Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hancin Ummee, sai da ta sauke ajiyar zuciya, tabbas ba boka ba malam, haduwar Mammee kawai ta isa a so ta. "Dan Allah Maman Noor ki dena bani kunya,ai is normal, Yaya da qanwa su samu sabani, kuma a ranar su shirya, kowa ya ji qaunar d'an uwan shi a ruhin shi kamar ba abinda ya taba faruwa, ni irin zaman da nake da ku kenan, shi ya sa ba na jin haushin dik abinda kuke min, raina kam na baci a lokacin, da na juya baya ya wuce, dan haka ki daina ban hakuri, indai ni ce na jima da yafe maku, Allah ya yafe mana" "Ameeen Subai'a mun gode, Allah ya qara maki hakuri, Allah ya min arziqi da samun kyakkyawan hali irin naki" "Ameen maman Noor," Nan fa Ummee aka baje baki akai ta hira, Mammee na aiki, ta na taya ta hirar,har ta gama girki Ummee ba ta tafi ba, gashi ta na son ta shiga wanka, abinci ta zubawa Ummee ta ajiye ta ce ta na zuwa. Guduwa ta yi ta sheqa wankan ta, ta sha ado da qamshin ta, sannan ta fito,mamaki ne ya kashe Ummee, basu taba zama na awa sama da daya ba tun da can, da an zauna za a bata ran juna, yau kam gashi ta yi a qalla awa uku a wajen Mammee, kuma a dan zaman da ta yi ta koyi abubuwa masu yawa. Bayan fitowar Mammee cikin ado da kwalliya, da qamshi ne Ummee ta ce ta tafi, "Kin ji yaran can shiru, ko me suke tattaunawa sai Allah, bari na je na ga me suke yi" Dariya kawai Mammee ta yi, a ran ta ta na ayyana koma me suke ai da auren su, b mtsal bane. ko da Ummee ta koma ganin Aaseeyah ta yi kwance a gefen Mahboob kusan kawunan su a hade yake, ya sanya hannu ya naqale ta a jikin shi su na bacci,dakawa Aaseeyah duka ta yi a cinya da qarfi, "Tashi rasai, a nan za ki zo ki nunan rashin ta ido, wai ke me miji ko? Kin wani naniqe shi, kamar ze gudu" Cike da jin kunya Aaseeyah ta tashi, har ta fara takawa dan tafiya bangaren su ta juya,cikin tura baki ta ce, "To wai ma ni kika ga na riqe shi, ko shi ya riqe ni,kuma wannan dukan da ki ka dakan in fata ta ta daye fa?" 'Kar fa 'yar banzar yarinyar nan ta ce se ta rama' "To ai ke din ce se a hankali,baki cika kai ba Aaseeyah, banda ke ai ni suruka ce,to taho ki shiga dakin su Umaimah ki sallar la'asar ko?" 'Ki gama kame kamen ki, tunda ki ka tadani bacci da duka ba abinda zai hana ni ramawa, ko ban dake ki ba sai kin ji yanda na ji,ina so mu shirya amma ki na min mugunta,mu zuba mu gani' Ummee dai ta tabbata ta tsokano ma kanta jangwam, dan haka ta dinga jan Aaseeyah a jiki, har da cewa wai Aaseeyah ta koya mta girki, irin na su na zamani. 😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂habaaa hajiya Ummee ya da jin tsoron Aarce haka? TAUBASHI PAGE 50 Aaseeyah ta maida hankali kan karatun ta matuqa, domin ta san in ba ta nutsu ba za a dinga yi ba ita ne kawai, har yanzu bangaren islamiyya ya fi qarfi akan bokon ta, hakan kuwa daukaka ne babba a rayuwar ta, ta sani da ba islamiyyar bokon ma ba zama zatai ba. Yesmeen ta samu qaruwa ita da matar Hussein, wato Tasneem, Yesmeen ta samu yarinya mace, suka sa mata sunan kakar su wato Ayshaa(Humairah),Tasneem kuwa sunan mahaifiyar ta aka saka wato Asma'u, suna kiran ta da asalin sunan ta, dan Tasneem ta ce gwanda a kira ta da sunan mahaifiyar ta kowa ya san takwara ta yi mata. A wajen renon Asma'u Hussein ke samun kwanciyar hankali, domin ya na matuqar son yarinyar, shi ne wankin kashin ta, wankan ta, sanya ta ta yi bacci, in dai ba ya kula da ita to ya na wajen