Gazaa ya saki, sannan ya ce,
"A ina za mu hadu?"
"Duk inda ka ce za mu zo,"
Sanar da CP Aliyyu inda za su hadu Gazaa ya yi, da sauri sika shige motocin su, aka sanya mahaifin Gazaa a mota shi ma, Aaseeyah kuwa sabbin kayan da Gazaa ya sanya ta sauyawa su ne a jikin ta, binjimemiyar T-shirt ce da bagen wando,kanta ba dankwali, qafar ta ba takalmi, haka suka fito a maboyar ta su, da ke cikin surquqin daji,danna ta suka yi a mota suka sanya mata baqin abu suk rufe mata ido.
Da gudu suke tafiya, duk inda suka wuce qura ke tashi.
Ba su tsaya ko.ina ba sai nesa da wajen da za a yi musayar, CP Aliyyu ne tsaye, da wasu yaran shi, sai mahaifin Gazaa da ke daddaure a cikin sarqoqi.
Aaseeyah Sam ya janyo da qarfi, ya wurga gaban Gazaa, yaran Gazaa na kewaye da shi ko ta ina da munanan makamai, bindigogi ne manya a hannun su, za kai mamakin yanda akai aka shigo da irin muggan makamai haka a ce gwamnati ba ta sani ba.
Takawa CP Aliyyu ya fara yi zuwa tsakiyar wajen, Gazaa ma na kusantar inda CP Aliyyu yake ya yi, wata dariyar mugunta Gazaa ya saki, duba da yawan 'yan sandan da Aliyyu ya zo da su, dika dika ba za su fi mutum bakwai ba, Hannu ya daga Sam ya.......
Comment more ku sha typing.
TAUBASHI
PAGE 34
Sam ne riqe da Aaseeyah, da ganin ta a jigace take, bakin ta ya bushe sosai, sai kalle kalle take,Sam na isowa tsakiyar filin ya wurga ta gaban CP Aliyyu, durqusawa ya yi da niyyar ya taimaka mata ta tashi, ya fasa, tunawa da cewar ita din matar aure ce, da hannu ya yi alama, nan 'yan sanda biyu suka riqo mahaifin Gazaa dan tahowa da shi gaban su CP Aliyyu, ba bu wanda ya yi zato ballantana tsammani, duba da cewar Aaseeyah ko bindigar wasa bata taba riqewa ba,kuma ga ta shajaran majaran, amma cikin zafin nama, ta mirgina daga qasan da take ta zare bindigar CP Aliyyu a qugun shi ta harbi Gazaa a qirjin shi, Sam na qoqarin sake mata harsashi, ya ji abu ya bige shi mai tsananin qarfi a cikin shi sai da ya juya, ido ya zaro sanda ya sanya hannun shi a ciki ya ga jini, har a lokacin bai bar qoqarin harbin Aaseeyah ba, nan da nan bangarorin biyu suka bude ma juna wuta.
CP Aliyyu zaro d'ayar bindigar shi ya yi, sannan ya amshe ta hannun Aaseeyah ya wurga ta bayan shi ya na tafe ya na harbi, su na zuwa jikin mota ya wurga ta ya rufe, jikin ta sai rawa yake,hawaye sun qafe mata, ta rasa yanayin da za ta shiga,murna ne? Baqin cikin ta yi kisan kai ne? Ko kuma tsoro ne? Tunda ba ta san makomar ta ba wajen hukuma.
'Yan sandan da CP Aliyyu ya sa su tsaya daga nesa for back up ne suka iso wajen saboda qarar harbi da suka ji, suka saka mutanen Gazaa a tsakiya, mutanen Gazaa sun razana matuqa, domin ganin shi a qasa kawai ya rage masu qarfin guiwa, wasu na kuka suke harbin, ga na hannun daman Gazaa shi ma a qasa, wasu miqa wuya sukai, suka aje makaman su, wasu kuwa sun gwammace su mutu ana gumurzu,sun san koma me ya faru dai kashe su za ai, dan haka basu daina bude wuta ba, sai da aka kashe su din, sun samu nasarar kashe 'yan sanda guda uku, da jinyata wasu.
