Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wa kk magana?" "Magana kuma, sai ka ce mai aljanu,an gaya maki ni Aaseeyah ce? Dan yarinyar nan ita da mai aljanu ba su da maraba" Dariya suka sa, nan fa hira ta kacame akan Aaseeyah,Umaimah ma ta shiga suka yi ta hira,su na tsaka da hira Aaseeyah ta fada dakin a guje ba sallama, ihu suka saka kowa na neman mafaka sabida gigitasun da ta yi, ba ta tsaya a ko ina ba sai tsakiyar su, cikin rashin sani kuwa ta take wayar Ummeen su, nan da nan screen ya fashe, ko a jikin ta ta zauna tare da nade qafafun ta, ta zura hannun ta cikin rigar ta ta zaro chocolates din ta da by now in chocolates na tsiro tuni sun tsiro mata a jikin ta. Su na hada ido da Umaimah Umaimah ta bata fuska, dan ta san daga ina take, ita da Umaimah yanzu sun zama kamar kishiyoyin juna, a yanzu sun san me Yah Noor ke yi da su, musamman Umaimah, gwanda-gwanda Aaseeyah har yanzu gani take kamar ita ke jin dadin taba jikin Yah Noor amma shi ba ya jin komai,bangaren Umaimah kuwa da kan shi ya ke koyar da ita duk wani salo dan su gamsar da junan su cikin sauqi. Dan haka Aaseeyah ba ta jin haushin Umaimah kamar yanda Umaimahn ke jin haushin ta, saboda a ganin ta sabon da tai da hawa jikin shi tun yarin ta ne ya bi ta, in ba ta je wajen shi ta zauna jikin su na gogar juna ba bata jin dad'i,Umaimah kuwa ko ta yi ma Yah Noor magana akan tarayyar da ta kula ya na yi da Aaseeyah sai ya kada baki ya ce, 'Allah ya kiyaye na kula wannan yarinyar, ai asiri za ta tona min ba ta da sirri sam, kawai dai ina bata ne tunda ita ma qanwa ta ce kamar yanda kk qanwa ta, kuma masoyiya ta' Da wadannan kalaman ya ke samu ya dan kwantar mata da kishin da ke damun ta, banda alaqar da ta hada su da Noor zumuncin su kullum ya na nan, qawancen su da son junan su qaruwa yake a kowanne rana a kowanne lokaci, ko da iyayen mata sun musu fada akan ziyartar juna da suke yi a tsakanin su kowa ba zai zauna a bangaren shi ba, ba su ji, duk sanda suka so ganin junan su za su tafi. .......cike da bacin rai Yesmeen ta janyo wayar ta kalli Aaseeyah da ke qoqarin bude ledar Layer chocolate ta danna abakin ta, "Wannan wanne irin iskanci ne Aaseeyah ji yanda kk take wayar Ummee, kin wani shigo ba ko sallama kin firgita mutane" "Ba abinda aljanu ke yi ba kenan? Firgita mutaneeeee" Ta qarasa maganar ta ta na wara hannun ta kamar dodonniya. "Ko kun zata ban ji me kuke ta fada ba, kun fi minti biyar kuna gulma ta," Zama sukai kowa na qoqarin ta sammasa abinda take sha, sun bar Yesmeen cikin tashin hankali, da kyar wayar ta kunu, amma fa screen ya tsage har layi uku, No Hassan ta goge a call log, sannan ta fara tunanin ya zata yi ta aje ma Ummee wayar ta, gashi kowa ya san a hannun ta ta fashe. Aaseeyah ce ta amshe wayar kawai tafara qoqarin bare wani abu a jikin wayar, qara suka sa dukan su, su na qoqarin amshe wayar, ta na gama daye screen guard din ta wurga wa Yesmeen wayar ta ce, "An iya sata ba a san yanda za a fidda kai ba, in halin ki ne sata gobe ma ki qara" Cike da murnar ganin waya ta dawo daidai ta fita a guje dan maida wayar kar wani tsautsayin ya faru, tana samun nasarar aje wayar ta fita daga kitchen din, dan dama a saman fridge ta gan ta ta sungume. Rayuwar su Yesmeen ta zama kowa na boyewa 'yar uwar ta wani sirri na boyayyar soyayyar da ke tsakanin ta da cousin din ta, iyayen su kuwa kowa na ganin ba ya dan shi a tarbiyya,da kamun kai nutsuwa da