jarabawar da Allah ke masa a rayuwar shi, wani ya samu, wani ya yi rashi, duk yanda rayuwa ta zo maka, ka godewa Allah kawai, sannan ka tsarkake imanin ka a gare shi.
Rayuwar gidan mutanen Jordan sai godiya,kamar koda yaushe, arziqi na qaruwa masu sakamakon habaka da kasuwancin qarafan su ke yi, har qasashen waje yanzu an san da kamfanin su, hakan ne ya sa iyayen suka sake zama busy, sun damqa ragamar kula da tarbiyyar yaran a hannun mata kacokan, wannan dalilin ne ya sa Mammee sake qaimi wajen kula da tarbiyyar Aaseeyah, ita da kan ta ta ce bata yarda da karatun Aaseeyah da Noor a daki ba, a na fita tsakar gida under bishiyar ced'iyar dake wajen su na karatun, hakan bai wa Noor dad'i ba sam, ya so a bassu a dakin, amma ba komai, watarana sai ya yi abinda ake hana shi, ko da aure ko ba aure.
Aaseeyah ta fara gane inda aka dosa a karatun,murna a wajen ta ba a cewa komai, yanzu a SS3 suke ita da Umaimah,Ummu Suleim da Yesmeen kuwa sun yi candy, dan haka Aaseeyah da Umaimah sun samu sabbin masu koyar da su a gida, Noor ya koya masu sanda yake free, domin ya fara aiki a gidan Talabijin na NTA dake nan kano, abu na masu hannu da shuni, ba su rasa aiki, sai d'an talaka,duk cancantar shi sai ya nemi aiki ya rasa, sai wanda Allah ya taqaita wa wahala,wasu kuma kan su samu sai sun bada maqudan kudin da ko gidan su na gado su ka siyar wani bai isa hada kan kudin ba, Allah ka shiryar da mu da wannan zamani da muke ciki.
Mahboob na zuwa aiki a kamfanin Dangote Abbu ne ya sama mashi aiki a wajen, in ya fita sai yamma yake komawa a gajiye, bayan isha'i yake koyar da su, da sun kammala zuwa tara na dare, zai kwanta dan hutawa.
'Yaj biyu na shekarar su ta qarshe wajen kammala Jami'ar su, ba tare da sanin kowa ba sun samu wasu zafafan 'yan mata a makarantar wanda suka yi wa alqawarin aure, dan kuwa sun wa kan su alqawarin auren sabbi a leda gadagau,su na tantamar kyautatuwar budurcin su Ummu Suleim.
Su na da burin sanar da wannan kyakkyawan labari na auren su a ranar da suka kammala jarabawar qarshe.
********************************
Zaune ta ke a saman kujera sanye da dogon wando, da ya matse ta sosai, sai riga wadda ta ke sakakkiya, kalar blue, gashin ta a daure a dunqule a dokin wuyan ta, abinci take ci a saman kujera, ta na kallon TV tare da murmushi, ganin yanda Noor din ta (inji Aaseeyah fa ba ni na fad'a ba, kar ku manta ta ce shi za ta aura... wink) ke gabatar da wani shiri mai farin jini a wajen manya,domin kuwa hira ne da 'yan siyasa,dattijan qasa,da jami'an tsaro kala kala,ita ba wai shirin ke burge ta ba,kwarewar Noor ke bata sha'awa, bayan sallama da gabatar da sunan shirin nasu, sai ya fadi baqon su na wannan rana, nan da nan hankalin Aaseeyah ya bar kan na Noor ya koma kan matashin da aka kira da suna CP Aliyyu Nuhu Kacako.
"Masha Allah"
Shi ne abinda Aaseeyah ta furta, tare da maida remote din ta aje, ta fasa sauya tashar da tai niyya.
