ya ce,
"Ni dai ban yafe maki ba, last week din can sai da kk ja Malam Salisu Tumbi ya jibgen kamar wani jakin noma, kawai dan na kalle ki,"
"Habaa Sabeer yau fa za mu bar makarantar nan, ganin juna zai mana wahala, wataqila har abada ba za mu sake ganin juna ba, dan Allah da son Annabi ka yafen,"
"Kin san Allah Aaseeyah? Ko rasuwa na ga za ki ba zan yafe ba"
"Subhanallahi, haba Sabeer, me to ka ke so na maka wanda za ka yafe min?"
Kallon ta ya yi ya na murmushin 'yan iska, dan sunkuyawa ya yi daidai fuskar ta ya ce,
"Ki min kiss a gaban 'yan aji a kunci na, shi kenan, na yafe miki,"
Murmushin mugunta ta yi, sannan ta ce,to zan maka, amma sai ka kulle idon ka,
Nan da nan ya juya ya dagawa abokan shi hannu, suka sa ihu.
"Ehhhhhhh...ehhhhhhhh"
Shi ne abinda matasan ke fadi, juyar da kuncin shi ya yi, ya kulle idon shi,sannan ya tsaya jiran ya ji kiss din Aaseeyah, ajin ya yi tsit kamar an dauke wuta su ga me zai faru, banda abokan Sabeer da ke ta ihu,matsawa ta yi daf da shi kamar za ta sumbace shi, ta daga hannun ta cikin zafin zuciya da zafin hannu ta wanka masa mari sai da ya juya.
Sannan ta saka murmushi ta na abu na mai jin kunya, kamar wadda tai kiss din gaske, idanun Sabeer sun kada sun yi jawur, ya dafe kuncin, ga kwalla nan na qoqarin gangarar mishi ya na matsewa, abokan shi me za su yi banda dariya, hall din gaba daya dariya suka dauka, baqin da suka zo jarabawa makarantar ba su san halin Aaseeyah ya wuce nan ba, mamakin ta kawai suke, sai tafi suke suna ihu,ita kuwa sai rufe fuska take ita a dole ta ma namiji kiss ta na jin kunya,
"Ni ki ka mara? Ki ka mare ni ko? Za ki san kin mare ni, sai kin yi danasanin marin nan Aaseeyah"
"Ni yaushe na mare ka? Haka na ke nawa kiss din, abinda ka nema a waje na shi na baka,dan haka ba ka isa min komai ba, dole ma na kai qarar ka wajen malam Salisu, sabida wadannan kalaman naka a mana iyaka da ni da kai, ko dan gaba in wani abu ya samen an san kai ne"
Ai ya na jin za ta sake hada shi da malam salisu Tumbi ya shiga bata hakuri, ya na fadin
"Aaseeyah ai kin maren kin mari banza, ba abinda zai same ki, wasa nake, dan Allah ki bari mu rabu lafiya,ba na son case,"
"To ka yafe min? Duk abinda na maka?"
"Na yafe maki har qarshen rayuwa ta ba zan sake daga maganar nan ba, na yafe maki"
"To na gode,"
Komawa ta yi ta yi zaman ta cikin qawaye,an gama jarabawa amma ba su ga damar tafiya ba, sai zuba hira suke, dama dan ta tsaida su ne amma wasu qoqarin ma fita suke su koma gida, wasu yawo za su wuce, wasu party,kowa da abinda yake son aikatawa a wannan rana ta qarshe, Aaseeyah da qawayen ta kuwa waqa suka hada ma makarantar su ta gado, tun su na 'yan mitsi mitsi suke zuwa, ga shi sun girma cikin ta,yau kuma za su bar ta.
Ba su suka bar makarantar ba sai qarfe hudu na yamma.
