akan labarin Mahmood Little ba, saboda ba hurumin ta bane, ba komai ake kwashewa a fada ma qawa ba da sunan an zama daya, wani abun za a iya amfani da shi a lalata rayuwar ka, ko a tozarta ka.
Bayan sun yi sallah ne suka je wajen da suke zama, anan su Yesmeen suka tadda su, suna tsaka da hira Mahboob ya dawo, Aaseeyah ba kunya ta tsallake su ta bishi, Amatullah na mata tsiya Yesmeen ta ce,
"Kin ga Aaseeyah kowa ya san ta wajen rashin ji, amma kula da miji da bashi kulawa da soyayya ba wanda ya yi zato, duba da yanda samari basa gaban ta,amma dubi yanzu abinda take yi mu da muka jima da aure ba ma yin shi"
"Haka ake so, dama in baka samu miji naka na kan ka ba, ka guji zurfafawa a soyayya da kulawa, in ka samu naka na halal, duk wani abu da ka ga ya dace to sai inda qarfin ka ya qare fa"
"Haka ne Amatullah, Allah ya sa mu dace,"
A cikin gidan su Aaseeyah kuwa, abinci ta gabatar masa da shi, da komai da komai da ya dace, ta so ta zauna ta bashi ko ta taya shi zama ya ci,ya ce ba komai ta je wajen su Yesmeen kar su ga ta bar su.
Ba dan ta so ba haka ta tafi, ta na zuwa ta ga Amatullah na qoqarin tafiya,
"Tab wai da tafiya zaki baki sanar da ni ba? Lallai da kuwa na maki rashin M,tsarabar taki fa?in baki dau naki ba kin dau na Aunt Firdous da Mama ai"
"Kayyaa kin ga na manta ko, lallai da na tafi sai nai dan qaramin hauka dan haushi"
Komawa sukai a tare Aaseeyah ta dakko mata kayan, cikin mutuntawa suka sake gaisawa da Mahboob, (sun gaisa cikin wayewa ta addini, ba wannan haukan wasan qawar mata dinnan da mijin qawa) Amatullah na kula da su, dik inda Aaseeyah ta yi idon Mahboob na wajen,ya na murmushin da ke nuna tsananin son da yake mata, ita ma in ta kalle shi sai ta saki murmushi, a haka ta hada mata kayan a leda ta ce ma Mahboob za ta raka Amatullah bakin mota,
"Ok Hayatee sai kin dawo,"
Kashe mata ido daya yayi cikin salon son ta da yake ji kamar ya ma gangar jiki da ruhin shi yawa, murmushi ta yi wanda ya gamsar da shi cewar ta ji dadin duk abinda ya mata a wannan lokacin,
Suna fita Amatullah ta sauke ajiyar zuciya, sanan ta ce,
"A baya ina tunanin ba wanda suka kai mu soyayya ni da miji na, to ku kam kun zarta Lailah da Majnun din ta, waiiii,to dik sanda zan sake zuwa gidan nan ba zan zo ba ya na nan, saboda kar na katse maku kallon soyayya"
Dariya kawai Aaseeyah ta yi, ta na kallon hanya, idan ta na waje daya,
"Wato Amatullah ba zan iya fassara yanda nake jin Yah Mahboob ba a rai na, duk yanda na so fadi baki na baya iyawa, ni kadai na san ya nake ji game da shi,"
"Ai fa na ga alama; ba sai kin min bayani ba, dan na kula shi kan shi bayanin baida bayanin bayyana kan shi"
Dariya suka yi, Amatullah ta shiga motar ta ta wuce suna daga ma juna hannu.
****************************
Bayan watanni bakwai, cikin Aaseeyah ya shiga watan haihuwar shi, Umaimah ta samu qaruwar samun Namiji sun saka mashi sunan Abbu,su na kiran shi da Ameer, Ummu Suleim ta samu Muhammad Bashar.
