hannin shi, ta ga uku ta gota har da rabi, da sauri ta tashi ta masa sallama,zata je ta yi wanka ta shirya Islamiyya,jiya sun yi fashi saboda shi, yau kam dole su tafi.
Tsaf ta fito cikin uniform din ta da ya sha wanki da guga, rataye da jakar ta, za ta wajen su Yesmeen, ya na dogare a bakin qofar parlourn shi, ta gilma, limshe ido ya yi, Aemana ce ta fado masa a rai,
"Atamanaa an takunu bi khair"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya san fad'a kawai ya yi, amma shi is not Ok.
Su na ta hayaniya suka fito,Umaimah ce ta je gaban shi da gudu gudu, ta ce,
"Yah ka zo muje ka ga makarantar mu, ko ka na wani abu ne?"
"Ah ah, ba na komai, mu tafi"
Nan fa suka tafi ta riqe hannun shi, Aaseeyah ta galla mata harara,
"Dalla sake mai hannu, tunda ba 'yar jagora ya ce maki ya na nema ba,ki ja a ce miki 'yar iska me riqe hannun maza"
Dariya sosai Mahboob ya ke, ganin yanda Aaseeyah ta dage ta na ma Umaimah fada, ya kan manta waye babba a tsakanin su,
"Wai ni kam wace babba a dikan ku"
Ummu Suleim ce ta kalle shi, ta ce,
"Ni ce babba, sai Yesmeen, sai umaimah, sai wannan mara kunyar, gani take ta girme mu ma dika, tunda ta kamo mu a jiki"
Nan fa suka dinga fadin irin rashin kunyar da take masu, sauya fuska ta yi daga jin haushi zuwa abin tausayi, idon ta ya fara kawo ruwa,
"Ku yi hakuri, ban san ku na jin haushi na haka ba, yau kun fadi duk abinda ke ran ku game da ni"
Hawaye ne ya zuba a idon ta, sauran kad'an dama su isa makaranta, da gudu ta qarasa ta shige gate din,
"Yah Mahboob rabu da ita, in ka na neman Emotional blackmailer ka samu Aaseeyah ka shafa faaaatihaa ka gama,"
"Ke wa ya fada maki ya iya turanci,"
"I knw what she meant,and yes i can understand and speak english as well, ni ma fa a Nigeria aka haifen,sannan ko a Jordan mu na huld'a da turawa a company din mu"
Baki suka sake suna kallon shi, sun iso bakin gate ya ce,
"To sai kun dawo ko, a yi karatu sosai, ku bawa Aaseyah hakuri, umarni na baku, ba bu kyau ku na tare ku na bata ma juna rai, ku 'yan uwan juna ne, yarinta ke damun ta, kar ku damu da girman jikin ta kun ji ko?"
"To yah mun ji,za mu bata hakuri"
"Sai kun dawo"
Shiga suka yi, suka tarar da Malam Buhari da Aaseeyah a gefe ta na ta rizgar kuka, gaban su ne ya fad'i suka hau kallon juna, wanne sharrin ta qulla musu kuma?
Qasa qasa cikin rad'a Aaseeyah ta ce ma Malam Buhari,
"Ka gani ko, sun san laifin da suka yi shi ya sa ka ga su na kallon juna"
"Kwarai da gaske kuwa,ja'irai marasa gaskiya"
"Malam me muka yi"
"Dan gidan ku za ki tsaya na fad'i me kuka yi ko kuwa, yanzu ina ganin ku kamar masu hankali wannan ce mara hankalin ashe ku ne shashashai, dan kawai ta maku nasiha ku yi sauri kar ku makara jiya kun yi fashi shi ne zaku hauta da fad'a sai da kuka saka baiwar Allahn nan kuka, ashe..."
"Malam qarya tak...."