Ko da suka koma gida, sun tarar Mammee ta masu girki mai dad'in gaske da qayatar wa, wanka suka fad'a, su Yesmeen suka jera abincin a babban parlour, kowa ya hallara har Ummee, nan fa Mammee ta ce a yi addu'a, Mahboob ya fara kwararo masu addu'a cikin harshen larabci, ana addu'a Aaseeyah ta sunkuya kunnen Ummu suleim ta ce,
"Kar fa ku ji ya na zuba larabci ku zaci ko wani cikakken malami ne shi, ai larabci yaren shi ne,ni da ni aka ce nai addu'ar da hausa zan kayata"
Girgiza kai Ummu suleim ta yi, tare da kallon Aaseeyah ta gefen ido.
Bayan sun gama addu'a aka ci aka sha, nan Mahboob ke sake jin labaran rashin ji na Aaseeyah kala kala, ya yi dariya tun ya na saman kujera sai da ya fado qasan carpet, ita kuwa ganin ana biye mata ne ya sa ta sake bajewa ta na bashi labaran rashin jin ta, anan asiri ya tonu, ta fadi gaskiya ita ta fasa wa yarinyar nan kai a soron gidan su, Mammee kuwa ta ce da wa Allah ya had'a ta ba da Aaseeyah ba, dundu ta durma mata, ta na qoqarin sake mata wani Aaseeyah ta kwasa da gudu ta yi bayan Ummee da ke kusa da ita, ai ko ta ture ta, ta na fadin,
"Dalla matsa min ni, ki je can ku qarata,in ma kashe ki za tai ai uwar ki ce,kuma kin cancanta"
Tsit wajen ya yi,saboda mummunan furucin Ummee, ita kuwa ko a jikin ta, kaza ta yaga ta sake loda wani a plate ta miqe dan komawa bangaren ta, Aaseeyah kwafa tai, sannan ta ci gaba da hirar ta.
(Aradu mata mu iya kalaman mu, wasu fa haka suke, ana zaune cikin farin ciki in suka yanko magana sai ta tarwatsa taro, wasu haka suke sam ba su iya magana ba, ba su tattauna magana kafin su fade ta sam,in ki na mace ba ki iya magana ba, kin rasa babban makami na zama cikakkiyar mace ta gari)
TAUBASHI
PAGE 26
HAERMEEBRAERH
Da misalin 11:05am iyalan gidan Abul Mudalleeb Jordan ne a babban parlourn gidan, su na karyawa, ana hira, Ummee ce kadai ta kama baki ta tsuke kamar takashi, a hankali ta ke kurbar kunun gyadar da Mammee ta yi kamar mara zuciya, in ba ka son mutum ai har abun hannun shi ne ko?
Bayan sun kammala cin abinci, Abbu da Abee na dan hirar su sama sama, yaran mata suka kwashe komai suka gyara wajen kamar ba a ci abinci wajen ba, su na tafe suna hira, Aaseeyah na masu rawar kai, ita a dole an kammala sakandire.
Sun zauna da 'yan mintuna Abbu ya yi gyaran murya, sannan ya musu sallama suka amsa baki daya, sannan ya ce,
"Da farko dai ina roqa ma mamatan mu gafarar Allah da rahamar shi, ina mana fatan muma samun kyakkyawan qarshe, bayan haka, ina taya Umaimah da Aaseeyah kammala makarantar Secondary, muna fatan sakamakon jarabawar su ya fito da kyau, inshaa Allahu,"
"Ameen ya Allah"
"To abu na gaba kuma shi ne, kun dai san kyau da martabar duk wata d'iya mace shi ne d'akin mijin ta ko?"
Kallon juna sukai su na qunshe dariya qasa qasa,banda Aaseeyah da tunanin ta ya lula wata duniyar,
'Aure? Wanne irin aure kuma? Ya zan yi da burin da ke cikin zuciya ta? A gaskiya ni ba zan yarda da wata maganar aure ba, ko ana ha maza ha mata, su dai da suka girmen dama sin isa aure, nawa nake?'