Ummee ta buga qasa ta kuma ta ce sai Aaseeyah ta koma gida, saboda can gidan duk yara ne, in haihuwa ta tashi wa zai kula da ita, Abbu ya ce su Yesmeen ma mazan su ne suka kula da su, amma Ummee ta ce su daban, ba su da rawar kai da iyayi irin na Aaseeyah, Mammee ta ji dadin abinda Ummee ke yi, dan ita kan ta hakan ne a ran ta shiru kawai ta yi, kar a ga rashin kunyar ta.
Mahboob kuwa cewa ya yi indai za a dawo da Aaseeyah to fa shi ma tattarowa zai ya dawo gidan, in ya so sai su zauna a bangaren su, haka kuwa akai, Aaseeyah kuwa ba ta son dawowa, saboda kulawar da Mahboob ke bata gani take kamar zata ragu.
Amma kuma sai ya bata mamaki, duk abinda yake mata bai fasa ba, dan akwai sanda ya na tsaka da yi mata tausa, ita kuma ta na chatting da su Umaimah a group din da suke da shi ta whatsapp, Ummee ta shiga, bai bar abinda ya ke ba,hasali ma sake maida qafar ya yi cinyar shi da ya ga Aaseeyah ta na son janyewa, Ummee kuwa ba abinda ya dame ta, kwadon lansir din da tai wa Aaseeyah ta ajiye a dan table qarami ta ja mata gaban ta,sannan ta dungure mata kai,
"Munafuka, ki na nan kin mallake min yaro, har tausa yake maki, nan nan uban ki ko yatsan qafata be taba ja ba,shi ne dan kin ganni zaki wani janye qafa, dauki kwadon ki ci, akwai ruwan dafaffan zogale ma, na aje maki a fridge na matse maki lemon zaqi na saka ginger da yar tsamiya kadan,sai sugar,in kawo yanzu ko sai anjima?"
Cikin jin kunya Aaseeyah ta ce
"Sai anjima,"
Har Ummee ta zauna ta fara hira, Aaseeyah ta ce,
"Ummee zan sha yanzu"
"Ahaff ai na san ban dunguri banza ba, ni da na sani, na san dama jira ki ke na zauna ki tada ni tsaye, an maki baki rama ba? Ai ba Aaseeyah bace,ba zan dakko yanzun ba dan uwaki, sai sanda na ga dama"
Mahboob ne ya miqe da sauri zai je ya dakko,
"Ka na fita ina sheme ma kai da wannan murfin, dawo ka zauna, ko kai ka hada min abuna? Na fasa badawa se me"
Kukan shagwaba Aaseeyah ta saka,Mahboob kuwa ya rikice da roqon Ummee, abu kamar wasa sai suka ji Aaseeyah ta buga salati,sannan ta damqi Hannun mahboob da qarfi sai da ya duqa bai shirya ba.........
Abun ya zooooooo😂😂
TAUBASHI
PGE 61
Abu kamar wasa qaramar magana ta zama babba, Aaseeyah dai naquda ce gadan-gadan mai zafi ta tunkaro ta,Fadin ta ke a kai ta asibiti, Ummee ta kafe ta dage sai abun ya kusa, ba me zuwa asibiti da wuri,tun Aaseeyah na daure wa ta fara kuka, Mammee da ta ji labari alwala ta yi ta yi sallah raka'a biyu ta roqa wa d'iyar ta sauqi wajen Allah, tare da fatan Allah ya sauke ta lafiya cikin rufin asiri da aminci.
Mahboob idanun shi sun yi jawur saboda tausayin Aaseeyah, cikin zuciyar shi kuwa alqawarin ninninka addu'ar da ya ke ma mahaifiyar shi a kullum ya yi, ashe mata haka suke shan wahala? Ashe mace abar a tausayawa ce, a so ta, a ririta ta kamar kwai, a girmama ta, a mutunta ta? Lallai zai zama miji kuma uban da aka jima ba a yi irin shi ba a tarihi,zai zama gwarzon miji kuma alfaharin 'ya'ya da iyayen shi, zai nuna ma duniya cewar ya haifu daga mace,mace jaruma ce, jarumar da kafin a samu irin ta sai an tona.
