Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya gaggaya mata maganganun da ke barazanar tarwatsa zuciya da kwakwalwar ta, anya za ta iya hakuri da shi kuwa? In ta hakura da shi ta auri wa, wa zai kwashe ta a haka, inaaa ba ma zata iya son kowa ba bayan Mahboob, in nacin da take masa bai ishe shi ba, za ta qara akan na da. Ba inda ta fita, duk yunwar da take ji na tatsar tumbin ta,da turarukan shi ta yi amfani,ta gyara gashin ta bayan ta busar da shi,rigar shi ta samu mai kalar baqi,ta sanya, da short din shi in ya saka dame shi ya ke sosai, saboda roba ne, itan ma dame ta ya yi, ba dan na maza bane sai na ce ya mata kyau. Gashin ta kalar brown mai duhu ta sake bazawa ta hanyar zira yatsun ta ta tsakiyar shi,takawa take cikin juya qugun ta da naturally haka take ba dan ta yi niyyar yin yanga ba, fita ta yi itama zuwa parlour ta fara yawatawa, fridge ta bude ta debi fruits ta fara ci, ba ta wani ji qoshi ba, madara ta tsiyaya a glass cup ta na tafe ta na sha, qara kallon ko ina take kamar yau ta fara shiga gidan, tunani ne ya shige ta, da gudu-gudu ta nufi qofar fita ta rufe ta ciki, dudduba library din shi tafara don ganin ko za ta samu wani bayani akan shi, abinda ba ta taba yi ba kenan bincke, dan haka a tsorace take, tafin hanun ta har zufa suke, cikin sauri ta ke komai,amma ba ta ga wani abu da ya wuce sanin da ta masa ba. Daki ta koma nan ma ta fara duba wa ko za ta ga wani abu da zai taimaka mata,ta kwaso takardun shi masu mahimmanci kenan ta ji ana buga qofa kamar za a balla a shiga,cike da tashin hankali ta kalli wajen ta ga yanda ta yi kaca-kaca da d'akin, tunawa da yanda ta maida parlourn ne ya sa ta sakin 'yar qara,wayar ta da ta dau ringing ce ta sake tsorata ta, zabura ta yi ta haye gadon, Sunan Mahboob ta gani,ta sake ta a saman gadon ta maida masa takardun shi, passport don shi ne na Nigeria ya fadi tare da wani passport din, ba tare da ta san sun fadi ba ta fita daga d'akin da gudu ta fara qoqarin maida kayan parlourn da ta firfitar, maqotan shi da ke kusa ne suka bude qofa dan jin qarar bugun nashi ya yi yawa,ko kallo ba su ishe shi ba, bude qofar ta yi tare da sakar mashi yaqe, bankad'a qofar ya yi da qarfi sai da ta bugu da gini, sannan ya shige ciki, ganin gidan shi a barkace ne ya tabbatar masa da abinda ta yi,tura qofar tayi ta rufe dan ta kula da yanda maqotan ke qoqarin leqawa dan ganin me ke faruwa, wani mugun kallo ya ke bin ta da shi, wanda ya sa ta jin kamar ba a tsaye take ba,dafe kujera ta yi,ta zauna a hankali, cikin daga hannayen ta kadan ta bude baki da niyyar masa bayani, ta ga ya shige daki, "Wannan wanne irin mutum ne wai?" Dakin ta bi shi, a tsaye yake a wajen passports din shi da ke qasa, dauka ya yi ya najuya su a hannun shi,kallon ta ya yi, cike da tsana da takaici,ya tsani binciken da take mishi, ya tsani naci. Jakar ta da kayan ta ya kwasa, ya watsa mata, tuni ta fara kuka ta na neman ya yafe mata. "Daga yau ba na son na sake ganin ki,ba zan hana ki zuwa office ba dan ba ma'aikata ta bace, amma ki tabbatar hanya ba ta sake had'a mu ba,na maki al'qawari kk sake had'a hanya dani, sai kin tsane ni" Tura ta ya yi wajen gidan shi, ya rufe qofar shi,abincin da ya siyo mata ya kalla, cikin jin haushi ya sa qafa ya ture qasa, ya zube a saman kujera. "Wannan wanne irin naci ne?" (Hummmm maza mutanen mu,ke da kk sakewa namiji jiki da sunan soyayya