ciki, sai sanda akai sa'a Baba ya dawo itama Yabi ta zo, kuka nake ta yi saboda yunwa, rabo na da abinci kwana daya da yini daya, ko ruwa na sha qullen ciki yake,gashi dare ya fara yi,na rasa wajen wa zani na samu abinci,na yi roqo a maqota ba wanda ya ban komai, duk masu son taimakan daga maza har mata wani abu suke nema a waje na, ina tsaka da kukan yunwa da kewar Isya Baba ya shigo,da alama a buge yake, duba da yanda yake dan hada hanya.
Duk ba qarfi jiki na,da kyar na iya daga kai na na kalle shi, daga baya na maida kaina na kwanta, muryar Baba na ji ya na cewa,
'Yabi zo nan ki kwanta,dan iskanci ki na ganin na dawo ba za ki zo ba?'
Da kyar na budi baki na ce,
'Baba ni ce, bansan inda Yabi take ba,'
'Ahhh Saratun Baba, ke ce anan? Taso ki zo mu gaisa'
Mamaki ne danqare a raina, amma dake yunwa ta damen, ina son na lallaba shi ya ban wani abu ni ko gari ne na sha ko ba sugar, sai na rarrafa na je wajen shi, ina zuwa kuwa ya kai min sura, na dan ja baya na ce,
'Baba ni ce fa ba Yabi bace'
Domin ba abinda ban sani ba game da kwanciyar aure a wannan lokacin, ba ruwan su da wai muna wajen ko bama nan, da sun buqaci juna labulen da suka raba tsakanin mu za su ja, ya rufu da kyau bai rufu ba ba ruwan su, haka za su yi abun su su tashi, dan haka na gane me yake nufi da ni.
'Baba da Allah ka taimaka min yunwa nake ji, ji nake kamar zan mutu'
'Zo nan na baki kudi ki siyo nama a waje ki kawo mana mu ci, ki hado da lemo,'
Cikin rawar jiki da farin ciki na isa gaban shi, domin amsar kudin siyan naman, tunda ya kama hannu na ban iya kwacewa ba sai da mahaifin ciki na ya lalata rayuwa ta, ya maida ni cikakkiyar mace, sannan ya sauka ya kwanta ya na bacci har da munshari."
Hawayen da ya cika idanun Aliyyu ne suka gangaro, da sauri ya sa hannu ya share su,da ya na da hali da kuma ya san wace ce ita tun kafin a zo Abuja tabbas da ba zai bari a yanke mata wannan hukuncin ba, duk da bai ji labarin tabargazar da ta ci gaba da rayuwa a ciki ba, zuciyar Eliza ta qeqashe dan haka ci gaba ta yi da labarin ta da cewa,
"Ina farfadowa daga sumar da na yi, na fashe da kukan azaba,ban bata lokaci ba wajen rarrafawa na dauko wuqa na samu cikin mahaifi na na ciki na na daba masa sau ba iyaka, sai da jiki na da komai na wajen ya koma kalar ja, da jinin shi, n lalube aljihun shi na debe kudin ciki kaff, kudade ne masu yawan gaske, tunda dawowar shi kenan, bai samu zuwa gidan karuwai ba balle su cinye kudin.
Nan take na cire kayan jiki na, ina kuka, jiki na na rawa, ga ciwo da na ke ji a kota ina a jiki na, kayan Yabi na sanya, na saka takalmin ta, na fita daga gidan, cikin sa'a ba wanda na hadu da shi, saboda dare ne lokacin kowa ke fita neman na abinci, masu yawon karuwanci, masu abincin dare, masu aikin sayar da kwaya,da dik wani abu dai da suke neman kudi da shi, duk an tattafi, da dama 'yan caca ne sai masu zama wajen masu suya, da shaguna haka ko wajen cin abinci.
Abinda na fara yi shine nesa da gidan mu, da unguwar ma baki daya, na isa tashar mota, a nan na sai abinci da abun sha, na ci na qoshi, sannan na biya kudi na shiga gidan wanka na yi wanka mai kyau, na samu wani driver na masa bayani ina so na je Arewa, sai ya fara min lissafi a arewa wanne gari? Nai shiru, ya ce kano? Jigawa? Katsina ko sokoto? Zabin farko na bi, na ce Kano,nan da nan kuwa ya ce na jira sai gobe da yamma motar shi zata yi lodi, ya ce zan iya kwana a ciki in ina so, ganin yanda na ke a jigace ne ya sanya wannan mutumin mai suna Mic ya taimaka min, a nan motar nai bacci qunshe da kudi na a marata.