Zuciyar shi ta quntata matuqa da hana zuwa asibitin da Ummee ta yi, ji ya ke kamar su qi bin umarnin ta, amma ya za su yi, wannan rikitacciyar matar in ba su bi umarnin ta ba cewa za ta yi an raina ta.
A nata bangaren kuwa Ummee ta na jiye musu zuwa asibiti da wuri ne saboda wulaqancin wasu daga baragurbin ma'aikatan jinya, ma'aikatan jinyar yanzu wasun su sun lalace da tozarci da cin mutuncin marasa lafiya,musamman talakawa da 'yan qauye,ta sani ba wanda zai kalle su ya wulaqanta su, amma ta na gudun kar su je a samu akasi basu hadu da na kirki ba, dan ita ma zata baje musu basirar tsohuwar ajiyar rashin mutuncin ta ne.
Aaseeyah na tsaka da cin azaba ta ji kamar za ta yi fitsari, a hankali ta furta hakan, nan da nan kuwa Ummee ta kama ta, suka fara tattakawa dan zuwa bayin da ke cikin dakin su, to dama bangaren daki uku gare shi,guda biyu lafiya lau suke ana amfani da su, guda daya qofar ta lalace,in aka rufe ana wahalar bude ta,gashi AC ta baci,kuma ba fan a ciki.
Suna tsaka da tafiya naquda ta murdo, cikin gigita da rauni Aaseeyah ta ce,
"Ummee ku kai ni asibiti kar na mutu, ni kadai na san abinda nake ji,....ku taimake ni....baya na zai balle....marata kamar ana naushi na...Ummee baya na.."
"Za mu tafi amma sai nan da minti talatin"
"Minti talatin? Ai kafin minti biyar ma na mutu Ummee.."
Cikin kuka Aaseeyah ta qarasa maganar ta, tura baki gaba Ummee ta yi, ta saka hannun ta a bayan Aaseeyah ta na matsawa,a haka ta raka Aaseeyah ta yi fitsari, ta na shan majina ta fito, dafe take da murfin qofar dakin zata rufe naqudar ta sake murdo mata, a gigice ta hau neman abun dafawa, ai kuwa ta dafe kan Ummee, ji ka ke qummmm ta buga da gini, a kidime Ummee ta sake qarar wahala,ta hau lalube, dishi-dishi take gani,bata zame ko ina ba sai qofar dakin da ke kallon na su Aaseeyah, ta bude qofa ta shige ta danna murfin ta rufe ta saka sakata, bakin gado ta zauna ta na muzurai, a hankali ganin ta ya fara dawowa, wata iriyar zufar wahala take ketawa,kafin ka ce kwabo goshin Ummee ya haye,idanun ta sun kad'a sun yi jawur dan azaba,numfashin wuya ne kawai ke fita mata.
Can bangaren su Aaseeyah kuwa sai da abun ya lafa mata, hankalin ta ya tashi, dan ta tuna sarai da abinda ya faru, Mahboob ne tsaye a kan ta ya na ta jera mata sannu.
Bude baki ta yi dan sanar da shi me ya faru,sai ruwan haihuwa ya fashe mata,cikin gigita kuwa ya taimaka mata ya saka mata hijabi saman doguwar rigar ta mai siririn hannu, wayar shi ya dauka suka fita zuwa asibiti, Ummee na daki bata san duniyar da ake ciki ba, dan ta lula duniyar azaba, kan ta mugun ciwo kamar zai fashe haka take ji.
Danasanin hana kai Aaseeyah asibiti kuwa ta yi shi ba adadi, a dan zaman da tai a dakin, a ran ta take ayyana,
'Shegiyar yarinyar nan nakasani ta so yi,Allah ne dai ya nufa da sauran kwana na a gaba, ta samu kai na ta buga da gini kamar ana fashen kwakwa, bari ta ji sauqi za ta ci uban ta ne, da ni take zancen'
Shafa goshin ta tayi ta ji yanda ya haye, gashi ya yi tsami bata mulmula ba, dole ta hakura,ji take da ma kukan ta tayi tunda ba kowa a dakin, da wanan azabar da take sha, amma firr hawayen suka qi zuba.
