ilimi akan zaman takewar rayuwa kuwa"
"Babu komai Mammee indai ina da ke ban da damuwa a duniya"
Maganar ta shigi Mammee sosai,
'In bani da rai fa?'
Shi ne tambayar da Mammee ta wa kan ta a zuciya, surutun Aaseeyah ya dawo da ita daga gajeran tunanin da ta fad'a, tashi ta yi ta bata waje, dan ta na da abun yi, Mahboob tun dazu bai ce komai ba,in banda nazari da kallon Aaseeyah da yake, ya na ta shawara da zuciyar shi,shin ya ta ya ta roqon ci gaba da karatun ne ko kuwa? Me zai yi? Ji ya yi kujerar da ya ke zaune ta dan fada alamar an zauna a gefen shi.
Wani qamshi ne ya ziyarci hancin shi kamar na sweet, ga qamshin ta mai sanyi da ya riga ya sabawa hancin shi shaqar qamshin nan, jan numfashi ya yi, qamshin bakin ta na shigewa qofar hancin shi, a hankali ya sauke idanun shi akan ta, sannan ya dan ja baya kadan, domin bai aminta da kan shi ba da kusancin da ke a tsakanin su, qamshin bakin ta na fizgar shi sosai ba kadan ba, me take sawa a bakin nata ne yake qamshi mai dad'i haka?
"Yah Mahboob, dan Allah ka sa baki mana, ...ok here is a deal, in dai ka sa baki aka barni na ci gaba da karatu, na maka alqawarin auren ka, amma indai ba a barni ba, ba zan taba auren ka ba, ka dai san Abee ba zai min auren dole ba ko? Mammee ma ba za ta bari ba, bar ganin su na son ka, sun sha fad'a min tare da min alqawarin ba za su min auren da bana so ba,ya ka gani? Za ka tambayar min ko kuwa na nemo wani mijin?"
Cikin hade fuska ta qarasa maganar ta, wanda ya tabbatar wa da Mahboob gaskiyar zancen ta, wani irin kishi ne ya tasar mishi, yaushe ma zai bari Aaseeyah ta auri wani ya na raye,inaaa, shi ne mijin Aaseeyah, ba zai bari ta auri kowa ba sai shi,kallon ta ya yi sannan ya ce,
"Aaseeyah in ban manta ba kamar karatun lauya gaba dayan shi daga shiga university zuwa service da law school shekara biyar ne ko?"
"Ah ah Shekara shida ne yah mahboob"
Da sauri ya juya ya kalle ta a razane, me yake jira har shekara shida bai aure ba? Ruwa take so ya koma ko me? Shin bata san iya qoqarin da yake ba na danne sha'awar shi ne so take ta lalata masa shiri gaba daya wannan yarinyar.....
"Sam ba zai yu ba Aaseeyah, ina nan zaune har ki kai shekara shida ki na karatun Lauya, haba ki tausaya min mana"
Dan sake matsawa tai kusa da shi, sannan ta ce,
"Kaiii ba fa zan kai haka ba muyi aure ba, ina karatun sai a daura auren, shi kenan inna gama gaba daya sai a yi biki sai na tare, ya kace,"
Ta na magana ta na daga masa gira, da bude yatsun ta dogaye da suka sha jan lalle, yawu ya hadiya har sai da qarar shi ta fito, shi dai yau ya shiga uku, yarinya qarama ta sashi a qarshen kujera ta na qure shi, in ya qi amince mata ya rasa ta, in ya amince mata nan ma bai tsira ba, baya ya sake ja, sannan ya ce,
"Aaseeyah to ki min bayanin yanda karatun ya ke kasancewa na ji, ko zan iya amincewa"
"Yauwaa yanzu kuwa zan maka bayani, a dan iya ilimin da na samu game da karatun lauya, na tabbata kaima za ka amince, karatu ne mai matuqar amfani a al'umma"
Baya Mahboob ya sake ja, Aaseeyah bata san ma ta kusan hayewa jikin shi ba tsabar yanda ta matsu a samu wanda zai fahimci manufar ta, qarshe dai Mahboob sauka qasa ya yi ya bar mata kujerar, ta ranqwafo ta fara zuba bayani,
"Ka gane ne ko,two ways ne ake shiga University din,ko mutum ya shiga da JAMB da WAEC result ko NECO,Ko in kayi Diploma ko IJMB sai ka shiga with Direct Entry shima u need Waec ko Neco,ana son mutum ya zama ya na da 5 credits including English da Literature for BUK da UDUS u must have Islamic Studies too,Sai Jamb zai rubuta English, Government ko History ko wani Art course, Literature in English and Islamic Studies wasu na cewa ana iya sa Hausa ma,Sai in ya samu admission...ya gama University,Sai Law Skul shekara daya ,sai service, shi kenan, yauwaa ana zuwa Abuja a yi call to bar to mutum ya zama cikakken lauya kenan,"
"To duk wannan dogon bayanin Aaseeyah lissafin shekara 6 kenan? Gaskiya lokaci ya ja da yawa haba ke kuwa ki tausaya min mana, ni fa ba yaro bane, ina buqatar mace a kusa dani"
"To ba gani ba,"
Rintse idon shi ya yi,
'wannan yarinyar sokuwa ce, a haka take son tai karatun lauya,ba ta da ilimin zaman duniya, ko dake wataqila in ta shiga mutane, zata waye, rayuwar ta ta qare ne daga makaranta sai gida, qawayen nata su ne dai tun na yarinta ba a sauya wasu ba.'