ahir din ki, abinda aka riga aka bude ko an gyara tabon shi tabbatacce ne, ba dinkin da zai hade ki ki dawo da budurcin ki,ba maganin da zai hade ki qarya ne, za dai ki matse amma budurci daya ne, in ya tafi ya tafi, budurci mutunci ne, qima ne, daraja ne, in kk rasa shi baki da wadancan qualities din kenan, kin zama abar wulaqantawa a wajen miji, kin zama abar gorantawa musamman in ki nada kishiya,ko mijin ki ya na da shaquwa da yan uwan shi musamman mata, sai sun sani,ki zama mara qima da daraja a wajen su, tabbas gaskiya ne da ake cewa duk abinda namiji ya yi ado ne,ba wai dan ya yi daidai ba, kin taba jin an ce namiji bai kai budurcin shi dakin aure ba? Na tabbata ba ki tab ji ba ko da kuwa duk unguwar su salihai ne shi kadai ne bunsuru, shiru za ki ji, da ace zaki je ba naki budurcin da kin shiga uku awajen shi, wallahi mata mu bude ido mu kama kan mu, shi ya sa auren yazu ba albarka, an gama barbada a titi, da an shiga ciki wata daya biyu wasu sun ma rabu, masu d'an hakurn ne za a zauna a ci gaba da gasa juna. Mu kiyaye) Aemana a qofar wajen ta murje idon ta saboda 'yan sa ido, ta saka kayan ta da kyau, ta nufi wajen aje motoci,a hanya kan ta isa wajen da motar ta take, ta juya ta kalli gidan da Mahboob yake, wanda na haya ne mai hawa hudu, kowa da apartment din shi a wajen,wasu zafafan hawaye ne suka zubar mata, kafin ta cije labban ta da suka bushe ta yi gaba.... Shin ya kamata ta hakura kuwa ???? TAUBASHI PAGE 11 An gama hutun sallah, dalibai sun koma makarantun su, kama daga islamiyyu zuwa boko, kamar yanda kuka sani, lokacin da aka koma makaranta, wasu yaran murna sike,saboda za su rabu da ayyukan da suke taya iyayen su,za su koma gagara a makaranta, wasu kuma su na murna ne kawai domin su din masu son karatu ne, wasu kuwa baqin ciki su ke dan ba ma su son makaranta bane, haka ma bangaren iyaye, wasu na murna za su rabu da rabon fad’a, da yawan bata masu gida da yara suke,wasu na jin haushin masu taya su aiki za su koma makaranta su barsu da aiki. Aaseeyah na daga cikin masu murnar komawa makaranta, Yesmeen da sauran ‘yan uwan ta kuwa su na daga masu baqin cikin komawa makaranta, ko dan baccin safen da suke samun yi a hutun. Sabbin uniform din su sun sha guga fess da su, takalman nan sun sha wanki da guga sai kyalli suke, fuskar Aaseeyah dauke da annuri,drivern su bai samu dawo wa daga hutun sallah ba, sai ranar laraba, dan haka Noor ne zai kai su, cikin shirin tafiya makaranta shi ma ya fito, goye da jakar shi,rige rigen shiga gaban mota Yesmeen da Umaimah suke,Ummu Suleim tai tsaki ta rab’a su ta shiga baya ta zauna, kan ta ke sara mata saboda rashin baccin safen da batai ba. Aseeyah ce riqe da lunch bag din ta da har yau bata daina dauka ba, sai dai ta yi sabuwa mai kyau, ta kan ce, ‘In ba dan me rai da kwad’ayi ba, me zan da wani abincin bayan na Mammee na, Mammee na ta fi kowa iya girki’ Ko da ta zo ta ga su na ta fada, Noor na masu magana ba su ji ba sai ta matsa kusa dasu,ta taba Yesmeen ta ce , “Dan matsa Yah Noor na min magana b na jiyo wa” Yesmeen na matsawa ta bude gaba ta fad’a, ta na dariya, qoqarin fiddo ta Umaimah ke yi Noor ya daka masu tsawa, “Ku ba na son hauka,meye haka? Wai ku ba ku san kun girma da wannan shiriritar ba ko? Dalla malama rufen qofa ki shiga baya” “Yah Noor ni..” “Dalla in ba za ki tafi ba rufen qofa ta kar ki sa ni makara” Cikin qunar rai