Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta yaushe za su gaida Hajiya Kakar ta, sai ta ce sai sanda ya shirya, a haka za ta shashantar da shi a bar maganar. Ya yi ma Mahboob dik iya tambayoyin da zai masa, ya fahimci yaudarar Mahboob ta yi da kyakkyawan hali har ya amince zai taimaka mata. Aliyyu ya fara gajiya, domin kuwa a yau ya cika wata shida cif cif da zurfafa bincike ta qarqashin qasa, batare da nasara ba,kuma yau ne ya cika sati biyu cif bai je wajen ta ba. Yau ya qudirta inhar bai samu wata shaida ba, to zai yi amfani da wannan hoton lambar motar da ya dauka,ya kama Eliza da Alh. Munkaila har sai sun sanar da su alaqar su da matasan, ya gaji da jele gidan su yarinyar da by now iyayen su sun san zargin da yake mata, duk wani hope n auren shi ya rushe musu,addu'a kawai mama take Allah ya bayyana gaskiya d'anta ya daina wahala a banza. Shiryawa yake cike da gajiyawa, sai tsaki yake dokawa,turaren da Eliza ta ce masa ta na son qamshin shi ya fesa, "Ni na ma tsani wannan turaren, bayan wannan case din ba zan sake amfani da shi ba," Kwalar rigar shi ya gyara da kyau, sannan ya bude qofar dakin shi ya fice, addu'ar nasara Mama ta mishi,sannan ya fita daga gidan,sai gidan su Eliza. 'Zuwan bazata shi ne daidai' Murmushi ya yi, a lokacin da ya tuna rabon shi da zuwa yau sati biyu, ya ce mata ya yi tafiya,in ya dawo zai sanar da ita ta masa abinci mai dadi kamar wanda ta saba. "Sarah here i come, ki shirya wa zuwa na, ko na samu shaida,ko ba shaida asirin ku ya kusan tonuwa da izinin Allah" Yana shiga layin gidan ya mata waya, ta amsa, "Hello babe,ki na lfy?" 'Lfy qlou Autan maza,ya Abuja? Ya aiki? Aiki ya boye ka ko nema na ba ka yi kwana biyu gaskiya aikin kan nan na shiga haqqi na ni dai' "Ohhh dear i am so sorry,albishirin ki," 'Goro' "Yanzun nan na dawo, shiga ta gida kenan,nan da awa daya da mintuna zan zo gare ki, ba zan iya bacci ban gan ki ba" 'Wowww ba kasan iya yanda nai kewar ka ba, barka da dawowa Autan maza,ina nan ina jiran ka' "Sai na zo," Kashe wayar ya yi, ya tada motar ya qara danna hancin motar shi cikin layin, a gefen gate din gidan ya yi parking,ta yanda ba lallai a kula da shi ba, saboda bin layin jerin motocin da ya tarar a bakin qofar wani gida da ya yi. Gate ya ga an wangale,cikin sauri ya zaro wayar shi,ya shiga wajen daukan video,ya fara dauka,motoci ne masu numfashi ke fita daga gidan cikin sauri,cikin sa'a kuwa ya dinga daukan motocin da lambar motocin,sai da mota biyar suka fita daga gidan, sannan aka kulle gate din. Adana videon ya yi a wayar shi, sannan ya zauna daidai, ya kunna ya na kallon videon da ya dauka. Bai mamakin ganin Hon. Mamman Accu ba saboda ya na cikin suspect, motar shi ba baqin gilashi gare ta ba, mamakin ganin ASP Shalele ne ya fi damun shi,a mota daya suke. Motar Sanata Kabiru kuwa ba boyayya bace awajen shi, ya riga ya gane ta a cikin motocin, sauran ne bai san na su waye ba,amma koma su waye magana ta qare ai. Kamar ya koma gida amma sai ya fasa,bai sanar da ita qarasawar shi ba ya shiga gidan, gaisawa suka yi da mai gadi,cike da girmamawa dan sun saba da juna yanzu. Ciki ya shiga direct, Eliza ce ke ta masifa ta ruda dattijuwa iya da masifar a kwashe kayan parlourn saboda zuwan Aliyyun. Ta kwashe komai sauran cups din da suka yi amfani da su. Wayar shi ya zaro a wayance ya dauki hoton bayan ya cire flash light. Sai da ya gama hoton ya yi sallama, a razane Eliza ta juya gare shi,ta gigice da ganin shi ba tare da sanarwa