tare da addu'ar Allah ya jiqan magabatan su, ya amsa da.
"Ameen,"
"Kin ga waccan 'yar rigimar taki, ta yi baccin ta, bari na gama na kai ta daki"
"Yo ba dole ba, tsokana da rashin ji irin na Aaseeyah sun isa gajiyar da ita, ba dan ma ba mai yawan bacci bace har na rana sai ta yi"
Dariya suka yi a tare da suka tuna fitinar ta, Mammee ce ta maida ta dakin ta ta mata addu'a ta fita, ta ja qofar a hankali sannan ta bi mijin ta d'aki, dan taya shi wanka da shiryawa.
**************************
Alhaji Muhammad Abdul mudhalleeb Jordan na shiga bangaren shi ya tadda ba kowa, hatta da Ummeen su Noor, kada kai ya yi, cikin takaici na rashin kulawar ta a gare shi, a ce mace kamar kasa, nan da nan ta yi bacci, a qalla ko za tai baccin a same ta da niyyar tarar mijin ta, bacci ya ci qarfin ta, ilai kuwa ya na murda knob din qofar dakin su, ya gan ta shame shame ta na ta kwasar baccin ta, 'yan siraran qafafun ta dogaye na yashe a saman gado, kowanne ya kalli nashi waje, ta sanya rigar bacci ta dora zani a saman ta, cikin tsaki da takaici ya ajiye jakar shi, ya nufi kitchen, ko azziqin aje masa abinci saman teburin cin abinci ba ta yi, sai jifa jifa, sanda ta ke da buqatar shi,to fa xa ta jira dawowar shi, kuma zai samu komai tsaf yanda ya kamata, ko da ya wuce qofar dakin Noor karatun qur'ani ya ji ya na tashi daga MP, wata nutsuwa ce ya ji ta kama shi, murmushin jin dad'i ya yi ya isa kitchen din, zuba taliya ya yi da ya tsana a abinci, da miyar kaji, ya dau juice ya dora a trey, ya dau fruits ya zuba, ya saka cup da duk wani abu da zai buqata ya tafi parlour ya zauna, sai da ya ci ya qoshi, sannan ya bar komai a wajen shi ma y tafi, a ran shi ya na ayyana,
'Tunda banda qimar da za a ajen abinci kan na dawo, ai an yi aikin gyara waje'
Wanka ya yi sannan ya bi lafiyar makeken gadon nasu tare da yin addu'ar bacci ya kwanta,sai juyi yake ya na sakewa tare da siririn tsaki, ga mace har mace kyakkyawa abin son kowa amma ba halin biyan buqata sai sanda ta so, in ba ta so ba sai dai ya kalla ya dauke kai, ba dan Allah ya sanya mishi imani ba, yanda ya ke haduwa da mata kala kala, har a wajen aikin su akwai mata, ai da sai ta jefa shi wani hali,in ya yi yunqurin qara aure ta tada bala'i da masifa, ta ce har Zainab ta mutum ba wanda ya mata kishiya, ga Subai'a nan ma,ita kadai ce, dan haka ita ma ita d'aya za ta rayu a gidan ta, dalilin haka ne shi ma ya qi daukar mata mai aiki duk nacin ta, da ta matsa masa ya ce, Zainab da Subai'a ma ba su da mai aiki,dan haka ita ma sai tai hakuri,ta yi qorafin ta fisu dawainiya,ya mata kallon ke 'yar rainin hankali ce ya kyale ta, kullum a haka suke, ya qi sam a dau mai aiki, duba da sun fita tsafta a hakan duk da ita ma ba qazama bace, amma ba za a kira ta mai tsananin tsafta kamar su ba,wani dogon tsaki ya sake ja, ya janye abun rufar da qarfi ya rufe har kan shi, cikin bacci ta ji an fizge bargon, a firgice ta miqe ta na kiran,
"Su waye? Waye nan?"
Ko budewa bai ba, ya lumshe ido ya na jin takaicin ta a ran shi, ba a fi minti daya ba ya ji minsharin ta, alamar ta koma baccin ta kenan.
Tsaki ya ja, sannan ya fara istigifari zuwa hailala, har bacci ya dauke shi.
*****************************
"Hello...Hello...Yah Mahboob,wai yaushe za ka dawo ne? Kai kullum sai dai ka ce ka na nan tafe, har yanzu ba ka iso ba, inda kk da nisa ne? Bangon duniya ne?"