Da safe na fita na je gidan wanka na yi buqatu na na je na sai abinci, na dawo na tarar ya kawon tea da bread na nuna masa abinci na sannan na masa godiya, ya ce ba komai.
Har yamma muna tare da shi, anan ya fuskanci ban san kowa ba ma a Kanon kawai zuwa zan yi, alqawari ya min da cewar in mun je zai hada di da wadanda za su kula dani,
'We day talk seens u never tell me ur name na, me i don tell u my name na watin bi ur name?'
(Muna ta magana tintuni, baki sanar dani sunan ki ba,ni na sanar da ke suna na,ke baki fadan sunan ki ba?)
Shiru na yi, na wani dan lokaci,sannan na ce masa,
'My name na sarah'
Nan ya dinga yaba suna na, har lokacin shigar da fasinja ya yi, aka loda mutane a motar, qin karbar kudi na ya yi, da na bashi, nai ta masa godiya kamar zan kwanta, bayan yaya na shi ne mutum na farko da ya taimakan a rayuwa domin Allah ba tare da na bashi komai ba.
Motar mu ta tashi zuwa garin kano, tinjimin bajimin gariiii....
Chaiii i swear na gaji, mu dakaci Sarah Eli zuwa gobe inshaa Allah dan jin ci gaban labarin ta, i hate to tell u that ur comments ar not convincing at alllllllll
TAUBASHI
PAGE 48
"......Mun isa garin kano da safe misalin qarfe 10am,bacci ma nake ta yi a lokacin, ban san an iso ba,sai da na kusa da ni zai fita ya tashen, na duba na ga ba kowa a motar,da sauri na fara zare ido dan gani na a sabon gari, ko ta ina hausa ke tashi,ba kamar can Lagos ba da kusan ko ina zaka ji ana turanci,nan Mic ya leqo ya ce na sakko, na fito, ya kammala abinda zai a tasha, muka hau taxi muka nufi wata unguwa, tun a hanya yake waya, ban san dai me ake bashi amsa da shi ba na ji ya ce,
'Ok we will wait for u then'
(To za mu jira ka)
Mun isa gidan su Gazaa a wannan lokacin, muka jira a waje, dan mai gadi ya qi ya bar mu mu shiga, dik da Mic ya sanar da su shi yayan Sam ne, amma haka aka qi barin mu shiga, gashi ina son zagawa, a nan waje na zaga, a cikin fulawowin gidan.
Mun kai bayan isha'i muna jiran su basu dawo ba, Mic ya gaji liqis, duk da na bashi kudi ya samo mana abinda za mu ci ya qi karba, ya ce akwai kudi a wajen shi, da kudin wajen shi ya siyo mana bread da lemon kwalba muka sha, sauro duk sun gama cizon mu,Mic ya fara gyangyadi ba jimawa motoci uku suka danno gidan a guje, ba shiri muka ja baya da gudu muma, har mota guda ta shige muka ga mai bi mata ta tsaya,qasa suka yi da glass din motar, Sam ya leqa tare da fadin,
'Bro Mic,how na,oya come inside'
Bayan sun shige ne, mai gadi da ya ga Sam ya mana magana sai ya barmu muka shiga, rungume juna suka yi da Sam da Mice, ni kuma ina rakube a gefe, ina jiran su gama magana, dan ban iya gaisuwa ba balle ba na gaba da ni girman shi, magana Mic ya ja Sam suka jima su na yi a gefe, ban san me Mic ya fada masa ba har yau da nake baka labarin nan, Sam ya kallen da idon tausayawa sannan ya ce min,
'Meye sunan ki?'
'Saratu'
'Ok muje ciki, ki yi wanka, ki ci abinci, zamuyi magana'
A wani daki mai kyau aka ajiye ni, Sam ne ya nuna min yanda zan amfani da abubuwan cikin bayin, ya bani riga da wandon shi wanda zan saka innayi wanka.