Kamar a mafarki ta ji Abbu na zayyana qudirin Mahboob akan ta, wani irin yanayi ta ji ta shiga wanda ta kasa tantance shi, farin ciki ne,baqin ciki.ne, ko mamaki, ne ya kama ta? Shin me za ta kira hakan.
Nan take hankalin Noor ya tashi,cikin kad'a kai ya ke kallon Abbu, da ke ta zabga murna da farin ciki shi da Abee,
"Mun kula da cewar 'yan samarin nan kun riga kun sauqaqa mana komai, domin na samu labarin kuna hana duk.wasu manema auren qannen ku zuwa wajen su, balle har magana ta kawo wajen mu, hakan na nuni da cewa kuna son qannen naku da aure kenan, dan haka muka yanke shawarar Noor zai auri Umaimah, Hussein zai auri Ummu Suleim, sai kuma Hassan ya auri Yesmeen, inshaa Allahu, muna roqon Allah da ya sanyawa wannan had'i albarka,ya ba ku zaman lfy, Allah ya hore mana abinda za a yi hidimar biki da shi"
"Tabdijam...yau na ke jin wani abu wai shi kwadon allura da gatari,wannan wanne irin sabon salo ne kuka zo mana da shi? Ba shawara ba tuntubar yara ko su na da wanda sike so, ah ah kawai kun gama yanke hukunci, to hasashen ku bai daidai ba, sannan duk munafikin da ya fada maku wani Mahboob d'an 'yar uwata zai auri wannan jemammiyar yarinyar ya maku qarya, ballanta wai 'Yan biyu na su auri 'yan biyun waccan matar, duk wannan had'in ba mai yuwa bane"
Gaba daya hankulan Yesmeen da Ummu suleim sun tashi, Mahboob kuwa qoqarin magana ya ke, amma ta hana shi, inda ta ke shiga ba nan take fita ba, Hussein ne ya daga murya ya ce,
"Ni fa Abbu ina da wadda na ke so zan aura, mahaifan ta ma sun rasu, a gidan wani d'an uwan su take da zama, ba ma wani dangin ta bane na kusa, kawai dai dan ba ta da wajen zama.ne take a wajen su, tausayin ta da kamun kan ta ne ya sa na ke son auren ta, ni ban ta ba cewa ina son auren Ummu Suleim ba tsakani da Allah a matsayin qanwata na ke kallon ta, nothing more"
"Ni ma nan dai ba na son auren Umaimah, dama ni da Aaseeyah mun riga mun daidaita, ta san ni zan aure ta"
Umaimah kafe Noor da ido ta yi, wanda ke zubar da hawaye, ji take kamar ya cire zuciyar ta ya samu wuqa mai kaifi ya yayyanka ya sa a blander ya markade ya zubar, me take ji wannan mara dad'in sauraro,a wacce duniyar take? Anya kuwa ba mafarki take ba.
Nan fa hayaniya ta kaure tsakanin yaran da iyayen, Mammee mamakin duniya ya kashe ta, zaune kawai take ta na ganin yanda Ummee ke zuba rashin mutunci akan hadin da akai, sannan yaran ta maza sun matuqar bata mamaki, kusancin da ta kula da shi a tsakanin su ashe ta musu fahimta baibai, to in ba son auren su suke b tun da me zai sa su hana kowa zuwa wajen su?
Aaseeyah kuwa irin halin da Mammee ta shiga na rudani shi take ciki har yanzu bata fito ba, ba ta jin za ta iya fitowa da kan ta ba tare da an taimaka mata ba,.wannan wanne irin kwado ne haka ake yi a gidan nasu.
Wata tsawa Abee ya daka masu, gaba dayan su sun firgita da jin tsawar, a zaton su ma Abbu ne, dan shi ne mai d'an zafi zafi, Abee sam ba mai hayaniya bane balle har ya daga murya irin haka.
