ba mu da kudi sai mu je gidan mu a samo kudi, har mahaifiyar mu ta gan mu rannan, sai ta ce Mammee ce ta sa na ke sata (sunkuyar da kai qasa ya yi, da alamar jin nauyin idanun mutanen wajen, sannan ya ci gaba)
A haka dai muka ci gaba da rashin ji, har Allah ya kai mu lokacin graduation din mu, sai suka ce za a had'a party, kowa zai kawo dubu goma goma, a take na ce ba zan ba, saboda ba yanda za ai na samu wadannan maqudan kudin a lokacin,nan da nan suka dinga zuga ni, suka ce za su taya ni satar kudin wajen mahaifi na, tunda a lokacin mun saba sata din kawai sai na ce shikenan muka saka lokaci da dare bayan kowa ya yi bacci zan bude masu qofa sai su shigo su saci kudin su tafi, washegari da dare sai mu yi partyn"
Kuka sosai Mahboob ya barke da shi, tare da jijjiga, Aaseeyah da Umaimah tare da su Ummu Sulein kafe shi da ido sukai cikin fahimtar inda labarin shi ya dosa, hawaye ne ya zuba a idanun Umaimah, ta matsa daga gefen shi, kallon ta ya yi cikin quncin da zuciyar shi ta mishi ganin yanda ta ke masa kallon tsana,abinda ya ke gudu kenan dama.
"Uhumm sai akai yaya?"
Numfasawa ya yi, sannan ya ci gaba, tunda ya dakko labarin dole ya qarasa.
"Ko da na bude masu qofa ba wanda ya ga shigar mu, har suka dauki kudin, su na qoqarin fita, Abana ya rufe qofa, tare da jingina a jiki, mahaifiyar mu ta fito daga daki, ta na kuka, ganin har da ni a satar da aka jima ana musu
'Yanzu Habeebee har da kai ake mana sata dama? Abun har ya kai sata da dare? Gaba me kuke son ku zama kenan, ko dake ba laifin ku bane, laifin waccan mayyar ce ita ta maka asiri ka lalace, (Mammee)'
'Dan Allah ku yi hakuri, party za mu yi, ina tsoron ku san ina neman kudi masu yawa na san za ku yi ta bincike akan abokai na shi ya sa muka shirya hakan'
'Ko me ka ke so da ka tambaye ni zan baka, dan ku fa muke neman kudin, in ba mu maku ba wa zai maku? Me ye amfanin dukiyar tamu? Ban kudin nan, ba zaku dauka ba, ku kuma ku bar gidannan kafin na kira maku 'yan sanda, kar na sake ganin ku da d'ana, ran ku zai baci,'
Kudin da Gazaa ya ciro wanda suka sata a gidan mu sun ban mamaki, ban zaci za su saci kudi mai yawa haka ba duba da cewa dubu goma kawai muka yi za a sata, Sam ne cikin fushi ya zaro bindiga, duk a zato na ta wasa ce,sai na ga Gazaa ya rude ya na cewa ya aje bindigar nan, amma yaqi,Gazaa ma dakko bindiga ya yi a bayan aljihun shi, ya nuna Sam da ita, ya ce ya ajiye, amma yaqi, nan da nan Sam ya saita mahaifi na a gaban ido na, ya harbe shi a qirji"
Kuka sosai Mahboob ya ke, tunda abun ya faru yau ne rana ta biyu da ya bayyana me ya faru a wannan mummunan daren,sai da ya yi kuka ya qoshi sannan ya ci gaba.
"Kafin in magana Gazaa ya harbi mahaifiya ta da ta je kwace bindigar a hannun Sam, nan take itama ta fad'i, ganin haka ne ya sa su guduwa suka bar ni a wajen, da kudin da suka dakko,ina tsaye kamar an dasa ni na ga Abee da Abbu, tare da su Mammee da Ummee, Ummee na ganin 'Yar uwar ta a qasa ta fadi a qasa a sume, kakannin mu ma a asibiti sika bude idanun su, tun daga ranar Jad Abdul Mudalleb bai qara lafiya ba, sati biyu da rasuwar Mahaifa na shi ma ya rasu, saboda ciwon zuciya da ya kama shi, Jad Auwal ya zo ta'aziyya, anan ya ji labarin abinda ya faru, ya sa 'yan sanda suka je aka kamo su Garzali da Sam, aka miqa su kotu aka yanke masu zaman gidan maza,ni kuma a lokacin sai iyaye na suka boye cewar da ni aka yi satar, har Jad Auwal bai san hakan ba, shi ya bada shawarar na bi Khala Lila da ta zo ta'aziyyar mahaifin ta, a can na ci gaba da karatu, har na samu aiki, bayan rasuwar ta na so na dawo amma inna tuna abinda ya faru sai na ji ba na son na sake saka qafata a Nigeria.