"Kin san ban niyyar dukan ku ba za ki ja maku jafa'i yanzun nan in ina magana ki na katse ni, ke dai an ce jinin larabawa ce amma kin fi kama da 'yan waccan qasar masu qananan ido,....to ahir din ku kar na sake jin wata ta sa yarinyar nan a gaba, rai zai baci, maza ku bata hakuri"
Cikin bata fuska suka hada baki suka bata hakuri, ta yi kalar tausayi da fuska ta daga kai,
"Ki hakuri kin ji, in banda ma ke da saurin kuka ai ba abun kuka anan, ku tafi aji, Allah maku albarka"
"Ameen malam"
Su na tafiya Aaseeyah ta ce,
"Yau gargadi aka maku, gobe duk wadda ta sa na zubda hawaye, yasin sai an dake ta"
Ba su kula ta ba dan sun san hali, tafiyar su sukai ajin suma.
Ko da aka tashi suka je gida,kowa bangaren ta ta nufa, suka yi sallahr magariba, suka ci abinci, sannan suka nufi wajen Mahboob, ya zurfafa a tunani, har sai da Umaimah ta zare hannun shi daga tagumin da ya zuba kamar mace,
"Yah me ya sa lokuta da dama ka ke zama cikin damuwa ne? Yah ina son sanin labarin iyayen mu, domin ba wanda ya taba ban labarin su daga farko zuwa qarshe"
Murmushi ya yi mai ciwo,
"Labarin su labari ne mai sanya idanu zubar hawaye, zuciya za tai qunci,sannan za ki tsane ni, ina ganin a bar maganar kawai ba sai an yi ta ba,"
"Dan Allah Yah Mahboob ka bamu labari, ni ban taba sanin cewa Umaimah qanwar ka bace, sai da ka dawo"
Shiru ya yi sannan ya ce,
"Ku je ku kwanta,zuwa gobe da an yi sallar isha'i zan fara baku labarin duka ahalin nan ba ma na iyayen mu ba kadai"
"Yahhhhhhhhh, Allah ya kaimu, i can't wait to hear the story of our family"
"Me too"
Ke/kai faaaa????
TAUBASHI
PAGE 17
Kamar yanda Mahboob ya musu alqawari kuwa haka suka taru, Mammee ta soya musu gyada mai gishiri suyar ta yi dad'i sosai, kowa ya nutsu,musamman Aaseeyah da ita ce qarama ba ta san tarihin su ba kwata-kwata.
Mahboob kuwa sun saka shi a tsakiya,kamar TV, lumshe kyawawan idon shi ya yi ya sauke cikin na Aaseeyah wadda tsabar son labari ji take kamar ta haye masa cinya ko za ta fi saurara da kyau. (Sai ka ce o'o da ba a kama suna).
"Duk labarin da zan fad'a maku, na san shi ne ta wajen iyayen mu, sannan wasu sun faru a gaban ido na, wasu da ni su ka faru, ina son, kar ku yanken hukunci ko katse ni har sai na kai qarshen labari na,"
"Toh mun ji dan Allah kai sauri ka fara bamu labarin,"
"Aaseeyah ta fara karya doka,....sannan in bamu samu gamawa ba zuwa 11, kowa zai je ya kwanta sai gobe mu qarasa"
"Allah ya kaimu,"
********************************
"Shekaru da dama da suka gabata an yi wani mutumi mai suna Abdul Mudalleb ya na zaune a qasar Jordan, a Irbed City, can wani gari da ake kira da Ar-rathma, kakan mu Abdul mudalleeb,maraya ne,wanda yake zaune cikin dangin mahaifan shi, fad'i nan tashi can, ba shi da takamamai mariqi,saboda iyayen shi asali ba masu hali bane, tun a wancan lokacin,wasu na zumunci tsakani da Allah ba dan dukiya ko nasaba, ko ganin idon mutane ba,wasu kuma su na watsar da zumunci, musamman in ba a samu marayan an barmasa dukia ba, ko kuma ba a samu iyayen da suka tsaya sosai akan had'a kan yaran su ba.