Mahaifin Gazaa kuwa qoqarin guduwa cikin daji ya yi, ba dan rashin kwarin jikin shi ba, da gurguwar qafar shi, tabbas da tuni ya tsere, amma ko nisa bai ba wani d'an sanda ya hango shi, ya kuwa dana masa harsashi, nan take ya fadi qasa, bai bar shi ba sai da ya harbe shi sau uku, tattara sauran 'yan fashin CP Aliyyu ya yi, aka daure masu hannaye, tare da sanya su duqawa a saman guiwowin su, mai daukan hoto a cikin police din ya koma mota ya dakko camera ya hau aikin shi na daukan hotunan su, nan CP Aliyyu ya sake sanyawa bindigogin shi hardashi, ya harbe mutum takwas da ke gaban shi, suka fad'i matattu, rami wasu 'yan sandan suka haqa aka binne su a wajen.
Duk abinnan da ke faruwa Aaseeyah ba ta da masaniya, dan kuwa ta jima da sumewa, qarar harsashi, tashin hankali da yunwa da qishirya su ne suka taimaka wajen sumewar ta.
Bayan kammala komai, CP Aliyyu ya bada umarnin a tattara police din da suka mutu, da kuma wanda suka samu raunuka a mota dan kai su asibiti,nan take kuwa aka bi umarnij shi, sai da ya tabbatar an gama sanya kowa a mota, sannan ya je dan ya fiddo ta a motar 'yan sandan da ya wurga ta, wasu su samu su shiga,ita kuma ya sanya ta a wadda ya zo da ita , ganin ta ya yi a sume, cike da tashin hankali ya koma motar shi ya hau neman ruwa, kaff wajen ba ruwa, bai bata lokaci ba wajen kinkimar ta a hannun shi ya danna ta a motar shi, mazaunin direba ya shige, ya tada motar a guje, sauran 'yan sandan suma bin shi su ka yi, qura sai tashi take a dajin, kafin suka samu suka hau kwalta.
Tafiyar rabin awa ce ta kai su cikin gari, CP Aliyyu ya yi ma kano sanin d'akin shi, dan haka asibiti mafi kusa aka nufa da Aaseeyah, a hannu ya shiga da ita, nan da nan kuwa Nurses suka karbe ta, aka kira likita ya shiga duba ta.
Sun samu nasarar bata taimakon gaggawa, ta farfado,gaba daya ta koma wata abar tausayi,ta rame, fuskar ta busasshen jini, ga lips in ta sun kumburo saboda wahalar da suka bata.
Samun nasarar dawowar Aaseeyah cikin hayyacin ta, ya sa murna ta kama CP Aliyyu sai a sannan ya tuna da kiran mutanen gidan su, ringing d'aya ta yi Abbu ya d'aga tare da tambayar ,
"Yallaba ya ake ciki?"
"Alhamdu lilLAAH, Alhamdu lilLAAH, komai ya daidaita, komai ya zo qarshe, muna gayyatar ku zuwa asibitin Murna Hospital gaba dayan ku"
Hamdala sosai Abbu ya dinga yi, wadda ta sanya mutanen parlourn miqewa kamar su warce wayar suma su ji me ye ya ma Abbu dad'i haka?
Ya na gama waya ya kwasa zuwa bakin qofa, ya na tafe ya na masu bayani, Mahboob faduwa ya yi ya kai goshin shi qasa, domin godiya ga Allah, Mammee ta jima a duqe wajen godiya ga Allah, domin tun da ta ji Abbu ya kama sunan yallabai, kuma ta ji ya na Hamdala to tabbas tasan an samu nasara, komai ya tafi daidai.
Qarshe dai ita da Mahboob aka bari a baya, a mota guda suka tafi a ciki.