aiki, da ya dawo kuwa Tasneem za ta dangwara masa jaririyar ko abinci ba zata bari ya ci ba, ta hau shagwaba ita ta dame ta da tsotso da kukan banza,ba zai ce komai ba zai amshe ta, dan shi ba ya daukan kula da ita aiki sam, sai nishad'i. ************************** "Subai'a kin ga me cewa mun dame ta, ta na karatu, ta bige da bacci," "Ai in ta na karatun nan, ba ta son ko ruwa a motsa in da hali" "Ai kuwa bata isa ba,yanda ta sa mukai ta magana cikin rad'a kamar barayi sun je sata sai ta farka" "Ummm uhmm Maman Noor, kullum sai ta yi qorafin ki na hana ta bacci, da kin ga ta na bacci sai kin yanda kika yi ta farka, ko dake ba ruwa na, ke da surukar ki" Mammee ce ta kwashe robobin da suka gama bare green beans da yankan karrot a ciki, suna son yau su yi girki tare a hadu gaba daya a ci a babban parlourn gidan. Mammee na tafiya, Ummee ta isa gaban kujerar da Aaseeyah take, ta janye littafin dake cinyar ta,cikin magagi Aaseeyah ta kai wa littafin ta wafta,cike da mugunta ta cakawa Ummee biro a hannu, qara Ummee ta kwalla kamar wadda aka zarewa rai, Aaseeyah na ganin ta'asar da ta wa Ummee sai ta koma ta lumshe ido kamar mai bacci, ita a dole bata san ta yi ba, Mammee ce ta shiga da sauri ta ga Ummee ta dafe hannu a qirji, can kuma ta sake ta na yarfe shi. "Ke ki ji muguwar yarinya za ta bulan hannu da biro, daga janye mata littafi na ga ta kwanta akai kar ta yaga," Dariya Mammee ta danne ta ce, "Kayya amma bata kyauta ba,sannu, ince dai ba jini" "Yo ba gwanda ya yi jinin ba ma na san me nake ciki, wata azaba na ji ta ratsa ni daga kwakwalwa ta har tafin qafata" Kamar a mafarki suka ji Aaseeyah da ta wayance da bacci take ta kece da dariya, tattara littafin ta ta yi ta gudu daki, ta na tafe ta na fadin, "Hajiya Ummee surukata ta mutunci, Allah y bar qaunar dake tsakani na dake" "Ya bar qauna ko ya dasa qauna, ai da da qauna a tsakanin mu da baki din ga azabtar da ni ba, muguwa kawai" Mammee sai a lokacin dariya ta kwace mata, har da hawaye, ta ce, "Maman Noor ki na da abin dariya, kema sarai kin san halin yarinyar nan da da kika ga ta yi luf kamar me bacci kwashe ta ki kai da tafi, da ta miqe ai, Aaseeyan ce ke magagi? Yarinya da ko tsakiyar dare tashi take ita daya tun tana qarama" Shiru Ummee ta yi ta na murmushi, cikin sanyin murya ta ce, "Ina zan san yarintar Aaseeyah tunda na dorawa kaina baqin hali a baya, ba abin alherin da ke hada ni da ita sai mugunta, mistake kadan zan mata in ta dinga ganan zaba, sai na ji kamar na kira ta mu sasanta" Murmushi Mammee ta yi ta ce, "Rayuwa kenan, gashi yanzu komai ya zama tarihi" "Haka ne, muje na taya ki, kafin waccan me kan kwanon ta ce ban aikin komai ba sai ci,kin san shekaran jiya haka ta min, ta ga ina cin shinkafar da kk dafa wai Hajiya Ummee kenan, ba a iya aiki ba an iya gabzar risi, ke ki ji" "Maman Noor Allah ya hada ki da surukar zamani, kuma wai a cewar ta yanzu ta nutsu" "Ai ni dai na ce kan a ga nitsuwar ta sai ta haihu" Suna ta hira suna dariyar su gwanin sha'awa suna had'a abinci, qasan ran Mammee kuwa cike take da godiyar Allah, wannan shi ne abinda ta ke fata take buri, gashi ya tabbata. Aaseyah ce ta fito sanye da atampa zani da riga, ta kafe kan ta da dauri mai kyau, wanda ya fitar da kyakkyawar fuskar ta fess,fuskar ta ba wani cikakkiyar kwalliya, sai zallan kyaun da Allah ya mata,qamshin ta mai sanyi na biye da ita dik inda ta gilma, Ummee ta tafi bangaren