Kakan mu ya kasance ya na noma a gonar da mahaifin shi ya rasu ya bar mishi,in ya noma abinci ya na rabawa biyu, ya ba wa dangin shi kaso d'aya, kaso d'aya ya siyar a kasuwa domin buqatun shi na yau da gobe, a wajen kasuwancin shi ne ya had'u da wani mutumi da ake kira Auwal Is'ma'il, wanda shi kuma mutumin Nigeria ne, ya shigo qasar Jordan ne dan neman ilimi.
Wannan bawan Allah Auwal a Nigeria mazaunin jihar Adaman Yola ne, a can wata qaramar hukuma ta Mayo Belwa,asalin bafulatani ne, amma in ya n larabci ba mai cewa ba balarabe bane sai wanda ya san shi.
Abotar su ta yi qarfin da har suka ba wa junan su labari, ta nan Auwal ya fuskanci irin wahalar da Kakan mu Abdul Mudalleeb ke sha tsakanin dangin shi, nan ya bashi labarin yanda na shi dangin ke da riqon zumunci a Nigeria, ya sanar da shi a wancan lokacin qanin mahaifin shi ke riqe da su shi da qanwar shi mai suna Ayshaa, kusan da damar fulani diyar su ta fari mace sunan da suke saka mata kenan.
A kullum Auwal bai da hira da ta wuce ta Ayshaa, har ta kai da ya dakko labari Abdul zai qarasa masa sunan wadda yake bada labarin akan ta, watarana Auwal ya ce wa Abdul.
'Aboki na, tafiya mabud'in ilimi ce, ka ganni yanda na ke tafiye tafiye dan neman ilimi, da ace kai ma za ka dage da neman ilimi, lallai da al'ummar musulmi sun qaru da basirar ka, ka ga da ace zaka shiga qasa ta Nigeria da ka samu ilimi mai tarin yawa,"
'Amma ai ka baro qasar ku ne ka zo nan dan neman ilimi kai ma'
'Kwarai kuwa, a tarihi na na sanar da kai ba wannan qasar kawai na je ba dan neman ilimi, shi ilimi ba ya kad'an har garin jahilai zama ake domin a sami ilimi a cikin jahilcin nasu'
'Haka ne, to a taqaice dai ka na min tayin zuwa qasar ku kenan'
'Kwarai da gaske, da ace za ka je qasa ta, da na nuna maka abubuwa na ban mamaki, domin kamar yanda na ke fad'a maka,Nigeria qasa ce da ta tara abubuwa masu tarin yawa, wanda ba su da iyaka, babu ce kawai babu a cikin ta, ina baka goron gayyata zuwa qasata watarana'
"Haka Malam Auwal ya gama watannin da ya rage masa ya sanar ma da Abdul lokacin komawar shi qasar shi Nigeria, a nan ya mishi fatan alkhairi, sannan ya sanar da shi zai je garin shi ganin gida shi ma, in Allah ya bashi iko ya na son dawowa kafin Auwal ya koma qasar shi, anan ya tambaye shi yanayin tafiyar shi zuwa Nigeria, Auwal ya sanar da shi, tare da tambayar me ya sa yake tambaya? Ya ce ba komi, kawai ya na son sani ne.
Ko da Abdul ya koma garin shi, kamar yanda ya kula ba wanda ya damu da shi, sai qalilan masu zuwa a cinye kud'in kasuwancin da ya samo, da sun qare su watse, tunani ya zurfafa, ya ga ba abinda ya rage mishi, banda ya bi Auwal zuwa Nigeria, domin ya amince wa Auwal sama da yanda ya aminta da 'yan uwan shi (wannan zumunci ya halaka).