Su na zuwa suka ga qofar asibitin cike da 'yan jarida, ana hira da CP Aliyyu, ya na bada bayanin yanda suka sha artabu da manyan 'yan ta'addan, rabe su Mammee ta yi ta bi bayan su Abee, Mahboob ya so wucewa CP Aliyyu ya zo wajen shi, hannu suka miqawa juna,Mahboob ya hau zuba godiya,cikin asibitin suka nufa suma
"Ku za mu yi wa godiya ina maka murnar samun jarimar mace kamar Aaseeyah, ba tsoro attattare da ita, wataqila ba dan abinda ta yi ba, da ba mu yi nasarar kashe Gazaa da mutanen shi ba, she is very couragious and brave,she is....i don't knwo how to descrive her, she is masha'Allah"
"Ok maganar mata ta muke yallabai kar a manta dai,ina tuni"
Hannu CP ya daga ya na dariya, ya ce,
"Ai na miqa wuya yallabai Mahboob,na hakura, yabon gwani ya zama dole in ji hausawa, ko kai ne dole a yabe ka, balle yarinya qarama,kamar Aaseeyah"
Hannu CP ya miqa ya bude masu qofa, cikin dariya suka shiga dakin, Aaseeyah na ganin CP Aliyyu hankalin ta ya tashi, baya ta fara ja, tare da kuka,ta na fadin,
"Dan Allah ka rufan asiri kar ku kashe ni nima, su suka kashe mahaifan Yah Mahboob, sune sanadin da kakannin mu sika rasu, dan Allah ka rufan asiri,"
Kuka take sosai, kukn da ya bama kowa mamaki, domin ba su taba ganin Aaseeyah tayi irin shi ba, kuka ne mai cike da tsoron mutuwa, da tashin hankali.
Mahboob ne ya yi saurin rungume ta,sannan yace,
"Aaseeyah dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki nitsu,kar ki ja wa kan ki wani ciwon, ki daina irin wannan kukan,ba abinda ki ka yi mara kyau,"
Ture Mahboob ta yi da hannayen ta biyu,ko motsawa bai ba, saboda ba wani qarfi a jikin ta,
"Ta ya za k ce bn aikata komai ba, ni na harbe su da hannu na,wannan hannayen sun aikata kisan kai,na zama mai kashe mutane,"
Kuka ta ke sosai,ta na sambatu, likita Nurse din da ke tsaye a gefe ta kira,cikin qanqanin lokaci ya zo ya shiga tare dabasu umarnin fita,
"Haba yallabai, kun san ba a son mara lafiya irin haka a sanya shi cikin damuwa, sai ta iya kamuwa da wani ciwon kuma,ku je waje ku jira ni"
Allurar bacci aka yi wa Aaseeyah ta koma bacci, CP Aliyyu dole ya tafi office,domin shi ma ya na da na sama da shi, ana buqatar shi, a office, duk dai game da case din,dan haka sallama ya musu ya wuce, tare da alqawarin zai dawo zuwa gobe.
Godiya Abbu da Abee, tare da Mammee suka yi ta mishi, Mahboob hannu ya bashi, suka sake ma juna sallama, sannan ya ma CP godiya, tare da raka shi har jikin motar shi, sannan ya koma ciki.
******************************
Washegari da Aaseeyah ta samu ta farfado, Mahboob ya mata bayanin iya abinda ya sani, amma dik da haka Aaseeyah ba ta daina jin tsoron any moment police na iya zuwa arresting din ta ba,a asibitin Mammee ta samu ta mata wanka sama sama, ba dan komai ba ,sai don son ganin ko an cutar mata da Aaseeyah, sai da ta duba ta tsaf ta ga ba wani matsala, sannan ta rage mata dattin jikin ta, ta sauya kayan ta, ta na kwance idon ta rufe komai na gilma mata kamar a TV take kalla, sallamar su Hussein ta dawo da ita daga duniyar tunanin ta, kowa da kowa ya hallara, har Ummu Suleim da Musa.