"Yauwaa Yah Mahboob ka ga shi kenan in zan je Law skul di na sai na je Yola ko? Tunda dama ni bana jin ma na taba zuwa"
"Ok"
Shi ne kawai abinda ya iya furtawa ta sa shi a tunani mai zurfi, ya kasa fita daga tarkon ta, roqon Allah yake ya kawo masa agaji, sai kuwa ga agajin ya zo, domin kuwa kira Mammee ta kwala mata, ai kafin ta miqe shi ya miqe ya ce mata sai an jima za su hadu, tini ya fice kan ta sake magana, ba haka ta so ba, ta so su qare magana, amma ya tafi ya barta da zancen da ke cin ran ta,
'Gwanda ma ka taimakan nai karatun kan ai auren,dan in ma ban zama lauya ba, nai alqawari a raina na daukan ma kakanni na fansa, in kai ba ka damu da mutuwar iyayen ka ba'
Sallama ta yi ta shige dakin Mammee ta na zancen zuci.
*****************************
A qarshe dai kowa ya amince da kuma bada yardar Aaseeyah ta ci gaba da karatun ta, amma da sharad'in duk sanda Mahboob ya buqaci daura masu aure ba za ta qi ba, ta yi na'am da hakan, a inda ta ke ta tsallen murna, da godiya, Abbu da Abee har ma Mammee sun mata nasiha sosai, ita kuwa ta fara shirya kan ta dan rubuta JAMB.
Hussein kuwa an kad'a shi dambu taliya yaqi yarda da auren Ummu suleim, ita ma ta yi fushi ta ce ba za ta auri wanda ba ya son ta ba, ta ba ma iyayen su dama su zabar mata miji, ko wane ne za ta aure shi, tunda abun nashi ya zama tozarci, ta shiga qunci matuqa, amma hakan bai sa ta zama mai rauni ba, ba ta bi shi dan ya so ta ba.
Abee kuwa ya mata alqawarin sama mata miji nagartacce, dan haka ya duqufa neman sanin parsonal information din Sakataren shi, ya na yabawa matuqa da kamun kai da nutsuwar yaron, dan haka ya sa a masa bincike sosai akan shi, domin shi ya ke wa Ummu suleim kwad'ayin aura.
***************************
Lokacin yin JAMB ya yi,Aaseeyah ta zana jarabawar, ta yi nasarar samun makin da ake nema, Mahboob da kan shi ya tsaya mata, ya taimaka mata har sai da ya ga ta samu shiga Jami'ar Bayero da ke a nan cikin garin Kano, duk sanda ta ke da lectures shi zai kai ta ya dakko ta in ta gama.
Ta fara karatun ta cikin nasara da qoqarin maida hankali, yanzu ba ta son saka shiririta a karatun ta kamar yanda ta yi a baya, yanzu lokaci ne na.maida hankali dan cikar burin ta.
Watanni uku cif da maganar auren su Noor, Abee ya gama.magana da Musa Sakataren shi, ya ba shi dama dan ya je ya gana da Ummu Suleim, a gani na farko suka aminta da junan su, ya sanar da iyayen shi sun je sun ga iyayen ta, komai ya daidaita.
Yanzu an saka maganar auren su baki daga nan da watanni hud'u masu zuwa.
Budurwar Hussein har gida ta biyo shi gaida Mammee,Aaseeyah tadawo daga makaranta, ta na ganin ta ta ji b ta son ta, sam jinin su bai hadu ba, a wulaqance ta dinga kallon ta, Mammee kuwa sai yabawa yarinyar take, ta na fadin.