Bayan tafiya ta ne mahaifin Gazaa ya shiga ya fita aka fitar da su, yanzu haka shi ne ya gaji mahaifin nashi a harkar fashi da makami"
Umaimah kuka Ummee kuka, Aaseeyah kuwa fuskar ta ba wani abu da za ka iya ganewa, kallon shi kawai take,wai da sa hannun shi a kisan iyayen shi, tunda ta maida labban ta cikin bakin ta ta qura masa ido, ba abinda take tunani sai kallon shi kawai da take.
Shi kuwa idanu yake rarrabawa tsakanin Umaimah da Aaseeyah, kamar su kadai suke da alhakin yafe mishi laifin shi, ba ya son su ji tsanar shi a ran su,amma da alama ya makara.
Hannun shi ya matsa ya dora akan na Umaimah, a tsorace ta zame hannun shi a nata ta matsa nesa sosai da shi, ta na sake rusa kuka, bude baki ya yi zai magana, ya ga Aaseeyah ta miqe ta na qoqarin fita, da gudu ya je gaban ta ya duqar da kan shi saitin fuskar ta, idanun shi sun matuqar sauyawa daga farare zuwa jajaye.
"Ban san me zan ce maku dan ku yarda ba ni na kashe su ba, ban ma san su na dauke da bindigar wasa ba balle a ce bindigar gaske, ban san za su iya kisa ba, na yi danasanin sanin su a rayuwa ta, ina kan yin danasani, na tsani rayuwa ta, na tsani duk wani abu da na aikata a baya, har yau ban dai na neman gafarar Allah ba, dan Allah kar ku tsane ni, kar ku tsane ni ba zan iya jure tsanar ku ba a gare ni, dan Allah kuma ku yafe min kamar yanda su Abee suka yafe min, ku yafe min, ba zan iya rayuwa ba ku ba.....Umaimah ke qanwata ce, uwa daya uba daya, na san dole za ki ji haushin abinda na aikata, amma ki sani akwai yarinta a tare dani a wancan lokacin, sannan ban san su na da bindiga ba, ban san za su iya daukan rai ba, dan Allah kar ki tsane ni, na tuba, dan Allah kar ki tsane ni"
Juyawa ya yi dan komawa wajen Aaseeyah ya ga bata wajen, durqusawa ya yi a gefen Umaimah, bai san hawaye sun zuba mishi ba sai da ya ga baya gani sosai, sannan ya ji dumin su a kuncin shi, ya bata tausayi matuqa, amma tsoron shi take ji, bata san dalili ba, sai take ganin kamar itama zai iya kashe ta, ko ya yi sanadin da za ta mutu, tunda gashi shi ne sanadin mutuwar iyayen su,tashi ta yi ta fara taku za ta shige bangaren Ummee, yunqurin binta ya yi Noor ya riqe shi,
"Ka basu lokaci,dole duk wanda ya ji wannan labarin for the first time hankalin shi ya tashi, ka dubi Ummu Suleim d Yesmeen ka ga irin halin da suka shiga suma, mu ma ka fama mana miqin da ya jima a zuqatan mu, muna jin zafin abun kamar a sanda ya faru, ba dan mun tsane ka ba, is natural a ji haushin abinda kai ne silar faruwar shi, so ka basu lokaci"
Hancin shi ya ja da ya yi jawur saboda shiga damuwa, ya gyada kai dan ya fahimta, kallon Mammee da Ummee ya yi, ya ce,
"Dan Allah ku basu hakuri, ku sake basu hakuri ba ni da niyyar yin sanadin mutuwar iyaye na, babu d'an da zai so kashe iyayen shi da kan shi, ku fahimtar da su,"
"Inshaa Allah they will come around,komai zai wuce, kamar yanda Noor ya ce ne ai, sun tsorata da labarin ne, amma ka basu lokaci" in ji Mamme, a qoqarin ta na kwantar masa da hankali.
Daya bayan daya suka fara fita, aka bar Yesmeen, Ummu suleim,Noor, 'Yan biyu,Umaimah, Yesmeen ce ta tambaye Mahboob bayan ta tsaya a gaban shi,
"Ya akai kakar mu ta rasu ita? Kai ka kashe ta?"