Umaimah ta samu ta shiga baya ta nata aunawa Aaseeyah harara ita kuwa sai dariya take, can ta hango fuskar Ummu Suleim ba walwala, cikin nuna yanayi na kulawa ta ce, “Lafiya ki ke kuwa Ummu suleim?” Dan tsaki ta ja sanan ta ce, “Aaseeyah Kai na ke ciwo, da so samu na ne ina kwance yanzu ina baccin safe” Wani murmushi Aaseeyah ta sake wanda ita kadai ta san ma’anar shi. “Ni kuwa da kk ganni nan ba qaramin farin ciki ne a raina ba,komawar mu makaranta buri ne da na jima da shi a kwanakin nan” Yah Noor ne ya taka wani irin birki, sai da ta bigi gaban motar da goshin ta sakamakon rashin daura belt, Kallo mai ma’anoni da yawa ya mata, siririyar dariya ta sake, sannan ta daga hannayen ta biyu, ta langwabe kan ta kamar mutuniyar kirki, “Ba abinda ka ke tunani bane Yah Noor, na maka alqawari,ba za ka ji wani labarin da ya sab’a abinda ka ke so ba” “Ki tabbatar kin kula, kuma kin kiyaye, in ba haka ba,ba za ki so hukuncin da zan maki ba” “Na amince” Tafiya sika ci gaba, ba su tsaya ko ina ba sai makaranta, har su ka isa su Yesmeen ba su bar tunani akan abinda ya faru ba,me su Aaseeyah d Yah Noor ke magana akai ne? Ko juya wa Aaseeyah ba ta yi ba balle ya saka ran samun sallama ko godiya daga wajen ta,da kallo ya bi ta, dan ganin kamar ta fi kowa kyau a makarantar gaba d’aya, Umaimah a wannan lokacin ji take kamar za ta fashe dan haushi, a yau za a yi ta ta qare in sun koma gida, tsaki ta ja a hankali sannan ta dalla ma qeyar shi harara ta bude motar da qarfi sannan ta doka ta rufe ta wuce, bai ko san ta na yi ba, ta dan yi gaba a zaton ta zai mata maganar abinda ta yi, ta ji shiru, sauri ta qara ta shige makarantar ta su. A aji kuwa Aaseeyah ta na ta gaisawa da kowa, cikin sakewa,Rahmah hankalin ta a tashe ya ke, dan kuwa ta san karon su da Aaseeyah ba zai mata kyau ba, amma sai ta ga ko a jikin ta, tunani ta yi a ran ta, ‘Wataqila tunda Jubeir ya ce bai sami nasara akan ta ba shi ya sa bata kula ni ba’ Hannu ta gani a gaban ta, da alama ana son gaisawa da ita ne, da ganin hannun ta san na wane ne, wani irin faduwar gaba ne ya sake samun ta, kif-kifta ido Aaseeyah ta yi,tare da maida shi gefe, “Habaaa Rahmah dear, ai ko sallama za ki amsa min a matsayin ki na musulma ko?” “Aaseeyah ki fito fili ki bayyanan bacin ran ki, wannan fara’ar da ki ke nuna min na san ba gaskiya bane” Cikin qarfin hali take maganar, “Me ki ka min ke kuwa da zan maki abu ba domin Allah ba? ‘Yan aji ku tambayar min Rahmah me ta min da zan fushi da ita a ranar farko na dawowa makaranta” Hannayen ta ta goye a qirjin ta, ta na bin Rahmah da wani irin kallon da ya ke gigita ta da sanya ta cikin damuwa da nadama. “Uhumm Rahmah ke ‘yan aji ke jira, ko yah, ko ba ku son sanin me Rahmah ta min?” Nan mutanen da ma hankalin su da baya kan su kowa ya matso, su na kallon yanda Rahmah ta muzanta, idon ta ya cika da hawaye, qiris ya rage ta fashe da kuka, “Rahmah qawar amana, mai so na da qauna ta, mu na jiran ki fa, ko ba zaki iya fada ba? Ko kin had’iyi gatari ne? Ohk bari na fada masu…” “Dan Allah ki rufan asiri kamar yanda Allah ya rufa maki asiri, sharrin shaidan ne, da hassada, amma inshaa Allahu ba ke ba ma har abada ba zan sake yi wa wani abinda na maki ba,plsss Aaseeyah forgive me” Zuciyar Aaseeyah ce ta yi laushi ganin hawaye sosai na zuba na nadama a idon Rahmah,dukan hannun ta na dama ta yi da na hagu, bata so Rahmah ta karaya