ido Tasneem ta yi cikin murmushi da jan hanci, ta ce,
"Fine, zan baku labari na, amma you guys should promise me ba zaku sanar ma da kowa ba, bayan Hussein da ku ba na son kowa a gidan Jordan ya san tarihi na, can u do that for me?"
Cikin zumudi da son jin labarin ta suke amsa mata da sun yi alqawari ba mai ji bayan su, ba wanda za su sanarwa.
"Ok, ya isa ku daina zaquwa kamar labarin nawa wani abun dad'i ne,.........kamar yanda kuka sani ni marainiya ce, so zan baku labari a taqaice ba sai mun tsawaita ba, ni kadai ce wajen iyaye na kafin su rasu,Yayana da nake gidan shi kafin aure na,ba uwa daya uba daya muke da shi ba,Cousin dina ne d'an wan mahaifina ne, shi ma maraya ne kamar ni,ya girmen sosai, iyaye na ne suka riqe shi bayan nashi iyayen sun rasu, ni kuma da nawa suka rasu sai ya riqe ni a gidan shi.
A lokacin ba shi da aure muka fara zama daga ni sai shi,tun ina da shekara sha uku ya fara nuna min ya na son jiki na,amma bai kusancen ba, ya dai fara nunan alamun ya na so na, ya na yawan taba wasu sassa na jiki na,tun ina jin zafi har na daina jin zafi,na saba,ya so matuqa ya fara kwanciya da ni amma Allah bai bashi dama ba time din.
Watarana ina zaune ina karatu, ya dawo gida da rana, ina sauraren redio, ina sanye da doguwar riga da ya siyo min daga wata tafiya da ya tabayi Ghana, riga ce doguwa har ta na ja da qasa, ta kama jiki na ta kowanne lungu da saqo, ta na da hannun shimi, kai na ba dankwali, ban ji shigar shi dakin ba sai zaman shi a kusa da ni,a dan tsorace na tashi ina ware idanu, ya kalle ni cikin dariya ya ja ni na zauna a cinyar shi,ya ce min,
'Matsoraciya, ni ne ba dodo ba, ki na son ganin dodo ne?'
Cikin mamaki na kalle shi na ce,
'Yah Inuwa dama ana ganin dodo a gaske ba tatsuniya ba?'
'Ki na son ganin dodo ne?'
'Zan so ganin shi na ga irin muni da siffar tsoron da aka ce ya na da shi'
'Dik qarya ne,bari ki ga dodo, har ma ki yi wasa da shi, ba abinda zai miki,'
Kuka ne ya ci qarfin ta,sai da ta yi kuka sosai sannan ta ci gaba,
"In taqaice maku labari a ranar Yah Inuwa ya fara nuna min al'aurar shi,ya sani na kama da hannaye na, ya na gab da kwantar da ni a saman gado na muka ji buga qofa, a dan tsorace ya tashi ya maida wandon shi, ya gyaran riga ta, ya ce na maida wando na, sannan ya gargade ni kar na fada ma kowa abinda muke yi, sirri ne, inna fada ma mutane za a dinga zagi na a ce min 'yar iska, tun a sannan na san ba abu ne mai kyau ba,tunda har za a kira ni 'yar iska, to tambayar da na sanya wa raina ita ce, shi kuma fa? Ba shi ya koya min ba, shi me za a kira shi kenan?
Ina wannan tunanin na ji muryar maza, dattijai, guda uku, Baffanin mu ne suka zo daga qauye, suka ce za su tafi da ni, be kamata mu zauna daga ni sai shi ba, shi kuwa ya bada ma idanun shi toka ya ce ba mai tafiya da ni, shi ne dole na,shi ne ke da haqqin kula da ni,nan dai ya fara masu rashin kunya, ya na nuna masu ai su din zumuncin nesa gare mu da su, dan haka shi ya fi cancanta ya riqe ni,daga baya dai wani Baffan mu ya ce to in haka ne dole ya yi aure dan a samu mace da zata kula da tarbiyya ta, indai ba shi ke son aure na ba.
Ya ce ya ji zai yi aure, dan akwai wadda yake so, amma ba zai basu ni ba, haka suka koma ko gaishe su ya ce ba zan je ba, ya na tsoron kar na fita su dauke ni ta qarfi.