"Yarinya nitsatssiya, da ganin ta ba mai hayaniya bace"
Aaseeyah juya idon ta ta yi ta shige dakin ta, ta ajiye jakar ta tai kwanciyar ta, dan ba wajen ta aka zo da waccan mai bleaching din ba.
Bayan ta zo tafiya ne ta dage ma Hussein sai ta yi wa Aaseeyah sallama, har dakin Aaseeyah ya kai ta, ganin qayatuwar dakin Aaseeyah sai da ta ji anya ta kawo kan ta gidan tsarar auren ta kuwa?
Cikin sarqewar murya ta kalli Aaseeyah da ta dage mata gira daya ta kafe ta da ido da alamar me ye? Ta ce,
"Qanwar mu ni zan wuce, ga wannan na zo miki da shi, sai kin zo, ina sa ran za ki kawon ziyara nima"
Sheqeqe Aaseeyah ta kalle ta, ta dauki mai da sabulu,da turren,ta karanta jikin man,ga shi balo balo an rubuta ya na bleaching ta ce,
"Allah sarki na gode, amma ni ba na shafa irin wadannan mayukan, kinga wancan shi ne mai na, basilin nake shafawa, da kin koma da shi,inshaa Allahu kafin biki zan kawo maki ziyara, tunda kusa da makarantar mu kike"
Turaren ta dauka,duba da yanda fuskar Tasneem tanuna rashin jin dadin asmsar komai da b tai ba.
Cike da jin kunya Tasneem budurwar Hussein ta dau mai da sabulun ta, ta mayar cikin qaton hijabin ta, Aaseeyah ta raka ta qofar dakin ta, ta komawar ta ciki,
"Ina laifin Ummu Suleim, kawai ya bi ya dakko mana wata nunar rana, ni ban ga wani kamun kai anan ba, mace sai ka ce dangin doki, namiji ma sai dai a bar shi kawai da jaye jayen magana"
*****************************
Shirye shiryen biki ya fara ba kama hannin yaro, bangare guda kuma Aaseeyah na qoqarin haduwa da CP Aliyyu,duk wata hanya da take qoqarin bi bata samu dama ba, har ta fara saduda.
Wataranar Juma'a,kwatsam ta shiga wani madaidaicin shago da ke kan hanyar ta ta komawa gida a adaidaita sahu,ta hadu da shi, a tsaye a bakin motar shi,ba uniform, sanye yake da manyan kaya, kasancewar ranar juma'a ce, da dikkan alamu masallaci za shi.
Ya na danna waya ta fito shagon riqe da ledar ruwa da lemo da ta siyo, qishirwa take ji sosai bata jin zata iya bari ta isa gida, ledar ce ta tsinke ruwan ya fadi, kallon ruwan ta yi, ta cije leben ta na qasa cikin takaici, ta na qoqarin duqawa ta dauka, ta ga an miqo mata ruwan, fuskar shi dauke da murmushi, ya ce,
"Ga ruwan naki Madam shagwaba, daga faduwar ruwa a qasa shi ne har kin cije baki ki na son ki kuka ko"
Dan murmushi ta yi,nan da nan ta hade fuska cike da mamaki, da tsananin murna, ta ce,
"Oh my God !CP Aliyyu Nuhu?"
Dan hade girar shi ya yi, sannan ya daga kai da mamaki,ya ce,
"Uhummm? A ina kk sanni haka?"
"Wayyoo Allah na, ba za ka gane ba, ina matuqar qaunar yanayin yanda ka ke gudanar da ayyukan ka na sadaukarwa ga qasar ka da al'ummar ka, duk sanda za ai hira da kai a gidan redio ko TV ba na fashin saurara, lokuta da dama in Yayana zai hira da kai ya na fada min, ni kuma har fashin makaranta nake dan kawai na kalli shirin ka"
Kallon qaramin bakin ta mai dan tudun lababba yake,
'Yau na hadu da wadda ta fi Amatullah surutu'
Gyara tsayuwar shi ya yi ya na ta sauraron surutun ta, bai aune ba sai jin kiran sallah ya yi, daga masallacin da yake son zuwa, ai da sauri ya damqa mata ruwan, ya ciro card din shi ya damqa mata, sannan ya ce ta neme shi a no da ke jiki, ya tafi kar ya rasa sallah, Aaseeyah ji take da a gida ne ba abinda zai hana ta taka rawa, Hamdala ta dinga yi wa Allah da ya sauqaqa mata haduwa da shi.