da wuri ba, amma ba komai, za ta huce haushin akan uban gayyar, kallon ta tayi, ta saki murmushi, “Ok na yafe maki to, amma akwai sharadi” “Me ne sharadin, zan yi komai ki ka ce, in dai zaki yafe min” “Ba wani abu bane mai wahala, adashe za mu shiga, na cin awara, in kin yarda kullum za ki sai min awarar dari biyar har zuwa sati biyu, ni kuma ranar zubi na, ma’ana ranar siyan tawa inna siya ba zaki ci ba ni kadai zan ci na gyatse, kin amince?” Kasancewar kowa a duniya akwai abinda ya ke mugun so, to Aaseyah ta san ba abinda Rahmah ke so sama da awara,gashi Rahmah kudin da ake bata d'ari biyu ne kullum, gashi an ce ta na siyan awarar dari biyar, lallai wannan hukuncin shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa,ina za ta nemo dari biyar kullum in ba sata za tai ba,ta kuma tabbata ba wai Aaseyah ta yafe mata bane. “In hasashe na ya yi daidai tunanin inda za ki samo kudin ki ke yi,…hummmm ga shawara, me zai hana ki je wajen Junbeir in kun yi abun nannnn…. Sai ya baki dari biyar ki zo ki sai mana awara” Nan da nan taro ya dau cece ku ce, me su ke aikatawa? Kowa da abinda ya ke fadi, ran Aaseeyah kwal, dan kuwa ta jefa zargi a zuqatan mutane, Rahmah kuwa ba abinda take in ba kuka ba da bayani, Aaseeyah kuwa takawa ta yi gaban ta ta ce, “Kar ki damu, tunda da alama ba ya biyan ki, na cire ki cikin ‘yan adashen cin awara, kar ki damu, zaki iya zuwa cikin mu kema duk sanda kk so, amma fa sai kin rabu da Jubeir, domin ba za mu ci gaba da huld’a da bara gurbi ba” Nan fa taro ya dauka, wasu har sin yanke hukuncin Jubeir ya ci amanar Aaseeyah ne da Rahmah, tunda kowa ya san Aaseeyah da Jubeir a tare, wataqila ta kama su suna wani abun da bai dace ba ne, nan dai kowa ke qoqarin fadin abinda ya fahimtan fuskar Rahmah ta kumbura saboda kuka, su na haka Aaseeyah ta zame ta yi zaman ta a mazaunin ta ta na kada qafa ta na murmushin samun nasara, kyakkyawar zuciyar ta na ta yunquro mata akan bata kyauta ba, daya bangaren kuwa na nuna mata ta yi daidai, kuma ta kyauta, hakan abun farin ciki ne tunda ta rama abinda su Jubeir suka mata. Har aka fita break Rahmah ba ta daina kuka ba, ta na ji ta na gani kowa ya ware ta, ba mai son zama a inda take, da gudu ta bar wajen da suke zama dan yin break din,ta na kuka, labari ya fara baza makaranta, a yanzu kowa kallon ‘yar iska ake mata, Jubeir kuwa gani kawai ya yi abokan shi na qus-qus,duk ya tsargu, ya yi roqon duniya su fada masa me ke faruwa sun qi,wani ne can daga gefen su ya daga murya ya ce, “Haba Jubeir, ban taba sanin kai kwaro bane sai yau, ka had’e qawaye kana kwantarwa, baabaaaa ka na jan kaya Alaji” Kallon mamaki ya ke ma mai maganar sannan ya ce, “Ban fahimta ba” “Ka na nufin baka gane maganar da nake ba? Ina magana ne akan Aaseeyah da Rahmah, haba Jubeir ajin su d’aya fa” Gaban shi ne ya fadi, wa ya kawo musu gulmar abinda ya faru tsakanin shi da su Aaseeyah, hayaniya ce ta kaure a wajen, kowa na fadin albarkacin bakin shi, a nan Jubeir ke jin abinda Aaseeyah ta yi wa Rahmah, ya tabbata nashi sai ya fi haka,wani abu ya hadiya mai daci, tare da jin tsoro mai tsanani ya kama shi, duk abinda za ai ba ya son gidan su su san me ya aikata. Barin wajen ya yi ya tafi neman Aaseeyah, da niyyar ya bata hakuri, ko kuma ya tsorata ta, akan kar ta sanar da kowa me ya faru, ko da ya isa wajen da suke cin abinci, Aaseyah ta aje hijabin ta gefe saboda