ba, "Yallla...laabai,kaiii...nee?" "Supriseee,ai ni na ce ma mai gadi kar ya sanar da ke zuwa na, na yi kewar ki dear," "Ka tsorata ni,ban zaton ka yanzu ba" "And sai gani kwatsam, meye na tsorota kamar wata me laifi?" Yunqurin faduwa ta ke saboda yanda qirjin ta ke bada wani irin bugu,wataqila da za a saurara da za a ji yanda zuciyar ta ke bada jini dikkan sassan jikin ta cikin gaggawa, "Hhaaabaa... Autan mmazaa...wanne irin laifi zan yi ni kuwa? Ai ko na yi laifi na san zan tsallake tunda ina da kai" Wani irin kallo ya mata na ko uwata ce bata da gaskiya sai na garqame ta balle ke,jikin ta ne ya sake ta kalle shi, "Yallabai kar kasa zuciya ta ta karye mana, ba ka ce komai bafa" Zama ya yi a kujerar da ke kallon ta sannan ya dauki ruwan da Iya ta ajiye masa ba jimawa, ya kurba sannan ya ce, "Ai ke ta daban ce a waje na, so ina ganin ba ma sai kin tambaya ba" "Yauwaa ko kai fa,ina zuwa, just give me one sec,zan je na sauya kaya na" "Ya kamata kam, dan ina shigowa na ga abokan partyn naki na fita" Tari ne ya sarqe ta, ta na yi ta na neman iskar shaqa, tun da take a rayuwar ta bata taba shiga damuwa irin wannan ba, hukuma basu taba rab'ar su irin haka ba, Aliyyu ne ya miqa mata ruwa ya tsaya a kan ta, tare da watsa hannayen shi dika a aljihun shi, ya na bin ta da kallon da ya sake rikita ta,dan gudun kar ta zargi komai ya zare hannayen shi,ya tabbata ta tsorata matuqa, "Sannu, sannu sha ruwa, ki je ki sauya kayan ki, dare na yi zan tafi" "Ba abokan party na bane, wajen Abbana suka zo, abokan shi ne,da uncles di na" "Ok, ni ban ma wani kula ba, kawai dai na ga fitar su ni kuma lokacin ina waya" Cikin ajiyar zuciya ta kalle shi, ta sakar mishi murmushi, sannan ta miqe da sauri ta shige dan sauya kaya. Ba jimawa ta dawo, Aliyyu janta da hira ya dinga yi kamar ba wani abu a ran shi, hakan da ya yi ya kwantar da hankalin ta, ta gamsu da cewar bai gane komai ba. Sai qarfe goma da rabi ya bar gidan,direct ofishin su ya nufa, suka hau bincike da amintattun jami'an tsaron da ya saba da su a wajen. ************************* '.......anan muka kawo qarshen labaran mu na yau,ga maimaicin mahimman kanun su. Kunji cewar 'yan fashi da makami sun shiga gidan hamshaqin dan kasuwar gwalagwalai na kano wato Alh. Usama Bege sun kashe shi da iyalan shi, sun sace dik wata kadara daya mallaka,kun ji cewar gwamnatin tarayya ta......' "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,Mammee kin ji wani mummunan labari kuwa da aka nuna yanzu? Kinga yanda aka yi wa wani mutum yankan rago a gidan TV kuwa? Wayyoo Allah na, yau na ga tashin hankali,har yaushe mutum zai iya kashe d'an uwan shi mutum kuma ya kwana lfy?" Kuka sosai Aaseeyah ke yi kamar ta san mutumin, Mammee ke ta lallashin ta, da kyar Mahboob ya samu ya lallabe ta ya tafi da ita dan kai ta makaranta. Da safiyar kuwa Aliyyu ya debi jami'an 'yan sanda suka zagaye gidan Alh. Munkaila, sannan ya aika wasu gidan Ho. Mamman Accu. Shalele kuwa a daren suka garqame shi, ya ke cin kwakwa,da shaidar da ya bayar akan su Eliza aka tafi kamo su,Aliyyu ya shiga tashin hankali da ya ji sunan Sarah wai Elizabeth. Cikin qunar zuciya ana bude gate din ya fada, yaran shi suka bi shi, bacci take shaqa abun ta, tunda su C boy suka mata waya suka sanar da ita nasarar da suka samu, ta gama murna ta maida kai ta ci gaba da bacci. A rude iya ta shiga dakin ta ta taso ta,kan ta fito an sanqame Alh. Munkaila an sa masa ankwa. Ko da ta fito ta ga AIG Aliyyu da kan shi cikin