ta dan shiryawa, Mammee na daki ta na nata shirin, Aaseeyah kuma ta debi abincin ta je ta fara jerawa ta na gyara wajen. Ta na gamawa Mahboob na dawowa, sannu da zuwa ta mishi, ta yi hanyar fita, hannun shi ya miqa ya ja ta jikin shi, ya kwantar da ita a qirjin shi, cike da shagwaba ya ke magana, "Gaskiya ni dai na fara gajiya, ace miji ya dawo daga aiki, gashi ga matar shi amma ba wani cikkkiyar kulawa" Hancin shi ya goga a wuyan ta, cikin daukewar numfashi ta zame jikin ta,kan ta a qasa ta ce, "Yah Mahboob ba kyau neman magana,ba abinda ba na maka in ka dawo, sai dai in ba na nan," "Ki na taya ni wanka? Ko kin taba taya ni shiryawa" Zaro ido ta yi, ta ja baya, bakin ta bude, magana ta so yi sai ta ma rasa me za ta ce, kallon shi ta yi daga sama har qasa, sai ta ga kamar ana mata zooming din shi, ta gan shi wani gabjeje, "Ni..ni zan maka wanka? 'Yar ni din nan? Kalle ka fa" Murmushi ya yi sannan ya ce, " ba ki san ana ma miji wanka ba?" "Ni dai dan Allah ka bar wannan maganar kar wani ya ji" "To na bari sai mun tare zaki min ko?" "Subhanallahi" Kwace hannun ta tayi, ta fita da gudu, mayafin ta ya riqe ta fizge ta qarasa fita daga parlour, shima fita ya yi ya tafi dakin shi,ruwa ya watsa ya fara shirin zuwa cin abinci, domin kowa na gidan ya san da cin abincin. Abbu da Abee sun fito cin abinci sai suka kalli juna suka sanya murmushi tare da nuna junan su, "Ohhhh da alama yanzu anko za mu fara a gidannan" "Ba ni da matsala da hakan" in ji Abee "Abbu Ummee ce ta siyo maku kaya iri daya, wai hakan zai qara had'a kan ku" "Tabbas na ji dad'in hakan, Allah ya muku albarka,Maman Noor, mun gode, kin ga kin tuna mana baya, da tamu mahaifiyar ke siya mana kaya iri daya, mahaifin mu kuma in ya tashi sai ya dinka mana har shi iri daya" "Allah ya jiqan su ya musu rahama" "Ameen, Mammee yunwa nake ji, a fara cin abincin" Murmushi Mammee ta yi ta kalli Noor ta ce, "To Noor yanzu kuwa, na kula kwana biyu baka wasa da abinci ga shi nan har qiba ka fara" "Mammee ai tunda Umaimah ta iya irin girkin ki cin abinci na y qaru" Suna dan hira sama sama, su Mmmee suka zuba ma kowa abinci, bismillah kowa ya yi suka fara ci. Bayan sun gama Umaimah da Aaseeyah sika gyara wajen, hira sosai suka yi, abinda basu taba yi ba, Abbu ne ya ce ya sanya hakan ya zama doka a gidan, duk juma'a a hadu a ci abinci tare. Washegari a makaranta Aaseeyah ke jin labarin komawar Aliyyu aiki Abuja,ta sanar da ita irin kewar da Mama ke ta yi na rashin Aliyyun, ko abincin kirki bata ci, "Allah sarki, zan kuwa fada ma yah Mahboob ya dinga zuwa wajen ta, wataqila zai dan debe mata kewar Yah Aliyyu" "Allah ya sa" "Ummm yauwa Amatullah,ni kuwa dan Allah na tambaye ki, wata ce ke tambaya ta ni kuma na ce ban sani ba amma zan tambaya mata, "Me ne ne tambayar? Allah ya sa na sani" "Ameeen,iuhmm dama wai cewa ta yi mace na yi wa mijin ta wanka? Duk girman shi," Dariya sosai Amatullah ta yi sannan ta ce, "Ummm ina jin dai wannan qawar taki sunan ta daga A ya fara ko?" Fuskar Aaseeyah kamar an kara a wuta dan dumi, kunya kamar qasa ta bude ta shige, "Ah ah...umm ni dai dan Allah ki fadan, na ga dai namiji babba ai mace ba ta tsaya yi masa wanka ba ko? Ai bai dace ba" "Kinga Aaseeyah, duk macen da kika ga ta na wa mijin ta wanka, ta shafa masa mai, ta saka masa kaya, ta fesa mata turare, to tabbas cikakkiyar mace ce, abu ne mai sauqi mijin nan ya zama a tafin hannun ta, domin ta