Da hannu Mammee ke mata daquwa, amma ta qanqame wayar ta na wani jijjiga ita a dole an bata haushi.
Daga dayan bangaren murmushi mai sauti ya saki, sannan cikin hausar shi da ba sosai ya ke mai kyau ba, saboda yanayin Arab accent da ya ke da shi, ya ce,
"Ki yi hakuri Mahboobatee, ina nan tafe kin ji? Ki yi ta kallon hanya daga gabas zan zo watara,"
"To ni ina na san maka wani gabas"
Dariya ya yi sosai sannan ya ce,
"Ashe Aaseeyahn Abee ba ta sallah?"
Nan fa ta daddage an ce ba ta sallah, ta hau bayani,
"Habaa Allah ya kiyaye, yanzu kai aka ce maka bana sallah, ai na zama kafira kenan, ina sallah kai, ina Asuba, azahar,la'asar, ina magrib, isha'i ne dai watarana bana yi, amma shi ma bacci ke dauke ni, ba laifi na bane,gabas din ce in ba sallah zan ba, ba na gane wa"
"To duk sanda kk fara gane gabas ki min waya ina nan dawowa inshaa Allah,"
"To Yayan mu,dan Allah kar ka kira su Umaimah, ka rama mun kiran ka da sukai shekaran jiya ba su ban ba,"
Shiru ya yi, dan ya na son jin muryar qanwar ta shi yau, amma kuma ba zai iya ce ma Aaseeyah ah ah ba,
"To inshaa Allahu ba zan kira su ba sai gobe"
"Ka ma kira suuuu za su fadan neee, ai ba ma boye ma juna komai,"
Dariya ya sake yi, shi dai ya na son jin shirirtar Aaseeyah, wato ya ma kira su take fada masa,
"Ba san kira ba ma,sai an jima, zan fita wajen aiki,a yi karatu da yawa,Assalamu alaikum"
"To Allah ya bada sa'a, wa'alaikumussalam ustazu"
Ta na kashewa ta miqawa Mammee waya ta na fadin,
"Yah Mahboob ba dai iyayi ba, a yi sallama kafin a yi waya bayan an gama a yi sallama,"
"Wai ke me ya sa baki da kunya ne? Duk abinda na ke nuna maki ba ki dauka, ba fa kowacce magana ba ce in ta maka dad'i a rai za ka furta ta a bakin ka ba, sa'an ki ne kk cewa ya cika iyayi?"
"Mammee yi hakuri bari na je kafin su yi ta jira na, Mammee ki min addu'a kar a daken na manta ban home work di na ba na maths, kin san na tsani calculation"
"Tsaya surutu kin bata sama da minti sha biyar anan,kuma ba addu'ar da zan maki sai dai ma na ce Allah ya sa a dake ki, tunda ba ki son karatu, ko na ce ki zo mu yi gudu kk"
Nan da nan idon ta ya kawo kwalla, ta san addu'ar mahaifiyar ta, ta sha mata addu'a kuma ta na ganin karbuwar ta, ta tabbata yau ko mai masu Math bai dake ta va wani malamin sai ya jibge ta a banza.
Zafi ake amma hakan bai hana ta rugawa dakin ta ba ta fito da kaya masu yawa ta nemi rigar sanyi ta saka ta fice a guje, duk kiran da ake kwala mata ba ta waiga ba, sai da ta isa bakin motar da Umaimah ce da Ummu Suleim a ciki su na jiran su ita da Yesmeen.
"Ai in ba ku makara ba baku jin dad'i"
"Eh din, makarar ma kwarewa ce, wani ko ya je ya makaran ma kasawa yake"
Shiru Ummu suleim ta mata, dan in ba haka ba, kan su isa sai ta saka Aaseeyah kuka in sun je kuma sai ta mata sharrin da za ta ja mata duka a banza,Yesmeen na shiga driver ya ja suka tafi, sai hayaniya suke a motar.
Su na zuwa ana qoqarin rufe gate, da ihu Aaseeyah ta ke ma driver magana ya yi sauri kar Malam Salisu tumbi ya rufe gate, ai kuwa su na isa ana rufe gate din, wani kuka ta sake saboda tunawa da addu'ar Mammeen ta, ta tabbatar amsuwar ta ce ta zo, daga baya ta dago ta na share hawaye ta na dariya, su Umaimah na ganin haka kuwa su ka hau roqon ta kar ta ja masu duka, ko kallo ba su ishe ta ba ta saba jakar ta ta fice...........
