Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai da safe, sun farka tare da tambayar an gama ne, Aaseeyah ta ce, "Yo me ma akai, ai ku dai ba wanda za a zauna bata lokaci a bawa labari bane, gobe ni kadai zai bawa labarin,ni kadai ke sauraron shi, sai Umaimah ita ma in gyangyadi bai sure ta ba" Ba su kula ta ba dan bacci ya ci qarfin su, ba su kaiwa haka ba su kwanta ba, gwanda ma mazan, in su na kallo sukan jima sosai. Bayan tafiyar su Umaimah Aaseeyah ta fara raba idanu, wa zai raka ta nasu bangaren? Dan sosa kai ta yi ta na wage haqori, tace Mahboob ya raka ta, murmushi ya yi, a zaton shi tunda ba ta jin magana ai bata da tsoro, sai gashi ta bada shi. Nan dai ya miqe dan raka ta, su na tafe ta na waige waige, motsin mage da kan shiga gidan da dare ne ya firgita ta, ta rarumi Mahboob, tare da sakin siririyar qara,tsayawa ya yi kamar an gina shi a wajen, saboda yanda ta riqe shi na aika masa da manyan saqonni,jin yaqi gaba ya qi baya ne Aaseeyah ta jijjiga shi tare da jan hannun shi, akan su tafi, dan tsoron magana ma take,haske ne ya haske su ta baya, a tsorace Aaseeyah ta tsanyara ihu, ta kwasa da gudu zuwa bangaren su Mahboob kuwa duk da ta sake shi bai dawo hayyacin shi ba, sai da ya ga Noor a gaban shi da fuska mai bayyanar da fushi da bacin rai................ Tooo ni ma na gaji aradu. TAUBASHI PAGE 18: "Ya Noor lafiya kuwa?" "Kar ka wani maida ni ban san me nake ba mana," "Kamar ya ya kenan? Me ya faru?" "Ohhh ka na nuna kai ba ruwan ka dinnan ko? Ka tsaya a matsayin ka na yayan ta, na ga kana wani shisshige mata, kar ka dawo da abinda ya wuce, yanzu ba yara bane mu," "Hummm Noor kenan, ai ko a baya ni yayan ka ne,kuma yanzu ma ni yayan ka ne, tsaurin ido ne ya ke sa ka ka ke ganin kamar sa'anni muke, laba'as,matsa min na wuce" "Ba wata laba'as, ba wani larabci ni ma da ban iya shi ba,in shuwayya shuwayyan ce ni ma dik na sani,ba kuma abinda za ka nuna min, Aaseeyah tare ka gan mu da ita, kar ka ce za ka shiga tsakanin mu, dan na ga take taken ka" Abun ma dariya ya bawa Mahboob sosai, "Ohhhh abun haka ne, kace ghaiwr ke damun ka, ok na gane, mu yi wani abu d'aya mana," "Ba wani kishi da ke damu na, kuma ba abinda za ai, ka ga ina baka girman ka, kuma ina qaunar ka a matsayin ka na dan uwana, sannan mun jima sosai bamu hadu ba, ka riqe wadannan martabobin da na baka a zauna lafiya." "To shi kenan na ji, tun da ba za ka tsaya ka ji ma.me zan ce muyi din ba, Allah ya bawa mai rabo sa'a, sannan na gode da wadannan mutuntawa da ka bani, sai da safe Ibnu Al-3am" Cikin hadewar fuska Noor ya ce ma Mahboob, "Sai da safe" Idon Noor kamar zai fadi dan harara, da zaku kalli idon shi a lokacin da dariya ta ma mutum yawa, saboda ko hararar ma bai iya ba, amma dai dole sai ya nuna bacin ran shi da harara. Kowannen su wucewa ya yi zuwa sashen su, da Noor ya so kwana wajen Mahboob amma ya fasa, 'Har yanzu ya na nan da halin yarinta komai ya na so a bar mishi shi kad'ai,Aaseeyah ba kayan wasa bace,Allah ba wa mai rabo sa'a, in kai ne da rabon ta zan taya ka farin ciki dan uwa, in ba kai bane zan taya kaina murna' 'Me ki ka yi wa zuciya ta ne Aaseeyah, kin min qanqanta da so, amma zan amshi wannan baqon yanayin da na ke ji game da ke, ya na raya min zuciya ta daga mutuwar da ta yi shekara da shekaru' Juyi Mahboob ya yi sannan ya lumshe ido bacci mai dadi ya dauke shi, cike da mafarkai masu rikitarwa. Da safe da