hankali. A haka shekaru suke shurawa, har Allah ya basu ikon shiga Senior secondary school. Jubeir shi ne yaron da ya kafa gwamnatin soyayyar shi da kyar a wajen Aaseeyah, ta yanda duk makaranta an san ya na son ta, ita ma kuma haka, Jubeir yaro ne kyakkyawa, kuma dan masu hali, ajin su daya da Ummu Suleim, a wajen Ummu Suleim ya dinga kamun qafa har ya samu ta hada shi da Aaseeyah, a hankali ya ke nuna mata kalar tashi soyayyar,wadda ta ke gani mai tsafta ce, domin kuwa daidai da yatsan ta Jubeir bai taba riqewa ba,hakan ba qaramin qima ya ja mishi ba a waje Aaseeyah, ta yanda duk inda ta zauna sai ta bada labarin shi, a gida ne kawai take shakkar maganar shi kar Mammeen ta ta ji. Yau ma kamar yanda suka saba zama a bakin qofar gate kafin azo daukn su, su na hira,Jubeir ya kalli Aaseeyah ya ce, "Aarce na" "Na'am my Jubeir," "Kin kuwa ta ba ji daga bakin mutane cewar ke din kyakkyawa ce da baki da na biyu wajen kyau?" Murmushi ta yi har sai da hushiryar ta ta bayyana, qasa qasa ya yi da muryar shi sannan ya ce, "Kin san kuwa na tab'a jin wani yayana yana cewa masu hushirya su na da d'ad'in kiss" "Innalillahi Jubeir, u ar a bad boy, subhanallahi,Jubeir kai ne kuwa ka ke magana irin ta 'yan iska?" Ta na magana tana kare fuskar ta saboda nauyi da kunyar shi d ta kama ta, ga shi ba ta san dalili ba maganar tashi ta saukar mata da wani yanayi a jikin ta. Tashi ta yi daga wajen, ta na murmushi, murmushin shi ma yake, a qalla burin shi ya kusan cika nan ba da jimawa ba, har aka zo daukan su ba ta sake bari sun hada ido ba, sai dai ta dinga satar kallon shi cike da shauqin son shi, shi ma ya na magana da abokan shi ya na kallon ta,drivern su Aaseeyah na zuwa ta bi bayan su Yesmeen suka shige, sai da ya ga tafiyar su sannan ya shiga tasu motar, wadda ta jima a wajen ana jiran shi amma saboda isa da taqamar arziqin uban shi bai je sun tafi ba. ***************************** Ramadan ya kusa, murna wajen su Yesmeen ba a magana, domin duk shekara ake haduwa dika family din a babban parlourn gidan da aka rufe shi, a ci a sha a gaggaisa a yi ma iyayeyn su da 'yan uwan su da suka rasu addu'a. Bikin sallar su na kai a qalla kwana uku, domin ba su kadai ke bikin sallar ba, 'yan uwan Haj. Subai'a, Haj. Fateema da Haj. Zainab,su ma sukan zo dan sada zumunci, da 'yan uwan mahaifiyar su Alhaji Ibraheem,da ke zaune a garin Yola. Bayan kwana ukun nan sai kowa ya koma garin shi gidan kuma ya dawo kamar yanda yake. Siyayyar kayan sallah ne niqi-niqi a hannin 'yan matan, inda yayun su maza ne suka kai su, ko da suka dawo kowa ta yi bangaren ta, tun a hanyar dawowa cikin Aaseeyah ke mata ciwo, tun ta na daurewa har ta fada ma Yesmeen,nan suka dinga mata ftan samun sauqi, Noor ne ya taimaka mata da kayan ta har bangaren su, ko da ya ajiye mata ya koma nasu gidan. Kwance take ta kasa fidda komai ta ga me ta siyo ma, sai murqusu take, Mammeen ta na shigowa hawayen ta na gangarawa, kuka ne ya kwace mata mai cin rai, irin na shagwababbun yaran nan. Cikin kulawa Mammeen ta ta kalle ta, "Aaseeyah me ke damun ki?" "Mammee ciki na, nan wajen ke min wani irin ciwo tun da nake ban taba jin ciwo mai azaba irin shi ba, numfashi na kamar zai dauke" Murmushi Mammee ta yi, in numfashi zai dauke ta ina wannan maganar ke fita? Dafa marar ta ta tayi, sannan ta mata addu'a, tare da yi mata sannu, dakin ta ta koma, ta dakko pad da sabbin panties guda biyar, ta nufi dakin