Ummu Suleim da Yesmeen dama masu jikin qiba ne su, dan haka sun yi dumi mui abun su, sun qara haske, da alama kwanciyar hankali ta samu a wajen su, Umaimah da Noor ma sun zo.
Matar Huseein ma ta dan yi jiki ba laifi,amma fa ta yi baqiqqirin, asalin kalar ta ta fito,dan kuwa ya hana bleaching,ya qi ci gaba da sayan mayukan bleaching, kuma in ya ga ta siya ya debe ya zubar.
Idanun shi kyam kan na Ummu Suleim, da sauri ta dauke idon ta, ta mayar saman na mijin ta, zuciyar ta cike da tausaya ma Hussein, kamar wanda ya yi shekaru da aure,duk ya wani sauya ya yi duhu ya fada.
Yanzu ba wata soyayyar shi a ran ta in ba ta mijin ta ba, hankalin ta ya kwanta sosai, Musa ba qaramin son ta ya ke ba, soyayyar da ya ke mata ne ya sa shi bauta mata da hidima, a haka ya sace zuciyar ta, da gangar jikin ta.
Sun kai azahar kafin suka yi sallama da su Mammee su ka tafi.
Ummee zuwan ta daya, saboda ita ke girki a kawo asibitin, ta ji dad'in yanda ta ji labarin Aaseeyah ce ta kashe su Gazaa da hannun ta, domin ko ita da za ta samu dama wataqila da ta yi namijin qoqari irin na Aaseeyahn Mammee.(Anyaaa Ummee,baqin hali dai mun shaide ki da shi, amma jarumta kuwa wala)
A kwana na hudu aka sallami Aaseeyah ta koma gida, ranar Mammee ta dirje ta kamar jaririya, tun ta na jin kunya har ta ware, saboda dadin wankan da ta ji,Mammee ta sa ta tai shaving, ta yi brush, har sau biyu ta na wanke bakin ta, daga qarshe ta sanya ta wanka da ruwan da ta dafa lalle da ganyen magarya, ta zuba madarar turare da musk fari mai kyau din, ta na tsaye ta nuna ma Aaseeyah yanda za ta wanke lungu da saqo na jikin ta, Aaseeyah ji ta yi kamar ba ita ba, jikin ta har wani santsi ya ke, ga qamshi na fita daga jikin ta,su na gamawa, suka wanke wajen dan kar ya kama, ya yi ja.
Daure da towel ta fita, ta fara tunanin nata da ke sanya ta shiga yanayi na tsoro Mammee ta ajiye mata kayan da za ta sauya, zama ta yi tare da sauke ajiyar zuciya mai qarfi, Aaseeya ta jingina jikin ta da na Mammee.
"Aaseeyah ya kamata ki cire duk wani tsoro da tinani a ran ki,domin ba zai haifar da komai ba sai damuwa,an fada maki ba wata matsala, amma kin qi yarda, yau Aliyyu ya na nan tafe ya maki bayani da bakin shi, wataqila za ki fi yarda da abinda muke fadi maki"
"Mammee ban taba zaton zan kashe ko da bera ne da hannu na ba, ba na mantawa sanda Yah Mahboob ya dawo,yara na sanya suka kamo min berayen da na sanya mi shi a daki, a tuna ni na zan yi karatun lauya har na samu damar maka su a kotu, alqali ya yanke masu hukuncin kisa da kan shi, a rataye su mu gani, da idanun mu, a rage mugun iri a al'umma, Mammee sai gashi da hannaye na biyu na dauki ran bil'adama"
Kuka ta fara yi, abinda Mammeen ta ba ta so kenan, rungume ta ta yi, ta na lallashin ta,
"Da hukuncin alqalin da hukuncin ki duk daya ne a gare su, sun cancanci mutuwa kar ki dorawa kan ki damuwa na fada maki, kin san iya adadin mutanen da suka kashe, a gidajen su? Akan hanyoyin su ta kasuwanci ko komawa ga iyalan su? Kin san kasuwanni nawa suka shiga suka yi fashi da makami suka talauta mutane masu neman halak din su? Ina baki umarni, ki cire damuwar komai a ran ki, ko da za a kama ki dan kashe wadannan azzaluman ba zan bari ba, wannan alqawarin uwa ne, ba zan bar wani abu ya same ki ba indai ina numfashi."
