwantar da ita, farkawa ta yi, ta miqe da sauri,wanda hakan ya sa ta yi dana sanin tashi da saurin, yar qara ta saki kadan sannan ta ce,
"Me...mee...me zaka min?"
Daga hannu ya yi, sannan ya ce,
"Na ga kin yi bacci ne zan kwantar da ke,"
"Ah....ah ba na so... zan kwanta da kai na"
Murmushi ya yi ya fita, ya na fita ta lallaba ta kwanta,duk jikin ta ciwo yake mata, musamman hannayen ta da suka sha matsa, da cinyoyin ta, ta na dora kan ta a pillow wani qayataccen murmushi ya subuce mata,soyayyar Mahboob ta ke ji ta na ratsa dik wani sashe da lungu na jikin ta,ji take ba zata taba iya rayuwa ba in ba shi a kusa da ita,a hankali ta fara lumshe ido,saboda nauyin da suka yi da bacci, da gajiya.
Mahboob ya shiga kitchen kenan dan hada masu abinci, ya sake jin bugun qofa, tsaki ya dan yi ya fita,
"Yaran nan ba za su bar mu mu huta ba,dama ba a hada mu waje daya da su ba"
Yesmeen ce dauke da abinci,gaida shi ta sake.yi ta miqa masa, godiya ya yi ya shiga dan ajiyewa, ba zato ba tsammani ya ga ta bi shi ta shige parlour,
'Wai yarinyar nan bata san ba a zuwa ma sabon aure da sassafe bane? Su waya je musu?'
A zuciyar Yesmeen kuwa tausayin Aaseeyah ne cike, dan ta tabbata Aaseeyah bata san komai ba game da rayuwar aure, ga shi maza ko shimfidar masallaci ne tsabar ustazanci sun san ya zasu sarrafa mace,ta na da yaqinin Aaseeyah na buqatar taimakon ta, amma ina take?
Ta na kalle kalle Mahboob ya shiga ya ce,
"Gashi har yanzu bata tashi ba"
"Ok to bari na je anjima zan dawo"
"To sai anjima din, in ta tashi zan fada mata zata kira ki"
"Ok"
Raka ta ya yi, ya rufe qofar daga nan,
"Yara sai sa idon tsiya"
Yesmeen kuwa da ta koma ta bawa Hassan labari,sai ya yi dariya ya ce,
"To da nufin ki kawai ya zuba mata ido? Ke kin damu wataqila ta na can hankalin ta kwance"
"Anyaa"
Haka suka ci gaba da hirar su ya na shirin fita.
Bangaren gimbiya Tasneem kuwa tun daren jiya ta fara kai qorafin ta ga Hussein,ta zayyana masa qarya da gaskiya akan Aaseeyah ta wulaqantan ta, ta tozarta ta, sannan ta nuna mata tun yanzu ba zata yi zumunci da ita ba sai da Yesmeen 'yar uwar ta.
Ran Hussein ya baci, an taba masa matar so,tun daren jiya suke maganar har sukai bacci,yau ma da ita suka tashi,su na ta bawa juna shawarar yanda za su zauna da su Aaseeyah har Yesmeen din ma.
**************************
Umaimah ce zaune a qasa ta miqe qafafun ta ta na karyawa, Mammee da Ummee na saman table suna karyawa suma, Abee da Abbu sun fita tun 8,yau wata biyu da auren su Aaseeyah d Mahboob, Ummee ce ta ajiye spoon, bakin ta cike da abinci, ta ce,
"A gaskiya rashin Aaseeyah a gidannan ba qaramin asara bace, ka ji gida shiru kamar an yi rasuwa"
"Yanzu Maman Noor mu ba mutane bane?"
