su ka tafi, sai da suka ci suka qoshi sosai har da guziri, sannan suka tafi gida.
Mammee ce ta kalli Aaseeyah da ta maida hankali wajen duba littafan ta, ta ce,
"Aaseeyah ni kam kin kula da wani abu kuwa dangane da matar Hussein? Ban sani ba ko hasashe na ne, amma sai na ga kamar akwai wani abu mara dad'i a tsakanin su"
"Exactly Mammee, ni ma ina ta wannan zancen a rai na, kinga yanda ya ke bata rai, ita kuma ta na nuna ko a jikin ta, kamar akwai wani abu dai"
"Tabbas, ni sai na ga kamar ya fad'a ma, aure dika dika sati uku amma ace miji ba walwala?"
"Koma meye Mammee shi ya ja ma kan shi, addu'a za mu taya shi, Allah ya kawo masu farin ciki da zaman lafiya kawai"
"Haka ne, Allah ya kyauta, Yayan ki ya dawo dazu ki na wanka, ya kawo maki cake din da kk ce masa wai ki na so, na aje maki a fridge, amma Hussein ya yanki kadan"
Cikin murna Aaseeyah ta miqe ta nufi kitchen ta dakko cake din ta mai kalar pink, an yi rubutu da kalar fari a jiki, an rubuta.
"I LOVE YOU"
Sai flowers da aka zagaye cake din da shi, masu kalar dark pink,abun ya qayatar da ita sosai, murna ta dinga yi, tai ta maimaita I LOVE YOU din, Mammee ta shiga daki ta bar Aaseeyah na ta kallon cake ta kasa ci dan kar rubutun ya goge, sai murmushi take, ta na karanta rubutun jiki, sai ta dan lakaci gefe ta tsotse, ta karanta tai dariya, ta sake lakata.
"Ni dai in dai ba za a kallen a ce min I LOVE YOU ba zan yi kuka, na gaji da jira, "
Cikin subul da baka ta ce
"To ai dama da kai nake Yah Mahboob ba da cake din ba,"
Ta na gama fada ta ware idanun ta a kan shi, da gaske shi ne ya shigo, da gaske shi ne a gaban ta, ta zaci kawai tunanin da take ne.
Cike da jin kunya ta sa yatsun ta ta rufe idon ta,hijab din da suke sallah da shi a ninke a parlourn ya warware ya yafa mata, domin ba zai juri kallon ta a haka ba, daga shi sai ita a parlourn.
Sake qanqame hijabin tai ta ce,
"Yah Mahboob ba kyau sand'a, ka mugun kwarewa a sand'a"
"Ah ah ni ba sand'a nai ba, har Mammee da ke d'aki ta amsan sallama ta,ke da ke zaune anan ba ki ji ni ba, kin fad'a duniyar shauqin so"
"Yah Mahboob haka ne so? Ni fa cake dina nake kallo,by the way, na gode sosai, Allah ya qara bud'i"
"Ameen Mahboobatee"
Daukan cake din ta yi ta nufi dakin ta da gudu, ta na dariya.
Shi ma murmushi ya yi, ya wuce kitchen ya dau abincin shi ya koma bangaren shi. Shi ya ce a na bar masa ko ya zo ya ci anan, ko ya tafi da shi, ba ya son yawan shigan Aaseeyah wajen shi su kebe su kadai, ko hira yake so ya yi da ita sai dai ya zo nan wajen si.
************************
"Sire yau fa mun samu wadannan masu laifin sun fad'a mana da wanda suke aiki, mu na neman izinin ka dan zuwa kamo shi, a yau yau din nan,"
"Waye shi wannan mai laifin?"
"Yallabai, ya na da manyan cases a nan wajen mu, tun shekaru masu yawa da suka gaba ta, amma saboda daurin gindi da suke da shi a gwamnati ya sa ake kyale su"
"Lallai laifin shi ya zo a wrong zamani wannan karon, domin kuwa ba ruwa na da sanayya, na baku izini a je duk inda yake a kamo shi, in ku na ganin ku na buqatar taimako na a kamo shin ku min magana, i will gladly help u"
Sara mishi dan sandan ya yi, sannan ya fice, cikin sauri, mota biyu suka dauka, suka kai ma Unguwar su tsohon dan ta'addan sumame.
