su na da alaqa da Saratun, hummm lallai zai ga tashin hankali, sai dai ya sake ni ya aure ta, amma ba zan taba raba shi da wata ba'
Shin hukuncin Aarcee ya yi daidai kuwa????
TAUBASHI
PAGE 41
Mahboob bai sake ganin Aaseeyah ba sai ranar Monday, duk kuwa iyakar qoqarin shi na ganin sun hadu, kwana d'aya amma ji ya ke kamar ya yi kwanaki bai gan ta ba,ranar Mondayn da sassafe ya shirya ya zauna a parlour, ya na karyawa ya na kallon qofa, ya kusan kammalawa ta fito, cikin shirin ta na zuwa makaranta, hijabi ta sanya tun daga sama har qasa, ta dakko niqabi ta buga, banda idanun ta ba abinda mutum ke iya gani, dan mugunta ta na fita waje ta buga baqin sun glasses, abun ma dariya ya so bama Mahboob, wato shi ake wa wannan shigr ninja din,ba komai, indai za ta zauna a motar shi na mintunan da za su isa makarantar ai ba damuwa.
Ko gama cin abincin bai ba ya bi ta, Mammee na ta fad'a, ta ce,
"Ai ba fa zai dauki shawarar mu ba, sai ka yi indai mace ce, dan ka na son ta ka ke mata rawar jiki haka, gaba ba zata tankwasu ba kuwa"
Sun fara tafiya ya ji shirun ya yi yawa, cikin muryar shi mai dadin sauraro,ya ce,
"Yanzu ko gaisuwa babu? Babu sallama? Habaa Aaseeyah mu fa musulmai ne"
"Assalamu alaikum"
"Wa'alaikumussalaaammm Mar'atee"
Cire glass din ta yi suka hada ido, madadin ya ji haushin harar da take zuba masa, sai ya sa hannu ya dafe saitin zuciyar shi,
"Kaiii Mahboobatee kar ki qarasa gawar da ba taki ba fa, irin wannan kallon soyayya haka"
Dage niqab din ta yi dan in ma baiga harara take ba ya gani da kyau,murgada masa baki da fari da ido ta yi da kyau,sannan ta maida kanta gefe,
"Masha'Allah, a gaskiya tunda nake bantaba ganin mace kyakkyawa kamar ki ba Aaseeyahn Mammee,gaskiya na yi dacen mata na kuma godewa Allah da ya bani ke mace tamkar da ba adadi,Allah ya ninninkamin son ki a raina Ya mar'atee"
Aikuwa ta na jin addu'ar ninkuwar so tai katsal ta ce,
"Ameen"
Da sauri ya kalle ta suka hada ido ta na waro nata cike da jin kunya, habaa me Mahboob zai yi in ba dariya ba,su na tsaka da dariya wayar shi ta dau ringing, a daidai lokacin ya na qoqarin shiga gate din makarantar su Aaseeyah.
"Assalamu alaikum,......ok gani nan zuwa yanzun nan,kun fito?...ok gani nan, da na ajiye ta zan zo,a yi hakuri na bata lokaci....to gani nan"
Dariyar da ta dan fara yi ta gimtse, sai da ta sanya qafar ta a waje ta ajiye masa glass din nata da niqab din, sannan ta ce,
"Dama.na san ba zaka sauya ba,laifi na ne da na yarda da kai,har na saki jiki komai ya wuce"
Kwallar da ke idon ta ta mayar, ta fice tare da doka masa murfin qofar kamar zata karya ta, cikin gudu-gudu sauri-sauri ta shige ta bar shi tsaye a wajen ya na kiran ta.
"Aaseeyah kenan,ba komai,ni dai na san ba abinda na ke aikatawa mara kyau, wanda ma nai a baya ina neman Allah ya gafarta min"
Tada motar shi ya yi,ya nufi inda za shi.