"Ke Subai'a kema dai kin san me nake nufi, yau wata biyu da auren yaran nan amma ji nake kamar an yi wata biyar"
"Ni dai bana wani kewar ta Maman Noor kedai da kk kewar fadan ku ke kk damu"
"Ai ko qarya kike, ko rabon fadan namu ai abun kewa ne...har kin tuna min shekarun baya, watarana ina shara a parlour, ina dan lungun nan da muke aje takalma? Na duqa ina sharewa kawai sai na dinga sharo ledar maggi, maggi kala wajen uku, sai tsoro ya kama ni, musamman da na ga ba gwaguya akai ba balle na ce bera ne, kitchen dina na je na duba duk robobin maggi na na ga komai daidai,sai kawai na sa a raina wataqila beraye ke kwaso ledar su ajen a wajen,...na yi shara na gama, ah ah, ba sai ga abu ya zama kullum nai shara sai na shari ledar maggi sama da biyar ba,sai ko na fara tsorata na ce wataqila aljanu ke girki a wajen, na tsiri zaman parlour na ga dan iskan aljanin da ze doran tukunya,wai daga shiga ta daki nai sallar la'asar na dawo, yarinyar nan ta biyo wa su Umaimah makaranta, kawai ina fitowa na ga ta na lashe ledar maggi ta na turan lungun kujera, na ce ohhhh dama kece aljanar da ke zubar min da ledar maggi, ta na jin muryata ta bi ta qofar kitchen a guje, bata sake zuwa ta sha min maggi a parlour ba"
Dariya Umaimah take har da hawaye, Mammee ma dariyar take, cikin dariya ta ce,
"Ashe shi ya sa maggi na ko leda nawa na bude ba ya kai wata ya qare, har rage saka maggi na dinga yi a miya,"
"To kin ji me satar maki maggi yau"
"Ummee ba fa ita kadai take sha ba, har da Ummu Suleim, ai ita Ummu Suleim ta iya taku ne, in ta diba ba ki taba ganewa, bata diban sama da uku"
"Ke ki ji yan banzan yara, ashe sun jima suna mana satar maggi,to ni kwata kwata ban kula maggi na na qasa ba,Allah ya shirya mana,ai dai yanzu sun yi aure, kuma za su haifa, su kuskura yaran su suyi fitina su ce za su tsawatar sai na barar wa da yarinya hauru"
Dariya Umaimah ta sake ballewa da ita,
"Lallai Aaseeyah ba zata tsufa da haure ko d'aya ba"
"Ya danganta da yanda ta ke ma yaran ta"
Hira sukai ta yi suna tunawa da quruciyar yaran nasu.
******************************
Aaseeyah ta fara zuwa aiki ita ma, suna da Chamber na su na kan su ita da Amatullah,ta so Mahboob ya barta ta na tuqa motar ta da kan ta wadda Abee ya sai mata, amma ya qi sam, ya ce ba yanzu ba.
Tasneem na matuqar kishi da zuwa aikin da Aaseeyah take yi, kai da ma komai na Aaseeyah,soyayyar da suke zubawa a gidan,kulawa da girmamawar da suke ma juna,kwalliya da tsaftar da suke da shi,qamshin da gidan ya fara kamawa saboda yawan ta'ammuli da turaren wuta da Aaseeyah ke yi, Hussein in ya na shaqar qamshin Tasneem ta dinga masifa da bala'i kenan.
Aaseeyah na hankalce da duk abinda Tasneem ke yi ba ta dai da lokacin ta ne yanzu, saboda wani case da suke handling akan domestic violence, ta na so sai ta nutsu yarinyar ta samu justice sannan ta dawo kan Tasneem,in ta na bawa Amatullah labari Amatullah kan ce
"Rabu da ita Aaseeyah irin su banza ake da su da kan ta zata aje tsanar da ta maki,"
Aaseeyah kan ce,
"Inaaa irin su Tasneem iri na suke nema kan su nutsu, ko kin san har Yah Hussein yanzu da kyar yake amsa gaisuwa ta in ta na kusa?"
Haka zata yi ta bawa Amatullah labari,Amatullah na jinjina halin shirme irin na Tasneem.
Bayan sati biyu da kammaluwar case din da Aaseeyah ke yi, watarana suna zaune ita da Yesmeen,a dan wajen shaqatawar gidan, an zuba kujeru irin na simintin nan da dan table, ga ciyayi a wajen da shuke shuke gwanin sha'awa, Yesmeen ta juya baya suna magana da Aaseeyah, sai Aaseeyah ta hango Tasneem tafe,zanin ta daban riga daban, abun kunya ne a ce ta na zaune a wannan gidan ta na irin wannan shigar, duk da ba wani hanshaqin gida bane amma mazauna cikin shi masu aji ne.
Hijabin da ta sanya duk ya cukuikuye, kofin roba ne a hannun ta ta zubo juice ciki, itama a dole sai an sha jusi irin na su Yesmeen.
Aaseeyah saurin miqar da qafar ta tayi ta kara wayar ta a kunne, Yesmeen bata ji waya ta yi qara ba sai maganar Aaseeyah da ke tashi, sai ta yi zaton ko ita ta kira, Tasneem ce ta saki cup din hannun ta juice din ya malale a qasa sakamakon jin hirar Aaseeyah da ta yi a waya.