Cikin tsananin fad'a da bacin rai ya fara magana,
"Ashe ku mutanen banza ne? Ba ku da tarbiyya ba ku ganin girma da qima balle mutuncin mu, mu na zaune a nan amma ku na mana hauka da ihu, wa ye sa'an ku a nan, inni ban da mutuncin da za ku ban girma, Yayah Fa? Ashe ba ku da mutunci? In ku na da qorafi ba za ku bi komai a sannu ba masifa ce za ta warware maku komai,....kai kai Noor ashe ba ka da mutunci har da daukan hannu ka shaqe wuyan yayan ka? Ina ilimin ka ya tafi? Ina sanin ya kamata da kowa ya san ka da shi? Me ye abun fad'a anan? Ku diba halin da 'yar uwar ku ta shiga, sai da Yesmeen ta yayyafa mata ruwa ta dawo da numfashin ta, amma duk kun kacame da hayaniya da ihu,....ke kuma Maman Noor kin ban mamaki, in su yara ne ke ba uwar su bace? Ta ya za ki biye masu ai ta sai an yi da ba za ai ba? Ku kuke da iko da mu ko mu muke da iko da ku"
"Ko da wasa Ibraheem ahir din ka da yi min fad'a miji na na raye, bai mace ba, kai qanin miji na ne na biyu ba miji na ba, ba ka isa ka min fad'a ba"
"Dalla rufe mana baki shashasha daqiqiya kawai, kalli can, kalli Subai'a, ta shiga rudani daga alama, daga yanayin fuskar ta,ita da diyar ta sun shiga rudani, amma me kinga suna wannan haukan da ki ke, dama bana tsammanin abun masu hankali daga wajen ki, ki ja bakin ki ki min shiru, yara namu ne, daga wanda na haifa sai 'ya'yan 'yan uwa na, kar na sake jin bakin ki, idan ki ka sake magana duk hukuncin da ya biyo baya ke ki ka jawa kan ki, kin ji ko baki ji ba"
Yau fa Abbu ya fita a giya matuqa, kuma Ummee ta tsorata, ta shiga hankalin ta ainun, bakin ta ta ja ta tsuke, ta na muzurai.
"Kai Noor me ka ke cewa dazu?"
Gyara zama Noor ya yi da kyau, sanan ya ce,
"Abbu dama ni da Aaseeyah mun riga mun had'a kan mu, ta amince zan aure ta, kuma.na ji kun ce za a bawa Mahboob ita, in haka ta faru an raba ni da masoyiya ta fa kenan, an bawa yayana,"
Kallo suka mayar wajen Aaseeyah da tai shiru ta takure waje guda,a yanzu tunanin ma ta daina yin shi, kallon kukan da Umaimah ke yi kawai take, tausayin ta na ratsa ta.
Shin tausayin Umaimah za ta ji ko kan ta, domin zuciyar ta na cikin rudani.
"Aaseeyah magana ake maki, shin da gaske ne kun daidaita tsakanin ku ke da Noor?"
Daga kai ta yi,ta kalli Mahboon da idanun shi suka yi jawur saboda damuwa, ya na gaf da bakin kujera ya hade hannayen shi waje daya, ya na jiran ya ji amsar da Aaseeyah za ta bayar.
"Ke mu ke jira fa"
"Ni ma ban sani ba, ni dai kawai na san ina son na ci gaba da karatu na, ba na son aure yanzu, dika dika shekara ta sha bakwai da watanni, ba na jin na kai aure,su dai da suka girmen su ya kamata a fara yi wa aure,"
Wata ajiyar zuciya Mahboob ya sauke,ko bata zabe shi ba ya ji dadi da ta nuna ba ta amince da Noor ba, Noor kuwa gaban ta ya je ya durqusa ya ce,
"Kin manta? Kin manta mun tsaida magana ni..ni...ni ne mijin ki? Fada musu, ki fada musu ni ki ke so"
"Yah Noor na amince kai ne miji na saboda ka ce min hakan, amma ni ba na jin son ka a raina irin na soyayya, ban san me zuciya ta take so ba, ban san me ne ne soyayya ba,"
Umaimah ce ta janye hannun Noor daga jikin Aaseeyah ta juyar da shi saitin ta, ta kafe shi da ido, sannan ta ce,
"Ni kuma fa? Ni wa zai aure ni in ka auri Aaseeyah? Wa zan je wa a haka, wa zai yi maraba da ragowar yayan ta?"