Sin yi nasarar shiga gidan, bayan artabu da musayar wuta da suka yi da 'yan ta'addan, cikin nasara suka kama shi, sakamakon ya na zaune ya na hutawa, ba abinda ya ke taimaka masa wajen yin tafiya, yaran shi wasu an kashe su, wasu an samu kama su da shi, wasu sin tsere,mata na ta ihu su na guduwa, sai da suka yi bincike sosai a gidan, aka kwashe manyan miyagun makamai, da kayan shaye shaye, sannan suka loda su a motar shiga ba biya, sai ofishin 'yan sanda.....
TAUBASHI
PAGE 32
Yau wata daya kenan tsananin ciwon kai da qirji sun matsawa Mahboob, sakamakon haka ne ya sa ko aiki ba ya zuwa, gaba daya mutanen gidan hankalin su ya tashi, Umaimah da Aaseeyah sun fi kowa shiga damuwa, ranga-ranga aka wuce asibiti da shi,Aaseeyah kuka Umaimah kuka, Noor na ta faman aikin lallashin Umaimah,fad'i take ,
"Yah Mahboob dan Allah ka tashi, kar ka mutu ka barni ni kadai, ba zan iya ci gaba da rayuwa ni kadai ba uwa ba uba, ba kuma d'an uwa ba, dan Allah Mammee ku taya mu addu'a,Allah na roqe ka ka bawa yaya na lfy"
"Umaimah ki daina wannan maganar, wa ya fada maki mutuwa zai yi? Koma me ya faru, ko ya na raye, ko ba ya raye ni zan maye maki gurbin kowa, ki daina kukan haka ya isa"
Kada kai kawai take, dan kowa zai tallafe ka a ganin ta ba kamar iyayen ka ba.
Aaseeyah na lafe jikin Mammee ta na share hawaye, da majinar da ke zuba a hancin ta saboda kuka, Mammee na ta shafa hannun ta da sigar lallashi, sun jima sosai a asibitin kafin likitan da ke diba Mahboob din ya fito, Abee ya ma magana dan ya bi shi Office.
Bayan sun zauna, Abee ya tattare hankalin shi ya mayar wajen likita,kamar yanda shi ma likitan ya fuskanci Abee da kulawa.
"Ranka ya dade, yaron ku na cikin mawuyacin hali, domin kuwa gaf yake da kamuwa da ciwon cancer, wasu daga alamomin ta duk da ba masu yawa bane sun fara bayyana a tattare da shi,ga shi ciwon ya fara qoqarin taba huhun shi, shi ne dalilin da ya sa yake wahalar fidda numfashi,"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Cancer likita? Me ya hada mu da ita? A binciken ka ka na ganin me ya jawo masa wannan ciwo, hasbunallahu wa ni'imal wakeel"
"Yallabai ka kwantar da hankalin ka, ba wai ta kama shi bane, alamu sun nuna ya na gab da kamuwa da ita, in har bai yanke alaqa da sigari ba, shan sigari na kawo illoli ga kwakwalwa, da huhun masu shan ta, su na dauke da sinadarai masu yawa wanda jiki ba ya buqatar su, illa ne gare shi, wasu sinadaran na hana wasu kwayoyin halitta na jiki su yi aikin da ya dace, taba sigari na da illoli masu matuqar yawa, wanda da masu shan ta sun san rabin su, da sun guje ta da qafafun su,dan haka ina mai baka shawara, ko da a yanzu mun masa maganin da yaji sauqi da izinin Allah, to fa dole a kula da duk wani abu da zai maida shi shan sigari"
"Mahboob din ke shan sigari? To yaushe? ......ya salam, wataqila tun a Jordan ya sha, dan dai ni ban taba ganin ya sha sigari a gidan nan ba"
"Yallabai ko ma dai a ina ya sha tabbas binciken mu ya nuna ya na shan sigari, dole ne in ana son lafiyar shi a samu a raba shi da ita"
"To...to likita, inshaa Allahu, za mu yi iya bakin qoqarin mu, na gode likita"
Ko da ya koma ya samu sauran iyalin sun yi jigum jigum, shi ma layi ya bi, ya yi zurrruuu ya na kallon kowa, Umaimah da Mammee tare da su Aaseeyah sai tambayar shi suke me likita ya ce, shi kuma ya ce sai sun koma gida.