Tun kafin su isa asibiti da minti hudu kan baby ya leqo, su na isa kuwa, Allah ya had'a su da midwife mai mutunci,mai suna Amina Muhammad Boboi,nan da nan kuwa ta amshe su cikin mutuntawa da karramawa, ba bu bata lokaci Mahboob ya miqa musu akwatin da suka yi parking komai na haihuwa a ciki,kaya ne kala kusan biyar dan a cewar Aaseeyah a zab'a a darje ya fi a dinga kame kame.
Cikin ikon Allah kuwa ta samu ta haifi sankaceciyar yarinyar ta mace,nan da nan midwifes din suka hau duba lafiyar ta da ta jinjirar, abu kamar a mafarki, minti sha biyu tsakanin haihuwar Aaseeyah ba sai wani ciwon mai tsanani ya sake tunkaro ta ba, cikin sauri kuwa Midwifes biyu suka nufe ta, dayar ta ce,
"Sister Ameena da ma na fada maki twins ne"
Nan da nan suka taimakawa Aaseeyah cikin mintuna uku ta sake samun kyakkyawar budurwar 'yar ta, itan ma gyara ta akai, kamar yanda aka yi wa 'yar uwar ta, tsakanin su minti sha biyar ne.
Aaseeyah kuwa ana gyara ta baccin samun sauqi na dibar ta.
Mahboob ko dattin asibitin bai gani ba, haka ya dora goshin shi a qasa ya na sujjadar godiya ga Allah akan kyautar da ya masu ta yara biyu a lokaci daya, kyautar da basu taba zato ba.
Dakin hutu guda aka kai Aaseeyah,nan da nan kuwa asibitin ta shaida 'yar dangi ta haihu, mutan gidan har Mammee ba wanda bai je ba,mazan su da matan su har da su Abee da Abbu,Amatullah da Maman su ma sun samu zuwa ganin mai jego da yaran ta,Aaseeyah kuwa da kyar ta iya shan tea saboda baccin da take ji.
Ana ta hira da hayaniya ne Mahboob ya ce ma Mammee.
"Mammee ina Ummee? Ba ku taho da ita ba?"
"Ah ah, ba tare kuka zo ba dama?"
"Ah ah, ni da Aaseeyah kawai muka zo,dama na ga ta raka Aaseeyah fitsari, sai na ce bari na je na sauya jallabiyar nan na saka wata, ina zuwa sai na ga Aaseeyah ita daya a durqushe,kafin ta min magana muka ga ruwa na zuba, shi ne muka yo asibiti"
"Kar ka damu, da dikkan alamu ta tsaya a gida ne ta dora ruwan wankan wanke kishiyoyin ta, ya kamata a mata waya a sanar da ita, ruwan mutum biyu za ta dora ba d'aya ba"
"Gaskiyar ki ne Yesmeen,ki ra ta" in ji cewar Ummu Suleim.
Nan da nan kuwa aka dinga kiran layin Ummee, ya na ringing ba a d'aga ba,Ummee na daki ita kadai, sai zufa take yanka wa, saboda rashin fan da AC a dakin,gashi ta na jin ringing din waya amma ba damar dauka ta sanar da halin da take ciki.
Wani marayan hawaye ne ya gangare mata a kunci,ko yunqurin goge shi batai ba, tunda dama tun dazu take neman shi yaqi zuwa.
A nan dakin Ummee ta yini har la'asar sai da Aaseeyah ta cika awannin da ake ba me haihuwa, tunda ta haihu lafiya suka sallame ta suka yi gida.
Gyangyadi ya fara daukan Ummee ta ji hayaniya, firgigit ta miqe ta isa bakin qofar dakin,da guiwar hannun ta ta sa ta dinga buga qofar, cikin haushi da takaici, duk wani bacin ran ta ta dinga saukewa a jikin qofar,ai kuwa nan da nan hankalin mutan parlourn ya yi kan ta.
