karɓi wayar ta hau qorafi,
"Iyyyiii in ba dan an mai dani mara mahimmanci ba ace se kowa ya gama magana za a bani? To ni irin wannan rashin bani mahimmancin ne ke damuna yan....."
"Innohta kwantar da hankalin ki,indai waya ce yanzu muka fara, albashi na na farko zan sa a sai maki waya mu dinga ganin juna kullum"
"Alhamdulillahi,amma ba wayar nake so ba dai, kina ji ko...."
Nan Innoh ta zauna ta dinga rattab'a wa Mommy duk wani abu da take so wanda ta sani sarai ya fi karfin arziqin Mommy ko nawa kuwa za a bata a matsayin ta na sabuwar zuwa aikatau,sannan gashi ko albashin ma ba a yanke mata nawa za a bata ba, daɗin dad'awa bata ma san wanne irin aiki Mommyn zata yi ba a biya ta, hatta da Ɗan litin bai tambaye ta wanne kalar aiki zata fara yi ba, fatan su kawai da burin su bai wuce na ta cika musu burikan zuciyoyin su ba da duk kud'in da zata samu, cikin lissafe-lissafen kuwa ba a bar Ameerah a baya ba ita da Sule.
Dan kuwa Sule yace babbar waya yake so ta b'aro masa dal a leda saboda shima ya dinga ɗaukan hotuna mai kyau, dan kuwa yanzu a social media daga hoton ka ma ana iya gane wace iriyar waya kake amfani da ita.
Wayar Mommy ce ta fara nuna ba caji kafin su hakura suka yi sallama da juna, bayan ta yi musu alqawarin biyawa kowa buqatar shi da zarar ta samu kuɗi, qasa ta koma wajen su Billy nan ta samu har sun gama cin abincin sun koma wani parlour na daban, kwalabe ne masu arnen kyau da kofunan gilasai a gaban su suna zuba wani abu ja dake cikin kwalaben suna sha a hankali cikin yanga da k'warewa.
Ita dai ta san bata qoshi ba, yaqe haqora ta yi ta na kallon su, da sauri Hajiya K'waisa ta ajiye nata cup ɗin ta na wani fari da yarfa hannaye ta ce wa Billy,
"Billy jata can dan Allah ta ci ta qoshi kar ta yage ni"
Cike da dariya Billy ta ce,
"Kai Hajiyata wanne irin ta yage ki sai kace wata kura?"
"Ke Mommy ki ke ko wa? Dole ne fa ki koyi sarrafa leb'en ki da haqoran ki ta hanyar da zaki burge masu kallon ki ba wai ki dinga yaqe su yanda kike yi ki na firgita jama'a ba, bakin ki bai da munin da za a dinga magana akan shi a koda yaushe amma rashin iya sarrafa shi shine matsalar ki, nawane masu irin bakin ki maza ke nema ke har da shegun mata irin su Hajiya Badariyya? To ki sa kunnen ki da kyau ki saurare ni, idan har ki na so ki mori sabuwar rayuwar nan da kika shigo to ki kimtsa kan ki, ki dinga gyara bakin ki, ba koda yaushe bane zaki dinga sakin gandar leb'en shafatataaaa ki na yaqe haqori kamar zaki sari icce ba kin gane? Billy ku je can bana son hayaniya zamu huta da baby please"
"To Hajiyata yanda kika ce haka za a yi, kuma zan koya mata yanda zata yi ta gyara duk abinda ya dace ta gyara"
"Good ! Na san zaki iya bana jin ki ta nan wajen ai"
Direct dining table suka nufa Billy ta k'wala wa Ruby kira tace a kawo abinci da dikkan cokula da wuqaqen da ake amfani da su wajen cin abinci.
Bayan an kawo dik abinda ya dace a kawo ne Billy ta zauna ta dinga nuna wa Mommy yanda ake amfani da cokula da wuqaqen har ma da cokula masu yatsu babban da qaramin,hatta da kala-kalan kofuna na shan ruwa da lemo da giya duk sai da Billy ta yi wa Mommy bayanin yanda ake amfani da su, Mommy ta riqe wasu, wasu kuma bata riqe ba, na giya kuwa ko sake bi ta kan shi bata yi ba dan kuwa a cewar ta me zai haɗa ta da giya tana musulma? Cikin nuna k'ware wa da taqama Billy tace,
"Ai kuwa dole ki iya amfani da su Mommy idan har Babbar yarinyar ki ke so ki zama ba mai riqe wa Babbar yarinya jaka ba, domin kuwa wani wajen ma idan kin je giya ita za a baki a matsayin ruwan da za a tarbe ki da shi musamman idan kin yi dacen zuwa Abuja ko qasar waje,"
"Giya dai giya da muke jin ana cewa haramun ne shan ta Billy?"