Ba wanda ya sani a dangin shi ya saida gonar shi, ya tara kud'in shi,ya tafi wajen 'yan uwan shi ya musu sallama, ya ce za shi yawon bud'e ido, zama waje d'aya na mata ne, nan suka masa fatan alkhairi, wasu kuma suka hana shi, su na hango masa rashin nasara a tafiyar, dake y san ya wa ran shi tafiyar bai biye wa maganganun su ba, ya hade 'yan kudin shi ya koma wajen Auwal, ya sanar da shi tareza su koma Nigeria, Auwal ya yi murna matuqa,dan haka lokacin tafiya na zagayowa suka koma Nigeria a tare.
Tun daga shigowar su Nigeria Abdul Mudalleeb ya kamu da son qasar,ya gasgata Auwal,qasa ce mai tarin albarka,ba abinda ya fi bashi sha'awa ganin yanayin yanda kowa ke neman na kai, ga qasar noma, har sika isa Yola bakin shi ya kasa rufuwa tasbihi kawai ya ke ga Allah.
In taqaita maku labari dai, daga kallon farko da Abdul Mudalleeb ya yi ma Ayshaa ya kamu da qaunar ta, haka abun yake a wajen Ayshaa, bayan wasu watanni aka daura masu aure, suna zaune a gidan su Auwal, ba takura ba hantara,su ci mai kyau su sanya mai kyau,Ayshaa ta kafa rigimar ita sai dai su tashi, tana son su bar garin Yola su koma wani garin da zama, tun tashin ta a nan gidan ta rayu, yanzu aure ma a ce anan zata rayu, gashi Allah ya azurta su har sun samu cikin fari, ba tare da ya fada ma kowa asalin dalilin barin shi Mayo ba ya ce ma Auwal ya na so ya bazama Nigeria ne da kudin da yake da shi, da wanda ya samu ta dalilin noma anan,dan ya qara sanin Nigeria,Auwal ne ya basu shawarar komawa garin Kano, gari mai albarka, mai karbar kowa da kowa, gari mai maida d'an wani nata.
Haka kuwa akai,ko da Abdul Mudalleb ya tafi kano sai da Ayshaa ta yi da ta sanin ce mishi su bar Mayo ya je ya sama masu waje da sana'a a kanon daga baya ya zo ya tafi da ita, ya jima matuqa be dawo ba,a haka suka dinga rayuwa har ta haifi yaron ta na fari wato Abbu,ya ci suna Muhammad,ta yi kuka har ta ji ba dad'i, a nan ta ke sanar da mutanen gidan ita ce silar tafiyar shi, Malam Auwal ya bata hakuri, da tabbacin zai dawo, ya san halin Abdul Mudalleb ba zai tafi ya barta ba, tabbas akwai abinda ya riqe shi"
"Ta bangaren Abdul Mudalleb kuwa ya shigo kano ya ga kano ba yanda ya zata ba, a cike ya gan ta, kowa hada-hadar gaban shi yake yi, noma shi ne babban abinda ya kware akai, ya zo da niyyar siyan fili domin yin noma,aka cuce aka siyar mishi da filin da qasar wajen ba ta noma bace,gashi ya rasa mai siya da azziqi kamar yanda ya siya, ganin haka ya gina dan dakin katako a wajen, ya aje jakar shi ya shiga gari a dama da shi, kullum ya fita ya yo buga bugar shi nan ne gidan shi wajen kwanan shi, ya bude kwado ya shiga, da safe a gidan wanka da bahaya yake lalurorin shi.
Ya na nan cikin kewar matar shi da cikin da ya barta da shi, ya fara tunanin ko shi ma zai tsunduma sana'ar qarafa (jari bola) da ya ga wani mutum da ke kusa da shi na yi ne? Tunda ba shi da kudin da zai kafa wata sana'a yanzu, filin shi kuwa haka nan ya ke jin ba ya son ya saida, dan haka ya ma mutumin sallama, ya fara masa bayani a cikin 'yar hausar shi da ya fara koya a wajen Auwal,da Ayshaa,nan dai mutumin ya bashi buhu, da qarfen tono,ya masa godiya, ya bazama gari, da zafi, da rana, damuna, ruwa da iska sun qare a kan Abdul, gaba daya ya sauya kala,ya sha zama a dan d'akin katakon shi ya sha kuka, tare da danasanin zuwa Nigeria, amma in ya tuna matar shi da cikin da ya barta da shi, sai ya samu nutsuwa da kwarin guiwar neman na kai.