Ta na isa gida...........
Sai mu jira mu ji mi zatai zuwa anjima ko gobe, iya comment iya typing inshaa Allah.
TAUBASHI
PAGE 28
HAERMEEBRAERH
Can qasan kayan ta ta nemi waje a wardrobe din ta ta boye card din CP Aliyyu, tare da yin murmushi,
'Alhmdu lilLAAH wannan shi ne matakin farko n yin nasara ta inshaa Allahu'
Wanka ta shiga,ta fito daure da towel, idanun ta har rufewa suke dan tsabar gajiya, da bacci, amma ba tai sallah ba, dan haka dole ne tayi sallah kafin komai, ta na gama tsane ruwan jikin ta, ta zira doguwar riga, ta sanya hijabin ta,ta tada sallah, ta na idarwa ta ja wayar ta, ta kunna suraul Baqara, ta haye gado, ta na azkar din bayan kowacce sallar farilla ta na zabga hamma, Mammee ce ta doshi dakin, ta ji karatu na tashi, ta tabbata bacci Aaseeyah ta ke, dan haka ta dan leqa a hankali, kwance ta gan ta ta na lumshe ido, alamar bacci, jan qofar tayi a hankali, ta koma,dan ta san ko me zatai ba za ta ci abinci ba sai ta yi baccin nan.
"Yarinya sai kafiya, kaff tarihin gidanan ba macen da ta yi gaba a karatun ta, gashi nan ita ta kafe ta na shan wahala tun kan akai ko ina, Allah ya sanya albarka, amma kam mata na jin jiki,"
Murmushi ta yi ta qarasa saka ruwan robar a cikin fridge.
Aaseeyah ta farka bayan la'asar kadan, alwala ta yi ta yi la'asar sannan ta cire doguwar rigar,ta samu riga da wando masu sauqi ta saka,Fev. Color din ta, wato pink, (yarinyar nan bata gajiya ne da saka kaya pink? Anyway it is her choince ina water na?)
Ta daure gashin ta waje guda, kamar wata babyn roba, ta na zuwa parlour ta tarar da Hussein kwance a kujera, ya na waya da Tasneem, ya na sauraran ta, bayan ya jima ya na sauraron ta a qarshe ya ce,
"To ustaziya Tasneem, inshaa Allahu na daina, abinda ke qara min son ki kenan, tsananin tsoron Allahn ki, da nutsuwar ki, ga ki da sanin ya kamata,ina son ki my Tasneem"
Wani guntun tsaki Aaseeyah ta saki, tare da maqale baki da hannu ta maimaita me yace cikin muryar tsokana
"Ina tanci tashneemmm yanyanyanyannn"
Hussein ne ya zaro mata ido ya miqe tare da qoqarin make ta, ta fita a guje, bata tsaya ko ina ba sai bakin qofar kitchen, tsaye ta gan shi ya na ajiye plate din da ya ci abinci, da cup, da sauri ya kalle ta ya ce,
"Ke kuma ke da wa?"
"Ni da wancan mara rabon mana, ya na can ya maqale ma waccan guzumar murya, nai imani ta girme shi fiiiuuu da aniya, amma ji yanda take wani abu kamar yarinya, wai can wa'azi ta gama masa, shi ne ake fada mata ana son ta, abun wani banbarakwaiiii"
Dariya ta ke ta yi, Mahboob na kallon ta cikin sha'awar yanda take komai nata kamar bata da damuwa a duniya,shi kuwa ga shi ya na fama da matsananciyar qaunar ta, amma kamar ba ta san ya na yi ba,
"Ki na kishi ne?"
Me ne? Kishin me, akan waccan nunar ranar? Allah kiyaye, su je can su qarata,"
"Ki na kishi ya ce mata ya na son ta, ke kuma ba wanda ya taba cewa ya na son ki wooooo"
Shiru ta yi, dan gaskiy ba ta ji dadin maganar shi ba,kamar goranta mata ya yi fa ba wanda ya taba cewa ya na son ta, idanun ta ta kafe a qasa, ta na wasa da yatsan ta babba na qafa a jikin qasan wajen, kanta ya koma gefe, ya bayyanar da gefen fuskar ta, da Mahboob ke jin zai iya shekaru ya na tsaye ya na kallon wajen bai gaji ba.