"Mommy bana son abinda kike min fa? Haramun nawa ki ka aikata kafin ki zo nan? Ke har tsoron haramun kike yi dama? To bari ki ji na faɗa maki,idan zaki cire wannan tsoron ki cire idan baza ki cire ba kuma sai ki yi ta yi, ba inda ɗaukakar ki zata je zata b'are,"
Shiru Mommy tayi, kafin daga baya ta kai hannu zata yagi naman kazar da ke gaban ta, da sauri Billy ta sanya hannu ta dakatar da ita ta yi mata nuni da wuqa da cokali mai yatsu, b'ata rai Mommy ta yi tace,
"Ki wa Allah ki bari na ci na yau kaɗai,"
Murmushi Billy ta yi sannan ta kyale Mommy ta koma gefe ta dasa wayar ta tana yi wa Mommy video ba tare da Mommyn ta kula da hakan ba,gaba ɗaya ta maida hankalin ta kan cin kayan daɗin da ke gaban ta, hannu bibbiyu ta sanya tana cin abincin kamar tsohuwar mayunwaciya,lemo ta ɗauka ta kwankwad'e na cikin cup ɗin da aka zuba gaba ɗaya, ta na cire cup ɗin a baki ta saki wata muguwar gyatsa mai qarfin gaske, sannan ta kalli Billy wadda ta yi saurin kashe camera ɗin ta ta miqe ta na murmushi tace wa Mommy,
"To an ci an qoshi sai mu je ko?"
Murmushi Mommy ta yi sannan ta duqa zata fara tattara kwanikan da ta ci abincin da su da niyyar kai su kitchen Billy ta ce,
"Idan baki nuna wa masu aikin gidan nan sama ki ke da su ba to tabbas watarana sai Sallau ya aike ki, mu je za su tattara"
Kallon inda Zubaida ke tsaye Mommy tayi ta sakar mata murmushi, da sauri Zubaida ta b'ata rai ta ɗauke kan ta daga kallon Mommy ta hau tattare kayan wajen, mommy kuwa cikin ranta ta ke ayyana,
'Da alama idan na samu dama a gidan nan yarinyar nan zan fara kora, dan na ga ta tsane ni tinda na zo gidan nan take harara ta'
Sama suka wuce basu sake komawa wajen su Hajiya K'waisa ba da ke can ɗaya parlourn suna shan barasa da saurayin ta.
Suna shiga d'akin Mommy Billy ta buɗe wardrobe ɗin mommyn ta ga yanda Sallau ya jera mata kayan da suka siyo d'azu,murmushi ta yi sannan ta koma saman gadon Mommyn ta kwanta tana faɗin,
"Washhh Allah na na gaji,bari na huta"
Mommy ma zubewa ta yi a gefen ta suka kwanta, wayar su suka d'akko suka kunna data kowa ya shiga inda ya fi kauri, Billy direct TikTok account ɗin ta ta shiga, Mommy kuwa ta shiga WhatsApp ɗin ta, Messages ta gani suna ta riqe-riqen shiga wayarta sai ta juya ta na so ta tashi ta sanya caji,Billy na ganin haka ta nuna mata gefen gadon tace,
"Ba sai kin je ko ina ba, cajar ki kawai zaki d'akko ki jona,"
"A gaskiya Billy kuna jin daɗin ku, sai yanzu na ke ganin wauta ta ta qin biyo ki tun farko."
"Ai gaki yanzu kin biyo ni, lokaci bai qure maki ba ki maida hankali kema ki zama wata abar kwatance kamar wannan baiwar Allahn"
Da sauri mommy ta qarasa saka caji ta kwanta a kusa da Billy suna gogar jikin junan su, nan Billy ta dinga nuna wa Mommy manyan 'yan mata dake rayuwa a social media da kuma boyayyiyar rayuwa irin tasu ta 'yan bariki,mamakin irin dukiyar da matasan matan ke kashewa har ma da mazan ne ya sanya mommy yin shiruuuu ta na hango kan ta ta zama mai hamshaqin kuɗi irin su, ta tabbata ita iyayen ta ba za su qi ɗaukakar da zata samu ba ba kuma za su damu da sanin daga ina ta samo kud'in ta ba, dan haka jawo su zata yi a jiki da kyau su ci arziki su bar arziki a mazaunin sa.