Aaseeyahn da su. Tsaye ta gan ta hannun ta da jini, ta na ta rusa kuka, tare da kiran ta shiga uku mutuwa za tai, "Ke meye haka? Ki nitsu, ki min shiru na ce!" ukan ta ta rage a hankali amma hawayen ta na zuba kamar an kwara mata ruwa a fuska. "Zauna ki ji," Komawa ta yi ta dan dofana jikin ta a qasa, sannan ta kalli hannin ta da ta dangwalo jini a jiki. "Aaseeyah kin san wannan jinin me ne kuwa?" "Mammee daga nan fa na ji abu na zuba da qarfi da zafi ina tabawa na ga jini, Mammee mutuwa zan yi ko?" "Aaseeyah kenan, a gaskiya da sauran ki, kar fa ki manta SS 1 kk yanzu, ina karatun da kk na islamiyya akan haidha? Ta ina da kk san haidhan ke fita,ina ake cewa za a wanke kafin a yi wankan tsarki, ke yanzu fisabilillahi duk baki gane komai ba? Sai aukin addu'ar Allah ya sa ki fara haila ko? To ga haila nan Aaseeyah,duk macen duniya na haidha, sai dai in bata kai lokacin ta ba, ko bata da lafiya, ko kuma ta tsufa ta wuce lokacin ta" Shiruuuu Aaseeyah ta yi tare da tunanin dama haka hailar take qawayen ta suka maida shi wani babban abu ake ta tattaunawa akai? "Aaseeyah muje ki gyara jikin ki, ina da mahimmiyar magana da ke" Tashi ta yi cikin langwabewa suka shiga bayi Mammee ta nuna mata yanda ake kula da kai, suka fito a tare. Zama suka yi su na fuskantar junan su, cikin nuna ma Aaseeyah maganar da za su yi mai matuqar mahimmanci ce Mammee ta kira sunan ta, sai da ta ji faduwar gaba saboda tunda take bata taba ganin fuskar mahaifiyar ta a haka ba, tabbas abinda take shirin fada mata ba na wasa bane.............. Pls Read Understand Comment Vote. 💅🏻 TAUBASHI (COUSIN) 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH Page 6: "Da farko ina qara godewa Allah da ya bani abinda na jima ina buri, wato 'ya mace, sannan ya nuna min girman ta, ina fatan Allah ya bani ikon sanya ta a hanya da bata tarbiyyar da na jima ina fata, (ta manta cewa tun a yarinta ake bada tarbiyya, ba wai sai mace ta fara haila bane ta cancanci a bata tarbiyya abinda ka gina yaro akai tun yarinta da shi ya ke tashi). Aaseeyah wannan jinin da kk ga ya na zuba a jikin ki shi ake kira da jinin haidha, wanda duk wadda ta fara shi hukuncin Allah ya hau kan ta, in ta yi abu mai kyau ladan za a rubuta mata a littafin ta sabo da aka bude mata, in ta yi mara kyau za a rubuta mata zunubin abinda ta aikata,a lokacin da rayuwar ta ta qare ta koma ga Allah, to a lokacin ne za a bata littafin ta,in ta karba da hannun dama tabbas ta yi dace, in kuwa ta karba da hannun hagu ta halaka, Aaseeyah ki sanyawa ran ki cewar kamar yanda inna yi abu mai kyau Allah zai ban lada, to kema haka ne, innai mara kyau zan samu zunubi kema haka ne, ni da ke ba mu da banbanci a wajen Allah, sai dai qarin wasu hukunce hukuncen da suka banbanta tsakanin budurwa da matar aure. Aaseeyah ki sani kin zo lokacin da za ki kula da kan ki, ba bu ke babu wasa da maza, kar ki kuskura ki sake jikin ki har wani ya yaudare ki, ya lalata maki rayuwar ki, kar ki zalunci kowa domin Allah na yafe laifin tsakanin shi da bawan shi, amma baya yafe laifin bawan shi da wani bawan nashi, ki guji daukar abinda ba naki ba, domin ranar lahira sai wuta ta cinye haramun da dan Adam ya tara a jikin shi ko da zai samu damar shiga aljannah, ba a shiga aljannah da haram, ki guji gulma da munafurci, annamimanci,da shirka ga Allah, ki kiyaye dokokin Allah, Allah zai kiyaye ki. Aaseeyah duk abinda ya shige maki duhu game da rayuwa