Ina gama wanka na saka su, tashin lagos ina saka kayan da suka fi wannan ma, leqawa ya yi ya kira ni muka hadu gaba dayan mu har Gazaa muka ci abinci,a nan Sam ya gabatar da ni a matsayin Cousin din shi daga qauye,iyaye na sun mutu shi ne yayan shi ya kawo ni wajen shi, Gazaa ya min sannu da mutuwar iyaye na, nan take kuwa na fara kuka tunawa da irin rayuwar da na baro, da mahaifina da na kashe, shi ne musabbabin kukan, na ga gata a ranar, domin kuwa gaba dayan su sun nuna min damuwar su.
Sai da suka cika min ciki da abinci da madara, aka ban magani na gajiya dana kwaso, Sam ya raka mu dakin da zamu kwana ni da Mic, washegari kuwa da sassafe Mic ya tafi, na mishi godiya daidai wadda na iya, ya ce ba komai,taimako ne.
Mu na karyawa Gazaa ke tambayar suna na, har Sam zai magana, sai nai sauri na ce,
'Eliza'
Kallo na Sam ya yi, sannan ya kalli Gazaa, cikin yarda da magana ta Sam ya daga kai ya ce,
'Elizabeth ba, sunan kakar mu aka sa mata'
'U have a nice name there'
(Ki na da suna mai kyau)
'Thank u sir'
(Na gode yallabai(
'No don't call me sir just call me Gazaa'
(Ah ah kar ki kira ni Yallabai ki kira ni da Gazaa)
Murmushi na yi for the first time, a cikin kwanakin da na yi ina wahala.
A hankali muka shaqu sosai da Sam, har ya zamana ya fara hilata ta na sakankance da shi sosai, kaini shopping,ya kai ni wajen shaqatawa, har na bashi asalin labari na, ya tausaya min sosai, sannan ya ce na masa alqawari ba zan sanar ma da kowa wannan labarin ba, na kuma daukar masa alqawari.
A hankali kuma soyayya ta qullu a tsakanin mu, har muka zama kamar mata da miji da shi, daga baya suka bude min yanayin sana'ar su, har na zama kamar jari a cikin ta, domin kuwa tsadaddun kaya suka siyo min, wajen gyaran jiki Gazaa ya sa aka kaini, daga baya ma da ya ga abun na buqatar gyaran kullum mai gyara ya aje min a gidan, ita ta koya min duk wani abu da ya kamata uwa ta da ubana su koya min.
Kafin na cika shekara biyu a gidan na zama wata kilalliyar mace mai aji, har ta kai Gazaa ma watarana ya na gayyata ta dakin shi na taya shi kwana, daga Gazaa sai Sam su kadai nake kulawa a gidan, su ne manya.
Sukan fita dani wajen masu kudi, dan na shiga jikin su, a saba da ni in mutum ya kaini gidan shi ni zan bude qofa a shiga ai fashi a fita, dan ba na yarda akai ni hotel.
Fara aiki da ni sai ya zama masu kamar mabudin arziqin su,ni na samo masu Sanata Kabiru, Hon. Mamman Accu, da Shalele, Alh. Munkaila kuma ya shiga qungiyar mu ne ta dalilin Sam.
Arziqi ya wadace mu,mun bunqasa mun kuma yi zarra a cikin harkar fashi da makami, muna iya qoqarin mu na ganin mun kare kan mu daga fadawa komar 'yan sanda Sam shi ne ya sai mana gidan dake wani qauye a nan garin kano ni da shi saboda ko da wani abu ya faru muje mu boye.
Kwatsam watarana mun rabu da shi cikin so da qauna, dan daren ranar ma sai da ya saci jiki ba tare da sanin Gazaa ba ya je waje na, washegari kawai na ji an kashe shi.
Sauran labari kuma ka san dik abinda ya faru,alfarma daya nake sake roqa a wajen ka shi ne, ku yafen, kai da Mahboob, kuma ina maka fatan ka samu mace nagartacciya Aliyyu domin kai mutumin kirki ne, Allah ya qara daukaka ka akan aikin ka,ya kuma baka kariya,na gode sosai da soyayyar da ka nuna min tun baka san ko ni wace ce ba"
Aliyyu kam ya shagaltu da sharar hawayen tausayawa Sarah, zuciyar shi ta karye matuqa da jin labarin ta,tunda yake bai taba jin labari mai ban tausayi haka ba, dan rayuwar aikin shi kawai ya sa a gaba,mene ne laifin ta? Laifin ta ne ko na iyayen ta abinda ya faru a rayuwar ta? Haka ya kamata iyaye su raini yaran su? Shin iyaye mata ne suka fi laifi a wajen bada tarbiyya ko iyaye maza? Tarbiyyar yara a hannun wa ya fi cancanta uwa ko uba ko yayu? Ko kuma al'umma? Shin in aka ga mabuqaci barin shi ya kamata a yi har ya nema wa kan shi mafita ko tausaya mishi ya kamata a yi domin rayuwar shi ta daidaita?