Ajiye abincin ta yi ta na qarewa bawan Allahn kallo,tun daga kan fular shi ta 'yan sanda har zuwa daidai hannayen shi da ake nuna wa, Baqine irin mai sheqin nan, fuskar shi ya ajiye gashin baki, wanda ya mata kyau sosai, dan a ganin ta bata taba ganin baqin mutumin da gashin baki ya amsa ba kamar shi, ya na da matsakaitan idanu wanda in ya lumshe su sai su yi kamar ya na jin bacci ne.
Yatsun hannun shi dogaye, farcen nan ya sha yanka fari qal da shi, ba qaramin kyau Uniform din suka mishi ba, muryar shi ce ta katse mata tunanin surar shi, turanci ta ji ya na jefawa lokaci zuwa lokaci, wani abu ta hadiya mai qarfi, lallai mutumin nan, ba mamaki tashin turai ne?
Har ya zauna a kusa da ita tare da amshe plate din abincin ya fara cin abinci, duk bata sani ba, sai da ya gama ya dora mata a saman kan ta, da dan qarfi, sannan tai sauri ta kalle shi, kunya ce ta kama ta, sai ta hau noqewa ta na masa surutai na kare kai, kamar ya tambaye ta.
"Kin ga ni ban tambayi komai ba, sai dai yanzu zan tambaya, ya jarabawar yau? Ina fatan ta maki sauqi kamar sauran"
"Alhamdu lilLAAH Yah, komai ya na tafiya normal"
"Allah ya bada nasara, in kin gama kallon dan sandan ki kawon abinci na, and i am sorry na cinye maki naki"
Murmushi ta yi sannan ta nufi kitchen da kallo mahboob ya bi mazaunan ta sa suke tsokane masa ido.
'Bari Yah Noor ya zo na masa tambayoyi game da CP Aliyyu'
Hummmm i don't think zai baki amsar da kike nema Aercee....
Ko ya kuka ce nasoya Aercee????
TAUBASHI
Page 24
Ta na tsaka da karatu Noor ya dawo, tattara komai ta yi, ta debar mishi abinci daga bangaren su, ta shiga d'akin shi, Ummee na ta mata surutu,
"To jarababbiya, yanzu abun na ki ya wuce manne mishi da ki ke a tsakar gida, har da wani salon iskancin debo masa abinci daga wajen ku, kamar na ce maki ban iya dafa abincin da yara na za su,"
Aaseeyah leqo kan ta ta yi ta ce,
"Yo in ma dai kin iya ni ba ruwa na, d'an ki ne ke son cin wannan din, sai ki mai magana ya daina ci in an kawo"
Ta na gama fadin haka ta danna sakatar dakin, ba qaramin aikin Ummee bane ta ce za ta shiga ko suyi cacar baki ko ta daki Aaseeyah,Aaseeyah na ganin tai nasarar rufe qofa kan Ummee ta qaraso ta wani buga tsallen murna, zuciyar ta dama a riqe take a qirjin ta da tsoro.
Murmushi Noor ya yi, dan ya san rigimar Ummee da Aaseeyah tun ba yau ba,tun su na bashi haushi, yanzu dariya suke bashi.
"Mata ta ba ki jin magana, akwai ki da shegiyar tsokana, yanzu ina ke ina tsokanar suruka in ba kin zama surukar zamani mara ji ba"
"Yah Noor banni da Ummeen nan, sai ana mata zangan-zangan"
"Auuu Ummeen tawa za ki wa Zangan-Zangan? Anya ma ki na son auren nan kuwa,"
Da sauri ta je gaban shi ta na shagwaba,
"Ni ina soooo"
"To shi kenan, zauna ki jira ni, bari na dan watsa ruwa,...ko kuma ban abincin nan na ci yunwa nake ji, sai ki min tausa ko? Kin san dama miji in ya dawo daga aiki tausa matar shi ke yi masa, dan ya hutar da shi gajiyar da ya kwaso, ko ba za ki min ba?"