Bata ji takun shi ba, sai hannun shi ta ji a gefen fuskar ta mai cike da kwantaccen gashi mai kyau, lumshe idon ta tayi, ta maida kan ta jikin hannun na shi, sannan ta bude idanun ta da suka dan sauya launi akan nashi,cikin murya mai kamar rad'a Mahboob ya ce,
"Ina son ki, ina qaunar ki, ina maki abinda ya fi so, da qauna,ban san me ne abun ba, wataqila ko dan ba shi da suna ne, amma ina ganin ya kamata in rad'a mishi suna, ina maki boyayyan so, har yanzu ban nuna hannu na akan me na fi so a game da ke ba, yarintar ki ne? Rikicin gangan din ki ne? Qiriniyar ki ne? Ko kuma halayen ki masu kyau ne? Shin ko kyakkyawar surar ki ne? Hannu na har yanzu bai sauka akan abu d'aya ba Aaseeyah, abinda kawai na sani shi ne, ruhi na na qaunar ruhin ki,ina maki son da ban san ya yake ba nima, ina fatan kema watarana za ki so ni, kamar yanda na ke son ki, in ranar nan ta zo kuwa zan zama cikakken mai sa'a a duniya"
Aaseeyah ji ta yi qafafun ta sun narke, ya gama narka mata duk wata tsoka da qashi na jikin ta da kalaman shi, zama tai a qasa dabar ta nade qafafun ta, sannan ta kafe shi da ido,hawaye na zuba a idanun ta kamar wadda aka wa dukan tsiya,shessheqar kuka ta fara, shi kuwa rikicewa ya yi, ya durqusa gaban ta, tare da kama dogayen yatsun hannun ta, ya ce,
"Aaseeyah me y saki kuka? Ko abinda na fad'a ya bata ran ki ne?"
Ta na kukan ta harare shi, sannan ta sa hannu ta goge majinar hancin ta, ta goge ajikin wandon ta, ta goge hawayen ido d'aya ta kalle shi ta ce,
"Wanne irin b'acin rai ana zaune qalau, wani abu na ji ya na min yawo a jiki na, ba zan iya misalta shi ba, farin ciki ne, ko baqin ciki ne, ban sani ba,amma ba na son abun ya tafi, duk da nauyin da na ji ya min a qirji na,ya narkar min da dikkan wata gab'a ta jiki na, ba n son na daina jin hakan, amma ina son na miqe sai na ji kamar qafata ba zata iya daukan jiki na ba,"
Dariya sosai Mahboob ya ke a wannan lokacin da ta gama magana, ganin ya na mata dariya ne ya sa ta bare vaki za ta rusa mashi kuka, da sauri ya saka yatsan shi a lips din shi, ita ma ya dora mata daya, tare da fadin,
"Shiiiiiiiii, na yi shiru kema dan Allah ki hakuri, taso na taya ki tashi, wannan abun da kk ji bai kyauta ba da ya hana ki tsayuwa"
Cikin maqale dariyar shi, ya miqa mata hannu, da kyar ta tashi, ta na bin hannun su da suke a sarqafe da na juna da idon ta da ke digar hawaye, tunda take ba ta taba jin wannan yanayin ba, za ta iya bada komai na ta dan dawwama a cikin shi,za ta iya tsayar da lokaci da hakan mai yuwa ne, dan su dawwama a haka,lumshe idanun ta tayi, Mahboob ya zaunar da ita a kujera, parlourn ba kowa, sai qarar AC da ke fita a hankali,
"Ina zuwa,"
Daga masa kai ta yi, shi kuma ya koma kitchen ya debo mata binci, dan Mammee kan ta fita asibiti ta ce masa Aaseeyah ba ta ci abinci ba, ta na fama da matsanancin ciwon kai, shi ne dalilin zuwan ta asibitin.
Da abinci da ruwa ya koma, ya ja qaramin table ya aje mata, ji ta yi gaba daya ta nemi yunwar da ke addabar ta d'azun ta rasa.
"Na qoshi,"
"Why? Me ki ka ci? Indai ba kin ci abu a makaranta ba, ba na jin a qoshe ki ke, yau da safe ma na ga ba wani abun kirki ki ka ci ba ki ka tafi,dan Allah Aaseeyah ki ci wani abu kin ji?"