wajen mata ne, ta na ta dangwalar yaji ta na cin awara, kamar daga sama ta ji muryar shi, ta yi kewar muryar shi sosai, amma wannan sirri ne tsakanin ta da zuciyar ta, sai ta hukunta shi, “Ba ki ji ina maki magana?” “Dan Allah Junbeir ka je na yafe maka, na fada maku kai da ita kun dace da juna, ni Aaseeyah Ibraheem,Abdul mudalleeb Jordan ba za ka taba samun biyan buqatar ka a waje na ba, ita da ta yarda ta ci amana ta a bayan ido na, ta mallaka maka kan ta, ku je can ku qatara, karatu iyaye na suka aiko ni, na yi kuskuren bijire musu na fada soyayyar ka, amma na godewa Allah da ya nuna min wane ne kai,kuma yaya na ya amsar min ‘yanci na, domin tabon da ke jikin ka kadai ya ishi shaidar abinda ya faru” Maganganu ne suka kaure a wajen, marasa dad’in sauraro a kunnuwan Jubeir da Rahmah,sun matuqar tayar da hankalin su, sun kuma faranta ran Aaseeyah, domin kuwa kowa ya tabbatar da cewa Jubeir da Rahmah na aikata ba daidai ba, Aaseeyah ta tsallake rijiya da baya, Allah ya tseratar da ita daga sharrin Jubeir. Hijab din ta ta sanya ta tattare ledar awarar ta ta danna a lunch box din ta ta saka a jaka ta zuge ta rataya a wuya, ta zo gilmawa daidai inda Jubeir ya ke tsaye ta dakata, tare da yi mishi magana qasa-qasa. “Dama in malami ya koyar da d’alibi, akan samu d’alibin da ke wuce malamin a ilimi, Jubeir ka koyar dani makirci da blackmailing mutane, to ya ka ga wasa na? Ina fatan ya doku da kyau” Cikin kashe masa ido d’aya da wurga hannayen ta a aljihun rigar ta ta bar su a wajen,Jubeir ya kasa ma daga qafar shi a wajen tsabar kunya, Rahmah kuwa gate din makarantar ta nufa da gudu, ana tare tare, haka ta fice, bata tsaya ko ina ba sai gida, ta yi rantsuwa sai dai a sake mata makaranta amma ta bar wannan kenan har abada. (Ban bancin mace da namiji kenan, ita kunya ta dame ta har ta na ganin za ta bar makaranta, shi kuwa ko ya ji kunyar na dan lokaci ne, mata mu ake bari da abin kunya mu kiyaye) Ranar Jubeir ya ga wariya a wajen abokan shi, ba dan su din ba su yin abinda ya so aikatawa ba, ah ah sai dan kawai na shi ne ya fito fili. (Kun san mutane ko kana aikata abu, sai ka take ka boye ka danne, ka dinga fadar na wani, ana mantawa a daidai sanda ka daga duwais din ka dan hango na wani, wani shi ma na can na hangen naka, mu zama masu rufawa juna asiri) Yesmeen da su Ummu Suleim da suka ji labarin dake yawo, sun sha mamakin yaushe haka ta faru? Tunawa da maganar Aaseeyah da Yah Noor a mota suka yi, da kuma abinda sika ji labari Aaseeyah ta fadi na yayan ta ya dau mataki akan Jubeir, kenan Yah Noor ya san me ya faru? Shi ne su bata fad’a masu ba. Magana wasa-wasa har gaban shugaban makaranta, ko da aka kira su office din mai makarantar su dan jin ba’asi, Aaseeyah ta karkace ta shera qarya, akan Jubeir ya neme ta taqi har gidan su yaje ran sallah, suka hada baki da Rahmah zai mata fyade yayan ta ya cece ta, shi ne bai samu nasara ba suka fara soyayya shi da Rahmah, har ta ga videon su su na kiss, wata zabura Jubeir ya yi, sai da ya ba wa Aaseeyah tausayi na d’an lokaci, amma daga baya ta ayyana a ran ta, ‘Dani ka ke zancen,’ “Subhanallahi, d’aliban wannan makaranta mai dumbin tarihi da nasaba ke wannan aika-aikar? Lallai wannan magana babba ce, dole ne a sanar da iyayen ku, kai kuma korar ka za mu yi, ba ma buqatar yara irin ka a nan, ke kuma kin kyauta da kk tsaya tsayin daka kk kare mutuncin ki, Allah