Shiru ta yi, can da ta tuna mai ya kawo ta sai ta ce,
"Zan maka mana, zauna ma na baka abincin da kai na"
Ba kunya ba tsoron Allah Noor ya dinga bude baki qanwar cikin shi na bashi abinci, sai da ya qoshi ya dakko ruwa ya sha da yake ajewa a dakin shi,ya yi hamdala ya baje a a Katifar shi qatuwa, ya na lumshe ido, hannu ya miqa mata, ya mata nuni da kusa da shi, zama ta yi jikin ta ba kwari,shi kuwa Noor ji yake kamar ya cika burin shi a yau, a yanzu a kan ta, amma dole ya jira, lokacin da ba mai zargin shi,lokacin da ita kan ta ba za ta iya banbance waye ba.
Cikin murya mara sauti ya ce,
"Ban ji kin fara min tausa ba, ko na je nai wanka na ne?"
Qasa ta koma, ta kama qafafun shi ta fara masa tausa, nunfashi kawai Noor ke saukewa, jin hannayen ta masu laushi a jikin shi, kifawa ya yi ruf da ciki, cikin shaqaqqiyar murya ya ce,
"Ba fa iya nan ake tausa ba Aaseeyah, har sama ake yi, tunda kin ga zama na yi baya na ciwo yake, ya kamata dai a mana auren nan na huta,"
Jikin ta ya yi sanyi qalau saboda baqon yanayin da take ji in ta taba shi, da sauri ta fara mishi har baya ya na sauke numfashi sannu a hankali,Noor qoqarin fada da shaidaniyar zuciyar shi ya dinga yi, da ta ke raya masa munanan abubuwa.
"Yah Noor?"
"Uhummm"
"Yau ma na gan ka a TV, ba ka ga yanda ka yi kyau ba, gaskiya ka na ma mutanen nan tambayoyi masu zafi, wasu har rudewa na ga suna yi, gaskiya ka san kan aikin ka, amma wannan dan sandan na yau akwai wayon tsiya, ko ina ne gidan su? Ka san abun gado ne wata qila ya gaji wayo a gidan su"
"Ai ni ma na kula da haka,shegen wayo ne da shi, akwai tambayoyin da na so ya amsa min su, ya fayyace ma duniya, amma sai ya nuna harkar aikin su ce ba zai bayyana ba,....immm ina ga kamar a Nassarawa gidan su yake, baban shi ai shi ne tsohon IG of police da ya yi murabus,ko baki gane IG Nuhu Kacako ba?"
"Laaa dama d'an shi ne? Tabdijm gidan hukuma kenan, "
Kauda kan ta ta yi ta na dariya,ko IGn bata gane ba, in banda Yah Noor dika dka yaushe ta fara gane duniyar da abinda ke cikin ta,bangaren karatu duk da ana masu History ba ta taba jin sunan shi ba balle tarihin shi, ba su hulda da ire-iren mutanen ina za ta wani san former IG of Police,dariyar ta ta qunshe tace,
"Yah Noor na ji kamar ana kiran sallar isha'i, ka tashi ka watsa ruwan ka tafi masallaci,"
Qoqarin tashi take ya fizgi hannun ta ta fada jikin shi, ya zauna sosai, tare da matse ta a jikin shin sai da ta saki qara,
"Yah Noor da zafi fa, gaskiya ka daina min haka b naso,ka sake ni in tafi,zan yi kuka fa, saura qiris na fara..ka sake ni,"
Sakin ta ya yi ya na maida numfashi, murmushi ya mata idanun shi na lumshewa,hararara ta banka masa, ta turo baki, tare da kwashe plates din, sai da ta kai qofa ta bude, sannan ta ce,
"Ba zan sake kawo maka abincin mu ba, mai matse ma mutane qashi har sai sun fara targade"
Da sauri ya bi ta,yau duk gudun Aaseeyah ba ta tserewa Noor ba,ta na jin ta a hannun shi ta fashe da kuka, ta tsani ta na son tserewa laifin ta a kama ta, hankalin ta take ji ya tashi ainun,maida ta d'akin ya yi, fuskar shi abun tausayi, ya ce,
"Yanzu dan kin kawon abinci kin min tausa na rungume ki dan na nun maki godiya ta shi ne kk jin haushi na? Indai dan haka ne ki hakuri, ko ruwa kar ki sake kawon, zan kuma nemi wata matar da zan aura, dan b zan auri wadda ba za ta iya kula da ni ba, mai bayyana sirrin duk abinda muka yi ba"
"To ni wa ka ji na ce zan fad'awa"
Bakin ta a ture take maganar, ba dan qoqarin rufawa kan shi asiri yake ba kar ta je ta na fadin ya rungume ta a waje, da ba a binda zai hana shi kissing din ta.