tuna masa baya da mahaifiyar shi ke kula da shi, zai ji zuciyar shi ta aminta da ita sama da kowace mace, domin ita da girman shi ta zauna ta ke kula da shi, zai ji bayan mahaifiyar shi da ta kula da shi ya na yaro b wadda zata wuce matar shi a duniya, ko aure nawa zai yi ba zai ji dadin auren ba sama da yanda ya ji nata, sai dai in waccan za ta ririta shi sama da yanda take masa, Aaseeyah tun ba yau ba na kula ki na da saura a sanin rayuwar gidan aure, amma inshaa Allah zan koyar da ke duk abinda ya kamata ki sani" "Ai kuwa da na gode, amma fa mamaki ta ishe ni, ta yaya za a ce qarjejen qato ya tsaya a gaban mace ta masa wanka," Ihu ta dan saki ta rufe fuskar ta, sannan ta ce, "Abun da kamar wuya gaskiya" "Humm haka dai ki ka ce, amma na san irin ku, da kun ji dadin gidan miji sai kun fi kowa iyayi" Murmushi kawai Aaseeyah ta yi, gidan su Amatullah suka je tare, ta gaishe da Mama, tare da yi mata kalamai masu kwantar da zuciya, soyayyar da ke tsakanin Aliyyu da maman shi mai girma ce. Sai gab da magariba Amatullah ta aje Aaseeyah a gida,sai da ta shiga ta gaisa da su Mammee sannan ta tafi. Mahboob ran shi in ya yi dubu ya baci, ba dan komai ba sai dan missed calls da ya ajiye wa Aaseeyah masu yawa bata neme shi ba, gashi ya je daukan ta bai same ta ba,hnkalin shi ya tashi cike da tsoron ko wasu ne suka sake dauke ta ya je ya na ma Mammee maganar rashin ganin Aaseeyah da rashin daukan wayar shi da batai ba, suna tsaka da maganar su Aaseeyahn suka koma. Ganin su da Amatullah ne ya sanya shi sake fuska, har ta tafi bai nuna ma kowa ran shi ya baci ba, bayan Aaseeyah ta koma ciki daga raka Amatullah, ta tadda shi ya na ma Mammee sallama, magana ta mishi amma ya yi kamar bai ji ba. Wuce ta ya yi ya fita, baki ta sake galala, ta na kallon shi, dage kafada ta yi, ta zauna kusa da Mammee, zata fara surutu Mammee ta tashi ta bata waje ita ma, binta dakin ta yi. "Mammee wai me ya faru ne? Na maki magana kin yi shiru shi ma na masa magana ya yi shiru" "Ki tambayi kan ki amsa na wajen ki ai, 'yar kan ta, me zuwa unguwa ba izinin miji" "Ohhh ohhh,matsalar kenan? Mammee gidan su fa Amatullah na je ba wani wajen ba, sai na sanar da shi yanzu zani gidan su Amatullah?" A saman kujerar dake dakin Mammee ta zauna tare da tankwashe qafafun ta, Mammee na fidda kayan baccin ta ta juya ta kalli Aaseeyah ta ce, "Tunda na ke kin taba ganin na je wani wajen ba tare da sanin Abeen ku ba?" "Ah ah, amma Mammee ni fa..." "A gida kike? Amma kin tambayi izinin mu? Ya fi mu iko da ke, izinin shi shi ne gaba da namu, kin ma duba wayar ki kuwa?" "No, why?" "Saboda ya kira ki ba ki amsa ba, he was so worried ya zo ya na tambayar kin dawo, ya shiga damuwa da tashin hankali,ko kin manta me ya faru a baya ne?" "Ya salam, Mammee dan Allah kar ki maida wannan qaramin abun ya zama abun magana babba,gidan su Amatullah na je fa kawai" Ran Mammee ya fara baci, "Shut up,in kika sake fadan inda kika je sai na fashe bakin ki, uban wa kika sanar wa za ki gidan su Amatullah, ke ki ke da kan ki? Ko baki san datajar aure ba ne? In qafa daya ki ka taka inda mijin ki bai amince ba bai kuma yafe ba Allah sai ya kama ki da wannan laifin, Amatullah din na san da ta san baki nemi izinin mijin ki ba ba zata yarda ki bi ta ba, domin na kula ta na da sanin addini, tunda ke kin watsar da naki ilimin gaba daya," Hawaye ne kawai ke zuba a idon Aaseeyah, zuciyar ta na ta quna, akan