Cikin tsawa da rashin son a ja magana Noor ya ce
"Ke Umaimah me ki ke fadi haka, wannan wace iriyar banzar magana ce haka? Saken riga,...dalla malama saken riga"
Umaimah idanun ta sun bushe, gaban Abbu ta je ta durgusa ta ce,
"Abbu dan Allah ka sanya Mammee ko Ummee su duba ni, indai sun samen a matsayin budurwa na amince ku min hukuncin duk da ya dace da ni,saboda na mishi qarya, sanin kowa ne, ba inda muke zuwa, daga makaranta sai gida, a ina na lalace? Yah Noor shi ne ya maida ni kamar matar auren shi,Ummee kin manta..kin manta sanda na ke zuwa tun ina qarama.ina kuka ina fad'a maki gaba na.na min zafi, ina ganin jini, ina jin ciwo, me kike fad'a min, ba kora ta ki ke ba?ba fad'a ki ke mim ba? Ki kore ni, ki ce 'Tafi ki ban waje'...Yah Noor shi ne ya maida ni haka, tun ban san me ne ne saduwa da kebancewa ba tsakanin namiji da mace, har na sani, har ta kai ina zuwa d'akin Yah Noor da kai na in kowa ya yi bacci, sannan na fita kafin kowa ya tashi, bai taba hana.ni ba, bai taba kora ta ba, sai dai ma yi min tarba da kyakkyawar kulawar shi, na sani bai taba cewa ya na so na ba, na sha tambayar shi akan hakan, ya kuma tabbatar min baya so na, amma...ammaa Abbu ban taba tinanin hasashe na zai zama gaskiya ba, ya ce wai...waiii Aaaseeyahh ya ke sooooo"
Ta qarashe maganar ta cikin kuka, kowa a wajen ya daskare a wajen, jin cewa wai Noor kamili, salihi ne ke aikata wannan mummunan abun, Ummee kuwa ba baki, domin tabbas ta tuna lokutan da Umaimahn ke kawo mata wadannan qorafin na jin zafi da jin ciwo a gaban ta.
Abbu ya ma rasa mai zai ce, qarar naushi da faduwar Noor ce ta dawo da su daga kidima da dimuwar da suka.shiga.
Mahboob ne ke ta naushin Noor ko ta ina, jikin shi sai rawa ya ke, tsabar tashin hankali da jin zafin labarin da Umaimah ta gama.bayarwa, cikin kuka Mahboob ke magana, riqe da wuyan Noor a hannun shi, an yi an yi a banbare Noor an kasa.