Daga nan sai Billy ta qara shiga shafukan wasu zafafan mata da samari nan take Mommy ta sake mannewa da jikin Billy ta na kallon hotuna da videos tare da tambayar Billy,
"Yanzu wannan ma musulma ce? Ko dai arniya ce ne baku sani ba tun farko?"
Dariya Billy tayi sannan tace,
"Musulmace mana, Sunan ku ɗaya da ita amma ana kiran ta da Pretty H, kuɗi ne da ita dan ita ruwa biyu ce, ke watarana ma takan rikid'e ta zama ruwa uku, irin su ba qananan kuɗi suke samu ba, dan kuwa sai ta iya sai maki irin gidan nan sama da goma,"
Cikin zaro ido da nuna tsantsar kwad'ayin abun duniya Mommy tace,
"Dan Allah fa? Yanzu kawai dan tana matsayin ruwa biyu sai ta yi kuɗi haka? Ohhh dama nima iyaye na 'yan wata qasar ne da na samu kuɗi masu yawa"
Dariya sosai Billy tayi kafin tace,
"A gaskiya Mommy da sauran ki, ke yanzu wa ya ce maki ruwa biyu na haihuwar qasar waje ake nufi? Babu komai da sannu zaki gane yaren namu yanzu dai abinda ya fi mahimmanci shine kafin lokacin da za a yi maki zafafan hotunan da za a ɗora a sabon account ɗin ki na social media da za a buɗe miki dole ne ki gyara rayuwar ki, wannan sakin bakin da kike yi duk ki dena, bakin ki kadarar ki ce a hankali zan koya maki yanda zaki sarrafa shi ina fatan ba zaki yi min musu ba a dikkan abinda na sanya ki yi har ki k'ware?"
"Ni kam Billy me zai sanya ni yi miki musu? Ai na ji na bi ne a tsakanina dake, me son ka ne kaɗai zai jawo ka wajen harkar samu, ba zan gaji da yi miki godiya da fatan alkhairi ba Billisious 'Yar Sanata"
Dariya suka yi suka tafa sannan Billy ta shiga nuna mata followers ɗin ta da comments ɗin mutane akan shigar ta da yanda take sanya kaya masu tsada da hawa motoci masu numfashi.
"Yanzu na sake ganewa duk motocin nan da kaya da gida wasu na qarya neeee wasu kuma gaskiya ne,"
"Yauwaa 'yar gari, ashe kin gane, nan gaba ma zaki fi gane ya harkar take, tinda duk sanda ki ka samu had'ad'd'un gayu masu ji da nera suka fara huld'a da ke ba sai an ce maki nan wajen yana da kyau ba tsaya a cire maki hoto hajiyata"
Dariya suke ta yi kafin Billy ta dura wani shaqiyyin ashar ta tashi zaune tana duba wayar ta............
[09/08, 10:37 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA: HAERMEEBRAEH
PAGE 12
"Billy me ya faru kike zabga irin wannan ashar ɗin haka? Hotunan...."
"Kin ga Mommy ki kwanta ki yi bacci sai da safe zamu yi magana, kar kuma ki fito duk hayaniyar da zaki ji"
Cike da mamaki Mommy ke bin Billy da ta fita a hayyacin ta da kallo, Billy kuwa cikin tsananin ɓacin rai ta bar d'akin ta sauka qasa, kwance ta ga Hajiya K'waisa a jikin saurayin ta suna hirar su ta soyayya, sai shagwab'a take zubawa kamar bata da wata damuwa a duniya da ta wuce na ta faranta wa wannan kyakkyawan matashin rai.