".......eh ai nake fada maki ta maida Yah Hussein kamar bawan ta, ....ga baqar qazanta,kullum sai ya yi mita akan qazantar ta,ni ke bashi hakuri,..... ga ba ta iya girki ba,keee sai dai kin ga wadda ya aura,...... shi ya sa na wa Mammee maganar ki,tunda dama can kuna son juna,......kinga sai a samu a yi abinda bai samu ba da,ku yi auren ku, wataqila ya samu nutsuwa a wajen ki,......masha Allah, ga ki da kyau, ga tsafta, ga iya kwalliya, ga uwa uba addini,......ah ah Mammee dai bata ce komai ba har yanzu, amma gobe inna je zan sake lallaba ta,..... gwanda a yi auren kin sama masa kwanciyar hankalin da ya rasa"
Da gudu Tasneem ta juya gidan ta da kyar take ganin gavan ta tsabar tashin hankali da gigicewa,wani irin kuka ta saki mai qara da ciwo,ta hau wurgi da duk wani abu dake gavan ta ta na fadin,
"Ba zai yu ba...ba dan iskan da ya isa ya ma miji na aure....sai na ga bayan shi....miji na nawa ne...ni kadai....ni kadai ce matar Husseini har a lahira....."
Hummmmmmm Aaseeyah ki na da d'abi'ar dakko min magana ni hameeda.........
TAUBASHI
PAGE 55
"Aaseeyah ke da wa ki ke waya?"
Cikin dariya Aaseeyah ta ce,
"Ni da waya ta"
"Ban gane ba?"
"Ina nifin ni da waya ta nake magana, ba da kowa ba,kin ga, waccan 'yar rainin hankalin nake so na nuna wa bata iya komai ba a fagen rainin hankali, kin gane?"
Cikin dage girar ta guda ta ke tambayar Yesmeen, kada kai Yesmeen ta yi tare da jinjina shi, sannan ta ce,
"Na gane, amma dai ina tsoron kar shirin ki ya lalace, baki gama sanin yanda Yah Hussein ke tsoron Tasneem ba, wanda shi a ganin shi tsantsar soyayya ce"
"Na kula da hakan gaba daya, ni kuma na yi alqawarin zan sa ta san mahimmancin kan ta da kan ta, dan in bata san kan ta ba, ba yanda za ai ta san ya zata kula da wani"
"Humm Allah ya bada sa'a, nake fada maki matar nan halin ta sai ita,"
"Kar ki ji komai, bari na kira Mammee na fada mata plan dina, dan kar ta batan shiri"
Ta waya suka qulla duk wani abu da suke son kullawa.
Da dare ma bayan Mahboob ya dawo ta bashi labari, ya so ya hana ta, dan shi ba ya son matsala da qannen nashi, amma ta masa bayanin dalilin da ya sa take son shiga lamarin su Tasneem din, addu'ar nasara ya mata sannan ya ce amma in fa Tasneem ta debo mata 'yan daban cikin gari ba ruwan shi, dan ya kula gaba daya kan ta ba a daidai yake ba.
Dariya Aaseeyah ta yi ta ce,
"Humm da ta san karo na da 'yan daba ina primary 5 da batai gigin kira min su ba"
"Aaseeyah baki rabo da labarai masu bada dariya, na so a ce na ga quruciyar ki,naso ace ina nan ki ka girma,"
"Lallai da jikin ka ya fada ma, dan da gani zakai mugunta ma yara, ni kuma ba abinda zai hana na yi maganin ka"
"Koh?"
"Eh mana"
"To yanzu ban labarin 'yan daban"
"Nop sai wani jiqon,ina da abun yi yanzu,"
Tashi ta zo yi ya maida ta ta zauna,ya na qoqarin janye dankwalin ta dan ganin kyakkyawan gashin ta da ya leqo ta daurin dankwalin ta aka hau buga qofa da qarfi, tsaki Mahboob ya yi sannan ya ce,
"A gaskiya zama da yaran nan ba qaramin takura bane,kamar ba su son mu zauna hira sai an samu masu damun mu, ko 'yan qananan yaran su zo ko iyayen su"
Aaseeyah na tafe ta na masa dariya ta bude qofa, Hussein ta gani idanun shi jajawur, gefen shi Tasneem ce, ta sha riga da zani na atampa complete,har da jan baki,ga uban dauri ta kashe, bata qamshi ba ta wari,amma fa an sha gayu, kyaun ta ya bayyana gwanin sha'awa, amma fa idan ta ya yi ja da alama ta yi kuka.