uniform, sai da iya ta kamo ta, "Babe lfy? Ya na ga mahaifi na a daure? Me ke faruwa?" "Enough of ur games u stupid whore,arrest her, ina umartar ki da ki shiru domin duk abinda kk ce a yanzu zai zama shaida akan ki a kotu,ku fito da ita" "Baby pls kar ka tonan asiri na fita tsirara a haka,ka bari ko kayan azziqi na saka" "Ke kin damu da zama tsirara ne? And don't u ever call me that,na tsane ki,ki sani ba wata alaqa a tsakanin ni da ke,ku tisa ta gaba mana mu je,ku na batan lokaci" "Yallabai ko bata saka kaya dan kan ta ba a bata ta saka dan idanun mu" Wani daga cikin 'yan sandan ne ya fada, dan tun da Eliza ta fito idanun shi ke kan qirjin ta d mazaunan ta. Riga Aliyyu ya ba ma iya umarnin ta dakko,a gaggauce ta je t dakko ta miqa mata ta saka sukai waje da ita. Ko da suka isa ofishin 'yan sandan, an riga an kamo dikkan wadan da Aliyyu ya bada umarnin a kamo,an danna su cikin cell,daki guda aka ware aka sanya Eliza. Ta na shiga dakin ta fashe da kuka, wani irin wari da dattin shaddar cikin cell din ne ya sanya ta fara yunqurin amai,gashi safiya ne cikin ta ba komai, yunwa ta ishe ta, dan haka ba abinda ke fitowa sai yawu. ASP shalele na maqale a kwana, gaba daya ya sauya saboda wahalar da ya ci,da kyar Hon. Mamman Accu ya gane shi,ko magana ya kasa tsabar zoqin da goshin shi ke masa. Cikin saurin magana Hon. Mamman ya ce, "Wa nake gani kamar Shalele?" Daga kan shi ya yi da gefe daya ya fi girma, ya gyada kai a hankali, alamar shi ne, dikkannin su wajen shi suka nufa, su ka hau tambayar shi me ya faru, ya kasa magana sai hawayen azaba yake fitar wa, hankalin Sanata Kabiru ya ta shi, dan haka masifa ya fara ya na fadin. "Kai ku bani waya na kira lauya na,ina da wannan 'yancin ai, ku ban waya na kira IGn da kan shi, duk sai kunyi danasanin kawo ni nan da kukai," Hayaniyar su ta dami Aliyyu, cikin wata gigitacciyar tsawa ya dakatar da hayaniyar su, "Ku min shiru,ko yanzu na aikata maku abinda ni da ku za mu yi dana sani, kun san da goyon bayan wa kuka zo nan wajen? Bayan IG da kan shi har shugaban qasa ya taimaka mana da kayan aikin da za mu kama ku, ba ku da wani gata a qasar nan da zai cece ku yanzu,qarshen ta'addancin ku ya zo qarshe da izinin Allah daga nan Abuja za ku,a can za mu miqa ku hannun kuliya,dan haka ku min shiru ba na son sake jin bakin kowa a nan" Da qarfi ya daki jikin qofar da suka tsaya suka yi cirko cirko kamr zakaru, a guje suka ja baya, saboda ganin irin fushin da Aliyyu zaki ya ke ciki. A cikin taku qalilan ya var wajen ya fita daga hedikwatar gaba daya. Bincike ya gama kammaluwa, an tarkata su Sanata zuwa kotu. Aliyyu ji yake kamar an zare masa qaya a maqoshin shi. Motar da aka saka Eliza a ciki ne ta zo wucewa ta gaban Aliyyu, gani ya yi duk ta sauya a cikin lokaci qanqani, tsaida su ya yi,ya je saitin inda take ya ce, "Sarah,ko kuma Elizabeth zan ce? Kin bata rayuwar ki a banza,kin kuma bata wayon ki a wofi, yanzu kin ga sai ki je ki girbi abinda ki ka shuka ko?" wani irin kallo ta mishi da ya caki qahon zuciyar shi, saboda kasa fassara shi da ya yi, "Ba zaka gane ba, domin an haife ka cikin sa'a d nasara,da kuma yalwar azziqi da soyayyar uwa da uba da 'yar uwa,irin mu sai mun dage irin yanda na yi sannan muke samar wa kan mu ingantacciyar rayuwar da muke so,da ka taso a irin rayuwar da na taso,wataqila da a harkar zamu hadu,har mu kai ga auren da bamu samu damar yi ba yanzu" Maida kan ta qasa ta yi, 'yan jarida na ta daukan ta hotuna da video, Aliyyu kuwa bai san me