"Qanwar ka ce fa Noor ta kowanne bangare, uwa d'aya uba d'aya ne kawai.ba ku.had'a ba fa, tun ta na yarinya ka ke lalata min qanwa Noor? Ba zan taba yafe maka ba, kuma na rantse maka kai za ka auri Umaimah,"
"Mahboob sake shi, sake masa wuya, ba ya numfashi..ka sake shi na ce! "
Kallon Ummee ya yi wadda ke zubar da hawaye, sannan ya kalli Mammee da ke qoqarin banbare hannun shi daga wuyan Noor, ganin hawayen ta sai ya raunata zuciyar shi, Allah ya sa mashi son matar tun ba yanzu ba, sake shi ya yi ya fadi qasa yarab, da gudu Ummee ta duqa ta na tattaba shi, Abbu da Abee komawa sukai suka zauna, Abbu ya duqar da kan shi qasa,Abee kuma na bin ahalin na su da kallo,
A hankali Abbu ke furta,
"Laifin mu ne wannan Ibraheem...Ibraheem laifin mu ne, neman kudi muka sa a gaba, muka damqa komai a hannun mata, in mun fita tun safe sai yara sun yi bacci mu dawo, zuri'ar mu ta lalace Ibraheem sabo da sakacin mu, da mahaifan mu za su ga wannan rana wataqila da ita ce ajalin su ba mutuwar Mahmood da Zainab ba, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ya Allah ka sassauta mana,Allah ka kawo mana dauki a wannan lamarin"
"Tabbas laifin mu ne Yayah, amma za mu gyara komai,"
Hawayen su suka share, sannan suka ja hankalin mutanen da ke wajen,
"Duk wannan abu da ya faru ba laifin kowa bane illa laifin mu, mun maida neman kudi mahimmi a rayuwar mu sama da iyalan mu, wannan shi ne sakamakon abinda muka aikata na sakaci da tarbiyyar yaran mu, makarantu kadai da iyaye mata ba za su bawa yara tarbiyya cikakkiya ba, dole kowanne yaro na buqatar namiji a wajen cikar tarbiyyar shi, ku yafe mana baki d'ayan ku, a bisa ga sakacin da mukai da rayuwar ku"
"Wannan gaskiya ne Yayah, muna neman gafarar ku, sannan mu na mai tabbatar da hukuncin auren da muka zartar a tsakanin ku, musamman kai Noor da Umaimah, 'yan biyu kuma haka, kai Hussein ka san dai bai kamata ka qi auren Ummu Suleim ba ko?"
Aaseeyah ce ta gyara zama ta ce,
"Abbu indai har za a tirsasa, Yah Noor auren Umaimah sabida ya lalata rayuwar ta, to ina ganin a tursasa Yah Hussein shi ma ya auri Ummu Suleim, Yah Hussein ko ka amince ko na sanar da su Abee abinda na gani a tsakanin ku"
"Ke baqin labarin ya ishe mu haka, kowa dole ya auri wanda aka ce ya aura mu rufawa juna asiri,"
Mammee ce ta kalli Ummee da ta dage ta na sharhi, yanzu ta dawo hanya kenan tunda ta ji komai da ya faru na lalacewa ya shafi yaran ta, amma sabuwar tambayar da ta shiga zuciyar ta shine me ke faruwa tsakanin Ummu Suleim da Hussein din ta?
"Abbu ni kuma.fa?"
"Mahboon yanzu maganar ka kai da Aaseeyah dole za mu sake duba ta, duba da yanda ta fara turjewa, ba na fatan ka auri Aaseeyah ba tare da amincewar ta ba, ke kuma maganar wani ci gaba da karatu ki aje ta a gefe"
"Abee me ya sa? Kowa ana mishi abinda ya dace, ni me ya sa ba za a min abinda ya dace ba? Abee karatu nake so na ci gaba"
Mammee ce ta ce,
"Kee ki mana shiru, ki bari a gama da wannan case tukunna"
"Ammaa Mammeeee"
Wani kallo mammee ta mata, wanda ya sanya ta hadiye me ke ran ta,Noor da ya samu farfadowa daga suman da ya yi, ne ya ji Abbu na sake jaddada auren shi da Umaimah, kuka ya fashe da shi, ya na fadin,
"Ba zai yu ba, ba zan aure ta ba, ko za ku kashe ni ba wanda ya isa ya aura min Umaimah, na tsane ta, ba na son ta,ita ta sani,ba soyayyar ta a raina"
Hummmmm sanu shafaffe da mai, inji Hameeda, ku ji dannema so yake ya ci double tabb😃
TAUBASHI
PAGE27
HAERMEEBRAERH
Noor ya haukace matuqa, ba ya can ba ya nan, shi ne har Yola wajen Kaka Auwal, domin ya sa baki a bashi Aaseeyah, amma inaa abun ya ci tura, qarshe Abbu kiran shi ya yi ya zazzage shi, sannan ya ce in ya sake zuwa wani waje dan ya kai qarar su, sai sun fad'i abinda ya ma Umaimah, aka hana shi Aaseeyah, da mutuncin shi ya zube wajen mutane,gwanda ya kama bakin shi, amma ya qudurta a ran shi zai basu mamaki, sai sun gwammace ba su hana shi Aaseeyah ba.