Ta window na hango su, sanda za su tafi,suma ta nan suka ganni, tsawa ya min akan na rufe labule na koma ciki, nan da nan kuwa na koma.
In taqaita maku labari kafin Yah Inuwa ya yi auren nan sai da ya sanni diya mace, sai da ya kusance ni har ban san sau nawa ba.
Ya yi aure lokacin na fara sanin ciwon kaina, matar shi na da dangi a gari sosai, so kusan ko da yaushe ta tafi suna, ta tafi biki, ta tafi ta'aziyya, ko ta je ganin gida, bata sati daya bata fita ba, ku a sati ma sai ta yi fita uku ko biyu,a dik fitar da zata yi sai Yah Inuwa ya neme ni.
Ina SS 3 na samu ciki ba zato ba tsammani,mun shiga tashin hankali ni da shi,ta yanda ko ruwa ba mu iya sha, tsoron mu kar matar shi ta gane,da week end ya dauke ni muka je wani private hospital,aka gwada ni, ciki wata uku, ya shiga na hudu ma, nan dai aka sa aka markade ciki, mace ce, namiji ne Allah shi ne mafi sani"
Ba Tasneem ba har Aaseeyah sai da ta koka Yesmeen kuwa dama ta jima ta na hawaye, ta tsani harkar fyade ko kuma irin wannan mummunar soyayyar ta Cousins.
"Yah Inuwa ya sa aka kwantar da ni a anan asibitin har na warke, na dawo hayyaci na na yi qiba, duk shi ke biyan kudin komai, ko da muka koma gida na yi mamakin irin tsarabar qauyen da na ga ya na fitarwa a mota, muna shiga Aunty na ta hau murna ta na ga mutanen Sakwaya,
' Ga mutanen Sakwaya,an je qauye an dawo,lallai ni ma zan je Sakwayan nan kin ga yanda kikai kyau?'
Yaqe na dinga yi, na hau fadin su na gaida ta, ta ce ta na ansawa, nan Yah Inuwa ya dinga fidda tsarabar su Daddawa, barkono, wake, kuka, kubewa, da kanwa, da tarkacen su aduwa,taura da dai abubuwa kala kala.
Wata na biyu da komawa ina hana shi kaina, qarshe da ya ga na qi yarda har lokacin zana jarabawar WAEC da NECO ya yi sai ya ce ba zai biya min kudi ba, qauye zai maida ni,dan ba zai ta kashen kudi a banza ba,hankali na ya tashi, musamman inna tuna qauyen mu duk zumuntar nesa muke da shi da su, shi kadai ne na kusa dani, kuma gaskiya ma dai na saba da birni, me zai maida ni qauye? A haka ya samu nasarar ci gaba da kusanta ta, har na shiga jami'a, na hadu da wayayyun maza da 'yan mata, anan na qara sanin darasin rayuwa, in ka na iskanci ka ga na wani sai tsoron Allah ya shige ka, na ci gaba da hulda da Yah Inuwa, amma kuma a wannan karon ba da son raina ba, sai dan kawai ya ci gaba da daukan nauyin karatu na,ta haka muka hadu da Hussein, ya na gani na ya ce da gani na 'yar hannu ce.
Na ce ya akai ya gane, budar bakin shi sai cewa ya yi,
'Ai mu maza da wahala mu ga macen da ake kwanciya da ita ba mu gane ba, shi ya sa mace mai kamun kai da wahala aje mata da kalmar iskanci sai dai aure, mace kuwa da muka san ta gama zubarwa a titi ita muke bi mu rage dare muma'
Kalaman shi sun sosa zuciya ta, ta yanda na ji na muzanta, na qasqanta,kuma na ji kunyar duniya da ta Allah, ashe kowa in ya kallen ya na gane me na ke yi? Nan da nan na fara kuka, ban san ya akai ba na ji na amince da shi a haduwar farko, har na sanar da shi abinda ke damuna.
Hussein ya tausaya min, amma ba yanda zai yi, a hankali muka fara soyayya ni da shi, kuma na yi dace Hussein na so na sosai, da na sanar wa da aunty na ita ta sa ni a gaba muka je wajen malamin ta aka qara ma Hussein so na da tsoro na.
Yah Inuwa ya so ya nuna qin aure na da Hussein Aunty na ta sake kai shi wajen malamin ta, aka rufe masa baki.