Aaseeyah ta so zama a wajen shi Abee ya hana, saboda shi din ba muharramin ta bane, Noor da Umaimah suka bari a wajen shi,suka koma gida.
Ko da suka shiga gida qarfe hud'u ta gota, Abbu ya dawo ya na jiran su koma ya ji me ke damun Mahboob din,a parlourn Ummee su Abee suka zauna, ya zayyana masu dik abinda likita ya ce, budar bakin Aaseeyah cikin murya mai sanyi ta ce,
"Ya salam. Ashe Yah Mahboob bai daina shan sigari ba? Gashi nan ya na neman ya illata kan shi a banza ya ja min masifa"
"Aaseeyah, dama kin san ya na shan sigari? Baki taba fada min ba ko Abeen ku, ko kuma iyayen ki mata ga su nan?"
Cikin rikicewa ta ce,
"Abbu...Abbu ya ce min ya daina..ba zai sake ba...shi ...shi ya sa na ga ba amfanin na fada"
Tsaki Abbu ya ja, ya ce, yanzu dai dole ne a san ya za a yi ko da ya ji sauqi ya daina shan ta kwata kwata, domin illa ce babba a rayuwar shi.
"Haka ne Yaya, Allah ya bashi lafiya,"
"Bari na je na hada abinci a kai ma su Noor" cewar Mammee da ta musu sallama ta tafi, Ummee kuwa kyabe baki tai ta ce,
"Son a sani tusa a bokiti, ko meye na sai ta fadi su Noor za ta wa abinci kamar banda hannun dafawa d'ana abinci"
"Fateema magana ki ke?"
Yaqe ta yi ta ce,
"Ah ah, ah ah, addu'a na yi na ce Allah ya ba ma Mahboob lafiya"
"Ameeen, ni zan tafi ciki, in ta gama ka min magana sai ni na kai musu na ga ya jikin shi"
"To yayah."
Abbu daki ya shige, Abee ya wuce bangaren su, Ummee ta shiga kitchen da sauri ta dora abinci mai sauqi, a qoqarin ta na son riga Mammee gamawa abincin duk ya cabe,duk da cewa ba laifi ta iya abinci ita ma amma ta doka rashin sa'a ranar.
******************************
Mahboob ya dauki wata d'aya ya na jinya, a asibiti, duk ya rame kamar ba shi ba,sai wani irin busasshen tari yake, an saka mishi oxygen.
Idanun shi ne kafe akan Aaseeyah da ke kuka,cikin dabara dan kar a gani, duk da cewa ya fara jin sauqi akan da amma har yanzu ya na jin jiki.
Janye oxygen din Mahboob ya yi,ya yafici Abbu da hannu, Abbu da sauri ya duqa wajen bakin Mahboob dan son jin me zai ce masa.
Da kyar ya ke magana, cikin sarqewar numfashi, sannu sannu, ya ce,
"Abbu, a aura min Aaseeyah, ba na so na mutu ba aure, Annabi Muhammad n tausaya m mtasan da suka rasu ba tare da su na da aure ba, ina son ko da mutuwa zan na mutu da aure na"
Salati Abbu ya sa sannan ya ce,
"Kul..kul na kuma jin maganar mutuwa a bakin ka, wa ya ce maka mutuwa za ka yi? Ka na nan tare da mu, sai na ga yaran ku, da jikokin ku, ka ji ko? Kai dai ka riqe nasihar da muke maka akan shan taba sigari in Allah ya baka lafiya kaji ko?"