Rasa ta inda zata fara nuna mata wannan hotunan Billy ta yi, da kyar ta samu natsuwa ta shige ta ta yi gyaran murya, a tare dikan su suka juyo suka bada hankalin su ga Billy, cikin murmushi da sakin baki irin na wanda ya sha barasa ya bugu Hajiya K'waisa ta kalli Billy tace,
"Laaafiyaa ki ka dawo ? Na zaci ma kun yi bacci ai duba da cewa yau kun gaji da yawa"
"Hajiya ko zaki iya tasowa ki ga wani abu yanzun nan? Ya na da mahimmanci ki gan shi yanzu yanzun nan,"
Da jin haka Hajiya K'waisa ta san tabbas wannan abun da Billy ke magana akai na da mahimmanci,dan haka sai ta tashi zaune da kyau ita da saurayin ta,ta yi wa Billy izinin ta isa gaban ta dan ta sanar da ita abinda take son sanar da itan, cikin ɗari-d'ari Billy ta isa gaban ta ta buɗe wayarta ta nuna mata hotunan da ta gani suna yawo a social Media,wata qara Hajiya K'waisa ta sanya tare da dukan table ɗin da ke gaban ta sannan ta ce,
"Ni Any za ta yi wa irin wannan cin amanar? Hotuna na da dana yarda da ita na aminta da ita ta ɗauke ni su zata baza wa duniya ta gani bayan ta yi min k'wacen fiancé d'ina ta bar qarqashi na? Lallai qarshen Any ya zo Billy, idan ban gama da yarinyar nan ba maganar mutane ta tabbata akai na uwata zina ta yi ta haife ni bani da uba,Allah ka tsinewa ranar da na san yarinyar nan, Allah ka tsinewa ranar da na jawo yarinyar nan a jiki na maida ita mutum har ta samu damar yaudara ta irin haka, Billy d'akko min makullin mota,"
Da sauri saurayin ta ya kama ta ya riqe gam a jikin shi yana lallashin ta,
"Baby calm down na ehhh ! Kar ki tada hankalin ki haka akan wannan abun, dan ta sanya tsofaffin hotunan ki a social media se me? Waye be san ki ba dama? Hakan ya rage maki masoya ne ko me? Kin san yanzu videos ɗin ta basa trending so take ki kula ta ki yi mata raddi ta yi going viral saboda ke ɗin shugaba ce kuma abar koyi ce a wajen qananan asshoshi irin ta,sannan ke kin san a kaff social media platforms ɗin nan ana ji da ke kin sani ko baby? To shiru ma magana ce ki kyale ta kar ki kula su, sannan yanzu idan kin je gidan ta duk abinda ya same ta ke za a zarga, ki kyale ta muna nan zata kawo kan ta da kan ta a lokacin ne ni da kai na zan taya ki salwantar da rayuwar ta"
Kuka sosai Hajiya K'waisa take yi ta na zage-zage, gashi Billy da saurayin ta Samuel sai danne ta da bata baki akan kar ta yi retaliating ta kyale maganar suke, kwalbar barasa ta buɗe ta d'aga sama ta kafa a bakin ta ta dinga kwankwad'a, bata ajiye ba sai da ta sha mai yawa, a nan Hajiya K'waisa ta gama koke-koken ta da zage-zagen ta ta yi bacci, Samuel da Billy ne suka tallabe ta suka kai ta d'akin ta suka kwantar,Sam yaso k'warai ya kwana da ita dan ɗebe mata kewa amma yana da tafiya a gaban shi, dama sallama yazo yi mata, kuɗi ya ajiye mata masu yawa in dollars ya yi gaba.
Ko ta kan kud'in Billy bata bi ba ta hau cire wa Hajiya K'waisa kayan jikin ta dan ta ji daɗin bacci, tunawa da gargad'in Samuel kafin ya tafi ne ya sanya Billy murmushi,
"Aikin banza wai lalle a mazaunai ni me zan yi da ita? Ai wannan sai kai dama, shashasha kawai"
Tsayawa ta yi ta qarewa Hajiyan tata kallo bayan ta cire mata makeup da gashin kanta, dariya ta tintsire da ita sannan ta ce,
"Waiiii sunan wani abu wai shi siddabaru in ji masu sihiri,"
Ajiye komai a inda ya dace ta yi sannan ta rufe d'akin bayan ta kashe mata fitila ta koma nata d'akin ta kwanta tana maida numfashi,
"Kaiiii ina buqatar wanka da ruwan d'umi mai kyau, kyawun ta yanda na gajin nan Man na nan, amma ba komai zamu haɗu anjima ta TikTok, wataqila ma yana can yana jira na,"
Wanka ta faɗa ta jima a cikin ruwan d'umi ta na gasa jikin ta dan har bacci ma ya fara ɗaukan ta ta buɗe idanun ta sannan ta fita daga kwamin wankan ta d'aura towel ta koma cikin d'aki,sai da ta tsane jikin ta sannan ta kunna laptop ɗin ta ta shiga TikTok ta danna Kiran Man ta tarar yana jiran ta kamar yanda ta yi zato.