Daga baya kuma muka samu nasarar yin aure, shi ne dalilin da ya sa kuka ga na tashi ba wata cikakkiyar tarbiyya, ba dan ba na son zama ta gari ba, ah ah ban samu masu dora ni akan daidai bane, amma na godewa Allah da ya hada ni da ku, ina fatan Allah ya yafen laifuka na na baya, ya kiyashe ni da aikata abinda na bari a baya"
"Ameen Aunty Tasneem, a gaskiya kin ga sharrin Cousin a rayuwa,da zaki bani dama sai na maka Yayan nan naki qara a kotu, ya girbi abinda ya shuka"
"Hummm Aaseeyah kenan, ai wata shari'ar ki yarda sai a lahira kawai,domin ni hukuncin da alqali zai masa ba zai taba burge ni ba, ina son mai kowa mai komai ya hukunta min shi da kan shi"
"Kuma fa haka ne Tasneem, Aaseeyah ina ga maganar ta gaskiya ne, bar shi kawai, shi da Allah, azzalumi kawai"
Yanda Yesmeen ta fadi azzalumin ya basu dariya, dariya suka yi, suka tashi dan zuwa yin sallar la'asar.
****************************
Hutun qarshen shekarar nan da Mahboob ya samu, ba shi da tunani sai na ya dauki matar shi su zagaya ko da qasashe biyu ne, zuwa uku, su je yawon bude ido, ita kuwa Gimbiyar tashi, ta na nan ta na zabga girki, da gyaran gida, ta qayata gidan kamar a wani hamshaqin hotel,ko ina walwali yake da daukan ido,sanye take da riga kalar yellow mai santsi, da dan golden belt din ta,riga ce iya cinya,qasan mai fadi, ta riqe ta ta sama,hannun shimi gare ta,sai wani ado da akai da duwatsu masu haske,riga ce mai tsadar gaske, amma qanqantar ta ta sa naji haushin kudin da aka siye ta da su, sai dai ba komai kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa Mahboob na yin ido hudu da Kyakkyawar matar shi, jakar shi sai da ta subuce a hannun shi,gashin ta da ta daure a saman kai, ya na reto a bayan ta ta sa hannu ta kama ta na wasa da shi ta na murmushi.
Cikin takun yanga da sace zuciyar mai kallo take isa gaban Mahboob din, duqawa ta yi ta daga jakar laptop din da take kyautata tsammani in screen bai fashe ba to wani abu ya samu matsala a jikin ta.
A gujerar da ke kusa da su ta ajiye, ta juya dan tsokana za ta tafi ta bar shi a wajen, hannu ya sa ya ja ta jikin shi, ta saki wata qara mai dauke numfashi, sassanyar ajiyar zuciya ya sauke a dokin wuyan ta, tare da lumshe idanu, ya shaqi qamshin ta wanda ba ya gajiya da shaqa.
Hannun shi ya sa ya na shafa dantsen hannayen ta da suke a bude,kwantar da kan ta ta yi sosai a qirjin shi, cikin murya mai sanya nutsuwa ta ce,
"Rouhee sannu da dawowa,bismillah mu je mu zauna mun gaji da tsayuwa,"
Dan had'e girar shi ya yi kadan cikin rashin fahimta, sannan ya daga fuskar ta daga jikin shi ya na bin fuskar ta da kallo.
"Maadha ta'anee kun gaji? Ke da wa? Ni ai ban gaji ba, ta ina zan gaji ki na a hannu na?"
"Ina nufin ni da...."
Hannun ta ta dauka ta dora saman marar ta da ke a shafe kamar ba komai.
Sake hade gira ya yi cikin rashin fahimta, tura baki ta yi, dan ita duk wannan shirin dama na masa albishir ne,kuma ita ba zata iya furtawa ba, in dai be gane ba sai dai tai ta masa kwatance, ko kuma ya bari sanda ya girma ya gani.
Dan ture hannun shi ta yi cikin tafiyar shagwaba ta zauna a saman kujerar dinning table, ta hade hannayen ta a qasan marar ta, ta yi alamar ta tallabo cikin da bai girma ba, ta na murmushin jin kunya, ware ido Mahboob ya yi da bude baki cikin dariyar farin ciki, nuna ta ya yi sannan ya sanya hannun shi shima biyu a ciki ya na juya su alamar ya dau yaro ya na jijjigawa, daga masa kai ta yi ta na dariya, dafe kan shi ya yi da hannu biyu, idanun shi sun cika da kwallar farin ciki, da dan gudu gudu ta isa gare shi ya wara hannayen shi ya daga ta sama , ya hau juyawa da ita, murna suke ta yi tare da godewa Allah, zaunar da su ya yi a kujera sannan ya ce,
"Ya akai ki ka sani?"