Daga kan shi ya yi, tare da yin murmushi mai ciwo, Aaseeyah cikin damqe kukan ta ta bar dakin, da ta fita ta saki kuka mai cin rai da zuciya,
'Shin da gaske Yah Mahboob zai mutu ya barni? In ya mutu ni ma mutuwa zan yi, rayuwa ta ba ta da amfani da ma'ana in ba shi a cikin ta, na amince na kuma tabbatar da cewar ina son Yah Mahboob a yanzu, ya Allah ka bashi lafiya, shi ne abin so na,'
Bayan komawar su gida Abbu ke sanar da Abee mai ya faru, Abee kuwa ya bada shawarar kawai a aikata abinda Mahboob ke so, hakan ne kawai maganin matsalar.
Bayan shawarwari da suka yi da Kaka Auwal shi ma ya bada goyon bayan a daura masu aure, in ya so ko bayan ta kammala makaranta ne an yi biki, kan nan ana saka ran Mahboob ya warware.
Sati daya da maganar nan, aka daura auren Mahboob da Aaseeyah a asibiti, ya na kwance gadon asibiti,sai murmushi ya ke, Aaseeyah kuwa na gida, indai abinda Mahboob ke so kenan, ba ta da ja, ita ma ta na son zama mallakin shi, wataqila ta ma fi taimaka masa da jinyar shi.
An daura aure akan sadaki dubu arba'in,Abbu ya damqawa Aaseeyah kudin a hannun ta da suka koma gida, sannan ya mata nasiha sosai, kowa kuma ya dora nauyin daina shan sigarin Mahboob a wuyan ta, alqawari ta musu na inshaa Allahu za ta yi iya qoqarin ta zai daina shan sigari.
Watarana har kwana ta na yi a wajen shi, bai da buri da ya wuce ya ji ta riqe masa hannun shi, in tai haka har bacci ya na samu, a haka ita ma take bacci, da safe in ta tashi, sai jikin ta ya yi ta ciwo, musamman wuyan ta,amma ba shi zai hana gobe ta sake ba.
Mahboob ya fara samun sauqi sosai, shi da kan shi sai ya ji ya na kyamatar sigari, dan ko tuna warin ta ya yi, sai ya ji tsoro da tsanar ta sun kama shi, ta kusan sa shi macewa bai ci moriyar rayuwa da matar shi Aaseyah ba.
Yau ne ranar da aka sallami Mahboob daga asibiti, kuma yau ne suka tattara za su koma gida, Noor ke tuqa motar da suke ciki,Shi Umaimah, Mahboob da Aaseeyah, su Abbu kuma na gaban su, shi da Abee, Mammee da Ummee na gida, domin tarbar masoyin su Mahboob.
Sun kusan shiga layin unguwar su, wata baqar mota mai girma ta sha gaban su,gilasan ta ma baqaqe ne, da wata iriyar qara da tada qura sosai ta tsaya,kamar qiftawar idanu, suka bufe gefen da Aaseeyah take suka dauke ta a hannu, suka wurga a tasu, kamar qifatawar idanu, har sun bace da ita.
Qura sosai suka bude su da ita, ta yanda ba su ganin komai, sai da ta lafa,Mahboob kuwa suma ya yi da ya fuskanci me ya faru, a guje Noor ya isa gida, cikin tashin hankali ya kinkimo Mahboob din da taimakon Umaimah,suka fidda shi suka aje a qasa, Abbu da Abee da ke tsaye ba su jima da isa ba ne suka nufe su da gudu, tare da tambayar
"Lafiya? Me ya same shi kuma? Lafiya qlou fa muka rabu a asibiti,"
Cikin Kuka Umaimah ta ce,
"Abee sun sace Aaseeyah,wata baqar mota ce ta zo ta tsaya gaban mu, ta tada qura, suka sace Aaseeyah, shi ne dalilin suman Yah Mahboob"
Jijiyoyin kan Noor sun tashi, sun yi burdun burdin,da sauri ya shige mota, Abbu na kiran shi, amma inaaa, bai zame ko ina ba, sai gidan talabijin da ya ke aiki, nan da nan ya shiga bangaren yad'a cigiya, da tallace tallace.
