Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ke,Allah kadai shi ne shaidar me nake ji game da ke, ba baturiya ba ko balarbiya ce bata da waje a zuciya ta, ke kadai ce mace a dika mata, kin gane? Wannan shi ne gaskiyar abinda ke zuciya ta,ba zan maki qarya ba Aaseeyah" Rungume shi ta yi da qarfi ta na murna, shi ma farin cikin ya ke ya samu nasarar shawo kan ta da kyar. Washe gari kuwa a gidan Sister Ramlat ta wuni, har dare ta na can, sai da akai isha'i sannan suka koma hotel din su,cike da kewar rabuwa da juna. Satin su daya suka bar US, suka tafi Saudiya, Aaseeyah ta maida hankali sosai wajen yin Umara,ta yi addu'a sosai, har Mahboob na mamakin yanda ta dage ta na addu'a duba da cewar bata da wata matsala a rayuwa. (Humm Shuwayya Shuwayya rayuwa sai da addu'a, ko duniyar nan Allah ya mallaka maka dole ka yi addu'a ka gode masa, ka roqe shi shiriya da tabbatuwar imani) Sun dauki kimanin kwanaki goma curr,Aaseeyah ta yi ziyara, ta yi ibada, har gidan Aunty Zahra'u sai da ta ziyarta, ta ga su Muhseen da Muhseena๐Ÿ˜๐Ÿ˜ (Masoya na) Aunty ta cika ta da tsaraba mai tarin yawa, dik da bata san da zuwan ta ba. (Wannan shi ne halin Aunty na,Babbar yaya uwa๐Ÿ˜๐Ÿ˜ kyauta da fifita dan uwan ta akan kan ta,wannan shi ne halin aunty, ina son ku 'yan uwana,Allah ya qara mana zumunci da qaunar juna) Duk wata siyayya da tsaraba Mahboob auna su Nigeria yake, dan haka daga su sai kayan sawar su. Aaseeyah ta yi murna, ta yi tsalle da farin ciki da jin qasa ta gaba da Mahboob ya zaba masu a matsayin suprise,wannan qasa ba wata bace face qasar Jordan, qasar kakan su, tushen iyayen su maza,a Amman suka fara sauka kafin daga baya su isa Irbed City, har qauyen Kakan su sai da Mahboob ya kai ta ya kuma gabatar da ita a wajen dangin su na nesa da suka rage, wanda sun cire ran sake ganin wani daga zuri'ar Abdulmudalleeb. Ranar da suka koma Irbed suna kwance a hotel din da suka kama, Mahboob na bata labarin makarantar su, tare da yi mata alqawarin washegari zai kai ta, har inda ya yi aiki, duk zai kai ta, kamar daga sama ya ji muryar ta, cikin sanyi da damuwa ta ce, "Har yanzu ban ji ka na maganar zuwa wajen Aemana ba" Shiru ne ya ratsa dakin na wasu mintoci, kafin daga baya ya sake gyara mata kwanciyar ta a jikin shi. "Inshaa Allahu, in ki na so mu je za mu je, a gaskiyar magana cikin zuciya ta ina son mu je mu ga ya ya take, amma ina tsoron kar na yi magana ki ce ko har yanzu ina son ta ne,ni kuma ba bu sauran soyayyar ta a raina, kawai ina so na ga irin rayuwar da ta ke yi ne a yanzu" "Ko zan yi kishi ba zan taba yi da Aemana ba, domin kuwa ko da a ce na fi ta son ka, ta riga ni fara son ka, ta riga ni komai da kai,kuma ita din ta na riqe da wani abu mai mahimmanci wanda muke nema a wajen ta, sai ta.bamu shi za mu samu cikakken farin ciki" Dan hade girar shi ya yi cikin rashin fahimta, daga kai ta yi ta kalli yana yin shi, tabbas bai fahimci me take.nufi ba, kissing din kuncin shi ta yi a hankali, sannan ta ce, "Ina nufin sai ta bamu yardar ta da kuma yafiyar ta,kafin muga dawwamammen farin ciki a rayuwar mu" "Haka ne" Hira suka ci gaba da yi, wadda ta juye da soyayyar su mai burgewa. ************************** Washe gari........ Ga washegari nan mutuniyar ku๐Ÿ˜‚ TAUBASHI PAGE 59 Mahboob ya dauka neman Aemana abu ne mai sauqi, amma inaa, ba bu inda bai duba ba a qasar Jordan amma ganin ta ya masa wahala, tambaya kuwa ya yi ta har ya gaji, tun ya nafita da Aaseeyah neman inda Aemana da iyayen ta suka koma har ya daina fita da ita, saboda ba ya son yawan yawon da suke babyn su ya samu matsala. Hankalin su gaba daya ya tashi, Aaseeyah a baya ita ke kwantar masa da hankali,amma yanzu da suka tasamma kwana sha uku a Jordan ba Aemana ba labarin ta ita ya koma lallashi, dan kuwa har da kukan ta ta na roqon Allah ya bayyana masu Aemana a dik inda take,saboda ta na son su roqe ta ta yafe wa Mahboob. Yau ma bai qasa a guiwa ba, ya shirya tun sassafe kafin Aaseeyah ta tashi ya shirya ya fice,ya na tsaye a qofar gidan iyayen Aemana na da, ya ga wani matashi da akwati a hannun shi, da alama daga tafiya ya dawo, kuma da dikkan alamu mazaunin awajen ne. Sallama yamasa, suka gaisa, sannan ya tambaye shi, ina su Aemna suka je? Matashin bai san sunan Aemana ba sai na mahaifin ta,dan haka ya gane su, ya kuma san inda suka koma, nan take ya sanar da Mahboob, shi kuma murna ta sa ya rungumi matashin tare da yi masa godiya, ya tafi da gudu ya samu taxi ya isa hotel din da suka sauka. Ta na zaune a saman sallaya ta yi sallar dhuha ta na ta addu'o'i, ya shiga, shafa addu'ar ta yi ta juya ta na kallon shi, ba bata lokaci ya dora labbn shi saman nata, tun ta na biye shi ta ji abun ba na qare bane, ta dan ture shi sannan ta ce, "Me ya sanya gwarzon maza farin ciki? Allah ya dawwamar maka da annashuwa da farin ciki har abada masoyi na" "Na samo gidan su Aemana, sun koma Riyad da zama, dan haka gobe can mukai" Aaseeyah murna kamar an mata albishir da abinda ta fi so. Rungume shi ta yi daga baya ta sake shi, ta hau hada masu kayan su. Dariya ya yi ya ce, "Tun yanzu ba zaki bari gobe ki hada ba?" "Da zafi zafi akan daki qarfe" Murmushi ya mata sannan ya fara taya ta, su na yi su na hira. Da safe kuwa kwatancen da aka masu nan suka isa,ko da taxi ta ajiye su, Mahboob tsoro ne ya kama shi, ya hau tunanin anyaa nan ne? "Aaseeyah anya nan ne? Wanne irin kudi baban ta ya yi haka da zai mallaki wannan katafaren gidan?" "Mu dai nemi izinin shiga, dan da alama gidan akwai matakan tsaro kala kala" Ai kuwa sun sha kwakkwafi da kwakwaf kafin su samu shiga. A wani kantamemen waje aka ajiye su, parlour za a kira shi ko me ne (yan gayu ya sunan irin wajen nan?) Waje ne mai kujeru kashi kashi, kowanne seti akwai kalar adon da akai a wajen shi, setin kujeru uku ne amma qayatuwar wajen abun kallo ne. Su na zaune aka gabatar masu da shayi, Aaseeyah kallon dan kofin tai tai tsaki kadan, qasa qasa tai da murya ta na ma Mahboob rada, "Ka san matsala ta da mutanen nan? Baqar