TAUBASHI
PAGE 49
A ranar da Aliyyu zai koma Kano a ranar aka yanke ma su Eliza hukuncin su, wanda shari'a ta tanadar ma mutane kamar su, ya na zaune a jirgi, ya kalli time da ke manne a agogon shi, lumshe ido ya yi, wasu hawaye masu zafi suka sauka a idanun nashi, bai damu da wa zai ga babban mutum kamar shi na kuka ba, tausayin Eliza da ke danqare a cikin zuciyar shi, ya masa nauyi, ya kuma tokare kowanne angle na ran shi ya fi ye mashi jin kunyar a gan shi ya na hawaye.
Har suka isa Kano bai dawo normal ba, shi kenan rayuwar ta ta zo qarshe,ba tare da ta tanadar wa kan ta wajen zama mai kyau a lahira ba, ta tanadar wa kan ta wuta,da azabobi na ubangiji,ta sha wahala a duniya, rayuwar da ta yi ta jin dadi qalilan a duniyar, gashi ta tafi lahirar bata shirya ma kan ta mazauni kyakkyawa ba.
A qofar gidan su Mahboob ya sa drivern shi ya tsaya, domin ya na isa Airport ya tadda shi ya na jiran shi, kasancewar ya san da dawowar shi a ranar.
Izinin shiga aka musu,suka shiga shi da dan sandan da ke kula da lafiyar shi,Mahboob ne ya fito, cikin fara'a da walwala, amma yanayin da ya ga fuskar Aliyyu sai ya hadiye farin cikin zartar ma da su Eliza hukunci da akai, parlourn Mammee shi ne masaukin da ya musu.
Aaseeyah ce ta fita sanye da dogon hijab, ta dan rusuna ta gaida shi, bayan sin gaisa ta zauna a kujera cike da murna, ta na fada wa Aliyyu ai sun ga komai a TV.
Wani murmushi ya mata mai cike da quna, da nuna baku san komai ba,dakatar da fara'ar da take tayi, ta ce,
"Yah Aliyyu ka sha lemo mana, and me ya faru gaba daya ba ka farin ciki da kawo qarshen wadannan masu tada zaune tsayen a cikin al'umma, kai ne fa jigon samun wannan nasaran amma sam ban ga ka na farin ciki ba"
"Aaseeyah da ace kin san me na sani game da Sarah, da sai kin koka a matsayin ki na mace,domin ku na cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne right?........"
Kafin Aliyyu ya gama basu labarin da Eliza ta bashi Aaseeyah ta far shessheqar kuka,tsananin tausayin ta ya gama kassara duk wata tsanar ta a ran ta, ji take da ma ace bata mutu ba, za ta iya raba Mahboob da ita, ada bata jin zata bar wata mace ta rabe shi, amma da ta san asalin labarin Eliza da ta ja ta ajiki, ta taimaka mata wajen sanin Allah, wannan shine babban abin tausayi a rayuwar Eliza,duk wanda bai san waye mahaliccin shi ba rayuwar shi ba ta da ma'ana.
"Allah mun gode maka, Allah mun gode maka, Allah ka sakawa iyayen mu da alkhairi, Allah ka qarawa rayuwar su albarka da imani,Allah ka tabbatar da mu akan imani da ikhlasi,ashe halin da take ciki kenan? Duk farin ciki na na kawar da su a al'umma ya kau,rashin samun nagartattun iyaye, da tarbiyya mai kyau tabewa ne a cikin al'umma, shi ya sa ake samun masu shye shaye,masu fyade, masu yankan kai da tsafi,'yan fashi da makami, da dik wata lalacewa dai, rashin tarbiyya da samun tsayayyun iyaye a cikin al'umma musiba ne,Allah ka qaro mana shiriya"
"Ameeen Aaseeyah, lallai Sarah abar a tausaya mata ne, batai sa'a ba sam a rayuwa"
"Mahboob qarfin zuwa na wajen ku shine, Sarah ta roqe ni da na baka hakuri, da kai da Aaseeyah ku yafe mata,ta yi kuka sosai, ta yi nadama,ta roqi gafarar ku, ina fatan za ku yafe mata?"