A gaban shi ta dinga shafa mai ta na juyi shi kuwa yana daga can gefe ya na screen recording ɗin video ɗin da suke yi, ganin hirar tasu ta qazanta ne ya sanya ni rufe musu qofa na koma d'akin Mommy,ina shiga na tarar da ita ta baje a gado ta na ta neman inda za ta ga wannan hoton da ta fara gani a wayar Mommy, hoton ya yi mata kama da ta san fuskar amma ta rasa a ina ta san fuskar.
Duk duban ta bata gano inda zata ga wannan hoton ba, dan kuwa ita bata TikTok datar da take sanyawa qarama ce watarana ma da wannan App ɗin take amfani wanda ake kira da d'an mukulli wato free data da ita take WhatsApp, dan haka gajiya ta yi da bincike a Facebook ta kashe data ta saki wata hamma mai tsaho ta na tuna sanda Billy ke yi mata albishir ɗin gobe za su je a sauya mata sabuwar waya, sannan ta fara lumshe ido ta kwanta.
Cikin zuciyar ta take ayyana,
'Ban fa yi sallah ba,anya ba zan daure na tashi na yi sallah ba yanzu?.....kai bari na bari da asuba na haɗe su yanzu bacci nake ji, naga ma tunda na zo ba wanda na ga ya kai goshin shi qasa a gidan nan mutuwar yawa kuwa Kaka ce'
Sake muskutawa ta yi ta kwanta da kyau ta ja bargo saboda sanyin AC dake ratsa ta, a haka Mommy ta kwanta ba tare da ta rama sallolin dake kan ta ba,ta bar su sai gobe ta yi su dika da asuba.
A can d'akin Billy kuwa bata samu kwantawa bacci ba sai qarfe uku na dare, dan kuwa bayan hira da suka sha da Man transfer na kuɗi masu yawa ya yi mata, daga baya ta yi qarar account ɗin Any domin a rufe shi sannan ta kwanta bacci ba tare da ta tuna sallah ba balle ta yi ta.
************
Washegari da safe ba wanda ya farka a cikin mutanen nan uku da asuba balle har a yi maganar sallar asuba ɗin, mommy ce ma ta farka qarfe goma na safe ta yi wanka ta wanke bakin ta sannan ta yi alwala ta rama sallolin ta, wanda dika raka'a biyu ta dinga yi wai qasaru take yi, sannan daga qarshe ta yi asubar wannan ranar ta tashi, Hajiya K'waisa kuwa da matsanancin ciwon kai ta tashi saboda giyar da ta kwankwad'a a daren jiyan,dan haka Sallau ya yi mata had'in hangover ya kai mata ta sha ta na yatsina kamar ta na shan magani, daga qarshe ta tashi ta shiga wanka ta gama ta fito ta yi shafe shafen ta da tsara kwalliya kamar ba abinda ya faru a daren jiyan.
A d'akin ta ta yi breakfast sannan ta ɗauki makullin motar ta ta fita ba tare da ta sanar da kowa inda ta tafi ba, tinda Mommy ta idar da sallah ta ke hamma dan kuwa yunwa take ji sosai,tunani ta fara yi shin kayan jiya zata mayar jikin ta tunda basu yi datti ba kuma sababbi ne, ko wasu zata saka a jikin ta, ko kuma a cikin nata nada da tazo da su zata saka ta fita cin abinci?
Rasa wanne zata sanya ta yi kafin hankalin ta ya ɗauku wajen wata riga kalar rawaya nan take ta ɗauka ta sanya ta a jikin ta,dan kuwa rigar bata da nauyi gata mai kyau da ɗaukan hankali,ta na sanyawa kuwa rigar ta zauna das a jikin ta kamar an auna ta, ga kalar ta bi fatar jikin ta ta yi kyau, kallon kanta a qaton madubin da ke gabanta tayi,nan take ta yi juyi sannan ta kalli gashin dokin da aka haɗe da nata ta ga yanda ya kwanta a kanta kamar asalin nata,murmushi ta yi ta maida leb'unan ta ciki ta tsuke su,a hankali ta sake su sannan ta qara gyara su ta busowa kan ta sumba, ta na nan tana shiririta har sha biyu da mintuna biyar suka wuce, murd'a qofar d'akin ta aka yi aka shiga, Billy ta gani sanye da guntun wando da guntuwar riga kan ta sanye da hula irin wadda ake sakawa idan an sanya gashin doki,zama tayi a saman gadon Mommyn ta na qarewa halittar mommyn kallo da kyau,cikin ranta take yaba kalar fatar Mommy da kyawun dirin ta, bakin ta ta kalla ta ga yanda take wani tsuke shi tana yanga,murmushi Billy tayi tace,
"Ko ke fa, haka kawai da ki dinga wani sakin leb'e kamar ganda, mu je mu karya, na ga Hajiyata ma ta fita da alama asibiti zata je,"
Tashi tayi ta yi gaba Mommy na biye da ita, har sun kusan sauka daga bene Mommy tace,
"Hajiyan bata da lafiya ne da zata je ganin likita?"