"Ya salam ba ni na kashe ta va Yesmeen, ba zan taba kashe kowa ba, ku fahimce ni, rashin mijin ta ne da d'an ta suka sa tai ta jinya, ina Jordan ta rasu, ban samu zuwa ta'aziyyar ta ba sai Khala Lila ce ta zo a lokacin, dan ta riga Khala Lila ma rasuwa"
"Its all ur foult, kai ne silar rasuwar mutane da dama a zuri'ar mu,u ar a monster, ba ka cancanci ka rayu ba kai ma, da ma ka bisu ne sanda suka rasu, amma dake abun bai dame ka ba ga ka har yanzu a raye, su da suka damu ka ga ka yi sanadin rasuwar su,"
Fadin hakan da Yesmeen ta yi bai wa Umaimah dad'i ba, wata kusan ta fi wata,
"Ba shi da laifi a rasuwar kakannin mu, kar ki sake bashi laifin rasuwar su, tunda kike kin ma taba musu addu'a ne? Sai yanzu da kk ji sanadin rasuwar su za ki dora akan d'an uwa na?"
"Ni ma d'an uwa na ne ai,"
"Sai da ya fara zama d'an uwa na kafin ke,ki san kalaman da za su fito daga bakin ki"
Mahboob ya ji dad'in tare mishi da Umaimah ta yi, amma ba zai bari su yi fad'a a tsakanin su ba,wata shawara ce ta fado ran shi, dan haka d'akin shi ya shiga ya hau tattara kayan shi.
Ya na gama had'a kayan ya fito, ya share fuskar shi tass kamar bai kuka ba, sai jan da ta yi kawai,ta gaban su ya wuce, nan fa Umaimah ta bi shi da gudu, ta na kwala masa kira, bai tsaya ba sai da ya je tsakiyar gidan,
"Ina zaka Yah Mahboob ?"
"Zan koma Jordan ne, inna tafi za ku samu sauqin baqin cikin da na sanya ku ciki,ina roqon gafarar ku, ku yafe min"
Aaseeyah da ke labe jikin labule sakamakon kiran da ta ji Umaimah na kwala masa, ji ta yi ya na maganar komawa Jordan, zuciyar ta taji ta fashe, kamar an yarda tangaran a siminti, me ne ne wannan take ji mai zafi da ga jin kalmar barin su da ya yi, inaa ba zata taba bari ya tafi ya bar su ba, a da bata san shi ba shi ya sa ta hakura,zumuncin su ya tsaya a waya, yanzu kuwa ta san shi,kuma ta na jin wani abu mai girma game da shi, wanda ta ke ganin ba zata iya rayuwa ba shi a cikin ta ta rayuwar ba.
Sakin labulen ta yi, ta fita, ta na isa gaban shi kawai sai ta kama akwatin shi, wani irin sanyi ya ji, amma bai nuna ba,
"Aaseeyah da dikkan alama ba ki yafen ba, ki saken akwati na na tafi wataqila in kuka samu ba ku gani na komai zai wuce maku watarana,"
"Ka ji na ce maka na ji haushin ka ne da fari? Labari muka nemi sanin yanda komai ya faru, ka fada mana,to meye nawa a ciki?"
Shiru suka yi, dan kuwa ta sa su a rudani, wannan saurin miqa wuyan ba halin ta bane, amma yanda fuskar ta ta nuna gaskiyar abinda ke ran ta, sai kawai suka amince cewar da gaske take, abun bai wani shige ta ba.
A tare suka koma ciki, ta na ajiye mishi akwatin shi ta nufi bangaren su, littatafan ta ta shiga fiddowa, manya da qanana, na boko, cikin sauri take komai, sai da ta tara su waje guda, ta kwasa da kyar ta nufi bangaren su Yesmeen, a dakin Noor ta zube su, ta hada zufa, sannan ta ce,
"Yah Noor ina son ka koya min karatun abubuwan da a ke mana a makaranta, ina son daga yau, na fara daukan ta daya, na gaji da daukan na takwas da sauran su"
Kallon ta ya yi da mamaki, Aaseeyah da ko aikin gida aka bayar ba wai yi take ba, sai na malami mai duka.
"Ki na cikin hayyacin ki kuwa?"