Ya sanar da batan Aaseeyah, cike da qunar rai, da zafun zuciya, ya na gama sanarwar ya fita ya samu kujera ya dafe kan shi, sai ga hawaye,
"Su waye suka sace ki qanwa ta? Su waye wadannan mutanen?"
Kamar tambayar wani yake, sai kuwa ga amsa ya samu,
"Su Gazaa ne suka sace ta, domin kuwa su na sace ta suka mana waya suka sanar da ofishin mu, sun yi haka ne saboda su na son police su sakar masu shugavan su, kuma mahaifi a wajen Garzali"
"Cp ban fahimta ba,meye had'in Aaseeyah da wannan case din? Me za su amfana da shi? In sun kama Aaseeyah?"
Dan gyara tsayuwa CP Aliyyu ya yi, sannan ya sosa qasan kunnen shi, ya ce,
"Sun zurfafa a binciken su,cikin watannin da mahaifin su ya yi a wajen mu, sun gano cewar ni ina son Aaseeyah, abu d'aya ne suke zargi, wanda ba gaskiya bane, a cewar su Mahboob ne ya yi shune ma gidan nasu muka kai musu sumame, dan haka daukar fansa ne akan mu"
Wani kallo Noor ke ma CP, ta ya ya san Aaseeyah har ya fara son ta? Shin Aaseeyah ma na son shi? Ko shi ya sa kwanaki ta masa tambayoyi akan CP Aliyyun?
"Yanzu ba lokacin sanin How? Why? And when bane, lokaci ne na nemo Aaseeyah, da kuma ceto rayuwar ta a hannun wadan can 'yan ta'addan"
Miqewa suka yi, suka fita,zuwa ofishin su Aliyyu.
Noor ya ma Abee waya ya sanar da shi komai, nan da nan ya sanar da Mammee da su Mahboob abinda ke faruwa, Mammee ta kasa kuka, ta kasa magana, ta na nan zaune ne kawai shiruuuu, ta na tasbihi a ran ta, so take ta samu sauqi a zuciyar ta, hankalin ta ya dawo jikin ta kan ta tanka.
Mahboob kuwa ko kunya ba ya ji, kuka kawai yake abin shi, ji ya je qirjin shi na matsewa matuqa, hankalin shi na qara tashi a duk wata daqiqa.
Ko da suka isa ofishin CP Aliyyu, sun tadda su suna qoqarin downloading videon da su Gaza suka tura masu.
Wajen zama Cp Aliyyu ya basu, nan suka zauna Video na gama budewa, Mamme ta kalla, kawai sai ta sanya kuka mai qarfi da tsanani, tare da kiran sunan Aaseeyah, cikin shasshekar kuka........
Toooo makaranta mu dan tsahirta anan zuwa wani jiqon.
TAUBASHI
PAGE 33
Da sauri Mahboob ya rufe laptop din, saboda kar CP Aliyyu da yaran shi su ga mishi mata a wannan yanayi, (su Gazaa fa da suke kalla)
Kuka Mammee ta ke ta na neman taimako wajen Allah, Abee kuwa hankalin shi ya tashi, saboda da dikkan alama ta musu surutun nata na rashin kunya ne ya sa suka jibge ta, bakin ta da hancin ta jini ke zuba irin mai kaurin nan mai hade da yawu, Sam ne a wajen ya ke gana mata azaba, sun cire mata abayar ta da ta sanya a saman qananan kayan nata, wando ne pencil da ya matse ta sosai, ya fidda shape din jikin ta, sai qaramar vest fara mai siririn hannu, ko bra ba ta sanya ba, ita da tsirara ba su da maraba, gashin kan ta duk ya baje a fuskar ta, hannayen ta a daddaure gefe da gefe, tsayuwar ma na neman gagarar ta.