*****************************
Da yamma ya je daukan Aaseeyah ya samu labari cewar ta wuce, bai ji haushi ba shima ya tafi gidan, ko da ya je bai tarar da Mammee ba, sun tafi asibiti ita da su Umaimah da Ummee duba Yesmeen da ke fama da lulayi.
Zaune take cikin riga da skirt na bature,rigar mai dogon hannu da dogon wuyan da ya rufe wuyan ta baki daya, sai skirt din da ya bi jikin ta ya fidda shape din ta sosai, kan ta sanye da hula kalar skirt din ta, ta duqufa ta na karatu ya bude qofar dakin, da sauri ta daga kan ta sukai ido biyu, nan da nan ta daure fuska, maida qofar ya yi ya rufe,
"Meye haka ka ke yi? Ka fitar min a daki kafin su Mammee su dawo su gan ka a daki na"
"To sai me? Miji ba zai ziyarci matar shi ba, ko kuma mammeen ce ta ce kar ki barni na shiga dakin ki? In ita ce sai na tafi saboda bin umarnin ta,in ra'ayin ki ne hakan sai ki hakuri dan ba inda zani,....kinga yunwa ma nake ji, kawon abinci na nan"
Wani mugun kallo ta sake mishi, guy dinnan ya fa fara kai ta wuya,ya samu ta kyale shi ko? Bari,
"Zan baka abinci, amma fa sai dai ka koma parlour, dan ba na cin abinci a daki"
Tashi ta yi, shi ma ya bi bayan ta, kallon yanda shape din ta ya fita a cikin kayan ya ke,
'Lokaci fa ya yi da za a mallaka min mata ta a hannu, haba, ai na yi qoqari'
Gani ta yi har ta shiga kitchen ya na biye da ita, juyawa ta yi ta kalle shi,cikin daure fuska ta ce,
"Koma can ka jira ni mana"
Ba musu ya fita, ya na leqen ta, har ya bace ma ganin ta, dan tsallen murna ta yi, sannan ta ce,
"Naga alama duwais din ka bai horu ba, bari na saka zawon sati yanda ko hanyar gidan su Saratun sai ka manta"
Dudduba magungunan ta fara ta ga bata ga na sanya tutu ba, haushi ne ya kama ta, ta fara zuba masa abincin ta na qunquni, har ta gama zuba komai, ta yi tunani, robar yaji ta dakko, ta debi cokali daya ta zuba a miyar,ta juya,sannan ta dauka dan kai masa,
"Yanda ka sa qirji na suya kaima sai duwais din ka ya qone yau"
Ajiye wa ta yi ta samu gefe ta zauna, ko ruwan sha bata hado da shi ba, ta miqe qafafu a saman kujera ta na kallo, amma gaba daya hankalin ta na gare shi, sai zuba surutu yake, abincin ya kai bakin shi, ya ji yaji zauuuu, da sauri ya duba table din ya ga ba ruwa, shiru ya yi ya ci gaba da ci, da kyar ya ke dannawa.
Jin shirun nashi ya yi yawa ba tare da ya koka akan yajin bane ya sa Aaseeyah kallon shi,gani ta yi idanun shi sun yi jawur,hancin shi na yoyo, ya na ta gogewa da tissue da ke saman qaramin table din.
Dariya ce ta kama ta amma ta dake,har cikin ran shi ya zaci ko bata sani bane yajin ya zarce mata, shi kuwa ba namiji bane mai nuna wa mace matsalar girkin ta, duk yanda aka bashi zai ci, musamman da ya san ba haka aka saba ba.
Ya ci rabin abincin ya kalle ta cikin jajircewa ya ce,
"Aaseeyahn Mammee kin manta da ruwan sha"
Miqewa ta yi ta nufi kitchen,ta na shiga ta dinga sheqa dariya qasa qasa, har da kama ciki, in ta tuno yanda ya ke sakin lebe ga hawaye na qoqarin zuba sai ta sake tintsira dariya, sai da ta yi mai isar ta, ta bata mashi lokaci, sannan ta kai ruwan, ko cup din bai tsaya amfani da shi ba, ya bude murfin ya kafa kai, bai aje ba sai da ya qare.