kawai ta je waje bata nemi izini ba ake mata fada kamar ta aikata wani babban sabo? Mata nawa ne ke zuwa unguwa sai sun dawo su fada ma mijin, tunda take ai bata taba haka ba,kuma duk laifin shi ne da ya wani rude ya zo ya na neman ta, da be neme ta ba ai da ba wanda zai damu. "Ki tashi ki je ki bashi hakuri" "Kaii Mammee.." "Fita min a nan ki je ki bashi hakuri nace, ashe har kin fara fadi in fada da ni Aaseeyah?" Cikin zumbura baki ta bar dakin, ta nifi hanyar dakin ta, ta yi kwanciyar ta. "Ba hakurin da zan bashi, dan banga laifin da na masa ba".......... Tooh fa, gaskiya Aunty Asma'u qanwar ga taki Aaseeyah ta na buqatar lecture na musamman. TAUBASHI PAGE 51 Ta gaji da juyin da take bacci ya qi.zuwa,jakar ta ta dakko ta bude,ta lalubo wayar ta, danna wa ta yi, nan da nan kuwa ta yi ido biyu da 27 missed calls,yatsina fuska ta yi ta shiga call log din ta, Mahboob ya mata 22 missed calls Mammee ta mata 5 missed calls,shiru ta dan yi, ta na nazari, daga baya ta fahimci damuwar Mahboob din,kallon lokaci ta yi, ta ga qarfe tara saura minti goma,dan tsaki ta ja sannan ta miqe, ta nemi babban hijabi ta saka. Har za ta fita ta koma ta shiga bayin ta, ta dan jima sannan ta fito, da alama baki ta wanke,turare ta dan fesa,sannan ta gyara fuskar ta ta kalli kan ta sosai ta ta tabbata ba laifi Allah ya mata kyakkyawar fuska,murmushi ta yi ta kanne ido daya sannan ta zira takalmin ta kalar hijabin ta wato ja,sannan ta fita. Ta jima ta na buga qofar kafin ya je ya bude mata, ya na da tabbacin ba mai zuwa masa yanzu in b ita ba, dan kuwa a zaton shi ma ya na barin wajen su za ta bi shi ta bashi hakuri,amma ya ji shiru, cikin kasala ya tafi bude mata qofa,ya na budewa ta yi baya, ta na qoqarin faduwa, da sauri ya kai hannu zai tare ta ta sake ja da baya, ta na kifta idanu,kula da har yanzu fa idon ta a kan shi yake ne tai sauri kauda kan ta, cikin rawar murya ta ce, "Mammee ce ta ce na zo na baka hakuri,ka yi hakuri na fita ba da izinin ka ba, ba zan sake ba" Murmushi ya yi,sannan ya sake bude hannayen shi ya raba su a jikin qofar, kyakkyawan jikin shi da babu riga ne ya sake budewa da kyau, da sauri Aaseeyah ta juya zata koma, ya ja ta da qarfi cikin parlourn ya rufe qofar. Kuka ta sanya ta na bashi hakuri,shi kuma wucewa ya yi ya zauna. Kujera ya na kallon yanda ko ina na jikin ta ke rawa,me ye hakan? Ita ko dan internet din nan ba ta shiga da matasan yanzu suka bawa mahimmanci? (Ni ko na ce tarbiyyar da iyayen ta suk bata ba ta sabon Allah bace, ta bautar Allah da gaskiya ne, da kiyaye dokokin shi,yaron ko babban da ya bawa kallon finafinan batsa mahimmanci to tarbiyyar shi na da naqasu, ba mutumin kirki bane) "Aaseeyah haka ake bada hakuri?" "Eh mana, na ce maka kai hakuri, shi ne dole sai ka ci mutunci na ka firgitan lissafi, to ai Allah na ganin ka, tsakanin ni da kai an ga wanda ya bata wa wani" Kuka ta ci gaba da yi, shi kuma yana dariya ya tashi tsam ya isa gaban ta, zabura ta yi ta maqale a jikin qofar shiga parlourn, sannan ta ce, "Ni dai kai wa Allah ka saka riga, ko su Yah Hassan ba su zama ba riga irin haka, balle kai garjejen qato," Bata fuska ya yi ya tsani ta ce masa qato, qato bai ma da fasali kenan,duk kyaun jikin nan da Allah ya bashi. "Kin san ki ka sake kira na qato sai na maki aikin qatti? Ni ba mijin ki bane? Dan na zauna ba riga a gaban ki me ne ne, in ki ka kallen ki ka yaba lada zan samu, ko baqin