Video call ne ya shiga wayar CP Aliyyu? Da sauri ya dauka ya fara magana cike da gargadi, da masifa.
"Idan wani abu ya same ta....ba zan taba kyale ku ba, i will hunt u down kamar mafarauci da naman shi, sai na kashe ku d'aya bayan d'aya"
Da sauri Mahboob ya amshe wayar, ya fara leqa wa, ji yake kamar ya matsar da Sam ya kalli Aaseeyah, da ke fidda nishin azaba,
"Sam...Sam me nai muku za ku kama Mata ta, kar ka manta da abotar da muka yi abaya" Cikin tashin hankali, da zabura CP Aliyyu ya ce,
"Mata ! Wace matar ka? Ka na da cikakken hankali akan ka kuwa? Wannan fa budurwa ce, qawar qanwa ta Amatullah ce"
Ba wanda ya kula shi domin duk sun raja'a kallon Aaseeyah da ke cikin mawuyacin hali,
"Sam plss ku saki mata ta, na amince ku zo ku dauke ni, ko mai za ku min ku min,ko kashe ni za ku yi ku kashe ni,"
"Ohhhh Old friend, ai fad'an ba na ka ba ne kai kad'ai, fad'an na ku ne,sannan ni tun da ban taba son ka a matsayin abokin mu ba, na tsane ka Mahboob, na tsane ka,....amma tsaya ma.. shin ba ka da labarin abokin ka CP Ali ya na son matar ka? "
"Me ka ke cewa?" Mahboob ne ya juya ya na kallon CP Aliyyu, sunkuyar da kai ya yi, tare da shafa qeya cikin rashin nutsuwa, zai magana Abee ya katse su.
"Wannan ba lokacin sanin waye ke son waye ba, ku sama mana mafita yarinya ta na wajen wadancan azzaluman mutanen"
Suna tsaka da magana Gazaa ya shiga, fuskar nan kamar hadari, direct wajen Aaseeyah ya nufa, Sam ya dinga haska musu suna kallo, Mammee ta toshe bakin ta, idanun ta na tsiyayar ruwan hawaye,
"Hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem,hasbunallahu sa yu'utinallahu min fadhlihi inna ilallahi ragibuun, ya Allah ka kare min yarinya ta da mutuncin ta daga wajen azzaluman can, Allah ka dawon da ita gida lfy"
Wadannan tasbihi da addu'o'i ne ke fita daga bakin Mammee, domin addu'a ce kawai maganin halin da suke ciki. (Addu'o'i ne da in bawa ya yi su komai ya roqa da izinin Allah, Allah zai biya masa buqatar shi)
Hannu Gazaa ya sa ya dago fuskar Aaseeyah,ya matse bakin ta, sai da ta sake qarar azaba,sannan ya ce,
"Za ki sanar da ni inda saurayin ki ya boyen mahaifi ko sai na yanke maki kai?"
A hankali ta bude idon ta da ya yi jawur, ta ce,
"I wish na san inda ya ke, da da hannaye na zan saka mishi fetur, na kyasta mishi ashana, ya na ihu, ya na neman taimako, ni kuma ina kallon shi ina dariyar jin dad'in rage mugun iri da akai a cikin al'umma," ta tofa mishi yawun bakin ta mai tattare da jini,sakamakon sake matse mata bakin da ya yi ya sake fashewa.
Wata iriyar dariyar takaici Gazaa ya yi, a duniya bai had'a mahaifin shi da kowa ba, da hannun shi ya dauki ran mahaifiyar shi, bayan ya girma Baban shi ya bashi labrin qarya game da mahaifiyar shi, tunda ta haife shi ta yar da shi ta ma mahaifin satar kudin shi kaf, ya rasa ya zai ya kula da shi saboda rashin kudi, shi ne dalilin shigar shi fashi da makami.