"Baka kula cewa yanzu wata na biyu ban period ba? To shi ne hankali na ya tashi nake sanar ma da Mammee sai ta ce na je asibiti,naga alamar fuskar ta dauke da annuri,na rasa dalili, sai da na je dazu aka tabbatar da ina dauke da cikin sati biyar"
"Ya Allah, Alhamdu lilLAAH, wannan shi ne kyakkyawan labari na biyu da na ji a rayuwa ta ta duniya"
"Wanne ne na farkon?"
Kissing wuyan ta ya yi sannan ya kai ga bakin ta, sun jima a haka kafin ya ce,
"Ranar da aka ce an ban ke ni za a aura wa ke, ban taba jin labari mai dadin wannan ba, sai yau kuma da na ji za a samar min magajin Mahaifana, ko mace ko namiji sunan Babana da Mama ta zamu saka, kin amince?"
"Kwarai da gaske, ina jin ma na riga ka yanke wannan hukuncin"
Gyara mata zama ya yi a jikin shi, sannan ya zame band din da ta daure gashin ta da shi, ya fara yamutsa mata shi, hannun shi ta doke ta na masifa, sumbatar hannun nata ya yi ya na dariya ya ce,
"Yanzu kin ga yau na samu hutu, ina so ki fadi duk qasar da kike so mu je mu qarasa hutun mu a can, ko kuma a Nigeria in akwai wajen da kike son zuwa ki sanar da ni,"
Cikin murna irin ta yaran da aka bawa sweet ta ce,
"Yeeeeehhhhh,Yah Mahboob ina son zuwa Yankari, na san kai ma baka taba zuwa ba, ina so na je plsss,saboda wata 'yar ajin mu 'yar bauchi ce da muna BUK ta na yawan bamu labarin wajen, sun je da mijin ta, har da hotunan da suka yi na gani,"
"An gama, sai ina?"
Shiru ta yi ta na tunani.......
Makaranta ku bama Aaseeyah shawara ina da ina ya kamata su je shaqatawa Honeymoon??
TAUBASHI
PAGE 58
Shiru ta yi ta na nazarin ina da ina take mafarkin zuwa a rayuwar ta,
"Ka ga dai da fari ina matuqar son na ga na je makka, na yi ibada,na ganni gani ga dakin Allah, (Allah ka mana arziqin zuwa dakin ka ameen) sannan na biyu ina son mu je US, mu sauka a New York, akwai parks da wuraren zuwa na shaqatawa masu kyau an ce,daga nan ina so in kai ma Sister Ramlat ziyara , to zabin na ukun ina son ka bani mamaki ka zabar min da kan ka"
"Da gaske kin bani zabin qasa ta uku da kk son zuwa? Za kuwa ki gode min,"
"Really?"
"Da gaske,"
"To Allah ya nuna mana, yanzu muje ka ci abinci sai ka yi wanka,mu kwanta akwai gajiya a tare da kai da ganin idon ka, gashi na qara maka wata, tashi mu je"
"Ok mu je, amma fa in mun je qasashen nan ba za mu jima ba,saboda hutun ba wani mai yawa bane sosai, ga naki aikin kema"
"Ba komai, ni dai kawai fata na na dan fi jimawa a saudiyya in da hali"
"An gama, duk abinda ki ke so shi za ai"
Jagora ta mishi zuwa wajen cin abincin, hannayen su na sarqafe da na junan su, sai da ya fara zama ta zauna, plate ne a rufe da wani plate din a gaban shi,kafe shi ta yi da ido, ta na murmushi, sannan ta masa nuni da hannun ta alamar ya bude ya ci abinci, budewa kuwa ya yi, ya yi ido biyu d hoton scanning da aka mata,dariyar farin ciki ya fashe da ita, idanun shi har da wata 'yar kwalla, sai kyalli suke.