rowa, dubi dan kofin da aka kawo mana shayi, wannan bai fi na masa zuqa daya ba ya qare, suna abu kama...." Takun takalmin ta mai tsini, tare da qamshin ta ne ya katse Aaseeyah, ba dan ita ma gwanar qamshi ba ce, lallai da mun ce Aemana ta ma Aaseeyah fintinkau a wajen qamshi. Aemana tsayawa ta yi kafin ta qaraso, ganin Mahboob da wata kyakkyawa a gefen shi,a tare suka miqe, Aaseeyah na yabon kyau da nutsuwa da ta gani a tattare da Aemana, ko ina a rufe yake a jikin ta banda fuskar ta, da hannaye da qafar ta. A hankali ta qarasa isa gaban su, sannan ta musu izinin zama, qafafun ta a harde ta dora hannayen ta a saman cinyar ta, ta saki lallausan murmushin da iyakar shi lips din ta, domin kuwa mamakin ganin Mahboob ya hana ta sukini, ga wani irin tsoro da ya shige ta, na tonuwar asirin abinda ta ake boyewa shekara da shekaru. Bayan gaishe gaishe, Mahboob ya fara magana cikin harshen larabci, Aaseeyah da ta ji larabcin ya fara qure mata gudu, ta masa magana, ya na magana a hankali yanda zata gane me yake fadi, dan daga kai ya yi sannan ya ci gaba da bawa Aemana hakuri, da kuma sanar da ita zuwan da ya yi da matar shi domin bata hakuri,ya sanar da ita Aaseeyah ita qanwar shi ce, wato cousin din shi, kuma ita ce ta bashi kwarin guiwar zuwa ya nemi gafarar ta, ta na jin haka ta miqe ta rungumi Aaseeyah, Aaseeyah da ta tsaya kamar an gina ta, daga baya ita ma ta rungumi Aemana, Aemana ta sumbaci kuncin Aaseeyah gefe da gefe. Nan ta hau yabon kyaun ta, da nutsuwar ta, sannan ta kalli Aaseeyah ta ce mata ta yafe wa Mahboob saboda Allah, saboda ita kuma, amma ba dan haka ba,ta so ta bar shi da Allah, har a lahira a musu hisabi, amma yanzu ta yafe masa, ko a lahira ta yafe masa ba hisabi na komai tsakanin su, ta na fatan Allah ya yafe masu laifin da suka aikata a baya. Murna sosai Mahboob da Aaseeyah suka dinga yi, abinci ta sa aka hada musu, suna ah ah suna ah ah, Aaseeyah sai da ta kwashi girkin larabawa ta gyatse, anan Aemana ta ke gane ta na da ciki murna ta taya su sosai, sannan ta sanar da su cewar nan din gidan mijin ta ne, amma baya nan, ya yi tafiya,iyayen ta su na nan garin da zama suma. Lokacin da suka rabu da Mahboob ta yi shaye shaye sosai, daga baya ta shiryu,ta nutsu ta koma bakin aikin ta, a nan ta hadu da mijin da yake auren ta yanzu, sukai aure, ya qara bunqasa kasuwancin baban ta, shi ne dalilin komawar su nan da zama, ta yi iya qoqarin ta na boye babban sirrin da ke zuciyar ta. Bayan sun gama hira suka mata sallama da niyyar tafiya, ta ce bata san magana ba, dole sai da ta tsaida su, suka kwana, washegari,ta dau Aaseeyah suka shiga mota ta ja da kan ta, suka zaga Riyad, ga siyayya kamar ba a son kudin haka ta wa Aaseeyah, har da sarqar zinare, qarshe Aaseeyah sai da ta zubda hawayen alkhairin Aemana a gare ta. Kwanan su biyu a gidan Aemana, a na uku, sun shirya tsaf za su tafi, Aemana ta tsaida Mahboob, idanun ta na zubar da hawaye sosai, ta sanar da shi labarin da ya firgita su matuqa. Wani