Ya na gama sha, ya ji cikin shi na juyawa, irin juyin nan mai azabar zafi da ciwo irin na gudawar yaji, nan da nan kuwa zufa ta fara karyo masa, da kyar ya ke bude ido, irin gudawar nan in ta murda har numfashin ka ji zakai ya na ma wahalar shaqa.
Sai da ya lafa ya miqe ya na share zufa ya ce,
"Mar'atee bari na je na dan yi wanka na huta, anjima akwai inda za ni"
Cikin dariyar da ta kasa riqewa ta ce,
"To sai ka dawo, in ka je ka ce ina gaishe ta"
"Za ta ji, bari na je nai wanka na huta kafin anjima"
Bai jira ta cewar ta ba ya fice, dan gaf yake da son shiga bayi.
"Lallai ma Yah Mahboob din nan, da gaske fa yake wajen ta zai tafi, hankalin shi kuma kwance ya ke fadin zai miqa gaisuwa ta,ba komai,ai na ga yanda za ai ka je, in dai kuma ba toilete din su zaka shiga ba in ka je"
Kwafa ta yi ta shige daki, karatun ma ya daina shiga,
'Wataqila ya na can ya fitar da kayan da zai saka dan yi mata gayu,...ah ah, wataqila wanka yake....anyaa, da dikkan alamu ya na can ya na zazzage ciki'
Gani ta yi tunanin b inda zai kai ta, ta miqe ta sanya hijabin ta madaidaici, ta fita, zagaya wa ta yi ta bayan d'akuna, da nufin ta je windon dakin shi ta ga me yake, ta na gilmawa ta windon bayin shi ta ji qarar gudawar shi,a wajen ta baje ta na dariya,
Dariya take har da hawaye,ta na ji ya fita daga bayin ta koma windon dakin shi, nan ta gama dube duben ta ba ta gan shi ba, zagayawa ta yi ta gaba, ta leqa parlour, kwance yake rufda ciki a kujera, sai murqususu yake, dariya ta dinga yi,
"Dan Allah ba wajen Saratu ba ka tafi wajen Adama,dan rainin hankali"
Cike da nishadi ta wuce dakin ta, ko da su Mammee suka dawo an kusan magariba,da Mammee na sanar da ita Yesmeen na da ciki ta hau murna, da hamdala,tare da addu'ar Allah ya inganta,
"Da dikkan alamu matar Hussein ma ciki gare ta, dan mun hadu da ita ta ce ya siyo mata yalo ba a samu ba ke kin ga kuka? Yanda kk san wata yarinya, ko kunya ta bata ji ba, haka ta dinga saka yaron nan wahala a asibiti, ai kuwa Umaimah ta ce Aunty Tasneem kema a baki gado kawai, sai da na kwabi Umaimah amma ta so ta mata rashin kunya"
"Ai Mammee da kin barta ta mata tatas, kwata kwata matar nan haushi take bani, ta maida shi yanda kk san d'anta, ashe girki wannan bata iya ba kullum in Yesmeen bata zuba masu ba gidan yayan ta take wuni ta ci, shi kuma sai dai ya je ya siya,tunda kin hana shi zuwa cin abinci nan,duk a wajen Yesmeen nake samun labarin ta,ga baqar qazanta, waje d'aya yake morar ta wajen gayu,"
"Gayun banza, ai dai shi ya ga zai iya, Allah ya shirya ta ya basu zaman lafiya, Allah ya sauke su lfy dika, Allah ya gyara mata halayen ta ko sun ji dadin zama"
"Ameen, amma Mammee irin matar nan gyara mata zama ya kamata a samu a yi, dan ko nasiha ba ta dauka"
"Uhumm uhumm, ban saki ba, kin san Allah, kar na ji labarin kin je gidannan ma, in dai ba da ni ba, kar na ji labari, na san halin ki Aaseeyah, ban aike ki gyara matar mutane ba, ke kan ki mijin ki fama yake da shegen fushin ki, kike qoqarin gyara wasu"
Nan da nan ta ji dariya ta kawo mata, ai kuwa ta kece da dariya,
"Mammee ba laifi na bane, ki tambye shi me ya min, yau ma ba dan na dau mataki ba da tuni ina nan cikin qunci, amma yau ya na gida ba inda zashi,"
Cikin qanqance ido Mammee ta ce,
"Me ki ka masa? Kin san Allah na ji kyas kin mishi shirmen ki sai na daka ki, bar ganin ina kyale ki, girman da kikai ne ya sa na ke daga maki qafa, amma in baki san kin girma ba zan koya maki hankali nima"
Cikin dariya ta ce,
"Ki tambaye shi, ni in banda abinci da na kai masa ya ganni ne ma?"