ya tashi kasa gane takamaimai me mafarkin ya ke nufi yai,tabbas ya ga fuskar Aemana na kiran sunan shi cikin wahaltaccen yanayi, sannan ya ga fuskar Umaimah na kuka idanun ta na zubar da hawayen jini,sannan ya ga Aaseeyah na kusa da shi, amma kamar tana nesa, wannan wanne irin mafarki ne mai wahala? ******************************* Kowannen su ya gama gudanar da ayyukan shi na wannan ranar cike da zumudin son jin ci gaban labarin su, Yesmeen da su Ummu Suleim na kwance a gadon Aaseeyah su na jiran ta ta gama wanka ta shirya su tafi, qarfe takwas saura minti goma lokacin, sun matsu ta yi sauri ta fito. A gurguje ta sanya doguwar riga kalar pink da mayafi siriri kalar kayan, sai dan turaren ta mai sanyi da ta sanya, ta kalle su, "To na gama mu je ko?" Kallon dogon gashin ta da ya fito ta qasan mayafin Ummu Suleim ta yi ta ce, "Baki daddara ba ko, matso na gyara maki" Daure mata tayi ta yafa mata mayafin ta fito fess gwanin sha'awa, Umaimah kyabe baki tai, ta ce, " mayyar pink kenan,Sai wani yanga ki ke kamar kin fi kowa kyau," "Ga shi kin fada," "Umaimah a aje son kai a gefe kin dai san Aaseeyah ta fiki kyau," "Kuuut ta ina?" "Ta fiki shape, ta fiki hasken fata mai kyau, ta fiki gashi mai kyau" "Na fita ilimin boko ba" "Ni kuma na shallake maki ana mahammadiyya ba,na shiga aljannan ba" "Dalla kun dame mu da fada ku zo muje kan mazan su kame kujerun" Da sauri suka fita, Umaimah da Aaseeyah na ci gaba da shammatar junan su. Suna shiga Umaimah wai ita irin me yayan nan, ta tafi da gudu ta zauna kusa da Mahboob, Aaseeyah kuwa tsakiyar 'yan biyu ta zauna ta kwantar da kan ta a cinyar Hassan, sannan ta fara waqa, "Ahayyeee biyu ta fi daya" Tsaki Umaimah ta yi sannan ta sanya hannun ta a jikin Mahboob ta ce, "Yah Mahboob ka ci gaba da bamu labarin plss" "To Umaimah, mu jira Noor, zai kawo mana abun motsa baki," Aaseeyah ce ta kalli hannun Umaimah a jikin Mahboob, sai kawai ta ji haushin Umaimah ya kama ta, duk da cewar qanwar shi ce ta jini, ita a son ta kar wata mace ta rabe shi, sai ita kawai, dan guntun tsaki ta ja. Su na haka Noor ya shigo da Pop corn da ice cream ya miqa ma kowa na shi, ya miqawa Mahboob canji, ya ce kudin sun yi yawa, Mahboob karba ya yi ya yi godiya, Noor ya zauna gefen Umaimah, Mahboob da Noor sun saka Umaimah a tsakiya kenan, kallon Aaseeyah Umaimah ta yi ta mata gwalo, murguda mata baki tai, sannan ta ce, "Sai ka ce a gidan kallon turawa an siyo wani Ice Cream da Pop Corn," "Naga dai jiya gyada Mammeen ki ta soya mana muka ci" "Tooo ba ta kyauta ba kenan?" "Dan Allah me ke damun yaran nan ne? Akwai wata matsala a tsakanin su ne? Su na son yin fada da junan su," "Yah Mahboob dan ci gaba da labarin ka rabu da su, ba dainawa za suyi ba, wataqila dan sun ga shekarun su kusan daya ne" "Tabdijam na girme ta," "Girman kwabon?" "Dalla malamai ku mana shiru a fara" cewar Hassan da suka fara cika masa kunne da yarinta in ji shi. ********************************* Bayan an Haifi Noor, Mahaifiyar Fateema ta so ta koma gida wanka, amma Zainab da kakar mu Ayshaa suka hana, su suka yi mata wankan jego da duk wata kulawa da ake bawa mai haihuwa, kan su a hade yake,har sanda Noor ya kai shekaru biyu a duniya, daga sannan ne rikicin ya fara, a lokacin ne kuma Abdul Mudalleb ya matsawa Abee wato Ibraheem akan shi ma ya yi aure, domin ya ga yaran shi, Abee na sanar da mahaifan nashi komai lokaci ne, in lokaci ya