"Ok ke nan ba fad'a za ki ba? Amma me ya sa ki ka fad'a dazu, kuma a waje, in wani ya ji fa?"
"Yah Noor ba a so a ji ne? Na ga har taus...."
"Shhhhiii, wai ke wa ya ce maki in mata ta ma miji abu ana fada? Aure fa sirri ne"
"To ai mu ba ma'aurata bane"
Ran Noor ya fara baci, lumshe ido ya yi sannan ya wara su a kan fuskar ta,
"Shi kenan je ki ki ta fadin kin min tausa, na rungume ki, tunda ke ba macen sirri bace, ba zan iya auren irin ki ba, ana koya maki sirri tsakanin miji da mata kina nuna ke bamai sirrin bace, fita kawai jeki, in kin ga dama har Abee ki fadawa, ki fadawa Abbu ma"
Ganin ya yi fushi sosai ne ya sa ta kallon fuskar shi da sigar bada hakuri, amma yawuce bayi ya barta tsaye,sai ta ji bata ji dad'i ba sam,su na nan suna shiririta har an idar da isha'i, ko da ta fita tsakar gida, da Mahboob ta ci karo,kan ta a qasa za ta wuce shi, har ya so ya barta tawuce, dan da alama ranta bace yake,sai ya ji wani qamshin da ya sa ya yi saurin shan gaban ta ya tsaida ta.
"Aaseeyah daga ina kk da daren nn?"
"Daga wajen Yah Noor"
"Me ya faru qamshin turaren shi ya ke a jikin ki sosai har ana ji?"
Zare idanu ta fara,ta na ja da baya, ya gane halin ta by now, so take ta kyalla da gudu, hannun ta ya riqe ya zare ido ba wasa,
"To ni ba zan fada maka ba, tunda dai ya ce sirri ne, dama ni ba na riqe sirri, yanzu in fada maka,ya ce ya fasa aure na"
Fizge hannun ta tai ta na kuka ta shige bangaren su,hankalin Mahboob a tashe ya nufi bangaren su Noor, abinda ya jima bai ba, tun dawowar shi, Ummee ta san ko da can ba ya shiga wajen ta,sai in aike shi, iya karshi wajen Kakannin shi wanda hade yake da nasu, sai wajen Mammee.
Ta na daki ta na kwalliya ya shige gidan, so ba ta san da zuwan shi ba (yau ana buqatar Abbu kenan tunda ake kwalliya)
Su Umaimah kuwa mamakin ganin shi sukai,dan haka suka miqe su na bude baki,
"Ina Noor?"
Hanyar daki suka nuna masa, ya na wucewa su ka fara gulmace gulmacen shigar shi.
Banka qofar ya yi ba ko sallama, Noor na daure da towel iya qugun shi,gashin kan shi da ke a aske sai kyalli ya ke alamar an sa masa ruwa,Mahboob ne ya kalle shi cike da bacin rai ya ce,
"Me ka yi wa Aaseeyah?"
Gaban Noor ne ya fadi, amma sai ya dake ya ce
"Na ce maka me ka yi wa Aaseeyah?"