Aka tafi aka yi ta qoqarin budewa, da kyar aka samu qofar ta bude, hankalin Noor ya tashi, dan ya san dakin ba AC ba fan, ya san Ummee ta sha zafi, musamman da ke itan ba ma'abociyar son zafi bace.
Duk surutu da tambayar da ake waye a dakin Ummee saboda bacin rai taqi magana,Aaseeyah ce ta sanar da su Ummee ce a ciki, ta na ta qunshe dariyar ta.
Ko da aka samu sa'a aka bude qofar, hatta da dankwalin Ummee ta goshi ya jiqe da zufa, fuskar ta ba dan farar mace bace da an ga maiqo,wuce kowa ta yi,ta nifi parlour,su na hada ido da Aaseeyah, Aaseeyah ta kasa riqe dariyar ta, ga azaba ta na ji a jikin ta amma dariya har da hawaye, Ummee kuwa bangaren ta ta tafi,a can ta tadda Abbu ya na ta buge bugen waya ya na sanar da dangin Ummeen cewa d'an su Mahboob ya samu qaruwar tagwaye.
A hasale Ummee ta shiga ta na mita,bayi ta shiga ta fesa wanka tai alwala ta rama sallolin dake kan ta.
Aaseeyah kuwa na can na ba ma su Yesmeen labari cikin dariya, ba wanda bai dara ba a wajen, Mammee ce ta ce,
"In kin gama dariyar ki shirya wanka, Aaseeyah ki raba kan ki da iya shegen nan tamm"
"Mammee ba laifi na bane,kema kin san ba yanda za ai cikin hayyaci na na taba lafiyar Ummee, na je kama qofa dan na tsaya sosai kar na fadi Ummee ta zo da niyyar taimaka min na tsaya sosai, maida hannun nan nawa da zan na hada da kan ta na buga a gini, shi ne ta na farfadowa daga suman tsayen da tai ta shige dakin can ta kulle ta maida sakata"
Wata dariyar kowa ya sake ballewa da ita banda Mammee, nazari Mammee ta yi, ba me yi wa Aaseeyah wanka yau sai Ummee.
Ai kuwa bangaren Ummee ta je, ta bata hakurin abinda ya faru, sannan ta ce,
"Maman Noor na hada ruwan wankan, Ummu Suleim na can ita da Tasneem suna ma jarirai wanka shi ne na ce bari na sanar da ke na had'a na Aaseeyah"
Cikin dakewa Ummee ta ce,
"Anya zan iya mata wanka, baki ji kai na ba kamar ana luguden kab'aki a ciki, tsabar ciwo da saramin da yake,yanda kika san da gayya fa, haka yarinyar nan ta hademin kai da gini, ji kike quuuummm,duba nan, duba,duba ki ga yanda goshi na ya haye, na tabbata wannan malulu da shi zan koma lahira"
Hadiye dariya Mammee ta yi da kyar, sai da ta nisa sannan ta ce,
"Ai ina ganin be kamata kuwa ki zauna ta na azabtar da ke ba, na hada mata ruwan wanka, ya kamata ki je ki gasa ta da kyau"
Shiru Ummee ta yi na dan lokaci, cikin murmushin mugunta ta miqe,sai ta nemi bacin ran dake addabar zuciyar ta ta rasa,
"Ina zuwa, jeki gani nan, in ta san wata bata san wata ba dan uban ta Ibraheem,gani nan zuwa yanzunnan,bari na dakko tawul zata ci malafar uban ta yau a gidannan"
Mammee bata ce komai ba dan ta na tsoron tai magana dariya ta fita, kad'a kai kawai ta dinga yi, a haka ta bar bangaren Ummee zuwa na ta, ta na shiga kuwa ta dinga dariya kamar sabon kamu.
Labartawa Abee me ya faru ta yi, Abee ya ce,
"Anya kuwa a bar Aaseeyah da Fatima waje daya da ruwan zafi tafasasshe? Ki na ganin ba matsala?"