Mammee ce ta tashi za ta shige dakin ta ta ce,
"Kar ki zaci ban gane me kika masa ba rannan, na san komai, ki kiyaye ni dai na ke fada maki, in ba haka ba nima zan ari iya shegen naki na hukunta ki da shi"
Mamme na shigewa daki Aaseeyah ta ce,
"Tooo zan kuwa fara kula ko ruwa kk ban ba zan sha ba, sai dai na debi nawa,"
Ummee ce ta shigo a kidime, ta na fadin,
"Aaseeyah ku na da maganin tsaida gudawa kuwa? Dan Allah in akwai maza ki dakkon, Mahboob ba lafiya,"
Cikin nuna damuwar qarya ta tashi, ta shiga kitchen, ta yi tsayuwar ta,daga baya ta koma ta ce babu, fita Ummee ta yi ta aiki.mai gadi ya siyo mata magani.
Aaseeyah bata so hakan ba, Ummee sai sintiri take tsakanin sashen Mahboob da nata.
Kuka Aaseeyah ta kada a cup, ta nufi dakin Mahboob din,dan ta ji an ce ta na maganin zawo, kuma ma dai Mahboob ya tsani kuka, ta na zuwa ta miqa masa, ta ce,
"Anshi Ummee ta ce a kawo maka maganin zawo, bamu da na bature sai na gargajiya,"
A wahale ya miqa hannu ya karva,ya na dubawa ya ga yauqi yauqi, kallon ta ya yi, ya ga ba wasa,
"In baka sha ban na koma da shi, ina da abin yi, dan ko sallah ban ba da ka ganni nan"
Ba musu ya sa ya fara sha, Aaseeyah na sane da cewa ya tsani kuka, dan haka kafe shi ta yi da ido ta na riqe dariya.
Wani irin yunqurin amai ya dinga yi, ta miqa masa ruwa, kasa sha ya yi, ya kalle ta, ya ga yanda ta hade girar sama da ta qasa,
"Aaseeyah anya ki na so na kuwa yanzu? Ke ce fa sanadin shiga ta wannan halin amma ko tausayi na baki ji kk ta dauren fuska, ba wai ina maki mitar abincin ya yi yaji da yawa bane, ah ah na san baki sani ba kema, amma dan Allah gaba ki na kula da saka yaji a abinci"
Ta kasa riqe dariyar ta, nan ta kwanta ta na ta tintsira dariya, har da hawaye, kallon ta ya yi, ya yi.murmushi,
"Meye abin dariya, ke fa dariya va ta maki wahala in kin so"
"Wai kana fama da kan ka, amma ta daure fuska ta ka ke, in banda kai, ka ji da tsuu din ka mana, ina ruwan ka da fara'a ta?"
"Yanzu da kika yi dariyar ba ga shi na.ji dadi ba"
"Dan baka san ma'anar dariyar tawa bane"
"Meye ma'anar ta?"
"Basshi kawai, bari na je nai sallah"
"Ok ni ma bari na qoqarta na tashi"
"Ammmm...na ce da qarfe nawa zaka gidan su Saratun?"