A haka Abdul ya samu shekara ya na tarin kud'i da kuma qoqarin kafa shi ma nashi wajen sai da qarfen, ya samu yaran da za su na aiki qarqashin shi a dan filin shi, ya na siya da adalci, ba ya ha'intar su kamar yanda wasu masu siyan qarafan ke cutar su, nan da nan ya samu yara. Masu yawa da ke aiki a qasan shi, kafin wani lokaci, ya fara gina doguwar katanga a filin shi, ya kewaye shi, tare da sanya qofa, bai cika shekara da wata hudu ba sai da ya gina daki ciki da parlour a cikin wajen, amma na katako mai qarfi, aka masa fenti ya fito fess kamar ba dakin katako ba, makewayi aka mishi, da shadda daga gefe, sannan aka siminte qasan wajen, yasa langa langa ya kewaye wajen, can daga waje kuma ya na sana'ar shi, a hankali ya fara siyan su katifa, ledar d'aki, da sauran kayan tarkace na gida, kadaran kada han, daga nn fa ya fara shirin komawa Yola, tare da taraddadin anya zai gane waje kuwa? Allah ya sa Malam Auwal a grin Mayo Belwa ba boyayyan mutum bane, sabida ilimin shi, ko da ya je da tambaya ya isa gidan.
Malam na qofar gida ya na karantar da mutane, Abdul Mudalleeb ya isa, duk ya yi duhu akan hasken shi na asalin balarabe, nan fa suka rungume juna suna kuka, ba wanda ya lallashe su, saboda kowa da ya san Malam ya san babbar damuwar shi bai wuce na Abdul ya dawo gida lafya ba ne.
Kayan Abdul Malam ya dauka da kan shi, sika shiga ciki, tun a soro ya ke kwalawa Ayshaa kira, ta na zaune cikin rashin walwalar da ya zama mata jiki.
Da jin kiran sai ta zaci ruwan alwalar shi za a miqa masa, ba tare da ta juya ba takalli inda Muhammadu ya ke wasan shi da tab'o ta ce,
"Muhammadu kai wa Yaya ruwan alwala kaji, ka dauka a hankali kar ka fad'i"
Komawa ta yi ta jingina da gini,
"Ayshaa taso ki ga wa nake tafe da shi,taso taso mai gidan ki ya dawo"
Wani murmushi ta yi mai ciwo, hawaye na zuba mata tace,
"Kayyaa Yaya am bari fadin haka, kar muhammadu ya ishen da tambayar ina Baban shi"
Durqusawa Abdul ya yi a gaban ta ya riqe habar zanin ta sannan ya ce,
"Sai ki nuna ni, ki ce masa gani na dawo ya yafe ni,"
Wani irin kuka Ayshaa ta saki; ita da Abdul, wanda ya sa ta shidewa har sai da a aka shafa mata ruwa ta daidai ta, ko kunyar Malam Auwal bata ji ba ta rungumi mijin ta, su na ci gaba da kuka, Mal. Auwal wajen ya bari baki bude, sujjadar godiya ga Allah ya yi, sannan ya sa d'alibai akai addu'a aka godewa Allah.
Ayshaa kira Muhammad ta yi ta nuna masa mahaifn shi, nan fa Abdul ya dauke shi, ya hau masa tawai, Muhammadu na surutu, kamar ya wuce shekarun shi, a ranar sun nuna ma junan su yanda suke kewar juna ba kadan ba.