ya sa ba kalamanta sun narka zuciyar shi, zai so ace bai saurari kalaman ta ba,saboda tasirin da suka yi a zuciyar shi. Juyawa ya yi ya shiga motar shi sai gida....... TAUBASHI PAGE 47 Duk murnar da su Mama da Amatullah ke taya Aliyyu na kawo qarshen wannan case din bayan ya koma gidan ba jin su yake ba, hankalin shi na kan kalaman Eliza, sun dabaibaye zuciyar shi,sun hana shi sakat. Haka ya kwana da maganar a zuciyar shi,da sassafe kuwa wajejen qarfe takwas saura minti biyar ko karyawa bai ba, ya ce wa Mama za shi Abuja, akwai wani aiki da ya taso masa na gaggawa. Jirgi ya bi dan isa da wuri,ko da ya isa ya tarar har an shiga kotu da su Eliza,an fara fafatawa,kwararrun lauyoyi na ta fafatawa,lauyoyin su Alh. Munkaila qoqari suke sai an sassautawa su Alh. Hukuncin da ake qoqarin yanke masu, wanda hakan su da kan su sun san ba mai yuwa bane,saboda manyan laifukan da ake tuhumar su da shi na shugabantar fashi da makami, garkuwa da mutane,ko dukiyar su tare da kisan kai na rayukan da ba za su lissafu ba. Aliyyu wajen IG ya je, sun jima suna tattaunawa, IG ya sanar da shi yanzu tunda case din ya qare sai ya dawo Abuja da zama,office din shi na nan na jiran shi, ba yanda zai yi dole ya dawo din, uzirin shi ya qare,amma ba ya son yin nesa da iyayen shi. Suna zaune har aka kammala yankewa su Eliza hukuncin kisa ta hanyar rataya, manema labarai har sun samu sun fara watsawa a gidajen talabijin da na redio, sai haska su Eliza ake a gidajen talabijin, an saka hoton ya yi dishi-dishi ta yanda in ba wanda ya musu kyakkyawan sani ba ba zai gane su ba,zuciyar Aliyyu ta karye da ganin Eliza daure kan ta sunkunye, manema labarai na ta son jin ta bakin ta taqi magana. Alh. Munkaila kuwa saqo har ya kai wajen mahaifiyar shi, addu'a ta dinga masa, da fatan Allah ya jiqan shi, ta ce ba inda zata je, da ta san halayyar da yake kenan da tun a baya ta dau matakin taimaka masa ya gyara, amma ya munafurce ta, tarbiyyar da ta ke bashi daban abinda yake aikatawa a boye daban. An tattaro su an kawo su ma'ajiyar su kafin aiwatar musu da hukuncin rataya, Aliyyu ya je domin ganawa da Eliza, ba bata lokaci kuwa aka basu wani daki wanda ke dauke da table guda daya sai kujeru biyu, abun sha aka gabatar masu, amma Eliza ta kasa saka komai a bakin ta, hawaye ne kawai ke zuba a idanun ta. Cikin karyewar zuciya Aliyyu ya ce, "Elizabeth..." "Pls Aliyyu call me Saratu, just for today,daga yau ba zan sake jin sunan ba wataqila sai a qiyama,and i am sorry for everything, dan Allah ka bawa Mahboob hakuri akan munafurtar shi da na yi da cin amanar shi da na yi,ka bama Aaseeyah hakuri domin da shawara ta aka sace ta, na san ka zo ne dan ka ji wace ce Elizabeth, ko kuma na ce wace ce Saratu, to ka karkade kunnen ka da kyau dan jin cikakken tarihi na. Asalin suna na Saratu Lawan Direba, an haife ni a garin Lagos, a wata unguwa da kusan hausawa nan suka fi zama wato Apapa,mahaifiya ta da mahaifi na mutanen KT ne, aikin tuqi mahaifina yake, dalilin komawar mu Lagos kuwa neman matan da mahaifi na ya sanya a gaba ba qaqqautawa shi ne dalilin da ya sa iyayen shi suka hado shi da mahaifiya ta d yayana Isya suka koma tare, bai so hakan ba ko kadan, domin ya na ganin hakan a matsayin takurawa da hana shi sakewa, gashi ba shi da wajen zama, shima watarana a motar shi yake kwana, ko ya kwana a dakin wata,ko ya je qasan gada ya kwana. Zuwan mahaifiya ta da Isya ne ya sanya shi dole ya samu wani waje, shima ba kyauta bane, amma daki ne falle