hoton yaro ta dakko, sun dauka tare ta rungume shi suna dariya cike da nishadi da soyayya da shaquwa,tun zuwan su ta sa aka killace shi, a babban gidan, domin ba ta son Mahboob din ya san da yaron, amma daga baya sai ta ga rashin dacewar hakan. Hakuri ta bashi da boye masa labarin cikin da ya tafi ya barta da shi,har ta samu qaruwar yaro, wanda ta saka wa suna Mahmood,sannan ta masa warning da cewa in har ya ce zai dauke Mahmood to za ta kashe kan ta, dan ba zata iya rayuwa ba shi ba,Mahboob ya yi kuka kamar ran shi zai fita Aaseeyah na taya shi, fadi ya ke ya na kuma wa, Me zai ce da Allah, me zai ce ma iyayen shi? Me zai ce ma yaron da ya yi sanadin zuwan shi duniya ta zina? Da kyar suka lallashe shi, sannan ya mata alqawarin ba zai dauke shi ba, amma ta masa alfarma, ya dinga amfani da sunan shi, ta masa wannan alqawarin ita ma, sannan ta yi waya aka kawo yaron, suna hada ido da Mahboob ya sake fashewa da kuka,tsananin kamannin shi da Mahboob kawai ya wadatar ka san cewar yaro nashi ne, ba a buqatar DNA,hasken fata da yanayin gashin Aemana kawai yake da shi, yaro ya tasa gwanin sha'awa, rungumar da Mahboob ya masa ta bashi mamaki, amma sai ya samu kan shi da sake kwantar da kan shi a kafadun Mahboob, Aaseeyah na tsaye ta na shafa sumar yaron, cikin zubar hawaye. Kiss Mahboob ya ma yaron a fuskar shi ba adadi, har yaron sai da ya tsaida Mahboob shi ma ya mishi guda biyu a nashi kuncin. Sake rungume shi Mahboob ya yi, ya na bawa yaron hakuri, Aemana na tsaye da wayar ta ta na masu video, da hotuna, idanun ta na hawaye. Da kyar Mahboob da Aaseeyah suka iya barin Mahmood little a Riyad suka koma gida Nigeria. Dik jikin su ya sake, ba wani laka, yanzu me za su ce ma iyayen su? Ashe rabuwa da Jordan da Riyad bai kama su ba, dole ne su qulla zumunci,tunda shi ne dai mahaifin Mahmood, ya akai Aemana ta samu ciki bayan suna amfani da protection? (Ikon Allah) Mutanen gida an kacame da murnar komawar su, Aaseeyah ce ta lallashe shi, ta nuna masa dole ne ya saki jiki, ya yi murna da kowa da kowa, sannan dole ne ya sanar da kowa gaskiya, domin boye gaskiya ba abinda zai ja musu sai tashin hankali a gaban rayuwar su, ya aminta da ita, amma tashin hankalin shi da wanne ido zai fadi ya na da d'an shege? A gidan su Abee akai walimar komawar su lafiya, har Ummu suleim da musan ta sun je, an ci an sha, an yi wasa da dariya, sun sha labarin qasashen da suka je wajen hajiya Aaseeyah talkative, Mammee sai murmushi take, ganin yanda ciki ya wa diyar ta kyau, ta qara haske, ta cika, ta yi kyau. Bayan tafiyar Ummu Suleim da Musa ne, ana hira Mahboob ya yi gyaran murya ya ce, "Abbu ina da magana, dan Allah ina son kowa ya bani hankalin shi, sannan ina neman afuwa a gare ku tun kafin na fada maku abinda nake son fada, domin na aikata babban kuskure a rayuwa ta mai muni, wanda in kuka ji za ku iya tsana ta akan hakan, ku yi Allah wadai da ni da na zo a zuri'ar ku, sa...." "Kaiiii Mahboob ba na son wadannan munanan kalaman,ka sanar