ki tambaye ni, inshaa Allahu zan maki bayani kin ji? Allah ya kare ki daga sharrin zamani,ba na jin ki wajen tsaida sallah, amma kinga azumin nan da za a fara bake za ai domin ba a azumi ko sallah in ana haidha, sai an gama, an yi wankan tsarki, duk sanda kk daina ganin jinin ki sanar da ni zan koya maki yanda ake wankan tsarki, da yanda za ki kula da kan ki, ba a rama sallolin da suka wuce in ana haidha, amma ana rama azumin da ya wuce mutum,dan ki na haidha ba shi zai sa ki daina karanta qur'ani ba, ki na da hadda ki ci gaba da yin karatun ki a komai kk, kuma ki yawaita tasbihi, tunda ba ki sallah; tasbihi ga Allah da hailala, da istigifari za su taimaka maki wajen samun kusanci ga Allah,bari na je na dora abinci, a hankali zan ci gaba da warware maki abubuwan da baki fahimta ba, domin abun da yawa." "To Mammee na gode, inshaa Allahu zan kiyaye abubuwan da kk fada min,amma Mammee, ina da tambaya" "Me ne ne tambayar ki?" "Mammee na ji qawaye na na cewa ba a taba maza in aka taba maza ana yin ciki, Mammee kenan ko Abee ba zai taba ni ba? Ko su Yah Hussein?" Murmushi Mammee ta yi ta ce, "Ba haka ake nufi ba, 'yan gidan ku maza ai su ba laifi dan sun taba ki, a waje ne ba a son ki bari kowa ya taba ki, kin gane?" (Ku ji shiririta,ta manta da miyagun cikin gida, na dai tabbata kun gane bayanin Mammee bai cika ba ko?) Daga kai ta ke alamar ta gane, dan haka Mammeen ta ta fita ita kuma ta koma ta kwanta tare da damqe cikin ta da ke murda mata sosai. Ranar har dare sosai su Umaimah ba su ga Aaseeyah ba, sun so shiga amma Ummee ta hana su ta sanya su aikin gyara kitchen a daren, wai gyaran azumi. Aaseeyah ta sha wahala dan har makaranta sai da ta daina zuwa saboda tsananin ciwon cikin da ke damun ta, har da allura sai da aka mata, duk ta fada ta rame sosai, ta ci burin a dauki azumi da ita amma ba hali, ta na ji ta na gani su Yesmeen ke tsokanar ta da gandiya sai dai ta gyada kai kawai, da alama dai Yesmeen ta dau bashi. Sai da tai kwana bakwai ciff kafin jini ya tsaya, Mammee ta koya mata yanda ake tsarkake jiki, tare da hada mata ruwan ganyen magarya, da ta tafasa da aloevera (matan aure na saka yar bagaruwar mata kadan ba da yawa ba) bayan ta yi tsarki da wannan ruwan na kwana uku,tare da shafa white musk a jikin pant din ta,Mammee ta tafasa kayan qamshi da suka hada da citta kaninfari da kimba, sai minannas, ta tace ta sa zuma mai kyau ta bata ta na sha, shi ma na kwana uku. Haka nan Aaseeyah ta fara jin wani sauyin yanayi na jin ita wata babba ce itama na shigar ta, dan haka ta dage itama sai Mammee ta sai nata bra ta fara sanyawa,da ta qi sai ta je dakin su Umaimah ta dau ta dayar su ta saka, a haka ta dinga tara bra daya bayan daya nasu a wajen ta sai da ta debi kusan bakwai wanda kusan na yesmeen sun fi yawa a ciki,sannan ta bari,sun sha fada da juna su akan satar bra, nan kuwa wadda ta sata na tsakanin su, ko da da rana daya ba wanda ya zarge ta tunda ba su taba tsammanin za ta dauka ba. Yanzu babban burin ta bai wuce a sai mata waya ba, domin duk qawayen ta na da waya, dan haka yau suka hada baki gaba dayan su akan za su ma iyayen su maza magana dan a sai masu waya, su na bangaren Mammee gaba dayan su suna hira,Hussein da Hassan na zaune a tsakiyar su kamar wasu sa'annin su, Noor ya shigo, shi a dole ga ustaz,kallo ya ga su na yi na wani American film, ba abinda ake sai soyayyah, cikin nuna shi din babba ne ya ce ma