"Yah Hussein sannu da zuwa bismillah"
"Ai ko baki ce mu shiga ba za mu shiga ki min bayani a gidan uban wa nake da budurwar da mukai alqawarin aure, kin je kin gama fada mata qarya da gaskiya,kin ja min bala'i da masifa, tun da na dawo ko ruwa ban sha ba, haka na fita ko karyawa ban ba,gashi yanzu ta sani a gaba da tambayar uwar wa zan aura"
"Subhanallahi Yah Hussein zauna na kawo maka abinci,"
"Dalla malama ni ba abinci ne ya kawo ni ba, in abinci nake so ai na san hanyar inda ake saida shi,fada min a gidan uwar wa nake da budurwa"
"Kaiii Hussein ka iya kalaman ka,kar ka manta Aaseeyah yanzu ba qanwar ka kadai bace, mata ta ce, ni kuma yayan ka ne, kar ka kuskura ka na dakawa mata ta tsawa haka, yanzu kai baka ji kunyar fadin ka san gidan saida abinci ba ga matar ka a kusa?"
"Shi ne ai,irin haka ai sai ta ji ba dadi ko Hayatee,ai wannan zagi ne da cin fuska ma a wajen ta,ta ya za a ce namiji kamar ka magidanci mai ajiyayyar mace kamar Aunty Tasneem ace wai ya na yawon siyan abinci, so ka ke mutuncin ta ya zube a idon mutane a ce itan ba mace ta gari bace? Kuma da ka ke maganar budurwa ni ba ni na yanke maganar auren ka ba, a cikin 'yan matan ka kaff ka tuna me suna Ruqayya,ita ce ta dawo yanzu ta kama.qafa da Mammee, Mammee ta duba gayun ta, da yanayin wayewar ta da ilimin ta n boko da arabiyya, sannan ta duba irin zaman da kake da matar ka,komi da kan ka ka ke yin shi,sai ta yarda za a je nema maka auren ta,beside ta na da hotunan ku da ke nuna kun sha soyayya a baya,"
Gunjin kuka Tasneem ta sanya tare da dora hannun ta a ka tq zube qasa yarab, ta na kiran,
"Na shiga uku na lalace ni Tasneem, kishiya da 'yar boko, ina zan saka raina, shikenan an raba ni da miji na har abada,"
Jikin Hussein na rawa ya hau lallashin ta, wani ashar ta danna tare da miqewa daga zaman 'yan borin da tai sannan ta ce,
"Inna yarda wata 'yar iska ta shigo gidan nan a matsayin kishiya ta shegiya nake,munafuki,ai dik laifin ka ne, tunda har da shaidar hotuna budurwar taka ta nuna wa Mammee,ba zan taba yafe maka ba indai ka qara aure, kuma gidan mu zan tafi"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, na shiga Uku, Aaseeyah yaushe wannan tashin hankalin ya bullo min banda labari sai yanzu? Ki bi ta ki bata hakuri dan girman Allah, in ta tafi ta barni mutuwa zan, ina son Tasneem,dan Allah Yah Mahboob ka sa baki, ka bata hakuri, kar ta tafi ta barni, ka yi tunani in Aaseeyah ta barka ya zak...."
"Kul kul na sake jin ka yi misali da Aaseeyah,zan sab'a maka, in zaka roqi alfarma na bata hakuri ka roqa kar ka sake misali da wannan mugun fatan akai na, tashi muje"
Sun jima sosai Mahboob na bata hakuri, daga qarshe Aaseeyah ta shiga bayan Mahboob ya koma, wani mugun kallo Tasneem ke bin Aaseeyah da shi, cikin kakkausar murya ta ce,
"Uban me ki ka zo yi min nan? Ina ce murna ki ke yayan ki zai qara aure? Sai ki bari in amaryar ta zo kin tare a bangaren namu"
"Aunty Tasneem ki bini a hankali, na zo ne na baki wata shawara da zata hana a maki kishiya, amma tunda cin mutunci zaki min na riqe shawarata, ki rungumi hakuri, domin nan da sati uku amarya zata shigo, an so ma a yi auren ne ba tare da kin sani ba, sa'a kikai ki ka ji ina waya,sai an jima"
Hussein na can ya na saka yarinyar su fitsari, ta tashi ta na kukan shagwabar za tai fitsari, abinda ya kamata a ce uwar ce ke yi uban ne ke yi.
Cikin sassauta kalaman ta ta ce,
"Ai ni na zaci har da ke ake qulle qullen nakasa zuciya ta"
"Akan me zan qulle qullen nakasa ki? Ki na da makaman da ita Ruqayya bata da shi, in ki ka riqe su, na tabbatar maki ko an auren ba zata kai labari ba, ballantana ma ana iya fasawa tunda dama qarin auren dalili ne da shi"
"Dan Allah ki sanar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 41