Cikin daga murya da nuna tsananin bacin rai ya ke maganar, sai da Noor ya dan ja baya,
"Ita ba ta fada maka me nai mata ba? In ka na ganin dukan ta nai, ko wani abu, ka je ka tambaye ta mana"
Matsawa daf da Noor Mahboob yayi har su na jin numfashin junan su, sannan ya saka yatsan shi manuni a qirjin Noor, ya ce,
"Qamshin ka na dikkan jikin ta ka ke nuna ba ka san me kai ba? Idanun ta na zubar hawaye amma ka ce ba ka san me kai ba? Ta na kiran kalmar Sirri a tsakanin ku amma ka ke nuna min kai mutumin kirki ne? Wankan me ka yi? Noor kallon da na ke maka a da daga yau ya sauya, ka san me? Zan saka maka ido, inna gane ka na wani abu da bai dace ba, inna gano wani abu....humm"
Tura Noor baya ya yi da qarfi sai da ya fada katifar shi, sannan ya bude qofar da qarfi ya fice, Umaimah da ke maqale ta yi saurin sake mannewa a bango, Mahboob na tafiya ta fad'a dakin Noor, hawaye na zuba a idon ta,zuciyar ta na quna ta bude vaki za ta yi magana, ya daka mata tsawa,ita ma ta daka mishi tsawa,
"Ba zan yi shirun ba ! Na qi na yi shirun,"
Cikin sassauta murya, da zubar hawaye ta ce,
"Ashe amana ta ka ke ci da Aaseeyah? Ba zan yafe muku ba, kuma sai Allah ya saka min, sannan sai na ci uban ta yau a gidannan"
Da sauri ta ke qoqarin barin dakin, Noor ya ja ta ciki,ya rufe qoqafar, lallashin ta ya dinga yi, ya na bata labaran qarya, har ta gamsu, nan fa ya fara gwada mata soyayyar shi mai kwantar mata da hankali, ni kuma na ja musu qofa na tafi wajen Mahboob Shuwayya-Shuwayya, dan ganin halin da yake ciki.
Sintiri kawai ya ke a dakin,ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba zai taba bari a masa kasassaba ba, yau zai maganin komai, yau za a yi ta ta qare........
Shuwayya-shuwayya me ka ke nufi da hakan?
TAUBASHI
Page25
Sauraye ke ta cizon farar fatar shi, amma bai damu ba, sai sintiri yake a tsakar gidan, mai gadi sai leqen shi ya ke ta dan qaramin windown dakin shi, mamakin ganin Mahboob a waje ya ke da sintirin da yake, tunani ya ke ko zai je ya tambaya ya ji me ne ne matsalar, ko abinda zai iya taimaka wa ne.
Ya na qoqarin fita ne ya ji horn din masu gidan, da gudu ya qarasa fita, ya fara bude gate, Mahboob ma da sauri ya isa gefen inda suke parking ya tsaya, su ma sun yi mamakin ganin shi a wannan lokacin, ko da suka fita kusan a tare su ka tambaye shi,
"Madha hadath laka?...madha turidu?"
Murmushi ya dan yi sannan ya sosa qeya ya kalli Abbu ya ce,
"Abbu ina so na yi magana da kai in ba damuwa, duk da na ga dare ne kun gaji"
"Too maganar tsakanin ka ne da Abbun ku ni to na yi ciki, na gaji sosai, ina buqatar hutawa, sai da safe"
"Sai da safe"
Mahboob bai ji dad'in yanda ya ware Abbun ba, kar Abee ya yi ta tunanin me za su ce,dan haka sai ya ce,
"Abbu zai sanar da kai abinda zan fad'a mishi"
"Kar ka damu, sai da safe"
"Allah ya kaimu"
Abee na hamma ya wuce su, ya shiga sashin su, Abbu kuwa ya samu waje ya tsaya, a jikin motar shi ya na jiran ya ji daga Mahboob din, dan haka ba bata lokaci Mahboob ya zayyana masa abinda ya ke shirin sanar da shi din, fuskar Abbu ce ta yalwata wajen murmushi, da godiya ga Allah, sannan ya sanya wa Mahboob albarka da qudirin na shi, sallama sukai, kowa ya nifi makwancin shi, Mahboob wani irin nishadi ya ke ji, ji yake iska na shiga jikin shi da kyau, da duk a takure yake da tsoron abinda zai je ya zo, amma da alama Abbu ya yi na'am da wannan lamarin, to ya san kowa ma inshaa Allahu zai amince.