Aasseyah, "Aaseeyah miqo min remote dinnan" Tashi ta yi ta na tura baki ta miqa masa, dan a yanzu ta san me ne ne jin dad'in kallon irin fina-finan nan sosai, wanda a da ko ta kalla ba ta gane ma me ake. Sauya tasha ya yi zuwa ta labarai, Mammee da ta je aje flask din ruwan zafi a saman dinning ta ga an sauya tashar ta ce, "Da kyau Noor, tun dazu nake ma yaran nan magana, sun maida ni ban san me duniya ta ke ciki ba, sun qi kashe wa, amma ai ga shi yanzu da kazo ka min maganin su, ace yara ba ku da aiki sai kallon tashar turawa?" (Laifin wa) Murmushin jin dad'in yabon da aka masa Noor ya yi, sannan ya maida hankali wajen kallon TVn da ya sauya, Huseein da Ummu Suleim na zaune daf da juna, su na hira qasa qasa, Aaseeyah kuma tunda ta miqa ma Noor remote ta samu waje ta zauna a gefen qafar shi ta dama, Umaimah na zaune a kujerar da ke kusa da ta shi, sai Yesmeen dake zaune kujera daya da Hassan, hira suke sosai kowa na ba dan uwan shi labarin makarantar su da irin rashin ji da qoqarin da suke, difff aka dauke wutar nepa, salati suka sa a tare, kowa na qoqarin tashi dan nema ma kan su hake, kusan kamar hadin baki, mazan kowa ya miqa hannu jikin wadda ke kusa da shi. Aaseeyah ce ta miqe a duhun dan zuwa amso torch light wajen Mammeen ta, shiru ka ke ji kamar ba su ne ke ta hayaniya dazu ba, a cikin duhun nan da za a kunna wuta ba tare da tsammani ba lallai da zuqatan iyayen su sun buga don tashin hankalin ganin abinda yaran su suke aikatawa. Tun daga fitowar Aaseeyah daga dakin Mammee suka farga da hasken da ke fitowa, nan da nan kowannen su ya nutsu,ya daidaita zaman shi, ajiye fitilar tai tare da fadin. "Lallai Nepa sun iya shiya,jiyanda suka dauke maku wutar jikin ku, kowa ya yi dif, ni na ma gaji da jiran Abee bacci nake ji," "Ni ma baccin nake ji, Umaimah ku tashi mu tafi gida" In ji cewar Noor. "Ka ji Yah Noor dinnan kamar tare ku ka zo" "Aaseeyah baki da kunya ko?" "Yi hakuri" "Kai ku tashi mu tafi sai da safe, in ya so ni da kai na zan roqa maku Abbu a sai maku waya, ai kun zama manyan yara yanzu, ku na buqatar wayoyi" Da sauri Umaimah ta kama hannun shi ta matse a qirjin ta cike da murna ta ce, "Dan Allah da gaske za ka roqar mana? Ka san fa kana fada ko ba ya so dole zai sai mana," Cikin sauri ya janye hannun shi, ganin yanda kowa ke kallon su, ya bata rai ya ce, "Ke me ya sa baki da hankali ne, ni sa'an ki ne kk riqen hannu haka, tashi nace mu je ku kwanta, ai ni na ce zan roqar maku ko?" Da sauri Umaimah ta miqe ta yi hanyar waje, Ummu suleim kuwa da Yesmeen kowa jan jiki ta fara ba su son tafiya, amma sun san tunda Noor ya bada Umarni dole a bi. Cikin qunquni suka fita suma, ko da suka shiga dakin su ba Umaimah ba alamar ta, tunani suke ko ta shiga bathroom, Shirin bacci suka fara, har sun kashe fiila Umaimah ta shiga, ta kunna, nan suka zuba mata ido, cikin dan daburcewa irin na mara gaskiya ta ke bin su da kallo tare da tambayar su dalilin qura mata ido haka da sukai, "Ba komai, kawai ina mamakin daga inda kk ne, bayan kin riga mu tahowa" "Daga kitchen mana,ina zani?" Taabbas daga kitchen din take, ta lungun store din dake manne da kitchen din, ita da Noor, abu a duhu, ba na dorar da me ya faru ba, baki na qanin qafa ta, ehe. Iyaka na ga Umaimah ta fito ta na gyara zani da rigar ta, daga baya Noor ya fita dauke da qaramar gorar ruwan sanyi cike da nishadi a fuskar shi. Ba wanda ya sake kula ta a cikin su suka kwanta