"To su yara ne da za su yi fada a gaban ruwan zanfin? Ai bar 'yar banza Maman Noor ta wanke ta, ka ga ta mata gashin da ni ban mata ba, ta fara jin magana daga yau"
Dariya sosai suke yi,a can bangaren Ummee kuma ta saka dogon wando da T-shirt,ta dora zani a saman wandon,ta dauki wani tawul mai mugun kauri ta fita bakin ta dauke da murmushi........
Himmmmm Ummee Allah ya bada sa'a ya kare hatsarin rayuwa....
TAUBASHI
PAGE 62
Ummee na murmushin mugunta, Aaseeyah na qunshe dariyar abinda ya faru da Ummee a goshi, a haka suka isa bayin,tunda Aaseeyah ta shiga ta ji ta fara zufa saboda tiririn ruwan hankalin ta ya soma tashi.
Saboda tsabar Ummee ta sawa ran ta ramuwar gayya ko zafin ruwan nan ba ta ji haka take jiqo towel dinnan ta yabawa Aaseeyah sai ta gantsare, tun Aaseeyah na jurewa kar ta koka a gaban Ummee,amma inaa, abun ya ci tura, fashewa ta yi da kuka mai tsanani jikin ta na rawa,cikin kukan ta ke magana,
"Ummeena na tuba, dan Allah ki sirka min ruwan nan, in ki ka ci gaba da samin ruwan nan hawan jini ze iya kama ni na mutu,dan Allah ki yafe min, na yi alqawari tsakani na da ke ba zan sake yin abinda zai cutar sa ke ba,"
"Ba ki tuba ba dan uban ki, alqawari tsakani na da ke? Ni za ki mayar ban san me nake ba Aaseeyah, yo tsakani na dake akwai wata amana ne da zan yarda ki alqawari a tsakanin mu? Inaaa, duqa a gasa baya da mara"
Yayibo towel Ummee ta sake yi za ta laftawa Aaseeyah, Aaseeyah ta goce ta yi yunqurin yarfawa Ummee, da sauri Ummee ta juya baya ya sauka akan rigar ta da zanin da ta daura,
"Ina kin ga halin ki? yau ko zaki ci malafar uban ki a hannu na, a shirye na zo, ai na san haka zata faru, duqa"
Da hannun ta ta danna Aaseeyah ta duqa, ta debo towel din ta yaba mata a baya, sai da ta gantsare, duk fatar ta ta yi jawur,ba abinda take sai kuka, da qarfi ta kwalla qara ta na kiran Mahboob, shi kuwa kusan tin da ta fara kuka,ya ke jin shi a kunnen shi da zuciyar shi, ga haushin su Yesmeen da ke kiran ta raguwa, shi ya san matar shi ba raguwa bace,jaruma ce, gashi ba ya son ya leqa Ummee ta zage mishi dangi tass,a dofane ya ke a kujera ya ji ta calla qara ta kira sunan shi, zumbur ya miqe ya na zare ido, ya na kallon qofar dakin, dariyar su Umaimah ce ta maida hankalin shi kan su, karaf ya ji Umaimah na fadin,
"....ai na fada maku muguwar raguwa ce Aaseeyah,Allah ne dai ya nu..."
"Akhrus! (Yi shiru!) in kk sake ce mata raguwa sai na bibbige ki, ke har kin isa ki kira ta raguwa, duba hannun ki, biyu fa ta haifa, haba Umaimah, ba zaki tausaya ma 'yar uwar ki ba,qanwar ki kuma,ashe baki da tausayi, ki na jiyo kukan ta fa, kin kuma san Ummee da gayya zata mata azaba da ruwan nan,....in ba zaki fadi alkhairi ba ki shiru,...tashi ma, miqawa Yesmeen yaran, leqa ki ga me ake mata...come on, stand up, je ki ga ni me ake mata"
"Yah Mahboob in Ummee ta ganni fa?"