"Dama na zaci ba zan iya maka magana ba, shi ya sa na ajiye hoton,"
Tashi ya yi tsaye bayan ya gama kallon hoton, ya durqusa a gaban ta, hannayen ta ya kama sannan ya hada goshin shi da nata, ya na murmushi,itan ma murmushi take, cikin murya mai sanyi ya ce,
"Ina son ki Aaseeyah,ke ce babban farin cikin rayuwa ta,ke ce rayuwa ta gaba dayan ta,Allah ya bani ikon kulawa da ke da kare maki mutuncin ki,Allah kar ya kawo ranar da zan bata maki rai ko da da gangan ne, in na bata maki rai Allah ya bani ikon ninninka faranciki a ran naki ya mantar da ke bacin ran da na sa maki"
"Yah Mahboob son da nake maka ya fi wanda ka ke min yawa, ba zaka taba bata rai na ba, indai ba sabon Allah ka yi ba,wanda ba na fatan hakan,so ka ma daina kiran bacin rai,tashi mu ci abinci"
"Habaa Maman biyu, ba d'an wani abu da zan samu a wajen ki kawai sai ki ce na tashi, haka ake?"
Murmushi ta yi a saman labban shi, sannan ta bashi kiss guda uku,
"Ga shi nan na baka wani abu,"
"Dan qara min mana"
"Nooo yara sun ce shari'an Allah uku ce, dan haka ba zan qara maka komai ba tashi, yunwa nake ji fa"
Da sauri ya miqe suka fara cin abinci, sai santi ya ke zubawa ta na ta dariya, dariyar ta kamar busar sarewa ce a kunnen shi, in ta na dariya bacewa ya ke ya shagala da kallon ta, sai ta tab'a shi sannan yake dawowa hayyacin shi, (su oo dan Allah a dinga dariya me kyau a gaban oga, kar a firgita masa lissahi,duk da dai ba kowanne lokaci bane zaki ta yanga agaban me gida, watarana dole ne ki sake jiki ki yi duk yarinta da shiriritar da kk ga dama gaban me gida, amma akwai lokacin da in kuna cikin shauqin soyayya da tarairayar juna ba a so ki bata moment din da shiririta, ki shagwabe ki maqale murya, dariyar ma ki irin ta 'yan gayu😂).
Ranar Aaseeyah ta ga kalar soyayyar da bata taba gani ba a wajen Mahboob, shi ma a na shi bangaren ji yake tunda suke ba ta taba gwada masa kalar soyayyar nan ba.
Washegari ya tashi da fara masu shirye shiryen tafiya, duk wani abu da take buqata sun je sun siya, sun fara sallama da mutanen gida,Mammee farin cikin samun cikin Aaseeyah bai boyu a fuskar ta ba, kamar a lokacin ne zata fara samun jika.
Ranar da za su tafi US kuwa Noor ne ya kai su Airport,Aaseeyah ba su rabu da Tasneem da Yesmeen ba sai da suka cika ta da lissafin abubuwan da suke son ta kawo masu in ta je,qarshe da ta ji abubuwan sun yi yawa cikin tsokana ta ce,
"Kyaun ta wannan ku samu takarda da biro kowa ta rubuta me zan siyo mata"
Dariya sukai suka hau rungumar junan su cike da jin kewa tun kan a rabu ma.
Har a cikin jirgi ba ta daina zancen Tasneem da Yesmeen ba, Mahboob kuwa bai gaji da sauraron labarin da in hadda ne ya ci a ce ya hadda ce by now.
Bayan doguwar tafiya a sararin samaniya suka samu isa US,already ya samar masu hotel din da za su zauna dake kusa da Liberty international Airport, mai suna Crosby street hotel.
Suna shiga dakin da suka sauka, ta fara cire takalmi, ta yarda hand bag din ta a qasa,sannan ta tafi da gudu ta haye saman gadon ta na tsalle, Mahboob ne ya riqe ta da sauri, ya na mata magana cikin lallashi ,
"Maman biyu plss yi hakuri da tsallan nan, ajiya ta kar ta samu matsala kin ji, a yi hakuri a yi murnar a zaune"
Dan tura baki ta yi sannan ta zauna, kafin ya bude baki ya yi magana ta zabura ta dauki wayar ta,jan shi ta yi ta hau daukan su hotuna, ba abinda Mahboob yake banda dariyar yarintar ta da ta bayyana a yau,murnar da take kamar ta qaramin yaron da aka bawa alawa.