Lokaci daya ya daure fuska, kamar bai taba dariya ba, kallon waje ya yi, ya d'aga murya, ya ce,
"Muji ! Kawo min fetur"
Da sauri wani basamuden baqin mutum ya je hannun shi dauke da bindiga zungureriya,ya na gama jin umarnin uban gidan nashi ya fice,
Cikin tashin hankali su Mahboob ke magana, kowa ya rikice, qoqari yake ya fadi maganar da zata sauqaqa zuciyar Gazaa karya kashe Aaseeyah, wani dan sanda ne ya shiga ya qame gaban CP Aliyyu, ya ce,
"Yallabai har yanzu ba mu gano inda suke ba,mun kasa sanin dalilin da ya sa na'urar ba ta linking din mu da su"
Cike da bacin rai Aliyyu mazan fama ya daki table din gaban shi, ya kalli wayar, ya kula Aaseeyah magana ta ke, dan haka tsawa ya buga, kowa ya yi tsit, har Abbu, ba wanda ya sake cewa kanzil.
"Ku sarara Aaseeyah na magana, Aaseeyah pls don't say anything stupid again,na amince na rasa ki tun kafin labarin soyayyar mu ya fara ya qare,amma ba zan so ki mutu a hannun wadannan azzaluman ba, dan Allah ki bar cewa komai, ki rayu ko dan mahaifiyar ki da mijin ki,na roqe ki"
Cikin dasasshiyar murya ta ce,
"In yau bai kashe ni ba, sai ya qare rayuwar shi ya na dana sani,"
Mammee ta san halin kayan ta, dan haka ta budi baki ta ce,
"Aaseeyah kar ki sake magana, domin Allah, ba zan iya hakurin rashin ki ba"
Dariya Sam ya saki, sannan ya ce,
"Na jima ban ga bacin ran Oga Gazaa hk ba, yau wannan mai bakin akun sai ta baqunci lahira,"
Muji ya kawo fetur, ba bata lokaci, Gazaa ya bude, ya tuttula shi a jikin Aaseeyah, sai da ya qarar da shi tasss, sannan ya zaro ashana a wandon shi, ya kalli videon,sannan ya kalli Sam, da alama magana su ka yi da ido, Sam ne ya manna fuskar shi jikin Camera dadai Gaza ya zaro ashana, ya na qoqarin kyastawa, ya furta,
"Bummmmmm" da qarfi.
Nan take ya kashe video call din, Mahboob ya sake wayar a qasa, shi ma ya fadi, idon shi biyu ba suma ya yi ba, amma ya kasa motsawa, taimaka mishi su Abbu suka yi, tare da zaunar da shi a kujera, CP Aliyyu na ganin irin damuwar da Mahboob ya shiga sai ya manta da ta shi damuwar, bindigar shi ya dauka, tare da sake loda mata harsashi, ya debi wasu ya zuba a inda ya dace a kayan shi, sanan ya fita, su Abbu ma rufa msa baya sukai, Mahboob da kyar yake daga qafar shi, sake hada ido suka yi da Aliyyu, tausayin Mahboob ya gama nakasa zuciyar shi.
Abbu ne ya ce,
"Yallabai yanzu ya za a yi?"
"Ku koma gida, inshaa Allahu yau komai zai zo qarshe"
Mota suka shiga, wasu 'yan sandan Aliyyu ya ware ya ce su je su kula da gidan su Abee, sannan ya dau wayar shi, ya dinga qoqarin kiran layin su Gaza, bugu kadan ya yi suka daga,
"Mu yi wani abu mana, ku ban Aaseeyah na baka mahaifin ka,"
Hannu ya sa ya yi nuni da a kawo mahaifin Gazaa,
"Ta ya zan tabbatar ba ambush za ku had'a mana ba?"
"Na maka alqawari ba wannan maganar, amma fa tabbas bani kadai zan zo ba, dan mu ma ba mu yarda da ku ba"
Dariyar mugunta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 41