cikin ladan kike min?" Tura baki tai, ta na qunquni, banza ya yi da ita kamar bai gani ba, ya koma ya zauna,sannan ya nuna mata dan nesa da shi ya ce, "Je ki zauna a can" Da ta so ta musa, amma da ta fuskanci ba wasa a tattare da shi, sai ta lallaba ta zauna, "Aaseeyah ni ban fushi da ke wai dan kin je gidan su Amatullah ba, fushin da nai na baki sanar da ni bane, duk macen kirki ko gidan iyayen ta zata sai ta tambayi mijin ta, wata sai ki ga sun yi yarjejeniya da mijin in akwai yarda tsakanin su, duk inda zata ba sai ta tambaya ba, in ta dawo ta fada, to amma mu ba mu taba irin wannan maganar da ke ba, amma kika tafi, kuma kin san an yi yunqurin sace ki, kinga dole mu shiga damuwa ko? Dan Allah ko dan gaba in zaki wani waje ko message ne ki aje min, inna gani zan iya kira mu yi magana,ko kuma na je ma na dakko ki in kin gama, ko baki so ina zuwa daukan ki ne?" Kada kai ta yi, sannan ta fahimci dalilin shi sosai yanzun dan hk hakuri ta sake bashi, sannan ya ce ya hakura, ya ce to ta tafi sai da safe,nuna masa ta yi ya raka ta ya ce ya na zuwa,riga ya je ya saka, ya sa ta gaba za su fita, riqe hannun ta ya yi ya na murzawa a hankali, ido ta rintse cikin murya mai rauni ta ce, "Sake min hannu na na tafi, dare ya yi," "Ki kwana a nan mana Mar'atee" "Tabdijam, in ka na so na kwana inda ka ke ka sanar a kawo maka ni kamar kowacce matar aure" "Haka kika ce? Bari gobe kuwa zan sanar," Da sauri ta hau bashi hakuri, don ita wasa take, ta kai karatun ta ina? Wannan garjejen qaton da gani ba da wasa yake lamrin shi ba, kiran shi qato da tai a ranta ne ya bata dariya. "Me kike wa dariya?" "Ba komai" Murmushi kawai ya yi, ba dan ya yarda da ita ba, sun isa daidai qofar su Aaseeyah ya sakar mata hannu,ta bude qofa, sai da ta ji ta a cikin gidan su sannan ta ce, "Yah Mahboob" Juyawa ya yi da murmushi a fuskar shi, sai ya ji ta ce, "Sai da safe qato, ka yi bacci lafiya irin na qatti kai daya" Bude baki ya yi ya kalle ta, cikin wasu sakwanni ya kai mata cafka, ta danna qofa ta rufe ta na babbaka dariya,dafe qirjin ta tayi da ta tabbatar bai kama ta ba, "An fada qato, ko ba qaton bane shi, dan an ce qato shi ne wato shi hausa ta ji bakin shi yanzu har da wani zai min aikin qatti,ku ji min bawan Allahn nan fa" Da surutan ta isa daki har ta cire kaya ta saka na bacci ta na surutai ita daya. Bayan ta kwanta ne ta kunna data, nan ta dinga ganin messages din Mahboob na alqawurran abubuwan da zai mata in ya kama ta,sai da ta gama karantawa tsaf, ta ji tsoro ba bata ji ba,amma ta san indai ya yi niyya zai abinda ya ce, to meye amfanin qin sake kiran shi da qaton? 'To qato na sai da safe, in mun hadu ka hadiye ni ma kawai' Murmushi Mahboob ya yi, ya kashe wayar shi ya kwanta, addu'a ta yi sannan ta kwanta bacci itama. ****************************** A cikin shekaru hudu da fara karatun Aaseeyah, nasarori da yawa sun same ta ta fannin karatun ta na lauya, da kuma karatun zaman duniya da take samu a wajen Amatullah, Mammee,da Maman aliyyu, domin watarana Mahboob da kan shi ya ke kai ta. Rayuwar hakuri kawai ya ke ciki, kullum ya na kallon mace har mace kuma mallakar shi amma ta hana shi komai,da ya matsa sai ta ce ya fada a gida a bashi ita, su kuwa iyayen su ganin ba su wani damu ba shi ya sa suka dakata har ta kammala karatun nata din. A shekarar da ta ke qoqarin tafiya makarantar lauyoyi da ke Yola, a shekarar Aliyyu ya samu

Chapter 32 of 41