yi zai yi ne. A washegarin ranar da suka yi wannan maganar tafiya Nijer state ta kama shi,zuwa bikin abokin shi da sukai makaranta daya da shi,a qaramar hukumar Edati, cikin qauyen Ndalada, tun safe ya je shiri, ya fito tsaf dan tafiya, ya ji hayaniya a tsakanin shiga bangaren mu da bangaren su Noor,ko da ya leqa sai ya ji Yaya da qanwa su na musayar yawu akan yaran su,akan abun wasa, Abun wasa nawa ne, amma indai na fito da shi Noor sai ya amsa, duk da cewar na girmi Noor sosai har a wannan lokacin mahaifiya ta na min kallon jaririn ta, saboda bani da qanne,ta sakalta ni sosai, ina ji na qaramin yaro, dan haka ban san na hakura na bar ma Noor abun wasa na ba, tunda shi ma ya na da nashi, kuma ba ya bari na taba masa,rikici ya kai Fateema ta mare ni, wanda hakan ba qaramin bata ran mahaifiyar mu ya yi ba, shi ne sabab din fadan nasu a wannan lokacin. Abee hakuri ya basu ya tafi, ya ma iyayen shi sallama, suka masa fatan alkhairi da sanyawa tafiyar albarka. Ba bata lokaci kuwa ya nufi Nijer state, ko da ya je har an daura aure,kasancewar kan ya isa qauyen ya jima, ksantuwar rashin hanya mai kyau, dan haka ya samu wasu daga bukukuwan al'ada da aka gudanar irin na Nufawa. Hayaniya ta yi yawa, shi kuwa ba mai son hayaniya bane, dan haka ya bar wajen, ya bi wata hanya wadda bai san ina ta dosa ba, bin hanyar ya yi har ya kai sanannen rafin garin dake da tarihi, wanda mutanen garin sun yarda da cewa kowanne ruwa ya na da oracle, kuma sun yarda cewar wannan rafin nasu ya na da kumurcin maciji a ciki, wannan dalili ne ya sa ba a zuwa da baqar tukunya,saboda macijin zai shige cikin tukunyar, tunda shi ma baqi ne. Dake garin kusan kowa dan uwan kowa ne, gari ne kusan a ce na dangi, kuma su na da zumunci sosai a tsakanin su. Zaune take a saman dan dutse, ta na daukan qananan duwatsu ta na jefawa, ta na kallon yanda tsakuwar ke bawa ruwan wani zagaye kamar na maganin sauro,gwanin sha'awa, idanun ta na cike da shauqin ganin abinda take yi, motsun shi ne ya tsorata ta, ta miqe tare da fadin "A'uzubillahi," "Yi hakuri 'yanmata na tsorata ki ko?" Sunkuyar da kai ta yi, sannan ta fara qoqarin barin wajen, da sauri ya bita ya na neman sanin sunan ta, domin da alama ita ma ta zo bikin, duba da yanayin kayan jikin ta ankon bikin ta saka, "Ki taimake ni kar ki tafi baki fadan sunan ki ba, in baki sanar da ni sunan ki ba zan koma rafin can na fada, sai cobra din da ke ciki ya hadiye ni shi kenan na mutu," Da sauri ta kalle shi ta ce, "Su na na Subai'a" "Masha Allah, sunan ki mai dadi,ke qanwar ango ce ko qanwar amarya?" "Ni...ni..ummm yar uwar su ce dika" "Ohh ki na nufin su ma auren dangin sukai? Lallai garin nan da wahala ashe su ban ke, tunda ni ba dan dangi bane" Kallon shi ta yi nan da nan idanun ta suka ciko da hawaye,qoqarin barin wajen take, suka ji muryar angon na kiran ta, "Ke me kike yi a nan wuce ki bar nan" "Ya ka ke korar mata ta ne? Ni fa na yi mata ko ba za ku ban ita ba?" "Allah kiyaye ka auri wannan, ta dalilin ta iyayen ta suka mutu, ta kunna ashana ta na wasa da shi suka mutu da gobarar da ta hada da hannin ta, she is an example of badluck" Da sauri Abee ya kalle ta, ya na mamaki, anya kuwa wannan mace mai sanyin hali da ganin za ta yi abinda ake zargin ta da shi kuwa? Hawayen ta na zuba ta bar wajen da gudu, ba ta sake komawa wajen bikin ba, har Ibraheem ya gama kwanakin shi ya bar garin, a zaton shi in ya koma