A haka Mammee tai ta lallashin Aaseeyah, har ta taya ta shiryawa, su na yi su na hira,abinci suka fara ci a cikin mazubi guda, Mahboob ya yi sallama, daga can parlour.
Mammee ce ta wurga ma Aaseeyah dan kwalin ta, ta sanya, suka dau plate din zuwa parlour, zama suka yi, suka ci gaba da cin abinci, Mahboob ya ji dad'in ganin Aaseeyah cikin nutsuwa, abu d'aya ya rage, hayaniya da rawar kan ta ne babu, ya yi alqawarin dawo mata da walwalar ta.
Abinci ya tashi zai zubo, Aaseeyah ta miqe, ta ce bari ta kawo masa, har zai musa Mammee ta daga nasa hannu, komawa ya yi ya zauna, ya na murmushi. Abinci ta zubo masa, da ruwa, ta ajiye gaban shi, ta koma ta zauna,
Har ya fara ci, wayar shi ta dau ringing,dagawa ya yi, tare da qamewa cikin wasa,
"Yallabai barka da yamma.....hhhhhhh....ai dole ne a baka girma domin Allah ya daukaka ka, ga shi ka qara samun wani girman,......to ya isa haka, mata ta ce, yaushe za ka shigo?.....ohhh ku na hanya? Kai da wa?....ok sai kun iso"
Sallama suka yi ya kashe wayar, Aaseeyah ta matse spoon din da ke hannin ta, ta na qoqarin danne damuwar ta na jin zuwan Aliyyu gidan su, musamman da ta ji cewar ba shi kadai bane wataqila zuwa akai kama ta, ko ma me ne ne, za ta yi hakuri, ko da hukuncin kisa za a yanke mata ba za ta daga hankalin ta ba balle na Mammee ya tashi.....
Cassssss ana yi ina jin dad'i ina tsayawa da typing ina hutawa 😂😂😜😜
TAUBASHI
PAGE 35
A babban parlour Mahboob ya sauke su, 'yan sanda masu kula da lafiyar Aliyyu na tsaye a bakin qofar shiga.
Mammee ta sha fama, tare da kwantar wa da Aaseeyah hankali kafin ta yarda za ta je gaida Aliyyu,su na tsaka da gaisawa Aaseeyah ta fito, ganin masu baqin kaya a qofar shiga parlour sai ya sake firgita ta, tabbas zuwa akai tafiya da ita, amma da an bi uzirin ta da ba mai ganin laifin ta,sai dai ita shari'a sabanin hankali ce, saddaqarwa kawai ta yi, ta taka zuwa qofar parlourn, kan ta a qasa, cike da tsoro a ran ta.
Ta na qarasa shiga ta ji muryar Amatullah, da sauri ta daga kan ta, Amatullah na mata murmushi, tare da yi mata nuni da kusa da ita, zama ta yi tare da gaida Aliyyu wanda ya samu matsayin AIG Of police yanzu.
Amsawa ya yi cikin sakin fuska, Amatullah na ta tsokanar ta, da cewar,
"Yayana ya bani labarin irin namijin qoqarin da kika yi,amma gaskiya ke jaruma ce, inaga ba ki sauya daga lauya zuwa 'yar sanda dan kin fi dacewa da bangaren"
Yaqe ta yi, wanda Aliyyu ya kula har yanzu a tsorace ta ke kamar yanda Mahboob ya sanar da shi, dan haka ya kira sunan ta, a daburce ta amsa, ta na kallon shi,
"Aaseeyah na kula gaba daya baki yarda da maganganun da na fada ma ki ba, da farko dai da kin aikata laifi, tabbas ko gida ba za ki dawo ba,za mu riqe ki ne a wajen mu, kuma da ban samu qarin girma a wajen aiki na ba, sannan ina so ki sani, a yanayin laifukan da su Gazaa da mahaifin shi suka ma qasa baki daya, an bamu umarnin harbe su a duk sanda muka dora idanun mu akan su, kinga kenan, ke taimaka mana ki ka yi,"
"Amma..Amma..'yan sandan da suka mutu fa? Su na da iyali, kuma laifi na ne, da ban fara bude wuta ba wataqila da..."