da mu me ke faruwa, in ji dai ba sakin Aaseeyah ka yi...." "Subhanallahi, Abbu, Ya salam, Abbu plss ka bar danganta saki a tsakani na da Aaseeyah, duk sanda na rasa ta mutuwa zan yi," "To me ne ne abinda ka yi ka ke wannan kalamai masu tsauri" "Abbu na aikata zina, sannan na samar da yaro ta hanyar zina, Abbu ina da yaron da ban sani ba mai sunan mahaifi na Mahmood a Riyad yanzu haka" "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, subhanallahi,....ya salam.... ya hayyu ya qayyum.... me ka ke fada haka" Wadannan kalaman ne ke fita daga bakin duk wani da ke zaune a wajen, kowa da kalar abinda ya ke fadi. Mahboob kuka ne ya dawo masa sabo, kunya da qasqanci ya ke jin sun dabaibaye shi,Aaseeyah ce ta basu labarin komai kamar yanda ya bata, da kuma abinda suka gani a tafiyar tasu,sannan ta dakko wayar ta ta nuna wa kowa yaron, nan take soyayyar balaraben yaron ta shiga zuqatan iyayen da ma kakannin. "Mahboob ka daina kuka, in dai ka tuba ga Allah wanda kuka sabawa, ka kuma yi tuban gaskiya, tuban da ka ke ganin ba zaka koma akan sabon da ka bari ba, to tabbas Mahboob ka gama komai, ba zamu tsane ka ba, ba zamu tsani yaron ka ba, sannan ba zamu yi Allah wadai da samuwar ka a zuri'ar mu ba, kowanne ahali akwai tashi matsalar, mu kuma tamu jarabawar kenan, muna fatan daga wannan ba zamu sake samun wani case na zina ba a zuri"ar mu,ka daina kukan nan haka na ce ya isa, inshaa Allahu, yanda nake ji a raina haka sauran yan uwa suke ji, Yaya amin afuwa na fara yanke hukunci kafin kai" Abee ya yi haka ne duba da yanda ran Abbu ya baci sosai, duk da ya ji son yaron a ran shi amma ran shi ya baci da abinda Mahboob ya yi, amma kuma kalaman Abee sun sanyaya ran shi, ya fuskanci Mahboob ba su ya wa laifi ba, Allah ya ma laifi, to in ya tuba ga Allah ai magana ta qare. Dan haka kowa ya tofa albarkacin bakin shi, Ummee ta ce, "A gaskiyar magana ba dan ka mata alqawarin barin yaron a wajen ta ba, da hannun mu ya dawo," "Ina ganin Maman Noor a hakura a bar mata shi, kamar yanda ta ce ba zata iya rayuwa ba shi ba, ina kyautata zaton amshe shi zai ja mata wani matsalar ko da bata rasun ba, domin da ganin yaron nan yanda suka rungume juna da uwar kin san akwai shaquwa, ki kalli hoton da kyau" "Haka ne kuma Subai'a, Allah ya raya shi a duk inda ya ke, Allah ya mishi Albarka, kai kuma daga yanzu ka koyi darasin rayuwa da kai da sauran 'yan uwan ka, da mutum ya yi zina gwanda ya auri mata hudu" Dariya wasu suka dan yi, daga baya aka ci gaba da hira kamar komai bai faru ba, da kyar Mahboob ya sake. Sai wajejen sha daya na dare su shidan suka kama hanyar gidan su, kowa ya yi godiya matuqa da irin tsarabar da ya samu, musamman iyayen maza da mata. Ko da suka shiga gidan su sun sha mamakin ganin wajen a gyare a tsaftace, ga qamshi na tashi, Tasneem ce ta bi bayan su, ta ce ma Aaseeyah, "To maman biyu, akwai abinci wanda ni da kaina na dafa maki, kala kala a fridge, ko da zaki ji yunwa, dumamawa kawai zaki ki ci, Allah ya sa