gida zai iya manta ta, amma inaa, bai da aiki sai na tunanin ta, a da bai damu da zuwa wajen aiki ba, amma dan ya rage tunanin ta ya fara zuwa aiki tuquru, har sai da Abaana (Mahmood) ya yi mamaki, nan dai sika zaunar da shi suke tambayar shi damuwar shi, dan tun da ya dawo suka ga sauyi sosai a tattare da shi,da kyar ya sanar da su labarin Subai'a. Abdul mudalleb kuwa ya ce su shirya su hudun su je garin inda hali a aura ma Ibraheem ita a lokacin su taho da ita, canfa ta kawai mutan garin sukai, amma ba dan da zai kashe iyayen shi da kan shi. (Hummm wannan zamani da mike ciki 'ya'yan sunnah ke ajalin iyayen su, Allah ya sa mu dace) Da zuwan su kuwa, sun samu labarin sabanin yanda Ibraheem ya ji, domin abinda aka sanar da su ta aikata ba da gangan bane, tsautsayi ne, kuma akwai yarinta a tare da ita, dika dika shekarun ta sha d'aya lokacin, ta yi hakan ne a qoqarin ta na son kunna risho dan dora ruwan zafi,kamar yanda mahaifiyar ta ta umarta, wadda ke dauke da tsohon ciki, A lokacin damina ne, ba a jima da gama ruwan sama ba, murhu da itace duk sun jiqe, ga shi tsakiyar dare ne, ga naquda ta taso ma mahaifiyar ta ganga ganga, mahaifin ta na tare da ita a quryar daki sun rufe qofa saboda kar ta ga yanda mahaifiyar ta ta za ta haihu. Ita kuma ta na ta qoqarin kunna rishon, cikin rashin sani ta dauki fetur ta zuba a matsayin kananzir ba tare sa ta sani ba,kasantuwar mahaifin ta na da babur din da yake kabu kabu da shi. Ta kunna ta fita dakko tukunya da ruwa ta ji ihu da qauri, da gudu ta nufi dakin domin shiga, amma zafin wutar ya hana ta kutsa kan ta ciki, sai ihu take ta na kururuwar neman taimako, mutane basu fito ba sai da wuta ta samu nasarar cinye iyayen ta a dakin nan, nan fa aka matsa mata da tambayar me ya faru, anan take bada labari tare da nuna galan din da tai amfani da shi wajen zuba kananzir din,ana shinshinawa aka ji warin fetur, wasu suka hau zagin ta har da duka, akan ta kashe iyayen ta, wasu kuma suka ce bata sani ba, wasu kam a tsakiya suka tsaya, addu'a suke Allah ya jiqan iyayen nata, bayan an kashe wutar aka duba sun qone qurmus, a hade da junan su, Subai'a ta shiga cikin tashin hankali mara misali, ta yanda makaranta ma in ta je bata gane komai, a haka ta gama secondary, mazan garin ba mai cewa ya na son ta da aure, sai dai da lalata, ta na zaune a gidan Ndazhitsu,(Mai gari kenan) wanda shi ne kakan ta. Bayan jin wannan labari mai ban tausayi, ne Ibraheem ya ji ya qara son Subai'a, ya na taya ta jin kadaicin da take ciki a wannan lokaci, tare da tsananin tausaya mata saboda maraicin iyaye. Nan fa Abdul Mudalleeb ya samu ya yi ma dattijan da ke sake tunzira cewar kar su yarda su dau mugun iri nasiha, wadda ta sa jikin su sanyi, suka ga rashin kyautawar su a irin kyamata da kyara da suka dinga mata a baya, a take Abdul Mudalleeb ya nema wa Ibraheem auren Subai'a, aka basu ba bata lokaci, tunda abokin shi da ya zo auren shi ya tabbatar ma da kowa ya san su, ya san garin su, da halayen shi, ba shi da matsala. An daura aure su Ibraheem sun kwana, washegari suka dawo Kano da amarya, an hado su da matar mai gari, da surukar ta, sun ga waje, suka koma bayan kwana uku. A bangaren su da Mahmood ya gina dama domin Ibraheem din da iyalin shi, anan suka zauna. Tunda Zainab da Fateema suka ji asalin tarihin Subai'a suka tsane ta, suke kiran ta da qabila, tun abun ba ya damun Subai'a har ya fara damun