Pls
Read
Understand
Comment
And
Vote.
💅🏻 TAUBASHI (COUSIN) 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
Page 3:
Wani shirgegen mutum na hango qato sosai ga tsaho ga qiba, dantsan shi na hannu ya yi cinyar wata yar duma-dumar, baqi ne sosai sai maiqo ya ke kasancewar yana yi ne na zufa, kumatun shi kamar an sinqe biredi dan d'ari, idanun shi da alama kan ya yi qiba manya ne, dan in ya zaro su ana dan ganin girman su, amma in ba zaro su ya yi ba, sai mutum ya rantse dan uwan su Jet lee ne,ya na da tafka tafkan zane a kuncin shi na uku uku,su na kyalli,hannayen shi da qafar shi yan gudil-gudil, salati su Umaimah suke su na addu'a saboda dukan shi akwai zafi, ko bulala daya ya maka sai ka ji a jikin ka, balle ta wuce daya.
Bayan driver ya ajiye su Aaseeyah suka tsaya a bakin gate din, su ka gaishe shi yaqi amsawa, shi a dole ga masu laifi, wasu yara aka ajiye su biyu maza, za su kai shekaru sha hudu zuwa biyar,sai wani bubbudawa suke, su ga yaran masu kudi,su na hada ido da Malam Salisu Tumbi su ka nutsu, kallon Ummu Suleim daya da ake kira Jubair ya yi, ita ma kallon shi ta yi ta dauke kai, dukkan nin su suna raya wa a zuqatan su, yawa ne a dake su gaban junan su, dan haka suka fara ba da hakuri ba qaqqauta wa.
Wata iriyar murya na ji ta yi magana a zato na wani yaron ne a kusa ya ke magana, ina daga kai gefe na na ga ashe Mal. Salisu Tumbi ne ke magana, murya ce siririya sam ba za ka ce qaton mutum kamar shi bane mai ita.
"Sai an fito first period za ku shiga, tunda ba ku jin magana, kan ku shige sai kowa ya karbi bulala uku-uku"
"Tabdijam, ai yasin ba qaton da ze daken"
"Wanne mara kunyar ke magana ina magana?"
Shiru ba wanda ya yi magana, dan har su Jubair su na shakkar Aaseeyah, in ka bata ran ta sai ta wahal da kai.
Dan bude qofar ya yi ya raba jikin shi, ya na sake tambayar wanda ya yi magana, ta daidai qasan qafar shi akwai dan fili kadan, ta nan Aaseeyah ta faki idon kowa ta kutsa ta falla da gudu cikin makarantar,Mal. Salisu Tumbi shi ma taka mata baya ya yi, ta na juyawa ta hango shi a juge ya na daga qafafun shi da kyar zuwa gare ta, zaro ido ta yi waje, ta qanqame jakar ta da ke bayan ta, da lunch bag din ta dake kafadar ta,tare da tattare hijab din ta ta riqe da kyau, har ta yi hanyar ajin su ta ga Maths teacher din su, tai kwana, 'yan ajin na hango ta a wannan yanayin sika hau gintse dariya, Mal. Salisu kuwa gudu kawai yake tumbin shi da nonuwa su na sama da qasa, duk ya hada uwar zufa, sai haki yake.
Bayan ajujuwan makarantar ta dinga ketawa da shi ta na dawowa, sun zaga kamar sau uku, ya tsaya ya na haki, ya kasa magana, sai nuna ta yake da yatsa, ita kuwa ta na daga nesa ta na dariya, da alama ko sau dari za a zaga ba zai dame ta ba sam, ji ya ke kamar zai shide saboda rashin iskar shaqa.
Wani malami ne ya isa wajen shi ya kama shi da kyar ya kai shi jikin dandamalin qofar azuzuwa ya taya shi ya zauna, idanun shi sun kada sun yi mugun ja, kallon inda Aaseeyah ta tsaya ya yi, ya ga ba kowa, lumshe idon shi ya yi, ya na lashe busasshen leben shi qanana ya na tunanin irin azabar da zai gana ma Aaseeyah duk sanda ya kama ta.
Ita kuwa ba ta shiga aji ba sai da ta ga malamin Maths din su ya fita, sannan ta fada, su Umaimah da ke waje ma tuni sun shige ciki,labari fa ya baza makaranta, kowa na ta dariya, dan ba yau dama Aaseeyah da Mal. Salisu suka saba drama ba, sai dai fa duk sanda ta shiga hannun shi itama ta na jin jiki.