guda na katako, a ciki suke rayuwa, mahaifiya ta da muke kira da Yabi ta sha wahala matuqa wajen shi,sai da ta kai ita ma ta falle, ta fara masa rashin mutunci, watarana har doke doke suke, su ji wa junan su ciwo, duk abinnan da suke suna son junan su matuqa, sai sun yi raga raga da juna za su koma kuma su yi jinyar juna. A wannan halin Isiya ya rayu, har ya tashi da taurin zuciya, ya yi fada da yara a waje ya yanke su ba wani abu bane a wajen shi, Yabi kuwa in an kawo qara da masifa take raka mutum, takan ce what if danta aka yanka wajen fadan fa? Ai gwanda shi ya yanka akai mata qara. Suna da shekara uku a lagos Yabi ta samu ciki, Baba ya ce bai san zance ba, da me zai ji? Da zaman biyan hayar dakin katako, ko da ci da su, ko kuma da yi musu sutura, ko da renon sabuwar haihuwa? Haka ya sa Yabi a gaba da masifa da bala'i sai ta zubda ciki, ta ce tunda ba cikin shege bane sai ta haifa, dambe suka kaure da shi, har Baba ya yi nasarar yi mata mummunan dukan da ya sa ta tai barin dole. Asibitin ma qin kaita ya yi wai bashi da kudi, a gida ta sha jinyar ta har ta warke, ya kawo mata jiqe jiqen magungunan yarabawa na wankin mahaif ta sha. Ba a rufa wata biyu ba Yabi ta sake daukan wani cikin,a wannan lokacin sai ta yi shiru ta qi ta sanar da Baba, sai ta fake da fushi take da shi tunda ya zubar mata da ciki, shi kuwa ko a jikin shi, gidan karuwai yake tafiya watarana ya kwana abun shi. Bayan wata uku da samun ciki na, tafiya gida ta kama Baba, sai yabi ta ce ya je kawai ba sai mun bishi ba, ya ce mata daga can za su yi wata tafiya kuma zai jima,ta ce ba komai, in ya samu hanya kawai ya dinga mana aike, a haka suka rabu,bayan tafiyar Baba Isya ya fara shaye shaye da qananun shekaru, dan a lokacin shekarar shi sha uku. Yabi bata wani damu ba, iyaka bata yarda ya kwana mata a daki in ya bugu,dan har fitsari yi mata yake yi,a hankali Yabi ta fara hulda da mazan qasan gada, ba wai kwana take da su ba, ah ah za ta je ne su gama shahancin su na tabe tabe su bat kudi, dan tunda Baba ya tafi ko sisi bai aika mata ba. A haka sai da Yabi ta kai watan haihuwa ta, ko rigar saka ni ba ta da shi,ranar kuwa da ta haihu a ranar Baba ya koma, ta na kwance jaririya na gefe, gashi ba mutunci take da mutanen wajen ba, ba wadda taje taimakon ta,ta na ganin Baba ta fara murna, shi kuwa da ya duba ya ga haihuwa ta yi sai ya dinga ashar ya na fadin ba diyar shi bace, sai dai ta fada masa a gidan uban da ta yi cikin shege, har ta haifi yarinyar ta. Rantsuwar duniya ta masa da bayani Baba ya ce ni ba diyar shi bace" Kuka sosai Eliza ta fashe da shi, da shassheka, in ba Sam ba ba wanda ya san wannan labarin, sai Aliyyu, cike da tausayawa Aliyyu ya miqa mata ruwa ta qi karba, dan ta qudirta ba zata sake saka komai a bakin ta ba har ta bar duniya, gashi ta jima rabon ta da abinci, ci gaba da labarin ta yi, Aliyyu na sauraron ta cikin tausayawa. "Har na fara rarrafe mahaifi na bai taba dauka ta ba, bai taba kallo na da idanun rahama ba, Isiya shi ke samo min abinda zan ci da mahaifiya ta, ta hanyar sace sacen da saida kwaya da dai kayan maye haka,Isya shi ne wanda ke kare ni innai ma Baba barna zai daken, sai ya zaro wuqa ya ce zai cakawa Baba in ya kuskura ya taba ni, dole Baba ya hakura dan tsoron Isya yake ji sosai. A haka na tashi Uwa ta na bin mazan banza dan ta sama.mana abinda za mu ci, yayana na saida miyagun kwayoyi,ya na sace sace, mahaifi na na tuqi da neman matan banza da kashe masu kudin da ya wahala ya nema