Da sassafe Abbu ya tambayi Ummee da yaushe yaran za su tafi jarabawa? Dan a lissafin shi yau ne za su zana ta qarshe,amma dan tabbatarwa ya tambaye ta,budar bakin ta sai ta ce,
"Ina zan san yaushe za su gama, ni da ba da ni ake zuwa zana jarabawar ba"
"Ke dai Fateema Allah ya shirye ki, yanzu ace Umaimah da Aaseeyah na zana jarabawa ke baki san yaushe ma za su gama ba? To me kike a cikin gidan da har vaki san me ke faruwa ba?"
"Ka ga kar ka sauken kwandon masifa akai, ina da abubuwan yi masu mahimmancin da suka fi tsayawa tambayar yaushe za a gama jarabawa, nan nan har su Ummu Suleim suka gama ban san sun fara ba balle gamawar su, dan haka dagan qafa na wuce"
Daga mata qafa ya yi ta sauka daga saman gadon ta bar dakin dika.
Tsaki ya ja,ya tuna jiyan da daddare har jiran shi ta yi, saboda biyan buqatar ta,harda zuba masa abinci da hannun ta, amma ynz tunda ta kau da sha'awar ta ya koma dan iska a waje ta, wani tsakin ya sake ja sannan ya shiga wanka.
A office ya samu Abee ya na ta aiki,ya nemi izinin sakataren shi sannan ya shiga.
Sakataren Abee shi ne babban sakatare da ke ma'aikatar tasu, Abbu shi ma na da tashi sakatariyar wacce ta ke kula da bangaren shi, da ba da izinin ganin shi ko hana wa.Abee ba yason zaman Sakatariya macea wajen Abbu, musamman wadda ya dauka aiki kwanan nan, yarinya ce wadda ba ta jima da kammala karatun ta ba, ba za ta wuce shekaru ashirin da hudu, zuwa da biyar ba,ga ta da ado da kwalisa, in ka shiga qamshin turaren ta ne zai fara maka sallama, kafin kyakkyawan murmushin ta, Abbu na matuqar jin dad'i in ya je Office, ji ya ke ya fi masa gida.
Abee kuwa ya sa mashi ido ainun, duk da bai ga wani mummunan abu na faruwa a tsakanin su ba.
Office din Abee shi ne babba a ma'aikatar, wannan na daya daga dalilan da ya sa Ummee har yau ta je jin haushin Abee, da mijin na ta ma, ya na babba amma qani shi ke riqe da dukiyar su.
Murmushi sakataren Abee ya ma Abbu, dan ba sai ya masa iso ba, da sallama ya bude qofar ya shiga.
Mamakin ganin Abbu Abee ya yi duba da cewar safiya ne akwai ayyuka da yawa,
"Bismillah Yayah, lafiya dai ko? "
Zama Abbu ya yi inda Abee ya nuna masa, sannan ya yi murmushi,
"Lafiya qalou, abun alkhairi ne ya same mu, na ga ba zan iya bari har wani lokaci mai tsaho ba, shi ya sa na same ka,"
"To Alhamdu lilLAAH, me ne ne wannan abun alkhairin da ya sa ka murmushi mai qayatarwa haka?"