Bude baki tai za ta yi magana, ya danna mata abincin a baki, taunawa ta yi ta na murmushi, amma ta kasa hadiyewa, tunda take ba ta taba qin cin abincin Mammeen ta ba, saboda a wajen ta, Mammeen ta is the best cook ever, amma yau ji ta ke abincin ya qi wucewa, Mahboob ya kula in ya na nan, ba za ta iya cin abincin ba, dan haka jakar shi ya dauka, ya ce,
"Ina zuwa Aaseeyah ina son na je na dan zaga, na rage ciki na, na yi wanka"
Dariya ce ta kwace mata, da abincin da ta kasa hadiyewa a baki ta ce,
"Yah Mahboob rage ciki fa kashi kenan"
Wata dariyar ta sanya, sai ga abinci ya wuce, ta hadiye shi tass, ta na kallon shi ta n dariya,
"Eh mana, ko an fad'a maki mata ne kad'ai ke kashi"
Kunya ce kuma ta dan kama ta, ta turo baki ta ce,
"Ni ai ba na kashi, kai dai je ka kai kashin ka,"
Dariya suka yi a tare sannan ya dau jakar shi yafita, ko ba komai, ya sany ta murmushi, amma zuciyar shi na waswasi akan halin da ta shiga dan ya bayyana mata soyayyar shi gaare ta, ko dai ba ta son shi ne?
Rabin abincin ta ci ta ji ta qoshi, zama ta yi a wajen ta hade qafafun ta a qirjin ta, tare da kwantar da kan ta a jikin kujera, ta na tuna kalaman Mahboob, sake narkar mata da dik wata jijiya ta jikin ta suke, har sai da ta dafe qirjin ta, dan yanda bugun zuciyar ta ya qaru a lokacin.
Murmushi ta ke ta zubawa, tare da lumshe ido,ta na nan zaune ta ji qamshin turaren shi, tare da rufe qofar shiga parlourn su, bude ido ta yi ta kalle shi.
Kafe ta ya yi da mayun idanun shi, sannan ya nufe ta, a hannun kujerar da take zaune ya zauna, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, kamar mai shaye-shaye, amma ta fi kowa sanin ba ya shan komai, lashe lips din shi ya yi, tare da dora idan shi akan na Aaseeyahn, da sauri ta maida nata lips din cikin bakin ta, ta na ja da baya,bintaya dinga yi, har sai da suka kai qarshen kujerar, sannan ya sa hannu ya fizge ta ta fad'a jikin shi,a cinyar shi ya mata mazauni, ya matse ta, ya na shaqar qamshin ta,tare da goga hancin shi a wuyan ta, zuwa saman qirjin ta, motsin kwace jikin ta ta dinga yi, shi kuma ya na dariya,
"Kamar haka ne fa ki ke hawa jiki na ki na qarama, ki na motsi a jiki na ni kuma ina jin dad'i, ina biyan buqata ta da motsin ki a cinya ta,....hummm...kinga yanzu idan na yi niyya, ba kowa a nan, na rufe qofa, zan iya amshe dik wani abu da na ke so a tattare da ke, amma ba zan hakan ba, sai sanda aka daura mana aure,.....uhummm saura kwana nawa ma? Kwana tara ko? To sai ranar,....a ranar kowanne ango zai kasance da amaryar shi, amma ni...ni...ni da ke zan kasance, ke ce amarya ta, ki sa a ran ki, ba ki da miji sai ni, ni ne zan aure ki Aaseeyah"
Buga qofar ake da dan qarfi, Mahboob na mamkin rufe qofar da tai,qara Aaseeyah ta saki da qarfi,Noor ya matse bakin ta, ya manna ta da kujerar ya taushe, jikin ta ji tayi kamar an hade qasusuwan ta waje guda, hawayen ma ba su wani zuba,da qarfi aka fara buga qofar, kamar za a balle ta, sake matse mata baki ya yi,sai da ta ji alamar jini ne a bakin nata, yatsan shi ta jefa a bakin ta, ta gantsara wa cizo,sai da ta ji haqorin ta ya shige naman hannun shi ta saki, da qarfi ya saki mata baki ya na yarfe hannu, mari ya sauke mata mai mugun zafi, sai da ta ga gilmawar haske, ya nuna ta da yatsa sannan ya ce,
"This is not over,zan dawo, zan dawo domin ki, ke kadai,"
Juyawar nan da zai dan ya fita ta qofar kitchen ya ji wani naushi, ko shurawa bai sake yi ba, qasa wanwar ya zube, Aaseeyah ta kwalla qara tare da dafe kan ta, bakin ta na zubar da yawu mai jini a ciki, ta ce,
"Yah Mahboob ka...ka...kaaaa kaaashee shiii"
Mahboob tissue ya dinga yankowa ya na goge mata bakin ta, ko ta kan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 41