Ya basu labarin wahalar da yasha da abinda ya tara, da qudirn shi na komawa, nan fa Ayshaa tace bata san zance ba, ita ta hakura, za ta zauna inda Allah ya aje ta, Mal. Auwal ya ce bata isa ba kuwa, sai sun koma wajen sana'ar mijin ta, ya gama qoqari ta qi, ta na nufin duk wahalar da ya sha shekara uku a banza? Ta sha kuka ta gode Allah, Malam da kan shi ya ce zai raka su ya ga waje, shi da mai dakin shi, in ya so sun dawo ko bayan kwana uku ne.
Satin Abdul daya suka rankaya kano,ko da ya koma ya yi mamakin ganin yanda abubuwan suka habaka, (dad'in shugabanci da adalci kenan, da ya na masu mugunta da a lalace zai dawo ya isko komai)
Nan fa yaron da ya bari kula da komai a wajen ya fara hidima da su, bayan sun ci sun sha, Ayshaa ta ga waje, ita dai bai mata ba, dan gidan su na Mayo ya fi wannan sau goma.
Amma tunda an riga an zo ai magana ta qare,sai da lokacin tashi ya yi yaron ya samu Abdul ya damqa masa ribar da aka samu, nan ya kasafta kudi uku kaso daya na yaro da sauran yara, kaso daya na sake bunqasa wajen, kaso daya ya sa aljihun shi.
Su mazan su ka kwana a parlour da pilalla da tabarma, mata suka kwana ciki da Muhmmad.
Kwana biyu da zuwan su Malam yace su koma, sun ga waje ai, Ayshaa ta sha kukan rabuwa da yayan nata da matar shi da suke tare da ita tun yarinta har aure.
Bayan tafiyar su Abdul ya lallashi matar shi suke zaune lfy.
Ana haka ciki ya sake bayyana a tare da Ayshaa, sun yi murna sun godewa Allah tare da sanya ma cikin albarka.
Su na a wannan rayuwa ta dadi, da wuya ta haihu cikin damuna,ruwa na shiga masu ta saman rufi ko ta ina,a haka suke rayuwa su killace yaran su a gefe, su ma su qwaqume inda ruwan baya zuba sosai.
Yaro Mahmood na da shekara biyu Ayshaa ta sake samun cikin Abee,wato Ibraheem, daga nan haihuwa ta tsaya taso ace ta samu mace, wanda a lokacin da yarintar ta ba ta cire rai ba,sai da ta shekara hud'u zuwa biyar ta haifi Khala Lila,wadda ta taso cikin gata daidai misali,da soyayyar iyaye da yayun ta, duk abinda take so indai bai fi qarfin su ba za ta same shi.
Mahmood ne ya fara sha'awar makarantar boko,sakamakon yalwatar arziqi da ya samu mahaifin su, ya sai gida a cikin gari sosai can unguwar sallari, lokacin ba mutane kamar yanzu, sai jefi jefi, dan kuwa maqota anesa nesa suke.
Ya na ganin yara na zuwa makaranta shi ma sai ya fara son zuwa, ganin haka ne ya sa Abdul sanya yaran shi maza a makarantar boko, da ta allo.
Mahmood dake ya fi su son karatun,ya fi su maida hankali ya koyi abun kirki, Muhammad wasa ya sa a gaba, Ibraheem kuwa rashin maganar shi ke cutar shi, ko bai gane abu ba yana son tambaya sai ya kasa, a haka za a wuce shi.
A kwana a tashi arziqi na samun Abdul yaran shi na girma, filayen da ke gefen gidan shi ya siye, ya hade dagidan shi, katange wajen yayi, dan girman wajen in ka shigo daga waje sai ka ga dan ginin da suke zaune dan qarami.
Cikin kyautayi na ubangiji sunan Abdul mudalleb Jordan ya fara karada garin kano, kun san mutane wasu na son su ji an ce ga wani da yake ba dan qasa ba, nan da nan ya tara dukiya a garin kano, yaran shi sun yu jami'a sun kammala bangaren Engineering.