"Ke wawuya ce da zaki bari ta gan ki, dan leqawa kawai zaki,"
Cikin tura baki ta miqawa Yesmeen ya ran, ta na ta jan jiki, qara Aaseeyah ta sake saki, ta na fadin,
"Ummeena na tuba, ba zan sake ba, na miki alqawari tsakani na da Allah, ya na gani na, inna sake maki wani abu mara kyau ki rama,dan Allah ki hakuri, Yah Mahboob sai na mutu za ka zo ka cece ni ko, Mammeee, wayyoo Abee na, fata ta ta sale"
Ai riqe riqe ne ya kaure tsakanin Mahboob da Umaimah, su na shiga dakin qofar bathroom suka tsaya, Aaseeyah na jin an shiga ta sake bare baki, Mahboob na lallashin ta,
"Na yi gayya ne? Ko goro na raba da na ji jama'a sun taru min a qofar bayi kamar a hawan idi? Kar na bude na ga kowa za ai ba dad'i dani"
"Amma Ummee in ruwan da zafi a dan sirka mana"
"Taho ka sirkan mara kunya, shigo zo ka sirka,"
Qoqarin bude qofar take, Umaimah ta bar dakin da sauri, shi ma fita ya yi, ran shi a matuqar bace, an yi na yau ya ga wanda zai mata wankan azabar nan gobe.
Ko da Ummee ta leqa ba ta ga kowa ba tai murmushi ta maida qofa, sannan ta ce,
"Ga saura nan, na ma ji ya huce, maza sa sabulun nan ki wanka me kyau, bari na je na juyo ruwan da zaki zauna a ciki, shi zan miki adalci zan dai saisaita miki, ko dan lafiyar ki ma"
Tura baki Aaseeyah ta yi, tare da kwararo da hawayen idanun ta, ji take kan ta na juyawa, tsabar azaba, ko hauka take ai ta gama da tsokanar Ummee a rayuwa, tunda mahaukaci ma ya san ciwo.
Ummee na kwashe ruwa ta na dariya, hannun ta ta kalla ta ga sun yi ja, ita ma ta sha azaba, amma ganin Aaseeyah cikin wahala ya fi mata dadi akan nata, yarinya ta maida ta kamar kakar ta?
"'Yannema tun da aka haife ta ban huta ba, haba,yarinya sekace wadda uwar ta tai wrestling kan a haife ta? Bata da aiki sai mugunta, yanzu ai nai maganin muguntar ta, in batai laushi ba kuwa har abada sai dai nai hakuri da abinda zai biyo baya"
Ruwan da aka tafasa kaninfari,bagaruwar mata, dan gishiri kadan,ta kwashe, ta dan diga musk kadan a ruwan ta dinga dagawa da cup ta na saisaita shi, har ya yi daidai zama. (Bagaruwar ba mai yawa ta sanya ba, 'yar kadan ta saka,domin in ta yi yawa itama ta na illa)
A bayi kuwa Aaseeyah ta kasa saka sabulu, ji take kamar ta sale,dan haka ruwan ta sirka tai ta kwarawa a jikin ta, Ummee na shiga da bokitin ruwan zafin bakin Aaseeyah ya fara rawa ta na son tai kuka,
"Ke ba zafi, zama zaki, saboda kar ki zauna a bud'e"
"Ummee ki wa Allah ki barni haka, na maki alqawari na tuba, ba zan sake ba, har na had'a kai na da Allah amma ki qi yarda"
"Ai na yarda da ke, kuma ni ma nai alqawari da Allah ba zan cutar da ke ba, wannan ruwan ya na da amfani, ko da kuka je likita bata ce ki na amfani da ruwan dumi ki zauna ba?"
"An fad'a"
"To kin gani, tab'a da hannun ki ki ji ba zafi, ai ba zan abinda zai cutar da ke ta nan ba, tashi kin ji Aaseeyahn Ummeeee"
Dan murmushi Aaseeyah ta yi, dan sai ta ji sunan wani banbarakwai, zama ta dan yi a ruwan, ta ji ba zafi yanda ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 41