ya miki albarka, ita kuwa da ta gudu har gida za a aika ma iyayen ta su zo,” “Sir dan Allah ina neman alfarma, kar a sanar da iyaye na, Mammee na na da ciwon zuciya, in ta ji irin labarin nan zai dame ta” Kuka ta fara na jin kewar Jubeir, dan ta tabbata sai an kore shi,Mai makarantar kuwa ya zaci kukan tusaya wa lalurar mahaifiyar ta take, dan haka aka amince ba mai ji a bangaren iyayen ta, su kuwa dole ne a dau mummunan mataki a kan su. Sallamar su akai, kowa ya koma aji. Aaseeyah ta rasa halin da take ciki a wannan lokaci, shin anya ta kyauta kuwa? Shi ne abinda take tambayar kan ta, Nima kuwa na ce anya ta kyauta kuwa????? Rubuce-rubuce ya ke yi a laptop din shi ta shiga dakin, tura qofar ta yi ta kulle ta ciki, sannan ta kama qugu ta tsaya masa akai, kallon ta ya yi sau d’aya sannan ya kauda kai, “Umaimah me ye haka, wato saboda ina maki wasa kk raina ni ko?” “To ba dole ba, Yah Noor wai me ka ke nufi da ni ne? Ni ce ke kula da buqatun ka amma hankalin ka da soyayyar ka , tare da kulawar ka na gun wadda bata san ma kana yi ba,” “Umaimah na taba furta ina son ki? Me ye naki na kishi da Aaseeyah?” “Sabo da ita ka na son ta, ni kuma jiki na ka ke so kuma ka na min kalamai na yaudara” “A baki na ki ka ji na fad’I ina son ta?” “A idon ka na ga hakan” “Yah Noor abinda na ke son sanar da kai shi ne, ka ma cire ta a ran ka, domin ba zai yu ka gama amfanuwa da jiki na ba ka koma wa wata, ni da kai mutu ka raba, ba zan taba auren kowa ba in ba kai ba,” “Ki na da hankali kuwa Umaimah,” “Rasss da hankali na, ka taka a hankali, ka bar gani na yarinya, domin a yanzu na wuce sanin ka” Abun fa ya fara bashi mamaki, “Ka tsaya ka na kallo na, dole ne ka zab’a tsakanin ni ko Aaseeyah, zabin ka ne zai bani damar aiwatar da abinda ke raina” Shiru Noor ya yi ya na ganin yanda qaramar magana ke neman koma masa babba…… A taimakowa Noorr, kar asiri ya tTAUBASHI PAGE 12 Qoqarin amsa ta Noor ya ke, muryar Ummee ta katse shi, sakamakon kiran Umaimah da take, cikin jin takaicin katse ma Umaimah jin amsar da Yah Noor zai bata ta doka qafa a qasa cikin son yin kuka ta kalli Noor, ta ga ya na qunshe dariyar samun kubuta da ya yi, “Ba mu gama magana ba, I will be back soon” “Ina nan ina jiran ki qanwa taaaa,” Har za ta fita ta ga plate a ajiye, ta koma ta dauka ta na murguda masa baki, “Zan kama ki ne, za ki fadan waye sa’an ki, da kk murgudawa baki” “Ka kama nin mana” Yunqurin kama ta ya yi, ta fita da gudu ta na dariya,haduwa suka yi da Ummee, nan fa ta fara mata fadan bata share mata kitchen ba, kowa ya yi aikin shi banda ita, sai time din islamiyya ya yi ta ce ta manta. Shara ta fara tare da goge goge, ta na yi ta na murmushi, soyayyar Yah Noor a ran ta daban ne, ta na jin nishad’I da annashuwa a duk sanda ta tuna da shi, gani take in ba ta dawwama tare da shi ba zata iya rasa ran ta, matsalar ta daya ne, bai wuce yanda ba ya bata kulawa da mahimmanci ba,musamman in a gaban mutane ne, in kuma daga shi sai ita ne, kamar zai bude qirjin shi ya sanya ta, gaskiya dole ne ta dau matakim sanya shi fara son ta, kamar yanda ta ke son shi, ko fiye da haka ma. Dakin nata ba a share yake ba,duk ta watsa kaya ko ta ina, ga tsintsiya da parker ta dakko da niyyar shara,kawai ta samu waje ta yi kwance daga ita sai gajeren wando, iya cinyar ta, da wata qaramar shimi, ta kama ta sosai, gashin kan ta daure da

Chapter 8 of 41