Ranar duk wani motsi da Aaseeyah za ta yi a tsorace ta ke yin shi, su kuwa su Ummu Suleim suka hada kai bayan break suka je suka bashi hakuri, ya ce ya yafe musu, amma kar su sake makara, ya musu nasiha sosai akan rashin amfanin makara, da amfanin zuwa makaranta da wuri.
Sun ji dad'i da ya yafe musu, hankalin su ya kwanta, dan haka suka samu Aaseeyah cikin qawayen ta suka shawarce ta da ta je ta bashi hakuri, ta danna soyayyar doya a bakin ta wadda ta ji kwai da sauce din hanta,ta lumshe idanun ta da ke sawa yara na manne mata saboda su, ta ce,
"Ba hakurin da zan bashi, ko na bashi hakuri yanda na sa ya yi gudu kamar tsohon kare na yi imani sai ya daken, gwanda ya daken da hujja da na bashi hakuri kuma ya daken"
"Shi kenan, ke kk sani, mu dai ya yafe mana"
Hira su ka ci gaba da yi da qawayen ta, ta na basu labarin yanda ta sa malamin gudu, sai kwasar dariya suke, da damar qawayen ta su na tare da ita ne saboda kyaun ta, da kuma kasancewar abincin da take zuwa da shi mai dad'i ne, ba wai dan ita din mai qoqari bace,sam ba za a saka ta cikin yara masu hazaqa ba, baya baya dai.
Sadaf sadaf ya taka ta bayan ta, ga ni ta yi yara na darewa ana guduwa, yunqurawar nan da zatai dan guduwa saboda jikin ta ya bata Mal. Salisu ne, kawai ta ji ya yi ram da ita, ihu ta kwalla mai qarfi, tare da shure-shure, amma inaa ba ta isa kubuta ba, ranar Aaseeyah ta daku matuqa, ta yi kuka har ta ji ba dadi, ko da ta koma aji har an ci period daya, yara na ganin ta kowa ya kauda kai, dan yanzu da an hada ido da ita ta na iya huce haushin akan mutum.
Ko da aka tashi sun kai minti sha biyar a waje kafin azo daukan su, jikin ta har ya yi zafi saboda kukan da ta sha,su na isa gida ta wuce bangaren su, ko cire kayan ta bata yi ba ta kwanta a kujera, TV ce kawai ke aiki, ba kowa a parlourn, ta jima a haka har bacci ya dauke ta, ko da Haj. Subai'a ta fito ta gan ta kwance kada kai ta yi ta tattara jakar ta da takalman ta da lunch bag din ta ta wuce ta aje su inda ya dace, sannan ta dawo dan cire mata safar ta, jin jikin ta ta yi da zafi zauuu, da sauri ta daga ta ta raba ta a jikin ta, su na hada ido Aaseeyah ta fashe da kuka har ta na shessheqa, ita a dole an ci zalin ta,
"Aaseeyah me ya same ki? Ina ke maki ciwo?"
"M...m..maaa...malam..neeee yaaa dakeee niii"
Cikin tsananin bacin rai Haj. Subai'a ta sake tambayar ta da,
"Wanne malam din? Me ki ka yi da zai maki bugun sa'anni har ki kwanta ciwo haka?"
"Mmalaam Salisu Tumbi,"
"A gaskiya na gaji, na gaji da dukan da mutumin nan ya ke maki kamar shi na haifar wa ke ya daka, an fada mashi daga sama ki ka fado? In Abeen ki ba zai magana ba ni zan je gobe da kai na, na same shi, wannan ya zama na farko ya kuma zama na qarshe da zai dora hannun shi akan ki"
Hawayen wahala ne kawai ke zuba a idon Aaseeyah, da kyar ta iya tashi suka shiga ciki da Mammeen ta, wanka ta mata da ruwa mai dumi, sannan ta shirya ta cikin shadda doguwar riga ta daura mata dankwalin ta, ta sanya mata pant kalar shaddar ta, ta kwantar da ita a gado tare da rufe ta, nan da nan bacci ya dauke ta.
Da sallama Ummu Suleim da Yesmeen suka shiga sun biya mata makaranta, domin ta na qaunar islamiyya, ta na kuma ba da mahimmanci wajen karatun islamiyyar, bayanin rashin lafiyar ta Mammee ta musu, nan sika bata labari suma akan abinda ya faru, sannan suka bata labarin yanda ya yi punishing din ta, a nan Mammee ta gano Aaseeyah ce mara gaskiya, amma abin ka da iyayen zamani, duk da haka sai ta nuna ai ita yarinya ce me ya sa ba zai yi hakuri ba.