dai ki yaba abinci na, dan kuwa nima yanzu renon Mamme ce," "Masha Allah, gaskiya na matsu ciki na ya zazzage na dandana girkin ki," Murmushin jin dadin kalaman Aaseeyah Tasneem ta yi, ta musu sai da safe ta tafi wajen su. Aaseeyah ta dudduba abincin ta sha mamaki, anyaaa Tasneem ce ta yi wannan ita kadai? Ko dai an taimaka mata? Ina nissani tun da nima bana nan...... This page is for my fev fans,and friends, musamman wanda suka damu da a ci gaba da rubuto masu labarin Aaseeyahn Mammee,Aunty Asmah, Samrah and Maman Khaleel...... I heart u all๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜ TAUBASHI PAGE 60 Baccin safen da suka koma ba qaramin dad'i ya yi wa Aaseeyah ba, wadda wayar da Amatullah ke ta zabga mata ne ya farkar da ita, Mahboob qunquni ya yi ya ja pillow ya rufe kan shi, cikin kasala Aaseeyah ta miqa hannu ta amsa wayar, "My goodness qarfe sha biyu da rabi fa, kar ki fada min bacci ki ke?" "Shi ne sallamar ki?" "Sorry Assalamu alaikum, ya kuke? Na kira na sanar da ke yau daga office nan zan zo na amshi tsaraba ta na wuce gida" "Kar ki damu,ki zo har da baby na na yi wa tsaraba," "Ohhh u are such a durling, sai na zo, a tashi haka baccin ya yi yawa wata daya be ishe ku ba ne? Dama na fad'a sai kin...." Aaseeyah katse wayar ta yi ta na dariya, Amatullah kuwa a bangaren ta fada tai ta yi Aaseeyah ta katse mata waya bata gama fadin abinda ta ke so ba,daga baya ta yi murmushi, tare da yi musu addu'ar kasancewa cikin so, qauna, da zaman lfy har qarshen rayuwar su. (In ka yi wa wasu fatan alkhairi, sai fatan alkhairi ya same ka, in ka yi wa wasu mummunan fata sai ya same ka, wataqila bai same su ba) Juyawa ta yi ta ga yanda Mahboob ya dan bude bakin shi, labban shi suka bude, sai abun ya bata dariya, matsawa ta yi ta yi kissing lips din shi, ya juya cike da shagwaba ya rungume ta, shafa kan shi ta fara yi cikin sigar lallashi, tare da janye bargon da ya rufe su, sake manna kan shi ya yi a qirjin ta ya na shagwabar ta barshi ya dan qara bacci kadan, cikin rada da lallashi ta ce, "Ka yi hakuri Nisful hayatee,ka ga lokacin azahar ya kusa, yaushe ka tashi na maka wanka, na shirya ka, ka tafi masallaci? Daya saura fa yanzu" Dan bude ido ya yi kadan ya sake kulle su, rungume ta ya yi still kan shi na qirjin ta, fuskar shi ya dora saman qirjin ta ya kauda gefe, sannan ya ce, "A gaskiya ina ganin duk duniya ba wanda ya yi sa'ar mata sama da ni, Mar'atee kin cancanci a kira ki da suna Mar'atussaliha,in da abinda ya fi haka ma zan kira ki da shi,mata da yawa suna fadin sun maida miji kamar jariri, a gaskiya gatan da nake samu a wajen ki ya fi na jariri, ban san yanda zan kwatanta jin dad'i na a gare ki ba, amma na san yanda zan na dinga miki addu'a, dan haka daga yau ki sa a ran ki addu'a ta a gare ki ba mai yankewa bace, Allah ya miki albarka, albarkar Allah ta qunshi komai na alkhairi cikin ta, da albarka zan ta hada ki har qarshen rayuwar mu" Aaseeyah sarkin kuka, nan da nan hawayen farin ciki ya fara