Aaseeyah kuwa na can na fafutukar roqon barin ta ci gaba da karatu, so take Mammeen ta ta amince, in Mammee ta amince ta san Abeen ta ba matsala, domin duk abinda Mammee ta ce shi za ai to fa shi za a yin, saboda daraja da qimar ta da mazajen ke gani, har Abbu na bin maganar ta, domin girmama ta da yake, ta kama kanta da mutuncin ta, sannan ta na daraja shi kamar uba ba yayan miji ba.
Yau ma kamar kullum Aaseeyah ce zaune a gefen Mammee, Mahboob da ya dawo aiki, ya shiga dan cin abinci ya na kallon TV amma rabin hankalin shi na kan Aaseeyah, Hussein ya gama na shi nacin ya fita cikin fushi saboda ta qi bashi amsa ma ballantana ya sa ran amincewar ta a auren sabuwar budurwar shi, mai suna Tasneem,Hassan da Yesmeen sun karbi wannan hadin dan har Hassan ya rabu da budurwar shi ta makaranta, ya tattara dikkan kulawar shi ya miqa wajen Yesmeen.
Aaseeyah ce ta sake narkewa a jikin Mammeen ta a karo n ba adadi,kamar wata yarinyar goye, ko wadda za a bawa mama, cikin muryar shagwaba ta ke magana,
"Mammee ni ko? Ni ce na ke neman alfarma wajen ki amma ki ke qi ko? Ni Aaseeyahn ki ko, shi kenan ba komai Mammee,tunda nake ban taba tambayar ki ko da kudin hoda bane,balle turare, ban taba tambayar ki kudin mayafi ko takalmi ba, daidai da kudin kwalli bai taba hadani da ku ba, amma yau na tambayi abinda na ke tunanin zai inganta rayuwa ta da taku dika, amma an hana ni, shi kenan"
Rufe ido tai ta na kukan qarya, wanda bai sani ba sai ya rantse na gaske ne, dan leqawa da idon ta d'aya tai ta ga yanayin Mammeen ta, sai ta ga alamar zuciyar ta ta karye, sai kuwa ta qara sautin kukan ta,ta ce,
"Allah sarki rayuwa,su Ummu Suleim aure suke so, ga shi an ce za a musu auren su, ni na fad'i ra'ayi na amma an qi a barni nai abinda nake so, dika dika nawa nake, ba wani girman da za a ji kunyar barina karatu nai ba fa, daga yau inshaa Allahu ba zan sake maganar nan ba, har a gama Jamb din ma in ta wuce ni ai na qara bata shekara d'aya a banza kenan"
Dogon numfashi Mammee ta ja sannan tace,
"Aaseeyah za ki daina wannan shiriritar ko sai na make ki? Kudin hoda da turare da gazar dama kin taba tashi baki gan ki da su ba? Ba fa na son halin ki na daure mutum da jijiyar jikin shi, tamm,ki wani marairaice kamar marainiya, daga ni ni, ina da abun yi,maganar karatun ki kuma sai Abeen ku ya dawo mun tattauna mu ji ya zai kasance"
Wata runguma ta kai wa Mammeen tare da dora kai a kafadar Mammeen.
"Mammee Allah ya miki albarka,ke 'yar aljannah ce inshaa Allahu, ni dai bani da burin da ya wuce na zama lauya, ina sha'awar na ga ina kwatowa mata haqqin su, ina sha'awar na gan ni cikin kayan nan nasu baqi da fari,"
"Hummm lallai sai ki dage wajen qaro
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 41