ta, a lokacin sai zainab da Fateema suka rage yawan fada a tsakanin su, suka maida fadan kan Subai'a, ba qaramin wahala suka bata ba, Allah ya gafarta ma Ammee na" Hawaye ne ya ke zuba a idanun Mahboob da Aaseeyah,wadda a yau ne ta ji labarin mahaifiyar ta da ta jima ta na son ji, a duk sanda ta tambayi Mammeen ta labarin dangin ta sai ta ce mata dangin Abeen ta sune dangin ta, ta yarda da hakan, duba da hasken fata da kyaun ta, ta yi zaton ita ma balarabiya ce, ashe ba ta da alaqa sam da larabawa, marainiya ce, wadda ta sha wahala a hannun faccaloli. Cikin kukan da take ta tashi da gudu, ko tsoron hanyar yau bata ji ba,ta nifi sashin su, kowa a wajen jikin shi ya yi sanyi, Mahboob ma daki ya shige ya rufe qofa,saboda tunawa da azabar da Mahaifiyar shi ta ganawa Subai'a..... TAUBASHI PAGE 19 Ta na isa wajen na su ta ga dakin Mammeen ta a rufe, da alama sun shiga daga ciki, motsin ta ne ya sanya Mammee fitowa dan ta rufe wajen nasu, Aaseeyah ta gani a tsaye a jikin qofa hawaye na zuba a idon ta, su na had'a ido, Mammeen ta nufe ta dan jin dalilin kukan ta, amma sai ta wuce ta ta yi d'akin ta, ganin haka ne ya sa itama ta rufa mata baya,tare da tambayar ta lafiya ta ke kuka? "Mammee dan Allah ki rabu da ni, tunda ba za ki iya sanar da ni labarin ki ba, sai dai na ji a wani waje, wace irin azaba kk sha a gidan nan? Me ya faru ba yan Abee ya yi nasarar auro ki, ya kawo ki cikin matan da ba su qaunar ki? In kin san ba za ki ci gaba da ban labarin nan ba dan Allah ki je kawai sai da safe, ina son zama ni d'aya" Idanun Mammee ne suka kad'a sukai jawur saboda tunawa da baya da ta yi,ta dad'e da mantawa tare da maida komai bakomai ba, zama ta yi a gadon Aaseeyah tare da miqa mata hannu, sai da ta dan yi jinkiri sannan ta miqa hannun ta cikin na mahaifiyar ta ta, zaunar da ita ta tayi daf da ita. Sannan ta yi kissing goshin ta, ta fara share mata hawayen ta, "Aaseeyah rayuwar da ta riga ta wuce, ba bu amfanin tuna ta, ni ma ba wai ina alfahari da baya bane, muddin wani yare zai shigo hausawa sai ya yi hakuri, saboda yawan kiran shi da QABILA da zasu dinga yi, da kyamatar shi, ko da ya fisu zama musulmi nagari, in kuwa ba ya jin hausa sai baqin cikin su ya kusa sa shi hauka, domin a gaban shi za su zauna su zage shi har dangin shi, bai san me aka ce ba, sai dai ya ga dariyar su, tunda Mahboob ya ce zai baku labari na ke taraddadi, amma na san ban isa na hana ba,domin ra'ayin shi ne hakan, sannan wani abun ba zai zauna a boye ba har abada, ina ya tsaya da baku labari? Ko har ya gama?" "Ah ah sai gobe zai ci gaba, amma ni ba zan sake zama da su ba,saboda da bakin shi ya ce Maman shi ta baki wahala," "Ai ya wuce Aaseeyah na yafe mata, na yafe ma kowa har abada, ni ma ai da aka kaini bango na fara ramawa ba wai na yi shiru bane, so kin ga kenan dikan mu mun wahalar da juna ko" "Bani labari Mammee" Bayan ta sanar da ita in da ya tsaya masu ta gyara zaman ta sannan ta fara ba Aaseeyah labarin kamar haka, "To kamar yanda ya sanar da ke, na sha wahala tsakanin faccaloli na, domin kuwa Ibraheem ya tsaya da qafafun shi shima kamar Mahmood, arziqi na ta shigo musu,hadin kan su na qaruwa, duk yanda mace ta so raba tsakanin su qarshe ita ke kwanan rashin dad'i, haka ne ya faru da Zainab, da ta dage za ta had'a su fad'a ita Mahmood ya kusan saki, ba dan Abbu da Abee din ki sun sa baki ba, da kyar ya hakura, da ta ga ba nasara sai lamari