sauka a kuncin ta, Mahboob kuwa murmushi ya ke yi, sannan ya juya ya daga ta, ya maida ita jikin shi ya na lallashi, cikin shagwaba ta ce, "Ka sa kai na ya yi qatoto, sai nauyi yake min, kamar wata wadda nake maka wanka kullum ko nake goya ka, ko irin ina baka abinci a baki kullum dinnan" "Aaseeyah kenan, ba zaki gane alkhairin ki a gare ni ba, sai kin zauna kin nutsu da kan ki kin fara lissafi, sai Numbers sun qare maki wajen qirge,ko da ba kullum ki ke min wanka ko ban abinci a baki ba, amma ki na lura da sanda na fi son kulawar ki, ki na bani ita, sannan ko baki taba goya ni ba jikin ki ya zamar min wajen kwanciya ta, wajen hutawa ta, in banda ma ina tausaya maki ke da babyn mu ai...." Rufe masa baki ta yi da hannun ta ta na dariya, "To ya isa haka, ni dai kar ka fara sakin layin maganganun ka masu ban kunya, muje Amatullah will kill us in ta zo ta tarar ban shirya ba,ita ta min waya dazu" Da sauri ya dira ya kama hannun ta suka shige bayi. A leqen da na masu anan na gano yanda mace ke dirje miji ta masa wanka ya yi fes, kamar jariri,anan na hango yanda mace ke ririta miji kamar ta na dauke da kwai, qafafun ta na saman garwashi, kuma ba ta son kwan ya fadi ya fashe, gaskiyar Amatullah ne, domin kuwa kulawar da Aaseeyah ke bawa Mahboob Amatullah ba ta yi rabin shi ba duk tsahin rayuwar auren su. Bayan sun yi wanka ne sukai alwala suka fito a tare, nan ma ita ta fara shafa masa mai, sai qi yake ya na fadin ya yi alwala, hannun shi ta dan doke sannan ta ce, "Kai yanzu shafa man ma sai ya zama karayar alwala? A qafa ne kawai fa" "Lallai yarinyar nan baki san me duniya take ciki ba har yanzu, ban man nan ki gani, sanda banda alwala kin shafan" Amshewa ya yi ya qarasa ta na ta masa dariya,ya na cewa ya dai ji, basu yi minti uku da kammala shiri ba Amatullah ta iso. Sai da Aaseeyah ta saka abinci a microwave sannan ta je ta bude mata qofa, Mahboob kuwa a tsaitsaye suka gaisa ya wuce masjid ya ce zai dawo. Aaseeyah ta sha tsokana da tsiya kala kala wajen Amatullah, tun ta na iya ramawa har kunya ta hana ta magana. Aaseeyah da Amatullah sun yaba wa girkin Tasneem matuqa,domin a matsayin ta na me koyon girki ta yi wannan abinci mai dadi, ta yi qoqari ainun. Aaseeyah bata jira ba sai da ta kira Tasneem ta waya ta na ci ta na santi, ita kuwa ta na ta dariyar jin dadi. Bayan sun gama ne Aaseeyah ta dakkowa Amatullah tsarabar ta, da ta babyn ta, da na Maman su da na matar AIG Aliyyu. "Irin wannan tsaraba haka kamar dan mu kika je? Mun gode mun gode mun gode sosai" "Habaa ba godiya, yi wa kai ne, ai mun zama daya, bayan haka na baki labari mun ga tsohuwar budurwar Yah Mahboob, to ta yi aure, ita ce ta ja ni muka je shopping wasu abubuwan ma ban san ya zan amfani da su ba, har a sarqar zinare ta sai min," "Wowww she mst be filthy rich, Allah ya saka mata da alkhairi, da batai aure ba da na ji kishi, amma tunda ta yi aure ta qaro ma muna so" Dariya suka yi sosai, Aaseeyah ba ta yi gigin sanar da ita

Chapter 37 of 41