Tafiya suka so yi ba tare da sun jira ta ba tunda ba ta da lafiya, har sin fita suka gan ta ta fito a guje da jakar ta a hannu, hijabi a hannu,da dukkan alamu ba a san da fitar ta ba, gaba ta yi su ka bi ta a baya, su na fita suka hau tambayar ta ya akai ta taho ita da bata da lafiya,
"Zama waje d'aya tsautsayi ne, ina da karbar a dashe wajen Hafiza yau,kun sanni akwai cika alqawari"
"A baki da lafiyar ma sai kin yi fada, Aaseeyah ina tausaya maki sanda zaki yi fada da wanda ya fi ki qarfi" inji cewar Yesmeen.
"Ai ba qarfin jiki ne nasara ba, in shi ne ai da tuni ba ni a duniya"
Shiru sukai saboda sun san ba za su samu nasara akan Aaseeyah ba wajen magana.
Ko da suka je makaranta aji suka shiga suka hau karatu da sauran dalibai kafin malam ya isa.
Hafiza da Aaseeyah na ma juna kallon kallo, kowa da abinda ke saqawa a ran shi, Aaseeyah kuwa murmishin ta take zabgawa na mugunta, gaban Hafiza sai faduwa yake, ji take dama jiya bata shiga gaban Aaseeyahn ba a fanfo wajen alwala har ta watsa mata ruwan kwata, daga baya Aaseeyah ta maida hankali wajen qarin karatun da ake musu, su na cikin suratul Noor, a cewar ta ta na son surar saboda Yah Noor din su, kwata kwata ta daina ma hada ido da Hafiza, hakan ba qaramin kwanciyar hankali ya kawo wa Hafizan ba, sai addu'a take a ran ta Allah ya sa Aaseeyah ta manta, ganin har an kusan kiran sallah ba su sake hada ido ba Aaseeyah na harkar gaban ta ne ya ba wa Hafiza damar kwantar da nata hankalin ta ci gaba da nata karatun ta daina kallon Aaseeyah.
Ana kiran la'asar kowa ya fita domin yin alwala, gora ce qarama ta Faro a maqale a hannin Aaseeyah, a bakin kwata ta faki ido ta debi ruwan ta ta rufe, sai da ta bari Hafiza ta idar da alwala ta fito zuwa inda sike sallah kawai ta ja ta da hijabin ta, ta matse ta, tare sa kai mata wannan ruwan bakin ta, duk da Hafiza ta qi shan ruwan ta na ta qoqarin kwacewa bai hana ruwan shiga bakin ta ba, tare da bata mata kayan jikin ta, da kyar manyan su na makarantar suka kwaci Hafiza, sai kuka take,ita kuwa Aaseeyah fadi take ta na kumawa,
"Gobe ma in uwar ki ta haife ki da jini ki zuban ruwan kwata in magana ki ce min kin zuba din, bar ganin ki wata fakam fakam, ni ba na jin tsoron kowa,"
Wata ce a wajen ta ce,
"Laa bakin Hafizan ma jini yake, a kai su wajen Malam Buhari kawai,"
Ai Aaseeyah na jin kaiwa wajen malam da ta keta da mugun gudu sai ga ta a sahun gaba, duk neman da aka dinga yi mata haka suka gama ba su gan ta ba, suka gaji suka bari, nan Ummu Suleim ta taimaka ma Hafiza ta wanke hijabin ta, ta sake alwala lokacin har an tada sallah, suka je suka yi tasu, ta na ta bata hakuri,tare da gargadin ta akan shiga harkar Aaseeyah ko dan gaba.