ya juyo kaina, ta ce ni ce dangin mayu, na kame ma mazan su kurwa. Kamar yanda na lashe ta miji na sai yanda na ce ya yi yake yi, to su sun fi qarfi na, dama su na da labarin Nufawa akwai mayu, wataqila ma cinye iyaye na na yi na fake da gobara, a ranar na yi kuka har sai da zazzabi ya rufe ni, Abeen ki ya dawo daga aiki, ban girki ba, gashi na qi sanar da shi me ya faru, a wajen Goggo Ayshaa ya ji me su ka min, kin san ita Goggon su ce shi ya sa sike kiran ta haka. So ko da ya shigo daki ina ta rawar sanyi, ya zauna ya fara min nasiha, a lokacin na sake saka sabon kuka,ina danasanin kunna rishon da na yi shekaru da dama da suka wuce, da na sani da mahaifiya ta ta ce n kunna ce mata nai ba zan kunna ba, da rashin kunya na mata na qi kunnawa da suna raye, da ina cikin gata na,da ban wulaqanta ba a garin mu da gidan miji. Da kyar aka samu Zainab ta daina kira na qabila, abinci innai sai ta ce Allah kiyaye ta ci abincin qabila, a lokacin ba na magana sosai, sai suke zaton ban iya hausa ba yare na iya, sai su dasa kujera su banni da yaran su na kula da su, su yi ta gulma ta, akwai ranar da Zainab ta ce, 'Fatee an ya kuwa iyayen ta Nufawa ne?' 'Me ya sa ki ke kokwanto akai?' 'Ki duba da kyau, ta fi kama da fulani, Nufawa na da gashi eh na yarda amma ba irin na fulani ba, sannan ki duba hasken ta irin na fulani anyaaa' 'Anyaa me?' 'Anya gyatumar ta ba tai biye biye ba aka samu aka haifi bafullatana a boye' Ji na yi hankali na ya tashi da jin wannan mummunan cin mutuncin da suke min gani zaune gaban su su na zagin iyaye na da suka rasu, su na tsaka da dariya na isa gaban Zainab na watsa mata mari, sannan na ja ta, nan fa kokawa ta kaure a tsakanin mu, a lokacin Mahboob ya dan tasa kadan, ganin ina dukan mahaifiyar shi ya samo wani qarfe na mota da aka aje a gefen gate ba a amfanin komai da shi, ya shimfidan a qeyata, nan da nan jini ya balle,na fadi take a sume. Ban farka ba sai a asibiti,tsabar ciwon da kai na yake,ni na nemi a min allurar bacci,ba kowa a waje na daga Goggo Ayshaa sai Abeen ki, idanun shi sin kada sun yi jawur,Goggo Ayshaa na bashi hakuri, ta masa alqawarin za ta dau mataki da kan ta, to dake su nata ne, ni bare ce,haka maganar ta bi iska, har na warke daidai da ruwan zafi ba su dafo sun kawon ba,haka na koma gida na qarasa jinyar dinkin da aka min, kin sha tambaya ta me ya samen a wajen in ki na gyaran kai, to kin ji me ya faru. Ana haka na shekara uku gidan miji, Mahboob har ya shiga JSS 1, Noor kuwa ya na aji hud'u na primary, ni kuwa ko batan wata ban taba yi ba, ni ke musu abincin da za su tafi da shi, saboda iyayen su na baccin safe, ni kuma Allah ya sanya min son su, haka za su karba ba godiya su wuce, in sun dawo su ajen mazubin a bakin qofa su shige sashen su, ban taba jin haushin hakan ba, hasali ma ni dariya suke bani, ana so ana kaiwa kasuwa,sai dai abu d'aya da na kula da shi ta bagaren yaran wanda ke sake qaran qaimi wajen jan su a jiki, shi ne, duk abinda suke min da alama sanya su ake, musamman Mahboob, domin duk sanda suka fita unguwa su dika a wajen nan zai yini duk da ba ya kula ni amma zai ci abinci ya je yawon shi ya dawo ya zauna ina aiki ya na kallon gilmawa ta. A hankali na fara addu'ar neman haihuwa, a shekarar da za su tafi hajji na roqe su su min addu'a Allah ya bani haihuwa, ina son su roqar min na haifi mace, dan kuwa ina sha'awar mace, ina son samun

Chapter 13 of 41