"Babban abun alkhairin shi ne, abinda Mahboob ya sanar da ni jiya da dare, ya na son idan ba mu yi wa Aaseeyah miji ba, ya na so mu taimake shi mu aura masa ita, bayan ta kammala secondary din ta"
Murmushi sosai mai sauti Abee ya yi, idanun shi har kwallar farin ciki suka kawo, miqawa Abbu hannu ya yi tare da taya su murnar wannan lamarin, sun ji dad'i matuqar gaske, nan dai suka fara tattaunawa game da yaran nasu baki daya.
"Wato Yayah na jima ina jin labari wajen Subai'a yanda ta kula da kusancin yaran nan gaba dayan su, har take ganin kamar akwai soyayyah a tsakanin su, amma ni yanda take sanar da ni kamar Noor na son Aaseeyah, shi kuma Hussein Ummu suleim, Hassan kuwa Yesmeen, kusan ko da yaushe ina nuna mata damuwa ta akan rashin ganin manema na zuwa wajen yaran nan, ko da na wasa ne,nan ta ke sanar da ni ana zuwa ba ba a zuwa ba, yayun su ke korar duk wanda ya zo, kenan ka ga suna yi wa kan su kamun qannen nasu ne me ka ke gani akan hakan? Ko ka ji wani abu daga Maman Noor?"
"Kai rabu da wannan shashashar, ni ina rasa me ye amfanin ta a gidannan nan,nan nan tambayar ta nai fa yaushe yara za su gama jarabawa ba ta sani ba, kullum ta na gaban TV a daki, ba ta da aiki sai kallo kamar wadda ta warke daga makatanta, Allah dai ya shiryi Fateema, amma lamarin ta akwai abun takaici,"
"Ameen yayah, mata lamarin su sai an had'a da hakuri,"
"Kai hakurin ka ke? Ina ce kullum yabon matar ka muke gaba dayan mu akan nagartar ta, amma ita halin ta daban da na kowa,watarana ji nake kamar na sawwaqe mata kawai"
"Subhanallahi, dan Allah yayah ka daina jin hakan, duk rashin amfanin mace akwai amfanin ta a wani wajen, haka duk amfanin mace a wani wajen sai ta gaza, ka qara hakuri za ta sauya ne lokaci ne"
"Allah ya sa to, amma Fateema, Fateema, humm, Allah ya shirya,to yanzu dai bari za mu yi sai yaran nan sun kammala jarabawa mun hada su mu ji ya abubuwan za su kasance ko?"
"Eh yau ai su Aaseeyah za su kammala jarabawar su,"
"To da kyau, hasashe na ya zama daidai kenan,Allah ya basu sa'a, ba damuwa zuwa Juma'a dai ko asabar tunda muna gida, sai a hadu dika a yi maganar ko?"
"Eh haka ya yi,"
"To sai mun hadu an jima, bari na koma bakin aiki na"
"To Yayah sai an jima, Allah ya taimaka"
"Ameen"
*****************************
Aaseeyah ce a gaban ajin su, ta na tsaye kamar ta Allah, makarantar su akwai masu zuwa zana jarabawa daga waje,dan haka a hall din makarantar aka tara su suke zana jarabawar su, ko kunyar baqin da ke ajin Aaseeyah ba ta ji, dan ita ji take ba wata baquwar fuska, duk su ne.
"Abinda ya sa kuka ji ina ta roqon ku da ku yi shiru zan magana shi ne, ina so na roqi gafarar ku ne, akan duk abinda na muku daga randa muka fara karatu tun Nursary nake nufi har yanzu da muka kammala jarabawar qarshe ta secondary, a wannan makaranta,dan Allah ku yafe min, na san dik cikin ku ba wanda ban taba yi wa wani abu ba da ya bata ran shi, dan Allah ku yafe min, a rabu lafiya"
Kusan hada baki suka dinga yi ana "Na yafe miki, na yafe miki"
Mutum daya ne ya je gaban Aaseeyah mai suna Sabeer,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 41