da kan shi, cikin rashin kunya da rashin ganin qima da darajar na gaba da ni na tashi, dan Yayana Isya ya koya min rashin tsoro, duk wanda ya taba ni na rama, in ya girmen na sanar da shi. Kamanni na da Baba su suka ceci Yabi daga qazafin da ya mata, amma dik da ya tabbata ni jinin shi ce maganar azziqi bata taba shiga tsakani na da shi ba" Kuka Eliza ta sake fashewa da shi, abun na qona mata zuciya kamar ranar abun ke faruwa. "Eli...Saratu in ki na ganin ba za ki iya ci gaba da ban labarin nan ba ki barshi kawai," "Noo ni na fara ai ba tare da ka tambaya ba, ni zan qarasa maka," "Ki sha ruwa pls muryar ki ta dashe" "Kar ka damu Aliyyu, me ye ya rage kuma? Ba abinda ruwa zai min a wannan halin da nake ciki" Kurbar ruwan ya yi ya ajiye tare da maida hankali ga labarin da take bashi. "Aliyyu bayan na zama budurwa Yabi da kan ta ta fara tallatani wajen mazan dake qasan gada, Isya ne ya yi jan ido ya ce karatu zai sani na yi,duk sanda ya ji labarin na yi zina sai ya yanka ni ya yanka wanda ya yi zinar da ni,a haka na samu salama, yaya na Isya ya kan ce, 'Saratu matar manya ce, ku baku da ido baku gani ba? Sai ta yi ilimi indai ina raye, ba dan Saratu ba da ba zan zauna a nan ba da tuni na yi gaba' Soyayyar da yake nuna min ko iyaye na ba su min ita har Yabin ma, a haka na fara zuwa makarantar boko, ya so saka ni a Ilekewu,(islamiyya) ya fasa, dan a cewar shi, da na san Allah hana su sakewa zan(subhanallah). Boko kam na yi ta har matakin qarshe na secondary, ya na qoqarin sanyani a jami'a watarana ya tafi sayar da kwaya, aka kama shi, aka kai shi wajen 'yan sanda, is like wani ne ya masa shune, domin ba bata lokaci ko bincike ko jin ta bakin shi suka dinga dukan shi, da muka ji labari muka bazama muka tafi, sai suka ce ba za su bada belin shi ba ko da kuwa miliyoyi za mu vasu,haka suka miqa shi ga kotu, aka yanke masa hukuncin zama gidan yari,ya na gidan yarin aka samu wani a cikin gidan yarin ya kashe shi." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,Eliza calm down pls, ina ga mu bar wannan maganar haka, ba ki numfashi da kyau fa, Eliza pls mu bar maganar nan" "Basshi...barni..kawai..ka bari zan qarasa maka, unless ba ka son jin labari na" "Ina son ji amma ba ki cikin halin lafiya,ki bar shi indai ki na ganin za ki cutu" "Bayan kashe Yayana masoyi na da akai,na dawo gida ba ni da mai taimaka min, mahaifiyar da ta haifeni ce ta ke neman jefani harkar karuwanci dan neman kudi,mahaifina kuma kamar abun magani, sai ya fara kula ni, ba su koya mana gaisuwa ba, amma in ya dawo daga tafiya zai siyo min kayayyaki na kwalliya na mata, sannan zai ce min 'Saratu ba gaisuwa ne abun?' To ba su taso da mu ta yanda za mu koyi gaisuwar ba, ko wani abu da ya danganci gaisuwar, sallah wannan bamu ga suna yi ba, amma sunan musulmai suke amsawa. Bayan shekara daya da rasuwa Isya, na koma abar tausayi, sai in wuni ban ci ba, kuma ban sha ba, mahaifiyar mu rabon ta ma da ziyartar dangin ta tun kan a haifen, har na shekara sha bakwai bata taba cewa zata je gida ba, daga wancan shagon saurayi sai na wancan, in Baba ya dawo ta dawo gida, ko sun fara zaman lafiya qarshe da fashe fashen kwalba za a qare. Zaman ya ishe ni haka, sai na fara neman ko da lesson ne ina yi ma yara ana biyana, dan ba qaramar makaranta na yi ba, ina da ilimi daidai misali,amma haka na rasa samun wanda za su taimaken na koyar da yaran su su biya. Watarana ina zaune a dan dakin mu, wanda kusan yanzu ni kadai ke kwana

Chapter 30 of 41