"Kwarai, a da ban da dalilin maida hankali nai karatu amma yanzu na samu babban dalilin neman ilimi"
Toooo makaranta Aaseeyah ba ai karatu dan Allah ba sai da taji dangi an mammace, hala tsoro take kar ta zo kan ta ko?😂
TAUBASHI
Page 23
Noor ya yi mamaki matuqa, musamman da ya ga Maths sun fi yawa a littatafan ta, da English, dama su ne ba ta maida wa hankali, kuma ta sani kome take son zama a rayuwa sai ta iya su, ta maida masu hankali,Noor bai bata lokaci ba wajen fara koyar da ita Maths,sun yi sunyi Aaseeyah fa sam ba ta daukan haske, har ya fara jin haushi,ita kuwa qarshe kuka ta sanya, saboda ta riga ta sare tun yanzu, ta ajiye duk wani qudirin ta, ta tabbata in ba cikakken ilimi ne da ita ba, ba za a buga da ita ba a rayuwa, yanzu ilimi ya zama ado, da damar mutane yanzu sun dauki ilimi ta wata fuska, ba fuskar da ta dace ba, kowa da qudirin shi a zama mai ilimi, shi ya sa amfani da shi ya yi qaranci a cikin al'umma,za ka ga mutum da tarin ilimi, amma amfani da shi na masa wahala.
Hawayen da ke zuba mata ta sa hannu ta share, Noor tsaya wa ya yi da fad'an da ya ke mata, jikin shi ya yi sanyi, hannu ya miqa mata, nan take ta ji zuciyar ta ta sake karyewa, ta na jin ta kamar qaramar yarinya a gaban Noor din, a hankali ta taka zuwa gaban shi, bai bata lokaci ba wajen dora ta a cinyar shi, wata ajiyar zuciya ya sauke, kamar ta yaron da ya jima ya na son zama a jikin mahaifiyar shi.
Ita kuwa kuka ta sake barkewa da shi sannan ta juya ta na fuskantar shi,
"Yah Noor ashe da gaske ne da Umaimah ke cewa ni daqiqiya ce a bangaren boko, na iya tajweed, na iya qur'an da dik wasu littafa da ake mana a islamiyya, amma me ya sa na kasa iya bangaren boko?"
Kuka ta sake sanyawa, Noor kuwa bai bata lokaci ba wajen sake ware qafar shi ya sanya ta a tsakiyar shi, tare da jijjiga ta, ya na lallashi.
Ya na so ya mata magana muryar shi ta kasa fitowa,
"Shshshshshs"
Shi ne kawai abinda yake fada mata,yana ci gabada sauraron kalaman ta na kiran kan ta daqiqiya,kallon lips din ta da suka sauya kala zuwa ja mai daukan hankali ya ke, tare da ayyana laushin su. Zuciyar shi, bayan wasu mintina, ya sauke numfashi mai qarfi, tare da lumshe idanun shi, sannan ya bude baki cikin murya mai rauni ya ce,
"Aaseeyah ki na kashe min jiki da kukan ki,kin san ba na son damuwar ki ko? ....Zan iya shiga wani hali nima saboda damuwar ki,.... ba wani dalili ne ya sa baki iya boko sosai ba, illa da can baki bata mahimmanci ba,...ke ki na ganin in kk iya karatun islama kin gama, .....boko is optional,....wanda abun ba haka bane,..to wannan maida hankalin da baki ba shi ke tambayar ki yanzu,....kin gane?"
Daga kai ta yi sannan ta ce,
"Yah Noor to ka yi hakuri d ni mana ka daina min fad'a har Allah ya sa na fara ganewa, na maka alqawarin zan maida hankali,"
"Inshaa Allah zan qoqarta, ke din ce sai a hankali,"
Tashi ta yi ta fara tattara kayan ta saboda kiran sallah da ta jiyo,sallama ta mishi ta ce,
"Ammm, Yah Noor ko za mu dinga karatun a waje, mu saka kujeru, nan sai na ji ni a matse, ba iska sosai,"
"Zan na kunna AC sai a hada da fan, ya miki?"
"Ok, thanks ,bye"
Murmushi ya saki mai nuna kwanciyar hankali ya samu ga mai yin shi, ta na tafiya,ya fada bayi, wanka ya fara yi sannan ya fita masallaci.