Cikin hadin baki,suka furta,
"Na yafe mata,Allah ya yafe mana baki daya"
"Ameen,Allah kuma ya kare mu daga aikata sabon shi"
"Ameen"
"Ni zan wuce gida, hankalin Mama ya tashi tun a waya da ta ga ban koma gida a jiya ba,sai kuma in Allah y sake hada mu"
"Lallai duk sanda ka koma Abuja mama zata yi kewa, ko kuma in ka yi aure"
"Wannan tunanin ni kaina na sani cikin samuwa"
"Yah Aliyyu Mama's pet"
Dariya suka yi da maganar Aaseeyah.
Sallama suka yi, Aaseeyah da Mahboob suka raka shi har gate, ya shige motar shi ya tafi gida, Mahboob da Aaseeyah na komawa ciki, Ummee ta fita, ta kira Mahboob, har Aaseeyah ta bude baki ta ce b zai je ba sai ta tuna 'yan mutunci suke yanzu, dan kuwa har da dan abun kwadayi Ummee take aikawa Aaseeyahn.
Zumbura baki ta yi ta wuce, shi kuma ya bi Ummee,
"Almura, ai dama na san wannan yarinyar tuban muzuru tai, ina sane na kira ka, na tabbat ta so hana ka zuwa, se kace ita ce Zainabu,kaiii wannan yarinya Allah ya mata sauqin lamura, nan gaba fa in kuka tare ganin ka ma sai ya mana wuya a dangi"
Murmushi Mahboob ya yi kawai ya zauna a kujera, farfesun naman rago ta mishi, ya sha kayan hadi, sai tashin qamshi take,
"Zauna maza ka ci, Umaimah ma na aika masu nasu"
"Ummee bari na kai mu ci da Aaseeyah,ba ta iya cin komai ba tare da ta ajen ba nima"
"Uhumm ai sai dai in ba dangin Nufawa ba,sun gama da kai kaima da maitar tasu, cinye kurwa suke fa, ka duba ka ga yanda Subai'a ta cinye kurwa Ibraheeem,ba shi da magana sai ta ta, kai ma ka shiga sahu"
Dan bata fuska ya yi, sannan ya ce,
"Ummee wai sai yaushe za ki daina irin wannan abubuwan ne dan Allah, ita Mammee ta na son ki tsakani da Allah, duk sanda muka zauna yabon ki take, duk da a zaman da kuka yi ba abin yabawa, amma sai ta nemi abu ko guda daya ne ta yabe ki akai,ke kuma ba ki da aiki da ya wuce kiran ta mayya, ashe da Mammee mayya ce da gidan nan tun shekaru masu yawa kowa zai qare,me ye wai laifin ta? Mallake mijin ta da ta yi da kyawawan halaye? Mammee fa bata barin mijin ta daukar tsinke,ita ke yi masa komai,hatta da sanya takalmi da hula ita ke sanya masa,kin ko san Allah kadai ya san iya me take masa a daki,ga shi ta gwanance a iya sarrafa girki, bance ke baki gwanance ba,amma kullum sai ta dafa, sai ta ba mijin ta da yaran ta, ba ta qiwar girki,bata qiwar tsafta, ta yi wanka yau gobe ta qi yi, ah ah a rana sai ta yi wanka sama da biyu, ko kin san har yau Mammee bata daina yin irin abubuwan nan na gyran jiki ba? Wanda zaki ga mata na shafawa, na wasu awanni ko mintuna su je su wanke? Ummee meye laifin ta ne dan Allah"
Sunkuyar da kan ta qasa ta yi, cike da nadama da jin kunyar shi,
"Ba bu laifin da Subai'a ta min, ni mace ce me tsananin kishi, kuma na taso da hakan tun ina qarama, ban kuma samu mai tsawatar min ba har na kai ga minzalin aure aka aurar da ni, na taso ko a jikin Zainab na ga sabon abu sai raina ya baci, ko da kuwa tare aka siyo mana na lalata nawa sauran nata.
Abbun ku ya sha yunqurin yi min kishiya, saboda rashin kulawa da nake bashi, amma masifa da bala'ina sun hana shi, kuma gashi ban sauya halaye na ba,bashi da magana kullum sai ta nai koyi da Subai'a, na girme ta amma ta fini hankali da nutsuwa, da ire iren wadannan kalaman, shi ya sa ni kuma na ji a duniya banda maqiyya sama da ita."