"Aaseeeeyahhhh, ko ki fara bude wuta, ko kar ki fara, dama in aka samu irin wannan haduwar da jami'an tsaro da 'yan ta'adda akan samu musayar wuta,kuma ana mutuwa,to kinga kenan ko da ke ko ba ke, in Allah ya qaddara zasu mace za su mace, ki dai na bama kan ki laifin komai,maganar iyalan yan sanda banda kudin da gwamnati ta bama iyalan, nima na basu wasu kudade da muka samo a gidan su Gazaa,kudade ne maqudai da za su ishe su rayuwa indai sun san yanda za su juya su, na sani hakan ba wai ya na nufin mun biya rayukan su bane,ah ah mun tallafa masu ne kawai tunda kudaden ko da gwamnati ta san da su ba lallai ai abinda ya dace da su ba?"
Wata ajiyar zuciya ta sauke, ji ta yi kamar an zare mata wani qashi mai tsini da ya tokare wuyan ta, cikin hamdala ga Allah ta hau yi ma AIG Aliyyu godiya, Amatullah ce ta katse su da cewa,
"Tooo ke ashe ki na da mijin ki a hannu,ki ka qi sanar da ni, kin sa har na fara neman ankon bikin yayana"
Dariya wajen ya dauka da shi, Aaseeyah kuma kunya ta sa ta rufe fuskar ta,
"Amatullah ya isa haka, surutun ki ya yi yawa"
Mammee ce ta sallama,nan suka gaisa ta sake masu godiya, daga baya Aliyyu da Amatullah suka musu sallama su ka tafi gida.
***************************
Madaidaicin d'akin taro ne mai dauke da round table, wanda ke zagaye da kujeru, mutane ne guda biyar a kan kujerun, da ganin su ka san nera ta samu wajen zama a gidajen su da bankunan su, mazaje ne gaba daya wajen, sai wata budurwa guda daya, mai matuqar kyau, sanye take da wata yaloluwar riga kalar ja, bakin ta ya sha fentin janbaki, sai abun hannu, da dogayen farata, gashin ta da na kasa gane nata ne ko na qari ne ya sha gyara se walainiya yake,, hannun ta na hagu na riqe da siririyar sigari, ta na busawa cikin kwarewa.
Hon.Mamman Accu ne ya fara magana.
"A gaskiyar magana, ni ina da ja a maganar ku mai girma Sanata Kabiru,ta ya za ka ce mu manta da maganar Garzali mu samu wani,..ok ban qi a samu makwafin nashi ba, amma maganar maqudan kudin mu da shi kad'ai ya san inda ya ajiye su fa? Ka na nufin mu manta da su? Kar fa ka manta 'yan sanda sun bincike gidan kaff, ban ji an sanar da cewar an samu kud'in ba, ga kuma ASP Shalele da ke mana leqen asiri, ya na da tabbacin ba a ga wannan kudin ba, ina suke? Ba ku zargin wannan shegen yaron ya yi kwana da su shi da yaran shi?"