Sai da suka kwana uku su na shan soyayyar su, daga daki sai wajen cin abinci suke fita, daga sun gama cin abinci su dan zazzaga su ga wajen sosai sai su koma daki,kishi ke damun Aaseeyah shi kuma ke hana su yawo, ko ta ina ta gilma sai ta ga mata kusan tsirara,abun na mata ciwo, watarana sun dawo daga cin abinci wata baturiya ta qurawa Mahboob ido, ta kasa jurewa sai da ta isa gaban shi, ta ce mishi ya na da kyau, hannu ta kai zata shafi fuskar shi Aaseeyah ta tsaya a gaban ta,fuskar ta na nuna ki na taba shi zan yanke maki hannu.
A tsorace baturiya ta bar wajen, ta koma can nesa da su kusa da pool ta tsaya, wucewa suka je yi dan komawa dakin su, Aaseeyah ta faki ido ta wurga matar nan cikin ruwa.
Ta na wurga ta ta saqale hannun ta cikin na Mahboob ta na murmushi suka tafi, matar na ta ihu ta na zagin Aaseeyah da turanci.
"Shegiya nunar rana, kin zagi banza dan ba yare na bane, sa'a ma kikai na yi makaranta, Allah na tuba da ban makaranta ba ba sai dai ki ta haushi ban gane komai ba, duk wadda ta rabi miji na ta na tare da wahala kuwa"
Mahboob shi dai ba abinda yake banda dariya, sai da suka koma dakin ne ya kula da fuskar gimbiyar ta shi,
"Mar'atee lafiya?"
Banza ta yi da shi, ta cire kayan ta ta sanya na bacci ta haye gado, ta rufu har kan ta, lallashin ta Mahboob ya fara, amma sai da ya gwammace baccin ya bar ta ta yi, da kuka ta bude fuskar ta, hawaye kamar wadda aka ci zali,
"Kar ka sake taba ni, ka tafi wajen baturiya me farar fata, ni gobe ma zan tafi gidan Sis Ramlat, da na gan ta na ga yarana zan tafi na barka a wajen turawan, tunda ka fi son turawa"
Wani irin muskutawa ta hau yi irin na masu fushi, ta sake komawa bargon, kuka take da qarfi muryar ta na fita kamar wadda aka daka,dariyar da ke cin shi dole ya gimtse ya dinga lallashin ta,
"Haba Aaseeyahn Mammee, yanzu ke in aka ce ma zan so baturiya ai kin qaryata, saboda ba kala ta bane su,ga kala ta nan a gabana, bayan ke ba wata mace da ta ke dauke da kalar da nake so a duniya kaf,kalar ki ce kadai ke dauke hankali na har na ji ina son na kasance da ita har qarshen rayuwa ta, yanzu in banda abin ki dan Allah me zan da waccan nunar ranar, ki na ganin fuskar ta duk sun burn"
Bude kan ta ta yi ta sake bare baki da kuka,
"Wato har ka ma kalli fuskar ta ka ga sun burn? To ni ban gani ba, kai da ka gani se ka je ka kai mata magani ta shafa"
Kasa iya riqe dariyar shi ya yi, ya fashe da dariya, me ze yi ya lallashe ta ne? Ihun kuka ta sa mishi ta fada jikin shi ta na ta tirje tirje, duk ta yarda pillows da ke saman gadon, sai shagwaba take, gaba daya ta birkita masa nutsuwar shi da shagwabar ta, wata iriyar runguma ya mata, wadda ta ji ta har cikin ran ta,tasirin rungumar ne ya sanya ta yin shiru, da hannun shi na dama ya dinga goge mata hawayen da ke zuba, sai da ya gama kissing din ta cikin murya mai nuna tsantsan son ta ya ce,
"Aaseeyah bayan Allah da Annabawa da mazannin sa sahabban Annabin mu, sannan iyaye na, ke ce mace ta farko da ta samu wajen da har duniya ta tashi ba wadda zata samu wannan wajen, ke in taqaita maki ko yaran da za mu haifa ba za su samu matsayi da soyayya ta ba kamar yanda na ke son ki,Aaseeyah kalamai na min kadan in zan bayyana soyayyar ki, sai na ji ita kan ta kalmar so din ta yi qanqanta na danganta ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 41