Ko da aka tashi cike da murna Aaseeyah ke sake basu labarin abinda ta aikata hankalin ta kwance,har fadi take,
"Ni da na rama ma sai na ji qarfi a jiki na kamar kar mu koma gida da wuri mu yi wasan yashi"
"Ehhh mu yi wasan yashi"
Inji cewar Umaimah da Yesmeen, nan fa Ummu Suleim ta biye musu, suka diba da gudu zuwa wani waje da hanyar gaba daya ba ta da dad'in bi da abin hawa saboda yashi, nan suka dinga wasa ga magariba ta yi, su na tsaka da wasa Aaseeyah ta ce ita dai fitsari take ji,ga duhu ya fara shiga,
"Mu je gida dare ya fara, sai ki yi, lokacin sallah ma ya yi ga shi can an shisshiga masallaci"
"Ke Ummu Suleim dinnan sai ki ta katsewa mutane wasa, in za ki tafi sai ki tafi"
Kamar abun wasa suka ga Aaseeyah ta jujjuya ta kalli hanya, ba mutane sosai, kawai ta cire pant din ta, ta baza hijabin ta da rigar ta, ta yi kamar ta zauna a wajen, ta tsula fitsarin ta ta miqe, Yesmeen na ganin haka ta hau dariya itama ta yi, Umaimah ma haka, can Ummu suleim ma ta yi nata, nan fa suka maida abun wasa, su na ta dariya, tsinke Aaseeyah ta nemo ta dinga qoqarin juya nata ta na fadin,
"Bari na masa juyin waina"
"Gaskiya ku zo mu tafi gida, yau sai Ummee ta dake mu, Yesmeen kin sani ko?"
"Ke Ummu Suleim dinna shegen tsoron tsiya ne da ke,"
"Ehh na ji,ni dai na tafi"
Aaseeyah yi ta yi kamar ba zata tafi ba, ta tsugunna, har sun sakankance ba zata tafi ba, ta kwasa da gudun tsiya sai gida, bayan ta suka bi suna mata masifa akan za ta riga su zuwa gida.
Da sand'a ta shiga dakin ta, saboda Mammee na azkar din yamma, kayan ta ta cire ta watsar a qasa kamar kullum, ta shiga tai tsarki ta yi alwala ta tada sallah, ko da ta idar sai ta kwanta ta yi lufff kamar mara lafiya.
Mammeen ta na shiga ta gan ta a langwabe, duk sai ta tausaya mata kuma, da har ta na tunanin cin mutuncin ta akan dad'ewar da sukai,
"Sannu Aaseeyah ina ke maki ciwo?"
"Kai na ke ciwo Mammee kamar ana ta dokar min shi"
"Sannu bari na kawo maki abinci ki ci ki kwanta ko?"
"To Mammee"
Ta na fita ta miqe ta na rawar ta tsira daga fada, wataqila har da duka ma, ta na tunawa da su Umaimah dariyar mugunta ta kama ta, ta cire hijabi dan sad'ad'awa ta je ta ga dukan da za su sha Mammeen ta ta dawo dauke da abinci a qaramin trey da lemu a glass cup sai magani a gefe, wayancewa ta yi ta fara hamma tare da fadin,
"Ni na ji kan ma ya daina ciwo, saura kadan"
"To masha Allah haka nake son ji, ci abinci ki sha magani, bari na je na qarasa abinda nake"
Ta na fita ita ma ta fice, ta qofar kitchen, ta bude a hankali, sai wajen su Umaimah,ko da taje dukkan su kuka suke, da alama sun daku, idanun su ya yi jawur fuskokin su duk sun yi ja,sai shan majina suke, Umaimah kuwa har lokacin kuka take, dariya Aaseeyah ta dinga yi har da hawaye, daf za ta zauna kusa da umaimah taji motsin fitowar Ummee da gudu tai baya ta labe, fada ta ji ta na musu ta na fadin,
"Shahsahshan banza shashashan wofi, in banda girman jiki nawa Aaseeyahn take? Amma ita ce za ta dinga jagorantar ku wajen rashin ji,ko kunya ba ku ji, ba sa'an ta a cikin ku, amma ta fiku wayo da komi, ita ta na can uwar ta na lelen ta, ku ku na nan kun ci dan banzan duka, tunda ita ba kwaba ba hantara ce, komai tai daidai ne, to ni ba zan dau iskanci ba, uban ku za ku ci, duk wanda ya sake zuwa makaranta ya wuce lokacin dawowa sai na ma yaro dukan dahuwar gandar raqumi,"
Ai da jin haka Aaseeyah ta kece da wata mahaukaciyar dariya ta fita a guje, su ma da ke wajen sai abun ya basu dariya,kallon su Ummee ta yi cike da takaici, da alama dai Aaseeyah ta gama rinjayar yaran, kwafa ta yi ta shige kitchen ta zuba masu abincin da da tace su koma yawon su ci.
Ko da ta koma ta ga ba abincin da aka aje mata ta san Mammee ta dauke kenan, kitchen ta je ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 41