"Ai yau kam ba inda zani,baki ga banda lafiya ba"
Cikin dariya Aaseeyah ta bar wajen, ta na ayyanawa a ran ta,
'Da ka tafi mana, dan rainin hankali, na daina kuka, sai dai duwais din ka ya gaya maka,'
Ta na shiga ta yi sallah ta yi azkar ta ci gaba da karatun ta zuwa isha'i ta yi sallar isha'i ta kwanta.
Mahboob na ta mamakin dariyar da take ta yi, da tunanin yawan tambayar shi akan saratu da take yau.
Wayar shi ce tai qara, ya daga cikin muryar marasa lafiy masu fama da qarancin ruwa a jikin su Mahboob ke magana,
"Kaiiii yau ba na jin zan iya fitowa, ba ni da lafiya,......ok to inshaa Allah na ji sauqi zan zo....ok bye"
Ajiye wayar ya yi ya lallaba ya je ya yi alwala ya yi sallah.
Ko da aka kawo magani Ummee over dose ta masa, dan ta ji tsoron yanda in ya shiga sai dai kaji shaaaa ruwa na zuba.
Ya na gama sha, ya samu ya kishingida, Umaimah da Noor sun shiga suma duba shi, nan suka dinga hira, ba abinda yake sai kallon hanya, ko Aaseeyah zata shiga, amma shiru.
Mammee na can ba ta san me ke faruwa ba, ta n zuba ido ta ga Mahboob ya je gaishe ta shiru,a haka har ta gama aikin da za ta yi, ta shige.
Abee da Abbu na dawowa Noor ya sanar da su Mahboob fa yau ma ba lfiya.
Sai da suka duba shi sannan suk nifi sashen su, a sannan ne Mammee ke sanin me ya faru.
Ai kuwa dakin Aaseeyah ta shiga, ta same ta ta bingire da bacci,dasa mata duka ta yi a kafada ta kuwa tashi a firgice, ta na zare ido,
"Me kk saka mishi yau kuma? Dan na san last time da ya yi irin wannan maganin nan da na ke baki in kin kasa kashi kk bashi,na kuma debe su, ina kk samu wani?"
Kawai yarinyar nan sai ta saka kuka.
"Yanzu Mammee me zai saka ni bashi baganin kashi shi bai ce min ya na da matsalar kashi ba"
Yanda take kuka ba dan Mammee ce mahaifiyar ta ba ta san halin ta, tabbas dole mutum ya yarda bata da hannu a lamarin.
Abee ne ya shiga dakin dan jin muryar Mammee na tashi, abinda ba halin ta ba,
"Lafiya? Me ke faruwa?"
Zayyana masa komai ta yi, amma da ya kalli Aaseeyah sai ya ji tausayin ta ya kama shi,da alama bata da hannu a lamarin,
"Kinga Subai'a, mu bar wannan maganar muje ki duba shi dare na yi, ke da kan ki kika ce kin kwashe maganin to ta ya ta samu wani? Kinga kenan na farkon ma ba ita bace ko?"
"Hummm ba ka san halin Aaseeyah bane, ni da nake zaune da ita ni na san wace ce"
"To ki yi hakuri mu je ki gan shi,"
Su na fita Aaseeyah ta goge hawayen ta,
"Ai sai dai ki daken Mammee amma yanda ya sani kuka shi ma sai ya ji a jikin shi"
Kwanciyar ta ta gyara, ta rufe ido ta na murmushi.
****************************
A kwanaki uku da Mahboob ya dauka ba tare da ya fita ba, Aaseeyah da kan ta take zuwa makaranta ta dawo da kan ta, yaran AIG Aliyyu na kula da ita ba tare da sanin ta ba kamar ko da yaushe.