ta wuce bayi, ta fara gyara jikin ta, sannan ta dawo ta kwanta ita ma. Da asuba su na suhur Noor ya kawo maganar sai masu waya, ba bata lokaci kuwa Abbu ya yarda da maganar sai musu waya, domin a tunanin shi Noor na son su yi amfani da wayar ne kamar yanda ya ke amfani da tashi wajen jin karatu da sauran abinda ya shafi ilimi. Sati daya bai rufa ba sai da kowaccen su ta mallaki dalleliyar waya mai kyau da tsada, kowaccen su murna kamar ta zuba ruwa a qasa ta shanye,a cikin qanqanin lokaci yayun nasu suka sanya su tsundum a social network,su ma a dama da su. Duk da warning din da Noor ya musu akan kar su kuskura ya ga Lambar wani namiji a wayar su, duk sanda ya ga no wani namiji to fa zai amshe wayar, hakan bai hana Aaseeyah sanya No Jubeir a wayar ta ba, inda ta sauya sunan shi da Zubaidah,Jubeir ya ji haushin hakan amma ba yanda zai yi, tunda ta sanar da shi sharadin da yayan su ya sanya musu dika. Ba qaramin jin haushin yanda yayun nasu suke taka tsan-tsan da qannen nasu Jubeir ke ji ba, bayan ya san 'yan biyu farin sani, ya san yanda suke shanawa da 'yan mata, amma qannen su ko da jariri suka gani a waje indai namiji ne, to fa sai sun dinga bala'i, kamar za su cinye mutum. Dan haka akwai babban qudiri a zuciyar shi, na ganin ya dasa soyayyar shi mai zafi a zuciyar Aaseeyah ta yanda ba 'Yan biyu ba ko iyayen ta ne suka hana ta ganin shi ba za ta amince musu ba. Ai kuwa ba tare da ya yi wani yunquri ba, Aaseeyah ta sama masa wajen zama a zuciyar ta, domin kuwa Jubeir yaro ne son kowa qin wanda ya rasa,ko wanda ya rasa din ma zai fata a ce watarana ya samu, sai gashi duk makaranta baya kula kowa sai ita,hakan ne ya bata damar bashi dama domin ya zama masoyin ta. Soyayya suke da fari mai tsafta, abu na farko da Jubeir ya fara koyawa Aaseeyah shi ne qarya, ya koya mata yanda za ta batar da duk wata shaidar chats da suke, tare da koya mata yanda za ta danne soyayyar shi a gaban mutane, duk yanda ta ke jin son shi na mintsinin ta, da yanda ta saba da surutu Aasseyah haka take dannewa, sai da ya tabbata mutane sun zaci ba su tare sannan ya koma ta qarqashin qasa ya na dasa mata soyayyar shi mai tsaya mata a zuciya. Lokuta da dama in an sha ruwa ta zauna a daki ita daya su na chatting, sai ya sako mata magana wadda za ta sa yanayin jikin ta sauyawa, da buqatuwar abinda ya furta mata, a hankali ta fara developing wata iriyar soyayya mai cike da sha'awa a cikin ta. Wata ranar asabar,wadda ta kama jajiberin sallah, 'yan uwan ahalin sun zo dan yin bikin sallah, wanda yawancin su 'yan mata da samari ne, masu aure uku ne kawai, su ma mata ne, ba a jima da yi masu aure ba, a qalla mutane sun fi talatin a gidan, duk inda ka zauna a gidan da daren daba za ka gani ta 'yan mata da samari, Aaseeyah ce ke zaune ita daya a jikin wata flower da aka shuka daf da gate din gidan, ta na ta chatting da Jubeir har da ture turen hotuna, ta karkace sai danna selfy take ta na tura masa a daren kamar wata aljana, shi ma tura mata na shi ya yi. Duk samarin da suka zo Cousins din su suna ta gwada sa'ar su ta qi kula su, ta maida hankali wajen hira da masoyin ta, wayar shi ta ga ni, cikin murmushi ta daga ta kara a kunne tare da fadin, "Yanzu ka kasa hakuri goben ma ta yi ko? What if aka ce ba a ga watan sallah ba fa?" "Wannan tunanin ne ya sa ni zuwa qofar gidan ku a yanzu, dan ba na son a samu akasi," "What!" Ba ta san ta fad'a da qarfi ba

Chapter 4 of 41