"Ba abinda ya shafe ki bane, yanzu dai ki zo mu karya muna da abubuwan yi da yawa, dan ma Allah yasa ki na son wannan harkar a ran ki kuma dama kina da sha'awar harkar hutu samun dama ne baki yi ba, sai sauqaqa min aiki na kike yi,"
"Habaa Billisious 'Yar Sanata, waye baya son hutu? Ai duk wanda yace maki baya son hutu a rayuwar nan karya yake yi ko wanene shi, kawai dai ya dangata da hanyar da mutum ya zab'a ya huta."
"Hakane kema kin ce wani abu....Zubaida ba zaki kawo mana abincin bane ? Ko sai na zo na ɗauka da kai na ne?"
Cikin bada umarni da b'acin rai Billy ke magana, wanda hakan ya sanya Mommy sake gyara zaman ta, dan kuwa bata son ganin wannan zubaidar kallon da take yi mata na sa ta ji ta a muzance kuma a qasqance.
Cikin haɗe girar sama da ta qasa Zubaida ta shiga ɗauke da abincin su, ta na ajiyewa ta juya ta ci gaba da d'akko sauran, saida ta gama ne ta hau zuba musu, cikin ladabi ta kalli Billy tace,
"Ki yi hakuri Aunty na ga baku tashi da wuri bane shi yasa ban kawo ba gudun kar ya yi sanyi tunda baki son abinci da sanyi"
Hannu kawai Billy ta d'aga mata, sannan Zubaida ta bar wajen, Mommy ce ta saki murmushi bisa hango kanta da tayi ta tana zuba nata mulkin a gidan.
A haka suka ci abincin su suka tashi sannan suka koma sama, Billy ta shirya suka fita siyan waya da ta yi wa Mommy alqawari, ko da suka shiga shagon sai Mommy ta ga Billy suna hira da mai shagon kamar wasu qawayen juna anan ta kula da matar ta qi yarda yaran shagon su karb'i kuɗi wajen Billy,bayan sun gama da wajen wayar ne za su tafi matar tace,
" 'Yar sanata wannan babban kifin fa?"
"Qawata ce,sai anjima bari mu je muna da abubuwan yi sosai"
"Na ga alama"
A hanzarce suka bar shagon har sai da mommy ta tambaye ta wacece wannan ɗin,
"Itama ɗaya ce daga matan da Hajiyata ta taimaka wa a lokacin da suke tsananin buqatar taimako, daga baya ta samu wani saurayi ɗan siyasa mai kud'in gaske yake shagwab'a ta da nera, yanzu haka tana da manyan shaguna na saida kayayyaki kala-kala guda huɗu a garin nan ɗaya a Abuja, wannan wayar ma kyauta ta baki gashi nan sai a yarda wannan akwalar,"
Cike da zumud'i Mommy ta karb'i k'walin tana duba wayar tare da qudirin idan sun je gida a yau zata buɗe duk wani social media da a baya bata samu damar bud'ewa ba saboda rashin isasshiyar data,juyawa ta yi ta kalli Billy da ke tuqi cikin k'warewa tace,
"Amma me yasa naga kina sauri baki so ki gabatar dani sosai a wajen ta"
"Duba da abinda ya faru a daren jiya kaɗai ya isa ya sa ki gane a bariki baka yarda da kowa, kanka kaɗai ka sani a duk inda ka shiga"
Shiru mommy tayi kafin tace,
"Yauwaa dama ina so na tambaye ki game da abinda ya faru jiya, hoton wa...."
"Dan Allah tambayoyin sun isa haka Mommy,ko dai barin wannan harkar zaki yi ne ki fara aikin jarida?"
Tsuke baki Mommy tayi bata sake cewa komai ba amma fa zuciyar ta cike take da tambayoyi masu tarin yawa.
Ko da suka isa gida sun tarar da gidan shiru kamar babu kowa, ba tare da tunanin komai ba Sallau na buɗe musu qofar shiga gidan suka shiga ciki,Mommy na sanya qafar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 70