Ita kuwa alwala ta yi ta yi sallah, sannan ta yi shirin islamiyya,da za su tafi Umaimah da Yesmeen cewa suka yi tsoro suke ji, wataqila mutanen Gazaa na nan na bin su, da kyar aka samu suka yarda za su, amma da sharadin sai an raka su, Mahboob ne ya ce shi ya fi cancanta da ya na kai su ya dakko su, nan da nan kuwa Mammee ta damqa masa makullin motar da ya ke mallakin ta, duk da ba inda ma take zuwa da ita, ta na nan aje ne da sunan ta ta ce.
Aaseeyah ba ta yi gigin shiga gaba ba, Yesmeen da gudu ta shige, a zaton ta za su yi riqe riqe su ukun, sai ta ga ba wanda ya kula yin ta, sai kuma armashin shiga gaban ya ragu mata, dama dan ai ta rikici ne.
Ganin fuskokin Aaseeyah da Umaimah ba wani walwala kamar da ne ya sanya Mahboob jin ba dad'i a zuciyar shi, sai ya ji tsanar kan shi ta kama shi a karo na ba adadi, amma zai komai dan sake samun soyayyar su da yardar su a gare shi.
A hankali ya fara rera waqar soyayya da harshen larabci, yanda kalaman ke fita da yanda harshen shi ke juyawa ne ya sanya Aaseeyah leqen shi ta mirrorn gefen da take, ta wani kwaaanta sosai ta yanda ba zai hango ta ba, va ta san ya na ganin ta ba, hakan ne ya sa ya ci gaba, ya na wani lumshe ido,
'Ya salam, Yah Mahboob kyakkyawa ne a cikin kyawawa,muryar shi kamar sarewa in kana saurara, zaqin ta kuwa ya wuce zuma zaqi, kalli idanun shi kamar na wanda ke zuwa gyaran gashin ido a kullum,wayyooo masha Allah, kyawun shi na tsinka yawu aradun Allah, gaskiya ya kamata nima na koyo kwalliya, ai abun kunya ne namiji ya fi mace kyau'
"In kin gama kallo na da zagi na a zuciyar ki ki fito mun iso tun minti biyu da suka wuce"
Da sauri ta kalli gate din makarantar ta ga su Umaimah har sun kusan isa aji, wata zabura ta yi ta gyara riqon jakar ta za ta fita,
"Da gaske yanzu Aaseeyah abun har ya kai ki na zagi na a ran ki? Na fa baki hakuri, in ki ka daina kula ni ya zan yi da zafin da zuciya ta ke min,watarana fa za ta qone"
Cikin zare ido da tsoron kalaman shi ta ce,
"Dan Allah zuciyar ka ta daina zafi, ni ba zagin ka nake ba,cewa na yi ka cika dan banzan kyau kamar mace,kuma a gaskiyar magana ba qarya ko ha'inci ni dai ina kishin fina kyau da kai, dan haka koyon kwalliya zan fara zuwa"
Murmushi da dariyar da ta taho masa ya danne sannan ya kalle ta da kyau ya ce,
"Aaseeyah, wanne irin sab'o kike son ki yi? Ni din ki ke gani na fiki kyau? To ki sani,ke ce kawai ki ke ganin haka, ina nifin dube ki fa Aaseeyah,kafin a samu mace mai kyaun ki sai an tsufa ana nema ba a samu ba, kalli hancin ki, kalli lips din ki,kin kuwa ga kyaun idanun ki? Hummm ba zaki gane ba, je ki makaranta kawai, ki ma cire a ran ki wai kwalliya za ta qara maki kyau, abinda Allah ya halitta kyakkyawa yi masa kwaskwarima bata shi ne kawai, ki na da kyau ke ce kyau, kuma ke kyakkyawa ce, kin gane?"
Abinda ta ke ji daga saman kan ta, zuwa yatsan qafarta bata taba jin kalar shi ba, wani irin dad'i ne na an yabe ka, an daukake ka, ba ta san ya zata misalta girman abinda take ji ba a wannan lokacin, bude qofar ta ga ya yi, tare da d'an duqa mata,kamar wani driver, sanya qafar ta tayi a waje, ta na daga masa hannu, ta shige.
"Masha Allah, daga yau na gano abinda Aaseeyah ta fi so, a yabe ta ko da ba tai mai kyau ba, musamman a halayen ta,za ta maka yarinta da mugunta amma ta na son a yabe ta,ga uwa uba kuma yabon kyawun ta,indai wannan ne kan samu Aaseeyah"
Har ya isa gida maganar yake a bakin shi,ita ma har ta isa aji ranar Murmushi take zubawa da ta tuna da kalaman shi.