Alhaji Munkaila babban d'an kasuwa ne, da ke hada kasuwancin shi da kasuwancin makamai, da qwayoyi,in ka gan shi sai ka rantse mutumin kirki ne, ya tsaida gemu,ya saka manyan kaya, kamar na Allah, gyara zama ya yi sannan ya ce,
"Kai ma ka kawo naka ra'ayi wanda zai iya zama gaskiya, amma faku sani, Aliyyu ba mutumin banza bane, wanda zai dauki wadannan maqudan kudin, ya yi shiru,hakan ba mai yuwa bane, tsakani da Allah kowa ana fadin abinda zai aikata da wanda aka san mutum.ba zai aikata ba ko ba gaskiya ba,kuma ina ganin a bi maganar Eliza,mu bar maganar kudin, a samu wani makwafin Gazaa, in mu na son asirin mu ya rufu kenan, sannan kamar yanda ta ce, mu had'a hannu da kawuna, mu dau fansa a wajen wad'annan mutane biyu, Aliyyu da Aaseeyah,ko har yanzu akwai wanda bai yarda ba?"
ASP shalele ne ya ce,
"Na yarda da shawarar nima, dole ne mu dau fansa, kudin mu sun tafi a banza, masu nemo mana kudin an kashe su, sannan su ke taimaka mana wajen bamu tsaro daga abokan gaba masu sana'ar sirri irin tamu,dan haka dole ne mu dau fansa"
Matashiyar da aka kira Eliza ita ce tamiqe, cikin takun rangwadar da ke tafiya da imanin mazaje masu raunin imani,ta dora santaleliyar qafar ta a table din ta dora hannayen ta a saman qafar ta, ta daga kai tare da fesar da sigari, cikin hausar ta da ba bu gargada ta ce,
"Tunda kowa ya yarda da wannan shawarar, akwai wata shawara, amma ina so daga yau Alhaji Munkaila kai za ka zauna a matsayin uba a gare ni, wataqila lokacin aure na ne ya yi, na tabbata mutuwar matar ka ya zo min da sa'a"
Cikin takun qasaita ta fita daga d'akin taron, hips din ta suka bude baki su na bi da kallo, har ta bacewa ganin su,
"Ka ji Matsalar Eliza ba za ta zauna a yi magana a lokaci d'aya ba, ta yi ta jawa mutane rai,wataqila ta na da baqo," Alhaji Munkaila ya fada cikin fushi.
"Ko ba komai, ba ta African time ai kamar wani" in ji cewar ASP shalele.
"Shalele magana ka ke?"
"Ah ah Alhaji,ce wa nai...eh haka take, tai ta juya mu kamar zobe a hannun maqeri"
Haka taron ya tashi ba tare da sun san meye plan din da Eliza ta had'a ba.
*****************************
Aaseeyah ta koma makaranta, ta kuma maida wa karatun ta hankali, a yanzu ta gano cewar, komai za ka yi ka yi domin Allah, da neman yardar shi kawai, domin ka na naka,Allah na na shi, yanzu gashi yanda ta tsara daukan fansar Iyayen Mahboob da kakannin su ba haka abun ya kasace ba,sai ta bar karatun lauya? Ah ah, lokaci ne da zata maida hankali tayi karatun dan neman yardar Allah a cikin shi, da wannan karatun za ta iya samun aljannah ko wuta, hopely ta na nema Allh ya taimaka mata ya zama silar shigar ta aljannah
Aliyyu ya sanya ana kula da ita ba tare da sanin ta ba, domin ba ya jin is safe ta dinga yawo ba tare da ana kula da lafiyar ta ba, duba da irin mutanen da sukai gumurzu da su ba qananan mutane bane.
******************************
Kafin ta isa wajen Alh. Munkaila ya aika almajiran da suka yi hayar su, wajen da ta buqata, da misalin qarfe uku daidai ya fito daga kamfanin DANGOTE da ya ke aiki a ciki, a matuqar gajiye ya bude motar shi ya shiga, tuqi yake cike da lalaci.
Daga can waje wani matashi ne a saman babur ya na ta kallon duk wani motsi na Mahboob ya na sanar ma da Eliza ta waya, ta na zaune ta na duba lokaci, ranta a matuqar bace, duk abinda take ba ta son bata lokaci, lokaci na da matuqar mahimmanci a wajen ta, ta na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 41