A kwana na hudu, Mahboob ya murmure, sai ido da ya fada masa, ya shirya da yamma ya nufi gidan su Eliza, su na tsaka da hira wayar shi ta yi qara, ko da ya duba sai bai amsa ba,ya ce ma Eliza bari ya je ya shigo da baqo.
Ta na nan zaune kamar ta Allah, da doguwar riga ta yafa mayafin rigar, suka dawo shi da AIG Aliyyu, da dan sanda mai take masa baya, su na had'a ido da Aliyyu jikin ta ya dau rawa, bakin ta har karkarwa ya ke, ta miqe a tsorace ta na nuna shi ta ce,
"Mahboob me wannan ya ke a gidannan?"
"Kin san shi ne???????????
TAUBASHI
PAGE 42
Wayancewa ta fara yi, tare da qoqarin maida damuwar da ta shiga, cikin yaqe ta ke fadin,
"Ahhh waye bai san AIG Aliyyu ba? Ai indai ka na garin Kano da kewaye ba zaka rasa sanin jarumtar shi da jajircewar shi ba wajen taimakon qasar shi,ina yawan ganin labarai, da shirye shiryen da ake gabatarwa a gidajen talabijin"
Murmushi Aliyyu ya yi, cikin jin dad'i ya samu wajen da ta nuna masa ya zauna, da hannu ya yi ma d'an sandan da ke tare da shi, alamar ya jira shi a waje, qamewa ya yi sannan ya fita ya tsaya a bakin parlourn.
Gaishe shi ta yi cikin girmamawa da jin kunyar shi, hakan ba qaramin nutsuwa da ita ya sanya ma Aliyyu ba, ya na son mace mai kunya da nutsuwa.
In abun nan ya tabbata ba shi da abinda zai biya Mahboob da shi.
Izini ta dauka wajen su ta ce ta na zuwa, tashi ta yi dan shiga ciki, idanun su gaba daya a kan ta suka zuba su, duk da rigar da ta sanya bai hana su ganin kyakkyawan shape din ta ba.
Hannu suka.miqawa juna tare da tafawa,
"Lallai Mahboob ka iya zabe, ka zabo Aaseeyah a cikin mata, yanzu ka zabo min Saratu itama, sai dai har yanzu ba macen da ta kai Aaseeyah komai da komai,"
Mahboob ne ya bata fuska har ran shi bai ji dad'in kalaman Aliyyu ba, cikin zolaya Aliyyu ya sake cewa,
"Dama canje kai mana,kawai"
"Ya fa ishe ka, wannan din ma sai na hana ka na hade su su biyu, kai wai ba za ka dauke idon ka akan mata ta ba? Ga shi dai na samo maka wata ya kamata ka cire sunan ta a labban ka"
Dariya sosai Aliyyu ya yi sannan ya ce,
"Aboki na ina jin dad'in tsokanar ka,baka wasa wajen nuna kishi da kare matar ka, hakan na da kyau, shi ne cikar mazantaka, namiji ya zama mai kishin iyalan shi, kai dai Allah ya mana zabin alkhairi, in wannan din alkhairina ce Allah ya bani, in ba alkhairi ya kawomin mafi alkhairi ameen"
Eliza kuwa da ta shiga daki, wayar Alh. Mukaila ta kira, bata shiga ba kawai ta kira ta Sanata Kabiru, labarta masa komi ta yi, yanda ya ji ta kamar a tsorace ne ya bashi dariya,
'Haba Elli,meye abin tsoro, ai dik inda ta fadi sha ne a wajen mu, ki saki jikin ki, a daren farko in kin so zaki iya aika shi inda ba a dawowa, to meye?'
"Kai baka gane inda matsalar take ba, i love Mahboob, ina son shi, ya zan kuma auri Aliyyu yanzu?"