Aaseeyah ta sake maida hankali wajen karatun islamiyyar ta,dan yanzu ne take son sanya hankali a dikkan karatun ta, dan na islamiyyar ma ba ta maida masa hankali yanda ya dace, tsokana ne zalla a ran ta.
Ko da suka dawo daga islamiyya, ranar a wajen Mahboob sukai hira, har yanuna masu inda Kakannin su suka zauna a da, wajen a rufe yake, amma ya fasalta masu yanda wajen yake, lokaci zuwa lokaci in suka had'a ido sai su sakar ma da juna murmushi,Umaimah ma ta sake sosai da shi, Mahboob kuwa ya ji dad'in hakan.
Sai tara na dare suka mishi sallama suka tafi saboda washegari akwai boko
Tafiyar Aaseeyah ke da wuya Hussein ya ja Ummu Suleim suka yi maboyar su, dan tunda abinnan ya faru ba qaramin kulawa suke ba kar asirin su ya sake tonuwa.
Umaimah ma su na shiga ta tsiri kaiwa Yah Noor Tea din shi, Yesmeen kuwa ta waya suke ta shan soyayyar su da Hassan.
Ko da Umaimah ta shiga ta tadda Noor na tisa Haddar shi ta qur'ani, domin kuwa yanzu har jan sallah yake a masallaci,mutane sun bashi yarda matuqa, kuma su na girmama shi, ganin Umaimah ne ya sake tado masa da sha'awar Aaseeyah da ya yini da ita a ran shi, rufe qur'anin ya yi, ya isa gaban ta, jikin ta har rawa yake saboda ya saba mata da kusantar shi, gashi kwana biyu ya dauke mata wuta kwata kwata, yanzu kuwa da ta gan shi ya na qoqarin kusantar ta sai ta ji kwanciyar hankali ta kama ta, zargin ko da Aaseeyah ya koma yi ya ragu a ran ta, amma duk da haka sai da ta tambaya, ya na tsaka da kissing din wuyan ta ta ce.
"Yaaahh Noooor,"
"Uhumm"
"Meye tsakanin ka da Aaseeyah? Son ta ka ke? Ko ita ma abinda kuke yi kenan in kuka kebe?"
Tura ta baya ya yi, sannan ya qanqance idon shi,ya ce,
"Wai ke me ya sa har yanzu ba ki yarda da ni ba? Me zan da qaramar yarinya kamar Aaseeyah? Karatu muka fara da ita fa, sannan kin taba ganin tun da ta girma na dauke ta? Ko ta rab'u da jiki na? Ai ita ta dauki wannan abun da muke as iskanci, ba zata taba bari na ma na taba ta ba,so kar ki sake min maganar Aaseeyah, tashi ki fita"
Qanqame shi ta yi ta na girgiza kai, tare da bashi hakuri, firr Noor ya qi qarasa abinda ya fara, a cewar shi, dole ya kawar da tunanin Umaimah akan Aaseeyah kwata kwata, in ba haka ba, kishi zai iya sa ta tona masu asiri.
"Na ce ki tashi ki je, saboda ina taimaka maki maganin abinda ke taso maki a nan, shi ne kike ganin kamar ke kike taimako na ko? Ok yau na fasa tashi ki je kawai"
"Yahhh Noor plsss mana, ba zan sake maganar Aaseeyah ba,"
"Ok na ji, tashi kije kin ga kin dade, ki bari sai an jima kin zo,"
"Ka yi alqawari?"
"Na yi alqawari"
Da sauri ta gyara rigar ta da ya dage mata, ta fita, kwantawa ta yi, ta na jiran su Ummu Suleim su yi bacci, amma sun qi, daga mai waya ba a jin komai da take fadai, sai mai chatting, tsaki ta yi ta dinga juyi, ba su suka yi bacci ba sai kusan sha biyu, sai da ta tabbata baccin su ya yi nisa, iyayen su ma sun yi bacci sannan ta bude qofar dakin Noor a hankali cikin sanda ta fada, ganin ta na shiga Noor ya kashe wuta ya sa ban bi sahu ba, gudun ganin aika aika.
**************************
Rayuwa na zuwa da sauyi kala kala, lokuta da dama wasu mutane su kan dauka in rayuwar su ta yi tsanani, Allah ba ya son su,ya manta da su, ta ya ya mahalicci zai manta da abun halittar shi? Wasu kuna su na ganin haske da budi a rayuwar su, sai suke ganin kamar Allah ya fi son su.
Ba haka bane kowa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 41