Kafin su kammala karatun su dan zuwan da suke yi gida ne Mahmood ya hadu da Zainab diyar Malam Auwal, Yayan mahaifiyar su, soyayya mai qarfi da tsafta ce ta qullu a tsakanin su, kowa ya san da haka dan haka Malam Auwalu da Abdul Mudalleb suka tsaya mishi ya aure ta, nan ya shaci nan dinnan ya musu gini, madaidaici, da kan shi a hankali, dan sai da ya gama aka kawo ta ta tare, wani lokaci su Muhamadu su taya shi, su na yi ya na tsokanar Mahmood da me son girma, ya kan ce ya bar mashi girman, tunda har ya dakko aure.
Sai da suka ci qarfin gini, Abdul Mudalleb ya sa magina suka qarasa, hikimar barin shi ya fara ginin shi ne, dan ya girmama matar shi.
Bayan kammaluwar gini,aka kawo amarya, ta tare, da qaramar qanwar ta Fateema, wadda a lokacin Fateema ta na da shekara sha hudu, Zainab na da sha bakwai.
Rayuwar auren su gwanin sha'awa sike gudanarwa, ga girmama surukar ta kuma goggon ta da take da Abdul din kan shi, a shekarar Farko Allah ya azurta su da yaro namiji wato Mahboob,ni kenan, (ya saki murmushi shi a dole hyine babban yaya) daga ganin haka Abbu ya ce shi ma fa auren nan zai yi, tunda Mahmood na da yaro shi ba zai zauna ya zama gwauro ba ana ce na dinga miqawa Baba na soro abinci, a lokacin nan Ayshaa ta yi murna sosai cewar Muhammad ya fara tunanin aure a ran shi.
Sai da na shekara biyu kafin Muhammad ya samu ya yi aure,inda ya auri qanwar Zainab wato Fateema, ita ma anan gidan suka tare, a lokacin Mahmood ya bunqasa kasuwancin Mahaifin su, wanda girma ya fara kamawa, ya zamanantar da kasuwancin su, Abdul Mudalleeb na matuqar alfahari da Mahmood ba kadan ba.
Unguwar Sallari ta fara cika da gine-gine na zamani a wannan lokacin, Mahmood ma ba a barshi a baya ba, shi ne ya gina wannan gidan da muke ciki, kuma ta dalilin shi ne ya sanya dokar duk shekara ana sabunta fenti da gyara duk abinda ya lalace, shi ne wanda ya sanyawa su muhammad da Ibraheem kishin neman na kai, saboda su na ganin yanda mahaifin su ke yabon shi a kullum.
Fateema na da cikin Noor Abdul Mudalleb ya debi yaran shi kaff ya kai su qasar shi ta Jordan, ya gabatar da su wajen dangin shi, sai da suka shafe watanni biyu cur kafin su dawo, anan ne Khala Lila ta hadu da wani ma'aikacin asibiti d'an uwan Abdul Mudalleeb ne ya maqale ya ce ya ji ya gani shi ya na son Khala Lila, dawowar su Nigeria da watanni da ba su fi hudu ba aka mata auren ta ta koma Jordan da zama."
"Kaiii gaskiya na gaji, mu bari sai gobe, sha biyu da rabi fa na dare yanzu,labarin kuwa na da yawa"
"Kashhh Yah Mahboob din nan gaskiya ka iya katse labari, sai da aka kawo labarin gidan nan zaka tsaya"
"Ai ko wancan ma na gidan nan ne,"
"Haka ne,"
Dubawa sukai suka ga 'yan biyu har sun yi bacci,Yesmeen da Ummu Suleim ma haka, Noor kuwa dama ya riga kowa gyangyadawa, a cewar shi yara za a bawa wannan labarin ya san komai.
Umaimah ce ta yi miqa idanun ta sun kada sun yi jawur da alamar bacci ,ta fara tashin su yesmeen ta na ma Mahboob
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 41