'Wai ke daukan fansa kk shirin yi ko aure? Na ga alama har kin manta da Sam da ya maki halaccin da iyayen ki ba su miki ba,Abinda muka saka ki yi kenan? In kin san mijin aure kk nema sai ki mana bayani mu nemi mai kammala mana da Aliyyu, in kin auri Mahboob din kin gama da Aaseeyah a gidan nata, amma yanzu ga dama ta zo ki auri Alin ki kammala da shi a daren farko,Aaseeyah kuma ko yara mun sa su gama da ita, duk fa inda ta fadi mu sha ne'
"Mtwss ba zaka gane ba, ina zuwa kar su ga na jima"
Kashe wayar ta yi ta kalli fuskar ta a madubi ta yi ajiyar zuciya, sai da ta daidaita kan ta sannan ta fita wajen su, Dattijuwa iya ta cika masu wajen da kayan motsa baki.
Bayan ta zauna ta dan shagwabe fuska ta ce,
"Ya na ga ba ku taba komai ba?"
Aliyyu ne ya yi murmushi, ya ce,
"Ai ganin sarauniyar kyau ya sa ni dai ciki na ya cika"
Murmushi ta yi cike da jin kunya, hankalin ta na kan masoyin ta Mahboob, amma shi hankalin shi na kan wayar shi, ya na kiran Aaseeyah bata dagawa.
"Kai malam baka gabatar dani ba ka na ta danna waya"
Ajiye wayar shi ya yi ya sanya murmushi a fuskar shi, sannan ya ce,
"To Malama Sarah ga dai mijin aure nan,kin gan shi ya dan tsufa haka to dama neman mata yake shima, dan haka kar ki damu kan ki,ki ga kamar taimakon ki ya yi, kema kin taimake shi,ina fatan Allah ya sanyawa abun albarka"
Dariya Aliyyu ya ke dan an kira shi tsoho,a ido shi da Mahboob kowa na iya cewa sa'anni ne duk da Aliyyu ya girme shi,kenan in haka ne Mahboob shi ne tsohon ma.
"Na gode sosai Mahboob, ka taimaki rayuwa ta, yanzu in mahaifi na ya dawo zan sanar da shi, sai su sanar da kakata na samu miji, domin hankalin ta ya kwanta ta janye kalaman ta akan mahaifi na, in ya so duk sanda ka shirya sai a yi auren" in ji Eliza.
"Ai ni ko a satin nan kk ce na fito a guje zan fito, kamar yanda ya ce ne na tsufa ba aure, ina buqatar abokiyar rayuwa kusa da ni" Aliyyu ya qarasa maganar shi cikin murmushi.
Rufe fuska ta yi ita a dole ta ji kunya, a cikin mayafin ta kuwa takaici ne fal zuciyar ta, Mahboob bai kyauta mata ba, ta gama sa rai da shi,ya tashi ya kawo mata wanda mistake daya zatai asirin su ya tonu, domin yanzu hukuma su suke nema ido rufe, kashe su Gazaa ba a kama wanda suke sanya su ta'addancin ba ai aikin banza ne, domin a yanzu haka su Hon. Mamman Accu sun samu sabbin yara masu masu fashin kayan mutane, daga na gwamnati har na hamshaqan masu hannu da shuni.
Sun dan yi hira sosai kafin suka mata sallama suka tafi, Aliyyu sai yabawa Sarah yake, tare da yi wa Mahboob godiya, tabbas yau maman shi da Baban shi za su yi farin ciki ainun.
Sallama suka wa juna suka nufi gida.
****************************
Daf an kusan kiran magriba Aaseeyah ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda sanin cewa Mahboob na wajen wata, zuciyar ta na zafi saboda tsananin kishi da ke yunkuro mata ta sanya hijabin ta ta fita.
Wani yaro ne da ba zai wuce shekara sha hudu ba naga ta kira, ya na ganin ta ya washe vaki, dan sun jima tare ya na samo mata duk wani kayan rashin ji da take nema, kamar su kashin awaki, beraye,kyauro da dai sauran su.
"Shagari ina zuwa haka?"
"Zan je gida ne, shegiyar nake ji, rabo na da gida tun safe"
"Allah shirye ka, ka na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 41