"Subhanallahi, ai kuwa indai kika ajiye makaman tsanar Mammee ki ka kusance ta to fa za ki sake zama tauraruwa a idon Abbu, ko ba ki kula yanzu yanda Umaimah itama ta samu kan Noor ba? Duk koyarwar Mammee ce, in baki manta ba fa shi da ba ya son a danganta su duk da shi ya lalata rayuwar ta, amma yanzu saboda ya samu kulawar ta da soyayyar ta in kika je gidan su za ki rantse tunda suke ba su taba musayar yawu ba a baya, in ya yi fushi sai Umaimah ta tausasa masa zuciya, in ta yi fushi ya lallashe ta, baki ga yanda ya ke ririta ta ba, Mammee wannan shi ne fa amma ba wani maita, kyautatawa ne kawai, kuma an gina zuciya ne akn son me kyautata mata, da qin mai munana mata,dan haka Ummee dan Allah ki aje maganar maita a gefe, ku hada kan ku da Mammee,kowa fa da mijin ta ba kishiyoyi kuke ba"
"A dik gidan auren da kk ga ana samun matsala to ba a gina shi akan son Allah da manzon shi ba, ba kuma a gina shi akan soyayyar gaskiya ba,indai an gina shi da jigo me kyau, ma'aurata ba za su iya kwana daya ba cikin fushi da juna, a qalla awanni biyar sun musu yawa komai girman laifi, gidan da aka gina shi da tubali mai kyau ba su iya awa daya ke minti talatin suna fada da junan su, wannan shi ne dalilin da ya sa kike ganin kamar Mammee da Abee ba su taba fada ba, ko sun yi a nan take suke sasanta kan su"
"To Mahboob na maka alqawari da yardar Allah na daina duk wani abu da nake mara kyau, a yanzu haka sai na ji kamar an dauken wani dutse a raina me nauyin gaske, ashe sanyawa kan ka qin wani babbar cuta ce? Allah na gode maka da na samu waraka, yanzu ba sai gobe ba muje na bawa Subai'a hakuri"
"Ah ah Ummee, ni fa ba na cikin hakurin ku, ki je kawai ni kuma ki turon mata ta ta zo mu kwashi farfesun nan, ko ya kika ce?"
Kafadar shi ta dan doka da salon wasa,
"Dannema ashe dai farfesun na ran ka, to zauna na turo maka ita,bari na qaro maku spoon"
Ko da ta shiga bangaren Mammee ta tadda ta ta na shara,Aaseeyah na taya ta gyara wajen, ba wani datti amma sake qalqale wajen suke, saboda gabatowar yamma, ta tabbata ta na wannan hidimar ne domin mijin ta kar ya dawo ya tarar da datti.
Sallama ta yi ta sanar da Aaseeyah kiran Mahboob, cike da mamaki ta sanya hijabi ta tafi, Ummee ta jima a zaune ta na kame kame, ta kasa magana, Mammee kuwa kitchen ta nufa, ta dakko mata lemo ta zuba mata, ta hado mata da snaks,ta ajiye, gaishe ta Mammee ta yi, ita ma ta yi shiru, fuskar ta dauke da murmushi, ko ba komai ta fahimci wani abu na sauqin kai da nadama a idanun Ummee, to ba za ta bata kunya ba, har ta kasa magana, shi ne dalilin sake fuskar da ta yi.
"Wai ke Subai'a baki fushi ne? Ba kuma kya ramuwar gayya in an bata maki?"
"Subhanallahi, wa zan yi wa ramuwar gayya Maman Noor? Miji na? 'Diya ta? Yarana na gidannan gaba daya?Ko kuma ke da kike a matsayin yaya ta? Ba wanda ya bata raina a cikin ku ballantana har na riqe shi, ko na masa ramuwar gayya"
Hawaye ne suka gangaro a idanun Ummee, a duniya ba wadda ta tsana sama da Mammee, bayan bata mata komai ba, sai gashi ita a matsayin yaya ta dauke ta ma ba faccala ba,
"Dan Allah da son Annabin rahama Subai'a ki yafe min, ki yafe mana ni da 'yar uwa ta akan dik abinda muka maki, na cutarwa, mun zalince ki mun...."
Da sauri Mammee ta zauna kusa da Ummee, wani qamshi ne mai sanyi ya daki
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 41